You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kamin yayi ƙarfin halin cewa "lokaci ya kusa Ammy ke dai kiyi ta min addu'a" "har sai yaushe lokacin zai zo?ce min kayi cikin satin auren ku da MARYAM zaka min albishir har da cewa a likitance ne ka gano hanyar da zata samu ciki amman har yanzu shiru yau 5days da auren"Ammy ta faɗa tana goge ƴar ƙwallar da ta zubo mata.....
*Ku ƙara yawan COMMENT dan har yanzu bai kai yadda zai tabbatar min kuna son labarin ba*😰😰😰
Jikar Rabo ce🌚
[05/07 à 11:03] Matar Sadauki💞: *ƁOYAYYEN SIRRI*💞
By Chamsiya Laouali Rabo
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️
Page 15-20
"Please Ammy ..."ya faɗa cikin rawar murya yana girgiza mata kai alamun kar tayi kuka, murmushi ta ƙaƙalo taja mashi hancin kafin tace "tashi maza ka tafi gida matan ka na can na jiran ka "ɗan ɓata fuska yayi "Ammy yanzu ɗan gudadan kike kora ni da nike son nayi passé journée a nan sai dare na tafi"waro ido Ammy tayi tace "kaji sakarci sai kace wani ƙaramin yaro ?oh ni BINTU yaro sai ƙara sangarcewa yake ko lokacin da kake da mata guda ai baka wuni nan gidan balle yanzu"miƙewa yayi yana shafar ciki "Ni yunwa ma nike ji mi kika dafa?"sheƙar da shi Ammy tayi ta shiga latsa waya ,ganin ƴan ira'izan nata sun hau yasa shi fita yana dariya.
Ƙarar motar shi ya bayyanar da zuwan shi,da gudu LAURAT ta fito ta faɗa jikin shi tana dariya, kiss yayi mata a goshi sannan yaja hannunta suka shiga ciki ba tare da sun lura da MARYAM wacce ke jikin window tana leƙo,saurin rufe window tayi zuciyarta na mata ƙuna dama jin ƙarar motar shi ne yasa ta leƙo.
Suna shiga falo ya saki hannu RAULAT ya nufi ɗakin MARYAM ,a tsaye baki window ya tarar da ita tana shafe hawaye.
Zuciyar shi ta raya mashi ƙila ta ga lokacin da yayi kissing LAURAT, kawai sai jikin shi yayi sanyi dan yasan irin zafin kishin da MARYAM ke da shi tun a lokacin da suna soyayya.Ƙarasawa yayi ya kama hannunta ba tare da yace mata komi ba. "sannu da zuwa"MARYAM ta faɗa tana mai ƙoƙarin danne kishin da ya taso ,"yauwa baby kina lafiya dai ko?"kai ta ɗaga mashi kafin kuma ta shiga toilet ta tara ruwa cikin bawon wanka,ƙofar da taji an buɗe yasa ta waigo ABDALLAH ne tsaye bakin porte yana kallonta.Saurin rumtse ido tayi ta juya mashi baya ganin babu komi jikin shi ,takowa ya fara yi a hankali har ya zo inda take ruwa ya ɗebo ya watsa mata a fuska da gudu ta fito waje shi kuma ya rinƙa yi mata dariya.
Ko kafin ya fito har ta fitar mashi da wasu ƙananun kaya,sai da ya shirya sannan suka nufi falo wajan LAURAT wacce ta cika tayi fam dan takaici.
Duk irin yadda take ji bata nuna ba sai ma abinci da tayi siving su cikin tray guda,bayan sun gama ne ya jasu zuwa mota suka kwaso kaya.
Ko wace ya san favorite coulor nata LAURAT rose MARYAM kuma rouge(ja)sai dai ko waccen su da aka zo rabon kayan na ƴar uwarta take hange.
"In sayayyar bata yi maku ba ku kawo na bayar saraka🤨"ABDALLAH ya faɗa cikin ɓacin rai dan yasa suna son kawo mashi rainin hankali,jin haka yasa ko wace ta kwashi nata ta kai ɗaki kamin su dawo su cigaba da kallo suna ɗan taɓa hira.
Dare mahutar bayawa,gari yayi tsit baka jin motsin komi sai kukan tsuntsaye da haushin karnuka.
Cikin ɗarɗar ABDALLAH ya nufi ɗakinta, domin a al'ada amarya sati guda gareta kafin ayi rabon kwana,
"Ni fah na fara gajiya da Wannan abun "cewar MARYAM tana maida lumfashi,jawota yayi jikin shi "sai mi kike so?"ABDALLAH ya faɗa mata cikin kunne kamar mai raɗa turo baki tayi tace "nima ban sani ba "ta faɗa cikin jin haushi.
Wani abu yaji cikin zuciyar shi nayi mashi yawo shi ba daɗi ba kuma ba akasin shi ba "babyna gayamin mi kike son faɗa um?"
"Am abinda ke sa mutum ya haifi yara mana dan gaskiya ina son babies dayawa sannan kuma ko ba dan wannan ba ai yana cikin haƙoƙin aure"ta faɗa tana mai dariyar kanta,yadda take magana yasa shi lumshe ido yana jin wani abu na tsarga mashi nan kuma ya fara tunanin rayuwar su tun MARYAM na jiran amsa har barci ya ɗauketa.Wayar shi ce ta fara vibré alamun kira na shigowa,hannu ya zura ya ɗauko daga inda take ajiye "baby RAINA"shine sunan da ke yawo akan screen ɗagawa yayi ba tare da yace komi ba,jin yayi piking ta sauke ajiyar zuciya yayinda shi kuma ya lumshe ido.
Gaisawa suka fara yi kamin daga bisani su fara hira wacce rabinta duk RAINA ce ke yinta shi amsa mata yake da um..kawai.
RAINA na kashe kira ABDALLAH ya shiga saƙa da warwara "tashin hankali" faɗa a bayyane kamin ya kunna hutar ɗaki kallon MARYAM yayi yana mai jin tausayinta har ƙasan ran shi yau kusan sati guda amman ya kasa sauke haƙinta na aure,a duk lokacin da zai kasance ta rasa martabar shi yake ta ɗa namiji,wani tsoro mai game da tashin hankali suka ƙara dirar mashi da kyal ya iya shiga toilet yayi wanka.Tapis ya shimfiɗa yayi raka'a biyu Fatiha ~Ƙulhuwa lahu yana sallamcewa ya maida goshi ƙasa ya karanta *LA'ILLAHA ILLA ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTA MINA ZALUMI sau 43* sanan ya fara gode ma Allah a bisa ni'imomin da ya bashi na rayuwa kamin ya fara yi ma Allah kirari "ya ubangijina kai ka hallaci samai da ƙasai ba'a wajan wani ka kwaikwaya ba,ya Rabbi kai ne ke ba bawa abinda kaso a sanda kaso ga wanda kaso a lokacin da kaso,duk ni'imar da ka ba bayinka kai kayi niya ka basu ba iyawar su ko dubarar su bace ta basu haka uwanda basu da shi kai ka hana masu ba kuma dan baka son su ba sai dan haka kayi niya.Ya Rabb ina roƙonka ka yaye min dukannin wata damuwa da matsalar da ke damuna Ya Allah!Ya Rabb!Ya Samad..."kukan da yaci ƙarfin shi ne yasa shi ƙyalewa ya koma yin addu'ar a zuci baka jin komi sai sautin kukan shi wanda hakan ya tayar da MARYAM.Tsakiyar gado ta rabka uban tagumi tana hawaye tashin hankali biyu ga abinda ya gani cikin mafarki ga kuma mijinta na kuka.Hawayenta tayi ƙoƙarin tsayarwa kafin ta shiga toilet tayi wanka da alwala,bayan shi ta tsaya ta kabarta sallah ita ma cikin kukan take addu'a "ya Allah kar da kasa mafarkina ya tabbata kabarni ni da mijina mu rayu kamar ko wane ma'aurata duk masu biyar mu da sharri Allah ka mayar masu kayan su"haka tayi ta addu'a kafin ta shafa, rungumeta ABDALLAH yayi sai yaji jikinta yayi zafi alamar zazzaɓi ac ɗakin ya kashe kafin ya ɗauketa su koma bed,tsam ya rungumeta a ƙirji yana tofa mata addu'a ganin idonta kawai ya tabbatar mashi iskokai sun shafeta.Idonta ya fara canzawa babu baƙi sai fari wanda take juyawa kamar tana son bashi tsoro,suratul baƙara ya kuna yana kuma mai cigaba da yi mata addu'a har barci ya kwashe su.
Washe gari ABDALLAH ya tashi a gaugauce ya shiga toilet dan sun makara,a gida yayi sallah sanan ya tasheta tayi a dadafe.Jikinta yayi zafi sosai kamar huta cikin tausayinta ya fita ya haɗo mata tea sannan ya bata magani,bisa cinyar shi ya kwantar da ita bayan ya rufeta da blanket a nan tayi ta barcinta mai cike da mugayen mafarkai sai mitsirniya take amman taƙi farkawa,irin yadda jikinta ke rawa take ɓata fuska yasa shi fara mata addu'o'i.
Sai wuraren shaɗayan rana ta farka a lokacin jikinta yayi dama,wanka tayi ta shafa mai sai wani cin magani take tana game fuska shi da ABDALLAH kallonta kawai ya ke kamin ya shiga wanka ko da ya fito bata nan.
A falo ya tarar da su ita LAURAT suna karyawa sallama yayi masu kamin uwar gida ta gaishe da shi ya amsa yana kallon MARYAM wadda tayi kamar bata san da zuwan shi ba.
Zaunawa yayi yasa hannun shi dan cin abinci kawai sai MARYAM ta tashi,bai ce komi ba suka cigaba da ci shi da LAURAT.Bisa salon ta kwanta tana rawar sanyi har haƙoranta ke gamewa suna ƙara da sauri ABDALLAH ya fidda hannun shi ya nufeta yadda yaji jikinta ya ƙara yi fiye da na ɗazu yasa shi surarta sai mota dama da hijab ɗinta a jiki.Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare maƙoshin LAURAT tayi wani ƙyaci kamin ta shiga ɗaki tana murmushin mugunta.
Wani privé asibiti ya kaita,ɗibar jini suka yi kafin daga bisanin su ƙara mata ruwa.
Kusa da gadon yaja kujera ya zauna yana kallonta cike da tausayi guguwar sonta na taso mashi,hannunta ya kama yana ɗan murzawa kafin tunanin ya kiwo Ammy ya faɗo mai a rai.Bugu biyu ta ɗauka a yadda taji muryar shi kawai tasan babu lafiya"Ammy ina kwana kin tashi lafiya?"'lafiya lau mike damun ka?"
"MARYAM ce ba lafiya gamu a asibiti"yana gama faɗa ya gintse kiran sakamakon muryar shi da ta fara rawa, kasancewar Ammy tasan asibitin da suke zuwa a duk sadda wani bai lafiya yasa bata tambaye shi ba cikin sauri ta ɗauki mayafi hankali tashe dan yadda take son MARYAM ko ABDALLAH bata so hakanan.Cikin motar gida driber ya kaita a hanya gani take bai gudu saboda tashin hankalin da take ciki dan duk rashin lafiyar da ta sa aka kai MARYAM asibiti to ba ƙarama ba ce,zuciyata kuma taji ta ɗan kwanta tuna tayiyu ciki ne gareta bata san lokacin da tayi murmushi ba kuma a daidai nan suka shigo harabar asibitin.
A tsaye ta hango ABDALLAH da alamu isowarta yake jira "ya mai jikin?"ammy ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wurin shi "tana ciki da sauƙi"ya faɗa yana mai tura ƙofar daƙin.Fuskarta Ammy ta shafa wajan idonta da suka yi zuru-zuru kamar wadda ta daɗe kwance,kamin ta juyo ta tambayi ABDALLAH"mike damunta?"ɗan sosa ƙeya yayi yace "zazzaɓi ne amman likita ya ɗibi jininta bai kawo result ɗin ba har yanzu"murmushi yaga fuskar Ammy wanda yasa jikin shi yin sanyi dan ya gane ko na minene take.Dr ne ya shigo ya miƙa ma ABDALLAH result sai kuma yace "biyo ni office na faɗa maka abubuwan da ya kamata taci da uwanda zata bari ka san halin mata sai da kula"ya ida maganar cikin dariya bin bayan shi yayi kamar yadda ya buƙata bayan sun shiga office sun zauna yace "ulcère olser ke damunta sai kuma damuwa wanda hakan zai iya haifar mata da wani ciwon daban in ba ayi takatsantsan ba,sannan tana yawan cin yaji da abu masu yami wanda basu dace da lafiyar ta.Ya kamata ta kiyaye duk abinda zai tado mata olser sannan ya zamana tana shan ruwa sosai dan yana hana kumburewar ciki"godiya sosai ABDALLAH yayi kamin ya dawo room ɗin da MARYAM take.
Tunda ya shigo Ammy ta ƙureya da ido sai ya sunne kai yana murmushi dan ɓoye damuwar shi bai san kau a wajan Ammy ɗaukar shi tayi na farin ciki ne.
"Sannu baby kin tashi?"Ammy ta faɗa kai kawai ta iya ɗagawa kamin ta buɗe baki kaɗan "ina jin yunwa"har gamin baki suke wajan tambayarta abinda zata ci "taiba da ruwan tsamiya"
"No ki canza wani likita yace abar barin ki cin abu mai tsami"cewar ABDALLAH yana mai fidda mata ƙarin ruwan da aka sa mata.Turo baki tayi tana kallon Ammy tana wani ƙwal-ƙwal da ido kamar zata yi kuka "bari na kira LANTANA tayi maki"Ammy ta faɗa cewa ga ƴar aikin su "no Ammy ni taki nikeso"MARYAM ta faɗa tana ƙoƙarin tashi ABDALLAH ya taimaka mata "toh bari naje gida nayo maki" "am please Ammy kar asa yaji"ABDALLAH ya faɗa murmushi kawai Ammy tayi ta fita.
Juye fuska tayi tace "ni kabar kallona tunda ..."sai kuma ta ƙyale, murmushi yayi mai sauti yace "tunda ba ƴar gidan mu ba ce ko?"ya faɗa yana mai haurowa bisa gadon ya jawota ,magana yake mata cikin kunne mai kamar raɗa ture kan shi tayi wanda ke bisa kafaɗarta tace"ni yunwa nikeji ka sakeni"rigarta ya ɗaga kasancewar ta fidda hijab yana shafa cikin nata a hankali turo ƙofa aka yi tare da shigowa kai tsaye saurin janye hannun shi yayi daga cikinta yana cewa "Ammy har kin dawo"yadda yayi maganar cikin kunya yasa tace "a'a ina can gida har yanzu"dariya yayi kafin ya fice.Zuba mata tayi cikin plate sosai taci ta ƙoshi dan dama ita da taiba akwai amana.
Tafe suke cikin mota ABDALLAH ke driving Ammy da MARYAM gidan baya ta madubi yake hangen yadda ta wani kwanta bisa cinyar Ammy har suka kawo gidan a tunanin shi Ammy kawai zata fita sai yaga sun fito su biyo kamin ya tambayeta Ammy tace "nan zata zauna har ta ɗan warware kamin ta koma"ɓata fuska yayi yayinda MARYAM tayi mashi gwalo suka shige gida suka barshi.
*ASALIN LABARIN...* Alhaji Ahmed shine mahaifin ABDALLAH BINTU ita ce mahaifiyar shi wacce yake kira da Ammy.Tunda ta haifi ABDALLAH bata sake haifuwa ba wannan yasa Alhaji Ahmed sake yin aure har biyu amman ko wace da gidanta sai dai suma babu wacce ta haifu sai bayan dogon bincike aka gano alhaji baida wasu ƙwain haihuwa masu rai.
Duk da matan shi sun sani hakan bai sa suka tafi ba kasancewar shi mai dukiya.Ammy nada son yara sosai musamman macce kullum sai tayi ma Alhaji zancen ta ɗauko ɗiya gidan marayu amman sam yaƙi yarda.Ana haka kwatsam sai ƙaunarya ƴar uwar tawaicinta MUBINA ta rasu a nan ne ta ɗauki MARYAM kasancewar ita kaɗai ke macce kuma ƙarama dan a lokacin bata wuce 8years ba.
Tun daga wannan lokaci sunan MARYAM ya ɓace sai dai baby,tun ranar da ta dawo gidan Ammy da zama suke bata wata irin kulawa ita da ABDALLAH wannan ya shigar da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin MARYAM da ABDALLAH.
Tun ranar da ABDALLAH ya tafi karatu ba a taɓa ganin fara'ar MARYAM ba kamar ta yau,Ammy ce ta fito daga kitchen"oh baby ba dai har kin shirya ba ?"dariya tayi ta rufe fuska da tafin hannu "Ammy ƙarfe goma shaɗayan rana yace zai shigo fah""toh ai naga yanzu karfe tara ce shine har kin yi shirin tarbe?"ammy ta faɗa tana gyara mata ɗaurin gashinta da tayi ta maida shi baya a maimakon tsakiya, sannan ta jata ɗaki ta ƙara gyarata sosai.
11h cicif jirgin su ya sauka nan kowa ya fara fitowa,wani kyakyawan saurayi dan kimanin 28years ya fito fuskar shi tayi luwi-luwi sajen shi ya kwanta tsaf,waiwaye ya fara yi inda zai gan su sai ji yayi ance "yayaaaa!"da gudu ta rugo yayinda shi kuma ya buɗe hannuwan shi ta shige tare da laƙanƙameya suna dariya can ya direta ya kama hannunta suka ƙaraso inda Ammy take tana murmushi.Hannu ya bata suka yi musabaha kamin driver ta sa kayan shi boot su ɗau hanya.Dukan su a baya suka zauna baby MARYAM a tsakiya sai surutu take tana bashi labarin school yayinda shi kuma ya gyara mata tajewar gashin ya maido shi a tsakiya kamar yadda yake mata a kullum sadda yana gida "sai da nayi haka Ammy ta maida shi baya "baby ta faɗa tana kallon ABDALLAH wanda shi ma ita yake kallo "miyasa baki gaya mata haka na koya maki ba?"bata kai ga bashi amsa ba suka ƙaraso.
💞💞💞💞💞
Kallonta mum tayi tace "ina jin ki"kallon AMAR tayi wanda yake tsaye yana kallonta tun lokacin da ta ambaci sunan shi.
"Mum shafar aljanu ne"AMARA ta faɗa tana kuka "ta yaya kika san da aljanu ne ?"AMAR ya tambaye ta yana mai zama kan kujera "jiya nayi mafarkin ana yi maka RUƘIYA suna cewa ba zasu fita ba kuma kasan da yawan mafarkaina gaskiya ne"shiru falon ya ratsa suna ɗan nazari kamin wani kuma yayi magana Abba ya shigo fuskar nan tashi kamar hadarin gabas kai tsaye yace "mi ya gamaki da BALARABA?" gaida shi yaran shi ke yi yaƙi amsawa cikin gajiya da irin cin fuskar da yake mata mum tace "mi fa nayi mata TARZAN na tarar tana barbaɗa ma yaji kamar wata awara dan tsabar ƙetar tsiya"cikin mamakin yau ta maida mashi magana yace "ina ruwan ki ina ce dai nata ne kuma ko da kika zo kin tarda su in ma narkaken budo ta ɗiɗiga mashi ai nata ne"Abba ya faɗa yana mai ficewa.
"To mi TARZAN ɗin yayi mata ?"cewar AMARA tana jin zuciyarta na zafi "mi fah yayi mata ƙila kukan shi ya tasheta daga barci"mum ta faɗa "shine zata wani maki gami da Abba?wlh mum dan sun ga kina raga masu ne"AMARA ta faɗa tana mai fita waje ko ba a gayi masu ba sun san wajan TARZAN zata je ta dubaya.
Bawan Allah a kwance ta tardo shi yana ganinta ya shiga zagayenta,barkonan da yayi saura ajikin shi ta kakaɓe mashi kamin ta ɗebo ruwa ta sheƙa mashi .
*Asalin labarin....*
Alhaji SOULEYMAN shine cikakken sunan shi ɗan kasuwa ne sosai wanda a wajan yawon kasuwancin ne har ya auro BALARABA bayan doguwar soyayya da suka sha.Matsalar farko da suka fara fuskanta shine rashin haifuwar BALARABA wanda wajan zubde-zubden cikin da ta tayi aka cire mahaifar tun tana budurwa.
Yadda INNARO mahaifiyar SULEYMAN ta matsa mashi da batun ƙarin aure yasa yace mata ta nemo mashi matar aure ai ko bata ɓata lokaci ba ta auro mashi ƴar aminiyarta BALKISSA.
BALARABA bata san da aure ba sai da taga ana gyara ɓangaren sama wanda yake bisa bene nan fah hankali ya tashi babu yadda bata yi ba dan hana aure amman sai da aka yi.Tunda aka yi auren BALARABA ke nemanta da fitina amman sai ta shareta dan sai tafi wata guda bata sauko ƙasa ba,hakan yasa ko da ta samu ciki ma BALARABA bata san da shi ba.
Shekarar BALKISSA ɗaya da aure ta sukuto ƴarta macce yarinya taci sunan AMARA tun daga ranar farin ciki yayi ƙaura daga gidan alhaji SOULEYMAN ya bar ɗaukin BALKI da yarinyarta ana haka har ta samu cikin AMAR har ta haife shi......
Jikar Rabo ce🌚
[05/07 à 11:03] Matar Sadauki💞: *ƁOYAYYEN SIRRI*💞
By Chamsiya Laouali Rabo
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️
*MUTANE NA ƘORAFIN READ MORE YAYI YAWA SO ZAN MAIDA SHI PAGE BIBIYU MAIMAKON GOMA*
*CHAPTER 21-22*
Tun lokacin haifuwar AMAR suka rungumi rayuwar kulle, kullum suna sama duk ranar da kuma su AMARA suka yi gigin fitowa BALARABA sai ta saki ƙaton karenta mai suna MISHEL haka zai dinga biyar su yana habshi kamar zai tsizon su sai mum ta fito ta kore shi,BALARABA kuma tayi ta dariya.
Ganin kamar mum na tsoron kare yasa ta ƙaro guda amman macce baƙi ƙirin da ita MIKI ai kam tun daga lokacin mum bata sake barin yaranta fita ba in kuma sun fito sai in zasu unguwa.
Lokacin da AMARA ta kai 7years a lokacin AMAR keda 6years ganin tserewar su babu yawa aka saka su school guda mai game da islamiyya,mum ke kaisu da kanta ta kuma ɗauko su har suka shiga College a kuma wannan shekarar suka yi sabka alƙur'ani mai girma sai dai shi AMAR da kai yake da harda ƙur'ani.
Motoci sabbi ful Abba ya basu kanbacin cadeau wanda hakan ya jawo BALARABA ta gwadi hasaɗarta ƙiri-ƙiri tace bata yarda ba sai an sawo ma MOCTAR ɗan yayarta wanda take ruƙo,Abba bai son masifa haka ya sawo mashi irin ta AMARA ko gode balle nagode MOCTAR bai ce ba.
Mum ce da yaranta a ɗaki tana yi masu homwork kawai suka ji kururuwar mutane,da gudu duk suka fito waje "innalillahi wa'inna ileyhi raji'un"shine abinda suka furta suka yi tsaye kamar kowa suna kallon yadda motar AMAR ke ci da huta ita ɗaya duk da akwai motoci kusa da ita amman babu wadda ta kama.
Ruwa mutane ke zubawa amman yadda ka san ana zuba petur,ganin abun ya wuce ɗaukar hankali yasa duk suka yi tsaye suna kallo har sai da motar ta toye ƙurmus sai toka sannan hutar ta mutu da kanta.
Hankalin mutane ne kuma ya koma wajan MISHEL da MIKI uwanda ke ɗaure da kaca sai habshi suke suna fizge-fizge kamin kuma su ƙyale sai MIKI ta fara wani kuka,nan mutane suka lura haihuwa ce zata yi.
Ba a ɗauki wani lokaci ba kau ta haifo ɗan ɗanta mai kyau irin jan karen nan,gama haifuwar shi ke da wuya ya fara takowa zuwa inda ƴan tsirarun mutanen da suka rage ,daidai ƙafafuwan AMAR ya tsaya yana zagaya shi tare da sunsunar shi.
Duk da AMAR yana cikin kuka kuma ya kasance mai tsoron kare amman sai yaji wannan ya burge shi ,duƙawa yayi zai ɗaukar shi kawai sai yayi kamar zai cije mai hannu tare da yin kuka irin na jarirai karnuka, murya wani ya tsinkayo yana cewa "kar fa ka ɗauke shi da alamu faɗan tsiya ne da shi kana ganin dan masifa daga haifuwar shi har ya fara faɗa"ai kam kamar yasan abinda yake cewa ya ƙara sautin kuka wanan yasa iyayen shi yin kuka(MISHEL DA MIKI).
BALARABA wacce tayi kamar ta mutu a ɗaki nan kuma tana kallon duk abinda ake yi ita ce ta fito "kukan minene kuke alamu wani ya cuce ku"sai kuma ta tafi dan ɗaukar jaririn karen aikau ya cijeta da hannu ƙara ta saki ta ruga yabita yana habshi "TARZAN?TARZAN?TARZAN???"shine abinda AMAR ya faɗa yana kiran karen ,yana shirin bin shi mum ta jawo shi suka koma ɗaki.
Waya ta ɗauko ta kira Abba maimakon yaji haushi na ƙonewar motar sai cewa yayi "to mi kike so nayi?oh ni mai kuɗin banza wata kike so in saya mashi ga Alhaji mai zubda miyau,laifin shine wa ya san mugun abun da ke cikin motar"yana gama faɗa ya kashe kiran wasu hawayen baƙin ciki ne suka zubo ma mum, kamin ta kai ga share su taji AMAR ya ƙwala ƙara da gudu ta fito waje inda yake bisa terrasse.
Rigar jikin shi ya cire yana sosawa yayinda wani abu ke zuba kamar dussa , mum da AMARA na taya shi susar jikin yayinda kuma sai sautin kuka ke ƙara yawaita.
Kan suyi wani tunani kuma suka ga abinda ya ɗaga masu hankali AMAR yana fitsari jini .........
🥱🥱🥱 *Ba kuyi comment ba shiyasa nayi kaɗan*
[05/07 à 11:03] Matar Sadauki💞: *ƁOYAYYEN SIRRI*💞
By Chamsiya Laouali Rabo
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*☀️
___________________
BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM
*CHAPTER 23-24*
"Wayyo Allah na shiga uku mum kira abba aka shi asibiti"cewar AMARA tana kuka tana yarfe hannuwa,sungumar shi mum tayi zuwa ɗaki abun mamaki kawai sai fatar jikin shi ta fara komawa daidai ya bar jin ƙaiƙayi.Kayan jikin shi mum ta kawo mashi ya saka kamin cikin muryar da irin ta uwanda suka sha wahala yace "wlh mum ban son iskan waje ya buge ni ina kallo guguwa ta taso kamin iskan nan mai uban raɗaɗi ya fara buguna "AMAR ya faɗa cikin rawar murya ɗan tsagaita kukan da take tayi tace "AMAR miyasa baka karanta addu'a ba lokacin da guguwar ta taso?wanibi sharrin mayu ne"bai ce mata komi ba sai kuma ta aiki AMARA gidan HINDA mai bada maganin mayu.
Bata jima ba ta dawo aka kaɗa mashi cikin hura ya sha,kamin ya ɗan kishingiɗa ya fara tunanin abubuwan da suka faru yau masu cike da ban al'ajabi abu guda kawai yaji daɗin shi shine haifuwar TARZAN ai kam ya miƙe ya fito yana kaiwa bakin ƙofa jikin shi ya fara ƙaiƙayi da sauri ya dawo ciki dan har yanzu iskan bai lafa ba.Ɗakin shi ya shiga ya fara leƙen TARZAN ta glass ɗin window,ji yake kamar ya maido shi su rinƙa kwana tare sai dai abinda hankali ba zai ɗauka ba ne kwana da kare a shimfiɗa ɗaya.
Mum ce ta shigo ta tambayi jikin shi "da sauƙi sosai mum ina son TARZAN zo kiga yana shan nono"ya faɗa yana nuna ma mum,kallo guda tayi mashi ta saki murmushi tace "nima ina son shi sosai kamar a maido shi part ɗin mu da zama"cike da sha'awa suke kallon shi kamin AMAR yace "mum in kin lura kamar MISHEL bai son TARZAN dubi yadda yake taka shi da ƙafa yana turar shi"
"Nima haka na gani kamar MIKI tafi son shi"cewar mum.
Suna nan tsaye motar Abba ta shigo yana fitowa daga mota karnukan suka fara kuka a hasale yayi wurin su ya tabki MIKI da fuska kamar ya mareta "in ba iskanci ba mutum daga shigowar shi ki tarbe shi da kuka"Abba ya faɗa cikin banbami har zai tafiya TARZAN ya fara sunsunar