ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com ÿþZANYI BIYAYYA COMPLETE

*By FENERH*

"*Alhmdulillah masoya na Asali am back nadawo muku da labarin da zai kayatar daku, bazan iya kwatan tamuku mai ya Kunsa ba sai kun biyoni zakuji da kanku, masoya na godiya mara adadi naga kauna a last littafina naga masoya masu kaunar cigaba na Allah ya Kara budi da kauna inyita sambado muku labarai kuna ruwan na data , kamar yadda na yi wancan wannan ma hakane masoya is not for free gsky haryanzu bansamu kudin zuwa hajji ba, ina rokon Allah ubangijin kowa da komai, yanda nafara wannan rubutun lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya, Hmmm Alhmdulillah masoya masu son karuwata gasky ba Abinda zance muku sai godiya da fatan Rabbi ya bar kauna, tunban furta littafin na kudi bane wasu har Sunfara biya wasu kuwa suna jira infara posting su biya, Allahu yasaka muku da Aljannah ya"

"biya dukkan bukatunku na Alkhairi, one love Real fans*"

*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*



"Wani tsoho ne a tsugune ya zubawa wasu Y'an mata guda biyu idanu, dayar zatayi kimanin shekara Ashirin da biyu, sai kuma karamar mai kimanin shekara sha bakwai, gefe daya kuma wani matashi ne wanda kana gani shine Babba a cikin su ga mahaifiyar su na sharar kwalla da gefen zanin ta,"

"""Hajara yanzu bazaki iya yiwa mahaifinki BIYAYYA ba a rayuwar nan duk da bamuda Arziki amma, yana iya bakin kokarin shi ganin ya kyautata wa rayuwar ku, ya muku duk Abinda uba"

"nagari zaiyi wa ya'yan shi domin ganin rayuwar su ta inganta,"

"Cikeda rashin kunya da kuma nuna tsantsar rashin tsoro tace "" yanzu don girman Allah a rasa wadda za a Aurawa naka sasshe sai ni, saboda uban shi yagan mu talakawa, sai kuma ya lallaba ka kawai ka bashi yarka, wallahi bazan Aure shiba, cikin taushin murya da kwantar da kai yace ""haba Ummi yanzu ke bazaki iya taimako na ba ki fitarda ni kunya? Kinsani duk wani cigaban ku da nawa sanadin bawan Allah nan ne ya mun komai a duniya batareda mun hada Alaka ta jini ba, tundaga kan ilimin ku gashi yanzu yayan ku na bautar kasa ke kina 200 level kanwar ki na final year a secondary wallahi Ummi idan ban sharewa bawan Allah nan hawaye"

"ba na zama butulu,"

"""Wallahi baba tunda Allah ya nufe mu da karatun zamuyi koda taimakon shi ko babu zamuyi,"

"nidai bazan Aure shiba, ka bashi hakuri ya nema wani gidan,"

"Karamar ce dake kallon Y'ar uwar tata na kelaya rashin mutunci tace ""kai yaya Hajara yanzu kina kallon su baba na miki kuka saboda ki rufa musu Asiri fir Amma shedan na miki hudubar tsiya ko,"

"Hannu ta daga zata masgeta, yayan su namiji dake a fusace yace ""wallahi daina ganin baba yace kar in tabaki, Amma kina tabata Saina nakasa ki kema, ba kina kiran wani naka sasshe ba, HAJARA kibi A hankali duniya ce kina ya' mace Y'ar talaka Amma ego dinki yafi karfin ki a rayuwa,"

"""Wallahi kitabamin ya' kigani yayanku zanba umarni ya lallasa min ke, Malam kaga Y'ar son taka ko kaga diyar da kasha duk wata wahalar rayuwa saboda ita ko?"

"Tsohon da kana gani kasan rayuwar shi bai dauki komai da zafi ba yace ""RAHAMA, ki tayani"

"lallaba Y'ar uwar ki kinji kuje ciki Allah ya ma Rayuwar ku Albarka kinji,"

"Fuuuu HAJARA ta mike ta wuce d'an karamin dakin su dake tsakiyar gidan,"

"Kanwar ta ce ta kalli baban su"" baba kayi hakuri zata Amince insha Allahu, zan tayaka rokonta, ""To RAHAMA, Allah ya Albarkace ku kinji, Ameen ta Amsa ta wuce cikin dakin itama,"

"Kafin ya juya cikin natsuwa ya kalli D'anshi namiji da yayi shiru kana ganin shi kasan a zuciye yake,"

"""Gadanga kusar yaki, kayi hakuri kaji da halin Y'ar uwar ku, ka zama uba kazamo namiji ako da yaushe da zai tsaya akan Y'an Uwan shi, kaine Babba kaine gatansu,"

"Ko bana raye kaine zaka zamo jigo a rayuwar gidan nan, don haka tashi kaje Allah ya maka"

"Albarka kaji,"

"Wasu irin hawayen tausayin mahaifin shi ne ya lullube shi, ganin yanda yake fama dasu tsawon rayuwar su ya tsaya musu akan komai da wahalar neman shi har zuwa yau, ji yake dama shi mace ne da yau ya rufawa Mahaifin su Asiri ya Auri zabin shi, mikewa kawai yayi yabar gidan, Bai iya kara cewa komai ba, Amma Addu'a yake Allah ya sa baban ya fita sai ya lallasa ta a"

"gidan ko ya rage takaici,"

"Mikewa inna ma tayi zata wuce, yace "" zauna matar Aljannah uwargidana ta gari, komawa tayi ta zauna domin bata iya yimai gardama ko kadan,"

"Share sauran kwallar tayi ""malam sanyin ka yayi yawa,"

"Dariya yayi kamar bakomai a ranshi yace "" so kike inrika daukar zafi a cikin rayuwar da bamai dorewa bace larai, ki taya ya'yan ki da Addu'a ko mutuncin su kawai da suke tsarewa wani Abu ne bakya ganin tsananin mu zai iya janyo fadawar ta cikin hadari? Banason ta yi tunanin zanyi mata Auren dole, larai so nake ta yarda, yanda hankalina zai kwanta ko bayan Auren, Amma in mun tilasta ta"

"Anyi wane riba zamu samu yaron da baida lafiya tun tashin shi,"

"""Malam tuntuni nakejin kana maganar rashin lafiyar shi, wai Meke damun shi ne? Larai Addinin"

"mu yayi hani ga tsananin bincike, kada musulmi ya tsawaita bincike, Allah yagani tun yaron na karami mahaifin shi yafada min yasamu nak'asu suka fitar dashi kasar waje, bankuma taba binciken komai akai ba, yasha fadamin har yanzu yaron bawai ya samu lafiya bane, kuma kanin"

"shi ma yayi Aure tuntuni harda yara biyu shine dai ya rage saboda lalurar dake damun shi,"

"Rokona yayi a karon farko, yace min ""malam bala ina neman Alfarmar ka bani Y'ar ka Babba domin nasan ta mallaki hankalin ta zata iya rayuwa da shi, bazan iya watsa mai kasa a idoba tsawon shekaru yana min hidima bai taba gajiyawa ba sai yanzu kawai rana daya ya roki Abu guda daya kacal a wurina in kasa yimai, bazan iya ba larai,"

"""Gaskiya Alhaji Shu'ibu mutum ne mai karamci da mutunci ya fi karfin komai kam a wurinka,"

"""Kingani don haka ki tayani lallaba Y'ar ki larai, yafada cikin barkwanci, "" zan yi iya bakin kokari na insha Allahu malam,"

"A can cikin dakin kuwa RAHAMA ce ta dauki Quranin ta ta zauna gefen Y'ar uwar ta kan y'ar madai daiciyar katifar su dake kasan dakin, cikin kwantar da murya tace "" yaya HAJARA don soyayyar ki da manzon tsira kiyi BIYAYYA, zaburowa tayi, a fusace, ""wallahi kar inkuma jin muryar ki a dakin nan da sunan waike kina min zancen Auren da bazan taba yarda da shiba, zan naka d'a miki na jaki wallahi, ""shegiya mai kirar takand'a ke kije ki Aure shi mana, ""Haba yaya ai bazai yuwu ace kina gida ni inyi Aure ba,"

"Shekara nawa ke tsakanin mu? Kusan Biyar fa, kuma kinsani kece kikafi cancantar Auren yanzu you are not getting younger everyday,"

"Jifarta tayi da wani robar cream ta kauce tareda kara rungumar Qur'an nin ta da kyau, tace """

"uwarki ce ta ke tsufa baniba shegiya Y'ar iya yi iyami masu kunu da ruwan sanyi,"

""" keni yanzu da ajina da ilimi na inkare a Auren naka sasshe Wallahi ni ko ubanshi dakeda kudin bazan Aureshi ba, d'an kudin su da bai wuce cikin cokali ba, wane Arziki gare su wa yasan da su a duk fadin garin nan ma,"

"Ke baby mijin HAJARA na nan zuwa zanba kowa mamaki mijina sai an share titin layin nan motar shi zata shigo,"

"Kallon kanki ya tabu kawai RAHAMA ke mata, ganin yayar tata ta zauce kar itama ta biye mata"

"su zama daya yasa ta bude Qur anin ta fara tilawa cikin natsuwa,"

WAYE MALAM BALA?

"D'an Asalin garin jega ne dake jahar kebbi, neman kudi ya shigo dashi cikin babban birnin na"

"sokoto, ta sanadiyar sana'ar Albasa, tun yana saurayi har ya samu jari yayi Aure da wahalar"

"neman shi domin Almajirine tun yana karami iyayen shi suka kawo shi karatu wurin malamin shi, sai kuma Allah ya dauki ransu, malamin ya rikeshi tareda bashi kulawa har ya koyamai yanda zaiyi sana'a tun yana saro Albasa a cikin garin Alero yana siyar aa jega har ya fara zuwa sokoto da sana'ar ta mike,"

"Sanadiyar shigar shi sokoto ya bashi damar koyan karatun Boko kadan bamai zurfi ba domin ya lura komai na rayuwa saida ilimin nasara kake samun cigaba, koda kanada na Addini, a harkar"

"kasuwanci kana bukatar na zamani,"

"Yayi Aure da uwar ya'yan shi larai da ta kasance Y'ar uban rikon shi wato malamin shi, a lokacin ya dawo da zama cikin garin na sokoto, ya kama gidan haya a cikin Unguwar mabera gidane na kasa madaidaici,"

"Suna tafiyarda rayuwar su cikin sauki kasancewar itama larai macece mai biyayya da hakuri, har lokacin da ta haifi d'an su na farko Aliyu, rayuwa ta fara musu zafi lokacin da ta kuma haihuwar Y'ar su ta biyu, domin rayuwar HAJARA daban ce tun tana karama komai ta gani sai ta damu baban ta tanaso, haka yake fafutuka ya nemo mata, domin Allah ya dora mai kaunar"

"HAJARA wadda yasakawa sunan mahaifiyar shi,"

"Lokacin da ta isa shiga school kuwa tana shekara shida aka fara kokarin sakata makarantar gwamnati kamar yanda d'an uwanta ke zuwa, Amma fur taki tace wata makarantar kudi dake Unguwar su ita take so wanda a lokacin gaba daya sai ya Tara cinikin wata biyu na Albasar shi"

"zai hada kudin makarantar, kuma ga hidimar gida gata sutura,"

"Dole ya fara fafutukar neman canjin sana'a domin cikawa Y'ar shi burinta,"

"Amma Abu ya gagara, ranar yana zaune a bakin titin da yake kasa Albasar shi , wata katuwar crv ta faka,"

Ya tashi da Sauri ya nufi motar don ya saba da mutumin yana mai ciniki sosai don sai yasai

"kwando ma wata rana, mutumin kuma yana mai kyauta,"

"Fitowa mutumin yayi cikin shigar Alfarma irin ta wa inda suka jik'a da naira ya gyara madubin idanun shi ya mikawa malam bala hannu ba kyama, cikin ladabi ya rusuna sukayi musabaha, tareda tanbayar shi yau kwando za akawo ko rabi?"

"""Muje inuwarka muyi magana malam bala taimako nake nema Allah yasa ka Amince,"

"""Bismillah Alhaji, ya bashi bencin da yake zama, ya ko zauna, tareda fuskantar shi,"

"""Dama Alfarmar itace, ina son ka Ajiye wannan sana'ar kazo muyi aiki tare idan Badamuwa ka zamo driver na akoda yaushe, zan rika biyanka Albashi mai tsoka,shiru malam bala yayi, Alhaji shuaibu yace"" nawa ne ribar Albasar ka a kullum?"

"Shiru yayi nadan lokaci yana nazari kafin yace a kullum ina iya samun ribar dubu biyu, idan na siyarda ta dubu goma inkuma kasuwar tayi kasa bai wuce ma insamu Dari Biyar a rana wata rana har Dari biyu,"

"Kaga in za ayi cefane ma wata rana sai mun shiga cikin uwar kudin ma,"

"""Toh karka damu, yanzu dai zan hadaka da wani yaro na ya koya maka mota nan da sati biyu in kana da kai zaka kware da Y'ar dar Allah, ya ciro katin address din shi ya bashi yace ya same shi a gidan shi dake tamaje quarters,"

"Yayi godiya sosai, domin yana matukar bukatar canjin sana'ar domin wata rana ma Albasar tafka hasara yake musamman lokacin zafi taita rubewa,"

"Suka rabu A ranar da tsantsar farin ciki ya koma gidan shi, ya fadawa inna larai,"

"Tace ""malam zaka iya kuwa? ""Insha Allahu larai ki tayani Addu'a kinga HAJARA nakeso insaka ta makarantar da takeso HAJARA ta nason hutu larai ina son ta huta,"

"Murmushi tayi tareda kallon Y'ar karamar yarta RAHAMA dake wasan ta a lokacin, bata wuce shekara daya ba, tace to ""ya' tafa? ""Dukan su in Allah ya Y'ar da zasuji dadi, to Allah ya bamu"

"Alkhairi malam Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a, ya Amsa da Ameen,"

Alhmdulillah cikin watanni kadan rayuwar su ta canja domin

"Domin Alhaji shuaibu mutum ne mai dattako da sanin darajar d'an Adam bayan Albashi harda hidimar kayan Abinci yi musu yakeyi,,"

"Don haka har Account malam bala ya bude yana adana kudin shi, domin siyan gidan kanshi, ana haka mai gidan da suke ciki yanemi su tashi zai siyar da gidan, Hankalin malam bala ya tashi domin ko rabin kudin gidan baida da ya siya don haka, dole yafara neman gidan haya domin tashi su bashi gidan ya siyar,"

"Ranar yaje wurin aikin shi yake neman izinin Alhaji shuaibu domin komawa gida da wuri ya nemi haya domin notice din da aka bashi ya kusa cika,"

Anan Alhaji shuaibu ya nemi yafada mai waye mai gidan?

"Ya fadamai yace ko yanada number shi ya Bashi, yace eh ya ciro Y'ar karamar Nokia dinshi ya duba ya bashi, atake ya kirashi yace mai Alhaji shuaibu ne mai dala yabo ai kuwa cikin tsananin girmamawa ya gaida shi, ya tanbaye shi ina yake yana son ganin shi, cikin rawar jiki yace Alhaji lafiya? ""No akan gidan kane da kakeson ka siyar na mabera so ina son siya,"

"Cikin rawar jiki yace ansiyar maka Alhaji duk da wani ya taya Amma kai nasiyar maka, domin duk garin sokoto yasan waye Alhaji shuaibu Mai dala yabo, domin ya shahara ta fagen daukaka"

"da taimakon Al Umma,"

"A ranar ya biya kudin gidan tareda mallakawa malam bala takardum yace mishi nashine halak malak, kuka malam bala yayi sosai saboda jin dadin yadda Allah ya kawo Alhaji shuaibu cikin rayuwar su, gaba daya rayuwar iyalin shi ta inganta sutura Abinci Abin batarwa, ga inna larai ma tana sana'oin ta a Unguwar ya gyare gidan tsab ya zama na zamani da ajiyar da yakeyi, gini ne mai tsakar gida dakuna guda hudu ne a tsakar gidan ciki daya daya, sai kitchen da bayan gida sai kuma bandaki na bayan gida dana wanka,"

"Tsakar gidan fes yake ya lailayu da suminti wanda suke wanke shi kaida kai kasan cewar inna larai mace mai tsafta,"

"Ba Abinda zasuce sai hamdala,"

"HAJARA na makarantar da takeso, har lokacin da RAHAMA ma ta isa itama aka jefata, rayuwar su sai hamdala, Aliyu har ya kammala secondary ya shiga d'an fodio university sokoto, Shekaru na tafiya cikin fik'irar ubangiji da kuma Y'ar dar shi, har Hajara ta shiga itama d'an fodio wanda da taimakon Alhaji shuaibu duk karatun su ke tafiya ba tangarda don kowa yasan karatun jami'a ba Abu ne mai sauki ba,"

"While RAHAMA na Ajin karshe a secondary,"

"HAJARA yarinya ce mai mugun girman kai da rashin kunya ga sangarta sam bata taba Ajiye kanta kusa ba don komai tagani duniya sai tasa malam bala ya siyeshi, shikuwa Allah ya dora mai sonta fiyeda Y'an Uwan ta yace MAMAN shi ce ita gata da sunan mahaifiyar shi gata suna kama, domin fara ce tas irin farin fulanin Asali tanada jikinta mulmule kamar mai rayuwa cikin kankara,"

"Kyakkyawar gaske ce tanada kyau a fuskar ta da laushin fata saidai batada cikar halittar ya mace ta gefen sura kirjin tama saitaga dama takesa musu brah a gida inzata fitane dai take Amfani da mai soso domin karawa halittar ta Armashi, sumar kanta kuwa batada tsawo sosai saidai inka kalleta zakayi tunanin tanada shi saboda yanda suma ke kwance saman goshinta, Tana rikita Maza gida da school domin HAJARA akwai daukar wanka da gayu,"

"Akwai wulakanci domin har yau taki tsaida kwakkwaran saurayi saboda dogon buri a rayuwar ta don ita bama ta hango kanta a gidan gwamna tafi hangota a president Villa, tana ikirarin ita fa matar manya ce, inna tayi tayi ta rage mugun hali taki,"

"While RAHAMA kuwa she is very cool girl bata cika magana ba gata chocolate color ce ita mai haske ba mai duhu ba irin color din nan mai wuyar samu, kallo daya idan kayi mata idan tana tareda HAJARA zakace she is ugly but wanda duk yasan ainihin sirrin kyau yasan tafi HAJARA sinadaran kyau, eye lashes dinta is natural gira lips everything about her is unique she is very cam girl and simple,"

"Fagen jiki kuwa she is slim but akwai body figure ainihin coca cola shape akwai k,asa dai dai"

"jikinta haka kirjinta a full da har suna damunta kuma irin masu bajewar nan ne saman kirji, that's why she is always in hijab to hide her body,"

"A fagen aikin gidan ma itace kan gaba duk aikin gidan shara girki wanke wanke har wankin kayan su da na HAJARA gata bata taba damuwa da rashin yin HAJARA ba,"

"Tasan duk yanda zata tafiyarda rayuwar ta tundaga boko har islamiyya,"

"Bata wasa domin tayi sauka yanzuma takai izu talatin a hadda,"

"Gashi yanzu Ana fama da zancen Auren HAJARA da d'an gidan Alhaji shuaibu,"

*******************

"Kamar koda yaushe ta tashi da wuri ta gyara ko ina tareda taya innar su hada Abin kari, ita ta dauki na yayan su ta kaimai dakin shi dake farkon shigowar sai ta dauki nasu, inna tace "" Y'ar uwar ki taki tashi ko? ""Eh inna nayi ta tashin ta taki,"

"""Allah ya shirya, ta fada tareda cewa "" kiyi ki shirya karkiyi latti kinji? ""To inna nama yi wanka"

"saura kaya kawai zansaka,"

"Tafada tareda matsawa gefen fanfo ta wanke jikinta tareda nufar dakin su ta shirya cikin uniform dinta da sukasha guga riga da wando da kuma hijabinta fes, HAJARA nata juyi haka ta shirya tayi tafiyar ta, kudin mashin ta leka dakin baban su ta karba,"

"Tafito cikin natsuwa take takunta, a gefen titi tafiya take tana kallon titin kozata samu kabu kabu amma shiru gashi zata makara, ganin ta yi tafiya mai nisa bata samu achaba ba taja ta tsaya sai motoci ne ke wucewa da gudun gaske kowa na saurin zuwa bakin aikin shi domin kasancewar ta safiya ce,"

"Bata Ankara ba taji kamar anyi fatali da ita gefen titi domin wani irin iska da batasan daga ina yataso ba,"

"Jinta kawai tayi akasa ga kafarta datake jinta kamar ta karye saboda faduwar da tayi, ganin mutane sun nufota tareda mata sannu wani saurayi ne dake wurin ya dagata, ""sannu kinji halin yaran manyan garinga kenan basuda mutunci saboda sunga sunada kuddi,"

"Kallon jikinta tayi sai yanzu ta fahimci fatali mota tayi da ita gefen titi, Ga farin hijabinta ya koma brown,"

Wani irin tukuki taji yataso mata yaza ayi taje school a haka?

"Wajen da taka motocin sun tsaya a jere guda uku kirar Mercedes Benz bakake wuluk, a bayan su An rubuta A Yabo 3 wanda take iya gani,"

"Ko motsi motacin basu kuma yiba,"

"Matashin nan yace kije gida ko in kaiki ga mashin dina kije a dubaki ina fatan bakiji ciwoba, Hawaye ta sharce ta girgiza kai, tareda cewa "" wancan ne ya bugeni? ""Eh kiyi hakuri A yabo ne baida mutunci kyale shi yanzu duk wanda ya nemi zuwa kusa dashi zai sha wulakanci, ""Saboda shi waye tafada cikeda jin haushi shine mutum na farko da taji tana burin fadawa"

"magana domin yasan d'an Adam nada baiwa da daraja,"

"Jan kafarta ta farayi duk da tana mata zugI ta nufi wurin motocin, ko glass din su bakake ne wuluk baka ganin kowa a ciki ta bayan ta kwankwasa, drivern ya sauke glass ""hajiya kiyi hakuri oga na wacccan motar and ki tafi kawai, tunda har yace mu tsaya aga lafiyarki tukuna kinga he care,"

"""Bala'i ta fada wato yafi karfin ma yafito yabada hakuri,"

"Nufar motar tayi ana karkije karkije ta ki sauraran driver da kuma wannan matashin, Kwankwasa kofar bayan tayi saida aka dauki kusan minti Biyar kafin Yabawa driver damar sauke glass din,"

"A hakimce yake cikin gedzner sky blue tana maiko, ya kishin gida kamar wani prince ko sarki,"

"idanun shi masu daukeda black eye glass ya rufe ruf,"

"Saida gaban ta ya fadi ganin irin haduwar gayen da kyanshi yayi matukar yin kyau da haduwa farine tass kamar balarabe ga kanshi nan nade da sumar da tasha gyara,"

"Cikin natsuwa da sanyin muryarta tafara magana bayan ta tattaro natsuwar ta da kuma jarumta, ""Bawan Allah kabi a hankali ka kiyaye hakkin mutum kadaina daukar kanka wani kai bakowa"

bane a wurin ubangiji bace bawa dukkan mu daya muke bawanda yafi wani A wurin ubangiji

"face wanda yafi tsoron shi,"

"Don haka kadauki duniya da sauki ka cire girman kai,"

"Cikin natsuwa ya cire glass din idon shi da ya bayyana idanun shi masu matukar kwarjini da cikar haiba, ya bata wani disgusting look,"

"""How could you, impact how dere you show your ugly face to me? Yafada yana twisting bakinshi kamar dole who is your father by the way Y'ar gidan matsiya ta,"

"""Alhmdulillah ni ba yar kowa bace tafada cikin dacin rai domin kalaman shi is very hurt and"

"painful,"

"Amma nasan darajar d'an Adam sannan nasan mutuncin ubana Amma kai da bakasan darajar naka ba shiyasa kake kokarin tozarta nawa, bakomai kanka kayiwa bani ba zaka ga sakamako"

"kaje zaka gani, tafada tareda juyawa ta wuce yaron nan ya dauketa ya maida ita gida,"

"Tsawon rayuwar shi ba wanda yataba samun damar da wannan ugly face din ta samu a wurin shi shi A yabo wata kucaka ke zagi da cima mutunci, lallai sai yagano Y'ar gidan uban waye sai"

ya wulakanta iyayen ta da kuma tozarta su sai ya maida ita Abin kwatance cikin zafin rai yace ma driver drive and leave this nasty Area ... =ØŠÝ

*Matar Soja*

"2/28/21, 6:17 PM - Q: "

*ZANYI BIYAYYA*



*By FENERH*

"*Aslm ina mata masu sana'oi ko kasuwanci dake bukatar Ayi muku tallar kayan ku ta yanda zaku samu customers online, to ku garzayo domin kasuwancin ku ya bunkasa zamu tallata muku Hajarku domin samun cigaban kasuwancin ku,hajar ku zata zagaya ko ina ta fadin"

Arewacin Nigeria har ma da kasashen makotan mu*

"*munada lases masu inganci da kuma quality munada atamfofi na yayi da kuma shaddodi domin sabunta mai gida ku fito kuyi odar cikin farashi mai rahusa,akwai masu saukin kudi akwai kuma manya, ku fito kuyi tanadin sallah mata masu Aji, ance mai kwamin ido da wuri yake fara"

"kuka siyan nagari maida kudi gida, to place your oder just give us a call 0803 343 8895*"



"Wani irin zafafe ya fito daga cikin motar bayan anbude mai tangamemen ginin gidan na kalla, , dake cikin shahararriyar Unguwar nan ta masu hannu da shuni wato Tamaje quarters, shiga yayi yana Harbin iska saboda zuciya ji yake kamar ya kuma hada fuska da wannan yarinyar yau sai yasa an shaketa couse batada ma matsayin da zai bata hannun shi ya taba ta, ko Sallama kasan makoshi yayi shi bayan ya shiga falon, wata budurwa ce kyakkyawar gaske wadda kana ganin ta kasan kanwar shi ce, ta fara ganin shi ta ce ""yaya' matar dake zaune tayi saurin dagowa tace"" wane ya... Shiru tayi ganin zai wuce har yakai kofar wani part, tace ""kai, ba yanzu ka fitaba? Me kadawo yi? ""Momy please am hurting right now I can Answer your question please,"

"""Don't tell me rubbish my friend, dadyn ku na jiranka a office d'an iskan ci ka dawo,"

"Dawowa yayi ya zube kan royal chair din dake falon ya runtse idanun shi gam don baijin zai iya Amsa ta a yanzu,"

"""Ikon Allah, Husna kiramin lado inji, Meya faru?"

"Kafin ma ta rufe baki yayi sallama, drivern shi ne Amintacce,"

"""Lado Meke faruwa? Cikin natsuwa ya mata bayani tareda zube mai wayoyin shi da ya kawo mai,"

"Kallon shi tayi tareda zuba mai idanu, kafin ta zauna gefen shi ta dafa shi, ya bude idanun shi"

"da ke rufe sunyi mugun ja saboda zuciya,"

"""I pray ka canja hali, ""a haka za ayi maka Auren? Please change saboda karka cutar da Y'ar mutane Al Ameen,"

"Gyara zama yayi da kyau' no please momy ki roki Dady ya barni in nemi choice dina,"

"""A yaushe? How many times yake baka lokaci? Kodai Har yanzu baka samu lafiya ba ne? Shiru yayi bai iya bata Amsa ba ji yayi gaba daya walwalar shi ta Kara raguwa, duk da zafin da ya dakko ya ragu Amma wannan zancen Auren yafi komai daga mai hankali, wai shi za ayima Auren hadi? God wace mai tsautsayin ce?"

"Gyara zama yayi ya ce "" momy banda lafiya kunsani me

Please Login or Register in order to submit comment