gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading FARASHIN MUTUNCINA Gwagwarmayar Mutunci By Mom Islam Chapter 2 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na kyarma tace "dan Allah kayi haƙuri wlhi tunda nake a duniya ban taɓa ganinsa ba sai anan gidan naku"

Ƙarasowa yayi ya har inda take tsaye, kana ya janyota tare da hijabinta suka iso inda washing machine ɗin yake, kana ya hankaɗata saura kaɗan ta faɗi, yace "zan kwaso miki kayan yanzu daƙiƙiya kawai, yanzu haka ba boxer da singlet ɗin ma sai kice baki sansu ba"

Wata haɗaɗiyar ƙofa ya ɓude ta gilashi, kana ya kutsa kai ciki, daga inda Batool take a tsaye tana jiyo ƙamshin turaren dake tashi a cikin ƙayataccen ɗakin,

Fitowa Farhan yayi, hannunsa riƙe da kaya yana isowa gurinta ya watsa mata su, yana jan tsaki kana ya wuce parlon Mahaifiyarsa ya sake kwanciya bayan ya ɗauki remote,

Batool ta durƙusa ƙasa tare da fara kwashe kayan, gajerun wanduna ne kala biyar, kowanne sabo ne dan ita a ganinta babu datti ko ɗaya a tare dasu, to Meye ma zata wanke,

Ai bai gwada mata ma inda zatayi amfani da washing machine ɗin ba ya koma ɗaki,

Gabanta ya shiga faɗuwa tsananin tsoro da fargabar zuwa tambayarsa ya ɗarsu a zuciyarta,

Tana tsaye a rungume da Unders dinsa ƙirjinta na tsananta bugawa, wata Budurwar yarinya ta shigo, dan zata iya kaiwa shekaru sha takwas, ta girme wa Batool da shekaru uku kenan,

Cikin fara'a ta ƙaraso tana cikin shiga ta alfarma dan ba ƙaramin kyau tayi ba, iya shigar jikinta kaɗai ya isa ya tabbatar maka da yarinyar ba daga gidan talakawa ta fito ba,

Sallama tayi lokacin da ta ƙarasa takowa zuwa inda Batool take,

Sai yanzu ma ta lura ashe a mota tazo, ita da kanta ta tuƙo kanta,

Batool kam tasha mamaki, duba da ƙarancin shekarun Budurwar,

Amsa sallamar Batool tayi, bakinta na motsawa,

Budurwar tace "dan Allah Momy na ciki?"

"Bata nan taje kasuwa amma ta kusa dawowa"

Batool ta faɗa tare da sake cewa "dan Allah ki nunamin inda zan kunna wannan injin wankin"

Budurwar ta taho gurin injin ta kunnawa Batool inda zatayi,

Kasancewarta mai saurin riƙe abu har ta gane, tana shirin juyawa taji Muryar Farhan yana waya,

Da gudu ta faɗa cikin parlon tare da faɗawa jikinsa tana sakin dariyar farin cikin ganinsa tace "oyoyo bro nayi farincikin ganinka"

Ɗan janyeta yayi a jikinsa kafin yace "me kikazo yi Safna?"

"Gurin Momy nazo ko akwai matsala ne?"

"Noo babu kawai dai na tambayeki ne, amma har yanzu kina nan da wannan rawar kan naki ko?"

Wayarta ta Ciro ta ɗan mannu da Farhan kana tayi musu selfie, tana murmishi,

A gurin ta ɗora a status har TikTok, nan da nan ƙawayenta suka fara surutu kowanne na zuzuta kyawu irin na Farhan, itako daɗi takeji wai a dole sansa takeyi.

Bayan Batool ta gama wankin bata san inda zata shanya ba, dan haka ta shigo parlon dan ta tambaye shi,

Farhan na ganin Batool ta shigo ya wani gimtse fuska, babu walwalah ko kaɗan yace "ke me ya shigo dake?"

Kanta a ƙasa cikin sanyin murya Batool tace "dama ina so in tambayeka inda za'a shanya maka kayanne?"

Safna ta kalli Batool kafin tace "Bro wannan kuma wacece naga kamar Village girl?"

Farhan yace "wai ƴar aiki Momy ta samo.."

Batool tace "iko sai Allah gata kyakkyawa, ke zonnan"

Batool ta taho gaban Safna kana tace "gani"

"Ɗibi takalmana ki gogemin ƙura sukayi karki sakamin ruwa, amma ki bari ki gama shanyewa bro kayan"

Cikin bin umarnin maganar Safna Batool ta wuce ta duba inda zatayi shanya bata gani ba, kuma bai ce mata ga inda zata shanya ba,

Kawai ta yanke shawarar shanyawa a saman ƙarfen lilo tunda babu ƙura a jikinsa, kana ta dawo bakin ƙofa ta fara goge takalman Safna, bayan ta gama ta nemi guri a compound ɗin ya zauna saman wani dogon benci,

Duk kewarsu Mama yabi ya dameta, tun yanzu ta fara tunanin anya zata iya yin aikin nan kuwa, saboda wulaƙancin Farhan ɗin yayi yawa, ga Mahaifiyarsa mutuniyar kirki shikam ko kaɗan bashi da tausayi,

Tana zaune a gurin har Farhan ɗin ya fito shi da Safna, idanunsa ne suka sauka akan kayansa da ta shanya a saman lilo, wani irin baƙinciki yaji ya mamaye masa zuciya, ya ƙaraso inda Batool take, watsa mata yatsunsa biyar a saman kumatunta yayi, zafin marin da yayi mata ya shigeta sosai, hawaye na zuba a saman kumatunta a ido ɗaya ta sunkuyar da kanta hannunta na dafe da gurin da ya mareta,

"Tashi ki kwashe ki sake wankewa wannan ɗakin da yake kallon nan zaki shiga ki shanya, bayan kin shanyamin kaya akan datti, kin shanya a rana kinada hankali kuwa?"

Safna ta taɓe baki kafin tace "kaima in banda abinka bro ina ɗan kauye ina hankali"

Ƙarar shigowar mota sukaji, wanda yasa suka tsaya daga tafiyar da suka ci gaba dayi, cikin sauri Batool ta kawar da kanta tare da share hawayen da ya kwaranyo mata a idanu, dan bata son Momy ta fahimci komai,

Bayan drivern yayi parking, ta buɗe murfin motar ta fito, tare da cewa "oyoyo my Daughterna.."

Hajiya Suhaima tayi maganar tana ware mata hannayenta,

Tsakaninsu babu nisa safna ta karasa da sauri ta rungume Hajiya Suhaima, tana cewa "Momy nayi missing ɗinki sosai amma yanzu ai muna tare tunda na kammala karatu"

Hajiya Suhaima tace "Masha Allah gaskiya naji daɗi, yanzu kika shigo ne?"

Hajiya Suhaima ta tambayeta suna ci gaba da tafiya har suka iso ƙofar parlor,

Shima Farhan ɗin bin bayan mahaifiyar tasa yayi,

Suka zazzauna, Momy tace "Batool ta tafi ne ko tana nan?"

Farhan yace "wacece Batool ni ban ganta ba"

Momy tace "ƴar aiki mana"

"Oh eh tana nan ai kin wuceta a compound"

Momy tace "Safna kiramin ita zan sata aiki ne"

Safna ta turo baki cikin shogoɓa tace "Momy wannan yarinyar gabaki ɗayanta problems ce"

Hajiya Suhaima bata sake magana ba, ta miƙe ta isa inda Batool ɗin take zaune, tace "Batool me kikeyi anan ga rana ki dawo parlor mana"

Jiki a sanyaye ta fara tahowa har ta iso parlon, sai dai a gurin carpet ɗin da ake ɗora ƙafa ta tsaya, kasancewar Hajiya Suhaima ta wuce bedroom ɗinta,

Bata sonta haɗa idanu da Farhan ko Safna tunda ta gano itama Safnar ba ƙanwar lasa bace kamar inda tayi tunani,

Tana tsaye anan gurin har ma tsawon wani lokaci, Farhan ya daka mata tsawa kafin yace "ke Village girl tashi a bakin ƙofa kiyi gaggawar fita Bama buƙatarki"

Batool na jiyo maganar Safna tana ce masa wai Batool ɗin na tsamin datti,

Sosai maganar tayiwa Batool ciwo, tace "talaka ya shiga uku..."

Mom Islam 🍷
*FARASHIN MUTUNCINA*
(Romantic story)
💋💋💋💋

Mom Islam

Page 13-14

Farhan yace "kema kika tsaya kusa da ita da har kika jiyo tsamin da take yi,

Tana tsaye a waje, ta yi forwarding hannayenta taji Hajiya Suhaima ta ƙwala mata kira,
Kamar mai ciwon ƙafafu haka ta shigo kanta a ƙasa ba tare da ta kalli inda Safna da Farhan ke zaune ba, kai tsaye inda taji kiran ta wuce,

A kitchen ta samu Hajiya Suhaima ta zuzzuba cin-cin da meatpay a wani haɗaɗen tray, tace mata "ta ɗauka ta kaiwa Farhan da Safna"

Batool kam ƙirjinta ne ya bada rass bata ƙaunar ma taji sunansa, bata son yiwa Hajiyar musu kokuma ta gano wani abun, dan haka ta ɗauko plate ɗin da hannu biyu, kana ta fara tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki,

Sannu a hankali ta dinga takawa, a tsorace har ta iso gurin table ɗin dake gabansu, ta ajiye tare da cewa "Hajiya ce tace a kawo muku"

Farhan ya kirata, dan har ta fara tafiya zata koma kitchen ɗin ta dawo da baya, ɗaga plate ɗaya yayi wanda ke gabansa ya juye mata a jikinta, kafin yace "mayunwaciya kawai, wa zaici abinda ya fito daga hannunki?"

Ɗan sunkuyar dakai tayi ta fara kwashewa, bata gama kwashe wannan ba, Safna ta sake juyo mata wani a jikinta, tare da cewa "Momy ta kawo muku masifa gaskiya, nifa bana ƙaunar ƙazaman ƴan aikin nan, jibi dai ita wannan riga daban zani daban ɗankwalin ma daban, su kansu kayan jikinta abin ƙyama ne"

Ran Batool ya ɓaci sosai, sai dai babu inda ta iya da faɗan da yafi ƙarfinta, dan sai su haɗu suyi mata duka, kafin Hajiya tazo cetonta ai ta jigata,

Miƙewa tayi hannunta riƙe da plate ɗin a karo na biyu, ta koma kitchen dashi,

Hajiya Suhaima na ganinta tace "baki kai musu bane?"

"Nakai wai bazasu ci ba"

Batool ta faɗa a taƙaice,

Hajiya Suhaima tace "babu damuwa, ɗibi wanda zaki iya cinyewa ki ajiyemin ragowar"

Iya meatpay ɗaya ta ɗauka, hannunta na kyarma, Hajiya Suhaima ta ɗauko leda ta ɗibar mata kana tace "aiki zamuyi yanzu, jibi zan wuce Dubai, wannan tumatur ɗin a blanda za'a markaɗashi, sai wannan pepper da onion ɗinnan suma markaɗasu za ayi idan an gama sai a tafasasu ruwan ya ƙafe, kana zamu soya kaji kamar guda goma, ganin girman kajin yasa Batool zuba musu idanu "tabb yaushe rabonta da cin nama bare kifi, mutum ya samu ma ya samu abincin da zaici ya ƙoshi"

Koda Hajiya Suhaima tace mata ta fara markaden tace bata iya amfani da blanda ba, dole dai ta koya mata duk inda zatayi, aiko tanada fahimta ta zauna a saman ƴar kujera sai da ta markaɗesu tass kowanne tasa a cikin tukunya pepper da onion ne ya haɗesu guri ɗaya,

Tana miƙawa Hajiya Suhaima tana ɗorawa akan electric stove har ta gama taje sink ta kunna pampo ta wanke blandar kana ta kife,

Kajin a fige suke, kuma an yayyankasu tsaf, kawai sake wankewa Batool tayi aka sa a tukunya da kayan haɗi, aiko sai da sukaci babbar tukunya dan kajin manya manya ne bana Hausa bane,

Bayan sun gama dahuwa aka tsame aka tittila mangyaɗa kamar ruwa a wani babban kaskon suya,

Batool ce ta fara soyawa Hajiya Suhaima kuma tana baza dankalin turawa a wani babban basket,

Batool ta ɗauki tsawon lokaci kafin ta gama suyar, kana tace "Hajiya na gama, zanyi sallah"

"Okay je kiyi lokaci kam ya tafi sai kizo in sallameki kinga har ƙarfe huɗu tayi"

"To" tace tare da fitowa, sai kuma ta koma kitchen ɗin tace "Hajiya banɗaki fa?"

"Jeki parlor yana nan"

Ta wuce parlor zuciyarta na cike da tsoro haɗi da fargaba, sai dai duka basa nan a parlon dan haka ta ɗan saki jiki, tayi alwalar, bayan ta fito daga toilet ɗin ta hau saman carpet ɗin parlor tayi sallahar, hamdala tayi da taji Hajiya Suhaima tace zata sallameta ta tafi gida,

Jin kiran Hajiya Suhaima yasa ta amsa bayan ta idar da sallolin kana ta wuce kitchen ɗin lokacin ta gama ragowar aiyukan ta gyara kitchen ɗin,
"Batool yau zaki tafi gida amma zuwa gobe idan kinzo kwana zaki dingayi dan haka mukayi da mahaifiyarki"

Batayi mata musu ba, tayi mata sallama kana ta fito parlor,

Sake kiranta tayi tace "ta ɗauki cin-cin ɗinta ta bata wata baƙar leda wacce ta saka naman kaza manya manya a ciki, da kuma soyayyen dankalin turawa"

Batool tayi mata Godiya, dan ba ƙaramin yabawa da halin kirki irin na Hajiya Suhaima Batool tayi ba,

Ƙarfe huɗu da mintuna ta fito daga gidan, tana tafe tana farincikin yau su mama da anty Maryam zasuci nama da dankalin turawa,

Tsabar zumuɗi har da ƙarasawa da gudu saboda ta isa gida da wuri,
Tana isowa ƙofar gidansu ta zare idanun, duba da ganin dandazon jama'a da tayi sun taru sai hayaniya akeyi, kutsawa ta dingayi tana wucewa har ta shiga ciki,
Mama ta samu zaune a saman kujera ƴar tsuguno tayi uban tagumi hawaye na bin kumatunta, anty Maryam kuma na masifa tana cewa "ai ba mune muka ciba, shi da yaci yabar gari shi zaku je ku nemo kuma sai Allah ya saka mana"
Mama ta ɗaga mata hannu cikin Muryar kuka tace "Maryam kar in sake jin muryarki wlhi idan har na sake jin muryarki sai na ci mutuncinki, koba komai babu sa'anki a cikinsu dan haka ki kiyaye bakinki"
Wani daga cikinsu yace "idan har an amince zan nemi auren ƴarsa a madadin kuɗina idan kuma ba haka ba wlhi yau ɗinnan idan ba'a bani kuɗina ba sai na yi muku wulaƙanci da tozarci wanda kare ma bazai ci ba"
Mama da sai yanzu ta samu bakin magana, ta miƙe tsaye, rai a ɓace tace "auren biyan bashi kake nufi, to badai da ƴata ba, kaje can ka nemi da wacce zakayi"
Mutane suka fara cecekuce suna zugashi wai tunda mama tayi taurin kai kawai ya tashesu a gidan sai aga inda zasu zauna,
Aiko ya zugu sosai ma, dan a take a gurin yace "ya basu nan da anjima idan har basu tashi sun bar masa gida ba da hukuma zai zo a fitar dasu ta ƙarfi kuma a wulaƙance,
Yana gama faɗar haka ya wuce yabar gurin,
Mutanen dake biye dashi suma suka bi bayansa,
Batool tace "wannan tsohon mutumin waye zai aure shi, shi bai nemi dai-dai shiba?"
Mama ta fashe da kuka, tana cewa "mahaifinku ya jefamu a cikin masifa, ina shi ina cin bashin kuɗi har Naira miliyan ɗaya, dame zai biya da wacce sana'ar zai biya, na ajiye dubu goma ya kwashe to ina yakai wannan kuɗin, a iya sanina harda yau shekararsa biyar kenan baya bani kuɗin cefane, sai Maryam taje tayi tallar shinkafa wacce nake karɓota bashi da miya suma suka bashi nake karɓowa, sau nawa iyayena suna bani jari ina cinyewa..?
Mom Islam 🍷

*FARASHIN MUTUNCINA*
(Romantic story)
💋💋💋💋

Mom Islam

Page 15-16

Mama ta ƙarashe maganar tana kuka, Batool tace "mama wannan mutumin da yake cewa zai auri anty Maryam tsoho nefa"

Suna cikin magana sukaji ana ƙwanƙwasa ƙofa, mama ta dauki Mayafi ta je ƙofar gida, sai dai cikin rashin tsammani idanunta suka sauka akan jami'an tsaro da suka zo cikin fuskar da babu walwalah,

Kafin mama tayi magana ɗaya daga cikin jami'an guda uku, yace "an kawo mana ƙarar mijinki tare dake, babu wani dogon bayani ku tattara kayan ku kubar masa gidansa tunda ba gidan gado bane"

Wanda yakai ƙarar yana tsaye yana saurarar abinda mama zata ce,

Ɗan kawar da kai gefe mama tayi, nan fa ta lula duniyar tunani, idan har suka fita daga gidannan ina zasuje waye suke dashi da zai basu gurin zama, dan haka kawai tace "na amince ka auri Maryam ɗin"

Wanda ya kawo ƙarar ya washe jajayen haƙoransa bakinsa a cike da goro yace "Masha Allah, kokefa da kin amince tun farko babu wanda zai kawo miki wani jam'i gidanki,

Juyawa sukayi, Mama na tsaye idanunta na fitar da hawaye, Batool da ta biyota a baya ba tare da ta sani ba, tafi kowa kuka, dan haka ta koma ciki tana kuka mai sauti.

Da ganin Batool na gunjin kuka yasa Maryam janyota jikinta tana ce mata tayi shiru basu isa suyi musu abinda Ubangiji beyi musu ba,

Mama ma ta shigo idanunsa na zubar hawaye, cikin sanyin murya wacce ta fara dishewa da kuka tace "dan Allah Maryam haƙiƙa na tafka babban kuskure wanda nasani zaki kirani da azzaluma sai dai hakan shine mafita a garemu dan Allah Maryam ki gafarceni"

Cikin rashin fahimta Maryam tace "dan Allah Mama karki sake cewa zan kiraki da wannan sunan dan Allah ki daina kuka ni baki aikata min komai ba, mama"

Mama tace "tabbas nice na aikata miki komai saboda na bawa Alhaji Atiku ke a matsayin bashin da mahaifinku yaci, idan ba haka ba bansan inda zamu mu zauna ba nida Batool"

Ware idanunta tayi tare da sakin kuka itama, tace "mama akan me..?"

Sai kuma ta share hawayenta, saboda Maryam yarinya ce mai hankali da hangen nesa cikin kwantarwa da mama hankali tace "mama nayi miki alƙawarin zan zauna lafiya kuma bana son inga kina kuka dan Allah mama ki share hawayenki baki zalunceni ba, Ubangiji ya fimu sanin dai-dai,

Da wannan maganar ta Maryam yasa Mama ta ɗanyi shiru, gashi yamma tayi basu da kuɗin cefane,

Nama dasu cin-cin ɗin da Batool tazo dashi ta bawa mama, daga ƙarshe dai da shine sukayi abincin dare.

Washe gari, bayan sunyi sallahar Asbha, babu wanda ya koma barci, kowanne ya kama aikinsa, lokacin mama na daki tana azkar, Batool tayi wanke-wanke da wanke banɗaki da gyara ɗakinsu,

Maryam ta share tsakar gida ta haɗa wuta, indomie ta dafa musu da iya magin cikinta dan babu kuɗin cefanen shine baba ya gama kwashewa,

Bayan ta gama dafawa ta saka musu ruwan wanka, ta zubawa Batool takai nata ɗaki mama ma takai mata ɗaki,

Batool ce ta fara wanka bayan taci abincin, kana ta shirya cikin shirin tafiya gidan aiki, sabuwar atamfar da mama tayi mata ta sallahr da ta wuce ita ta saka da sabon hijabi, gudun yauma kar taje gidan Hajiya Suhaima su Safna da Farhan suce wari takeyi,

Ta wanke slifas ɗin takalminta tsaf, ta shiga ta gaishe da mama kana tace "zata wuce gurin aiki"

Mama tasa mata albarka kana tace "ta gaishe mata da Hajiya Suhaima" tace to kana ta yiwa Maryam sallama sannan ta wuce..
Sauri ta dinga yi a hanyarta ta zuwa gidan Hajiya Suhaima har ta isa, nocking tayi mai gadi ya buɗe mata, ta gaishesa kana ta shige,
Sannu a hankali yanzu take tafiya har ta iso ƙofar parlon, sai da tayi sallama suka amsa kana Hajiya Suhaima tace ta shigo,
Cikin Nutsuwa ta shigo tare da durƙusawa a ƙasa saman tiles kana tace "Hajiya Barka da safiya"
Idanunta ne suka sauka kan Dady da yake kallonta sosai, tace "alhji Barka da safiya"
Dady ya amsa murya a sake, kana yace "wannan itace ƴar aikin da kike bani labari?"
Hajiya Suhaima tace "eh itace, sunanta Batool"
Alhjin yace Masha Allah,
Bata san Farhan yana parlon ba, dan haka bata gaishe sa ba,

Tashi zaune yayi, tare da cire eyepiece ɗin dake maƙale a kunnensa kana ya kalli Batool yaja dogon tsaki kafin yace "Momy a duk ƴan aikin da kike ɗibowa babu ƙazama irin wannan yarinyar"
Alhaji ya kallesa kana yace "Farhan are you serious kuwa, ɗan adam yanada daraja Meye aibun wannan yarinyar?"
"Talauci da ƙauyanci mana Dad "
Alhaji ya girgiza kai bai ce komai ba ya tashi ya shige bedroom ɗinsa,
Hajiya Suhaima ta gyara zamanta tare da yiwa Batool nuni da ta zauna a saman kujera,
Batool ta miƙe zata zauna, Farhan ya dakatar da ita tare da cewa "kull karki sake ki zauna dan wllhi idan ta zauna daga yau ina iya daina shigowa parlonnan"
Dole dai anan inda take ta zauna, Hajiya Suhaima tace "Son kabi duniya a hankali"
Acan bedroom ɗin Alhaji hankalinsa ya karkata ga Batool, tabbas bawai yana yi mata kallon tausayi bane, kallo ne mai cike da tsananin so da ƙauna, sai dai shekarunsa sunyi mugun ja sosai, dan ya tsufa kuma yanada farin gemu sai dai yanayin jikinsa baya nuni da irin tsufannan da mutum zai ranƙwafa ko ya dinga tafiya da sanda,
Ya daɗe yana tunanin ta inda zai yi ya samu damar yin magana da Batool, sai dai tunowa da yayi Hajiya Suhaima zatayi tafiya gobe yasa shi cewa "alhmdulilah kana ya fito parlor hannunsa riƙe da key car"
"Zan fita"
Ya cewa Hajiya Suhaima tare da kiranta hanyar waje,
Batoo tayi tunanin Alhajin zai saka a koreta sai taga da Hajiyar ta dawo bata ce mata komai ba,
Tana nan dai a zaune, Farhan kuwa sai jan zaki yake lokaci zuwa lokaci, tashi tayi ta shiga kitchen, taga akwai kayan da ba'a wanke na su kwanuka da sauransu,
Fara wankewa tayi kana ta share kitchen ɗin Hajiya Suhaima ta shigo tana yi mata sannu,
Kana tace "yau baza'ayi girki ba, restaurant zamu tafi"
"Toh" kawai Batool tace, amma a zuciyarta tayi mamakin akwai abinci kala-kala ace sai a hotel zasuci abinci taɓɓ kashe kuɗi a gurinsu babu wuya, wasu na nema wasu na kashewa basa ko tunani,
Driving alhji yakeyi yana sake tuno fuskar Batool da ɗan ƙaramin bakinta,
Murmishi yayi, kafin yace "inhar ina raye babu abinda zai hana ban mallaki yarinyar nan ba a matsayin matata, wayoo rabona da soyayya tun wacce mukayi da Suhaima...!

Akwai zazzafar cakwakiya tsakanin uba da ɗaya shin ya Farhan zaiji barin gidan zeyi ko yaya😂
Mom Islam


*FARASHIN MUTUNCINA*
(Romantic story)
💋💋💋💋💋💋

Mom Islam

Page 17-18

Washe gari tun da Asbha bayan su Hajiya Suhaima da Alhaji sunyi Sallah, basu koma barci ba sakamakon yau ne zata wuce Dubai,

Kwance suke a kan bed ita da Alhaji, tun ɗazu take son tashi ta shiga toilet tayi wanka amma yaƙi amince mata, sai jagwalgwaleta yake yi, ya taɓo nan ya taɓo can haka dai ya dinga yi har na tsawon wasu lokuta, daga ƙarshe yai mata izinin ta shiga wankan, bayan ta shiga ta fito shima ya shiga yayi ya fito,

Ba wata kwalliya tayi ba, iya mai da powder da ta shafa, sai lipstick, kana ta ɗauko wata kyakkyawar baƙar Abaya a cikin drowarta tasa sannan tayi rolling Mayafin kana ta feshe jikinta da turarruka,

Alhaji ne ya shigo cikin shiga ta manyan kaya, shima yayi kyau Masha Allah, hannunsa na zube cikin aljihu ya dubeta kafin yace "Suhaima ƴar aiki zata ci gaba da zuwa ne kokuma har sai kin dawo"

Jin zancen tambayar tasa tayi mata wani iri yasa tace "kawai sai na dawo"

Sam beji daɗi a cikin ransa ba, dan haka yace "Allah ya nuna mana"

Bata kulashi ba, taci gaba da shirya kayanta, ƙarfe 9:am suka fito parking space lokacin Farhan ma ya fito yana sanye da wasu tsadaddun kaya Gucci sunyi masa kyau sosai,

A tare suka shiga motar, Dady a mazaunin Driver ya zauna kana Hajiya Suhaima a gefe, Farhan kuma a backside ya zauna,

Lokacin da Dady yake shirin yiwa motar key, bayan sun gama gaisawa da Farhan, Batool ta iso gidan cikin sauri dan gani take tayi lattin zuwa,

Ganin ilahirin mutanen gidan a cikin mota yasa ta ƙaraso ta ɗan durƙusa ta gaishe su, kana tace "Hajiya Allah ya kiyaye hanya"

Bayan sun amsa Hajiya Suhaima tace "Batool karki sake zuwa har sai na dawo nan da sati ɗaya"

Ta Ciro kuɗi mai yawa ta miƙawa Batool ɗin,

Godiya Batool tayi mata kana ta kama hanyar fita daga gidan,

Wani irin shauƙin sonta Alhaji yake ji yana mugun sake shigarsa, kawar da kallon tafiyar Batool ɗin yayi ba tare da ya bari kowa ya gansa ba.

Itako murna take tayi Dan tama kasa tsayawa ta duba ko nawa ne, ta dinga gudu sosai har ta iso gida,

Mama na ganinta ta hau tambayarta "lafiya Batool?"

Fuskarta ɗauke da murmishi tace "mama dama na gaya miki Hajiya zatayi tafiya shiyasa tace in dawo gida ta bani waɗannan kuɗaɗen"

Mama tace "ikon Allah Hajiya Suhaima bata gajiya da ɗawainiya Allah ya saka da Alkairi"

Mama ta karɓi kuɗin ta fara ƙirgawa, dubu biyar ne cif, mama kam tayi farin ciki sosai, dan wannan dubu biyar ɗinnan ta zame mata tamkar dubu hamsin, ta samu kuɗi a lokacin da suke da buƙatarsa,

Maryam ma tayi farin ciki, kasancewar tana kwance tana fama da ciwon kai,

Wata maƙociyarsu ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, wacce take siyar da kayan miya, dasu shinkafa, da mangyaɗa,

Mama na ganinta sai da ƙirjinta yai mummunan bugawa sakamakon tunawa da tayi tana binta bashin dubu huɗu,

Mama ta ɗan yi murmishi kafin tace "ki zauna mana"

"Ba zama bane ya kawoni dan haka na gaji da ɗaga miki ƙafa yau duk inda kuɗi yake ki shiga ki nemosa kuɗina zaki bani"

Mama tace "kiyi hakuri nima Mancewa nayi amma kina raina wllhi, ta cire dubu ɗaya ta bata dubu huɗu"

Ba tare da matar tayi mata sallama ba ta fice,

Suna nan zaune suna tunanin rayuwa, sukaji sallama daga bakin ƙofa lokacin ƙarfe shaɗaya na rana tayi,

Mama tace Batool taje ta leƙa taga ko waye,

Tashi Batool tayi, ta fito hannunta riƙe da ɗan ƙaramin hijabi, bayan ta saka a wuyanta ta sa takalmi kana ta fita dan ganin mai sallamar,

Alhji Atiku ta gani yana tsaye daga nesa da bakin ƙofarsu hannunsa riƙe da mukullin mota, yace "ke kiramin Maryam"

Batool na shirin gaishe sa, ya dakatar da ita, cike da isa da gadara yake bata umarni,

Ɗan kawar da kanta gefe tayi kana kafin tace "anty Maryam tana kwance babu lafiya"

"Wannan ƙarya ne wlhi ni za'ayiwa lumbi lumbi, to ba rashin lafiya ba, ko asibiti ne a kanta sai anyi wannan auren uban waye ya janyo idan ba hamaifinku ba?"

Rai a ɓace Batool ta sa idanunta a nasa kafin tace "kaga Mallam darajar tsufanka yasa bance maka komai ba, ka sani kome mahaifinmu yayi dole dai mahaifinmu ne, ehe kuma ka kiyaye harshenka..!

Tun da ta fara yiwa Alhaji Atiku kashedi tana nunasa da yatsanta ɗaya Alhaji mijin Hajiya Suhaima yake tsaye da mota shida wani yaro wanda

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment