You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
fita amma haryanzu ba ta dawo ba.
Ya ce "To ki kira lambar wayarta mana"
"Na kira bata shiga, Ubangiji Allah ya shirya mini wannan yarinya, ni duk godiyata ga Allah da ya zamana ba wani abin ashshan take aikatawa ba, amma 'ya mace dole sai da saka ido ai"
Saddam ya ce "Mhmm, In dai Laila ce, tana can neman abin wallafawa a shafukanta ne, za ta dawo na san, iyaka idan ta dawo ki zane ta wallahi"
"Ba zan dake ta ɗin ba, ziga zigi" Mama ta yi maganar tana hararsa.
Ya ce "Daga bayar da shawara? Allah ya baki haƙuri ai kun fi kusa"
Sai dai abu kamar wasa, har magariba babu Laila babu dalilinta, wanda hakan ne ya ƙara ɗaga wa Mama hankali, ba ita ba har da Saddam, babu shiri ya fita yawon neman ta.
Ga shi ita ba ƙawaye ne da ita ba, babbar ƙawarta Murja su na gama makarantar Sakandire aka yi mata aure, maƙwabciyarsu ce, da aka yi mata aure sai ta ci gaba da abotar da Bala, wanda yake Yayan Murja, wanda shi ne ya sanya mata sha'awar harkar sarrafa waya da kuma aikin jarida.
Laila ce rufe a cikin cell, sai rarraba ido take yi, ta kalli yadda duhun magariba ya fara yi. Ta jijjiga ƙarfe cell ɗin ta ce "Yallaɓai ka yi wa Allah da ma'aikinsa ku sake ni na tafi, babata dattijuwa ce ba ta da cikakkiyar lafiya, hankalinta yana nan a tashe na sani. Wannan kamun da ku ka yi mini kun take mini hakkina fa"
Babu wanda ya kula ta, daga cikin office wani ɗan sanda ne a zaune, sanye da uniform ya ɗaga wayarsa ya daddana ya saka a kunnensa.
"Allah ya taimaki honourable"
"Yauwwa ya aikin?"
"Alhamdillah, game da yarinyar nan ne, haryanzu ba ka ce komai ba"
Honourable ya ce "Eh ina sane, ku ajiye mini ita sai na waiwaye ta. Ba dai ba ta da kunya da mutunci ba, za ta gane ba ta da wayo ku ajiye ta sai na waiwaye ta."
Ɗan sandan ya ce "Na fahimce ka sir, amma ka san yarinyar nan mutane sun fara gane ta a shafukan sada zumunta, idan abu ya bayyana ka saka an tsare ta, kar abu ya zama surtu"
"Ba na san aikinka ba ne?"
"Sorry sir"
"Ka ajiye ta sai na waiwaye ta, zan saka maka kuɗin mai"
Gidan su Laila kuwa kwanan tsaye Mama ta yi, saboda rashin Laila a gida. Tuni Saddam da Bala suka kai ɓatan Laila gurin jami'an tsaro.
Da sassafe Bala ya zo musu da labarin tana gurin 'yan sanda, dan haka Saddam ya zo su je.
Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yanzu Laila ce ta kwana a hannun 'yan sanda me ta aikata har haka?. Ba zan iya zama a gida ba, mu je tare kawai"
Saddam ya dubi Mama ya ce "Dan Allah ki yi haƙuri ki zauna a gida, wallahi ko mun je babu abin da za ki yi, ki bari mu je mu gano tukuna"
"In kwana yarinyar ba ta gida, ta kwana a hannun 'yan sanda ka ce mini ba zan bi ku ba"
Bala ya ce "Saddam ina ga ka bari kawai mu je tare, hankalinta sai ya fi kwanciya"
Ba dan Saddam ya so ba, ya ƙyale Mama ta yafo mayafinta suka tafi.
*****
Alina na ta son sake tambayar Nadiya, inda za su tafi idan sun bar garin, amma ta fasa ganin yadda Nadiya ta nuna mata ba ta son tambayoyin.
Sai da Nadiya ta dangana da kai Alina Asibiti, aka bata magunguna da allurai, suka taho gida.
Da kyar Alina ta yi sallar isha'i ta kwanta, saboda baccin da take ji, a sakamakon magungunan da ta sha.
Baccinta ya yi nisa, ta din ga jin motsi da ɓuruntu a cikin gidan, a hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idonta. Gani ta yi an haske ta da wata irin fitila mai matuƙar haske, sai ta kasa tantance mafarki ne ko gaskiya.
Muryar Nadiya ta ji tana faɗin "Kar ku taɓa yarinyar nan, wallahi ba za ku iya ganin bayan Ismail ba. Babu ruwanku da ita. Ba dai shi ka ke son ka kama ba, ka kama shi, amma kamun da ka yi masa shi ne kuskure mafi girma da za ka aikata a rayuwarka".
"Shut up, da harbina za ki yi kenan?"
"Dole na kare kaina, abin da baka sani ba, tuntuni Isma'il ya san wane ne kai. Kar ka yi abu da ka, baka san abubuwa da yawa ba, zaka aikata mummunan kuskure"
A hankali Alina ta buɗe idanunta, ta yinƙura, ta miƙe tsaye a razane da ƙarfinta, tana son ganin suwaye suke wannan jayayyar da Nadiya, ammaba ta kai ga hakan ba, ta ji an shaƙa mata wani hankici ta baya, take ta ji ɗiff ta daina gane komai. Duhu ya ƙara mamaye ganinta.
1k ne a telegram.
Ayshercool
08081012143
*Jama'a Albishirinku, mun sake shirya tsaf domin kawo muku advance class, na koyar da sana'oi da muka yi firts batch, ga mu mun dawo domin kawo second batch, wanda zai kasance Advance class a kan na farko da muka gabatar*
*Ki na son fara sana'a, kin rasa yadda za ki yi? Ko kuma jarinki ne kaɗan kin rasa wace sana'ar za ki yi? To wannan classes ɗin naku ne, ku garzayo ku yi rijista domin kar a yi tafiyar nan babu ku. Daga sana'oin da za a koyar sun haɗa da;*
1. Graphic design
2. Magungunan mata
3. Sabaya
4. Turaren wuta
5. Fara
6. Candies
7. Skin care products
8. Importation
9. Snacks
10. Yoghurt
11. Oil perfumes
12. Bead work
13. Hair cream/oil
14. Dabarun kiwon kaji
15. Huluna
16. Spice's
17. Dabarun sana'ar kayan kitchen
18. Noma a zamanance
19. Dabarun kasuwanci
Dama ƙarin wasu, ga masu buƙatar sanin yadda tsarin yake kai tsaye su tuntuɓi wannan lambobin.
08081012143
08069611181
07037977211
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
SARA DA SASSAƘA...
YOTA 002
AYSHERCOOL
Page 15
Hankalin Maman Laila ya yi mummunan tashi, ganin a inda Laila take.
A babbar headquarter yan sanda ta jiha aka kai ta. Shi ma sashen da aka kaita, aka gaya musu wanda case ɗin yake hannunsa baya nan sai dai su jira.
"Yanzu Saddam a gurin nan duk maza yarinyar nan ta kwana? Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Wai laifin me ma ta yi ne?"
Saddam da ransa yake a ɓace shi ma ya ce "Mama tare da ke fa muka zo gurin nan, nima ban san abin da ta yi ba, sai dai mu jira mu ji me za su ce"
Bala ya ce "Ki yi haƙuri Mama, da yardar Allah yau zamu tafi da ita."
Duk magiyar da Mama ta yi, aka hana su ganinta. Har azahar su na gurin a zaune, sai bayan azahar wanda case ɗin yake a hannunsa ya zo, shi ma da ya zo ya ce musu su na da meeting da IG dan haka su ci gaba da jira.
"Wallahi ban da mahaifina ma ɗan sanda ne a cikin aikin ya mutu, da sai na tarkata su na tsine musu wallahi yan wahala"
Bala ya ce "A'a Saddam kar ka yi abin da za su ƙara shanya mu, kuma kowane aiki akwai ɓata gari, wani abin kuma yanayin aiki ne a haka, ba za a karya dokar aiki domin a burge ka ba"
Saddam ya ja uban tsaki kawai yana sake turɓune fuska.
Sai bayan la'asar aka saurare su, aka fito da Laila, fuskarta duk cizon sauro.
Cikin nutsuwa ɗan sandan yake kallon Mama, ya ce "Hajiya yarinyarki ba ta ji gaskiya. Ta je ta taɓa manyan mutane, ta ce da saka hannunsu ake ƙwacen"
Cike da takaici Mama ta ce "Laila, idan ba ki kiyayi rayuwa ba, wataran sai kin janyo an kashe mu. Allah wadaran wannan harkar jaridar taki. Wallahi ranka ya daɗe, babu irin jan kunnen da ban yi mata ba, a kan ta yi haƙuri ta bar wa Allah ba, amma ta ƙi. Ku dubi girman Allah ku yi haƙuri. Marainiya ce kuma 'yarku ce, mahaifinta tsohon ɗan sanda ne yarku ce"
Ya kalli Laila ya ce "Yarinya, kina da ƙanan shekaru, ki mori rayuwarki ta hanya zuba ido ga duk abin da ba ki da ikon gyara shi, idan ba haka ba, wahala za ki sha a banza." Laila ta sunkuyar da kai ta ƙi magana.
Ya daddana waya ya kira wata lamba ya kara a kunnensa. Bayan sun gaisa ya ce "Honourable batun yarinyar nan ne, dan Allah a yi haƙuri, ga mahaifiyarta tana ta kuka tana bayar da haƙuri, dan Allah su na neman belinta"
"Kar ka kuskura, ba zai yiwu ba, ai sai na banbance mata aya da tsakuwa, ko da wasa aka sake cewa ta fito ta yi soki burutsu irin wannan ba za ta yi ba"
"Amma ga mahaifiyarta a gurin ba dan ita ba...
"Babu ruwana na gaya maka, sai na wulaƙanta yarinyar nan, za ta ga ƙarshen rashin hankali" Ɗan sandan ya kashe wayar.
Mama ta riƙe haɓa, ta ce "Yanzu a kan wannan yar da ya haifa yake iƙirarin zai wulaƙanta? 'yar da ya haife ta? To Allah ya kyauta idan Allah bai wulaƙanta ta ba, babu wani wanda zai wulaƙantata"
"Shiyasa ake cewa, ku din ga ja wa yaranku kunne, ku din ga ba su tarbiyya su din ga iya bakinsu"
"Ku yi mata duk abin da za ku yi mata, kai ka ga alamar rashin tarbiyya a tattare da ita? Tsawon shekaru mahaifinmu na yi wa ƙasa hidima aikin ɗan sanda, ɗan abin da ya mutu ya bar mana, wasu sun yi kashe mu raba a tsakanin su, kuma a ce kar mu yi magana ƙasa za mu ci mu rayu? Idan hidimar wani ta tashi a cikinmu wani zai yi mana ne". Saddam ya ƙarasa maganar jikinsa yana rawa saboda baƙin ciki.
"Kai, ka zo har gurin aikin nawa ka nemi ka gaya mana magana, yaran talakawa tarbiyyar ce da ku? Zan saka a rufe ka wallahi"
"Ba rufe ni za a yi ba kashe ni za a yi" Bala ne ya danƙi hannun Saddam suka yi waje, yana rarrashinsa.
"Saddam mutanen nan, wasu ba mutunci ne da su ba, babu Allah a ransu. Ka rabu da su, na san abin da zan yi, ko ba yau ba zuwa gobe in Allah ya kaimu, Laila za ta fito"
Haka ya rarrashi Mama ma, suka sai Abinci aka ba wa Laila suka koma gida, ya din ga basu ƙwarin gwiwa a kan yana da hanyar da zai fitar da ita.
Tun da suka koma gida, daga Saddam har Mama babu wanda yake walwala. Duk da Mama na ta faɗan halin Laila na azabar kafiya.
Shi kuwa Saddam daga baya bai ga laifin Laila ba, dan yarinya ce mai sauƙin kai mara hayaniya, amma akwai kafiya, kuma duk abin da ta wallafa ya san tana da cikakkiyar shaida da hujja a kan abin da ta yi.
Bala kuwa shi ma rubutun ya wallafa a shafinsa, da bayanin cewar an kama Laila, saboda maganar da ta yi da sunayen yan siyasar da kama, da cewar an haɗa kai da su ana ƙwacewa mutane filaye.
Duk da wasu na jin haushinta, amma kasancewar ayyukan da take yi a shafinta ba siyasa bane kawai, ta kan faɗakar, koyarwar addini, girke-girke motivational speaking, idan baka ƙaru da ita ta wani fannin ba, za ka ƙaru ta wani, dan haka nan da nan mutane suka din ga reposting abin da ya faru.
****"
A hankali ta motsa, ta yinƙura domin tashi zaune, amma ta koma yuuu saboda wani irin azababben jiri da ciwon kai da ya ɗebe ta. Ta buɗe idonta a hankali ta din ga gani dishi-dishi, ga kanta da yake yi mata wani irin azababben ciwo.
Ta koma ta kwanata ta yi lamo, a hankali komai ya fara washewa. Ta kalli gurin ɗaki ne na Asibiti, da gadaje kusan biyar a ciki, sai dai itakaɗai ce a ɗakin. Ga hannunta ɗaya sanye da ruwa.
Hayaniya ta din ga jiyowa sama-sama, ana wani irin yare ana haɗawa da broken English.
Sai kuma ta ji ɗif an daina sai alamar takun takalma.
Ƙofar ɗakin aka buɗe, maza ne suka shigo zabga-zabga, sanye da kaakin soja a jikinsu. Sai dai a wanda suka shigo ɗin duk ya kere su a tsayi. Wandon sojoji ne a jikinsa, sai riga armless shirt army green. Gefen wandonsa a soke da wata 'yar ƙaramar bindiga.
Ya ɗan tara suma a kansa, sai dai yanayin askin gaban kan tafi cika, zagayen kuma kwantacciyar suma ce, gwari-gwari dai yanayin askin da ake kira da balatoli. An yi wani abu mai kama da arrow a gefen kan. Babban abin da ya sake jan hankalinta bai wuce sarƙar da take wuyansa ba, da ya zura ta a cikin rigarsa, amma saman chain ɗin ba za ta manta da shi ba, lokacin da ya zo tana Asibiti amma ya musa mata, ya ce ba shi ba ne. Gefensa wani matashin ne da za su iya yin tsawo ɗaya da shi, hatta askin kansu iri ɗaya ne, sai dai kowanne kamarsa daban. Sai dai ta tuna ranar da ta je sayen leda shagon Mamman da yamma ta gansu tare.
Kenan duk tsawon wannan lokacin da take ganinsa, wani abin ne shi daban ba abin da take tunani ba? Ashe Yaya Ismail ya fita gaskiya.
Tana nan kwance suka ƙarasa har gaban gadon take, sai dai tana kwance kamar an dasa ta, ta kasa komai. Suka ƙarasa suka kewaye gaban gadon take. Gani ta yi tamkar an canza shi, gaba ɗaya ya juye daga Mamman ɗin da ta sani, suka shaƙu, da suffarsa da kamaninsa sun koma wani abu na daban. Fuskarsa a tsuke tamkar bai san hanyar inda ake bi a yi dariya ba, babu alamar annuri, sai ɗan rarraba manyan idanunsa yake yi da suka ɗan kaɗa suka yi jawur, duk da idanunsa sun saba ba ta tsoro, amma sai ta ga gara lokacin da ta san shi a Mamman, babu alamar afuwa ko sassauci a cikin waɗannan idanuwan.
Wannan gashin na fuskarsa ma babu shi, fuskarsa tas take sai ɗan yarfin gashin baki kaɗan. A hankali take buɗe idonta tana lumshewa.
Ya riƙe ƙugunsa yana kallon drip ɗin da yake shiga jikinta ɗis-ɗis. "Kai Mega kamar haryanzu she's unconscious"
"Yeah" Ya faɗa a taƙaice, ya janyo side drower, ya ɗaukko file ya buɗe ya yi dube-dube, ya duba ya ɗauki ya biro, ya yi rubuce-rubuce a cikin file ɗin, ya mayar ya ajiye. Ya duba cikin kayan maganin da ke gurin, ya ɗauki wata allura, ya zuƙe ya fara zubawa a cikin drip ɗin.
Miƙa ta yi tana yamutsa fuska, jin yadda shigar ruwan, tare da allurar ya burkita mata jiki gaba ɗaya, ta ji wani irin raɗaɗi, ƙoƙarin tashi ta yi saboda yadda allurar ta gigita ta. Ya saka hannayensa ya danne ta. A hankali jikinta ya saki, bacci ya ɗauke ta.
Alfa ya ce "Mega, me ka ke yi mata haka kuma? Kar fa ta ƙarasa"
Mega ya ce "Shut up" Ya yi maganar yana ɗan zaro masa ido.
"An ƙi ɗin, ka san zuwa gobe in Allah ya kaimu Oga Musa za su zo, su ganta"
Ya kalli sauran sojojin da suka zo tare, ya yi musu alama da su fita. Bayan sun fita ya dubi inda Alina ke bacci ya ce "Ta na da magrine headache, tana cikin damuwa da kuma tsoro. Akwai buƙatar ta huta sosai ƙwaƙwalwarta ta samu nutsuwa. Sai ta zama stable ne za a iya samun bayanan da ake buƙata daga gare ta"
Ammar ya jinjina kai cike da gamsuwa.
"To yanzu what next?"
"Eh, zamu je gurin matar nan, ina son grabbing wasu abubuwan daga gare ta, ina buƙatar tattaunawa da ita"
Ammar ya yi shiru yana kallon Alina, ya kalli Mega ya ce "Omega, ka san tsabar soyayya kun fara kama da yarinyar nan?"
Tsaki Mega ya ja, ya saka ƙafarsa ɗaya, ya daki ta Ammar da ƙarfi tare da furta "You are not serious" Ammar ya biyo shi yana murmushi ya ce "Wallahi sai na rama"
*****
Laila na zaune a cikin cell, wani ɗan sanda ya buɗe ta ya ce ta fito. Ta tashi jiki a sanyaye ta fito.
Ɗan sandan jiya ne ya saka aka kawo mata kayanta ya dube ta ya ce "Kin ci sa'a, an bayar da umarnin gaggawa a sake ki, idan kin ga dama ki je ki ci gaba da iskanci. Ku ba 'ya'yan kowa ba amma kun fi kowa rashin mutunci. Kuma a nan da awa arba'in da takwas, ki koma ki yi video ki ba wa Honourable da sauran mutanen da ki ka kama sunansu, haƙuri ko kuma abin da zai biyo baya ba zai yi miki daɗi ba" Ba ta ce komai ba, ta karɓi jakarta za wayoyinta, ta fito reception, ta waiwaya ta kalli ɗan sandan ta ce "Na gode sosai Sir, abin da ya faru da ni ya ƙara mini ƙwarin gwiwar gwagwarmaya, ka gaya wa Honourable zan yi video na ba shi haƙuri. Ba zan sake ba 'ya'yan talakawa mun bar wa masu duniya su ci gaba da cin jahannama a cikinsu"
"Laaa" Ɗan sandan ya faɗa bakinsa a sake.
"Sir yarinyar nan fa ba ta daku ba"
"A'a ki je ga ki ga su nan ai, a banza za su illata rayuwarki, babu abin da aka isa a yi kuma, sauka lafiya"
Ɗaya ɗan sandan ya ce "Ikon Allah, gaba ɗaya fuskarta ta salihai ce"
ISP Sagir ya ce "Ta munafukai dai, ni na yi mamaki, daga sama fa aka bayar da umarnin sakinta"
Suka ci gaba da tattaunawa, Laila kuma ta tsare abin hawa ta tafi gida.
*****
Ɓangaren su Rahama kuwa, dawowar Sadauki inda ake tsare da su, ya ɗan sama musu sassauci, ana ba su Abinci an daina dukansu.
Tun da macijin nan ya sari Rahama, ba ta sake taka ƙafarta ba. Sai dai yau da ya dawo daga yawonsa, daga nesa da su kaɗan ya tsaya a kan babur, ya yi mata nuni da ta zo. Ta kalle shi ta kalli ƙafarta, ya sake yi mata alamar ta zo. A hankali ta yinƙura ta daddafa bishiya, ta miƙe ta tsaya ta ji ƙafafunta tamkar an ɗaura mata duwatsu.
"Ta ko da Bismillah, da sunan Allah" Ya yi maganar yana zuba mata ido, ta fara takawa a hankali cikin tsoro, yana zaune a kan babur ɗin yana kallonta. Ji take yi tamkar ta faɗi, amma ta daure ta ci gaba da takawa har ta je inda yake ta tsaya, tare da sunkuyar da kanta.
"Yayi kyau,koma ki je ki zauna" Ta sake juyawa ta koma, har za ta zauna cikin ɗaga murya ya kira sunanta "Rahama"
Ta waiwayo. "Waa ɗoo" (Zo nan)
Ta sake dawowa, sai cukuikuye jikinta take yi a cikin babbar rigarsa da ya bata.
"Ya jikin naki?"
"Da sauƙi"
"Alhamdillah, ba wata matsalar?" Ta jinjina kai.
Ya ce "Ba ki da baki ne?"
"Babu matsala" Ta yi maganar tana sunkuyar da kai.
"Allahumma yashfiki, je ki zauna Allah ya sauwaƙe. Je ki ki zauna"
Ta amsa da Amin, ta juya za ta tafi.
"Ke zo nan" Ta waiwaya ta sake tsayawa.
"Duk abubuwan alkhairin da na yi miki, babu ɗaya da za ki iya cewa kin gode?"
"Na gode"
"Wuce ba na so" Ya yi maganar yana kafe babur ɗin sa ya sauka daga kai. Ita dai ba ta sake cewa komai ba, ta koma gurin zamanta ta zauna.
*****
Arewapen
Zaune suke su biyar a cikin office ɗin, kowannensu sanye da kaakinsa na aiki. Sun baje wani map a kan table su na dubawa.
Ɗaya ya numfasa ya ce "Haryanzu mr. President, da al'ummar ƙasa, su na jiran ji daga gare mu, duk da pressure da aka saka mana, dole ne mu yi amfani da hikimomi da dabaru, dan kar rayuwar yaran ta salwanta"
Suka amsa da gaskiya ne.
"Commadore Edward, za mu jira, ku duba mana exact gurin da yaran suke, mu kuma za mu shirya duk abin da yakamata. Duk wani abu da zamu yi, za mu yi shi ne within 8days, mu fitar da kyakyawan result"
Commadore Edward ya ce "Babu case, komai zai tafi yadda aka tsara, akwai yiwuwar su canza guri, muddin suka farga mu na neman inda suke. Amma gano inda suke ɗin shi ne babban target, ba wani abu"
Suka kammala tattaunawa, suka yi musabaha da juna, sannan suka naɗe map ɗin suka bar office ɗin.
*****
Laila ce ta yi sallama a gidansu, Da sauri Mama ta fito daga kitchen, cike da son tabattar da Lailan ce. Tana tozali da Laila kuma sai ta tsuke fuska. "Sun ga dama sun sako kin kenan?" Laila ta jinjina kai ba tare da ta yi magana ba.
"Yanzu kin ga sakamakon mai bijire wa maganar iyaye ko? Babu yadda ban yi da ke ki bar maganar nan ba, amma ki ka ƙi. Ke ba kowan kowa ba, ba ki da wani gata sai na Ubangiji, amma fitina ta yi miki yawa Laila. Ni dai lafiya na rabu da iyayena da mijina, balle na ce ko hakkinsu ne yake bibiyata ya sanya ba kya jin magana ko kaɗan.
Saddam da shigowarsa kenan, ya ce "Haba Mama dan Allah, daga dawowarta ki yi haƙuri ta huta ta ci abinci mana"
Mama ta juya kansa da faɗan "Ba zan bari ta huta ɗin ba, ni kwana biyu a jere hutawar na yi? Yanzu abin arziki ne a ce mace ta kwana a hannun 'yan sanda har kwana biyu, gurin 'yan sandan ma, sashen kula da manyan laifuk, ita ba kisan kai ba, ba fashi ba?"
Saddam ya yi wa Mama shiru, ya dubi Laila da take kuka, ya ce "Shigo ki zauna rabu da ita"
"Eh a rabu da ni mana, tun da ga mahaukaciya tana faɗa ko? Ku je ku yi abun da ku ka ga dama, babu mai kashe ni lokacina bai yi ba"
Saddam kuwa murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ki yi haƙuri, ɓacin ran kin kwana biyu a gurin 'yan sanda ne ya sanya take yi miki faɗa, amma ki yi haƙuri. Ina fatan ba su yi miki komai ba dai ko?"
"Sun mare ni" Ta furta tana sake fashewa da kuka. Saddam ya yi shiru yana kallonta, wani abu ya tokare masa a ƙirji, idanunsa suka yi ja. Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Kar ki gaya mata an dake ki, ki yi haƙuri ni na fahimce ki, hakkinmu ne aka danne, shi ki ke fafutuka a kai, zan taya ki da yardar Allah ko ba za mu yi nasara ba, duk abin da ki ke nema, ki yi mini magana zan taimaka miki, amma ki daina kuka ki yi haƙuri" Ta jinjina kai tana share hawayen da yake gangarowa a kan fuskarta.
Ya miƙe tsaye ya ce "Bari na je gurin Umman su Bala, na karɓo miki ruwan zafi ki yi wanka, ki ƙyale Mama ta gama faɗanta ta huce" Jinjina masa kai kawai ta yi ya fice.
*****
Sannu a hankali suke ratsa tsakanin ofisoshin, har suka ɓulla can wani ɓangare da babu wadatattun ma'aikata a gurin.
"Alfa, tun da muka kawo mutumin nan fa, ba a sake bari mun gan shi ba"
Alfa ya ɗan sosa girarsa ya ce "I wonder, ina ta so na yi maganar amma dai na yi shiru, amma kamar na ji Oga Musa kan ya tafi yana cewa, za a canza masa guri, maybe ma a bar garin nan da shi gaba ɗaya"
Mega ya ja ya tsaya, ya ce "A bar nan garin da shu a kai shi ina?"
Alfa ya ɗage kafaɗa tare da faɗin"I don't know"
"Amma kana ganin ya dace a yi hakan, ba tare da mun ji komai ba, mussaman ni da na yi duk ƙoƙarin?"
"And someone is taking the credit of your work ba, so sad. Na tausaya maka Mega"
Abdallah ya ɗan yi shiru sannan ya numfasa ya ce "We shall see" Ya ƙarasa maganar ana buɗe musu wata ƙofa, da gurin yake ɗauke da duhu.
Mai tsaron gurin ya sara musu, sannan ya sake buɗe musu wata ƙofa, mai kama da ta fursinoni. Suka ajiye wayoyinsu a waje, da bindigoginsu, aka caje su. Mai cajesun ya damƙo wani abu a aljihun Alfa. Alfa ya zura hannu ya ɗaukko ƙaramin biro a jikinsa, aka karɓi biron aka ajiye, sannan suka shiga.
Tana zaune ta takure guri ɗaya, tamkar mai taɓin ƙwaƙwalwa, ta ɗago ta yi musu kallo ɗaya, ta mayar da kanta ƙasa ta sunkuyar.
Abdallah ya gyara zaman hular sojojin da ke kansa, ya ƙarasa gabanta ya durƙusa yana kallonta.
Sai dai ta sunkuyar da kanta, ta ƙi ɗagowa su haɗa ido.
"Nadiya ko?" Ya furta yana tsare ta da idanunsa.
Ta ɗago a hankali ta dube shi ta ce "Au ba ka ma tabattar da sunan nawa ba?"
Mega ya girgiza kaiya ce "A'a, ina son sake samun tabbaci daga bakinki ne. Ina son zan yi miki wasu tambayoyi ne, da nake buƙatar ki bani haɗin kai, ki yi mini cikakken bayani"
Ta yi murmushi