gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading SARA SA SASSAƘA Ƙiyayyar Gado By Aisha Adam Chapter 11 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi"

"To kana ina?"

"Mun je wani aiki ne, lafiya dai?"

Cikin dakiya take ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta ce "Kana gida ne, ko kuma sun tura ku dawa?"

"Ummi wai lafiya kuwa? Ina lafiya fa wani aiki dai muke yi, ina tare da Mega, mun je aiki ne"

"Shikenan Allah ya tsare" Ta katse wayar ta nufi cikin gidan. Sai dai ba ta bari ta koma bacci ba, ta yi alwala ta tayar da salla.

*****

"Alina" Nadiya ta kira sunanta.

Alina ta ɗago manyan idanunta, ta dubi Nadiya.

"Ki daure ki sayo mana buredi a gurin Mamman, ki karya" Ta jinjina kai ta karɓi kuɗin, ta fita. Sai dai kantin a kulle, haka ma shagonsa. Alina ta nemi guri ta zauna ta yi shiru, har sai da ta gaji da zama, sannan ta tashi ta koma gida, ta ce wa Nadiya baya nan.

Duk yadda Nadiya ta so mazewa ta kasa, ta fita ta ƙwanƙwasawa maƙwabcinsu, ta sanar masa da halin da ake ciki.

Alhaji Sadi ya ce "Amma da mamaki, ni jiya sai bayan na dawo ake ce mini, wai yanayin unguwar kamar babu lafiya, an ga wasu mutane na ta kaiwa su na komowa, ba a san suwaye ba. An kuma sanar da 'yan sanda ba su ce komai ba. Amma bari na tuntuɓi Alhaji Sadi.
Ba a jima ba, maƙwabtan da suka rage ba su fita ba duk su ka tattaru.
Har su ka fara yi wa Nadiya faɗan, dan meyasa ba ta sanar tun a daren jiya ba. Nan aka fara bin diddigin abin da ya faru.
Duk wani bincike da mutanen layin suka yi, babu wani gamsashen bayani, a kan haƙiƙanin abin da ya faru daren jiyan, sai cewar kawai dai an fuskanci yiwuwar samun tashin hankali a lokacin.
Suka dangana har ga gurin Jami'an tsaro, sai dai 'yan sanda suka ce, babu wani abu mai kama da tashin hankali da ya faru a unguwar, kawai dai mutanen unguwar sun tayar da hankalinsu ne, amma batun ɓatan Yayan Alina za su duƙufa bincike a kai.

Alina kuwa gaba ɗaya a kwana ɗayan nan, ta yi zuru-zuru, tashin hankali ya addabe ta, ta kasa cin abinci kukan ma kuma ta kasa, ga shi ta kasa gaya wa kowa, balle ta samu sassauci. Babbar damuwarta duk ta san laifin nata ne, ita ta ƙanƙame Mamman ta janyo shi kusa da su.
Daga ita har Nadiya wunin damuwa suka yi da tashin hankali. Maƙwabta suka din ga shigowa yi musu jaje, tare da fatan Allah ya bayyana Ismail.

*****

Ji ya yi an watsa masa ruwa mai zafi a jikinsa. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, ya buɗe idanunsa a hankali. Dishi-dishi yake gani. Amma ya tattara nutsuwarsa har sai da ganinsa ya zama clear, sannan ya ɗago kansa a hankali yana ƙarewa gurin kallo.
Ya motsa ya ji shi a ɗaure tamau, tamkar huhun goro.
Ya sauke idanunsa a cikin na su.

"Ka farko kenan?"

Ya yi shiru yana ƙare masa kallo ba tare da ya yi magana ba.

"Ina fatan zaka sauƙaƙa mana, kuma sauƙaƙa wa kanka, gurin amsa dukkanin abin da zamu tambaye ka, ko mu nema daga gare ka"

Ya yi murmushi sannan ya ɗago kansa ya ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya, ya tsayar da kallonsa a kan Mamman,ya ci gaba da kallonsa ba tare da ya yi magana ba. Kawai ya sunkuyar da kai yana murmushi.

*****

Su na kitchen su na aikace-aikacen su, suka jiyo saukkowar Ummi daga kan bene, tamkar za ta ruso benen, cikin rige-rige, suka fito daga kitchen ɗin su na jiran jin ba'asin saukkowarta daga bene da gudu haka.
"Ummi lafiya kuwa?"

"Safiyya, Ruƙayya"

"Ruƙayya meyafaru da Rukayyan?"

"Wai 'yan bindiga sun shiga har makarantar sun tafi da yaranmu. Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Ku taso mini Amir ya ɗaukko mota mu tafi"

Na'ima ce ta ƙarasa ta riƙe Ummi, ganin yadda duk ta rikice, ta ce 'Ummi ya za a yi a je makaranta a sace ɗalibai, a ina ki ka taɓa jin an yi haka?"

"Ga shi a radiyo ina ji, an sace ɗalibai hamsin a makarantar su Ruƙayya"

Safiyya ta ce "Ummi dan zatin Allah ki kwantar da hankalinki, kin san halin da ki ke ciki, ai babu wanda ya tabattar da an sace har da Rukayya ɗalibai sun kusa dubu a makarantar su. Kuma ki bari mu tabattar"

"Wane tabattarwa kuma? Radio za su yi ƙarya ne?"

"To zauna, bari a taso Amir ɗin"

Safiyya ta yi gaba tana kiran wayar Ammar.

*****

PRESIDENTIAL RESIDENT

Faruk Kankiya ne yake kaiwa yana komowa. Jikinsa har tsuma yake yi.

"Your excellency, dan Allah ka kwantar da hankalinka, komai zai zo da sauƙi"

Cikin ɗaga murya ya ce "Halilu when? Abubuwa na taɓarɓarewa za a ce komai zai zo ƙarshe ta yaya? A mulkina a shiga har cikin makaranta, a shiga makwancin ɗalibai, a kwashe yara mata 'yan makaranta. Kuma ka ce na kwantar da hankalina how? How Halilu? Gaya mini kaf tarihin duniya a inda aka taɓa haka. Sai a zamanin mulkina. Ko yaƙi ake yi ba a taɓa mata da ƙanan yara. Amma ni matan aka kaiwa farmaki. A mulkina wannan wane irin baƙin tarihi ne?"

Halilu ya yi shiru yana sunkuyar da kai, cike da tsoro da razani.

"Nan da mintuna talatin, a tattara masu riƙe da muƙaman tsaro a ƙasar nan, idan ba za su iya ba, su ajiye mini aikina"

Halilu ya jinjina kai ya fita yana jin tamkar ya ƙwato daga bakin kura da kyar.

****
Taimama suka din ga yi su na kallon duk inda ta kama su yi salla. Tsananin baƙin ciki da damuwa ya sanya Rahama kasa zub da hawaye.
Wanda suke da shigar kirki a cikin su kaɗan ne, ga su a zube a dokar daji a gaban mutanen da ba muharramansu ba.
"Anya ba daga rayuwata ba ne babu sa'a?"
Ramata ta kalli kanta, tana ƙanƙame jikinta, zuciyarta na wani irin zafi. 'yan yaran cikinsu da basu wuce Jss 1 ba su na ta 'yan koke-koke ƙasa-ƙasa.
"Yaya Baffa zai ji, idan ya samu labarin an sace ni?" Ta sunkuyar da kanta tana jin wata irin fargaba na ratsa ta.

****

Shiru ta yi tana kallon wayar hannunta, ta rasa abin da ma yake yi mata daɗi. Cikin sauri ta janyo ɗaya wayartata, ta shiga shafinta na sada zumunta ta wallafa dogon rubutu.
Duk da iya ƙoƙarin da gwamanti take yi gurin kawo ci gaban ilimi, mussaman a yankinmu da ilimin yake da yake fuskantar koma baya, mussaman ga 'ya'ya mata, hare-haren ta'addanci ya fara yawa, wanda hakan yana nuna gagarumin koma baya ga yankin. #Bring back our girls". Daga haka ta yi posting ta ajiye wayar.
Sadam ne ya fito daga ɗakinsa yana faɗin "Ke Laila, kina ina? Yau kin yarda gwamantin taku ta gaza ko? Saboda abin kunya da Allah wadai, an je har cikin makaranta an sace ɗalibai, mummunan abu na farko a tarihin ƙasar nan, da ya faru a gwamantinku"

"Kai kuma murna ka ke yi da hakan kenan? Gwamnati fa ba ta mutum ɗaya ba ce, ta al'umma ce kuma kowane ɓangare yana da wakili...

Saddam ya ce "Ba wani gwamanatinku ta gaza kawai malama, yanzu zan hau na wallafa rubutu a facebook na yi tagging ɗinki kuma an yi abin kunya"

Mama ce ta ja tsaki, bayan ta idar da sallar walha da kyar, saboda surutunsu, da musun da suke ta , sai rafkanuwa take yi. Kofin silva ta jefawa Sadam ta hau shi da faɗa.
"Wallahi Mama na fuskanci kema yar adawa ce, duk lokacin da muke maganar siyasa da yarinyar nan sai ki goya mata baya, ki din ga kora ta. Da alama ke ma tana shaƙa miki tsari ne, aishikenan na bar muku gidan ma amma dai gwamantinku ta gaza Yasin"
Mama ta kalle ta ta ce "Kar ki kula shi, ƙyale shi tun da bai san ƙaddara ba"

*****
Sanye suke da uniform su huɗu a office ɗin, sai kuma ƙarami da babban ministan tsaro, sai kuma President Faruk Kankiya.

"Wannan tattaunawar da muka yi, ta zamo ta sirri, bana buƙatar manema labarai su ma san me muka tattauna. Kwanaki bakwai kawai na baku, ku nemo inda ɗaliban nan suke a dawo da su, kuma bana buƙatar ko ƙwarzane ya samu ɗaliba ɗaya. A yi ƙoƙari a tabattar da lafiyar wanda ba a ɗauka ba, a damƙa su a hannun iyayensu. Kwanaki bakwai kawai na baku. Akasin haka za ku ajiye mini muƙamai na na bawa wasu".

General Jalal ya ɗan yi gyaran murya ya ce "Mr. President tabbas wannan kuskurenmu ne, zan iya cewa sakacinmu ne ma da har wannan al'amari ya faru. Amma mu na mai baka tabbacin da yardar Allah, yaran nan za su kuɓuta. Amma muna neman alfarmarka mako guda ya yi kaɗan...

A fusace ya ce "7days Lieutenant General Jalal, 7days kawai ku ke da shi, akasin haka ku ajiye mini muƙamaina"

"Ok sir" Haka suka tashi sumi-sumi suka fice daga ofishin.

Su na fita Barwa ya ciro wayarsa ya daddana. Ya kara a kunnensa.

"Jagora barka da wannan lokaci"

"Barkanmu dai Barwa, bamu labari"

"Shugaba fa ya ɗauki zafi ba kaɗan ba, kwana bakwai kawai ya bayar a nemo yaran nan, ko su ajiye masa muƙamansa ciki har da ni"

Ya kwashe da dariya ya ce "Ƙaryar banza ce ƙiba a kunne, shi ya isa ma? Zan yi magana da Boss Ɓagwai, tun da shi ne God father ɗinsa, dole ya janye wannan maganar. Kana ganin yadda muka fara raba kan ƙasar ko? To ba a yi komai ba ma. Sai ya tattara hankalinsa a kan yaran can, za mu sake ɓallo masa ruwa, kai dai ku ci gaba da bin abin da aka tsara. Ka kwantar da hankalinka yara dai ba za su fito yanzu ba, ka zuba ido...

*****

Tuni labarin sace ɗaliban makaranta mata, kimanin hamsin ya cika gidajen rediyo da kafafen watsa labarai da na sada zumunta na ciki da wajen ƙasa. Duk inda ka buɗe babu abin da ake yi sai maganar, saboda abu ne da bai taɓa faruwa ba a tarihi.

Sai da su Rahama suka kwana guda curr, babu ko ruwa a cikin su, a kwana na biyu, aka bi su da ruwa ɗaya mutum biyu, sai buredi mai yanka-yanka kowa guda biyu. Ƙafafuwan Rahama suka kumbura sosai saboda azabar tafiyar ƙafa da suka yi. Inda suke daji ne sosai da sosai, sai dai saboda tsabar surƙuƙinsa ko rana ta take, bata wadatar dajin da wadattacen haske saboda tarin dogwayen bishiyu.

****
Alina ta yi wata irin mummunar rama, ta yi zuru-zuru saboda azabar tsoro da kuma tashin hankali.
Tun safe Nadiya ta fita ta koma gurin jami'an tsaro, domin jin ko akwai wani labari.
Alina na zaune ta yi zuru a tsakar gida, ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofar gidan su.
Jiki a sanyaye ta sanya hula a kanta, ba tare da ta tambayi waye ba, ta buɗe ƙofar gidan.
Turus ta yi bayan tozali da fuskar Mamman, kawai ta hau bin fuskarsa da kallo.
Fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "'yan mata, abin da ya faru kenan? Na je gida duba jikin Innata, na dawo Alhaji yake gaya mini an nemi Yaya Ismail an rasa"
Tsuruu ta yi da ido tana kallonsa, ta ma rasa me za ta ce masa gaba ɗaya.

"Ya na ga kina kallona a haka?"

Ta sunkuyar da kanta, sai a lokacin hawayen da ta gaza zubarwa ta samu damar zubar da su, zuciyarta na wani irin ƙuna da tafasa.

Cikin tausasa murya ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah za a gan shi, an je gurin 'yan sanda an sanar musu?" Ta jinjina masa kai kawai.

"Ki yi haƙuri dan Allah, ki daina kukan nan haka" Ta ɗaga fuskarta a hankali tana kallon idanunsa masu bata tsoro, a yau ta samu kallonsu da cikakken ƙwarin gwiwa, amma ta gaza furta komai. Sai dai da ta ƙara matsawa kanta ta fuskanci akwai wata ɓoyayyiyar fuska a bayan wannan fuskar da yake mu'amalantarta da ita...

Ayshercool
08081012143

1k ne a telegram 0069685771
Aisha Adam stanbic
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN


SARA DA SASSAƘA...
YOTA 002
AYSHERCOOL

Page 12

Turus ya ja ya tsaya cikin tashin hankali, bayan da ya kunna wayarsa ya ci karo da batun sace ɗalibai da aka yi. Cikin sauri ya kira wayar Ummi. Sai dai wayar ba ta shiga.
Cikin tashin hankali ya lalubi wayar Amir, sai dai ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. Cikin hargowa Ammar ya fara yi masa faɗa "Wani irin iskanci ne zan din ga kiran wayarka ka ƙi ɗagawa?"

Amir ya ce "Ba ƙin ɗagawa na yi ba wayar na mota...

"Dalla ina Ummi take? Me yake faruwa ne?"

"Abin da ka ke son tabattarwa ya faru, an shiga makarantar su Ruƙayya an yi garkuwa da ɗalibai hamsin, amma Alhamdillah luckily she's not among, mun je ɗaukko ta ni da Baba Sani, sai dai tana cikin tashin hankali sosai da sosai"
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, ya nemi guri ya zauna yana faɗin "Amir, ka tabatta tana lafiya babu abin da ya same ta?"
"Eh lafiyarta ƙalau, sai dai a tsorace take ne kawai"

"Shikenan take care, zan sake kira in sha Allah " ya kashe wayar yana hamdala.
Wayar ce ta fara vibrating, kira yana shigowa.
Ammar ya ɗaga wayar ya saka a kunnensa.
"Yaya ake ciki?"

Ammar ya numfasa ya ce "She's safe, ba ta cikin wanda aka sace"

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Alhamdillah"

"Wai komawar ka sake yi da gaske?"

"Eh, ai ban gama ba, alamu sun nuna akwai sauran rina a kaba"

Ammar ya ja guntun tsaki ya ce "Ka na da matsala Mega, wannan ɗin ma da aka yi, ba wani appreciation na kirki, ana ma doubting idan mai laifin ka kama. Ka kuma koma, ban san me ya mayar da kai ba kuma"

"Ba aikinsu kawai na koma yi ba, wannan aikina ne, ina son gyara ɓarnar da na yi"

Ammar ya ce "Kuma sun san da hakan? Sun san ka koma?"

"A'a. Akwai abin da nake bibiya ne, and ban bayar da wayarsa ba, tana hannuna ina son za mu yi aiki a kanta"

Ammar ya ce "Good, keep it safe kar ka kuskura ka damƙa musu ita tukuna, ka fara tsayawa mu ga iya gudun ruwansu"

Mega ya ce "Kai na san abin da nake yi fa, idan na kammala abin da nake yi, idan na tabattar babu sauran wani abu, zan dawo soon in sha Allah"

"Anyway yadda ake ciki, ka yi mini magana. Take care"

"Shikenan" Ya katse wayar.

*****
Yana zaune a ƙarƙashin bishiya, yana shan sigari, gefensa wasu manyan matasa ne su huɗu. Riƙe da manyan bindigogi su na kaiwa su na komowa.
Ya ciro ƙaramar wayarsa ya duba saƙon da ya shigo.
"Da alama dara ta ci gida, 'yan maza sun shiga hannu"
A sukwane ya miƙe tsaye yana sake karanta saƙon. Da sauri ya fita ya sake danna lambar amma shiru.
Cikin sauri ya buɗe bayan wayar, ya zaro layukan da ke cikin wayar, ya kakkarya su, ya watsar ya cillawa ɗaya daga cikin matasan da ke tsaye a kansa wayar ya ce "Ka jajjage ta yanzun nan, mu bar gurin nan dawa ta ɓaci" Nan da nan suka je inda suka ajiye baburansu ƙirar boxers, suka hau suka bar gurin.

*****

Dattijo ne da shekaru sun ja, duk da hutu da jin daɗin da ake ciki, amma yanayin tsufa ya bayyana a tattare da shi, yake zaune a kan kujera 3 seater. President Faruk Kankiya na kan kujerar da ke facing ɗin dattijon cikin girmamawa.

Dattijon ya ce "Mu na mai jajanta maka, gami da takaicin abin da ya faru a mulkinka, na sace ɗalibai 'yan makaranta. Amma ina mai tausarka da baka shawara ka bi komai a nutse sannu a hankali, kar ka yi garaje ko gaggawa ko kaɗan, idan ba haka ba lissafi zai ƙwace maka. Batun bawa rundunar tsaro kwanaki bakwai su dawo da yara ba abu ne da zai yiwu ba. Kai ba jami'in tsaro bane ba Faruku, ka ba su dama su yi aikinsu domin ceto yaran nan cikin sauƙi ba tare da an yi asarar rai ba. Duk da a rahotannin da muke samu an kashe masu tsaron yaran, da yarinya guda ɗaya, amma ba ma fatan a sake rasa rai. Batun za ka sauke shugabanin tsaro ba shi ne mafita ba. Kamar yadda ka ke faɗa aiwatarwa ne naka, yiyuwar lamari na Allah ne. To su ma hakan ne, ka ba su dama, ka toshe kunnuwanka da surutu da tashin hankalin mutane za su ruɗuka ne kawai. Sai kuma ka je ƙafa da ƙafa makarantar, ka ga halin da makarantar ke ciki ka kuma jajantawa iyayen yaran da ba su ƙwarin gwiwa, ka nuna yaran nan da aka sace naka ne"

Jiki a sanyaye Kankiya ya ce "Na fahimce ka ranka ya daɗe, na kuma gode sosai da sosai da wannan shawarwarin da ake bani, atleast na samu releif na kuma fahimci kuskuren da na so tafkawa. Na gode sosai da sosai "

"Good, a yi ta haƙuri da yardar Allah komai zai daidaita" Ya jinjina kai ya tashi suka yi musabaha da dattijon ya fice.

*****

Jikin Mama ne yake karakarwa, tamkar mai shirin hawa bori. Hafsa da Mariya sun yi mata ƙuri da ido, su na jiran su ji me za ta ce, bayan ta sauke wayar daga kunnenta.
Hafsa ta ce "Mama mene ne? Me aka ce miki?"

Da kyar ta iya ƙwato "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ta miƙe tsaye ta fizgo mayafinta a kan gado"

Mariya ta ce "Mama kin ƙi yi mana magana, kuma jikinki sai rawa yake yi me aka gaya miki ne?"

"Mariya Naja, Naja'atu an ce ba a ganta a cikin sauran ɗaliban ba, shiyasa dama na ce da ku bari na je a duba"

Hafsa ta ce "A'a Mama, ko kin je babu abun da zai canza, yanzu ina za ki je?"

"Gurin su Babballe zan je na sanar musu"

Mariya ta ce "Mama babu abin da za su tsinana mana, dama ki rabu da su"

"A'a ku jira ni ni dai na je na gaya musu" Ta nufi hanyar fita, sai dai ta ji jikinta ya yi mata nauyi, da kyar take ɗaga ƙafafuwanta.

YELWA

Can garin su Ramata, tuni labari ya cika garin an sace ɗaliban makarantar su Rahama. Cikin matsanancin tashin hankali Baffa ya tafi makarantar ,domin duba waɗanda ba a sace ba, ko da Rahama a ciki, sai dai cikin ɗaliban kaf babu Ramata.
Jikinsa na tsuma ya fito ya samu wata baranda ya nemi guri ya zauna yana nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un.

Shugaban makarantar ne, ya nufo Baffa jikinsa a sanyaye ya ƙaraso gefensa ya zauna. Ya dafa kafaɗarsa cikin ƙoƙarin kwantar masa da hankali, ya ce "Ka yi haƙuri, Malam Bashir mu ɗauki wannan al'amarin a matsayin ƙaddara. Mu kuma yi addu'a. Gwamnati ta bamu tabbacin yaran nan za su dawo cikin aminci. Da yardar Allah za su dawo gare mu"

Baffa ya numfasa ya ce "Na yi imani da ƙaddara, na sani ko a gida hakan za ta iya faruwa. Ni tunanina ɗaya Ubangiji Allah ya tsare mana su, ka sani ni ita kaɗai ce da ni yanzu" Ya ƙarasa maganar cikin rawar murya.

"Ka yi haƙuri, mu ci gaba da yi musu addu'a, in sha Allah za su kuɓuta cikin aminci"

Har da jami'an tsaro aka haɗu a ka din ga tausar Baban Ramata, duk da akwai sauran iyaye da aka sace wa yara. Amma duk wanda ya ga yanayin mahaifin Rahama dole ya tausaya masa. Idanunsa da farar fatarsa ta yi jawur, jijiyoyi duk su ka fito raɗa-raɗa a goshinsa saboda tashin hankali. Har tasha wani jami'in tsaro ya kai shi aka saka shi a mota, ya nufi Yelwa.

*****

Tun da Isma'il ya yi ɓatan dabo, kwana na biyar kenan, mutane na ta shigowa yi wa su Alina jaje, tare da fatan Allah ya bayyana shi.
Sai dai haryanzu abin da yake ɗaure mata kai, bai wuce yadda Mamman ya nuna damuwarsa a kan ɓatan Yayanta ba. Ga shi tamkar ya yi mata asiri, ta kasa gaya wa kowa abin da ya faru.
Yau ma da ya aika yaro ta zo, Nadiya ba ta ce komai ba, dan a ganinta, zuwansa na ɗan ragewa Alina damuwar da take ciki.
Tun da ta fito ya tsare ta da ido, amma ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Ya nuna mata gefensa kan barandar gidan, ta nemi guri ta zauna.

"'yar ƙwalisa, kin ga ramar da ki ka yi kuwa?" Ya yi maganar daki-daki. Ta sunkuyar da kai ba ta yi magana ba.

"Alina, wannan yanayin da ki ka shiga, ba zai haifar da ɗa mai ido ba, ki yi haƙuri ki kwnatar da hankalinki. In sha Allah duk inda yake zai bayyana, amma wannan damuwar ba ta kamace ki ba. Tsananta addu'a yakamata mu yi a wannan gaɓar"
Ta yi shiru ta kawar da kanta gefe guda.

"Alina" Ya kira sunanta. Ta ɗaga kai a hankali ta kalli cikin idanunsa. A take abin da ya faru ya fara dawo mata, kuma tana da yaƙinin shi ta gani ba wani ba.
Tun da Isma'il ya ɓace sai a lokacin hawaye ya samu zubowa daga idanunta.
Cikin sanyin jiki ya ce "Alina kar ki yi kuka dan Allah. Ki yi haƙuri" Tamkar ya ziga ta, ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta tashi da sauri ta shige gida ta bar shi a gurin a zaune.

*****
YELWA

Duk da yadda 'yan uwan Baffa ke jin haushinsa, na ƙin aurar da Ramata ya kai ta makarantar boko, sun shiga tashin hankali da labari ya fara bazuwa cewar an shiga makarantar su Ramata an saci ɗalibai.
Ko da ya tafi dubawa ko har da Ramata a ka ɗauka, bai gaya wa kowa ba sai Juma. Ita kuwa yana tafiya ta je ta gaya wa su Maddibo. Aikuwa hankalin kowa ya tashi. Mussaman 'yan uwan mahaifiyar Ramata da babu yadda ba su yi ba, ya yi mata aure amma ya ƙi.

Sai bayan la'asar sosai sannan ya dawo gida.
Aikuwa ya tarar da gidan a cike da mutane.
Su na ganinsa suka yi kansa da tambayoyi a kan ina Ramata.
Jiki a sanyaye ya samawa kansa gurin zama.
"Kai Jibo, ina yarinya take ka dawo kai kaɗai?" Modibbo ya yi maganar cikin zaƙuwa.

"Ramata na cikin yaran da aka yi garkuwa da su" Ya ba su amsa kai tsaye, dan bai ga amfanin ɓoye-ɓoyen ba.
Salati suka saka gaba ɗaya.

Cike da takaici Sambo ya ce "Ka gani ko? Babu irin abin da bamu gaya maka ba, game da kai yarinyar nan can wata uwa duniya da sunan boko, ga shi yanzu ka salwantar da rayuwarta a banza. Ita kaɗai dama ta rage maka, yanzu ga abin da ka janyo"

Maddibo ya ce "Ya isa haka, Ramata dai 'yarmu ce, yanzu tayar da jijiyoyin wuya da hayaniya ba namu bane ba, iyaka kawai mu riƙe addu'a Ubangiji Allah ya bayyana ta"..

Baffa ya kwashi takaici da miyagun maganganu a gurin 'yan uwansa, duk da halin da yake ciki.
Yana ji yana gani, abinci ya gagare shi, salla sai ya sallame sau biyu, saboda rafkanuwa. Ya zauna ya ja uban tagumi, ya ji sallamar ɗan gidan Iro Yayansa Amiru, wanda aka so haɗa shi aure da Ramata, Baffa ya dage makaranta za ta yi.
Baffa ya amsa masa, ya yi masa iznin shiga.
Ya shiga yana sake sallama, Baffa ya yi masa iso, tare da nuna masa kusa da shi ya zauna.
Jiki a sanyaye Amiru ya ce "Baffa ashe tsautsayin da ya faru da Ramata kenan?"
Baffa ya sauke numfashi ya ce "Wallahi kuwa Amiru, an sace su Ramata. Duk ana ɗora mini laifin faruwar hakan, amma ni uba ne, ba zan taɓa aikata abin da zai cutar da 'yar da na haifa kuma ta kasance itakaɗai ta rage mini ba"

Amiru ya ce "Na sani Baffa, kuma na fahimce ka, sai dai mu haɗu mu yi haƙuri, mu yi ta addu'a Allah ya bayyana ta"

Amiru ya din ga rarrashin Baffa, sun daɗe tare sannan Amiru ya yi masa sallama ya tafi.

Sai dai Baffa bai karaya da lamarin ba, sai da dare ya tsala, ya tuna Ramatansa bai san a inda take ba, bai kuma san a yaya za ta kwana ba.
Tsakar gida ya fito, ya tsaya a tsakiyar farin wata, ya sakawa ƙofar ɗakinta ido. Lokacin da ya kai ta makaranta, tare da shugaban makarantar primary ɗin su Rahaman, sai da aka kai shi har ɗakin da aka bata, da gadon da aka bata ya tabattar da tana kauwwame a guri ɗaya, sannan ya amince wanda tsawon shekarun nan, ko ya kaita makarantar wasu lokutan sai ya yi ta damuwa da rashinta a kusa da shi. Balle yau da ba a san ma a inda take ba.
Ya ja da baya a hankali ya jingina da jikin danga, sai kuma abubuwa daban-daban suka fara dawowa kansa game da garin, baya tunanin kaf garin YELWA akwai wanda ya haɗu da masifu kala-kala kamarsa.

Please Login or Register in order to submit comment