google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

addini,NASIR shine sunan shi wasu kuma suce malam NASIR shaharar shi da tayi yawa yasa aka koma kiran shi da malam mai ruwan ikon Allah domin yana bada magani sosai kuma ana dacewa.




Malam Nasir nada mata guda tal mai suna RUMAISA sai dai dayawan mutane suna kiranta da RUMAI ,tun da suka yi aure sun kwashe shekara goma ko ɓatan wata RUMAI bata taɓa yi ba.
Son da malam NASIR ke yi mata ne yasa bai ɗauki wani abun babba ba sai dai yace lokaci ne bai yi ba,duk surutain mutane basu damun shi dan wasu har magana suke yaɗa mashi "in kura na maganin zawo tayi ma kanta"shine habaicin da ake mashi haka ma matar shi.




"Ni ban ga abun kuka a nan ba komi fa nufin Allah ne,ta yiyu kuma Allah ya jarabce ni ne dan ya gwada imani na sanin kanki ne mutane dayawa wurina suke amsar maganin haifuwa kuma sun dace"cewar malam NASIR yana rarashin matar shi da tun da garin Allah ya waye take kuka,"to malam sai muje wani gun mu nema mana ga MABARUKA nan sai baiwa mata magani take suna haifuwa ni ka..."saurin katseta yayi "Allah sawaƙe da in barki ki kisha maganin ƴan bori "
"Ai kam maganinta na yi ka san gado tayi"
"In bori gaskiya tayi ma kanta maganin da zata samu miji mana"cewar malam yana mai ficewa makarantar rana wadda yake koyar da almajirai.




Fitar shi ke da wuya ta zumbula hijab bata zarce ko ina ba sai gidan MABARUKA,wani gida ne na jar ƙasa tun daga soron gidan zaka gane sun yi bankwana da hanyar Allah ƙawonni ne irin na manya bisashe da ƙwanƙwamaye☠️💀 sai wani hoton ƙaton aljani jawur da shi ya fiddo haƙora waje da zaratan akaifu.


Zuciya na bugawa ta ƙarasa ciki tare da yin sallama "ba ayin wannan abar a nan gidan kibar kawo mamu Allah cikin gidan mu,ki cire takalmi ki shigo"taji wata murya daga can cikin wani kutuɓu na faɗa,takalmi ta cire ta shiga tana mai fidda niƙaf,dariya MABARUKA ta kece da ita kamin ta tsagaita "matar malam da kanta hhhh dama na rantse doli sai kun zo neman taimako na tunda yace zai ja da mu sai mun ga bayan shi"
"A'uzubillahi minna shaitanun rajim"RUMAI ta furta "keee!ba anan gidan ba ke matar malam da ke da shi duk sai mun yi maganin ku"cewar MABARUKA tana zaro ido waje "ta Allah ba taku ba eh gaskiyar malam da yace in bori gaskiya kiyi ma kanki maganin samun miji"RUMAI ta faɗa tana mai cigaba da ambaton sunan Allah .






Da ta dawo gida kuka ta fashe da shi tana danasanin zuwa,maganar MABARUKA kuma ya tabbatar mata da akwai wani *ƁOYAYYEN SIRRI* da malam ke ɓoye mata shiyasa bai son ko sunan unguwar da MABARUKA take a ambata.




Tana cikin wanga zulumin taji kamar an gitta ta gabanta an wuce,sai kuma taji kamar ana jan hijab ɗinta wani tsoro ne ya ɗarsar mata lokacin da taji kamar ana mata bincike cikin ɗaki.
Ta zabura ta diba sai taga tsintsiya ta miƙe da kanta tana shara "kwayat-kwayat" tukunyar da ke bisa murhu na buɗe kanta ta rufe kuma,da gudu ta nufi hanyar waje ƙyauren gida ya bada gammm ya rufe.......


Ƙarshen book one sai mun haɗe a part two


*Duk mai son cigaba zai iya tuntuɓar wannan number* +22795045822
Downloaded From https://tknovels.com.ng


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment