gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading RAYUWAR RAYHANAH! 1 Bayan Kaddararta by Takori Chapter 7 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rayhanah za ta zo ."

"Da yake Asabar ce duk suna gida, Khalipha ya dube su daya bayan daya, Jawahir ce kewa Azizah kitso, Rahane na shafa mata lallen Rani a kan yatsunta. Abida dama ba ta dawo ba."

"Basu ankara da shigowar shi ba saboda karar t.v don haka shima ya wuce dakinsa a hankali, babu wacce ta ankara da shigowarsa."

Sai da ya yi wanka ya shirya ya fito dining nan suka san ma yana cikin gidan. Kowacce gaishe shi take don tunda suka dan kara tasawa suka daina damukarsa sai dai gaisuwa ta ladabi.

"Ya dubi Rayhanah kadan ya ce,  Ki shirya asibiti zamu yanzu Rayhanah ."

A hankali ta juyo ta dube shi tana son ta tambaye shi waye ba lafiya? Amma ta kasa sakamakon kwayar idanunshi dake sanya mata wani al amari da ke taba zuciyarta da ilahirin gangar jikinta.

"Tsam ta mike ta dauko hijabi irin dogon nan mai hannuwa ta saka ba tare da ta tsaya ko duba madubi ba, da takalmi flat. Ta bi bayan Yaya Khalipha wanda har ya tada mota."

Karo na farko a rayuwarta da ta shiga motar Khalipha. Wani ni imtaccen sanyin A.C wanda ya cakude da kamshin (car fresh) din citrus da turaren da Khalipha ya yi amfani Azzaro Chrome (Legend) shi ya soma bakuntarta a sanda ta shiga gefen Khalipha ta zauna.

"Ya dan juya kadan ya dube ta suka hada ido, inda ya gano alamomin tambaya fal cikin idanunta amma ta kasa furtawa. Ya fi minti uku bai yi magana ba kuma bai ja motar ba."

"Rahane ta gaza hakuri ta ce,  Don Allah Yaya Khalifa waye ba lafiya? "

"Ya kunna motar a hankali ya fara yin reverse, sannan ya ce da ita,  Ki yi hakuri Rayhanah, Baba Rashidu ne ba lafiya amma mun taho da shi nan asibiti har ya fara samun sauki ."

"Kwalla fal idonta ta ce,  Tun yaushe ne? "

"Khalipha ya ce,  Tun jiya, ai sammakon da muka yi ni da Daddy Takai muka tafi ."

Ta jinjina kai sai ga hawaye ya balle a ka kundukukinta. Ta yi saurin juyawa tana kallon titi kada Yaya Khalipha ya gani.

Yana gaba tana binshi a baya har dakin aminity na male-ward din inda Malam Rashidu ke kwance.

"Da sauri Rahane ta karasa gaban Baban ta kama hannunsa, wannan lokacin kuka ne sosai ya kwace mata da ta fahimci halin da Babanta ke ciki."

"Khalipha (cikin bugun zuciya) da hawayen da Raiha ke fitarwa ya ce,"

" To kuwa zan maida ke gida Rayha, ciwo ba mutuwa bane, ke da za ki ba shi karfin gwiwa da kalamai masu dadi sai ki yi masa kuka? "

"Ta soma share hawayen da gefen hijabinta. Dai-dai lokacin da Khalipha ya matso kusa da Baban, don ganin kamar ya bude ido."

"Ya ce,  Baba ga Rayhanah ta zo, Baba Allah ya baka lafiya ."

"Sai ya mika mata hannunshi mai lafiyar ta kama, jikinta har rawa yake yi. Kamar wanda ya warke a take ya bude ido garau yana kallon diyar tasa, tausayinta yake ji sosai, don ya san ba ta da kowa a duniya da za ta bugi kirji ta ce nata ne sai shi sai Ubangijin da ya halicceta."

Yana ji a jikinsa wannan rashin lafiyar tasa ba ta tashi ba ce. Bayin Allah na gari (Saliheen)

Allah kan nuna musu karshen rayuwarsu. Duk da haka ya daure ya tattara kuzarin da Allah ya

"ba shi a lokacin muryarshi da sanyi kwarai ya ce,"

 Rahanen-Iya diyar Yalwati-na!!! .

"Sai ta yi murmushi idonta fal da hawaye. Ya ci gaba da cewa,"

 Idan Allah yasa na tashi abin da zan fara yi miki Rahane shine AURE. Bana son in kwanta dama ban ganki a dakin mijinki ba.

"Sai dai kuma da na yi wani tunani sai na ga cewa kina da Uba makwafina, wato Likita Mansur. Na yarda shi mai kaunarki ne saboda Allah ba don wani bayyananne ko boyayyen dalili ba."

"Don haka Rahane na horeki da yi masa biyayya kwatankwacin yadda kike mini. In ya saki ki yi, in ya hanaki ki hanu. Rayuwar dan Adam Rahane gajeriya ce, don da ta shigo saba in shi kenan ta kare komin jin dadi kuwa, kada ki shagala da dadin duniya ki manta da Allah."

"Duk rintsi ki yarda cewa mutum bai isa ya tsarawa kansa rayuwa yadda yake so ba sai yadda Ubangijinsa ya ga dama. Rahane ban bar miki gadon komai ba sai na tarbiyyar da na yi miki, wadda na tabbata za ta yi miki jagora har karshen rayuwarki."

"Kada dadin duniya yasa ki shagala ki manta ko ke wace ce; talaka, diyar talaka, jikar talakawa. Talakawan ma na kauye. Don haka ki taimaki talaka a duk inda kika samu dama kema Allah zai taimaka miki kamar yadda likita Mansur ya taimakeki."

"Ki zabi miji dai-dai ke, abin da nake nufi a nan shine, ki auri talaka dan uwanki wanda zai daraja ki ya mutunta tushenki, in har zai ci dake ya shayar, ya tufatar, kada ki kai kanki inda Allah bai kai ki ba  "

"Kuka take sosai tare da katse shi da cewa,  Baba don Allah ka daina wadannan maganganun, masu kamadawasiyya, ni ba wani aure yanzu a gabana neman ilimi zan yi, shine sutturar mara galihu. Kuma Baba ni wa zai min auren idan babu kai? Baba me yasa kake yanke kauna da rayuwa a dalilin zafin ciwo? Ya Allah kada ka nuna min wannan ranar, wato ranar da zan wayi gari babu kai  "

"Ta ci gaba da wani irin kuka, ta kifa kanta jikin karfen gadon da Baban ke kwance."

"Rahane dai ba ta sani ba, ba ta san abin da Khalipha ya ankara da shi ba. Ji ta yi an dafa kafadarta da wasu yatsu masu bala in taushi. Ba sai ta juyo ba ta san Khalipha ne tunda su uku ne kawai a cikin dakin, ba ta kuma ji wani ya murda kofa ya shigo ba."

"Ta dago a hankali ta dubi Khalipha idanunta kamar an gumbuda musu barkono. Shima nashin sun canja launi, ya kasa jarumtakar da zai rarrasheta bai san lokacin da hannayenshi suka yi motsi ba suka sarrafa kansu suka kai ga rungume Raihanah."

"Sannan ya rufewa Malam Rashidu ido, ya ja zanin gado ya rufe shi har kansa. Dai-dai lokacin da Mami da Baba Dacta da wasu daga cikin Phyisothearapists na ward din suka shigo."

"Idanun Mami a kan Khalipha dake rungume kam-kam da Rayhanah, ya kasa sakinta don kar ta fahimci abinda ya faru, ya rasa inda zai sa kansa, rikon da yayi mata mai karfi ne don kar ta juya, gaban Mami ya yi wani irin mugun faduwa ta tsaya turus! A bakin kofa."

"Da gudu su Baba Dacta suka karasa suka bude rufar da Khalipha ya yi masa, gaba daya suka ce,  Innalillahi wa inna ilaihir raji un! ."

Baba Dacta ya juya yana share idonsa da hankici. Da karfin gaske Rayhanah ta zame daga

"jikin Khalipha ta juyo da gudu ga Babanta, ta bude rufar ta ga abin da kowa ya gani."

"Dora haannu ta yi a kan kirjinsa wai ta ji bugun zuciyarsa, ba ta san alamun mutuwa ba, amma ta tabbatar Babanta ya mutu. Tunda ga shi ta ji ba ya numfashi. Zuciyar shi bata bugawa ko alama."

"Bayan wannan ba ta kara sanin me ke faruwa a duniyar ba, bayan gilmawar wasu taurari a idanunta. Da gudu Khalipha ya yi kanta shi da Baba Dacta, suka hanata kaiwa kasa, yayin da"

"su Mami ke rufe Mal. Rashidun, likitocinsa na ta rubuce-rubuce cikin file din sa."

****

"A gidan Hakimi aka yi jana izar Mal. Rashidu. Ya kuwa samu jama a na ban mamaki, kwana uku ana karbar gaisuwa, har zuwa lokacin Rahane na gadon asibiti jininta ya hau sosai, ta ki ci ta ki sha, sai ruwa ake ta kara mata leda-leda."

"Ba kuka take yi ba, don ta nemi hawayen a idanunta ta rasa. Kwance kawai take ba ta umh ba ta uhm-uhm sai kallon gilmawar mutane da shige da ficen likitoci."

"Wato shi kansa kukan (wuri shi ka samu), wani tashin hankalin ya fi karfin ka yi masa kuka."

"Kuka rahama ne a lokacin da zuciya ke ciwo, ciwo irin wanda babu irinsa a rayuwa. Rahane ta kasa kuka sai addu a take cikin zuciyarta ita ma Allah ya dau ranta ta bi iyayenta da Iya ta huta."

"Yanzu kam ta tabbata ta zama marainiyar gaba da baya. Da dai-dai da dai-dai Allah ya yi ikonsa a kan wadanda ya bata su zame mata garkuwa a rayuwa, kuma bango abin jingina."

Shi kenan kuma ita yanzu ba ta da kowa! Idan Baba Dacta da iyalinshi suka gaji da rikonta ina za ta je?

". ..........  Sai dai kuma da na yi wani tunani sai na ga cewa kina da Uba makwafi na, wato Likita Mansur  "

"Ta tuno kalaman Mal. Rashidu masu kama da wasiyya. Ashe hirar karshe ce Baba, kaicona da na katseka!!!"

"A wannan lokacin ne ta samu hawaye suka zubo, ba tare da ta san suna kwarara ba sai ta ji an sa tissue ana share mata."

"Ta juyo kadan sai ta ga Jawahir, ita ma kukan take tayata. Ta ce,  Rayha ki yi hakuri, Baba kwananshi ne ya kare, kin sani ko muma zamu iya mutuwa a kowanne lokaci. Addu a za ki yi mishi. Rayuwa yanzu kika fara ta Rayhanah, ko ba iyaye za ka rayu idan haka Allah ya tsara maka."

"Belle ke kin rayu da Baba, ya yi miki tarbiyya, ya baki ilimi dai-dai karfinsa. Sannan bai barki a hannun da za ki wulakanta ba."

"Rayha ki daure ki tashi mu ci gaba da fafutukar rayuwa, darussa za su wuce ki, alhalin Allah bai nufa rayuwarki ta zo karshe ba."

"Ina miki ta aziyyah Raihanah, Allah ya ji kan Baba, ya ji kansa ya yi masa rahama, yasa"

"Aljannah ce makomarsa, ya sanya mana dangana ."

"Kwanaki bakwai da suka biyo baya, aka yi sadakar bakwan Mal. Rashidu. A cikin wadannan kwanakin, kwana biyu kacal ta yi a gida, ragowar a gadon asibiti."

"Tuni Khalipha ya koma bakin aikinshi cike da alhinin RAYUWAR RAYHANAH!. Ga nakasa ga hawan jini, sannan ga maraiaci na uwa da uba da rashin dangi. Tausayi ba zai barshi ya ci gaba"

da ganin Rayha cikin wannan halin ba.

"Ta rame kwarai, ita dama shiru-shiru jiki ba jiki ba, yanzu abin ya koma daga eh, sai a a. Sai da Baba Dacta yasa aka soma rubuce mata Alkur ani tana sha tsayin sati biyu."

"Hatta Abida ta rage rashin mutuncin ta don ganin Rayhan, a yanzu kam wani dan Adam bai da abin da zai bata mata rai da shi, ko yankata za ta yi ba za ta daga ido ta kalleta ba balle ta san tana yi. Tunda ta jure rabuwa da Iya da Baba, to mene ne ma ba za ta iya jure shi a rayuwar duniya ba? Duniya ta fita a kanta sai fatan cikawa da imani."

"Sati biyu bayan nan suka koma makaranta suka soma shirin zana jarrabawar shiga aji shida. Rahane kam ba fus, sakamako bai yi kyau ba. Sun ba ta maimaicin shekara guda (repeating), yayin da su Abida suka shige aji shida suka barta a aji biyar."

"Amma maimakon Baba Dacta ya yi fada kamar yadda suka zata, sai ya ce  Rayhanatu a hakan ma kin yi kokari, Allah ya yi miki mai kyau a duniya, mai kyau a lahira a dalilin juriyar ki kan kaddarorin ki da kyawawan halayenki ."

"Sati biyu Khalipha bai zo gida ba, ba don komi ba sai don baya son abin da ke zuciyarshi a kan Rayhanah ya fito sarari. Ya zo wani limit da ba zai iya boye soyayyarta ba zuciyar ba za ta iya basarwa ba."

"In kuma har ya yi kokari ya boye din, to za ka iya karantar hakan cikin kwayar idanunsa cewa yana so kuma yana tausayin Rayhanah."

"Haka nan ya samu kansa da wani sabon tunani, wato ya kai Rahane waje, masu jajayen kunnuwa su duba lalurarta. Babu cutar da ba ta da magani. Likitocinmu ba finsu kwarewa aka yi ba, kayan aiki ne bamu dasu kamar sauran kasashen da suka ci gaba."

Daga fara aikin shi zuwa yanzu yasan yanada account mai nauyi don bashi da almubazzaranci kuma babu nauyin kowa a kansa. In ma ya kakare ya tabbata Baba Dacta zai agaza masa in ya gaya masa kudurin sa.

"To amma Rayhah ta balaga, shekarunta goma sha shida ya za ayi Baba Dacta ya yarda su tafi wata uwa duniya tare? Duk da neman magani ne?"

"Wata zuciyar ta ce,  To ka fito fili mana ka sanar da Daddy kana sonta ya aura maka ka tallafi rayuwarta da taka? In ta zama matarka shikenan babu sauran shinge. To amma anya ba ta yi kankanta ba? Ya tabbata ko Daddy giyar wake ya sha ba zai aurar da Rayha a wadannan kananun shekarun ba. Don haka furtawar ma bata da amfani."

"Da ya kwashi wata daya bai zo gida ba, kewarshi ta damu al ummar gidan, kada Azizh ta ji labari. Duk sanda Mami ta kira wayarshi sai ta jita a kashe, haka in ta yi amfani da social network baya responding."

Zuciyar UWA! Ba irin tunanin da ba ta yi ba. A yau dai ta kasa daurewa ta samu Daddy da zancen.

"Ya ce,  Lafiya ita ke buya Asma u, amma ba rashinta ba ."

"Duk da haka ta kasa sukuni, a ranar Alhamis Daddy ya daga kasar Ireland domin halartar taron  Old Students Alumni of Trinity University . Kwananshi daya da tafiya ta dauki hanyar"

"Abuja ita kadai a motarta, tana tafe tana zancen zuci."

"Khalipha na kwance cikin leather seat din falonsa bakake, a gabansa ash-tray ne na silver wanda ke cike taf da guntattakin Marlboro, a wannan lokacin ma abin da yake ta yi kenan, wato gajimare da hayaki."

"Ya yi baki ya bar kasumba ta cika masa fuska, wannan kwantaccen gashin nasa duk ya"

"kanannade saboda rashin gyara. Falon kaca-kaca ga kuma kura da kayan wuta suka yi, don ya hana yaronsa Jibril shigo masa daki balle ya gyara masa sai idan shi ya kira shi a waya ya sayo masa abinci."

"Kararrawar shigowa falon ta yi kara, ta yi ta sake yi yana kwance bai motsa ba. A zatonsa Jibril ne alhalin ya san ya hana shi zuwa inda yake in ba shi ya kira shi ba. Farar singilet ce a jikinshi da dogon bakin wandon DKNY."

A fusace ya mike ya bude don ya yi masa marin da uwarsa bata taba yi masa ba. Amma sai ya yi tozali da tashi uwar wacce ko cikin mafarkinsa bai zaci ganinta a nan ba.

"Kallon shi kawai Mami ke yi, bayan mintuna uku ta bi gefenshi ta shige falon ba tare da ya bata damar hakan ba."

Sai ta fara kiran  Innalillahi wa inna ilaihi raji un smoking ABDALLAH???

Sai ta zube cikin kujera ta saka mishi kuka.

"Jikinsa ya yi bala in yin sanyi, ya zube a gabanta ya kwantar da kai a cinyoyinta cikin matsanancin tashin hankali; mahaifiyarsa na zub da hawaye a dalilinsa."

"Ta kara dago ido ta dube shi,  Ashe addicted ka zama? Shi yasa baka nemanmu? Abdallah tun yaushe kake shaye-shaye ban sani ba? Me ya kawo ni ganin wannan bakin cikin? Me ya kawo ni, ni Asma u??? "

Sai ta mike za ta fice idanunta jage-jage da hawaye. Da hanzarin gaske ya cimmata ya rungume kafafunta.

" Wallahi Mami ki yarda dani, ban taba shan abin da zai fitar dani daga hankalina ba. Mami damuwa ce bana cikin sukunin da zan iya sarrafa kaina. Ina sha ne kurum don ta rage min damuwa. Marlboro ce kawai, wallahi Mami idan na taba shan wani abu bayan ita, Allah ya yi miki sakayya a kan tarbiyyar da kika bani ."

"Ta tsaya da kukan, ta shiga nazarin falon baki dayansa cikin bakin-ciki marar misali, ta ce,  Mene ne haka? Me zan gani haka? Kazami kuma ka koma? Me kake yi yau a gida ranar aiki baka je office ba? "

"Bai bata amsa ba, don bai san me zai ce mata ba."

"Ta girgiza kai ta ce  ai Shi kenan, ni zan tafi, dama na zo in duba lafiyarka ne. Don na san haka kawai ba za ka ki gaishemu ba. To na gani lafiyarka kalau bamu isa bane kawai mu ji damuwar taka ka gwammace ka lalata rayuwarka ."

"Da hanzari ta fita, bata barshi ya yi wani furuci ba. Kayan dake jikinsa kuwa ba za su barshi ya bita ba. Ko hutawa bata yi ba, ko ruwa ba ta sha ba ta dauko hanyar Kano."

"Allah ne kawai ya kawo Mami gida, amma ba nutsuwar zuciya ba. Wai Dan da ta haifa ne yake shan taba bata taba sani ba. Ko tun tsahon yaushe yake sha?"

"Duk tsantseninta a kan  ya yanta, duk jansu da take a jikinta don su zama abokan rayuwarta, a yau Khalipha ya nuna mata aikin banza take, ya nuna mata yana da wata damuwar da ba ta isa ya gaya mata ba, ya gwammace ya mutu a cikinta."

"Da asubahin ranar ta ji Malam Dahiru ya bude get, ta daga labulen dakinta tana kallon shigowar motarshi, wannan ya tabbatar mata tafiyar dare yayo, sai ta ji tausayi ya tsirga a zuciyarta."

"Har ya fito daga motar ya rufe ya ratayo bakar jakarshi ya shigo reception tana kallon shi. Ta koma bakin gadonta ta zauna, ko minti biyu ba ta yi da zama ba ta tsinkayi sassanyar sallamar"

"sa a kofar dakinta. Babu kuzari sam a jikinta ta ce,"

" Yes, come in ."

"A yadda ya shigo din cikin kayan da ta baro shi ne, bakar rigar sanyi kawai ya dora a kai wadda ta iso har gwiwarsa, bakin glass da bakin cover takalmi."

"Sai ta nuna mishi toilet dinta, tana daga zaune  Go take a wudu (alwala), a brush, a shave and a shower, then come to me& . . (Shiga ka yi wanka, ka yi brush, ka yi alwala, ka yi aski sannan ka zo gareni)."

Maimakon ya shiga nata toilet din sai ya juya nashi dakin ya bi umarninta.

"Ya idar da sallah ya yi addu o i masu yawa, yana rokon Allah yasa Mami ta fahimci ba shi ya dorawa kanshi damuwar ba, Allah ne ya dora mishi."

"Sannan ba shi da karfin zuciyar da zai sarrafata ko ya boyeta. Su kuma ba za su iya yi masa maganinta a wannan lokacin ba. Don haka ba zai iya fada mata ba, don fadar bazata yi wani amfani ba."

Mami ta ji shiru-shiru Khalipha bai fito ba. Ta kasa hakuri ta biyo bayanshi har dakin nasu.

"A lokacin shi yana shirya abin da zai gaya mata ne don ba zai iya gaya mata gaskiya yanzu ba. Ya san Mami da boko kamar Ibraheem, cewa za suyi Rayhanah ba ta isa aure ba ko su kushe zabin nasa. Ko suce  child abuse ."

"Don haka tuni ya tattara abin da zai gaya mata. Dai-dai lokacin da ta zauna gefen  sofa dinsa. Ya shafa addu a ya ce,  Mami kin zo lafiya? Ta ce,  Da ban zo lafiyar ba za ka ganni ne har dakinka da kafafuna eyi? "

"Ya yi murmushi,  Mami kin tayar min da hankali Allah, da baki tsaya kin ji uzirina ba balle damuwar dake damun nawa. Mami in kika yi fushi dani ina zan sa raina? Jahannama fa Mami, babu ni babu jin kamshin Aljannah. Mami don Allah kar ki kara yin fushi dani, kin ji Mami? "

"Jikinta ya yi sanyi kalau, ta ce,  Mene ne ke damun naka? Ya ce,  Mami SOYAYYAH! "

"Sai ta yi murmushi ta ce,  Alhakin Hibba ne, wace mai tsautsayin ce again? Ya ce,  Mami ban sameta ba, an kasa ni ."

"Ta kara yin murmushin ta ce,  Ba ita kadai ce diya mace a duniya ba, Allah yasa hakan ya zama mafi alkhairi. Wani zubin in Allah ya tsara abu, sai ka ga na gaban ya fiye maka amfani. Ni tuni ai na yi maka mata Khalipha, jira nake ka zamo settled tukunna kafin in gabatar maka da zancen ."

"Cikin Halifa ya karta ya bala in kadawa. Da sauri ya ce,  Um-um Mami, bar zuciya da abin da take so. Har yau din dai da nake gaya miki ban fidda rai da samunta ba. Wani sanadi zai iya zuwa idan har matata ce Allah ya bani in aureta. Tunda an ce matar mutum kabarinsa ."

 Ya ya sunanta? A ina take Dattijo? Su waye iyayenta?

"Ya ce,  Mami tunda a yanzun bani da damar aurenta sanin wadannan amsoshin ba zai amfaneki da komai ba ."

"Cikin rashin damuwa da lamarin ta mike tana fadin,  Toh! Allah ya maganta maka, ni na dauka wani muhimmin al amari ne, zancen Radhiyyah kuwa na baka sati har biyu ka yi tunani a kai ."

"A cunkushe da zancen ya ce,  Radhiyyah kuma? Gaskiya Mami bana son ki sa ranki ga abin da ba zai yiwu ba. Matakin iliminta ya wuce wanda nake so a macen da zan aura kafin in aure"

ta. Nafison duk wani ilmi da mace zata yi bayan sakandire tayi shi a gida na. Kuma da kadan na

"girmeta, in zan iya tunawa shekara uku na bata."

"Haba Mami, ai an dena irin wannan hadin auren yanzu a kauye ma ba a birni ba, gaskiya ta min tsufa."

"A perception dinki ban zaci akwai irin wannan tunanin ba, na abubuwan da aka yi a can wani karni can da ya shude. Na soyayyar ma yaya aka kare da shi balle na hadi?"

"Ki barni kawai in na samu wadda za ta maye min gurbinta da kaina zan gaya miki. Amma don Allah Mami kada ki kara daga maganar nan, kada zumuncin da ke tsakaninku da Mamanta ya lalace a kan abin da ba zai yiwu ba ."

"Cikin mamaki Mami ta ce,  Ni kake cewa haka Dattijo? "

"Da sauri ya gyara kuskurensa da cewa,  Ba nufina baki da iko a kai bane Mami, kawai ina gaya miki abin da zuciyata ke gaya min a kan maganar. Ki yi hakuri idan kalamaina sun bata miki rai, I m sorry Mamee! Ki yi hakuri don Allah ."

"Ta yi ajiyar zuciya sannan ta fita. Allah kadai ya san abin da take sakawa da warwarewa a zuciyar nan tata. Mami na son  ya yanta matuka, tana kishinsu irin kishin nan mara amfani, wanda ya kimsa mata tunanin cewa da akidar cewa ba za ta bari su auri wadanda suke mutuwar so ba, sai wadanda ke son su, don kar su rabata da su."

"Irin  yan uwansu su Hibbah, Nabila da Radhiyyah diyar aminiyarta Dacta Halima wadda ta ki auren minister saboda mahaukaciyar soyayyar da take yiwa Khalipha."

"Mami na da wannan kudurin cikin ranta tuni, wanda kuma take da yakinin ko za ta yi yawo"

tsirara ne sai ta cika shi. Saboda masifar son da take wa  ya yanta.

****

"ASabar, biyar ga watan Yuli, rana ce ta ziyarar  yan makarantar kwana. Khalipha na tsaka da aiki a Office kiran Mami ya shigo wayarsa. Ya dakatar da komai ya daga ya fara gaisheta."

"A gurguje ta amsa tare da cewa,  An zabe ni zuwa karbar (Award of the best paediatrician of Africa) a kasar Djbouti zamu tafi har Daddy gobe insha Allahu, so ba zamu samu zuwa ma yara visiting Katsina ba, shine na ce ko za ka samu sararin lekasu can Katsina tunda ba ranar aiki ba ce? "

"Khalipha ji ya yi kamar yana yawo a kan gajimare dan dadi. Ga dama ta samu ta ganin Rayhanah wadda yau sati shida kenan bai dora ido a kanta ba, ba da tsimi ko dabararsa ba."

"Domin dai Mami ba ta taba cewa yaje musu visiting ba, shi bama ya sanin yaushe ake yi sai dai Mamin ta ba shi labarin cewa yara suna gaishe shi."

"Amma sai ya dan danne farin cikinsa ya ce,  O,k, to ba matsala Mami zan yi kokari in gani ko zan samu zuwan in b azan je gida ba, Congratulations Mami! Safe journey  "

Suna murmushi dukkansu suka aje wayar lokaci guda.

"Aikin da ke gabansa kasa karasashi ya yi, ya

Please Login or Register in order to submit comment