You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
idan har Abba ya amince ka kawo macen da kake so,plz ka za6i salima dmn a cikin en matan da ke son ka duk tafi su sonka tsakani da Allah snn mace ce har mace bata da wani abu da d'a namiji ze kalla yace baya so son kowa ce qin wanda ya rasa.
A hankli Saifuddeen ya girgiza kansa yace"ni Sophie kawai zan iya rayuwa da ita a matsayin mata ta kuma inshaa zan aure ta da izinin Abba bama a 6oye ba.
Jamil yace"ta yaya saif?
Yace"jamil kafi kowa sanin irin qaunar da Sophie ke min,akaina ta gudo ta baro iyayen ta snn aikaina zata iya musulunta dmn ta aure ni,da haka ne nake tunanin idan ta musulunta Abba ze barni na aure ta.
Jamil yace"hakane tabbas Sophie ba abinda baza ta iya ba akan ka ina maka fatan alhairi Allah yasa ayi nasara"
"Amin"
Cewar Saifuddeen.
[11:14AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Monday 12/02/2018_ *芦禄禄芦芦禄SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 11*
Washe gari shigar sa office knn ko zama beyi ba se ga Sophie ta shigo,tsaye yayi yana kallonta lokaci d'aya duk ta rame idanuwan ta duk sun kumbura da gani tun rnr da abun ya faru take kuka har yau dan still qwallah ne tap a idon ta tana kallon shi.
Kafin tace komai yazo ya ra6a ta gefen ta ya fita,ta bisa da kallo hawaye na silalowa a hankli kan kumatun ta,Saifuddeen bai ta6a fushi da ita irin haka ba se wnn karon,gashi ta biyoshi har office d'insa dmn ta bashi haquri amma ya fita ya bar mata office d'in.
A hankli ta zube gurin tana kuka.
Saifuddeen kuwa da fitar sa kai tsaye office d'in jamil ya tafi Jamil da har ya zauna ze fara duba wasu files ya tsaya yana kallon saif har ya qaroso yaja kujera ya zauna muryar sa cikin yanayin damuwa yace"plz jamil kaje ka sami Sophie tana office d'ina ka mata bayanin komai and ina son ka kwantar mata da hankali ta yanda baza ta shiga damuwa sosai ba snn kuma ka gaya mata ko bayan ta koma England zan dawo gare ta very soon inshaa Allah zamu yi aure.
Jamil ya numfasa yace"Aa Saifuddeen kar fa a gaya mata abunda bazai yiyu ba taje tayi ta faman jiran ka a banza......Bakin ka ya sari d'ayan kashi,da Allah ni je ka gaya mata nasan tana can ta soma kuka.
D'an guntun murmushi kawai jamil yayi snn ya tashi ya fita.
Saifuddeen kuwa cike da damuwa ya had'e kansa da desk.
Can jamil ya dawo jikin sa duk a sa6ule ya zauna Saifuddeen da ya d'ago yace"what! ta fahimce ka ko kuwa?
A hnkli jamil ya lumshe idon sa tare da ware su akan shi snn yace"ta fahimce ni dmn sosai na kwantar mata da hankli amma duk da haka se da tayi ta kuka ita bata so ta tafi England tafi so ta zauna tayi ta jiranka har ko yaushe ne dmn tana tsoron yanda zata je ta fuskanci iyayen ta wa enda ba lallai bane su barta ta samu damar sake had'uwa da kai ba har kuyi aure.
Saifuddeen ya numfasa snn yace"kira ta awaya ka gaya mata ta tafi kawai komai zaiyi normal inshaa Allah da izinin iyayen ta ma za'a yi auren kar ta damu.
I have already told her but still dai ta tafi tana kuka,she dnt wnt miss u,and ga short note d'in da ta rubuta ta bani tace na baka.
Saifuddeen ya kar6i takadar ya ware ya fara karanta content d'in da ke ciki"
_Dear,am very sorry 4 wat i have coused for us,of course i should punished my self 4 that,bye take care of ur self and my kitty._
_Miss u!_
Saifuddeen da ya gama karantawa yasa hannu ya goge en guntayen hawayen da suka gangaro ta gefen idon sa kana ya tashi ba tare da yace da jamil komai ba ya fita.
Jamil da ya bisa da kallo ya girgiza kansa cikin yanayin tausayawa sbd yanda suke matuqar son junan su dole ka tausaya musu musamman yanda suka dad'e cikin qaunar juna.
Zarah ce ta fad'o mishi a rai wacce basu ko fara soyayyar ba,asali ma ko cikakken wata d'aya beyi da fara ganin ta ba amma da Saifuddeen ya gaya mishi Abba zai had'a shi aure da ita,wani irin yanayi ya tsinci kansa a ciki da baisan ma ta ya zai fisalta ba,wanda shi kansa yana mamakin yanda akayi soyayyar zarah ta kama shi lokaci d'aya haka da yawa duk da kasancewar ta baqauya amma shi sam qauyancin nata bai dame sa ba burin sa kawai ya mallake ta,kuma inshaa Allah zai mallake ta kmr yanda Saifuddeen ya masa alqawari,kul ba dad'e kul ba jima ze iya jira koma yaushe ne.
芦禄
Saifudddeen na ganin abun kmr wasan yara amma se shiryen shiryen auren ake da gaske ba kama hannun yaro dan kaf dangi da abokan arziki kowa ya sani,amma shi kam in banda jamil bawani abokin sa da ya sani dan hana jamil yayi ya snr da kowa acewar sa ba auren da zai snr da frnds d'insa ba ne wnn,auren takaici da har kullum mamakin Abba yake da har yayi tunanin had'a shi da wnn yarinyar,gabad'aya takaici da kewar Sophie duk suka tara mishi har ma ko yaje asibiti baya iya wani abun kirki yake dawowa.
Nusaiba kam duk da tasan halin yayan ta ko kad'an baya son zarah amma tayi farin ciki sosai dmn ganin take zai daina duk wani abun da yake yiwa zarah su koma son juna,duk qyamar da yake yiwa ba qauyen mutum dai se gashi baqauyar ce zata zamo matar shi,kai ba kad'an ba tsarin Abba ya birge ta dmn sam bata son halin yayan nata na tsanar da yake yiwa qauyawa abun na damunta sosai.
Saura en kwanaki da d'aurin auren ne Saifuddeen ya fito 6angaren su umma riqe da invitations d'inda Abba ya bashi na d'aurin aure dmn ya bawa abokan sa.
Umma na kallon sa ta windown falo gabad'aya ya keta su ya zuba su a cikin dustbin ya kakka6e hannun sa yayi ficewar shi,bata yi mamaki ba dan dama tasan abunda zai faru knn,girgiza kanta kawai tayi snn ta kalli Abba da ya haura sama se waya yake abun sa cike da fara'a.
Bin sa tayi zuwa d'akin nasa bayan ya ida waya ne ya kalle ta da fara'ar sa yace"ya akayi ne Maman yusra?
Tace"plz Alhj ka zauna ina son zamuyi magana"
Ba musu ya zauna kan bed itama ta zauna tana kallon sa a natse snn tace"nasan baka so amma kayi haquri abu ne da ya zama dole,kasan mahaifiyar saif dole ne tasan da auren nn amma naga ga dukkan alama baka snr da ita ba se ma harkokin gaban ka da kake.
Take duk wani farin cikin sa ya 6ace 6at ransa a 6ace yace"da wane dalilin zata sani mtr da sam bata qaunar shi tun yana d'an wata shida da ta barshi ta tafi ko da kuskure bata sake waiwayar sa ba.
Umma tace"Alhj kar fa ka manta kaifa ka sake ta ba wai ta tafi ne ta barshi ba.
Nasan ni na sake ta amma sam bata son Saifuddeen na gaya miki dmn a lokacinda ta sami cikin sa ba irin abinda bata yi ba dmn cikin ya zube amma Allah da ikon sa bata yi nasara ba har ta haife shi,a tunani na renon cikin sa da tayi na tsawon wata tara da yanda tasha wahala a gurin haifuwar shi zai sa ta so shi amma sam hakan besa ta damu dashi ba,masu aiki kawai ta barwa suna hidima dashi,nono ma se ta ga dama take bashi,har na gaji da baqin halinta na sake ta.
Umma tace"amma dai duk da haka haqqi ne akanta a snr da ita"
Yace"maman yusra kinfi kowa sanin bana son Saifuddeen yasan wace ce mahaifiyar sa dmn baqin ciki ne kawai a gare shi,a gurin hajiya ya tashi tun da yayi wayo ya fahimci cewa hjy kakar sa ce,ya fara damuna ina mahaifiyar sa,ban ta6a gaya masa ba sai dai kawai nace tayi tafiya da haka har Allah yasa mukayi aure nida ke,a gabanki na kawo shi nace masa gaki kece mahaifiyar sa da yake damuna kullum,kina kallon yanda ya rungume ki cikin tsananin farin ciki da jin dad'i wanda tun daga lokacin ya d'auka kece mahaifiyar sa da ta haifeshi har yau baisan bake kika haife sa ba and still bana so ya sani dan haka kar ki qara min zancen wnn banzar matar bana so.
Kayi haquri inshaa Allah hakan bazai sake faruwa ba.
umma ta fad'a tare da tashi ta fita daga d'akin.
kici6us tayi da Nusaiba tsaye a bakin qofar d'akin idonta tap da qwallah da alama ta ji duk abinda suke fad'i.
Wani irin kallo umma ke mata da kmr mamaki snn taja hannun ta da sauri ta tafi da ita zuwa d'akin ta,
tace "Nusaiba uban me kikeyi a bakin qofar Abbanku kika la6e kina sauraren abinda muke fad'i iye!
Da sauri ta girgiza kanta tare da share hawayen da suka zubo mata tace"wlh umma ba la6e nake maku ba,umman kd ce ta kira a waya ta tace na kai maki wayar tayi ta kiran wayar ki baki d'aga ba shine naje ban same ki a d'aki ba nazo d'akin Abba da niyyar maku knocking shi ne se.....
Shine se kika ji muna magana kika tsaya kina sauraren mu ko!to bari kiji in gaya miki wlh kar inji mgnr nn ta fito kinji ko!
Da sauri Nusaiba ta gyad'a kanta alamar taji snn ta fita daga d'akin kmr yanda umma ta umarce ta.
Taje d'akin su tayi kwance kan bed kmr wata marar lafiya dan gabad'aya se taji tausayin yayan nata ya kama ta yazai ji idan ya gano umma ba mahaifiyar sa bace bayan yana mata kallon ita ce ta haifeshi....."Nusaiba lafiya me yake faruwa?
zarah ta tambaya wacce tana zaune kan bed koda Nusaiba tazo ta kwanta.
A kafai ce Nusaiba tasa hannu ta share hawayen da suka sakko kan kumatun ta sbd ta bawa zarah baya bata iya lura da abinda take ciki,byn ta share hawayen ne snn tace"ba komai kaina ne naji ya d'an sara min shine na kwanta"
Muryar ta a sanyaye ta mata sannu.
Snn taci gaba da duba littafan ta na islamiyya da take dubawa sbd dama aikinta knn idan bata yin komai,wacce duk ta d'an fad'a sbd zullumin auren da za'a mata da wanda bata san ya rayuwar ta zata kasance ba,wanda tun rnr ta ganshi da Sophie suna wnn iskancin wani irin tsanar sa take ji a ranta ko ganin sa bata son yi asalima bata sake ganin sa ba d'in tun daga rnr dan kwata kwata ya daina shigowa cin abinci,gidan su jamil yake zuwa can yaci.
Saura kwana d'aya asa lalle suka tafi Rimin dako ita da Nusaiba da kuma Nadiya wato 'ya ga umman kd wacce shekarun su d'aya da Nusaiba sune suka zama en matan amarya tare da dije dake can.```
```A washe gari aka sa lalle snn suka dawo kano akayi sauran bukukuwa rnr juma'a aka d'aura aure and by 10pm aka kai Amarya ba kad'an ba zarah tayi kuka har ta gode Allah shike nn da gaske dai an d'aura auren nn har gata a d'akin ta an kawo ta,tana zaune kan bed kanta qasa fuskar ta a rufe da gyale kmr dai kowace amarya,su Nusaiba,nadiya da dije se sheri suke ta mata kmr yanda en matan amarya keyi tana jinsu bata tanka su ba dan ita kad'ai tasan irin baqin cikin da take ji a ranta an had'a ta da miji d'an iska dako qaunar ganin sa bata yi su har sunga gurin barkwanci.
Bayan kowa ya watse tana nn zaune kan bed ita kad'ai still fuskar ta a rufe se ci gaba take da kukan ta dan se kukan ma ya dawo mata sabo.
Qofar d'akin taji an bud'e da qarfi har sai da ta tsorata ba shiri ta miqe ta sauka daga kan gadon tana kallon Saifuddeen da shine ya banki qofar d'akin ya shigo yana mata wani irin mugun kallon da yasa ta soma ja baya,shi kuma se matsowa yake inda take har ya had'e ta da jikin gina,yana kallon ta fuskar nn tashi kmr wani zaki ba annuri ko kad'an,zarah kuwa gabad'aya ta kame jikin gina tana kallon sa a tsorace,wacce ba shiri ta saki qara sbd yanda yasa qafar sa ya daki qafar ta da qarfin tsiya se mutsustsuka qafar yake d'auke da takalmin sa masu masifar ciwo snn yakai hannun sa a bayan wuyan ta ya lotsa akaifun sa ciki sosai ya riqe mata jijiyoyin wuya gam tamkar ze 6alla mata wuya.
Ae kuwa take idanuwan zarah suka yi jajur se faman qoqarin qwatar kanta take amma ta kasa.
[11:14AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Wednesday 14/02/2018_ *芦禄禄芦芦禄SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 12*
Saifuddeen kuwa se qara matse mata wuya yake yana mai ci gaba da mutsustsuka qafar ta,Zarah dake ta qoqarin qwatar kanta ta saki qara cike da jin zafi cikin kuka tace"wae kai wane irin mugu ne me na maka!
A qufule yasa hannun sa da yatsun sa biyu ya mugun matse mata baki snn cikin kakkausar murya yace"ke! dan ubanki har tambaya kike,to bari kiji ba'a ta6a babbar jakar da ta shigo rayuwa ta ba ta lallata min duk wani tsarin na rayuwa ta ba irin ki,wacce ko d'aura min ke akayi a qafa bazan ta6a janki ba wlh se dai na tsinke na yar,dan haka tun wuri kiyi gaggawar cire cewa kin zo gidan nn ne dmn aure never!
Kisa a ranki cewa kinzo fursun ne inda zan azabtar dake na miki hukuncin laifin da kika aika ta a gare ni,dmn bazan ta6a barin ki ba wlh se na hukunta ki hukunci mafi tsanani da se kinyi nadamar zowar ki duniya!
Supid!!
Ya fad'a tare da jefar da ita gefe ta fad'i da qarfi har sai da goshin ta ya daki gefen bed da sauri ta dafe goshin nata tare da fashewa da wani irin kuka yayinda d'ayan hannun ta ke riqe da qafar ta da ya mutsustsuke duk tayi wani irin jajur,wuyan ta kuma ji take kmr still bai janye hannun sa ba sbd zafin bala'in da take ji,wacce tana jin yanda jini ke d'an silalowa a hankli daga bayan wuyan nata,ga bakin ta dake mata sululi sbd matsar da ya masa.
A ranta se Allah ya isa take ta mishi tana ci gaba da kuka a nn har bacci ya kwashe ta a gurin bata sani ba.
Washe gari da qyar ta iya jan qafar ta taje ta d'auro arwala tayi sallah.
Bayan ta idar ta koma kwanciya,byn wuyan ta da qafar ta duk sun kumbura tana jin kanta kmr wata mara lafiya haka dai ta samu bacci ya d'auke ta.
Se guraren 9 ta tashi tayi wanka ta shirya,zuwa qarfe 10 da rabi se ga su Nusaiba sun zo mata da breakfast d'inda umma ta basu su kawo.
Dama yunwa take ji tayi zaune taci se da ta qoshi,nan fa sukayi ta fira abinsu
Se bayan mutane sun fara zowa ne snn suka tashi zasu sauka downstairs zuwa falo a nn Nusaiba taga yanda zarah ke taka qafar ta da qyar tana d'ingishi,nadiya da dije sam basu
lura ba sbd suna gaba su suka fara fita.
Nusaiba da ta gani ta jata baya kad'an tana kallon qafar snn tace"6ter what's wrong,me ya sami qafar ki haka tayi jajur?
Zarah ta ta6e baki tace"yayanki mana mugu shine duk ya mutsustsuke qafar"
Me kika mishi?
Nusaiba ta tambaya
Zarah tace"hm meko mugunta kawai"
Snn ta yaye gyalenta dake yafe tun daga saman kanta tace"duba bayan wuyana ma ki ga duk ya kumbura sbd matsar da ya min"
Nan Nusaiba takai hannun ta a hankli ta ta6a gurin tana dubawa tace"kai oh my God!
lallai yaya saif Allah tun wuri kar ki barshi yaci gaba da miki haka"
Zarah tace"hm basshi Allah ya isa ne zai kama shi dan bazan ta6a yafe masa ba wlh"
Nan ta maida gyalen ta ta yafa har zuwa goshin ta da ya d'an yi ja duk ta rufe bata so mutane su gani,haka ma da suna saukowa daga staircase se taka qafar ta take a hnkli dan kar mutane su fahimta,amma duk da haka se da nadiya da dije suka fahimta har ma suka tambaye ta me ya sami qafar ta tace musu abune ya fad'o min a qafa shine naji ciwo.
Komai basu ce ba se sannu da suka mata snn suka qarasa gurin mutane dake zazzaune a falo duk mafi yawan su en rimin dako ne wato maman dije da sauran en uwa,wa enda a nn garin suka kwana gurin umma.
Take gida ya cika tamkal se yinin biki ake Saifuddeen kam tun da safe ya fita gidan be sake dawowa ba har yamma tayi kowa ya watse se su Nusaiba kad'ai wa enda suma tafe suke sun fito zarah ta rakosu bakin gate,odar da akeyi ne yasa suka tsaya mai gadi ya bud'e gate d'in,se ga jamil ya kunna motar sa a cikin gidan shida saifuddeen wanda motar shi ce ta sami matsala shine jamil ya kawo shi ba dan yaso ba sbd yarinyar da Saifuddeen yake tare da ita tana nn zaune a seat d'in baya se k'as k'as take tana cin chewing gum ta wani ci uban ture kaga tsiya,qafar ta kan d'aya tana faman danne danne a waya wacce tana d'aya daga cikin en matan da ke matuqar son Saifuddeen da se yanzu ne ya fara lokacin su,jamil kam abun har mamaki ya basa.
Su Nusaiba kam fita kawai sukayi sbd driver na waje yana jiran su ba tare da sun tsaya kula da wa enda ke cikin motar ba kawai dai sunga Saifuddeen da jamil basu kula da wacce ke baya ba sbd duhun glass d'in motar bazai barsu su iya ganinta kai tsaye ba se idan sun kula.
Zarah na tsaye har sai da suka shiga mota suka wuce snn ta koma daga ciki,idon Jamil qyar a kanta ganin yanda take d'ingishi ya kalli Saifuddeen dake qoqarin bud'e qofa ze fita yace masa"halan me ya sami zarah a qafar ta har take yin d'ingishi?
Wani banzan kallo Saifuddeen ya mishi snn yace"oho mata in ma kayi wani banzan tunani ne to ka ma watsar dan kasan wnn abar ko duniyar nn kaf za'a ban bazan neme ta ba wlh"
Ya buga tsaki tare da bud'e ganbun motar ya fita Jamil ya bisa da kallo d'auke da murmushi shi sam bai ma kawo wani tunani ba dan yasan halin abokin nasa bazai ma ta6a kula ta ba.
Yana kallon sa har suka shige shida yarinyar sa,ya girgiza kansa kawai
snn yaja motar sa ya bar gidan.
Saifuddeen kuwa koda suka shiga sun sami zarah tana kashe kayan kallo sau d'aya ta kalle su ta kauda kai taci gaba da aikinda take,Saifuddeen ya riqe waist d'insa yana kallon ta yace"ke dan ubanki gidan ku ba'a koya maki tarbiya bane da baza kizo ki durqusa ki gaida mutane ba!
Kafin zarah tace komai wacce yake tare da ita ta wani ya tsine fuska tana kallon zarah tare da fad'in"No dear ka barta kawai ni bana ma son gaisuwar ta,zo mu tafi"
Taja hannun sa suka haura sama zuwa d'akin shi,
zarah ta bisu da kallo ta6e da baki tace"an dai yi asara ga kyau amma ba kyan hali,Allah sa ma kaf karuwan duniyar nn zaka kawo a cikin gidan nn ni ina ruwana"
Nan ta ida kashe kayan kallon ta haura sama zuwa d'akin ta.
Washe gari da safe tana kwance kan dardumar sallah tana bacci se ga Saifuddeen ya shigo d'akin riqe da qaramin bokiti a hannun sa cike da ruwa,a tsiyace ya kwara mata su gabad'aya kan fuskarta,ba shiri ta farka tare da sakin ihu cikin mugun tsorata ta miqe a rud'e tana waige waige a tunanin ta ko tayi gamo da aljanu ne suka jefo ta rafi.
Saifuddeen dake kallon ta ya kwad'a mata gigitaccen mari yace"kalle ni nn nine kije ki bud'e qofa se faman danna doorbell ake duk an hana min bacci.
Zarah dake dafe da kuncen ta tana kuka tace"amma wlh se Allah ya isa min bazan ta6a yafe maka ba....wani lafiyayyen marin ya koma kife ta dashi ya nuna ta yace"mind ur tongue ban tashe ki dan ki gaya min mgnr banza ba,maza kije ki bud'e qofa nace ko yanzun nn nayi gunduwa gunduwa dake,kinzo se sharara bacci kike tunda an gaya miki nn gidan ubanki ne da zaki kwanta ki huta.
Da har zata ce bazata ba tayi shiru tana kallon farar kyanwar da ta shigo a tsorace taja baya dan mugun tsoron kyanwa take.
Saifuddeen da ya fahimta ya d'auki kyanwar yace"zaki je ko sai na cillo miki ita"
Da sauri ta girgiza kanta muryar ta na rawa tace a'a zanje wlh.
Nan ta fita da sauri sauri se fmn d'ingishi take har ta iso bakin qofa ta bud'e.
Mai gadi ne tsaye a bakin qofar wanda har ze juya yaji an bud'e qofar ya tsaya,se da ya gaida ta snn yace"dama ruwan gidan ne suka d'auke gashi ina so zan bawa flowers ruwa"
"to an gaya ma ni wani abu na sani na gidan nn ne"
Zarah ta fad'a ranta a 6ace tana kallon sa kmr shine Saifuddeen.
Mai gadin bai ce komai ba se haquri da ya bata ze juya se ga Saifuddeen,da saurin ta ta bar gurin dan still yana riqe da kyanwar a hannu sa.
Tambayar mai gadi yayi mene ne,mai gadi ya gaya mishi.
Nan ya fita yaje ya duba ruwan suka kawo.
Da ya dawo kai tsaye d'akin zarah ya nufa da niyyar gindaya mata sharuddan gidan,but yana 6ird'a qofar d'akin ya jita a rufe.
Zarah na jin sa tayi banza dashi se jiqaqqin tufafin jikin ta ta cire wato kayan bacci riga da wando da kuma qaton hijabin sallah da ke jikinta,se ta zamo daga ita se inner wears,half vest ce baqa da pant baqi mai kmr bomb short dan ya rufe mata d'uwawu sosai har zuwa gurin cinyoyin ta kad'an.
Sanyi take ji sosai har tana kakarwa amma bata nemi wani abu ta rufa jikinta ba,dan jin inner wears d'in jikinta take kmr suma sun d'an jiqe,tayi gurfane kan guiwoyin ta tasa tufafin da ta cire tana tsane ruwan da sauri tana matsewa a cikin bokiti.
Saifuddeen da yaje d'akin sa yana kallonta ta jikin laptop d'in shi se kallon ta yake kmr da mamaki,sbd gashin da ya gani da ita sosai mai sul6in gaske baqi wulik dashi ya zubo har saman gadon bayanta ga black half vest da black bomb short d'in jikinta sun qara fito da hasken fatar ta sosai se tayi kyaun duba kmr wata wayayya.
Ta6e bakin sa yayi snn ya rufe laptop d'in tare da cillar da ita gefe.
[11:14AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Thursday 15/02/2018_ *芦禄禄芦芦禄SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 13*
Snn ya maida duban sa gun wacce yazo da ita jiya a nn ta kwana tana kwance rufe da blanket se fmn sharara bacci take,hannu yasa ya yaye blanket d'in,ba wata sutura a jikin ta bai damu ba se tashin ta ya shiga yi.
A hnkli ta bud'e idon ta tare da jan blanket ta rufe jikinta snn ta tashi zaune tana kallon sa tace"ya akayi ne dear?
Yace"wanka zakiyi kiyi ki bar gidan nn kafin mutane su fara shigowa bana son qananun maganganu"
Tace"to da akwai abinda zanci idan na fito dan ni
Book Chapters
Chapter 5
Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37