gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading SARA SA SASSAƘA Ƙiyayyar Gado By Aisha Adam Chapter 15 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da maimaita faɗin "Tambayoyi? Ni za ka yi wa tambayoyi na baka amsa? Shikenan ina jinka faɗi"

"Suwaye iyayen Alina na haƙiƙa?"

Ta yi shiru tana ɗan kaɗa kanta, sannan ta ɗago fuskarta ɗauke da murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa ta ce "Kai da uban gayyar yake hannunku, yaya za ku zo ku na tambayata?, ai shi ya fi kyautuwa ku je tambaya? Shi ne yake da amsar tambayar ba ni ba"

Mega ya tsuke fuska, saboda yadda ya fara ƙuluwa da murmushin da take yi, ya ce "Ke nake tambaya yanzu"

"Ba ka da ikon tambayarsa, saboda an killace shi an hana ka ganinsa ko? Haryanzu fa ba ma a yarda da kai ba, na cewar ka kama Kacalla Sumale ba. Sannan ba ka da tabbacin yana ina a halin yanzu. Na san ka fara jin kanka kai wani jarumi ne, saboda ka kama shi, tabbas ka cancanci jinjina na ɗan lokaci, dan babu wanda ya taɓa gano gaskiya da ka gano a cikin duhu, sai dai gaskiyar ta suɓuce a hannunka, kuma ita ma ta yi duhu ta sake ɓacewa ganinka a cikin duhun.
Wannan kuskuren da ka yi zai iya zama ajalinka, dan duk wanda ya gano shi, sai ya kawar da shi daga doron duniya, idan ba wanda ya yarjewa ya gano shi ba. Abu na gaba kuma muddin Kacalla na rayuwa a doron duniya, zai iya zubar da kowane irin jini, zai kashe kowane ne, domin Alina! Ka tafka babban kuskure mai muni da hatsari gare ka da rayuwarka" Gaba ɗaya suka yi shiru su na kallonta.

Ta jinjina kai ta ce "Ƙwarai, zai ci gaba da bibiyarka, zai yi farautarka babu dare babu rana, saboda ita. Kacalla Sumale ya shallake duk yadda ka ke tunani, yana da abin da baka tunani. Ni kaina a tsawon lokacin da na riƙe Alina da ina da hali, sai na ba ta guba na kashe ta, saboda tsananin kishin yadda yake ƙaunarta fiye da ransa. Sai dai ina kyautata zaton baƙin alhaki ne yake bibiyarsa, saboda iyayen Alina ne jini na farko da Isma'il ya fara zubarwa a Duniya da hannayensa!"

Tsit suka yi gaba ɗaya su na jin ta, tare da yin jarumtar ɓoye mamakinsu, mussaman ma Mega.

Alfa ya ce "Ke ban gane ba, iyayenta ne mutane na farko da ya fara kashewa, to ta yaya aka yi ya ɗauke ta ya riƙe ta? Suwaye iyayen nata? Sannan kema kuma wace ce? A ina sauran ahalinta suke?"

"Wannan tambayoyin duk shi ne zai ba ku amsar su. Abin da ba ka sani ba shi ne, Ismail ya san waye kai. Shi ne ya kashe Malam Ɗayyabu bayan da ya yi masa ƙarya. Bai yi maka komai bane ba, saboda gudun halin da Alina za ta iya shiga. Sannan ai ina aikinka a kansa ne kawai, tun da ka gama aiki a kansa babu buƙatar ka zurfafa a kan Alina babu ruwanka da ita.
Ka sani ya gama tsara komai, a kan matakin da zai iya ɗauka a kanka, bai kai ga aiwatarwa ba, ka riga shi motsawa. Ina mai baka tabbacin zai fita, dan Kacalla Sumale ba mutum ɗaya ba ne ba, mutane da dama masu burin cimma muradai daban-daban a cikin mutum guda, kuma muddin ka na yawo a doron ƙasa ko shi ko na cikinsa za su hallaka ka, saboda ka gano abin da duk wanda ya gano mutuwa yake yi.

Har ya buɗe baki zai yi magana, ya jiyo muryar mai tsaron Nadiya ya ce "Oga Mega time fa ya yi, kar a zo a kama mu, daga ni har ku mu shiga matsala"

Mega bai iya cewa uffan ba, ya miƙe tsaye,, Alfa kansa bakinsa tambayoyi ne a ciki, gaba ɗaya maganganun Nadiya sun ɗaure musu kai, amma haka suka yi waje suka bar gurin.

Mega ya dafa kafaɗar Mai tsaron ya ce "Thank you Nelson"

"Welcome sir" Ya yi maganar cikin girmamawa yana yi wa Mega murmushi.

Yadda yake tafiya yana dukan ƙasa da ƙafafuwansa, tamkar ƙasar ce ta yi masa laifi. Ba tare da ya sani ba, haka yake ta wani irin huci, tamkar zai shiɗe saboda tashin hankali.

Sai da suka ƙarasa office ɗin su Mega, Ammar ya rufe ƙofa ya dubi Abdallah ya ce "Mega wata sabuwa in ji 'yan caca, ka yarda da maganganun matar nan kuwa?"

Ya jinjina kai ya ce "Biri ya yi kama da mutum, but was fooled Alfa, meyasa tun da muka kawo shi, bamu sake ganinsa ba ko jin inda yake ba, aka hana mu ganinsa mussaman ma ni da muka yi aikin tare da sauran jami'an?"

Alfa ya ce "Yes tambaya ce mai ma'ana, amma ni ban ji na yarda da ita ba, amma ni abin da ya bani mamaki, meyasa ya kashe iyayen yarinyar? Me kuma ya sanya ya ɗauke ta ya riƙe, yake yi mata irin wannan mugun so? Kai Mega akwai maganganu da dama a bakin matar nan da suke buƙatar fashin baƙi. Suwaye mutanen da suke cikin Kacalla Sumalen, suwa yake yi wa aiki?...

Ayshercool
08081012143


Downloaded From https://arewanovels.com


Please Login or Register in order to submit comment