google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gobe Monday.
Tunda ta juya cikin tako d'aya bata qara wani ba ta tsaya cak sbd kiran da saifuddeen ya mata.
Ya taso ya qaraso gurin ta ya juyo da ita yana kallonta kanta qasa taqi yarda su had'a ido,se hawaye ya gani suna saukowa daga kumatun ta,a hankli cikin damuwa yace"oh Allah mene ne kuma zarah?
Ni bazan iya ci gaba da zama a gidan nn ba,ina son kaci ka min alqawari na dan Allah in tafi.
Zarah ta fad'a tana mai share hawayen da suka zubo mata.
Saif dake sauraren ta,shi kam gaban sa ne yaji ya fad'i,snn lokaci d'aya yaji duk jikin sa a sa6ule,be iya ce mata komai ba se kama hannun ta yayi ya tafi da ita kan kujera suka zauna yana kallonta da kulawa yace"No zarah indai akan wnn abun ne da duk kika sa kanki a damuwa ni bazan sake ki ba,idan zaki cire damuwar ki cire,abu ne fa wanda dan ya faru tsakanin miji da mata ba komai bane,ni sau nawa ina nuna miki tawa buqatar bansa kaina a damuwa ba se ke,yi haquri kinji ki daina zancen nn dan Allah,ki gaya min duk abunda kk so zan miki.
Duk yana mgnr ne cikin rarrashi.
Zarah da still kanta ke qasa tace"ni alqawari na kawai nake so ka cika min dan Allah.
Handkerchief ya ciro ya share zufar da yaji ta d'an tsastsafo mishi a goshi sbd maganar da tazo mishi da ita. Yace"meyasa zarah ko wanda kk so ne yake matsa miki?
Girgiza masa kai tayi tare da fad'in"um um ni ba wanda nake tare dashi fa,kawai dai ina buqatar ka cika min alqawari na ne,bana son abunda ya faru dani ya sake faruwa dani ina jin kunya.
Da saurin sa yace"No zarah nayi miki alqawarin bazai sake faruwa da ke ba"
Cikin muryar kuka tace"kmr ya abunda ya faru dani fa ni kaina bansan ya akayi ba"
Saif da duk ya daburce yace"to shikenan naji amma kinsan idan na sake ki yanzu Abba zai d'auka ko dan ya hana ni auren Sophie ne naji haushi na sake ki,kuma dama ae ce maki nayi se idan na samu auren Sophie snn ko zan cika maki alqawarin ki.
Se a lokacin ta kalle shi qwalla tap a idonta tace"to ai ni da kai fa ba me qaunar juna meyasa baza ka sake ni ba"
Yace"yanzu ke idan na sake ki me zaki cewa su umma? muryar ta a sanyaye tace"nima ban sani ba".
Yace"To kin gani nima bansan me zan gaya musu ba kuma haka kawai baza ayi saki ba,dan haka idan har kina so in sake ki to kije kiyi tunanin abunda kikasan su Abba baza su ga laifin ko d'ayan mu ba,ko kina da wata hujjar ne yanzu?
Ya fad'a cikin tsare ta da ido.
A hnkli ta girgiza masa kai alamar a'a.
Yaji wani dad'i a ranshi har yana sauke ajiyar zuciya.
Yace"to kije ko yaushe kika sami hujja kizo ki gaya min,amma fa daga yanzu bana son in sake ganin ki a cikin damuwa ki sake kamar ba wani abunda ya faru idan ba haka ba ko kin kawo min hujja bazan saurare ki ba bare har na rubuta miki saki.
Gyad'a masa kai tayi zata tashi ya riqo hannun ta yana kallon er fincikar rigar da ke jikinta ta mata kyau sosai,cikin wata irin murya qasa qasa yace"ina zaki tafi me kika fito yi?
Zan d'aura ruwan zafin tea ne nasa a flask sbd ina so zanyi azumi.
Azumin ranko?
Ya tambaya yana me kallonta.
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
Yace"to nima zanyi se kisa ruwan dani qarfe hud'u zan zo na tashe ki kinji"
Bata yi magana ba se gyad'a masa kai da tayi.
Snn ta tashi ta wuce ya bita da kallo har ta shige kitchen,ya sauke numfashi a hankli tare da jingina bayan sa a jikin kujerar da yake zaune,idanuwan sa a lumshe se wani irin qaunar zarah yake ji a ranshi,da ya d'auka ko birge shi ne kawai take.
Wanda yana zaune a gurin idanuwan sa a lumshe har se da zarah ta gama abunda takeyi a kitchen ta fito riqe da flask,snn ya bud'e idanun sa ya bita da kallo har ta 6acewa ganin sa snn ya iya tashi ya kashe Tv da hasken falon ya haura sama zuwa d'akin shi.
Qarfen hud'un asuba koda yazo tashin ta ya samu har ta tashi tana bathroom se yunqurin amanta yake jin yana fitowa a bathroom d'in,kae tsaye ya shiga bathroom d'in da sauri.
Ya same ta gun washbasin kan ta a duqe riqe da brush a hannun ta tana ci gaba da yunqurin amai.
Ya tallabo fuskar ta yana kallon ta yace"mene ne?
Ruwa tasa ta wanke bakin ta snn tace"ba komai brush kawai nakeyi.
Saif dake kallon ta yace"wane irin brush ne kk yi haka,ki riqa sa brush d'in a hankli kinji.
Gyad'a masa kai tayi tare da kunna famfo ta wanke brush d'in tasa a d'an wani cute case dake manne a jikin bangon bathroom d'in nasa brushes ta bud'e ta saka snn suka fito yana rungume da ita a jikin sa.
A nn d'akin sukayi sahur zaune kan rug suna fuskantar juna,yayinda saif shan tea kawai yake amma hankalin sa na gun zarah se kallonta yake tayi musamman yanayin zaman ta duk yafi tafiya da imanin shi,wacce tayi zaman ne cikin matse cinyoyinta kmr zamanta tahiya sbd yanayin rigar ta dole se tayi irin wnn zaman,en kyawawan fararen guiwoyin ta a bayyane,duk tabi ta tsauwala sbd ta lura da kallon da saif keta yi mata.
Wanda koda suka gama sahur ya bar d'akin duk a jiqe yake jin kansa shiyasa yana zuwa d'akin shi ya gaggauta yin wanka.

Washe gari shi yakai ta school ya kuma d'auko ta.
Da shigar ta d'aki ta tu6e ta fad'a bathroom tayi wanka byn ta shirya snn ta tafi kitchen dmn girka musu abunda zasu ci idan ansha ruwa.
Saif yazo yayi tsaye a bakin qofar kitchen d'in yana kallonta,zarah bata san dashi ba se qamshin turaren sa da taji,ta juyo ta kalli bakin qofar kitchen d'in ta ganshi sanye da qananun kaya ya cire suit da alama wanka yayi.
D'an murmushi ya sakar mata haka ita ma snn ya qarasa gurinta tare da riqo waist d'inta ya d'an tafi da ita jikin sa yana kallon,tarugu tattasai da albasa da ta yayyanka tana d'an soyawa sama sama had'e da qoda da tayiwa gutu gutu,ya kalle ta yace"me zaki dafa mana ne?
Zarah dake motsa abubuwan da take soyawa tace"taliya ce zan dafa had'e da wake naga lokaci ya tafi"
Yace"wow that's my best food but sauran abubuwan da kika d'aura mene ne?
Ya tambaya had'e da kai hannun sa ya bud'e d'ayar tukunya wanda da saurin sa ya saki marfin yana yarfi da hannu.
Zarah ta kalle sa d'auke da er dariya a fuskar ta.
Saif da har ransa yaji zafi yace"dariya ma kike min kinji zafin wae,ya d'aura mata en yatsun sa kan kunci,se kuwa taji yatsun nasa da zafi,a hnkli ta kama hannun nasa tana dubawa har ma ta sami kanta da hura masa en yatsun nasa da taga sunyi ja.
Kafin take kallon sa cikin yanayin murmushi tace"kai d'in ne da kaud'i in bashi ba me yakai namiji da bud'e tukunya.
Murmushi kawai yayi ya koma kai hannun sa ze bud'e tukunyar yana fad'in "so nake inga abunda yake ciki"
Tayi saurin riqe masa hannu tana fad'in"meye haka zaka sake qone kan ka fa"
Saif ya kalle ta wanda shi kam ae qonewar yake so ya sake yi dmn ta sake hura masa iskan bakinta da yaji wani irin sanyi da dad'i na ratsa hannun sa har be so ta daina ba ma.
Wanda a hankli ya lumshe idanun sa tare da ware su a kanta yace"to gaya min meye a ciki?
Tace"d'ayar tukunyar farfesun kaza ne d'ayar kuma wake nake tafasawa.
Tayi mgnr ne tare da bud'e masa kowace tukunya ya gani.
Ya kama hannun ta yana dubawa yaga ita kam ba abunda yatsun ta sukayi duk da irin laushin su kuwa dan har ma tafi shi laushin hannu.
Zarah da ta fahimci dalilin kallon hannun ta da yake,a hankli ta zare hannun nata da ya kama,d'auke da murmushi tana fad'in mu d'in ne na daban aikin mu ne mun riga mun saba ba abunda wuta zata mana.
Au haba ae kuwa yanzun nn zan gwada in gani,saif ya fad'a tare da rungumo ta ta baya snn ya kama hannun ta zai kai a wutar gas cooker.
Da sauri cikin maqe hannu Zarah tace"Wayyo!
Ya saki hannun had'e da lakato hancin ta yana murmushi yace"matsoraciya nida da wasa nake miki to"
Murmushi kawai tayi tana kallon sa har ya fita daga kitchen d'in,snn ta maida hankalin ta gun aikin da take yi.

Da aka sha ruwa bayan sunyi sallah,a nn falo sukayi zaune kan rug suna cin abinci a plate d'aya,abun se yayi musu kyau kmr dama can sun saba.
Wa enda suna cikin cin abincin ne aka soma danna doorbell,saif ya tashi yaje ya bud'e qofa.
Jamil ne,saif ya masa iso ya shigo ya zauna yana me amsa gaisuwar zarah.
Yayinda saif yaje ya zauna a gaban zarah suna fuskantar juna wato inda ya tashi.
Invitation a hannun sa yana dubawa,snn ya kalli jamil da shine ya bashi invitation d'in yace"this coming Saturday za'ayi auren knn?
Jamil yace"eh"
Allah kaimu
Cewar saif kafin jamil ke cewa amin.
Wanda duk yana yin maganar ne da qyar cikin danne kishi,ganin tare ne fa suke cin abinci har ma wani dukan uku uku yaji gaban sa nayi.
Can ya tsinkayo muryar saif yana cewa zarah taje ta kawo masa abinci,yace"A'a am ok"
Daga haka ya miqe tsaye ze fita,saif yace"plz to ka d'an jira ni mana mu kammala cin abinci da akwai mgnr da nake son zamuyi"
Jamil da baya jin zai iya kallon su suna cin abinci tare yace"ok zan d'an fita na dawo kafin ku kammala cin abincin.
Saif yace"ok to"
Snn jamil ya tashi ya fita.
Zarah ta kalli saif tace"katin d'aurin auren sa ne?
Saif ya kalle ta yace"tukuna ae shi wacce zai aura ba a ko sake ta ba tukun"
Wani iri zarah taji zancen tace"kmr ya ba'a saki wacce zai aura ba?
Saif ya d'anyi murmushi yace"da gaske nake gaya miki ba a saki wacce zai aura ba yana jiran a sake ta ne snn suyi aure"
Zarah tayi er dariya tace"uhm kaima dai da wasa kake se kace baya da aikin yi zai tsaya jiran wacce aka aura wae har se an sako ta,ae komai sonda yake mata gwanda kawai ya haqura tunda har yaga an riga shi ita.
Saif dake kallonta yace"dan baki san yanda abun yake bane shiyasa,ita yarinyar tun lokacinda ya fara ganin ta yaji yana sonta,amma ita bata sani ba dmn bai ta6a gaya mata ba,yana shirin shigar da kanshi,kwatsam yaji za'a aurawa abokin sa ita,gashi abokin nasa sam baya son ta auren dole ne za'a masa da shi har yarinyar duk ba mai son juna,shine da yaji duk yabi ya rud'e ya gayawa abokin nasa irin sonda yake mata har ma ya buqaci ya bar mishi ita ya aura tunda shi baya so,duk da abokin nasa yayi mamakin sonta da yake haka yayi fafutuka na ganin cewa auren ya koma kan jamil,dmn shi kuma ya samu a barshi ya auri wacce yake so,amma se hkn be samu ba,duk jamil yabi ya damu,abokin nasa yace kar ya damu ya masa alqawarin ko bayan anyi auren ze sake ta ya aure ta dmn shidai baya iya zama da ita,ko zaman da zeyi da ita na d'an wani lokaci dan ba yanda zeyi ne kawai an turasasa mishi,amma burin sa bai wuce ya auri wacce yake so ba.
Zarah tace"Hm lallai abu se kace film shine yaqi yin aure yana jiran ta,to idan yarinyar tazo tace bata son shi fa bayan an sake ta?
Saif ya kalle ta kawai yace"bana jin cewa baza ta so shi ba sbd tana ganin kirkin sa.
Amma ae ganin kirki daban so daban.
Hakane amma kirkin mutum nasa a so shi.
Amma kuma na kasa fahimtar tsakanin sa da qanwar sa zainab yana ganin kirkin ta,amma baya sonta ita kuma sosai take qaunar shi har bata iya kula duk wani saurayi.
Zarah dake kallon sa tace"zainab wnn da ke dubani idan bana da lafiya?
Eh ita
Dama ba qanwar sa bace uwa d'aya uba d'aya?
A'a er gwaggwan shi ce da ta rasu,wato er qanwar mahaifin shi,shine baban sa ya d'auko ta ya riqe ta a hannun shi tun tana yarinya a gidan su jamil ta taso.
Allah sarki to meyasa baya son ta?
Nima ban sani ba kawai dai baya son ta asalima be ta6a yarda ya nuna mata cewa ya fahimci tana son shi ba.
Zarah tace"dan Allah to ka bashi shawara ya aure ta,zainab tana da kirki sosai kuma nidai naga dacewar su,ya daina jiran wacce ba lallai bane ya same ta,duk da dai yayi nisa baya jin kira dan da alama son wnn yarinyar ya zautar dashi tunda har ya tsaya jiran a sake ta ya aura,bata ko san yana yi ba ma,amma ko dan kirkin sa ina roqon Allah ya bashi ita se ya had'a su ita da zainab ya aura ko"
Shiru saif yayi ya kasa ce mata komai,yana jin wani irin haushi a ranshi kan me ma ya d'auko mata zancen.
"Ka bashi wnn shawarar dan Allah".
Zarah ta fad'a cikin marere ce fuska tana kallon shi.
Ransa a 6ace ya daka mata tsawa yace"da Allah yi min shiru naqi in bashi shawara!
Jiki sanyaye zarah ta zuba mishi ido tana kallon shi,kana ta miqe tsaye sbd doorbell da taji ana dannawa taje ta bud'e qofa,ras taji gaban ta ya fad'i ganin d'aya daga cikin en matan saif ne tazo,wacce shine karon farko da ta ta6a jin faduwar gaba da kuma wani irin abu da taji a ranta.
Saif da ya taso yana tambayar ta waye?
Kallon sa kawai tayi bata iya ce masa komai ba se barin gurin tayi ta haura sama zuwa d'akin ta.
_Wednesday 21/03/2018_
*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*




By
*Billy giro😊*




*Dedicated to»»»Zarah gwandu*



*«»Page«» 40*
Da shigar ta d'aki ta hau tu6e kayan jikinta,duk haushin saif take ji a ranta da bata ma san dalilin tu6ewar da take yi ba.
Bayan ta gama tu6ewa ta d'aura towel tayi zaune kawai kan bed tana tunanin shi kam wane irin mutum ne marar tsoron Allah asararre azumi fa yayi amma lokacin da suke yin bud'a baki karuwa tazo gurin shi suje su hau yin iskancin da suka saba,baya ko jin kunyar azumin da ya yini dashi
Mtsw tayi tsaki tare da fad'in"Allah kyauta"
Nan se ga saif ya shigo d'akin,sau d'aya ta kalle sa ta kauda fuskar ta gefe,be damu ba se qarasawa yayi ya zauna gab da ita tare da kai hannu ya juyo fuskar ta yana kallon towel d'in da ke d'aure a jikin ta da tsayin sa iya rabin cinya,ya kalle ta yace"ya haka kin tu6e ba mu ko kammala cin abinci ba?
"Shan iska nake"
Ta fad'a fuskar ta a d'aure,had'e da janye hannun sa ta sake kauda fuskar ta gefe.
D'an guntun murmushi saif yayi yana mamakin wane irin shan iska ne wnn duk irin sanyin split dake ratsa koina a cikin gidan.
Ya sake juyo fuskar ta yace"to ae se ki cire towel d'in kiyi zir ta yanda zaki fi jin iska sosai ko.
Zarah dake kallon sa duk haushin sa da take ji kawai ta sami kanta da yin murmushi,se kuma ta kauda fuskar ta,dan se ma taji kunya duk da dai yanayin maganar sa cikin zolaya ne da hakan ne ma yasa ta yin murmushi.
Saif da ya fahimci kunya taji yayi d'an murmushi tare da kama hannun ta yace"to tashi muje mu qarasa cin abinci.
Ta qwace hannunta cikin shan toka awa wata qaramar yarinya tace"ka tafi kawai ni bazan je ba kana min tsawa haka kawai ba dalili".
A hankli ya janyo ta jikinsa cikin muryar rarrashi yace"sorry ni kaina bansan meyasa na miki tsawa ba"
Zarah dake kallon shi a ranta tace"lallai wnn shi ya cika masifaffe,wato haka kawai ya mata tsawa da shi kansa baisan dalili ba,ba fad'a ba komai suna maganar su lami lafiya abu awa me aljannu.
Ta ta6e baki tare da fad'in"to bari na kawo mana abincin mu a nn dan bazan iya zama falo haka ba kar yaya jamil ya dawo ya same mu.
Ta qarashe mgnr ne had'e da miqewa tsaye,saif ya riqo hannun ta yana kallonta yace"kisa kayanki mana se muje mu qarasa cin abincin mu can yafi.
Zare hannun ta tayi tare da fad'in"Aa ni wanka nake so nayi idan mun kammala cin abinci.
Daga haka ta wuce ba tare da ta jira me zai ce ba.
Ya bita da kallo yanayin tafiyar ta jikin ta na karkad'awa abun sha'awa.
Kana ya kauda fuskar sa cikin sauke numfashi,yaso ace ta maida kayan jikinta ko zai samu natsuwar cin abinci,dan shi kam dai ya rasa wace irin jarababbiyar sha'awar ta ce ke damun sa da har ko yaushe take hana mishi sukuni,baya da halin ya tsura mata ido na minti biyu yanzu ne ya fara jin wani abu,azumin nn ma da sukayi da qyar ya samu yaga ya kai shi,bayan da sahur ma sai da yayi wanka,ko zuwan da yayi kitchen ya same ta duk a cikin juriya yake yin komai.
Wani numfashin ya koma saukewa a hankli ya kwanta yana jiran dawowar zarah.
Koda ta dawo still yana kwance idanuwan sa a lumshe,hannuwan sa duka biyu a bayan kanshi yayi pillow dasu.
Ajiye abincin tayi kan rug snn taje ta zauna kusa dashi tare da d'aura tafin hannun ta a hankli kan goshin sa,ya bud'e idanun sa a kasale da har suka soma canza kala yana kallonta yace"har kin dawo?
Gyad'a masa kai tayi tare da fad'in"har ma inata sallama baka amsa ba shine na d'auka ko baka jin dad'i ne"
Lafiya ta qalau banji sallamar ki bane sorry.
Nan ya tashi tare da kama hannun ta suka zauna kan rug.
Wanda suna kammala cin abincin ya tashi ya fita.
Nan ita ma Zarah ta tashi taje ta bud'e fridge ta d'an tsiyaya fresh milk a cup zata sha,se kawai ta tsaya shiru tana kallon fresh milk d'in,wacce kusan kullum haka take yi,tana son sha amma se byn ta tsiyaya a cup se kuma ta kasa sha ta mayar,sbd tuna cewa tana gama shan fresh milk ne wnn abun kunyar ya hau kanta.
Ko yanzu abunda ta tuna knn ta mayar da fresh milk d'in bata sha ba.
Ta kwashe kwanikan da suka ci abinci taje kitchen ta wanke snn ta dawo,kae tsaye ta fad'a bathroom tayi wanka snn bayan ta fito tayi sllr isha'i.
Tun lokacin da saif ya fita d'akin bai sake dawowa ba se 11.
Be qarasa ciki ba se tsaye yayi a bakin qofa had'e da jingina bayan sa a jikin ganbu,qafafuwan sa a hard'e haka ma hannunwan sa rungume a qirjinsa yana kallon zarah dake kwance ruf da ciki,daga ita se half vest da bomshort d'an guntu sosai wanda da kad'an ma ya sauka kan cinyoyinta.
Yayi minti biyu tsaye a gurin yana kallonta kafin yake sauke numfashi a hankli cike da kasala snn ya qarasa ciki ya zauna kan bed se kallonta yake tayi se kace wata er tsana a yanda yake ganin ta komai nata abun sha'awa,ya matsa gab da ita yana shafa sumar kanta da ta tufke da ribbon,jelar gashin na kwance a gadon bayanta,inda a hankli yake bin gadon bayan nata da ido har ya sauke idanun nasa kan arse dimples d'inta,kmr da tsoro yakai hannun sa a gurin yana shafawa a hankli ya tafi har zuwa santala santalan cinyoyinta yana jin kmr kar ya daina shafar su dan se yaji cinyoyin sun masa wani irin laushi kmr yana ta6a boobs d'inta da duk su yafi qauna a jikinta da bazai ma iya fisalta irin laushin su ba shiyasa gabad'aya duk yake rikicewa idan yana shafar su.
Hakan ya janye hannuwan sa kan cinyoyinta ba dan yaso ba se dan yana son ya gyara mata kwanciyar ta,sbd sanin illar yanayin kwanciyar da tayi na ruf da ciki yakan sa ciwon qirji,ciwon zuciya,baqin rai da kuma makamantan su.
Yana gyara mata kwanciyar ta yasa blanket ya rufa mata jikinta har zuwa qirjinta dan ya fahimci kmr sanyin split ya fara ratsa ta da yawa.
Bayan ya rufa mata jikin ta ne ya d'auke mata handout din da ya gani kan bed da alama karatu take tayi bacci,dan ko wutar d'akin ma bata kashe ba.
Yasa mata handout d'in a cikin jakar ta ta zuwa school snn ya kashe mata wutar d'akin ya fita.
Washe gari koda zarah ta kammala shirin ta na zuwa school ta fita,se fmn jiran saif take be fito ba ga lokaci yana tafiya.
Har tayi tunanin ko ta kira drivern da ke kaita yazo,se kuma taga shima wani qarin 6acin lokaci ne kafin ya iso gwanda kawai taje ta dubo saif d'in tukun.
Nan ta koma daga ciki kae tsaye ta nufi d'akin sa tana mishi knocking.
Se can aka bud'e qofar,ga mamakin ta ba saif ne ya bud'e mata qofa ba, d'aya daga cikin en matan sa ce wato wacce tazo jiya suna tsakar yin bud'a baki,ashe bata tafi ba a nn gidan ta kwana.
Hm
Zarah ta fad'a a ranta tana me kallon saif da ya fito daga bathroom daga shi se d'an guntun wando,snn d'an qaramin towel riqe a hannun sa yana tsane ruwan jikin sa,wanda suna had'a ido da zarah yayi saurin janye idanun sa dan haka kawai yaji ya sami kansa da jin nauyin ta.
Zarah da bata ma san abunda take ji a ranta ba da saurin ta ta bar bakin qofar d'akin,ta fita se waje a bakin titi tana neman adaidai ta,sanin baza ta samu ba yasa ta shiga kiran drivern ta.
Kiran be ma fara shiga ba kawai taji an kar6e wayar had'e da tsinke kiran.
Koda ta duba saif ne wanda har ya fiddo motar shi waje,yana sanye cikin farar jallabiya ya kama hannun ta se binsa kawai take da kallo har yasa ta a mota suka kama hanya,duk wani abu da takeji a ranta haka ta danne ta ciro handout d'in ta tana karatu da alama test zasu rubuta.
Saif da still yake jin nauyin ta se satar kallon ta yake tayi,yana son tambayar ta ko suna da test ne,amma ya kasa tambayar ta har ya sauke ta school.
Haka ma da suka gama lectures ya d'auko ta,zarah bata damu da kallon ko gefen sa ba shi kam se kallonta yake yana son ya mata magana amma ya kasa samun fuska har suka iso gida.
Da isowar su ta fita mota ta wuce ciki.
Saif ya bita da kallo kawai,wanda har satin ya qare zarah ba ruwan ta da shi,abun da yasha mata kai kawai takeyi d'an shirin da suka fara duk suka daina kmr basu ba,duk da sosai ya shiga damuwa,amma se harakar gaban sa yake dan kullum da klr macen da zata shigo gidan ta kuma kwana se safe snn ta tafi,kuma shigowar su da fitar su duk a idon Zarah shiyasa ma ta fita harakan sa kwata kwata ko school ma driver tasa yaci gaba da kaita har suka kwashe sati biyu a haka.
Yau Wednesday tana dawowa school tayi wanka ta shirya cikin qananun kaya kmr kullum duk ta dawo wankan qananun kaya take masu fito da ita,duk da

Please Login or Register in order to submit comment