ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

and manner da na"

tabbata wata diya mace  yar uwata ba ta taba samu ba.

"Idan na rike Uwais a raina bayan duka wannan ni imar da Allah ya yi min ta mallaka min shi matsayin mijina uban 'ya'ya na, na zama mara godiyar Ubangiji."

"Besides, an ce so hana ganin laifi Ya Uwais, ni fa ban taba jin haushinka ba, karewa ma komai ka ke yi burge ni ka ke yi. Rana daya ce na ji haushinka a rayuwata, ranar nan a Sudan&  ."

"Da sauri shi ma ya toshe mata baki yana girgiza kai, ""Kada ki tono abin da ya riga ya wuce, domin na tabbata alhakin wannan ranar ba nawa ba ne, naki ne. And i sincerely repented, so ni da ke duka masu laifi ne kuma tare za mu ke istigfari ."

Let s go for another  Ya rada mata sauran maganar cikin kunnuwanta.

" Umh&  Fahimah ta iya cewa domin dadin bakin Uwais in yana son abin da yake so yawa gare shi, ba ta da ikon musantawa don bai ba ta damar hakan ba ma."

"Ammi ba ta gansu ba sai karfe sha daya na dare. Fahimah sai baya-baya ta ke yi daga bayan Uwais da ganin ta ka ga mara gaskiya. Shi ko Uwais ko a jikinsa, karasawa ya yi da sassarfa ya rungume Ammi ya sumbaci goshinta. Da wannan damar Fahimah ta yi amfani ta gudu dakinta, ta barsu suna tasu soyayyar ta da da mahaifi. Har wata ajiyar zuciya ce ta kwace mata da ta ganta a dakinta. Ba tare da ta karbi query daga Ammi ba."

"Ammi kuwa ba ta bi ta kan wannan ba, farin cikin ganin Uwais ya ishe ta. Sun gaisa sun sake gaisawa har da musabaha irin ta larabawa. Ta ce,  Uwais kamar ba kai ba, Switzerland ta amshe ka, ina fatan an yi nasarar duk abin da aka je nema? "

"Uwais ya ce,  Nasara kam an same ta Ammi alhamdu lillah, ga sabon albishir da nake son yi muku, World Bank da muka je yin course dasu sun ba ni aiki tare da su a yanzu haka, na bar GT idan na dawo. Yanzun ban karasa ba saura sati 3 mu gama gabadaya, na ga cewa ya zama dole in zo in saita al amuran gidana ."

"Ammi ta ce,  Ina yi maka ta aziyya Uwais, Allah ya sanyaya, Allah ya ba mu rayayye. Sannan sai ka kai zuciya nesa ka yi hakuri da Amrah, don kuwa laifi kan laifi ka yi mata. Don haka ka jure duk abin da za ka gani ko za ka ji daga gare ta ko iyayenta, tunda kai ne mai laifi ."

"Uwais ya yi murmushi kawai ya mike, bai gaya wa Ammi abin da Alhaji Umar Dikko ya ce ba, na cewa in bai sako masa Amrah ba zai kai shi kotun koli. Da kuma hukuncin da zuciya ta kwashe shi ya yanke tun a lokacin ta sakin Ammi, yanzu haka takardar tana cikin kayansa, jira yake zuwa jibi in ya kara hutawa ya runtse ido ya kai wa Jabeer."

Yana addu ar Allah ya sa kada rabuwarshi da Amrah ta yanke kyakkyawar alakar da ke tsakaninshi da Jabeer Dikko.

Wanka ya sake yi sannan ya sa farar shirt (Hilfiger) da wandon jeans dark blue ya fito falon jaye da akwatuna guda biyu.

Ya samu Ammi tana marking takardun dalibanta da medical glass a idanunta. Ta daga kyawawan idanunta ta dube shi tana murmushi.

 Sai ina kuma? Na ganka ka dau wanka ka janyo akwatuna? Ko bikon za a tafi cikin daren nan?

"Murmushi Uwais ya yi ya zauna a gefenta yana bude akwatunan, ya ce,"

 Ammi bikon lafiya? Laifin me na yi da zan je biko? Na dauka bayan Amrah da Fahimah ina da damar kara guda biyu ba tare da na yi wa Ubangijina laifi ba?

"Ammi ta ce,  Haka ne, amma a al adance ka yi laifi ba a addinance ba. Ni dai ban yi wa kowa cikinku laifi ba daga kai har Amrah domin kuwa auren Fahimah na sa aka fara daurawa, ban kuma ce wani cikinku ya boye zancen ba, don haka can ta matse muku kai da Amrahn. Amma ina so ka yi hakuri ka dauki girma ka amsa laifinka, sannan ka bada hakuri ta dawo dakinta."

"Kowa ta zauna a gidanta, ban yarda da hada muhalli ba ."

"Uwais bai ce komai ba, ya rika fidda tsala-tsalan atamfofi, shaddodi da lesuka yana tulewa a gaban Ammi, ya ce,  Ammi ga tsarabarku. Sai ki zaba wa Fahhimah wanda zai dace da ita, I don t know her favourite colours yet, kuma ban yi azancin tambayarta ba ."

"Ammi farin cikinta ya fi gaban misali,  Allah ya albarkaci rayuwa Uwais. Amma ni tsohuwa me zan yi da wadannan kayan gayun? Na bar wa Fahimah bakidaya tunda tarewa za ta yi, ta je ta yi ta yi maka kwalliya da su ."

"Murmushi ya yi ta sake cewa,  Ina na Amrah? "

"Kamar ya ce mata,  She s no longer Mrs Shagari now . Ya tuno halin Ammi na dattaku ba za ta bar shi ya bada takardar nan ba ko da za su kai shi kotun."

" Zan kai mata jibi in za ni, don gobe tun safe har dare in na fita ba zan dawo ba, zan maida hankali a kammala komai na gidan Fahhimah ta tare jibi, don tare za mu koma Switzerland tunda sun yi hutu, wata daya ne na gama gaba daya don a reshensu na Najeriya za'a ajiye mu. Kuma a garin Abuja ne, don haka zan nema wa Fahimah transfer zuwa (BAZE) tunda ta gama year 1 ."

"Ammi ta ce,  Hakan shi ne daidai, ni bana bayan miji na wani gari matarsa tana wani saboda kananan dalilai. Duk abin da zai zama dole ba a barshi a nemi alternative a zauna tare a nemi lahira. Tunda duk wani buri na duniya an gama samunshi, ilmi, career da aure na hakikah."

Yanzu sai shirin tarbar abokai da kawayen Ammi.

"Sannan Uwais na aika takardar murabus daga aiki, idan kun dawo daga Switzerland kun nabba a a permanent sabon muhallinku, ni kuma zan koma SUDAN gaba daya, a can zan"

karasa rayuwata. In kun haifa ku kai min Khartoum zan rike muku .

Mu hadu a book 3 na karshe


Downloaded From https://arewanovels.com


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment