gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading RAYUWAR RAYHANAH! 1 Bayan Kaddararta by Takori Chapter 3 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaban Babana& amma shine"

zai aura min shi?

"Ran Dacta Mansur ya yi mugun baci, lallai ya yarda komai akai da matsiyaci sai ya ci kara."

"Wannan Mal. Rashidun a jahilan ma bai san a ajin da yake ba. Kai baka ce shi da bakinsa yake fadar rashin arzikin da Ado ya yi masa ba, wai ya boye Rahane har ya yi attempting keta mata mutunci a gabansa, wannan shine mijin da zai bawa aure."

"Ya ce,  Kai Malam! Ina jin dai ba lafiyarka kalau ba. Aure da wannan mutumin, mun hana, ya lissafa duk abin da ya kashe maka a biya shi, bayan ya gama zaman gidan kaso na keta haddin da yaso yi. Ba zan iya cin fuskarka ba albarkacin Rayhanah ."

"Ya dau waya ya ce,  Ibraheemu jeka ofishin  yan sandan nan ka ce su zo min da wannan"

mutumin da nasa aka kama yanzu-yanzun nan .

"I.M Takai tsaye ya yi rike da wayar hannunshi  What s wrong with Daddy ne? Ya dubi wayar hannunshi sosai cike da takaici, sannan ya dubi Nabilah diyar Hakimi da suke tsaye tare,  Mts! Daddy ya samu matsala Nabilah! "

"Ta ce,  Matsalar me? "

"Ya sake hura hanci ya ce,  Jirani ina zuwa . Ya juya ya fita."

"Cikin dan lokaci an kawo Ado fada. Malam Rashidu ya dube shi jikinsa yana ta rawa ya ce,"

 Yauwa don Allah ku sa a sake shi .

"Haushi ya kama Hakimi ya ce,  Kai Malam ka nutsu ka san a inda kake bama son shirmen banza ."

"Malam Rashidu ya koma cikin nutsuwarsa. Dacta Mansur ya dubi Ado sosai ya ce,  Da gaske kana son auren diyar Malam Rashidu? "

"Ado wanda ya ci kaniyarsa sosai a hannun  yan sanda ya ce,  Eh . Dacta ya ce,  Shine kuma za ka yi mata fyade a gaban ubanta? Ya ce,  Ba nufina kenan ba ."

"Dacta ya ce,  To meye nufin ka na tsaraita ta? "

"Ya yi shiru. Dacta ya ci gaba da kallonsa a ransa yana mamakin Malam Rashidu, wai wannan mutumin mai kama da  yan fashi zai aurawa innocent yarinya kamar Rayhanah."

"Ya boye mamakinsa ya ce,  Sulhu nake nema da kai ."

"Ado ya dago a fusace, sai kuma suka yi mishi kwarjini ya kasa cewa komai. Dacta ya ci gaba da cewa,  Ka lissafa duk abin da ka kashewa Mal. Rashidu da  yarsa zan fanshe su ba ta isa aure ba! "

"Ado ya gallawa Mal. Rashidu harara wanda ya takure ya yi lakwam yana kallon Ado a tsorace. Ado ya bude wawulon bakinsa ya ce cikin zafin rai,  Hakorana da aka zubar min fa? "

 Zamu makala maka na roba yanzu .

"Ya ce,  To a rabani da  yan sandan nan . Hakimi ya ce,  An raba ku ."

"Ado ya ce,  Naira dubu dari biyar zaku bani, kuma su tashi su bar min gidana ."

"Hakimi ya yi murmushi, ya jawo wata bakar akwati ya bude, ya dauko daurin kudi  yan dubu-dunu dauri biyar ya zube su a gaban Ado."

" Gasu, gidanka kuwa ko komawa ba zasu yi ba. Duk tarkacen dake ciki ma sun bar maka."

 Yan zaman makokin ma in kaso ka koresu ka koresu su zo nan su yi .

Ado ya gigice don dai kawai ya shaci kudin ne da gayya bai taba zaton ba za suyi musu ba.

"Ya kwashi kudi ya nade cikin rigarsa ya mike zai fita, cike da tsoron kada su kwace kafin ya kai kofa. Dariya ta kama Dacta Mansur ya ce,  Hakoran fa Ado? "

"Ya ce,  Barsu kawai, zan je kudu a sa min ."

Gaba daya suka sa dariya har Mal. Rashidu dake takure a gefe sai da ya murmusa.

"Karshen diramar Ado da Rahane kenan. Tunda ya hada kudin nan ya gudu ya bar Takai, ya bar  ya yansa da matarsa ba a kara jin duriyarsa ba. Aka bawa Mal. Rashidu muhalli a cikin gidajen bayin Hakimi, washegari ya fara aikinsa na kula da Dawakin Hakimi."

"Dr. Mansur da dansa I.M suka taho Kano da Rahane, bayan ta yi sallama da babanta."

RAHANE A GIDAN DR. MANSOOR

"Gidan Dr. Mansur Balarabe Takai babban gida ne mai tsarin gaske a unguwar Lamido Crescent, wanda ke rufe cikin bakin girgijejen get. Asalinsa Turawa ne suka zauna cikinsa shekaru masu yawa da suka gabata lokacin mulkin soja sanda suka bude kamfanin PZ da za su koma kasarsu suka sayarwa gwamnati."

"Lokacin da Dr. Mansur ya yi kwamishinan lafiya a Kano, lokacin Gwamna Kabiru Gaya, gwamnati ta bashi gidan ya zauna, da tenure din su ya kare ya yi kokarin da ya sayi gidan da taimakon mahaifinshi mai girma Hakimin Takai na III (Balarabe Sardauna)."

"Haka ya ci gaba da sabunta gidan, yadda zai yi dai-dai da zamanin da ake ciki har kawo yau."

"Gidan farin fenti ne da shi, kana shigowa cikin get din gidan mikakkiyar kwalta ce wadda zata sadaka da rumfar adana motoci a kalla biyar, ba tare da kowacce ta gogi  yar uwarta ba."

Idan ka yo gaba kadan grass carpet ne wanda zai kai ka bakin kofar reception din gidan. A cikin reception din matattakalar bene take wadda za ta sadaka da falon sama da yake kunshe da dakunan barcin jama ar gidan.

"Dakunan barci hudu ne a cikin falon, daya na Dr. Mansoor, daya na Mami, daya na I.M da Yayansa Khalipha, wanda a halin yanzu yake karatu a jami ar BAZE dake Abuja, yana karantar hulda da kasashen ketare wato (International Relation). Daya dakin na Abida da Jawahir ne, sai autar su Azizah."

"Abida shekarunta takwas, Jawahid goma, Mami ta dade bayan haihuwar Abida kafin ta haifi Aziza wadda ke da shekaru uku a halin yanzu."

"Saboda tsantsenin tarbiyya irin na Dr. Mansur bai warewa I.M da Khalipha daki a wajen gidansa ba, duk da girmansu tare yake dasu yana ganin kowanne motsinsu. Idan abokai ne ga"

"reception nan bai yarda ko baskwata su zauna ba, masu aikace-aikacen gidan ne a baskwatan."

Motar Dr. Mansur ta sako kai farfajiyar gidansa. Ibraheem ne ke tukin. Dacta na gaban motar rike da jaridar This Day da ya saya a go slow din roundabout na kofar Nassarawa. Rahane na

baya a makure jikin kofar motar kamar ka ce kyat! Ta bude murfin motar ta arta a na kare.

"Abida da Jawahid ne zaune a rumfar adana motoci tare da malamin Islamiyyarsu dake zuwa duk Alhamis da Juma a yana koya musu karatun Alkur ani da Hadisi, tajweed da Tawheeed, ga bakin allo (black board) an kafa musu cikin rumfar adana motocin. Ta bala in raina malamin, don Abida  yar rainin wayau ce, sabanin Jawahir da ko magana ba sosai take yinta ba."

"Jin shigowar motar Daddy Abida ta nutsu daga mintsinin Jawahir da take yi, shi kansa Malam Umar ya lura Abida ta shiga taitayinta, don haka ya juyo don ganin abin da ya nutsar da ita."

"Daddy ne da Ibraheem ke fitowa daga mota, tare da wata dukun-dukun din yarinya baka wuluk! Kanta a daure cikin wani bakin tsumma da wani sidadden silifa a kafarta, ko ina a jikinta ciwo ne, wani da plasta wani plastar ta daye."

"Abida ta soma zungurin Jawahir don ita ma ta juya ta ga abin da ta gani, amma Jawahir ta yi banza da ita ta ki juyawa ta ba da hankalinta sosai ga Malam Umar."

Malam din ya aje Alkur anin dake hannunsa ya isa ga Daddy ya tsugunna yana gaisuwa.

Daddy ya amsa ta hanyar bashi hannu sukayi musabiha. Tuni Ibraheem ya shige gida. Daddy ya kama hannun Rahane suka doshi reception.

"Rahane dai taku take a tsorace, don ita tunda Allah ya halicce ta bata taba ganin waje irin"

"wannan ba, kamar Aljanna da ake kwatantawa."

 Mami! Mami!!

Daddy ke kira a falon sama.

"Ta fito daga laundary inda take shanyar kayan Azizah data wanke cikin injin wanki, sanye take da riga da siket na wani bakin material mai yarfin light green flowers, gashin kanta kame da hair-bound, shima light green ya sauko har kafadunta. Duk wani likita kirki ne da shi, to haka Dr. Asma u Takai, musamman kasancewarta likitar yara."

"Amma a yau kam ga dukkan alamu za suyi fada da Dactan nata, don kirkin nata bai kai nan ba."

"Za ka rantse ba ta haifi Da kamar I.M ba, balle kuma Yayansa Khalipha. Ta fi kama da matashiya  yar shekaru talatin ba talatin da tara ba."

"Ta fito falon tana fadin  Dacta na! Shima ya ce,  Mamina!! . Ya juya ga Rahane,  Rayhanah matsa ki gai da Mamanku ."

"Sai a lokacin ta kai idonta ga Rahanen da ta zube a gabanta tana fadin  Barka da yamma Hajiya . A firgice ta juya ga Ibraheem, sannan Daddyn ta kasa tambayar komai."

"Dariya ce ta kama Ibraheem ganin idanun Mami sunyi mitsi-mitsi, ya lallaba ya shige dakinsa kada dariyar da yake yi ta fito."

Daddy ya yi murmushi ya isa ga Rahane yasa hannu ya cira ta daga zubewar da ta yi kamar bawa a gaban Ubangijinsa. Ya zaunar da ita a kujera yana ce da Mami

" Karin  ya na kawo miki, sauran bayani sai anjima, yanzu ba ta abinci da ruwa tukunna mun sha tafiya ."

"Ta dan saki fuska ta koma kicin ta zubo abinci a plate da robar ruwan Eva mai sanyi da lemun La-casera ta kawo mata kan tebir. Amma da ta kira yarinyar ta ce ta zauna a kujera ta ci, sai ta ga ta sauke plate din kan marbles ta bararraje abinta tana ci kamar Allah ya aikota saboda yunwa."

"Ta bi bayan mijinta cike da mamaki. Ta same shi yana cire safar kafarshi a gefen gado, ta"

"zauna a kasan kafafun nashi ta karbe shi. Sai da ya yi wanka ya kwanta yana hutawa, Mami ta"

"matsa jikinsa tana cewa,"

 Ina ka samo yarinya bakauya haka?

"Ya ce,  Garinmu Takai . Ta ce,  Yar waye? Ya ce,  Yar AMANA! "

"Ya tashi daga kishingidar da ya yi ya kama hannayenta masu taushi ya ce,  Mami batun yau ba ni da ke muke da bambancin ra ayi a kan al amura da dama, amma kowa ya kasa rinjayar dan uwanshi ya bi nashi ra ayin."

"Amma a yau ina neman alfarma Mami, wadda na san mai girma ce a gare ki, ita ce ki rike min Rayhanah kwatankwacin rikon da kike yiwa  ya yan da kika haifa."

"Ko da komai bai zamo hundred parcently equal ba, ki kwatanta kara da karamci. Rayhanah da ubanta ba shegiya ba ce. Sai dai marainiya ce ba ta da uwa, ta rasu tun lokacin haihuwarta. Ta girma a hannun kakarta, ita ma yanzu babu."

"Na tserar da ita ne daga kaskantacciyar rayuwa da ubanta ke so ta yi, wato early and abusing marriage, sakamakon wasu extraordinary characteristics dana gani a tare da ita."

"Ban taba haduwa da pateint din da ya shiga raina irin ta ba. Sannan ta gamu da  lalura wadda dole a tausaya mata, a bata kwarin gwiwar da zata fuskanci rayuwa a, duk yadda ta zo mata."

"Ta samu hearing impairment wanda bazamu ce a sakamakon hadarin da suka yi bane, har yanzu source din, bai bayyana garemu ba, har sai anyi CT Scan and MRI Scan, wadanda bamu da injinan yin su anan Nigeria, in kin lura akwai hearing-aid a kunnenta. Mami ban taba neman alfarma kin kasa yi min ba, a yau wadda nake nema ma ba za ta gagareki ba, tunda kin saba haihuwa kin san ciwon DA. Yadda naki yake a ranki haka na kowa yake a zuciyar nashi iyayen."

"Ki yi min alfarma cikin dimbin alfarmominki gareni, ki rike min RAYHANAH da zuciya daya, ni kuma duk abin da kike so zan miki Mami. Wallahi-wallahi ko da bani da shi zan nemo. Kawai ina so Rayhanah ta yi rayuwa mai kyau kamar  ya yanki. Ta yi ilimi, ba tare da nakasunta ya nakasta rayuwarta ba. Zan samu Mami? "

"Ta sauke idonta a hankali kan mijin nata, ta rasa shi wane irin mutum ne, mai maida damuwar wani tasa. Ba ta da muguwar zuciya ko kankani, sai dai ba ta son kowa ya rabi rayuwarta da mijinta da  ya yanta."

"Ba ma wannan ne abin tsoron ba, za ta hada  ya yanta ne da yarinyar da ko asalinta ba ta sani ba? Kai rigimar Daddy da yawa take."

"Ta ce,  Daddy zan yi maka alfarmar da kake so, amma a bisa sharadi biyu ."

"Kallonta ya yi, kallon ke nake sauraro. Ta ce,  Ka yi min alkawarin WATARANA ba zaka ce za ka hada aure tsakanin  ya yana da wannan yarinyar ba. Sharadi na biyu shine, zan raba musu daki da su Abida, don hankalina ba zai kwanta ba idan tana tare dasu ."

"Dariya ta bai wa Daddy sosai. Ya ce,  Mamee! "

"Ta ce,  Dacta naa!! "

" ki kwantar da hankalinki da Rayhanah, ba zan kawo abin da zai cuci su Abida ba. Am their Dad, remember? Baki fini son su ba!!!."

"Maganar aure da  ya yanki kuwa kisa ranki a inuwa sassanya, Allah zai baiwa Rayhanah miji na ban mamaki wanda zai kaunaceta domin Allah ya rungumeta da lalurar ta, ba  ya yanki ba,"

"masu hali da akida irin taki,  ya yanki ba sune kadai MAZA a duniya ba! MAZA ma tukunna, baki"

gansu ba Mami.

"In kin so ki aura musu  ya yan Queen Elizabeth, karshenta dai kenan ko? Ki rubuta ki ajiye, babu aure tsakanin  ya yanki da Rayhanah! Tunda ita baki dauketa cikakkiyar mutum ba ."

 Ba haka nake nufi ba Dacta na?  To ya ya ne?

" (A bit depressed). Ta ce,  Ni dai in hakan za a yi bani da matsala da yarinyar ."

"Dacta ya ce,  Mami, hoo! "

"Rahane tuni barci ya kwasheta a kan marbles din dining, inda ta ci abinci. A haka su Abida suka shigo suka sameta, Abida, Jawahir da Azizah suka sunkuya suna kallonta."

"Abida ta leka tafin kafarta ta ga faso da kaushi! Ta ce,  Ehoo! Yau faso zai yaga bedsheet din Jawahid, don kuwa ba dai gadona ba ."

"Aziza kuwa dukanta take tana cewa,  Tashi-tashi, cinnaka zai cijeki, ki hau gado . Jawahir kuwa hannunta ta kama tana cewa,  Tashi muje daki za ki dauki sanyi a nan ."

Ta bude idonta a hankali tana kallon su. Ba ta taba ganin kyawawan mutane irin wadannan yaran ba.

"Dacta ne da Mami suka fito tare jin hayaniyarsu, suka gansu zagaye da ita kamar sun ga wata sabuwar halitta. Mami ta ce,  Mene ne haka? Ku kaita daki mana ta yi wanka sai ta kwanta ta yi barcin ."

"Abida ta ce,  Ar! Mami kafarta faso! She is smelling bad!! Da soson wa za ta yi wanka? Dacta ya dunkule hannu ya danna mata,  Da na Uwaki. Ja ira mara hankali ."

"Ya matsa gabansu ya ce,  Kamata Jawahir kuje daki ki taimaka mata ta yi wanka, kin gani ba ta da lafiya ."

"Jawahir ta bi umarnin mahaifinta. Suka shiga daki da Rahane. Ta cika mata ruwan dumi a kwami, ta zuba dettol, ta bare sabon sabulun zest da sabon soso ta bata."

"Ta ce,  Ki yi wankan sosai kin ji, amma ki yi a hankali kada ki fama ciwukan ki ."

"Ta nuna mata hanger,  Ga towell nan, ki dauki wanda kike so. Wannan kwandon ki zuba kayan da kika cire kayan wanki ne a ciki ."

"Rahane ta ce,  Ai ban zo da wasu kayan da zan canza ba in na ajiye wadannan ."

"Ta ce,  Zan baki nawa in ji Daddy . Ta juya ta fita tana cewa,  Ki yi wanka sosai ."

Rahane ta yi tsaye tana kallon katon ramin da aka cika da ruwa aka ce wai ta shiga ciki tsulum! Ta yi wanka. To idan ta nutse fa?

"Ta kai hannu a hankali tana shafa gefen kwamin, santsi kamar jikin tarwada. Ga shi fari kal! Shi kansa ruwan kamshi yake. Ta fi minti ashirin ta shafa nan, ta kalli kanta a mudubi, ta kasa ko da cire kayan jikinta. Ga bayan gida tana ji amma ba ta ga masai ba, sai fararen tangaraye a rufe, da ta bude ruwa ne a kwance a cikinsu garai-garai, ta rasa inda za ta sa kanta, domin bayan gidan ya matseta. Ta kuma rasa a inda za ta yi, sai ta goce da kuka."

"Daga daki Abida da Jawahir suka jiyo ta, Abida ta kyalkyale da dariya ta ce,  Yanzu haka faduwa ta yi cikin soka-way ."

"Da sauri Jawahir ta iso bakin kofar tana buga mata tana cewa,  Lafiya? "

"Ta ce,  Tutu nake ji . Ta ce,  Mene ne tutu? "

"Ta ce,  Bayan gida ."

"Ta murda kofar ta shiga gaba-gadi, nan ta tarar ko kayan jikinta ba ta tube ba balle ta yi wankan, tana tsaye tana share ido. Tausayi ya kama Jawahir, ta bude masai ta zauna a kai."

"Ta ce,  Haka za ki yi ki yi bayan gidan. Sai ki murda nan ruwa zai fito ya kora shi. Nan kuma shima zama za ki yi ki danna nan zai yi miki tsarki. Ko ki fara gogewa da wannan (ta nuna mata tissue). Sai ki sa sabulu ki wanke da kanki. Kin gane? "

"Ta ce,  Eh ."

 To maza tube ki yi sai ki yi wankan. Ko in cuda miki baya?

"Ta ce,  A a, zan iya kada ki fama ni. Amma ba zan iya shiga wannan koramar ba ki zuba min a bokiti ."

"Duk dauriyar Jawahir sai da ta ji dariya. Ta ce,  Ba korama ba ce, amma tunda baki so bari in bude ruwan ya fita, sai ki kunna famfon ciki. Amma wannan famfon na zafi ne ."

Ta bude rariyar ruwan ya tafi. Ta kunna mata famfon ta dauko bokitin wanki ta cika mata sannan ta fita.

"Abida na durkushe bisa dan gadonta rike da ciki tana ta dariya, don duk tana jinsu. Jawahid ta kai mata duka ta falla aguje ta yi falo tana bawa Mami labari."

"Daga daki Daddy ya jiyota shima ya yi dariya, amma ya ciro wayar charger dinsa ya fito ya yi kanta, ta yi tsalle ta boye a bayan Mami tana  Na tuba Daddy Daddy Allah ya huci"

zuciyarka .

"Ya ce,  To kar in kara jin kina mata dariya in ta yi wani abun da baki sani ba, nuna mata za ku yi a hankali ba ki dinga yi mata dariya kina ba da labari ba ."

"Ta ce,  To Daddy ."

"[12/24/2019, 17:56] Takori: Haka ta yi jika-jikanta a tsaye cikin kwamin da bokiti, ta daga kafa za ta fito santsin kwamin ya kwasheta ya buga da kasa. Ta sake yunkurin fitowa ta sake shan kasa. Rahane ta ce,  Wannan bala i da me ya yi kama? Ta koma ta cure jikinta a cikin kwamin ta yi zamanta."

Jawahir ta ji shiru wajen awanni biyu tana zaune gefen gadonta tana jiranta. Da ta tabbatar ba za ta fito ba sai ta mike tana kwankwasa mata ban dakin.

"Daga ciki Rahane ta ce,"

 Ki zo ki fiddani na kasa fitowa .

"Jawahir ta murda kofar ta shiga ta kama hannayenta ta fito da ita, ta zari tawul ta daura mata suka fito."

Jawahir da kanta take shafa mata vaseline a hankali kada ta fama ta. Ta ciro wasu Pakistan ruwan kwaiduwar kwai cikin kayanta ta mika mata ta sa.

"Sai ta ga Rahane ta kasa sakewa a cikinsu, domin dai a wurin Rahane dogon wando sutturar maza ne."

"Ta ce,  Don Allah ki bani zani na atampa wadannan santsi garesu ."

"Jawahir ta yi dan jim, sai kuma ta bude wardrove ta dauko sabuwar danyar vlisco (Holland) dinta ta bata, ta daura mata zanin, ita kuma ta sa rigar. Ta taimaka mata ta daura dan kwalin, sai ta yi kyan gani."

"Lokacin ne Mami da Dacta suka shigo. Dacta rike da gorar ruwan Myer da ledar magunguna fara mai tambarin AKTH. Yana tafa hannu ya ce,"

 Yar Dacta! Kin yi kyan gani kamar ba ke ba .

"Ita dai murmushi ta yi, ta zame daga tsayuwa gaban Jawahir ta durkusa a gabansu. Da sauri Mami ta dagota ta zaunar da ita a bakin gadon Jawahir tana cewa,  Ki daina yin wannan durkuson mu mun yafe, ko da fatar baki ki gaishe mu kin ji? "

"Ta sunkuyar da kai kawai. Mami ta karbi gorar ruwan a hannun Baba Dacta ta murda tana juyewa a tambulan mai garai-garai, shi kuma yana ballo mata magungunan da ya kamata ta sha a lokacin."

"Daya bayan daya yake sa mata kwayar maganin a baki Mami na binsu da ruwa, aikinta kawai hadiyewa.."

Dai-dai lokacin da aka kira sallar magariba. A ka idar gidan duka tare suke yin sallah in har suna gida. Baba Dacta ne ke jan su.

"To yau ma hakan, karo na farko da Rahane ta taba yin sallar jam i a rayuwarta. Sai ta ga banbance-banbance da yawa da irin sallah da alwalar da suke yi a kauye."

"Ashe su kawai dungurawa suke yi su mike, babu irin wannan karatun sallar mai dadi da Baba Dacta yake yi, basa bin ka idoji da sharuddan da aka wajabta a kan sallar."

"Sannan bayan an sallame isha i, sai an dora da shafa i da wutiri. Sannan ayi hadaka wajen cin abinci a kan tebir. Wanda ba ta san wa ya dafa ya jera su a kan tebir din ba, ita dai kawai ta gansu, ta san kuma ba Mami ta yi ba don suna tare da ita."

"Daga nan kuma ta ga su Jawahir sun dauko wasu jakunkuna cike taf da litattafai har Aziza ta dauko nata, suka zube gaban iyayensu."

"Nan da nan suka canza harshe daga iyayen har  ya yan suna ta koya musu ayyukan makaranta. Jawahir ce ke tare da Daddy, ya yin da Abida da Aziza ke tare da Mami. Turanci suke yi zallah ba irin wanda ake musu a TAKAI SPECIAL PRIMARY ba."

"Sha awa ta kama Rahane, sai ta ja gefe ta tattara hankalinta a kansu, jefi-jefi Baba Dacta kan kalleta yana kuma sane da yadda ta kafa musu ido babu ko kiftawa."

"Karfe tara saura minti biyar duk suka rufe litattafan suka maida su jakunkunansu, suka diba suka yi dakinsu."

"Shi kuma Baba Dacta ya mike cikin tuma-tuman kujerun falon irin leather seats din da ko allura ba ta iya huda su, ya murdo labaran kasa na N.T.A yana sauraro."

"Kalar kujerun Orange and Black. To haka tattausan kilishin da aka dora akan farin marbles shima ruwan goro ne da ratsin baki, labulayen kuma light orange."

"Mami daki ta nufa ta yi wanka ta fito cikin shiri, lab coat dinta fara kal da farin gilashi da hand bag rike a hannayenta. Yau aikin kwana gareta a dakin yara na Isyaka Rabi u (Paediatric-Unit)."

"Ta russuna ta sumbaci goshin Baba Dacta, ta shafa kan Aziza dake barci a kan cinyarsa, ta dubi Rahane dake satar kallon su suna bata sha awa ta ce,  Ni na tafi aiki Rayhana, dauki Aziza kuje ku kwanta, da wuri ake barci saboda zuwa makaranta ."

"Ta mike ta ce,  A dawo lafiya . Ta dauki Aziza a cinyar Daddy ta yi dakin su Jawahir."

"Likitocin biyu suka bita da kallo cike da tausayi. Mamin ta fita, Dacta ya ci gaba da sauraron labaran tara cike da tunanin hanyoyin da zai bi ya inganta rayuwar Rayhana, wadda Allah ya sanya mishi kaunarta kamar, koma fiye da yadda yake kaunar su Jawahir."

Tana shiga dakin karamin gado ta dora Aziza wanda ta fahimci shine nata. Abida da Jawahir sunyi wanka sun wanke baki sun sauya kaya zuwa marasa nauyi wanda a ganinta kayan maza ne (wando).

"Abida ta balla mata harara ta ce,  Ga (diaper) nan ki sa mata . (Tana nufin Azizah)."

"Ta yi sukuti tana kallon ta don ba ta san wani diaper ba. Haushi ya kashe Abida, ta tashi da kanta ta sa mata."

"Rahane na tsaye saboda haushin da ta bata ba ta san sanda ta hankade ta ba, saura kadan ta bugu da karfen gadon Azizah."

"Jawahir ta ce,  Abida mene ne haka? Wannan ai rashin mutunci ne .

Please Login or Register in order to submit comment