ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com ÿþFAHIMAH Soyayya da Rashin book 2

By Takori Kabara



"Da kyar ta iya mikewa ta soma dafa bango, tana mikewar jini na tsinke mata. Daga nan sai wani duhu ya mamayi ganinta, ganinta ya dauke gaba daya ji ka ke yif! Ta fada a kan Fahimah da ke jan minshari sabida dadin A.C."

"A firgice ta farka, ta janye Amrah daga kan kafafunta tana salati. Ta mike jiki na rawa ta kunna kwan lantarki. Nan ta ga jini na fita a jikin Amrah, kuma ko motsi ba ta yi. Fahimah saboda gigicewa a guje ta fita dakin Ammi tana kwala mata kira tun daga falo."

"Hatta Baba Talatu da ke baskwata sai da ta jiyo kiran Ammi da Fahimah ke yi. Babban tsoronta kada a ce ta kashe matar Uwais. Cikin barci Ammi ke jiyo ihun Fahimah yana doso dakinta, don haka a bakin kofa suka ci karo. Fahimah ta hada hannayenta waje guda kasan habarta kamar mai roko. Ta ce,"

" Ki taimaka Ammi, Amrah za ta mutu a dakina, wallahi ban mata komai ba. Kawai tashi nayi"

na ganta a kaina jini na zuba. Na shiga uku Ammi&  .

"Ammi ta ce,  Ke da Allah can shashasha, haihuwa ce ."

Ta ture ta ta wuce dakin nata. Daidai lokacin da Baba Talatu ma ta karaso. A tare suka shiga dakin suna ganin halin da Amrah ke ciki suka gane wannan haihuwa ta zo da tangarda.

Ammi ta ce da Talatu maza dauko min wayata da mukullin mota .

"Talatu da gudu ta juya ta dauko. Ammi da Talatu suka ciccibi Amrah suka yi waje. Ammi na cewa, Fahimah ta dauko jakar da Amrah ta zo da ita gaba daya ba za a rasa kayan jariri ba. Ta"

biyo su.

"Asibitin Standard suka wuce don komai dare ba a rasa likita, suna zuwa aka karbe ta da gaggawa. Dubawa ta farko likita ta ce,"

" Amrah ba za ta iya haihuwa da kanta ba an samu matsala mai girma, sannan babyn a breach yake, abu mai sauki shine CS kawai don su ceceta ko babyn, amma ita ko babyn dole a rasa guda."

Sabida tsananin rudewa Ammi kalmar shahada ta ke ja. Fahimah kuwa sai mazari ta ke daga

tsaye. Likita ya ce maza mijinta ko mahaifinta su zo su sanya hannu don lokaci ya kure babu wani taimako da za su iya yi mata bayan CS.

"Talatu ce mai karfin halin ce da Fahimah,"

 Ba ni wayar Ammi da ke hannunki bayan kin latso min uban dakina .

"Haka Fahima ta yi, ita mantawa shaf ta yi da wayar Ammi na hannunta don a gida ta baro tata. Ta lalubo lambar Uwais hannunta na karkarwa ta bai wa Talatu."

"Bugu daya Uwais ya dauka don yana can kamar mai nakudar shima, yana jiran abin da zai biyo baya, me ya kawo Amrah gidansu har dakin Fahimah cikin dare haka, kuma ina Fahimar ta ke da ta barta ta daukar mata waya tsakar dare? Ya tabbata sha ani ya lalace kam, da ya ji shawarar mahaifiyarshi tun farko da haka ba ta faru ba."

Yanzu da wane yare zai yi wa Amrah bayanin da za ta fahimce shi? Kuma me za ta dauki Fahimah? Ba za ta kara yarda da ita ba duk son da ta ke mata yau zai koma kiyayyah.

"Talatu na kira yana dagawa, a nitse ta gaya masa halin da ake ciki da bayanin da likita ya yi. Uwais ji ya yi kamar kwarankwatsa ta fado a kansa, ya ji kamar ya yi fiffike ya ganshi a Nijeriya. Babynsa! Gudan jininsa da ya kwallafa wa rai yau ga kuskurensa zai yi sanadinsa."

 Ba ni likitar .

Kawai ya ce cikin tashin hankali.

"Ya gaya mata ba ya kasar, sannan iyayenta ba sa gari, ya amince a yi mata CS din da duk wani taimako da ya dace. Ya kara da cewa,"

" Likita ki taimake ni kada in rasa kowanne a cikin su. Don dukkansu ina so, and they mean a lot me. Kuma na yi mata laifi ina so in nemi gafarar ta& idan ta mutu a wannan halin bazan taba yafewa kaina ba ""."

"Gaba daya muryarsa ta karye kamar ba Uwais ba. Bolded and courageous a komai. Likita bata tsaya doguwar magana dashi ba don ta lura ba'a hayyacin sa yake ba, suka shirya Amrah"

zuwa dakin tiyata.

******

"""It s a baby boy, amma bai zo da rai ba. The mother is still unconscious, za ta dawo"

"hayyacinta in the next two hours in allurar barci (anaesthesia) ta sake ta, sai ku shiga ku ganta""."

"Siririyar nurse din ta fadawa Ammi, a lokaci guda ta mika mata jaririn nannade cikin farin shawul. Ammi hannu da jiki na rawa ta amshe shi ta bude fuskarsa su duka ukun suka zuba masa ido. Uwais sak! Fari sol bai debo komai a jikin Amrah ba. Hatta farcen yaron irin na Uwais ne."

"Fahimah jin wata irin soyayyar jaririn ta yi, ko don kamanninsa da Uwais, ta kifa kai jikin Ammi tana kuka. Uwais na ta kira babu wadda ta iya amsa wayar sa. Ammi ta ce, Fahimah ta zauna ita da Talatu za su tafi da jaririn maigadi ya kira makwabta a yi masa sutura."

Ba su jima da tafiya ba aka gungura Amrah zuwa aminity. Da sauri Fahimah ta bi bayansu

suka kwantar da Amraha kan gado suka yi mata duk abin da ya dace sanan suka fita.

"Fahimah ta ja kujera daidai kan Amrah ta zauna. Tana karanta addu a tana tofa mata. Ga karin jini ga na ruwa, tana da son haihuwa matuka, musamman da Uwais ya ce zai so  ya yansu ne fiye da son da yake yi wa kansa Amma in haka haihuwar ta ke lala - lala ta hakura. Lallai"

"wannan shi ne kafa daya a duniya, kafa daya a lahira."

"Ta tuno uban jinin da ta ga Amrah na zubarwa, wani matsanancin tsoro ya kara kamata."

"Tunda dai Allah ya taimake ta ba ta yi cikin ba, to ba za ta kara yarda ta yi abin yin cikin ba. Ta barwa Amrah Uwais su yi ta haihuwa, tarewar ma ta fasa ba za ta yi ba. Zata cigaba da zama"

da Ammin ta.

Wajejen karfe goma na safe Amrah ta bude idonta a hankali. Kafin idanunta su washe a dakin su sauka a kan jinin da ake kara mata. A lokacin ne ta fahimci a kan gadon asibiti ta ke.

To me ya kawo ta asibiti ita da ta kwanta a gadon Fahimah za ta yi barci?

" Masha Allah, kin tashi Aunty Amrah? Bari in kira likita . Ta ji muryar Fahimah a gefenta."

"Muryar da ta tado mata da ainahin dalilin zuwanta asibiti. Da sauri ta kai hannu kan cikinta ta ji wayam! Da azama ta yunkura za ta mike, daidai lokacin da likitan ya shigo, Fahima na biye da"

"shi. Da sauri ya maida ita kwance, ya ce,  Be careful Madam, akwai aiki a jikinki . Sannan ya tambaye ta,"

 Are you alright?

"Kai kawai ta gyada masa. Ta runtse ido da Fahimah ta zagayo gefen fuskarta, tana tambayar likita ko za a iya ba ta tea ta sha? Doctor ya ce, ta bari sai an jima, Nurse za ta zo ta ba ta da magani."

"Tunda Amrah ta rufe ido ba ta kara budewa ba. Don ba ta son ganin Fahimah, ba kuma barci ta ke yi ba. Har zuwa lokacin da su Ammi suka dawo."

"Ammi bata san Amrah ta farka ba ta tsaya tana gaya wa Fahimah har an binne yaron. Allah ya ba su wani mai albarka, Ya bai wa iyayensa dangana. Shi ma Uwais din yana hanya gobe duk da bai gama abin da ya kai shi ba."

"Wasu dumammun hawaye suka biyo ta gefen idanun Amrah, Dan ta ya koma, duk wannan wahalar da ta ci akan rainon cikin, duk a dalilin bakin cikin Fahimah da Uwais? Ko Uwaisu ne autan maza ta hakura da shi yau, in ba haka ba bakin cikinsa shi zai yi ajalin ta."

Ta soma tunanin hanyar da za ta bi ta tsere kafin Uwais ya zo ya tadda ita. To amma da

wanne ido za ta koma wa iyayen ta???

"Wannan tunanin ya sa Amrah fashewa kuka wiwi a fili. Su ba su san idonta biyu ba, kuma sun dauka kukan na rashin dan ta ne da ta yi. Su basu san abubuwan sun ma zuciyar ta yawa ba. Da wanne zata ji?"

"Ammi ta karasa ta kama hannunta tana ba ta baki. Ta ce,  Ki yi hakuri Amrah, insha Allahu mai ceton mu ne. Ba ki ganshi ba kamar Uwais ya yi khaki. Allah ya yi wa iyayen da suka rasa  ya yansu suna kanana babban tanadi a ranar gobe. Kada ki yi bakin ciki, ki yi addu ar Allah ya bada rayayye mai albarka, kin ji ."

"Amrah ko kallon Ammi ba ta yi ba, ta ci gaba da gunza kukanta. A ranta ta ce, duk abin da Uwais da Fahimah ke yi da sanin Ammi tunda ai a gabanta suke, and she is educated enough da za su yi irin wannan danyen aikin ba da saninta ba."

"Me kuma za ta ce mata yanzu? Ai ta bar mata danta ke nan har abada ta aura wa farkarsa, ko su ci gaba da watsewar su."

"Gaba daya sun kasa gane kan Amrah, tunda ta farko ta ki ci ta ki sha, sai kuka, sannan ta ki karbar lallashin Ammi."

"Har dare suna tsaye a kanta suna lallami, amma ko uffan ba ta ce musu ba. Sai da Ammi ta"

"koma ta kira babban likita ta ce ya bincike ta ko da wani abu da ke damunta daban, kada jininta ya hau."

"Likita ya shigo, ya ce duk su ba shi wuri zai yi magana da Amrah. Ya ja kujera a gabanta ya zauna, ya ce,  Madam, may I know your problem? Na dauka ke musulma ce, kin san mutuwa tana kan kowa babba da yaro? Na dauka za ki yi tawakkali ki yi masa addu a, ki roki Allah ya sake ba ki wani cikin gaggawa? "

"Amrah na kuka ta ce,  Doctor ni farin ciki nake da Dan ya koma. Ko bakomai zai dandani irin bakin cikin da ya kunsa min. Tunda gashi nan a dalilin cin amanar da yayi min shima ya rasa abinda ya kallafawa rai."

"Damuwata yanzu kawai yadda zan je Abuja. Ka taimaka min ka sallame ni a yau, kuma ka ba"

ni aron wayarka in kira direbana ya zo ya dauke ni .

"Doctor ya ce,  Babbar magana. Ba zan iya sallamarki ba sai jibi, a ka ida in aka yi wa mutum aiki sai bayan kwana uku ake iya sallamarsa shi ma in an tabbatar babu wata matsala da za ta biyo baya. Advisably ki bar ni in yi wa Mamanki bayani cewa kina son tafiya Abujan da zarar an sallame ki, na tabbata za ta fahimta ta kai ki da kanta&  ."

"Da sauri Amrah ta ce,  Doctor ba abin da ya hada ni da su, kuma in ba za ka taimaka min ba"

"wallahi ko a kan iska sai na tafi""."

"Ta ci gaba da rusa kuka. Doctor ya rasa ya zai yi da ita, da ma kuma yana da lambar Uwais da suke magana wadda waccan likitar data karbi Amrah ta bashi da za su yi handing over, sai"

"ya koma ofis ya kira shi, ya yi masa bayanin halin da matarsa ke ciki."

"Uwais ya rasa inda zai tsoma ransa ya ji sanyi, ga booking dinsa ma an ce ba zai samu ba a goben sai bayan kwana uku, na goben bai yiwuwa saboda hazo. Da kyar ya iya ce da Doctor ya kula sosai kada ya barta ta fita, har zuwa kwana ukun, wato ranar sallamar ta, zai turo matar Yayanta ta tafi da ita, ya tabbata za ta yarda ta bi ta."

"Daga nan ya kira Jabeer, a yadda Jabeer ya ji muryar Uwais ya tabbata ba lafiya ba. Ya ce,  Jabeer, I donno from where to start, don ko kai ba za ka yi min uzuri ba balle Amrah. Amma wallahi ka yarda da ni ina da niyyar gaya mata ne da zarar na dawo, don in samu ta haihu lafiya. Sai kaddara ta riga fata. Yau ga kuskurena da rashin jin shawarar mahaifiya sun jawo na yi asarar babyna ."

"Jabeer ya ce,  Hasbunallahu wa ni imal wakeel, me ya faru haka Uwais? "

"Uwais ya share zufar da ke yankowa daga goshinsa, ya kwashe komai ya gaya wa Jabeer, ya kare zancensa da cewa,  I never take it serious, (auren sa da Fahimah), kuma tunda na mallaki Amrah ban kara waiwayar zancen Fahimah ba."

"Na yi duk iya kokarina a kan Amrah ta fahimce ni ban iya rayuwa babu macen aure, ta dawo"

"B.U.K mu ci gaba da rayuwarmu. Amrah ta ki fahimtata da gangan, ta sa kafa ta yi tafiyarta Malaysia ta bar ni. As a man like me na san za ka fahimci halin da na kasance kuma na san ina da wata matar."

"Amma wallahi Jabeer ban taba tunanin auren zai je ko ina ba shi ya sa na dauki lokaci ban gaya wa Amrah ba, sai kuma ga ciki ta samu mai matsaloli, sai na kara jinkirtawa da niyyar zuwa ta sauka."

"Ban san ya aka yi Amrah ta zo gidanmu ba, har dakin Fahimah, har wayar Fahimah ta je hannunta. Daga nan komai ya lalace wanda I m sure shi ne sanadin nakudarta."

"I m sorry Jabeer, wallahi ban yi da niyya ba, haka Allah ya nufa. Jabeer babyna da na kallafa wa rai ya zo ba rai, sannan Amrah na can ta tubure musu Abuja za ta koma. Bayan already na yi booking ina tafe in three days ."

"Jabeer ma ransa ya baci sosai, amma sai ya yi hali na dattaku, ya ce,  Ka yi babban kuskure Uwais, kuma magabatanka ma sun yi kuskure tun a wajen neman auren Amrah ya kamata ku gabatar da wannan maganar, in ya so in yin yin, in barin-barin. Amma yanzu ka bata goma daya ba ta gyaru ba. Don ka san Daddy ba wai yana farin ciki da aurenku ba ne don dai ya ga Amrah na so ne ya hakura."

"Don haka ni ban isa in rike Amrah a gidana ba tare da iyayen mu sun ji zancen nan ba, don"

"Murjanatu ba ta taba haihuwa ba, ba ta san ya za ta yi da Amrah ba. Don haka in an sallame ta zan je in dauke ta a asibitin mu wuce Abuja ."

"A sautin muryar jabeer Uwais ya tsinkayi bacin rai sosai, don dai yana kokarin dannewa ne. Babban bacin ran Jabeer wai a ce har shi bai gaya wa yana da wata matar bayan Amrah ba? Duk yadda suke da shi, ai zai iya gaya masa ma tun lokacin auren in ya so ya roke shi ya rufa asiri. Wannan itace abota ta hakika. Amma ina? A lokacin idon Uwais ya rufe da son mallakar Amrah anyhow."

"Don haka yanzu kam yana bayan kowanne hukunci Amrah za ta yanke wa aurenta da Uwais don tana matukar sonsa, kuma ya yi betraying dinta a magana ta gaskiya."

"Shi ya sa har kullum mota suke kuka da maza a kan rashin amanar soyayya, da gaske ne su maza ba su da tabbas in dai a kan mace ne. Amma why Uwais? Mutumin da ya ke yi wa kallon wanda ya fi kowa son Amrah? (in kina tunanin namiji na da tabbas a kanki to ki daina- Takori)."

A yadda suka yi sallama da Jabeer a wayar ma duk da yana kokarin dannewa ya fahimci ransa ya baci sosai a matsayinsa na shakikin Amrah. To ina ga iyayenta da ita kanta?

Bai dora neman aurensa a bisa tafarki na gaskiya ba tun farko don haka he must try to be a

"man, ya yi dammarar facing every challenge da zai biyo baya kawai."

"Duk maganganun da suke yi a kunnen Murjanatu wadda ke zaune a gefen sa. Bayan sun gama ta dubi mijinta sai huci yake yi. Murjanatu akwai ilmi, hankali da kyakkyawan tunani, don haka ta ce da mijinta Jabeer."

" Uwais abokinka ne na gaskiya wanda ya kamata a ce cikin kowanne hali ka tsaya tare da shi. Kada ka bi bayan kanwarka ka manta da darajar abokan taka. A halin yanzu he needs your support most. Kada ka manta mahaifyarsa ce ta yi masa umarnin auren yarinyar nan, kuma ita ke rikonta sannan ta ce in bai aure ta ba, Amran ma ba zai aura ba. I m sure dalilin shi na amincewa kenan. Wato tsoron rasa auren Amrah."

"Kamar yadda ya ce din ne if you are in his shoe, ya za ka yi? Za ka yi zina ne tunda ita ta ki"

"zama, ko ko za ka tafi ga ajiyayyen halalinka da ke gefe? "

"Jabeer bai ce mata komai ba, amma yanayin fuskarsa ya nuna sassauci."

" Ki tashi mu je mu ga halin da ta ke ciki, ya ce tana asibitin standard ."

"Murjanatu ta dauko mayafinta ta bi bayansa, domin tuni shi har ya kai waje. Babbar damuwarsa ya san laifin Uwais shi ma sai ya shafe shi a wurin Daddy, tunda dai komai ma shi ne sila."

"Da tambayar sunan patient wadda aka kawo jiya, ta haihu dan ba rai Jabeer da Murjanatu suka dangana da dakin da su Fahimah suke."

"Suna tsaye a kan Amrah ita da Ammi, Fahimah rike da kofin shayi mai kauri, Ammi rike da plate din kwai da dafaffiyar hanta da Talatu ta kawo suna ta aikin lallashinta a kan ta ci, Amrah ko idonta ta ki budewa balle ta dube su, abin da ya soma hassala Ammi don dai ita ba ta san"

"laifin da suka yi mata ba, amma Fahimah ta fara shan jinin jikinta."

Sallamar Jabeer da matarsa a dakin ya sa Amrah ware dukkan idanunta. Sannan ta yunkura

"da karfi za ta tashi, Murjanatu ta yi gaggawar rike ta ta maida ta kwance tana fadin,  Oh no"

"Amrah. Ki bari ki samu lafiya, ga ni na zo. Sannu kin ji? And we re going to Abuja together ."

"Amrah ta ji hankalinta ya kwanta, sai ajiyar zuciya ta ke yi, ta kuma daina kukan. Abin da ya daure wa Ammi kai, wato su ne ba ta son gani, to me suka yi mata ban da abun arziki? Ko tana zargin su suka kashe dan Uwais da hannun su?"

"Murjanatu ta juya tana gaida Ammi, kallo daya ta yi wa Fahimah ta gane ita ce matar Uwais."

Class din yarinyar ya isa. And her black skin is expensive and radiant a cikin mata. Sai ta ji kwarai itama tana taya Amrah kishi da gaske.

"Kishi da wannan zukekiyar black beauty ai sai jarumar mace mai karfin zuciya, wanda ta tabbata Amrah ba ta daga cikinsu."

"Har dare Murjanatu na tare da su, ita ta sa Amrah ta karbi shayi ta sha. Abin da ya kara tayar wa Fahimah hankali shi ne, yadda tunda Amrah ta farka ta ki ko da duban inda ta ke."

Wannan ya tabbatar mata da kyar in wani bai lalata al amarin ba (ya riga Uwais gaya wa Amrah) wanda shi ne sanadin nakudarta da wannan fushin da ta ke musu har Ammi.

"Duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, don haka ta janye jiki daga inda Amrah ta ke. Daga baya ma ganin Murjanatu na nan ta ce da Ammi za ta koma gida ta yi wanka sai dare za ta dawo ta kwana. Ammi ta ce, Murjanatu ta tambayi Amrah me ta ke so a kawo mata da daddare?"

Amrah ta tsuke baki ta ki cewa komai.

"Ammi sai da ta kai zuciyarta nesa, amma da ita ma tafiya ta yi niyyar yi tare da Fahimah, amma ta taushi zuciyarta ta zauna. Ita kanta Murjanatu ba ta ji dadin wannan hali da Amrah ke nuna wa uwar mijinta ba. Amma Ammin tana wajen ba ta tashi ba, don haka ba dama ta yi mata fada."

"Da Murjanatu ta tashi tafiya bayan magriba da Jabeer ya zo daukarta, Amrah tuburewa ta yi ba ta yarda Murjanatu ta tafi ba, sai dai ta kwana da sassafe su wuce Abuja ko Doctor bai sallame ta ba."

"Kunya kamar ta kashe Murjanatu, don a gaban Ammi Amrah ta fadi maganarta kanta tsaye."

"Ita ma Ammin tun daga nan ta sha jinin jikinta cewa, abin da ta ke guje wa Uwais tuntuni ya faru. Wani munafikin ya yi masa riga malam masallaci."

"Sai ba ta ga laifin Amrah ba, domin laifi guda har da rabi Uwais ya yi mata. To amma ita kam babu ruwanta, wanda ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Ba yadda bata yi da shi ba akan ya fada mata tun farko ya ki."

"Dole Murjanatu ta kwana, Fahimah kuma da ta koma gida ta dauki wayarta a inda Amrah ta yasar da ita, sai ta duba missed calls dinta. A nan ta ga received call na Uwais da sha biyun dare kamar lokacin da yake kiranta kullum don yin midnight call."

"Ta tuna a inda ta bar wayar, da kuma barci da ya dauke ta da wuri. May be Uwais ya kira, Amrah ta dauka, shi kuma ya yi barambaramarsa da ya saba. Mutumin da in ya soma sakin romantic zance sai ta rasa inda za ta sanya kanta don kunya."

 Hasbunallahu wa ni imal wakeel .

"Fahimah ta fada a fili, ta zauna gefen gado ta dafe kanta."

Wannan ne ya sa ta kasa komawa asibitin da daddare. Ta ma kashe wayar don kar Ammi ta kira ta ce me ya sa ba ta dawo ba. Shi ma Uwais yau ba ta so ya kira ta. Kowa ya je ya ji da damuwarsa shi kadai.

"Ko barci ta kasa, sai kawai ta dasa nafilfili a tsayin daren baki dayansa. Takamaimai ba ta"

san me ta ke roka ba. Ko me ye bukatarta? Ban da Allah ya kawo daidaiton zukata cikin

"al amarin, domin ba za ta so auren Amrah ya mutu a kan nata ba. Ciwon  ya mace na  ya mace ne, ko ita aka yi wa haka duk son da ta ke wa Uwais sai ta hukunta shi, balle Amrah da ta dauki dukkan yardar duniya ta ba shi."

"Ita da ma a philosophy dinta babu sakankancewa a kan cewa namiji nata ne ita kadai. Ta sa a ranta bayan Amrah, Uwais na da damar da zai karo mata biyu, don haka ba ta taba yaudarar kanta ba kamar yadda Amrah ta dauka. To ina batun da ta ke yi mata a baya na cewa ta auri Uwais? Ashe dama duk a baki ne bai je har zuci ba zafin laulayi ne, lol? Ita kam tun daga wancan lokacin ne ta ji ta kara son Amrah, duk da hakan bai hana ta jin kishinta lokaci zuwa"

lokaci ba.

"Washegari da safe bayan ta yi sallar asubah da wuri ta shige kitchen ta shirya abin da ta tabbatar Amrah za ta iya ci, da wanda su Ammi za su ci, sannan ta dauko basket din zuwa waje da zummar zuwa bakin titi ta hau adaidaita zuwa asibiti."

"Tana fitowa harabar gidan motar Ammi na shigowa. Don haka ta ja tunga ta tsaya har Ammi ta yi parking a inda ta ke ajiye motar kullum. Fahimah ta karasa ta karbi hand bag din hannunta suka rankaya zuwa ciki. Tana fadin,"

" Da ba ki wahalar da kanki ba sun tafi Abuja tun dazu, kuma kin kama kin kashe waya balle"

"in gaya miki. Ni yau na ga abin da ya ishe ni, kishi hauka ne da za ki sabi hanyar Abuja da sabon CS a jikinki? "

 Hasashena ya tabbata! Fahimah ta fada a ranta.

"Jiki a sanyaye ta maida basket din kitchen ta koma daki. Ta kunna wayarta kenan kiran Uwais ya shigo, da sauri ta sake kashewa don ba ta da courage na cewa komai."

"Amma sai ga Ammi ta biyo ta da tata wayar har dakin,  Fahimah, don me za ki ki amsa wayar mijinki saboda wata can ta yi fushi da ku? Maza karbi ki yi masa ta aziyyar rashin da ya yi, ai shi ya ja wa kansa da ya bi maganata tun farko, da yanzu hankalinsa a kwance. Yana bukatar mai lallashin sa, maza karbi wayar nan kamin ki bata min rai ."

Fahimah ta karbi wayar. Ammi ta juya ta fita.

" Fah-himah, are you there? "

"Muryar

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment