gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading DR Chapter 10 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

'yan aikace-aikacen gidan kamin Mama tace,

"Khadija kije ki kwanta ki huta kamin lokacin girkin rana yayi kinji?!"

"Toh Mama saina fito."

Saida ta sami kankanarta da madarar ruwa ta had'a waje guda ta shanye sannan ta kwanta ko minti biyar yayi yawa tai bacci.

Koda Maman taga rana tayi kuma taji shiru kawai saita temaka mata da d'ora girkin domin tasan gajiyace ta hanata fitowa.

Sai wajan sha biyu ta farka shima dalilin kiran wayarta da ake tayi ne, da sauri ta d'auka tare da gaisheshi, cikin tashin hankali ya furta,

"Lafiyarki lau ko tun safe naketa kiran wayarki harna fara tunanin tahowa gidan.?!"

"Kayi hakuri Yaya Ahmad kwanciya nayi ne amma na tashi yanzu kuma lafiyata lau girkima zani d'orawa."

"Ok tohm my wife da har hankalina UA kwanta, love you dear."

Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta kashe wayar ta fita.

"Mama menene wannan naji yana ta kamshin kanunfari?"

Murmushi tayi kamin tace,

"Ki d'auka ki shanye tukunna sai nai miki bayani Khadijatu."

Sai da Khadija ta shanye tas sannan ta ajiye cup d'in tana sauraran k'arin bayanin Mama.

"Kinga wannan abun khadija, to ba komai bane face kanunfari sai mazarkwaila da zuma, kinga abu ukun nan na rantse da Allah wanda ya halicce ni babu wata d'iya mace da zata kama wa innan abubuwan ba tare da ta mallaki mijinta ba. Temakon da zata d'ora dashi d'aya ne shine iya kwanciya shikenan zaki iya zama da kowane irin namiji komai taurin kanshi da miskilancin shi kuwa, sabida mu lokacin mu duk babu irin wadannan kayan haukan da ake sai dawa yanzu sai 'yan dabaru wanda baza su tab'a cutar dake ba balle lafiyarki.

kinga ZUMA ita kadai ta isheki k'arin ni'ima ga KANUNFARI shima haka sannan kamshi zai zauna ajikinki musamman baki da kasanki sai MAZARKWAILA, kin dai san ita rakece sabida haka zanyi miki nasiha daki kiyayi kanki da duk wani nau'in magani da sunan shi na mata domin babu komai cikinsu sai cutarwa kinga akwai wanda malamai suke badawa wanda amfani dashi bata ne, sannan ko wane kalar magani zaki sha indai baki da biyayya ko gyaran jikinki da iya kwanciyar auren to tabbas babu wani tasiri da maganin zaiyi a zuciyar mijinki.

Yanzu fa babu kalar kashin dabbar da za ace beyin maganin mata wannan wace irin masiface yanzu kusan komaima magani ne wannan ai musibace sannan babu abinda suke sawa sai mutuwar aure, malamai nata tambaya meyakesa mutuwar aure tayi yawa awan nan zamani musamman a arewacin Nigeria, to ba komai bane face maganin mata, domin wani maganin daga randakikai amfani dashi shike nan zaki kashe ainihin ta jikinki kinga kenan mijinki bazai kuma jin dad'in kiba. dan haka ki d'aure ki kuma jurema wa innan kawai sun isheki zaman duniya domin kadda garin neman k'iba ki nemo rama duk da nasan mijinki mabukaci ne sosai amma ina so kadda hakan ya jaki inda zaki kai kanki ki baro."

Cikin matsanan tacciyar kunya khadija ta sadda kanta k'asa tare da yima Maman godiya domin ko rannan da taje gidan wani suna taga an baje dilarsu anata fad'in amfaninsu saida ta siyo kala biyu har tana tunanin idan tasami kud'i zata je ta siyo wasu ashe ashe hakan abun yake.

Ganin khadijan tayi zugudum da ita yasa Maman tace,

"Karfa ki damu baki da wata matsala indai zaki dinga cin kayan marmari kuma kin rike wannan sirrin to zaki godemin nan gaba, tashi kije ga girkin can koya k'arasa."

A hankali Khadija ta mik'e ta wuce kitchen tana jin kaunar surukar tata duk da tasan d'anta take wa tanadi.

*****

A gajiye ya shigo gidan sai dai yanayin arba da gimbiyar tashi yaji ya watstsake saima wani irin shauk'inta daya taso mishi a lokacin.

Sai da ya gaishe da Maman sannan ya wuce d'akin su yana Alla Alla ta biyo shi amma tak'i sabida Kunyar Mama.

BAYAN ISHA'I:-

"Mama dama wani tunani nayi shine nace bari nayi miki bayani sai naji menene shawararki akai."

"Akwai wasu kud'i masu yawa da suke mallakina shine na canza mota sabida zirga-zirga yanzu kuma ina so mukoma gidan wani abokina daya gina amma be tare ba sai insa abaje wannan acanza na zamani zuwa gaba kuma sai in gyara na baba (malam Mamuda) sai kuma afara temakama dangi, amma me kika gani ke?!"

Murmushin jin dad'i tayi kamin tace,

"Amma dai kayi tunani me kyau wallahi Allah yayi maka albarka ya kara bud'i ina fatan dai na kane bawai bashin banki bane??!"

Dariya yayi kamin yace,

"Kai Mama."

Itama dariyar tayi kamin tace,

"Aah to ai da gaskiya ta haka fa mutane suke yi yanzu kawai suje suciwo bashin banki sabida shirme sai daga baya kuma azo ana wallahi tallahi."

Dariya yayi yace "a'a Mama na wane kuma insha Allah bazan tab'a ciwo wa kaina bashin kowa ba."

"Allah yasa toh..!"

Yace "Amin."

****
Kan cinyarta ya zauna dan tsokana aiko tasaka ihu tare da k'iran "wayyo cinyoyina." Dariya yayi kamin yace "kai amma dai kekam anyi raguwa yo babyna ina naga wani nauyin da zaki min ihu?"

Ture shi tayi daga jikinta kamin tace "au haka ma zaka minko Allah ya kaimu wajan kwanciya lafiya zaka san nice raguwa."

Cikin dariya ya fara fad'in "wayyo Allah babyna bakece raguwaba nine nan ke kam ai nashaida ki jarumace ki rufamin asiri kadda jinina ya hau abani gado kija surutun al'uma ace Dr Ahmad a kwance sabida huran matar sh..."

Tayi saurin rufe mai baki da nata tana yi mai cakulkuli...

*MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€
*πŸ’—DR.AHMADπŸ’—*

36

*NA MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€

Edit by *Hajja ce*πŸ‘ˆ

*HASKE WRITER'S ASSO......*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)

*D*uk wata dauriya da Allah ya mallaka mata ita ajikinta saida ta jawota ranar, sosai ta galabaita hannunshi kamin ya saurara mata lokacin ko motsin kirki bata iyawa tsabar gajiya da wahala. Rungumeta yayi tare da saka mata kuka hadda sheshshekar shi tamkar k'aramin yaro, ita kam shiru tayi kawai tana sauke numfashi, saida ya dai-daita nutsuwarshi sannan yafara magana a hankali,

"Kiyi hakuri dan Allah ki yafemin wallahi kece rayuwata ina jinki ako ina na jikina khadija ke kadai ke samar ma da gangar jikina nutsuwa khadija ki yafemin laifin danayi miki insha Allah zan kiyaye gaba am Dr Ahmad dama kuma ance aure *DACE NE*."

Kwanciyar ta kawai ta gyara tare da lumshe idanunta tana jin maganganun shi.

"Please khadijana kiyi hakuri kidinga min magana wallahi ni kadai nasan irin wahalar danasha dalilin gujemin d'in nan da kika yi, kadda ki kuma hukuntani ta hakan kinji bazan iya jurewaba please."

"Dan Allah kabarni na huta barci nakeji nifa."

Cewar khadija wacce keta jera hamma gami da mik'a ko Allah zaisa jikinta ya d'an saki.

Matsa mata yayi saida sukai wanka a lokacin duk da irin sanyin da ake kad'awa.

Yana kwance yana ta baccin nutsuwa harta gama duk wani aikin daya dace duk wata macen kirki ace tayi kamin bud'ewar idanun mijinta, misalin su wanka kwalliya shiga me kyau gamida gyaran d'aki zuwa kammala kayan da zasu karya dashi. in kuma da yara harda shirinsu domin daga lokacin da aka ce miki kinyi aure toh faa wasu nauyaye nauyaye ne suka hau kanki maganar hutu dole ne ki aje su har sai kinga kin kammala komai daya kamata domin hatta hutunma zaki fijin dad'i idan har babu tunanin wani aikin a gabanki.

Shima kuma miji zaki ga yana d'aukar komai naki da muhimmanci sabida bazai tab'a ganin gazawarki ba kuma duk ranar daya ga baki yiba to zai iyayi shi da kanshi domin zai miki uzurin rashin lafiya ko kuma halin rayuwa, amma matukar baki sababa to ko rashin lafiya kike yi bazai yadda da hakan ba.

Ganin Ahmad zai makara wajan fita aiki yasa khadija komawa cikin d'akin domin da tuni tana cikin d'akin Mama bayan gama had'a abin karinsu.

Kamshinta ya fara shak'a cikin barcin shi kamin ya bud'e idanun shi, aikuwa tanata mishi murmishi kamar ba ita bace wadda take fishi da shi ba. jawota jikin shi yayi ya fara rungumarta tare da shinshinarta ganin yana nema ya rinjayeta ya sata nunamishi agogo da idanunta.

Marairaicewa yayi kamin yace mata,

"Please khadija kad'an zanyi saina shirya gaba d'aya ma na bar miki gidan."

Ganin yanda ya wani koma kalar tausayi ya sata biye mishi saida ya sami nutswa sannan ya shirya agurguje yayi karinshi, Maman tayi ta kallonshi tana mamkin kalarshi domin kallo d'aya zakai mishi kagane nutsuwar daya ke ciki. Saida ta rakashi har bakin zaure sannan ta dawo ita da Maman sukaci gaba da 'yan aikace-aikacen gidan kamin Mama tace,

"Khadija kije ki kwanta ki huta kamin lokacin girkin rana yayi kinji?!"

"Toh Mama saina fito."

Saida ta sami kankanarta da madarar ruwa ta had'a waje guda ta shanye sannan ta kwanta ko minti biyar yayi yawa tai bacci.

Koda Maman taga rana tayi kuma taji shiru kawai saita temaka mata da d'ora girkin domin tasan gajiyace ta hanata fitowa.

Sai wajan sha biyu ta farka shima dalilin kiran wayarta da ake tayi ne, da sauri ta d'auka tare da gaisheshi, cikin tashin hankali ya furta,

"Lafiyarki lau ko tun safe naketa kiran wayarki harna fara tunanin tahowa gidan.?!"

"Kayi hakuri Yaya Ahmad kwanciya nayi ne amma na tashi yanzu kuma lafiyata lau girkima zani d'orawa."

"Ok tohm my wife da har hankalina UA kwanta, love you dear."

Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta kashe wayar ta fita.

"Mama menene wannan naji yana ta kamshin kanunfari?"

Murmushi tayi kamin tace,

"Ki d'auka ki shanye tukunna sai nai miki bayani Khadijatu."

Sai da Khadija ta shanye tas sannan ta ajiye cup d'in tana sauraran k'arin bayanin Mama.

"Kinga wannan abun khadija, to ba komai bane face kanunfari sai mazarkwaila da zuma, kinga abu ukun nan na rantse da Allah wanda ya halicce ni babu wata d'iya mace da zata kama wa innan abubuwan ba tare da ta mallaki mijinta ba. Temakon da zata d'ora dashi d'aya ne shine iya kwanciya shikenan zaki iya zama da kowane irin namiji komai taurin kanshi da miskilancin shi kuwa, sabida mu lokacin mu duk babu irin wadannan kayan haukan da ake sai dawa yanzu sai 'yan dabaru wanda baza su tab'a cutar dake ba balle lafiyarki.

kinga ZUMA ita kadai ta isheki k'arin ni'ima ga KANUNFARI shima haka sannan kamshi zai zauna ajikinki musamman baki da kasanki sai MAZARKWAILA, kin dai san ita rakece sabida haka zanyi miki nasiha daki kiyayi kanki da duk wani nau'in magani da sunan shi na mata domin babu komai cikinsu sai cutarwa kinga akwai wanda malamai suke badawa wanda amfani dashi bata ne, sannan ko wane kalar magani zaki sha indai baki da biyayya ko gyaran jikinki da iya kwanciyar auren to tabbas babu wani tasiri da maganin zaiyi a zuciyar mijinki.

Yanzu fa babu kalar kashin dabbar da za ace beyin maganin mata wannan wace irin masiface yanzu kusan komaima magani ne wannan ai musibace sannan babu abinda suke sawa sai mutuwar aure, malamai nata tambaya meyakesa mutuwar aure tayi yawa awan nan zamani musamman a arewacin Nigeria, to ba komai bane face maganin mata, domin wani maganin daga randakikai amfani dashi shike nan zaki kashe ainihin ta jikinki kinga kenan mijinki bazai kuma jin dad'in kiba. dan haka ki d'aure ki kuma jurema wa innan kawai sun isheki zaman duniya domin kadda garin neman k'iba ki nemo rama duk da nasan mijinki mabukaci ne sosai amma ina so kadda hakan ya jaki inda zaki kai kanki ki baro."

Cikin matsanan tacciyar kunya khadija ta sadda kanta k'asa tare da yima Maman godiya domin ko rannan da taje gidan wani suna taga an baje dilarsu anata fad'in amfaninsu saida ta siyo kala biyu har tana tunanin idan tasami kud'i zata je ta siyo wasu ashe ashe hakan abun yake.

Ganin khadijan tayi zugudum da ita yasa Maman tace,

"Karfa ki damu baki da wata matsala indai zaki dinga cin kayan marmari kuma kin rike wannan sirrin to zaki godemin nan gaba, tashi kije ga girkin can koya k'arasa."

A hankali Khadija ta mik'e ta wuce kitchen tana jin kaunar surukar tata duk da tasan d'anta take wa tanadi.

*****

A gajiye ya shigo gidan sai dai yanayin arba da gimbiyar tashi yaji ya watstsake saima wani irin shauk'inta daya taso mishi a lokacin.

Sai da ya gaishe da Maman sannan ya wuce d'akin su yana Alla Alla ta biyo shi amma tak'i sabida Kunyar Mama.

BAYAN ISHA'I:-

"Mama dama wani tunani nayi shine nace bari nayi miki bayani sai naji menene shawararki akai."

"Akwai wasu kud'i masu yawa da suke mallakina shine na canza mota sabida zirga-zirga yanzu kuma ina so mukoma gidan wani abokina daya gina amma be tare ba sai insa abaje wannan acanza na zamani zuwa gaba kuma sai in gyara na baba (malam Mamuda) sai kuma afara temakama dangi, amma me kika gani ke?!"

Murmushin jin dad'i tayi kamin tace,

"Amma dai kayi tunani me kyau wallahi Allah yayi maka albarka ya kara bud'i ina fatan dai na kane bawai bashin banki bane??!"

Dariya yayi kamin yace,

"Kai Mama."

Itama dariyar tayi kamin tace,

"Aah to ai da gaskiya ta haka fa mutane suke yi yanzu kawai suje suciwo bashin banki sabida shirme sai daga baya kuma azo ana wallahi tallahi."

Dariya yayi yace "a'a Mama na wane kuma insha Allah bazan tab'a ciwo wa kaina bashin kowa ba."

"Allah yasa toh..!"

Yace "Amin."

****
Kan cinyarta ya zauna dan tsokana aiko tasaka ihu tare da k'iran "wayyo cinyoyina." Dariya yayi kamin yace "kai amma dai kekam anyi raguwa yo babyna ina naga wani nauyin da zaki min ihu?"

Ture shi tayi daga jikinta kamin tace "au haka ma zaka minko Allah ya kaimu wajan kwanciya lafiya zaka san nice raguwa."

Cikin dariya ya fara fad'in "wayyo Allah babyna bakece raguwaba nine nan ke kam ai nashaida ki jarumace ki rufamin asiri kadda jinina ya hau abani gado kija surutun al'uma ace Dr Ahmad a kwance sabida huran matar sh..."

Tayi saurin rufe mai baki da nata tana yi mai cakulkuli...

*MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€
[9:15PM, 3/5/2018] β€ͺ+234 803 478 2721‬: *πŸ’—DR.AHMADπŸ’—*

37

*NA MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€

Edit by *HAJJA CE*πŸ‘ˆ

*HASKE WRITER'S ASSO....*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)

_Wannan shafin nakune domin naga kuna jin dad'in labarin nan *DR AHMAD*, toh gashi kuyi yadda kuke so dashi_.

*Sister Ag*πŸ’•
*Sis Safara'u murtala*
*Real mai dambu*
*Ummumuhammad*
*Miss Marok'i*
*Khairat up*
Da k'awata ta kaina
*Sis Shafa'@t Omar*

*"K*inga wannan abun khadija, toh ba komai bane face kanunfari sai mazarkwaila da zuma, kinga abu ukun nan na rantse da Allah wanda ya halicceni kenan babu wata d'iya mace da zata kama wa innan abubuwan batare da ta mallaki mijin taba. Temakon da zata d'ora dashi biyu ne shine iya kwanciya da biyayya shikenan zaki iya zama da kowane irin namiji komai taurin kanshi da miskilancin shi kuwa, sabida mu lokacin mu duk babu irin wad'an nan kayan haukan da ake saidawar yanzu sai 'yan dubaru wanda bazasu taba cutar dake ba balle lafiyarki. kinga ZUMA! ita kadai ta isheki k'arin ni'ima ga KANUNFARI shima haka sannan kamshi zai zauna ajikinki musamman baki da kasanki sai MAZARKWAILA, kin dai san ita rakece sabida haka zanyi miki nasiha daki kiyayi kanki da duk wani nau'in na magani da sunan shi na mata domin babu komai cikinsu sai cutarwa kinga akwai wanda malamai suke badawa wanda amfani dashi b'ata ne, sannan ko wane kalar magani zakisha indai baki da biyayya ko gyaran jikinki da iya kwanciyar auren to tabbas babu wani tasiri da maganin zai yi.

YANZU fa babu kalar kashin dabbar da baza ace beyin maganin mata wannan wace irin masiface? yanzu kusan komaima magani ne wannan ai musibace sannan babu abinda suke sawa sai mutuwar aure, malamai nata tambaya meya kesa mutuwar aure tai yawa awannan zamani musamman a arewacin Nigeria, toh bako mai bane face maganin mata domin wani maganin daga randaki kai amfani dashi shikenan zaki kashe ainihin ta jikinki kinga kenan mijinki bazai kuma jin dad'in kiba dan haka ki daure ki kuma jurema wa innan kawai sun isheki zaman duniya domin kadda garin neman kiba ki nemo rama duk da nasan mijinki mabukaci ne sosai amma inaso kadda hakan yajaki inda zaki kai kanki ki baro."

Cikin wata matsanan tacciyar kunya khadija ta sadda kanta k'asa tare da yima Maman godiya domin ko rannan da taje gidan wani suna taga an baje dilarsu anata fad'in amfaninsu saida ta siyo kala biyu har tana tunanin idan tasamu kud'i zataje ta siyo wasu ashe-ashe haka abun yake.

Ganin khadijan tayi zugudum da ita yasa Maman tace,

"Karfa ki damu baki da wata matsala in dai zaki dinga cin kayan marmari kuma ki rike wannan sirrin toh zaki gode min nan gaba, tashi kije ga girkin can koya k'arasa."

Tashi Khadija tayi cikin jin kunya ta fita har tanajin tuntub'e da kifar d'akin...

*****

A gajiye ya shigo gidan sai dai yana yin arba da gimbiyar tashi yaji ya watstsake sai wani irin shauk'i daya taso mishi alokacin.

Sai da ya gaishe da Mama sannan ya wuce d'akin su ganin itama ta shige tana mai dariya.

BAYAN ISHA'I

"Mama dama wani wani tunani nayi shine nace bari nai miki bayani sai naji menene shawararki akai,

Akwai wasu kud'i masu yawa da suke mallakina shine na canza mota sabida zirga-zirga yanzu kuma ina so mukoma gidan wani abokina daya gina amma be tareba sai insa abaje wannan acanza na zamani zuwa gaba kuma sai in gyara na baba(malam Mamuda) sai kuma a fara temakama dangi, amma me kika gani?"

Murmushin jin dad'i tayi kamin tace,

"Amma dai kayi tunani me kyau wallahi Allah yayi maka albarka yakara bud'i ina fatan dai naka ne bawai bashin banki bane kaje ka d'akko?"

Dariya yayi kamin yace,

"Kai Mama?!"

Itama dariyar tayi kamin tace,

"Ah to aida gaskiyata hakafa mutane suke yi yanzu kawai suje su ciwo bashin banki sabida shirme sai daga baya kuma azo ana wallahi tallahi."

Yace,

"A'ah Mama wallahi nawa ne halak malak kidena saka ran Zan d'aggo abinda yafi karfina."

"Toh Allah ya kyauta ya kuma tabbatar maka da alkairi babana."

"Amin Mama na."

Daga nan ya fita ya koma d'akin su,

Kan cinyarta ya zauna dan tsokana aiko tasakar mishi ihu tare da kiran,

"Wayyo Allah cinyoyi na.!"

Dariya yayi kamin yace,

"Kai sharri kayan mata, amma dai kekam anyi raguwa yoo babyna ina naga wani nauyin da zaki min wannan ihu?"

Tureshi tayi daga jikinta kamin tace,

"Uhmm'ehm au hakama zaka minko? Allah ya kaimu wajan kwanciya lafiya zaka san nice raguwa."

Cikin dariya ya fara fad'in,

"Wayyo Allah ni Ahmad marayan Allah, babyna ba kece raguwaba nine nan mugun rago kekam ai na shaida ki jarumace ki rufamin asiri kadda jinina ya hau abani gado a asibiti kisa a gano abinda yasani kwanciya.."

"Ah'ah Allah dai ya kaimu kuma in gaya maka na tsumu zakasha mamaki.."

"Habba my Dijama kema kinsan indai akanki ne ni mugun ragone kuma dole shashasha wa..."

Bata bari ya k'arasa ba tayi saurin zura harshanta cikin bakinshi dayake ta faman motsawa daga nan wasan ya canza salo....

*MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€
[11:06PM, 3/5/2018] β€ͺ+234 803 478 2721‬: *πŸ’—DR.AHMADπŸ’—*

38

*NA MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€

Edit by *HAJJA CE*πŸ‘ˆ

*HASKE WRITER'S ASSO....*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)

*AFUWAN 'YAN UWA ANYI MISTAKE SO SORRY*πŸ˜‰

_Wannan shafin nakune domin naga kuna jin dad'in labarin nan *DR AHMAD*, toh gashi kuyi yadda kuke so dashi_.

*Sister Ag*πŸ’•
*Sis Safara'u murtala*
*Real mai dambu*
*Mmn Gausiya*
*Ummumuhammad*
*Miss Marok'i*
*Khairat up*
Da k'awata ta kaina
*Sis Shafa'@t Omar*

*C*ikin yaddar Allah Ahmad ya fara aikin gidan kamar yadda ya jima yana tsarawa, duk da cewa ginin bawai irin k'aryar nan ya shirya ba amma gaskiya yayi kyau kusan tsawannin wata d'aya kenan da sati biyu tun da suka fara aikin basu tsaya ba domin dama aiki in dai daka yan yinsu magana ta kare.

D'akin Mama ciki da falo ne kamar da sai dai yanzu an mai dashi na zamani kuma hadda karamin toilet a ciki, gefen nata d'akin Aminu ne dai-dai shi duk ya zuba musu kayan amfani dai-dai matsayin aljihun shi.

Sai d'akin su ciki biyu ne sai falo a tsakiya sannan toilet mai had'e da bathroom, gaskiya anyi komai cikin tsari dan kuwa ginin yayi kyau sosai haka kuma labulaye sai da aka sakama kowan ne d'aki, kujerun khadija masu matukar kyau ne Ahmad ya zuba mata, amma d'akin Mama babu abinda aka saka mata sai cafet wanda ya mamaye d'akin.

Sai d'akin Aminu daga gadon shi sai wajan ajiyar kayan shi.

Gyara ya kammalu harma ya fad'i randa zasu tare.

*****

Zaune yake akan kujerar shi dake cikin ofis d'in shi, waya ce a hannun shi sai murmushi kawai yake zab gawa har wani lumshe idanun shi ya keyi da alama ba k'aramin jin dad'in wayar ya keba.

"Please babyna kibar kukan haka nan in dai ba so kike in kasa duba marasa lafiya ba, yanzu zan duba wani amma idan na gama zan kiraki kinji ko?"

"Ok bye-bye.."

Yanke wayar tayi tare da murmushi duk da cewa ba wani dad'in jikinta take jiba domin kuwa wani irin murd'awa takeji cikin ta na mata kamar za tayo amai.

**

Ba tare da yayi mishi kallon sani ba ya fara tambayar shi abinda ke da munshi, mamaki ya hana mutumin magana kamin ya d'ore yace,

"Oh nikam gani na keyi kamar yaron k'anina wanda yarasu IRO?!"

Wani kallon zama kai bayani Ahmad d'in yayi mishi kamin yace,

"Allah ko?!"

Cigaba yayi da rubutun shi kamin yace,

"Zaka iya tafiya wasu su shigo idan baka da abunda ke damun ka."

Da sauri mutumin ya fara bashi hakuri kamin yayi mai baya nin damuwar shi, magunguna ya rubuta mishi kamin yace.

"Insun k'are zaka iya dawowa domin muga yana yin jikin naka, zaka iya tafiya."

Tsabar kallon daya kema Ahmad din ne yasa shi cin karo da kofar office d'in, cikin tashin hankali ya fice har wani sassarfa ya keyi ya kosa ya k'arasa wajan babban yaronshi daya rako shi,

"Rikeni zubairu rikeni zubairu ashe wannan yaron me sunan baba na wajan marigayi ne likitan wallahi shine..."

Shi kan shi wanda aka kira da zubairun sai da yayi mamaki kuma ya tab'a zuwa ganin likita yaga Ahmad d'in amma sam be gane shi ba domin rabon Ahmad d'in da garinsu tun rasuwar mahaifinshi da yaje so d'aya suka yi mishi wulakanci be kuma komawa ba.

Hannun uban ya kama kamin yace,

"Allah ya kyauta to kawuce muje wajan maganin inga idan kud'ina zasu isa na siya maka."

Wani murmishin takaici yayi bayan tsohon ya b'acema ganin shi tabbas ada ya manta yanada wasu dangi daga mahaifinshi sai dai ayau da yaga tsohon nan ya tuno komai daya manta yayi kuma kokarin ganin ya sharesu aran shi.

*****

Sukuku haka ya koma gida, damuwa fal cikin ranshi sama-sama suka gaisa da Maman ya wuce d'akin da yake nasu shida khadijan, sai dai yana shiga ya taddata tana ta amai tuni ta gama galabaita.

"Innalillahi."

Ya furta da karfi kamin ya rungumeta jikin shi be damu da aman dake jikin taba.

Shigar da ita yayi ban d'akin dake d'akin ya gyara mata jikinta kamin ya kwantar da ita ya fara gyaran wajan, sannan ya shiga yayi wanka. koda ya fito tuni tai barci dan haka jikinta kawai ya tab'a sannan ya bar d'akin ta wuce d'akin Mama.

"Mama naga baba salisu yau yaje asibiti."

"Allah sarki ya suke suna lafiya ko?"

Beyi mamakin jin hakan daga gare taba domin tuni ya san cewa mahaifiyar shi macece me kawaici da kauda kai tare da yafiya. haushi yaji dan haka be kuma maganar ba sai ma maganar khadija daya sako mata,

"Mama baby fa amai ta keyi dana shiga d'akin amma dai yanzu tayi barci."

A rud'e ta kalleshi kamin tace,

"Subhanillahi dama naga yau kamar bata jin dad'i girkin ma ni nayi, Allah ya bata lafiya amma dan Allah babana ka dubata idan ciki ne sai kafara hakuri kadda amai-maita irin wancan karan."

Sauke kanshi k'asa yayi yana cin abinin shi sabida kunya, ya jima bece komai ba kamin yace,

"Kun gama had'a kayan ko? sabida daga dare zuwa safiyar gobe nake so mukoma can sabida an kusa bikin yusuf d'in bana so in takura shi sai insa ai mishi gyare-gyaren inda muka b'ata duk da dai naga babu abinda gidan yayi."

"Eh hakan yayi aima ya kyauta wallahi Allah ya saka da alkhairi ni tun jiyama na gama kintsa komai harna Aminu, sai dai ko d'akin ku."

"A'a canma yanzu zan shirya kamin ta tashi daga barcin tace ita zata yi.."

"To Allah yayi albarka ya kara bud'i me amfani."

"Amin Mama na gode."

******

"Wallahi da gaske nake muku yaron Habiba na gani yayi kud'i ya zama babban mutun daga gani ya tara abin duniya yaron nan."

D'alha wanda ke zaune abin duniya yada meshi yace musu,

"Yanda za ayi

Please Login or Register in order to submit comment