gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading RAYUWAR RAYHANAH! 1 Bayan Kaddararta by Takori Chapter 6 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taimakon da yake yiwa al umma. Balle maraya da Allah da kansa ya ce a taimake su."

"Yana kallon su kowannesu bakin shi ya ki rufo. Ta ce,  Baba kai ne ka yi kyau haka? Shima ya ce,  Rahane ke ce? Sai suka sa dariya."

"Ta ce,  Allah Baba in a hanya na ganka ba zan ganeka ba . Ya ce,  Ni din kuma fa? Kin canza gaba daya Rahane ."

" Sai mu gode Allah Baba, suma mu gode musu. Mu ci gaba da zama dasu cikin amana, Allah ya ji kan Iya ."

"Sai tasa habar zaninta ta share idonta. Shima kokarin mai da kwallar idanunsa yake, ya ce,  Amin ya Allah, Rahane ki yafe ni a kan tirsasawar da na yi kan cewa sai kin auri Ado shine silar da Iya ta rasa ranta don ta tserar dake daga wulakantacciyar rayuwa. Wallahi nima kaina a lokacin ban san dalilin da yasa nake tsoron Ado ba, sai yanzu na gane ba haka ya barni ba, to Allah ya fishi ."

"Ta ce,  Kada ka ce kai ne silar rasuwar Iya Baba lokacinta ne ya yi, ko tana dakinta ajalinta ya zo, dole za ta tafi. Baba Dacta ya ce duk sanda muka tuna ta addu a za mu yi mata, suratul Mulk, Yasin da Ikhlas, shine soyayya ta gaskiya da zamu yi mata ."

"Ya ce,  Ikon Allah, Rahane har ilimi kin kara da hankali ."

"Ta ce,  Ai Baba makaranta muke zuwa safe da yamma, da dare ma su Baba Dacta na koya mana ."

"Ya ce,  Alherin Allah ya tabbata a garesu ."

"Himu ya bar wurin don basu ganshi ba, kuma baya so su ganshin. A soro na biyu suka ci karo da Nabila ta hado abincinsa cikin kwandon kayan abinci."

"Ta ce,  Ya Himu ina ka shiga ne? Ga shi ina ta kiranka ya ki shiga . A takaice ya ce,  Ina barga ."

Suka juya cikin gidan tare.

"Yana zaune ya mike dogayen kafafunsa a kan tattausan kilishin (sitting room) din da suke zaune, Nabila na faman zuba mishi jellop din cous-cous wadda ta ji kayan lambu, a gefe cikin dan tangaran farfesun hanta ne, ta diba a cokali ta kai bakinsa."

Ya yi murmushi ya karbi cokalin daga hannunta yana ci suna  yar hira. Sai dai duk rabi Nabilan ce ke yin hirar tana ba shi labarin rayuwar makarantarsu.

"Sama-sama yake sauraronta, He is curious about something different (wani abu daban yake son sani) kan Rayhanah da Babanta."

"Kadan ya ci ya cika ruwa a tambulan ya sha. Ya mike yana laluben mukullansa a aljihunsa ya ce,"

 Am coming Nabeelah (ina zuwa) .

"Ibraheem Mansur, (HEEMU ko I.M) kamar yadda kannensa da abokansa ke kiransa. Bai da shiga sharo ba shanu balle abin da bai shafe shi ba."

"Amma a yau, haka nan ya samu kansa da son sanin asali da tushen su Rayhanah, da rayuwarsu ta baya. Abinki da karamin gari, kowa ya san kowa."

Don haka bai sha wuyar samun tarihin su Rayhanah ba. An gaya mishi uwarta ta rasu tun

"lokacin haihuwarta, kakarta da suka yi hatsari tare ita ta raine ta."

Har makarantar su Rahane ya je ya binciko takardunta. Malamansu sun shaideta wajen kokari da son karatu. Sai ya ji hankalinsa ya kwanta da rayuwarta tare dasu.

"Sai dai ko a fuska bai nunawa Baba Dacta komi ba. Malam Rashidu ya samu kyakkyawar shaida daga bakin makwabtansa. Amma a da sam hankalinsa bai kwanta da zaman yarinyar tare dasu ba, saboda halin rayuwa da butulci irin na dan Adam."

"Sai kuma yake tambayar kansa, shin me yasa ya damu kansa kan yarinyar? Damuwa irin"

wadda bai taba yi a kan kowa ba??? Ya tattara zancen ya watsar ya shiga sabgoginsa.

"Da yammacin ranar yana barga tare da kaninsa Sha aban dan Hakimi, kowannensu ingarman doki ya zaba Sarkin Dawaki ya aza musu sirdi suka dane suka nufi  yar shakatawa bayan gari."

"Suna tafe hira suke yi kan sabbin gine-ginen zamani da Hakimi ke yi a cikin garin da ginin gidan saukar baki mai dauke da bukkokin zamani, inda Turawa ke sauka idan sun kawo ziyara. Haka nan Hakimi na sauke bakin alfarma idan sun zo."

Ibraheem ya yi sha awar wadannan gine-ginen sosai. Yake ce da Sha aban duk lokacin da ya tashi ginin gida zai sanya  Hut wato bukka ta gargajiya mai suffar zamani.

"Sanda suka dawo magariba ta gabato, suka sauka daga dawakan suka soma alwala a famfon wajen. Kamar an ce da Ibrahim  juya , ya hango Rahane na yankewa Babanta akaifa da nail cut. Sai dai bai jin me suke cewa a tsakaninsu."

"To haka washe gari da misalin karfe goma na safe ya shigo bargar domin an kawo sababbin (Polo Horses) daga Ireland duka na Baba Dacta ne, yake ba da hayarsu ga masu sana ar tseren Dawaki ake masa kiwon su anan bargar hakimi. Sun bambanta sosai da sauran dawakan ko daga koshinsu da shekin da suke yi da kuzari."

"Ya dan juya ido sai ya hango Rahane da jibgin kayan wankin Babanta da ta tattaro tana ta dirzarsu kamar Allah ya aikota. Shi kuma Baban yana gefe yana yiwa dawakin askin jelarsu da katon almakashi. Yana cewa,"

 Wato Rahane ba kya jin magana ko? Na ce ki bar wankin nan ya fi karfinki in na gama zan yi abina .

"Ta ce,  Albarka nake nema Baba, ka barni in samu, in ban yi maka ba wa zan yiwa? Idan"

mun tafi ban san yaushe zamu kara dawowa ba .

Ibraheem ya jinjina kai suka kara ba shi tausayi.

"Washegari suka yi sallama da kowa za su tafi, Rahane har kuka ta yi saboda ba ta son barin Babanta. Amma ba ta bari Baba Dacta ya gani ba, sauri ta yi ta dauke hawayen da yatsunta."

"Da gudu ta koma ta sake rungume Babanta, sannan ta shiga mota tana share hawaye da sauri."

"Har Ibraheem ya kunna mota ya hango Mal. Rashidu tafe da sassarfarsa rike da katuwar leda, don haka ya dakata."

"Baba Dacta ya sauke gilashi sai ya mika masa,  Yalo ne da kashu (cashew) babu yawa a yiwa yara tsaraba ."

"Hannu biyu Baba Dacta yasa ya karba, ya ce,  Yara sun gode Baban Rayhanah. Allah ya kara nisan kwana ."

"Ya sanya hannu cikin aljihu ya zaro naira dari biyu ya mikawa Aziza,  Ungo yarinya ka sha"

ruwa a hanya kin ji?

"Mami ce ta karba fuskarta fal fara a ta ce,  Aziza ta gode Baba ."

Ya daga musu hannu suka ja motar suka tafi. Abida ta juyar da kai gefen taga tana tsaki mara sauti. Kamar ta rufe Mamin da duka da ta karba.

"Su kuwa iyayen sun ji dadi har ransu. ALHERI komi kankantarsa dadi gare shi, amma ga wanda ya san mutuncin dan Adam."

"Kafin la asar sun iso Kano. A harabar gidan bakuwar mota ce kankanuwa mai santsi (one door, Camero) fake a harabar adana motoci."

"Ai kuwa daga Jawahir, Abida har Azizah fita suka yi a guje har Azizah na faduwa, ta kuwa fashe da kuka, don har bakinta ya fashe."

Da sauri Rahane ta fito ta dauke ta tana goge mata jinin dake fita daga bakinta. Mami na ta

fada za su kashe mata  ya sai ka ce yau suka fara ganin Khalifan. Amma ko jin ta basu yi ba balle su tsaya. Sai da suka dangane ga dan uwansu suka rungume shi.

"Khalipha na zaune ne a kan kujerar zaman mutum biyu, gwangwanin Maltina ne a hannunsa yana sha, amma saboda rungumar bazata da kannen suka yi masa gwangwanin ya fadi ya zube a cinyarsa."

"Farin kaftan nashaddah (hilton) ne sol a jikinsa dinkin Mohammed, amma haka suka wanke shi da Maltinar. Hakan bai sa ya yi fushi ba, surar Azizah ya yi daga hannun Rayhanah ya yi sama da ita ya cilla ya cafe."

"Ya ce,  I m missing you  "

Ya hadasu ita da su Abidar ya rungume gaba daya yana durkushe dai-dai tsahon su. Ba tare da ya ankara da bakuwar fuskar dake gefe ba.

"Ita Rahane daki ta wuce don ta ga hankalinsa na kan kannenshi ko ta gaishe shi ma ba jinta zai yi ba, ta ce bari ta bari sai ya nutsu sai ta gaishe shin."

"Khalipha bai samu kansa daga hayaniyar su Azizah ba sai da aka kira sallar magariba. Ya mike dauke da Azizah ya kawota dakin Mami, lokacin ita Mamin tana shirin yin sallah ta wuce asibiti, don yau ma aikin kwana za ta yi."

"A gadonta ya dire Azizah ya ce,  Mami Dactan nan (Himu) ya bar miki mukullin daki ne? Ta ce,  Ka duba yana jikin kofar ."

"Ya rungumeta ta baya ya daura kai bisa kafadunta ya ce,  You didn t miss me Mami  "

"Ta ce,  Sai in yi ta rawa ina tsalle ka dawo sannan ka yarda na yi kewarka . Dariya ya yi ya juya ya fita."

"Wanka ya yi, sannan ya daura alwala, ya zuba wata shadda kaftan ruwan kasa. Khalipha Mansur baya sanya kananan kaya sam, sai shaddah, yadi ko jallabiyar Saudi ( in a gida ne). Shi yasa Mami ke kiranshi (Dattijo) a yawancin lokuta."

Daga kallo na farko da ka yiwa Khalipha za ka gane mutum ne mai faram-faram da haba-haba da jama a (sociable) sabanin Ibrahim (anti-social in nature).

"To haka a kamanni da sura, Khalipha Mami ne sak, fari sol da shi, ga tsayi ga zati. Kwayar idanunshi ba baka ba ce (brown) ce mai sheki. Da ka ganshi ka ga Mami. Kamar ta yi kaki ta tofar."

"Khalipha na da kirkin da Ibrahim bai da shi, ko daga mu amalar kauna bayyananniya dake"

"tsakaninsa da kannensa, wadda basa samu daga Himu ko kadan. Don haka suma basu dauke"

"shi da wasa ba, suna bala in kaunarsa."

"Ya damu dasu suma sun damu da shi sosai ba kadan ba. Daga sanda ya zo gidan Mami da Daddy sun huta da koyar da yara aikin makaranta. Ya hada digiri dinshi mai daraja ta daya daga Jami ar (BAZE) a kan hulda da kasashen ketare, sai jiran posting din Bautar Kasa."

"Yadda kamanni da halayya suka sha ban-ban tsakanin Himu da Khalipha, haka dabi u da akidu. Khalipha dattijon ne da gaske, yaro mai halin manya. Don haka shi kansa Daddyn ma sau tari kan kira shi da (Dattijo)."

"Bayan sallar isha i duk suna bisa tebir kamar yadda yake a al adarsu. Rahane ta fito jaye da hannun Azizah, tana ta rigima duk hancinta ya toshe da mura. Rahane sai aikin share mata hanci take da hawaye duka, da guntun tishu dake hannunta."

"Ya dan juya ya dube su jin Mami na fadan a daina kunna A.C da daddare tunda ba lokacin zafi ne ba. Ya dan kara juyowa sosai ya kalli yarinyar don a da ya yi zaton idonsa ne bai gani sosai ba, ya dubi Mami ya ce,  Ina kika samo  ya? "

"Ta ce,  Allah ne ya bani ."

Kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru ya ci gaba da cin abincinsa. Don ya ga bai kamata ya ci gaba da yiwa Mamin tambayar a gaban yarinyar ba.

"Rahane kujera ta hau kusa da Jawahir, don ko kadan ba ta zama daf da Abida, sakamakon kisan mummuken da take mata,  yan yatsunta take murjewa da kafar kujerarta, ko ta faki idon kowa ta takata da tsinin takalminta da take sawa musamman don muguntar. Iyakaci a ga tana kuka in sun koma daki, tambayar duniyar nan Jawahir za ta yi amma sai ta ce babu komai Iya take tunawa."

"Sai dai kuma ta yiwa kanta maganin abun, ta daina yarda ta zauna kusa da ita. Wanda hakan bai yiwa Abida dadi ba, don dai ita nan duniya babu wanda take jin haushi irin Rayhanah."

 Zauna mana Rayhanah . In ji Mami.

"Ta zauna sosai ta fara cin abincin da Mamin ta yi serving dinta. Sakwara ce da miyar alayyahu da ganda da kifi, musamman don Khalipha Mamin ta yi girkin da kanta, don nan duniya ba abincin da Khalipha ke so irin sakwara."

"Sunanshi na ainihi sunan mahaifin su Mami ne da ya Musulunta wato (Abdallah). Dacta Mansur da bai iya fadi a matsayin sunan na sirikin sa mai rasuwa shine yake cewa Khaliphan, to sai kowa ya kama. Abdallah ta bace bat, sai Khalipha."

"Da kyar Rahane ta iya cin abincin nan saboda kallon ta da Khalipha ke yi jefi-jefi. Ga kukan Azizah ya dameta, jinsa take har cikin ranta. Ko kadan ba ta son kukan yarinyar."

"Garin kallon nashi ne ya hango aid din dake makale bayan kunnenta. Ya zare gilashin shi a hankali yana kara kalla ya ce,  Mami bakuwar taku ba ta ji ne? "

"Ta bata fuska ta ce,  Wai kai Khalipha baka gani ka yi shiru ne sai ka ce dan jarida? Ya maida gilashin sa yace,  Sorry Mum, I m curious in cases like these& .! ."

"Ta ce,  Iftila i na rana daya, sun samu accident ne shine sanadi . Yace  ta yaya accident zai zamo cause to hearing impairment? Ku dai kara bincikawa, haka kawai ma ji kan dauke, mostly as a result of typhoid fever ko meningitis, ko kuma hereditary factor (gado) na amosanin kunne (otesclerosis) . Mami tace"

" to Dr. Khalipha, babu daya kanwar biyu, professionals basu ga hakan ba har sai sun gudanar da CT Scan and MRI Scan wanda abune dake neman naira miliyan biyu cash. Kuma"

ba ayin shi a Nigeria.

Mahaifinta kuma ya tabbatar lafiyar ta kalau ta baro gida kamin suyi hadarin kuma bata gada daga ko ina ba (uwa ko uba) .

Ya mikawa Rahane hannu wadda ta sunkuyar da kai......

" Shake my hands, Rayha  "

Murmushi ta yi amma bata bashi hannun ba.

"Ya ce,  To shi kenan tunda bakya abotar dani . Ya fada cikin launin shagwaba da langabar da kai."

"Ba ta san sanda ta yi dariya ba, fararen hakoranta yiri-yiri farare sol suka bayyana. Babba dashi yana shagwaba a gaban mamarsa."

"Ya ce,  Do not your problem slow down, you will achieve a lot in life! "

"Ita bata ma ji mai ya ce ba saboda yadda harshensa ke harde da Turanci gangariya, sai gwani a harshen ne kadai zai iya fahimtarsa."

Wannan ya samo asali ne da haihuwar Khalipha da Himu da Mami ta yi a Ireland (Dublin).

Inda Khalipha ya yi karatun shi har zuwa aji biyar na sakandire kamin su tattaro su dawo Nigeria.

"A haka aka kare cin abincin. Koyarwar Yaya Khalipha daban take, ko yaro shine jaki wajen dakikanci dole ya gane koyarwar Yaya Khalipha."

"Da ya zo kan littafin Rahane, ya gane Rahanen na da rauni a lissafi (Mathematics) don haka ya tabbatar ta yi a gabansa dai-dai sannan ya kyaleta."

"A daren ne Mami take ba shi labarin Rahane, ya saurara da nutsuwa. Yana tsaye jikin balcony na dakinsu yana kokarin kunna Marlboro da lighter ya hango Abida ta fizge hearing aid din Rayha ta yi cilli da shi tana cewa."

" Banza  yar kauye, wadda bata ji said a inji, ai sai ki ji mu gani ."

"Da gudu Rahane ta bishi inda ta yar ta dauka, sai ta ga ya fashe. Abida ta gudu tana kyalkyala mata dariya."

"Durkushewa ta yi a nan tana kuka don ba ta san me za ta ce da Baba Dacta ba, domin ya yi"

mata gargadi sosai a kan takula

"da shi, ita kuma ba za ta iya ce da shi ga laifin Abida ba."

"Da hanzari ya ajiye abin da ke hannunsa ya fito zuwa harabar gidan, tsugunawa ya yi gaban Rahane ya karba yana gyarawa. Ido ta dago ta dube shi sai ta hau share hawaye da hanzari, don bata so ya ganta tana kukan ba. Da ya gyara sai ya mayar mata ya ce,  Tafi gida ."

"Tun daga ranar Khalipha ya sa ido a kan mu amalar Rayha da Abida, Jawahir da kuma Azizah. Ya gane Abida bata son Rayhanah sam-sam, komi ta yi sai ta kushe ta gwale, ta wulakantata. Ya ci gaba da bibiyarsu da hankali, nan ya gane kaunar da Jawahir ke wa Rahane, suna son junansu sosai, da kaunar da Rahane kewa Azizah wadda ta sayo mata kauna a zuciyar Mami."

"Tara Abida yake yi, bai yi kuma niyyar sanarwa Daddy ba shi zai yi maganin abin. Yau suna zaune shi da Malam Dahiru maigadinsu a kan benci suna hira, su kuma yaran suna can wajen shukokin grass-carpet suna wasanninsu ya hango Abida ta janyo mesar da ake bai wa shukoki ruwa ta saki ruwan a kan Rayhanah, tun daga kanta har kafafunta ta jikata sharkaf, amma ko"

uffan yarinyar nan bata ce ba. Ta ja mesar ta gudu da ta hango Jawahir na tahowa.

"Tun daga ranar ya lura Rayhanah ta daina shiga cikinsu. Ba ma ya ganinta kwata-kwata. Daga baya ya lura kullum tana daki ne kwance a gadonta lullube da bargo. Sai ta ji Mami ko Baba Dacta a falo sannan take fitowa, amma ko abinci in basa nan ba ta ci."

"Ganin haka shi kuma duk sanda zai ci abinci sai ya tura Azizah ta kirata, ya cika mata filet ya ce sai ta cinye a gabansa. Ya soma janta a jiki ta hanyar labarai da son jin damuwarta, da kuma ba ta misalan rayuwa kala-kala a kan kaddarar da Ubangiji ya yi nufi ga bayinsa, sai su karbeta su kasance masu godiya a gare shi, don in ya baka wannan, sai ya hana maka wancan, ya ga cewa za ka gode masa ne ko za ka butulce a kan wannan jarrabawar kankanuwa da ya yi maka?"

"Kwarai Rahane ke jin dadin hira da Yaya Khalipha, halinsa ba daya ne da na dan uwansa ba, komai nasu opposite. Ita Rahane yadda Yaya Khalipha ya damu da lalurarta ita ba ta damu kanta haka ba. Ita fa ko babu injin nan za ta iya zamanta lafiya, tunda tana da lafiya falil-lahil hamdu."

"Rannan da yamma kuma Jawahir tana falo, Abida ta ja Azizah daki ta cire mata pampers. Ta yi kashi fal! Rahane na kwance a gadonta cikin bargo kanta ke ciwo sosai ga zazzabi-zazzabi na neman kama ta. Ba ta son wannan na ura mai mayar da daki kamar firinji. Duk da Mami ta ce a daina kunnawa sai lokacin zafi su kam basa iyawa sai sun kunna in za su kwanta in ba haka ba ba za su iya barci ba."

"Abida ta kunso kashin pampers ta dawo dakin kamar abin arziki ta ce,  RAYHA! "

Ta dan janye bargon ta fiddo fuskarta idanunta duk sun kankance sunyi jawur alamun ciwon kai mai zafi. Ba ta yi wata-wata ba ta kifa mata kashin a fuska.

"Dai-dai lokacin da Jawahir ta shigo. Cikin karaji ta ce,  Abidaaaa! "

"Wannan ya janyo hankalin Himu da Khalipha wadanda ke zaune a falo suka yo dakin aguje saboda yadda ta yi maganar da karfi da kururuwa, tsammani suka yi Abidar mutuwa ta yi."

"Ta ce,  Ku duba ku gani, kashin Azizah ta kifa mata a fuska ."

"Ai kuwa Khalipa ya kama Abida da duka don dama bai iya fushi ba, kuma tarata yake yau ta kai shi bango."

"Shi kuwa Ibraheem juyawa ya yi ya fita ya ma bar gidan zuciyarsa na wani irin harbawa, tsigar jikinsa na tashi, don baya son ya yi kowanne action a kan Rayhanah balle har ya fassara"

reaction din sa a kanta.

Yana referring kowane motion dinsa a kanta da KARYA Bayan kuma sau tari tsoron kar

"zuciyarsa ta ce ya yi KARYAR yake kidima shi ya yi mata KARYAR. Ya damu da RAYHANAH fiye da kowa da komi a duniya, amma yana KARYATAWA da kalubalantar kansa a kullum. Wani gini ne ke tsiro na TAUSAYI da KAUNA tun ranad da suka baro Takai."

"[12/24/2019, 17:56] Takori: Khalipha ya ci gaba da kallon labaran CNN da Mu azzam Kanti ke kwararowa (Alkawari Bayan Rai). Lokaci-lokaci ya kan duba agogon (RADO) baki dake daure a hannunsa, sai kuma ya dan dubi kofar dakin nasu. Amma ko keyar Rayhana babu har karfe goma. Tuni Azizah ta yi barci a dakin Mami. Yana jin sanda Jawahir ta yi musu light off (wato ta kashe wutar dakin)."

Sai ya mike a hankali jikinshi babu kwari ya nufi dakinsa ya sunce ya daura tawul ya sakarwa

"kanshi shower, amma zuciyarshi ta ki yin sanyi. A azabce take matuka da zazzafar soyayya, wadda shi kansa bai san ya zai yi ya amayar da ita ba ga kankanuwar yarinya kamar Raihanah"

mai shekaru goma sha biyar wadda kuma ke matukar ganin girmansa.

"Ya daura Pjs ya kwanta a sofa, ya janyo kwalin Marlboro ya soma tada karamin hadari da hayakinta, duk don ya samu sassauci a zuciyarsa, ya danne wannan al amari da ya kutso cikin rayuwarsa ba da tsammaninsa ba, zuwa sanda Rahane za ta kara girma ta mallaki cikakken hankali yadda za ta fahimci al amarin, at least ko sakandire ne ta gama. Ya san Daddy ba zai hana shi ba idan ya ce yana so. To balle kuma Mami da ta mai da Rayhan diyar cikinta."

"Barci a wannan daren rabi-da-rabi Khalipha ya yi shi. Karshe shida dai-dai ya ji Daddy na buga mishi kofa, abinda bai taba yi ba."

"Idanunshi jajir kuma mitsi-mitsi cikin mugun barci mai dadi ya bude kofar. Kafin ya gaida Daddyn ya ce,  In ce ko ka yi sallah Khalipha"

"Ya amsa  Eh, Daddy na yi ."

To ka canzo kayan jikinka mu tafi Takai .

"Tuni ya nemi barcin ya rasa, ya ce,  Lafiya Daddy? "

"Ya ce,  Shiryo dai mu yi sauri kamin yaran nan su farka ."

"Saboda zullumi Khalipha a bai-bai yasa rigarsa, ya suro hula da takalmi ya bi bayan Daddy."

"Sai da suka hau titi dodar, sannan ne yake gaya mishi Hakimi ne ya kirashi a waya ya ce da shi Malam Rashidu ya fadi a bayi (toilet) rabin jikinshi ya mutu (Pralysed) jiya da daddare."

"Khalipha ya ce,  Subhanallah! To ai Daddy da mun taho da Rayha ."

"Ya ce,  Zamu taho dashi asibiti ne ai, idan na ga yanayin jikin nasa. Ba zan so ta ganshi in a bad condition ba, ka san damuwarta da mahaifinta ."

"Khalipha dai shiru ya yi, amma kar ki so ki tona zuciyarshi da damuwa ta yiwa yawa. Har ya fi Daddy damuwa. Har suka shigo garin Takai bai kara yin magana ba."

"Da hantsi suka isa Takai. A kofar gidan Hakimi suka yi parking. A dakin Hajiya Karima suka karya kumallo, kafin su shiga wajen da aka warewa Mal. Rashidu."

"Yana kwance bai san wanda yake kanshi ba, har Baba Dacta ya gama dube-dube da"

"aune-aunenshi a kansa bai san ana yi ba. Bakinsa a karkace rabin fuskarshi ya mutu. Duk wani taimakon gaggawa da ake yiwa masu lalurar Dr. Mansur ya ba shi, sannan ya gayawa Hakimi za su tafi da shi asibiti, kwararru a fanninsa su duba shi."

La asar lis suna cikin asibitin koyarwa na Kano. A take aka ba shi gado a (aminity) aka soma bincikarsa tare da gwaje-gwaje da dora shi a kan tretment din da ya dace da shi a (physiothearapy department).

"Sai magariba suka koma gida a gajiye likis. Suka yi sallah suka ci abinci suka samu nutsuwa. Bayan sunyi sallar isha i suka koma asibitin, zuwa lokacin ya bude idonsa amma baya magana, sai dai duk abin da suke cewa yana jinsu. Yana ta motsi da bakin yana son gaya musu wani abin amma ya kasa."

"Albarkacin Baba Dacta duka likitocin dake kula da shi basu dauke shi da wasa ba, kula suke da shi sosai ba dare ba rana. Khalipha shi ya kwana da shi."

"Washe gari da safe Dacta ya zo da Mami don ita kwanan asibitin ta yi, suka duba jikin nasa yana samun sauki ba laifi ba kamar jiya ba."

"Har ya yiwa Khalipha murmushi, Khalipha ya matsa gare shi shima ya yi murmushin. Ya ce,  Sannu Baba, Allah zai baka lafiya ka ji? "

"Ga mamakinsa sai ya ga ya yi masa alamar ya daga kai. Khalipha ya ce,  Zan je in yi wanka"

in dawo Baba .

"Sai ya rike hannunsa da hannunsa mai lafiyar ya ki saki, yana ta kakarin magana. Da Khalipha ya nutsu ya fahimci cewa yake  Ka zo da RAHANE ."

"Ya ce,  To Baba

Please Login or Register in order to submit comment