You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
my prince's insha Allahu soon munkusa zama iyaye"wayarshice tayi ringing dubawa yayi yaga mummy ce kiranshi video call kasancewar ya bar data bud'e d'auka yayi tare da Kallon mahaifiyartashi ta Cikin waya ya ce "mummynmu"Aira ma murmushi tayi ta ce " mummynmu ina yini"Cikin fara a Mummy ta ce ''lafiya qalau ya gajiya sarakan yawo kunje sai wahalarmun da jika kuke daga dai yanzu saiku nemu waje ku zauna"kallon juna Aira da Arman sukayi sai suka kalli Mummy kasa da kanta Aira tayi yayinda Arman ya ce "Mummy wani jikan kenan" cikin jikin daughter mana nasan k'ilama ya fara girma b'oyemun kawai kuke ko?A a a Mummy ai kinsan da tana da ciki kece zaki farajin wannan albishir din wlh bata da komai yanxu haka perioud take"Jikin Mummy ne yayi sanyi Dan duk daukarta tuni Aira ciki gareta har tafara sa ran Dan sosai ta matsu taga y'an jikokin nata murmushi tayi ta ce "To Allah ya kawo mai amfani" Ameen Arman yace yayinda Aira ta tashi tana Goge hawaye tayi bedroom da kallo Arman ya bita Nan suka cigaba da Hira Mummy Wanda hankalinshi Duka yana kan Aira saurin yiwa Mummy bankwana yayi tare da binta yana zuwa ya sameta ta hade kai da gwuiwa tana kuka subhanalla meye haka cutie me akayi miki kike kuka kin.manta ked'in amanace a wajena kukanki kamar yana nufin ban rik'e Amanar da aka bani ba ya k'arasa fad'a yana zuwa tare da rungumota "Cikin shashekar kuka ta ce " Yaya wata biyar Da Aurenmu amma har yanzu bansamu ciki ba nasan kaida Mummy Duka kunaso karfa naki haihuwa ka daina sona"Rufe mata baki yayi ya ce"Banyi tunanin haka daga bakinkiba cutie ko da haihuwa ko babu bazan tab'a daina sonki ba sannan haihuwa da kika sani ta Allah ce Duka yaushe mukayi Auren wata biyar nefa har zaki Fara mita sannan Nida Mummy Duka munasanki wa ya ce maki baki haihuuwa da zaki zauna kina kuka Cutie bantaba fushi dake ba Amma kika k'ara irin haka zanyi fushi ki maza ki Goge hawayen nan"Cikin Sauri ta Goge hawayenta tare da cewa "Sorry my hero bazan sakeba daga yau kayi hakuri please" gyada mata kai yayi ya ce "na hakura cutie na y'ar gatan Yayanta" murmushi tayi tare da Lafewa jikinshi tana jin dad'in daddad'an k'amshin turarenshi A haka bacci ya kwasheta Arman ya jima Rungume da ita yana Kara tunanin yarinta irin ta Aira wai kawai ta zauna ta dinga kuka sai kace wacce ta shekara goma bata samu haihuwa ba murmushi yayi tare da kwantar da ita a hankali ya ce "Allah ya shiryamun ke my cutie Gefenta ya kwanta yana kallon kyakyawar fuskarta mai cike da kwarjini da haiba wutar sonta na k'ara fisgarsa shafa fuskarta ya fara a hankali tare da Rungumeta yayi kissing d'inta a goshi a haka Shima bacci mai dad'i ya kwasheshi cike da gajiya Dan akwai gajiya sosai tattare dasu......✍🏿
*07026166536 domin magana da marubuciyar*
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[7/15, 18:39] Hajo hajo: 🅿️.........*101&102*
......Sune basu tashi ba sai washegari karfe Tara Arman yayi farkon tashi Kallon Aira yayi dake baccinta hankali kwance kallon agogo yayi yaga Tara hada wani Abu cikin Sauri ya Mike yayi saurin fad'awa toilet Dan baisan har yakai hakaba batare da yayi salla ba Bayan ya gabatar da salla kallon Aira yayi yaga baccinta take har yanzu kin tadata yayi Dan yasan tana fashin salla kuma tana buk'atar Hutu palour ya fito Inda ya samu sabon kuku din da ya d'auka A palour ya tarar dashi Yana mopping har ya gama shara jinjina mashi da hannu Arman yayi shikuma baturen ya gaisheshi cikin girmamawa Bayan Arman ya amsa zaunawa yayi tare da komawa ya d'auko paper da biro ya rubuta duk wani kayan abincin da zasu buk'ata Mik'a mashi yayi ya ce "yaje ya sayo " Arman yana zaune harya dawo sosai ya shigo da jibga jibga kayan abinci Inda ya shiga sintiri dasu store din Gida har ya gama Kallonshi Arman yayi ya ce "Idan kazo da safe zaka gyara iya palourn kawai da kitchen iyanan zaka dinga gyarawa 6am ya kasance kazo ka gama sannan daka gama ta kitchen zaka dinga fita idan kana buk'atar wani Abu ka kirani a waya kawai basai ka shigo cikiba " Jinjina kai Yayi Alamun ya fahimta "Check din kudi sosai ARMAN ya rubutamai sannan ya yanke albashin da zai dinga biyanshi mai tsokar gaske daga lokacin nan kukun ya shiga kitchen ya fara aikinshi.
Arman ko dayan bedroom d'in yakoma Bayan yayi wanka ya shirya d'akin da Aira take ya nufa Inda ya sameta ta fito daga wanka daure da towel jikinta hand drayer a hannunta tana busar da gashin kanta da ta wanke ta baya ya rungomata " Dan Kara Aira tayi Dan ta tsorata"Dariya Arman yayi ya ce "Sarkin tsoro nine fa" Cikin shagwaba ta ce "Shine ka tsoratani hero" Murmushi ya sakar mata ya ce "Sorry Prince's" amsar hand drayer din yayi tare da Fara yi mata "Dariya Aira tayi ta ce " Kai Zumah me ina ka iya gyaran gashi"yau xanfara akan matas kede kawai kisa ido kiyi kallo yarinya"murmushi Kawai Aira tayi suna kallon juna ta madubi shiya gyara mata kan nata yayi mata stretching ya shafa mata mayiyyuka masu k'amshi Bayan tayi mata Parking "Sosai yayi kyau sai kyalli gashinan yake ya dirar mata har gadon bayawow yaya Amma fa yayi kyau kamar naje saloon" Murmushi yayi ya ce "da kina wasa ne da mijin naki" jinjina mai hannu tayi ta ce "Thnks mijin da yafi na kowa" Peck a kumatu yayi mata ya ce "Nagode Matar da tafi ta kowa a duniya" Saida sukayi shiriritarsu nan ma tukwana ya rabu da ita ya fita palour ita kuma ta shirya Cikin doguwar rigar atamfarta green Street gown sosai ta matseta d'an a jiki D'aurin zarah buhari tayi Ita kanta data duba kanta madubi tasan tayi masifar kyau Turarruka masu k'amshi ta faffesa palour ta fito Inda ta samu Arman yana kallon ball Kallonta yayi tare da sakar mata smiles ya ce "Kinyi kyau My beautiful wife" Far da ido Aira tayi ta ce "Thnks my beautiful husband" ta fad'a tana k'arasa shigowa palour tare da zaunawa gefenshi ta zagaye hannunta a “yau shigar hausawa aka yimun kenan "Uhm hubby " Kinajin yunwa ko Prince's ya fad'a yana shafa kanta"Cikin shagwaba ta ce "Eh mana Baby " Sorry babyn Yaya muje tund'azu kuku ya gama breakfast banson na tashekime shysa"Kallonshi tayi da mamaki ta ce "Wai honey da gaske kuku ka d'auka Haba Darling meye amfanina a gidan kowace mace fa tayi Aure ita take girkama mijinta abinci meyasa bakasan na samu ladan wannan sannan nasan Mummy ma taji Bazataji dadi ba" kama hannunta yayi tare da mik'ewa suka nufi dinning ya ce "Bazakiganeba Cutie bazan juri ganinki kina wahala ba shysa Sannan lada kullum cikin samunta kike yanda kike kula dani kike jiyar dani dadi kadai ladan bata wasa bace ba saita girki bane kawai zaki samu lada akwai hanyoyin samun lada da yawa a Aure kuma girkin ma zaki samu ladar niyya tunda Kinga ninace na yafe Kinga kuwa ai kina da lada my prince's Mummy da kanta ta fara cewa Na d'aukar maki kuku"Uhm Yaya Amma dai Gaskiya ko ran Friday ne zan dingayi please karkace a a " To shikenan tunda kin ce Friday din saiki dingayi shikenan ko hankali ya kwanta"Murmushi tayi tana zama kujerar dining d'in Bud'e kulolin tayi k'amshi sai tashi yake serving d'insu tayi Inda ta zauna ta fara ci lumshe ido tayi Dan babu laifin abinci akwai dadi dukda ba irin namu bane"Kallonta Arman yayi ya ce "da dadi ko my prince's" yatsune fuska tayi ta ce "Uhm ba laifi amma da ni nayi da saitafi dadi" Dariya yayi ya ce "Ai daman inama za a hada abincin matas da wannan ai kinzarce wannan nesa ba kusa ba" washegari da Yamma suna zaune a palour suna kallo yayinda tana gefenshi tana shan tuffa Hakanan yau kawai ta tashi da tunanin Mamy kusan shekara kenan ba ta sanya mahaifiyarta a ido Dan tundaga aurenta da Alh Madugu rabonta da gida "wasu hawaye ne suka gangaro mata batare da ta sani ba "da mamaki Arman ya Kalleta ya Ce " Yadai me ya faru cutie "Cikin murya mai shirin fashewa da kuka ta ce " yaya Mamy"Ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka "Rungumeta yayi yana Lallashinta Ya ce " kiyi hakuri cutie komai zai daidaita insha Allahu kibar kukan nan kinsan bansan zubar hawayenki"yaya Kusan shekara fa rabona da Mamy nasan tana Chan kila cikin damuwa yaya Dan Allah kiramun ita a waya please "To yi shiru saina kira maki ita kinji" gyada mashi kai tayi tare da Goge hawayen mik'a mata wayar yayi Karba tayi tare da sanya number Mummy Cikin zumud'i ta danna mata kira cikin sa a kuwa taga ta shiga tana ringing Mummy ko tunda abunnan ya faru bata da zaman lafiya sosai hankalinta ya tashi akan Abunda akace Aira tayi kullum da bakincikin abun take kwana take tashi dukta rame yanzu haka bata da lafiya tana kwance Dan tunda abunnan ya faru yau lafiya gobe ciwo Danma Abba yana kula da ita bai nuna mata komai ba akan abunda y'arta tayi yauma tana kwance tana bacci taji ringing d'in wayar koda ta mik'e taga code din wata k'asa kuma ba na Niger ba bare tace y'an uwanta ne tayi mamaki sosai Tana shirin dagawa kiran ya katse Aira ko hawaye tayi ganin kiran ya katse Kallonshi tayi ta ce "Yaya bata dagaba"ki sake trying insha Allah zata d'aga " Sake kiran tayi cikin sa a kuwa ring d'aya aka daga wata nauyayyar Ajiyar zuciya ta sauke Wanda har saida Mamy taji daga waya Hello wake magana"Mamy ta fad'a "Sosai Aira taji nutsuwa jin muryar mahaifiyartata shashekar kuka ta fara ta kasa magana " Wai baza ayi magana ba"Mamy ta fad'a"Aira kasa magana tayi sai shashekar kuka "Mummy dukda taso ta gane ita ce ta ce " To idan baza ayi magana ba zan kashe ina da aikinyi"Cikin Sauri Aira ta ce "Mamy Aira ce" Aira Mamy ta maimaita cikin ranta dukda kewar y'ar tata da tayi hakan bai hanata fushi ba ta ce "Wace Airar" Airarki Mamy "ta fad'a tana cigaba da hawaye" tsaki Mamy taja ta ce "me kika kira na maki ai tunda kika zab'i namiji akanmu muma muka hakura dake Dan haka karki sake kirana " tana gama fad'ar haka ta katse kiran"Sosai Aira ta fashe da kuka tare da Fad'awa kan Arman ta ce "Na shiga ukku yaya shikenan Mamy Ma fushi take dani nasan k'ilama ita da Abba sun tsinemun yaya Ya zanyi da rayuwata"Sosai ta bashi tausayi Rungumeta yayi ya ce " Kiyi Hakuri Allah yana tare damu Insha Allahu babu wanda zai tsine maki cutie anringa an b'ata mu a wurinsune Wanda Goge hakan sai Allah insha Allahu nan gaba Gaskiya zata bayyana zasu yafe mana "cikin kuka ta ce " yaya sai yaushe Nifa Duka iyayena suke fushi dani ina tsoron hakkinsu yaya karya bibiyeni nasan ban kyautawa Mamy ba "daddabata ya fara ya ce " Insha Allah ba hakkin da zai bibiyemu cutie Allah da zuciya yake amfani kuma shi ya jarabcemu da son junanmu Wanda Bazamu iya rabuwa da junanmu ba Amma kina gani Iyayenmu saida sukayi yanda sukayi suka rabamu akan dalilinsu marar ma ana da tushe Sannan Abba da Daddy suma Allah zai fara kamawa da laifin yanke zumuncin da sukayi Bayan nasu suka hada da namu kin manta hadisin manzon Allah S a w da yake cewa "dukkan mai yanke zumunta bazai shiga aljanna ba " bana nufin iyayenmu bazasu shiga aljanna ba a a a ina nufin girman laifinsu yafi namu na farko dai Kinga ba zina muka aikata ba hasalima sharri akai mana"Sannan na biyu Aure da Mukayi ba haramun bane inbanda Lada da zamu samu saboda raya sunnar ma aiki da mukayi ko a mutuwar auren wancen ya isa ki gane Allah yana tare damu cutie sannan ki kwantar da hankalinki Mamy uwace bazata tab'a maki mugun bakiba Kinga kamar yanda Mummy tayi tsayin daka wajen ganin farincikinmu to hakan take ta bangaren Mamy itama uwace kuma har yanzu tana sonki kuma tanayimiki addu'ar alkhairi kisa wannan a ranki kinji my cutie ki kwantar da hankalinki "Shiru Aira tayi tana sauke ajiyar zuciya Tadanjin sauki a ranta nan yaci gaba da yi mata nasiha har ya samu ya mantar da ita damuwar da ta shiga.
B'angaren Mamy kuwa sosai tayi kuka Bayan katse kiran Sosai Abun yake damunta ga kuma bakincikinta na bin namiji da Y'arta tayi kenanma barin k'asar sukayi tunda gashi da code din wata k'asa Suka kirata sosai Mamy ke kuka ta ce " ina ganin rayuwa ni Rahama Y'ata mace kenan a duniya ta kasa zama lfy ta kasa barinmu mu zauna lafiya Ta gurbata rayuwarta akan d'an namiji sosai take kuka Amer ne ya shigo cikin maganarsu ta y'an koyo ya ce "Mamy miya chameki" Shiru tayi mashi tana cigaba da hawaye "Shima kukan ya fara tare da rumgumeta washegari Mamy ta tashi da Rashin lafiyar koda sukaje Asibiti shaida musu akayi jinintane ya hau tana yawan tunani da sa damuwa a ranta saida aka kwantar da su na kwana biyu kafin a sallamesu.
Kwana Ukku Aira tayi wanka Wanda ta fara salla daman Ka idar AL adartane kwana Ukku ko hud'u Daga ranar suka d'ora sabuwar rayuwarsu daga Inda suka tsaya batare da haufi ba soyayyar da Aira da Arman suke zubawa taban mamakice wacce zan iya cewa tsawon Rayuwata bantaba ga masoya masu k'aunar junansu irin haka ba ranar Friday tanayi Aira ita da kanta ta shiga kitchen ta girkama mijinta special food naban mamaki banda drinks da ta harhada da kanta Bayan taci gayunta cikin K'ananan kaya jiens da wando Sosai tayi wutar kyau Fitowa tayi a lokacin da yake shigowa Bayan yadawo daga masallacin Juma a wajenshi tayi tare da Rungumeta ta ce " highly wellcome my husband"Shafa kanta yayi ya ce "Thnks my Prince's" Kama hannunshi tayi ta ce "Muje ciki nasan ka kwaso gajiya a tare suka shiga ciki Ta taimaka mashi ya sake wanka Inda ya shirya cikin K'ananan kayan da sukayi mashi masifar kyau kai tsaye dining suka nufa tayi serving d'inshi tana murmushin ta Shima murmushin yak'e sakar mata na so da k'auna Spoon ta d'auka tare da zubo abincin takai saitin bakinshi tace ha a my honey" murmushi yayi ya d'aga bakin zuba masa tayi Arman koda ya tauna lumshe idanu yayi jin girkin da bai taba nin dad'in irinshiba da yana cewa duk duniya Mummy tafi kowa iya girki ashe Aira ma gwanace wajen girki"Ganin yanda yake lumshe ido yasanya Aira Dariya ta ce "Baby yadai mark nawa na samu" Jinjina mata hannu yayi ya ce "Ai mark d'inki ya wuce 100% saida trillion % Dariya sosai Aira tayi ta ce " a sa masa waigi"Dariya yayi ya ce "Serious fa Bantabajin girki mai dad'in wannan ba matas yayi dadi sosai yanda baki tunani kice yau dad'i biyu za Ajiyar dani gana girki gana bed ya fad'a yana kashe mata ido" Kashe mashi ido itama tayi ta ce "Yau kai din d'an gata ne Ai hero Har Arman ya gama cin abincin yana santi Da sanyawa Aira Albarka koda yasha drink dinma Shima sosai taji dad'inshi Aira ko sai dadi takeji yanda mijinta ke yabawa.
A satin ne ya fara koya mata mota kullum fitarsu suke Inda ba kowa Sosai take ganewa Wanda cikin sati ukku Aira ta iya tuk'a mota inbanda in sunfitama a shiririta Rabi ake karewa shiyasanyama bata iya da wuri ba ranar ta karshe ita ta tukosu har gida Sai murna take ta iya driving Dan yana daga cikin abunda tafiso ta ganta tana driving Aira sosai takeson Arman yasaya mata waya amma tanajin nauyi Dan bazata iya rok'arshi Abu ba hakan yasa ta hakura koda yaushe cikin waya da video call suke da Mummy.
Mummy duk yanda taso ta Ganar da mijin nata gsky abun ya gagara da ta ma d'auko masa maganar Arman yake dakatar da ita akwai lokacin da Kamar ya buge ta Sosai ya shiga mata bala I akan ta k'ara mashi zancen Arman ranta zaiyi mugun b'aci hakan yasa ta daina mashi Sosai Abun ke damunta d'an tama kasa samun y'ar damar da zatayi mashi bayanin abunda ke faruwa koda ta kira mahaifinta ta fad'a masa halin da ake ciki ce mata yayi karta sake mashi maganarsu ta rabu dasu akwai lokacin da yake so Akai Wanda shida kanshi zaizo ba yanzu ba sannan karta Fad'awa kowa maganar Aurensu Aira har yanzu taci gaba da rufewa.
Bayan wata Ukku idan ka kalli Aira ta k'ara murjewa da kyau Ga wani fresh da take karawa ko ina na jikinta ya cicciko tayi gwanin sha awa Shi kanshi Arman ya lura da Yanda tayi kallonta yayi ya ce "Cutie Kinga kuwa Yanda kika koma baki tab'a kiba Irin haka ba" Far da ido tayi ta ce "Allah ko Honey" Shafa Hips d'inta yayi cikin wani irin salo ya ce "Serious har nanma jifa yanda suka ciko Gaskiya na iya kiwo" Dariya tayi ta ce "Allah ko hero" Eh mana Baby "Uhm Gaskiya ne ka iya kiwo nikuma Fa ban iya kiwo fa kenan kaima ai kayi kiba gashi na sanyamaka Haske kaima ka k'ara Haske"Nina isa nace Cutie bata iya kiwo ba Ai kecema kikafi kowa iya kiwo My Prince's Hh Haske nima ai na goga maki namu na Fulani Gashinan yanda kike k'ara haskawa kamar wata Daren goma sha hud'u" turo baki tayi ta ce "Uhm Amma dai nafi goga maka nau da yawa wayau ma kakemun ka had'a Haske biyu na kusa amshe abuna" Dariya yayi tare da sungumarta ya ce "ayi hakuri kar a amshe a barni na cigaba da dangwalar arziki.
Sosai Arman yake lura da sauyi Daga gareta Yanzu Abu Kad'an zatayi tace ta gaji ga kwadayi da ta tarka kullum suna hanyar yawo sayayya ga bacci kamar kasa minti kadan sai bacci ya kwasheta shidai ARMAN baikawo komai a kanshi haka dai har wata guda yauma ta fito daga Bedrom d'insu Zuwa palour iskeshi tayi kan sopa yana kallo gefenshi ta zauna tare da d'ora kanta kafarashi ta ce " wash na gaji wlh kamar nayi wani aiki da yawa"Da mamaki ya Kalleta ya ce "Daga daki zuwa nan ne kika gaji ko wani aikin kikayi" girgiza mashi kai ta yi ta ce "ba abunda nayi y'ar tafiyar da nayi ce Na gaji wlh" galala yayi yana kallonta cike da damuwa ya ce "Cutie kodai Asibiti muke tafiya Nifa abunnan naki ya fara bani tsoro Kinga Inma wata chutar ce Saisu gani'turo baki tayi ta ce " um um naki Nida lafiyata qalau ba abunda ke damuna"Ba yanda baiyi da ita ba akan su tafi Asibiti takiya A haka baccima ya kwasheta a jikinshi"Kallonta ya tsayayi yana k'are mata kallo Sosai cike da damuwa Dan yana tsoron ace wani abun ne ya samu cutie d'inshi Dan baccin nan nata da kasala bana lafiya bane.
Washegari Suna zaune kan Bed suna Video call da Mummy a laptop d'in Mummy Aira sai shagwaba take zuba mata akan taki zuwa ganinsu"Murmushi Mummy tayi ta ce "yi hakuri y'ar Mummy insha Allahu zanzo nan kusa" ihun murna Aira tayi ta ce "yeyeye Mummynah Allah ya kawomun ke lafiya wlh munyi missing d'inki sosai ko Yaya" ta fad'a tana kallon Arman dake gefenta "gyada mata kai yayi ya ce " eh Mummy munyi missing naki sosai "to Karku damu ina nan zuwa kusa " Bacci ne ya kwashe Aira batare da ta sani ba ta kwantar da kanta jikin Arman "Kallon Arman ta Cikin laptop Mummy tayi ta ce " son ya naga daughter tayi fresh ta k'ara k'iba da fari Jifa ana waya ta bige da bacci Anya baku b'oyemun wani Abu kuwa?cike da damuwa Arman ya ce "Wlh Mummy tayi wata hud'u ina Ganin haka tattare da ita ga bacci kamar kasa yanzu fa Rabin rayuwar a bacci takeyinta ga kasala komai tace ta gaji ni tsoroma nake Kar wata chutar ta shigarmun ita" cike da zak'uwa Mummy ta ce "wata hud'u fa kace Arman Tana zazzabi da ciwon kai ko amai?a a a Mummy batayin ko daya Saidai ciwon kan Shima ba Koda yaushe ba"yaushe rabonta da perioud" Tunani yayi sai yanxu ma ya kawo tunanin a ranshi kwata kwata cikin Sauri ya ce "Mummy ai takai wata Ukku ko fi batayi perioud ba" Salati Mummy tayi ta salamce ta ce "kudai anyi mashiririta Nifa ince Yarinyar nan Ciki ne da ita to ka maza ku shirya ku tafi Asibiti yanzu yanzu" ciki mummy"Arman ya fad'a da mamaki"Tabbas kuwa cikine da ita Ah Alhamdulilla ni Fatima burina ya cika Ka marmaza ku tafi Asibiti kuna dawowa ku kirani ku sanarmun wata nawane "Mummy tafada cike da farinciki tare da katse kiran hamdala kawai take tana godewa Allah Arman ko Sakato yayi yana tunani Tabbas shi gama zama soko wlh Sai yanzu shataf ya kawo a kanshi kodan ba sanin sign din masu ciki yayi ba cike da farinciki ya mike ya ce ''Alhamdulilla Allah na gode Maka kallonta yayi tare da shafa Fuskarta ya ce " Thnks you cutie Thnks you so much kingama yimun Komai a rayuwa sannan ya shafa Cikin tare da kissing d'in cikinta da ya d'an fara tasowa Sam shi baima lura da Hakan ba sai ya zaci ko k'iba ce ta sanyata fara tumbi ya ce "I love you so much My unborn Allah fitomun da ke\kai lafiya Farkawa Aira tayi taga Arman yana shafa cikinta Da mamaki take Kallonshi Shima kallonta yayi sai sakar mata murmushi yake " Juyamai idanu tayi ta ce "Yadai " murmushi ya sakar mata tare da mik'ar da ita ya ce 'Yau rana ce ta musamman a garemu cutie ina d'auke da Babban Albishir Wanda Ke ya kamata ki farayimun shi Amma ni zanyi maki "albishir kuma honey na me kenan" Sungumarta yayi tare da nufar toilet da ita ya ce "Wanda kika jima kina burin samu shi yayi mata wanka ita dai Kallonshi kawai take yanda yake wani sabon tattalinta da tarairayarta har mai shi ya shafa mata hatta kayan da zata sanya shiya fiddoata tare da sanya mata Bayan ya sanya mata hijab ya kama hannunta ya ce Muje my cutie" Muje ina Yaya"bai bata amsaba saboda ya fad'a mata Asibiti zasu yanzu zata kawo mashi kalula suna fita mita suka shiga ya yi motar key sukabar gidan kai tsaye wani had'adden clinic dake ba nesa dasu Suka nufa Bayan yayi parking a Farfajiyar asibitin Kallonshi tayi tare da marairaicewa ta ce "Darling me zamuyi a Asibiti kuma ?Murmushi ya sakar mata tare da kama hannunta ya ce " zaki gani my cutie yana gama fad'ar haka ya fita tare da bude mata itama ta fito kai tsaye cikin clinic din suka nufa babu wani layi hakan yasa suna shiga suka samu ganawa da likitan Bayan sun gaisa da Arman Cikin harshen Turanci yayi mashi bayanin abunda ke damunta "Itadai Aira na jinsu tayi jugum " wata nurse ya kira Tare da had'ata Da Aira yayi mata bayanin irin awon da za a mata ba jimawa Aira tadawo ta zauna Bayan an gama d'aukar abunda za a d'auka ba ayi 20 minute ba Nurse din ta dawo tare da mik'awa Dr result d'in karantawa Dr yayi da murmushi a fuskarshi ya kalli Arman tare da mik'a mashi Hannu sukayi musabaha ya ce "Congratulation your wife she's pregnant for 4months one week...✍🏿
*Ni da Yaya Arman na kudine akan 200 kachal katin mtn ta wannan number 07026166536*
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[7/16, 21:47] Hajo hajo: 🅿️........*103&104*
.....4months One week "cike da farinciki Arman ya Mike Aira bata gama mamakinta ba Taji an d'auketa anyi sama da ita juyata sosai Arman yayi tare da Rungumeta ya ce " Alhamdulilla My cutie kingamayimun komai a rayuwa Allah ya saukeki lafiya ya k'arasa fad'a yana kissing din wuyanta "Da mamaki Aira ta ce "Yaya kana nufin wai ciki ne dani" Eh
Book Chapters
Chapter 30
Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41