ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Cikin kulawa ya zagaya ta shiyyar da yakan koma cikin gidan. Ya tarar da HILAL tsaye bakin qofar cikin shiga ta masu tsaron qofar kamar yadda suka saba tsaiwa da kuma sanya suturarsu,ya dage masa qarfen tsaron da akan rufe qofar cikin matuqar girmamawa yana bashi hanya. Hannunsa kadan ya motsa alamun yabawa hilal da jinjina yana wucewa cikin gidan.

Kansa tsaye ya wuce sashensa yana qoqarin jingine tunanin don bibiyar beno akan aikin daya turashi. Agogo ya kalla,zuwa sannan ya tabbatar beno yana dab da isa gurin indai ya isa akan daidai lokacin da ya tsara masa,don haka ya qara sauri yana murza key ya buda sassan yana shiga yana motsa labbansa da sallama.

Saman kujera ya hangeshi,abdii ne kwance rigingine,ya kife wani littafi saman qirjinsa da alamu suka nuna yana tsaka da karantawa bacci ya daukeshi.

Can qasan ranshi yayi murmushi wanda sam bai nuna ba koda saman labbansa,ya taka a hankali ya zare littafin yana ajiyewa gefe.

Ko yaushe abdii yana maida kansa yaro saboda shi. Koda yaushe abdii baida zuciya indai a kansa na,baya fushi sam,ko me zai gaya masa don yayi nesa dashi kaman yadda ya buqata baya yarda da hakan,baisan wanne irin qauna haka yake masa ba. To amma a irin wannan yanayin da al'amura suka fara bayyana kansu sam bayason abdii din ya cika kusanci dashi.

Gefan qafafunsa ya tsaya ya miqa hannunsa kadan ya tabashi,sai ya bude idanunsa kuwa da sauri.

"Ka koma ciki ka kwanta" Yace masa kawai yana haurawa sama idanunsa kan agogo yana ci gaba da lissafa lokaci.

Kayan jikinsa ya zare bayan ya samu signal na beno,ya kuma musanyasu da wasu farare qal din pyjamas masu dogon hannu da tsananin taushi. Wani irin kyau yayi duk kuwa da cewa ba tufafi bane na ado,sassalkar sumarsa ta kwanta luf saman kansa ta kuma dan hargitse kadan garin sanya pyjama din jikinsa,sai ya qara fita ya duba ma'ajiyar coffee dinsu,ya sameta cike da zazzafan coffee. Yana da sauqin kai a abubuwa da dama,da kansa ya zuba cikin wata qawatacciyar tea pot.



Sosai balcony din ke masa dadi,wannan ya sanya ya taka zuwa ciki dauke da tea tray din,ya kuma dora saman wani stool dake da wata zagayayyar sofa me taushin gaske.


*AKHNAN*

Tafukan hannayenta duka biyun ta shafa saman lallausar fuskarta data haska cikin rolling din dake saman kanta,wanda ta yishi da mayafin after dress din jikinta data sanya saboda sallar isha'i da tayi yau a makare.

Duka yau din bata iya tsinana abun arziqi ba,tun bayan da sukayi magana da mammina akan gobe zata gabatarwa da sultane mijin data zaba. Zataje ita daya,ba zata mata rakiya ba wannan karon,fuskarta kuma ba zata bayyana ba,don magana ce tsakanin uba da d'iyarsa.

Tana jin nauyin sultane har cikin jininta na yadda zata iya kallonsa ta gaya masa ga mijin da ita take so ta aura,ga kalar zabinta. Mijin da ko sau daya taqi yarda taga koda hotonsa.

Maida idanunta tayi ga aisa dake kwance rub da ciki sama gadonta,yau haka kawai tayo qaura ta taho dakinta kwana. Ta taho da dukka ayyukan sahel couture tace a nan zatayi,wai ko hakan zaisa hankalin akhnan ya koma ga kamfanin. Tun dazu take aikin tana kuma mita.

"Komai na enterprise ya tabarbare.......komai baya tafiya akan tsari da doka,kina wasa sa shugabancinki,komai yana shirin lalacewa,iya abinda zamu iya riqawa nida shehnaz munyi......mammina ta kasa aiwatar da komai akai,ban sani ba,tsananin yardar data bawa mutanen ne ko kuwa?" Aisa ta fada da gasken gaske tana hango downfall na kamfanin. Tana gano yadda wani taqi kadan ya rage kamfanin yakai qasa warwas,ta soma jin kishin wahalar da sukasha a kamfanin,ta soma jin ANYA BA ZATA KARBA ba kamar yadda mammina ta fada?.

"Ta rayuwar me sahel couture din ake yanzu haka........idan sahel ta fadi dasa hannunki a ciki......mammina tace ki karba saboda tasan a yanzu banda energy din komai amma kin wofantar......ki daina complaining min komai aisa" Ta furta tana miqewa daga saman abun sallar. Iska me kyau takeso ta shaqa sama da wadda ke cikin dakin ko zatayi tunani me kyau,saita ware rolling din,saidai bata sauke dankwalin duka a kanta ba,ta doshi qofar da zata sadata da private bedroom balcony dinnata.

Da kallo tabi akhnan,ba wani abu da yake daidai a yanzun a tare da ita da gaske ne........tana jin kawai zata karba......zatayi accepting,ba tare da TUNANIN KOMAI BA ta soma rubuta doguwar wasiqa me dauke da sharhin karbar office din akhnan din a madadinta wadda za'a sanar da kowanne department.

A hankali take takawa a cikinta tana zuqar fresh air din da kyau tana aikewa hunhunta,ta kama dankwalin da kyau cikin jikinta tana curewa guri daya saboda sassanyar iskar dake kadawa wadda keda dan qarfi kadan kadan. Gaba ta matsa jikin qarfen da ya yiwa gurin qawanya ta sanya hannunta ta dafeshi tana duban qasan stairs din daya kasance wata farfajiya dake bayan gidanta da takan zauna lokaci lokaci.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Iska ta fitar sirirya daga bakinta,tana dan ji a jikinta kamar ba ita kadai bace tsaye a gurin,saidai ta sani,ba wani mahaluqi daya isa ya tsaya a inda take tsaye a lokaci irin wannan idan ba aisa ko shehnaz ba,wanda dukkansu ba daya daga ciki. Ido ta lumshe sannan ta budesu tana jin wata kewa tana ratsata,a wasu watannin baya da suka shude,ba wani abu da yake bata nishadi irin wannan lokaci. Tana jin dadin tsaiwa a wajen,tana jin dadin irin iskar da gurin yake bayarwa,tana kuma sake samun cikakken nishadin da tunda ta tashi a rayuwarta nishadin kawai ta sani,batasan wani abu waishi baqinciki qunci ko bacin rai ba,sai a wadannan kwanakin,sai a wadannan lokacin da aka hana rayuwarta da tunaninta sakat akan 'YA'YA MAZA!.

Yunqurin shigarsu rayuwarta kawai yana neman gigita mata rayuwa,ina ga ance yau gasu cikin rayuwartata?.......da dukkan qarfin ikon da zasu mallaketa su kuma sarrafata?.....ita ta dade da fahimtar sam BA ALKHAIRI ciki wannan halittar a rayuwar mace me gata da 'yanci irinta.

Siririn tsaki taja tana dauke idanunta daga qasa tana dawo dashi sama saboda wannan kalar qamshin da take jiyoshi kamar nesa kadan da ita. Kai tsaye kuma idanun nata suka sauka a kansa,sanda yake tsaye gaban nasa qarfen balcony din,ya maida hankalinsa sosai ga wayar hannaunsa yana dannata da wani irin sauri kamar me wasa da abun wasan yara saboda tsananin haddade mazauni da muhallin kowanne keyboard dake fuskar wayar.

Beeno yake maidawa amsa da sauri gudun faruwar kowanne kuskurd,ya fadi masa kada ya sake yayi magana dashi saidai ta hanyar tura saqo,yaci gaba da zama a gurin kuma har zuwa sanda zasu tabbatar ba fita ko motsin wani,sannan yanaso ya yiwa gurin alama......gobe akwai na'urar da yakeso su sanya a gurin.

Tsaiwa yayi cak bayan ya tabbatar saqon yaje,sai kiran omar ya shigo masa,abinda ya sanyashi daga kansa daga kallon wayar ya karata a kunnensa wannan. Shuru yayi manyan fararen idanunsa suna dan juyawa kadan,kafin a nutse ya motsa kyawawan labbansa da dumin coffee din daya fara sha ya sake sanyasu suka zama masu laushu,color dinsu kuma ya fita sosai

"Yes...." Ya amsa maganan omari da wani irin calmness da haka kawai yakejin jikinsa yana mutuwa.

"No omari......" Ya sake amsawa yana lumshe idanunsa da mamakin baqon yanayin dake shiga jikinsa lokaci daya.

"Continue observing......don't act yet.....I'II handle it" Ya fadi yana gyada kansa a nutse. Zare wayar yayi daga kunnensa,hankalinsa yana kan device din dake maqale a kunnen nasa wanda yake monitoring motsin beeno da kyau.

"Reduce the noises beeno,motsinka ya danyi yawa" Ya fadi a hankali a nutse yana jj kaman shine a gurin yana sake matsawa gaban balcony din hankali da idanunsa suna kan wayarsa. A hankali ya zare dubansa daga kan wayar yana daga idanunsa a sanda yake sanyata a aljihun wandon jikinsa.......kai tsaye idanun nasa suka zarce kanta,sanda take tsaye cikin wani haushi da bacin rai dake tsirowa daga qasan ranta.

Tana sanye da fararen kaya yana sanye dasu......ashe bayan jubah da jallabiyyar da yake sanyawa har yana da zabin sauya kaya cikin dare haka don ya samu sakewa cikin masarautar da take mallakin ubanta?.......tana tattaki saman farfajiyar data kasance tata ita daya a matsayinta na 'YA GUDA kuma mallakin sultane muhammad hammud......shima ya samu irin wannan chance din a matsayinsa na BAGIDAJEN malamin da ba abinda ya sani sai zallar litattafai larabci da yaren da qila na uwa ne.......sai hausarsa da yake yinta da qyar wadda sam bata mata dadin saurare.


zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


*BOOK 02///PAGE 22*
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________



Ta mallaki sashe guda......shima sultane ya mallaka masa sashen daya kasance cikin sassan masu girman daraja cikin gidan. An bashi masu tsaronshi......an wadata shi da dukkan abinda aka wadatata dashi.....to wai shinma mens bambancinta da wannann BAQON kuma DAN CI RANI wanda ya shigo cin arziqin mahaifinta?.


"Morsa safiyya ce sila" Sashen Zuciyarta dake cike da tsanarta ya gaya mata kai tsaye. Ta gamsu sama da dari bisa dari ba,duk wata matsala daga matar yake,duk wani hanya da zata tozarta gami da qasqantar da matsayinta itace a gaba gaba......waishin TA YAYA ZATASO WANNAN MATAR?.....HAR GABAB ABADA!.

Kai tsaye idanunsa suka gauraya guri daya,wanda kafin yakai ga hakan idanunsa suka soma sauka ga sassalkan gashinta da iska ke wasa dashi tana watsashi daga hagun fuskarta zuwa dama. Bata kwanciya da kowanne nau'in ribbon saboda takura,wannan ya bawa iska daman kada gashin nata duk yadda taga dama bayan ta zame dankwalin nata daga kanta zuwa kafadar hagunta ba tare data sani bama saboda tsabar yawan tunani da bacin ran dake cunkushe fal qasan zuciyarta.

Sosai ta kafeshi da dukka kallonta.....wadannan idanun ababen zargi ne a gurinta.....wadannan idanun da take da muradin musu zuzzurfan kallo,wanda ta tabbatar idan tayi hakan tsaf zata iya ganewa da fahimta.....SHINE NA HIPPODROME?.

"SHINE" Wasu lokuta zuciyarta ke gaya mata. Ta tabbatar qaqqarfan haushi da tsanarsa da takej bayan rashin jituwa na cikin jini da jijiya da takeji akan dukka gidadawan malamai irinsa......wanda basu da wani arziqi daya wuce na zama su karantar da takarda.....akwai wani kwantaccen abu na daban kuma daya qara assasa hakan.

A yau tana jin zata zurfafa kallon wadannan idanun da batasan me ya banbantasu da sauran idanu ba .......duk da kaifin da takeji yana shigarta.....duk da kaifin da takeji kamar suna dashi,shigen kaifin da takanji cikin idanun sultane wasu lokutan da suke hanata duban sultane din kai tsaye a yawancin lokuta.

Duk da 'yar qaramar tazarar dake tsakaninsu amma hakan bai hanashi hangen tsananin IZZA da GIRMAN KAI gami da TSIWA me qarfin gaske cikin idanunta ba,ya barta ne taci gaba da duban qwayar idanunsa kaman yadda ya fahimci muradinta kenan......kamar yadda ya fahimci tanaso ta karantashi ne ta idanun da yayi imanin koda shekara guda zasuyi tsaye a gurin ba zata iya karantar duk abinda takeson ta karanta daga gareshi ba......sai idan shi yaso......sai idan shi yaga dama ya buda mata hakan.

Duk wani motsinta na binciken abokin tseren wasanta yana da masaniya akai.....zuwan tamim na qarshe....wanda shi ya yarje su bashi gwajin tsahon da komai nasa. Yayi hakanne saboda yana son tantance zurfin kwanyarsu,yana son gane zurfin tunaninsu da tsinkayensu,amma sai yaji duka ya rainsu da wannan gwajin ya kasa kaisu inda ya kamata ace sunkai.

Har gwara ita yana mata kallon mace me rauni ta kowanne fanni,amma ga tamim fa?,da yake cikakken namiji daya zama amintacce a wasu kebantattun ayyuka na musamman cikin gidan?.

Damqe qarfen tayi da kyau tana qwararawa kanta gwiwar ci gaba da kallon tsakiyar qwayar idanunsa a sanda taji wani abu me haske yana ratsa cikin idanunta,yana soke duk wani confidence nata.......a sanda take hangen kallon da yake mata da bai nuna komai ko wani yanayi na ita din ta masa kwarjini ba kaman yadda ta saba yiwa kowa da zai kalli idanunta haka kai tsaye a gurare daban daban,wani irin calmness duba yake mata don qure qarfin gwiwar da takeji tana dashi.

Da wani irin mugun sauri kamar numfashinta yana shirin qwacewa daga hunhunta ta kauda fuskarta gefe tana sauke wani kalan numfashi me tsananin nauyi. Sai ya janye idanunsa shima daga kanta yana sake fiddo wayarsa a nutse abinsa saboda duba mintunan da beeno ya shefe ba tare da ya sake jin motsinsa ba kwata kwata.

"Me yasa na kasa?" Ta tambayi kanta.

"Me yasa yake kasancewa a duk inda bana buqatarsa?" Ta sake tambayar kanta a wannan karon baqinciki da bacin ran yadda ta gaza ci gaha da dubansa yana mamaye Zuciyarta. Bata samu sakamakon komai ba,sai rikicewa da kokwanton SHINE?....BASHI BANE da Zuciyarta ta sake afkwa a ciki.

Sake matse qarfen tayi da hannunta tana sake jin baqinciki da sabuwar tsanarsa tana ratsata. Ta kasa Karantarsa ta cikin idanunsa,ta kasa gano komai.....me yasa?.

"Are you on the line?" Ya tambayi beeno muryarsa can qasa.

"Yes obbo.......inajin ba zamu qara minti takwas ba a gun.....naji kaman akwai alamun koda kowanne lokaci za'a iya fitowa" Kai ya jinjina.

"Good.....use silent device kayi snapping min pictures na wadanda suka fito......shut the flash and sound"

"Yes sir" Ya fada cike da girmamawa. Katse wayar yayi,daidai sanda yaji muryartannan da yawancin lokuta tana zuwa kunnensa ne da sautin tsiwa tana fadin.

"Masarautar mu tana da doka......tana kuma da qa'idojin da bai kamata a dinga yawo barkatai a cikinta ba a dukka lokacin da mutum yaga dama......wasu suna da buqatar sirri sosai......da janye sanya idanu a kansu". Shuru yayi yana dubanta duba na kai tsaye. Yana hasashen inda a jimma ne......inda a Ethiopia ne lallai sai wannan attitude din nata na tsiwa ya sauya.

shirunsa ya haifar mata da kokwanton daya tilasta mata waiwayo ta dubeshi,sai ta sake kawar da kai.

"Har yanzu baka haddace dokokin rayuwa cikin masarautar agadez ba.........idan kanason tsira da idanunka lafiya ka guji kallon gimbiya akhnan haka kanka tsaye babu ko martabawa da girmamawa bare rusunawa". Baisan wani siririn murmushi ya kubce masa ba,yayi qasa da idanun nasa bawai don cika umarninta ba.....aah....saidai yadda namakinta ya sake cikashi.

Tana rayuwa a wannan 'yar qanqanuwar duniyar tata ba tare da tasan cewa duniya ta cika da manyan masarautu ba......duniya ta cika da manyan sarakuna dake da tsananin girma qarfi da tasirin da inda a zamanin yaqe yaqe ne loma guda zasuyi da masarautar tata da abinda ke cikinta. Wani sashe na fadar aba jifar ya tuna......wanda ba kowa a ciki.....wanda yake yashe cike da kayan alatu na alfarma da ake sauyawa duk shekara......amma ba kowan da zai zauna a ciki duk tsaruwa sa tsadar abubuwan daya qunsa.....muhallin da ya kusa girman sassanta da wanda yake ciki da wanda iyayenta mata biyu dukka suke ciki.

"Wanda ke buqatar sirri da wanda ke cikin nutsuwa.....mutanen da qirjinsu bai nauyaya sa zuzzurfan tunani da tsoron rushewar gobensu ba.....a irin wannan lokacin suna cikin dakunansu kwance suna bacci cikin cikakkiyar nutsuwa" Yayi maganan da wani irin salo da harshe da ya sake sanyata kallonsa a sace a karo na biyu.

Kansa ya daga shi kuma yana duban taurarin dake sararin samaniya,ya rage duban nasa kadan yana sake motsa kyawawan labban nan.

"Duk wanda shimfidarsa ta gagareshi......tabbas damuwa da neman mafita dole ya watsoshi waje". Wani iri shock taji ya kamata,wata irin tsarguwa ta saukar mata.

Damuwa da rashin mafita?.....anya baisan komai ba?,baisan abinda yake faruwa dama wanda zaya faru gobe ba?. Wani irin fargabar rasa izzarta da girmanta ya sanyata lumshe idanunta sannan ta budesu. Zaya zame mata babbar barazana da abun kunya indai har sultane ya gama sanar dashi komai. Bataso bata kuma barin abinda zai taba izzarta sam,bata bada qofar gano lagonta,don haka ta sake maida dubanta kanshi cikin wani irin fushi,dai dai sanda yakai cup din coffee dinsa bakinsa hankali kwance idanunsa cikin cup din yana duban abinda ya rage bai shanye ba.

"Ka sake da yawa cikin masarautar nan" Ta furta tana jinjina kai bacin ranta yana bayyana muraran saman fuskarta. Baikai ga sauke cup din ba wata iska me qarfi ta taso ta yaye dankwalin kanta gaba daya,bata kuma direshi ko ina ba saikan fuskarsa ta lullube idanunsa harma da cup din coffee din da yake sha.

Tsaiwa yayi cak da hadiyar coffee din,lallausan qamshin dake jikin dankwalin ya soma shigewa hancinsa sosai. A hankali ya saka hannunsa guda daya ya yaye dankwalin,riqeshi yayi a hannunsa yana dubansa kafin ya maida idonsa kanta.

Duba yayi mata irin na dazu,normal duba ne amma sai takejin kamar wannan kallon da yayi mata yasha banban da wanda yayi mata dazu. Wani irin nauyi taji yana cikata,sai take jinta kamar tana tsaye a tsakiyar waje ne dake da tarin al'umma ba tare da cikakken kallabi ko hijabi ba,duk da yalwatacciyar after dress din dake jikinta wanda a qasanta wasu lausasan riga da wando na bacci ne kalan farare suma.

"Subhanallah" Ya fada a hankali yana zare idonsa a kanta,gashinta wuyanta dama saman qirjinta dukka sun bayyana,duk da yadda take hade jikinta guri guda dashi baisan meye ma'anar hakan da takeyi ba. Jira take ya cillo mata dankwalin amma tana jin girman kai da izzar tambayarsa,saita ci gaba da hade jikinta guri daya kawai fushi yana sake mata tasiri da tunzura Zuciyarta.

Takowa ya sakeyi a nutse zuwa gaban qarfen balcony din,zura dankwalin ya soma yi ta cikin qarafunan.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)


"Bama wanzuwa a gurbin da ba'a gayyacemu ba......kaman yadda bamu aminta da fita cikin dare ba idan ba damuwa ce sila ba......"

"Wannan ba abinda ya shafeka bane" Ta fada da hanzari saboda zuwa yanzu tana jin kamar yasan komai daya shafeta,kamar yasan dalilin fitowarta,ita kuma ba abinda tafi tsana a duniya irin kasan weakness dinta.

Cak ya tsaya bayan ya kammala dauren mayafin daidai sanda ta fadi ba damuwar tasa bane,sai ya daga shanyayyun idanunsa da zuwa yanzu suka sake janyewa ya zube mata su.

"Na sani" Ya fadi kansa tsaye,sannan ya juya da wata irin nutsuwa ya kwashe tray dinsa da wayarsa yana takawa cikin ginshirar nan tasa yana wucewa.

Da idanu ta rakashi har zuwa sanda ya maida qofarsa ya kulle ya zuge labulensa. Maida kallonta tayi ga dankwalinta,yadda iska ke wasan kura dashi jikin qarfen balcony dinsa.

Wani irin takaici da baqinciki suka cika Zuciyarta. Dankwalinta ne daure jikin qarfe kaman wata tsintacciyar mage?,koda bawon ayabar da taci ta jefar abar girmamawa ce cikin masarauta......koda kwalin data gama shan abu abun girmamawa ne gurin daukeshi daga gurin,yau ga suturarta tana yawo tsakanin iska da qarfe?.

Juyawa tayi da wani irin sauri tana komawa cikin bedroom din nata,yanayin shigartata ya janyo hankalin aisa ta miqe daga kwanciyar rub da cikin ta ta zauna sosai.

"Waye shi?,me ya dauki kansa?.......qasqantaccen malamin da baisan komai ba bai iya komai ba sai koyarwa.......sultane ya bashi dama d qofar da zai iya maida min magana!" Ta fadi cikin hargagi muryarta na shaking. Idanu aisa ta zuba mata,ta fahimci inda maganan ta dosa.....ta kuma gano komai

"Akhnan......calme toise mana.....sultane ya fiki sanin dukkan abinda ya dace...."


"Don Allah tsaya mana aisa.....me yasa ba'a ajiyeshi sassan baqi ba?.me yasa sultane zai kawoshi kusa dani ya dinga takuramin?....ko ya dinga rainani yana ganin matsayinmu daya?,sultane ya dauki matsayin d'ansa ya bashi......wannan banyi magana ba.......ya dauki muhallin da iyalinsa da 'ya'yansa kawai suka cancanta,shima bance komai ba........yanzun kuma anzo gurin da bazan lamunta ba......bazan dauki qasqantar da matsayina ba".

"Biftu mana!" Aisa ta fadi tana mamakin yadda akhnan ta zafafi lamarin da yawa,duk da bata gama sanin ainihin meye ya faru a yanzu ba,amma don takun saqa tsakaninta da kowanne malamin addini tasan ya qara qulluwa ne bayan hakeem da akayi niyyan bata,a yanzu tasan sai abinda yaci gaba,don kamar hakan ya qara matsa mata qaimi ne.

"Biftu" Aisa ta sake kiranta da nutsuwa. Wannan karon idanunta da suka juye da bacin rai ta zubawa aisa din,tana jin kamar zata dameta da qabli da ba'adi,zata kuma hanata aiwatar da abinda ta qudura.

"Guy dinnan ina miki rantsuwa da Allah ba ordinary mutum bane..... Ki tsaya ki fahimta da kyau.....ba ordinary sheikh bane......"

"......eh,na sani na kuma gani,sau biyu yana niyyar rungumata da sunan taimako,kuma a gobe basai jibi ba zan gayawa sultane komai,ya nisantani dashi,ya kuma karbi matsayin dansa daya bashi don bai cancanta ba". Baki aisa ta rufe tana dubanta.

"Akhnan......ki dauki komai da sanyi fa?......kada kizo ki fola masa" Motsa bakinta tayi da zummar sakin ashar wa aisa,amma kasancewar bata saba ba saita kasa fita.

"Na rantse da Allah gwara na auri tantirin mashayi dan iska mara galihu"(fata na gari lamiri inji bahaushe,yana da kyau ka dinga iya harshensa ka iya yiwa kanka fata me kyau).

Dukka idanunta aisa ta fidda waje,mamakin akhnan yana mamayeta,wanne irin tsana ta yiwa sheikh haisam?.....mutumin da iya tsahon rayuwarta a duniyarta cikin nutsatsen nazarinta bata taba ganin NAMIJI daya tattara dukkan abinda takeso ba kamarsa.....bama ita ba.......tunda taji shehnaz na fada tabbas ba wata d'iya mace da zata aza idanu a kansa taji baiyi mata ba. Wani irin dabi'u ke tare dashi da kowacce rana take sanyasu zama ita da shehnaz suna tattauna banbancinsa da sauran masu karantarwa.

"Na aika ko zai dinga daukana karatu weekend kawai idan munzo daga Niamey amma yace a bani

Please Login or Register in order to submit comment