You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ji yadda nake ji ba, ni kadai nake iya fahimtar kaina.
Bayan na sauka na ba shi dubu daya ya ba ni canji na nufi gate din dake bude na shiga, a lokacin ne wata motar ta iso kusa da gate din zata fice. Daidai saitin da nake tafiya mai motar ya tsayar ya sauke gilashin kasa.
“Noor kika ce min sai friday?”
Na kalleshi Abdull ne a cikin motar yana sanye da facing cap. Ban ce masa komai ba na nufi bangaren da Mama take. Ina tana kofar na jita a rufe na fara kwankwasawa.
“Bata nan fa ta fita”
Na juyo na kalleshi sai ya saka hannayensa aljihu ya cire hular kansa yana kallona.
“Sai dai ki shiga bangaren Hajiya”
“Aa ba sai na shiga ba, zan koma gida kawai”
Na fada ina mamakin Hajiyar mahaifiyarsa ce ta Safeena tsakanin shi da Safeena gidansu waye ne? Ko kuma shi da ita Yaya da kanwa ne oho.
“Okay Let me drop you off Girly”
Ban masa musu ba ya wuce gaba na bi bayansa har muka isa gurin motar na bude na shiga, shi ma ya shiga yaja motar muka fice daga gidan. Tafiyar kamar ta kurame haka ta zama bana cewa komai sai tunanin Zafeer nake da irin rayuwar da yake ta fada min zamu yi. Ban ankaro ba na ji hannunsa a cinyata yana shafa ni.
“Kin yi shiru baki cewa komai Noor”
Na yi saurin buge masa hannu.
“Miye haka?”
Sai yayi murmushi.
“I'm sorry daman ina gwadaki ne kawai”
“Gwada ni kamar yaya to see what?”
Asking with little bit of confuse.
“To see if you're wife material...”
“Sauke ni a nan”
Ya dube ni da sauri.
“A nan?”
“Eh a nan zan sauka”
“Ba gidanku ba ne ai”
“Na ce ka sauke ni a nan zan sauka”
Wata kila bakin hadarin da na hada a fuskata ya firgita, domin na daure fuskar sosai babu alamar wasa. A dole ya faka gefen titi ni kuma na bude na fita na bar masa motar a bude.
“Kin ga ni fa gwadaki ne kawai nake ba wani abu ba...”
Ban kula shi ba na cigaba da tafiya a kafa, ya so gwada bina a motar yana min magana da ya lura ba zan saurare shi ba kuma ba ni da niyar shiga motar sai ya motarsa yayi gaba. Tsaye nake ina jin kamar na fasa ihu na fadi na yi birgima a guri. Kusa da ni wata motar ta tsaya wannan karon ina ganin wanda ya fito motar sai na ji sabon kuka ya taso ni gaba, wani irin shagwaba da narkewa na fara yi kamar wata yar baby.
“Me ya faru? Me kike yi a nan?”
Ya tambaya tun kamin ya karasa fitowa daga motar, matsawa na yi kusa da inda ya faka motar ina kuka har da shessheka.
“Kareem...”
Ya kalleni hankali a tashe.
“Me ya kawo ki nan Noor waya taba ki?”
“Kowa ma taba ni yake...”
Ya kama hannuna ya ratsa da ni ta cikin wasu itatuwa da ke gurin muka shiga ta can ciki gurin da ke da sanyi da iska mai dadi, sakin hannuna yayi.
“Fada min me ya faru?”
Na daga kai na kalleshi kawai hawaye na sauko min. Cikin kwantar da murya da lallabawa ya ce
“Can i be your best friend?”
Na daga mishi kai.
“Okay daga yanzu na zama best friend dinki, yanzu fada min damuwarki”
I don't know why, how and when, i just find myself laying on his chest idanuwa na zubar da kwalla.
“Zafeer zai yi aure Kareem...”
Mun dauki 12-seconds a haka, ni da shi babu mai motsi kamar mun mutu, but zuciyata na bugawa da wani irin karfi kamar yadda nake jin tasa ma tana bugawa, sannan ya matsa baya hakan ya saka dole na dago daga jikinsa, he look straight into my eye ball ya ce.
“Noor ki daina saka turare mai yawa haka idan zaki fita, Haramun ne”
“Kai turaren ne damuwarka?”
“Saboda yana dagawa mutane irina hankali turare is my weakness, my weak point”
Ban gama fahimtar abun da yake fada ba, na ganshi slowly yayi kasa ya zauna akan turbaya ya nade kafafuwansa ya dago yana kallona.
“Zauna karanta min damuwarki, maybe zamu iya solving matsalar...”
Na zauna a gurin ina fuskantarsa da irin zaman da yayi.....
Na maida idanuwana kasa ina jin wani sabon kuka na tunkaro ni, ban sani ba raini ne ko kuma yarda ce ta saka nafi sakewa a kusa da Kareem ne kamar yadda nake sakewa da Zafeer sosai ko ma fiye da haka. Ina jin son fada masa damuwata ko da kuwa ba zai saurare ni ba, na kan ji kuka sosai idan ina kusa da shi musamman idan damuwa ta yi min yawa, tsabanin sauran mutane.
“Noor...”
Wata kila yanayin yadda ya kira sunana ne ya kara masa kwarjini a idona lokacin da na kalleshi.
“Ka rame, Kareem”
“Ke ma kin rame, ni da ke duk muna cikin damuwa mabanbanta, fada min taki”
“Ya aka yi kasan ina nan?”
Ya kalli gurin ya sake kallon ya sauke ajiyar zuciya.
“Na kan gwada zuwa nan yanzu, saboda ina jindadin gurin, bana son zaman office a yanzu saboda zaman yana tuna min da Hafiz, na kan zauna a nan na yi tunanin rayuwa, mafita, da kuma nazarin rayuwa”
Na sauke kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna.
“Ke waya kawo ki nan?”
“Wan...”
Sai kuma na kalleshi da saurin ina jin kamar na yi barin zance.
“Wani...? Wani? Har kin fara samari?”
“Ba saurayina ba ne...”
Na fada masa yadda alakar take.
“To me ya sa ya sauke ki a nan?”
“Taba ni yayi sai na ce ya sauke ni a nan”
“Taba ki?”
Na daga mishi kai.
“Ki yi taka tsantsan da zaman yanzu, okay”
Na daga mishi kai sannan na fara karanta masa damuwata. Na yi tsammanin zai taya ni bakinciki ne amman sai na ga mamaki karara a fuskarki.
“Amman Noor ke kika fara gudunsa, yanzu kuma ya samu mai son shi, so kishi kike ko kuma kina ganin kamar ya ci amanarki ba”
“Ban sani ba ina dai jin babu dadi, kuma hakan yana nuna kamar ya daina so na, zai yi rayuwa da wata ba ni ba”
“Sai hakuri, wata soyayyar bata nufin daurewa har abada, wata alakar kuma mai daurewa ce, ke dai ki yi addu'a duk abun da yake na kwarai mai alheri a gareki Allah ya tabbatar miki”
“Tohm”
Idona ya cika da hawaye, sai ya leko fuskata.
“Bayan wannan akwai wata damuwar?”
Na daga mishi kai, na fara fada masa yadda zaman gidamu ya dawo yanzu ni da Hana duk ba ma jindadinsa.
“So yanzu so kike na yi ma mahaifinku magana ko kuma Yaya?”
“Aa kawai dai na fada maka ne”
Yayi min murmushi yana kallona.
“Kin san na zama best friend dinki a yanzu zski fada min damuwar da bukatunki a duk lokacin da hakan ya taso, hakan ya miki?”
Na rausayar da kai Ina zane a kasa.
“Toh kai fada min damuwar kai ma a kana cikin matsaloli”
A take na ga murmushin dake fuskarsa ya gushe damuwata ta bayyana karara.
“I don't want to talk about this da ke? Ba zaki fahimta ba Noor”
“Zan fahimta mana, gashi kai ma ka fahimce ni kuma ina ganewa idan kana cikin damuwa”
Wannan karon dariya yayi.
“Tun mutuwar abokina ban yi hirar damuwata da kowa ba, kuma ban nemi shawarar kowa ba hakan kuma yana kara jefani a matsala”
“Toh fada min damuwarka a yanzu”
Na fada ina kallonsa da idanuwa kamar na yan fari. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.
“Wasu abubuwa na aikata da nake tsananin nadamarsu a yanzu, sai dai kuma na fi nadamar babban wanda shi ne silar dukan ukun”
“Fara fada min babban”
“Amincewa na auri macen da bana so bata so na, shi ne babban domin shi ya janyo kananan matsalolin”
Na kalleshi da duba mai kyau.
“Kana nufin ko da ka auri Yusura baka sonta bata sonka?”
Da mamaki yake kallona.
“Why Yusura kika sani ko na taba aure kamin ita?”
“Ban sani ba, amman ai ita ce na lura ba ku zaman lafiya, bata son ka, ko shiyasa kake cewa bata kishinka a baya?”
“Ashe kina da hankali Noor har kanki ya kawo wuta haka?”
Na yi murmushi.
“To miyasa ka aminta”
“Saboda Momy na ne, akwai wata budurwa da na yi a lokacin baya, mun so juna amman Momy ta ce ba zan aureta ba, saboda bata yarda da tarbiyarta ba, ita kuma a lokacin akwai wanda take so, amman a haka Momy ta gabatar mana da matsayarta, ni kuma ina tunanin babu hanyar sakawa iyaye sai biyayya a garesu, na amsa mata da na amince, ita kuma ta amsa da hakan saboda tana tsoron kar ace ta yi butulci bayan irin rikon da Momy ta yi mata tun tana karama har girma”
Ya dan yi shiru yana kallon wani gefe.
“A haka muke ta rayuwa a haka muka haihuwa haka muke har yau, kuma a haka zamu rayu a nan gaba, amman a yanzu abun yana ci na sosai”
“Ka fada min daya sauran uku..”
Ya dube ni with seriousness ya ce.
“Na aikata wani abun da yake hana ni sukuni a yanzu, zunubi ne mai girma”
Jin haka ya saka ni mamaki.
“Shirka kai yi?”
Ya girgiza kai alamar AA.
“Wani ka kashe?”
Ya girgiza min kai.
“Ko dan kana zubar da ciki?”
Nan ma kan ya sake girgizawa.
“Zina ka yi?”
Ya kalleni.
“Me yasa Zina ta zo miki a kai?”
“Saboda tana cikin manyan zunubai”
“Haka ne, gashi dafinta yana ta bibiyata”
“Ita ma Allah yana yafe ta, zunubi ne mai girma, amman malamai sun ce Allah yana yafewa idan an tuba da gaske”
“Na tuba da gaskiya, amman ina jin kamar akwai wani illa da na yi ma kaina akanta”
“Illar me?”
Yayi shiru tare da sauke kansa kasa.
“We shouldn't talk about this...”
“Safeena ce matar?”
Ya kalleni da sauri.
“Me yasa ita ta zo miki a rai?”
“Saboda na lura da tana kishina lokacin da take zaton ko akwai soyayyar a tsakaninmu, kuma ta zo gurinka ka tuna? Amman tana da aure ko?”
Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya daga min kai.
“Tana da aure kake tare da ita?”
“A da ba, amman yanzu na riga na daina, macen da mahaifiyata bata so, kuma abokina ya tsana yake ta kokarin ganin na guje mata amman hakan be samu ba sai bayan rayuwarsu it pain me, and tana da iyali ina da iyali be kamata muna haka ba, abaya duk ban gane haka ba sai bayan na rasa mutane masu muhimmanci”
“Da gaske ka daina?”
“Na daina saboda ba abu ne mai kyau ba, Na rantse da qur'ane da wanda ya aiko da shi da gaskiya na daina kuma ba zan sake ba, daman tun farko bana so kawai dai na biye sherin zuciya ne kuma bana son ta ga kamar da gaske na yaudareta ne na ki aurenta shiyasa na biye mata, amman yanzu Wallahi bata burge ni gaba daya”
“Indai da gaske ka yi nadama, Allah mai yafiya ne zai yafe maka, kuma ni ma zan yi ta rokon Allah ya yafe maka”
“Na gode”
Ya fada da murmushi a fuskarsa irin na wanda ke kokarin kore damuwa.
“Sai kuma nadamar me kake yi?”
“Na rashin amincewa da kudurin abokina kuma abun da zuciyata take ta muradi a yanzu”
“Akwai abun da Hafiz ya bukata baka masa ba?”
“Yeah, and yanzu ina bakincikin haka”
“Minene?”
“Ba zan iya fada miki ba”
Ya amsa min da sauri.
“Amman I'm your best friend”
“Na sani, amman ba zan iya maganar nan da ke ba”
“To fada min muradin zuciyarka”
Yayi murmushi ya mike tsaye.
“Noor kina ta min tambaya kamar wani karamin yaro”
Ya kalleni da sani irin duba, yayinda yake tsaye ni kuma nake zaune a gurin.
“Kin samu kaina sosai”
“Zauna Kareem”
Na bukata sai ya duba agogon hannunsa.
“Akwai inda ya kamata na tafi”
“Gurin budurwarka? Ita ce muradin zuciyar?”
Ya dawo ya zauna with shock.
“Ganinki ake kamar baki da wayo, amman kina da shi Noor yanzu na gani”
Na yi murmushi ina boye fuskata, shi ma murmushin yayi yana kallona.
“Ni dai fada min toh wata kake so?”
“Me yasa kike son ki sani?”
Na bude idon kuma na yi shiru.
“Akwai, akwai wacce nake jin tsananin sonta a yanzu, amman ina ajin kamar ita din mai tsabta ce ni kazami ne, saboda na aikata sabo a baya, da ban dauka ina sonta ba sai yanxu na san ina sonta, ina jin farinciki da farincikinta, ina damuwa da damuwarta, ina son kusanci da ita, amman ina tsoron yadda za'a kalli lamarin, domin na yi ma kaina illa tun farko na gujewa shawarar makusanci na, but i feel guilty, I'm hopeless”
“Kana sonta sosai?”
Ya rutse idonsa da wani farin ruwa ya fara taruwa a ciki.
“Kamar yadda kake son Safeena?”
“Fiye, kaunarta rayuwata ce, ina sonta irin son da nake jin ita kadai ce bukatar da ta rage min a duniya yanzu, ina sonta irin son da nake jin da za'a raba ni da komai a yanzu a bar ni da ita ba zan ji komai ba, she's my last hope ina jin kamar aurenta ne zai yaye min damuwata kuma zai saka na fahimci waye ni”
Tausayinsa ya kama ni, as well as nake jin wani abu marar dadi yana zagaye kirjina.
“Kareem”
Na kai hannu na gafen fuskarsa zan yi masa magana irin wadda ban taba zama da wani na bashi irinta ba.
“Lokacin da nake tafiya makaranta, Malamin ya taba fada mana cewa Allah yafe yafe ko wane laifi amman ban da shirka, kai kuma ba shirka ka aikata ba, Allah zai yafe maka, kai mutumen kirki ne mai taimako mai juriya, saboda Yusura bata son ka kar ya karya maka guiwa ka ji cewar kamar wata ba zata so ka ba, kana da kyau kana da kudi kana da hankali, kuma dan ka aikata sabo kar ya hana ka ganin kamar ba zaka dace da rahamar Allah ba, ance babu mai yanke kauna daga rahamar Allah sai batattu, Kareem indai ka tuba da gaske zaka dace there's no need to feel guilty about it, kawai ka aureta”
Ina masa maganar yana juya fuskarsa a hankali a tafin hannuna da yake kuncinsa na dama, sai da ya shinshina hannuna sannan ya bude idonsa ya mike tsaye.
“Kin karfafa min guiwa, thank you”
“Yanzu ka yi min alkawari ba zaka bari yarinya ka guje maka ba? Zaka aureta?”
Ya tsaya kallona har na mike tsaye na sake fada.
“Ka yi min alkawarin Kareem, ina sonka da farinciki, bana son na ji kana damuwa kuma indai har ka samu wanda kake so a yanzu be kamata ka bari ta maka nisa ba ko be kamata ka yi ta zama a haka da bakinciki ba, ina son ka yi aure ko dan matarka muguwa, kuma zaka samu farinciki idan ka auri wanda kake so”
Ya miko min karamin yatsansa yana kallon kwayar idona.
“I pinky promise you zan aureta”
Na ji dadi domin har ga Allah ina son Kareem da farinciki. Ina jin damuwa da matsalar ko da kuwa be fada min ba. Na lakam yatsan ina dariya sannan na yi gaba ina tsalle da dariya har da daga hannuna sama ina jin wani irin farinciki.
Kallona kawai yake yana murmushi har muka fito daga gurin.
“Noor ga wannan ki hau Napep, I'm sorry ba zan iya kai ki gida ba yanzu, dole sai kin yi taka tsantsan da rayuwa, saboda mutane za su saka miki ido kuma kin san waye mahaifinki”
Ya miko min 5k. Na karba na cire 1k na mayar masa da sauran.
“Yayi yawa wannan ya isa”
Ya karba ya rike yana kallona. Har na fara tafiya sai kuma na juyo ina murmushi jindadi da farinciki a fuska fal.
“Thank you so much Kareem you make me feel so special, wani be taba zama da ni ya fada min damuwarsa ba, ban taba bawa wani shawara ya dauka ba, ba a taba tsayawa an saurare ni kamar yadda kaka yi ba, ba a taba daukar kalamaina da muhimmanci ba sai kai, ban taba bawa wani shawara ya yarda ya dauka ba sai kai, ka saka na ji kaina a dabam, am felling so proud so good so happy”
Ina maganar ina shisshekar farinciki. Murmushi yayi min yana yawo da idonsaa fuskarsa.
“Your Welcome, My Best sweet friend, daman you're special mutane ne ba su gane ba”
Na yi dariya mai sauti ina tafiya baya baya kamar ba ni ba, gaba daya na manta da wata damuwar da bakinciki a lokacin har sai da na isa unguwarmu, sannan komai ya dawo min. Na yi mamakin ganin Abdull zaune a kofar gidanmu, ganina ya saka shi mikewa tsaye yana kallona har na karasa. Hade rai na yi na bata fuska sosai domin ban jidadin abun da yayi min a dazun ba.
Ina kokarin wuce na shiga gida ya sha gabana.
“Haba kyakkyawa wannan fushin na minene? Tun da na sauke ki a can na zo nan gidanku jiranki aka ce baki dawo ba”
“Me zan maka?”
Na tambaya fuska babu annuri.
“Hakuri zan baki na abun da nake miki, kuma na fada miki gaskiyar abun da yake raina”
Na gyara tsayuwata.
“Uhmm”
“Zaki taimaka mu tafi gurin motata mu tsaya? Please”
Na kalli gurin da ya faka motar nesa da gidanmu. Na fara tafiya sai ya jera da ni yana tafiya har muka isa gurin motar ya fi ni tsaye sosai domin ya dara Kareem tsayi.
“Da farko dai zan fara da baki hakurin abub da ya faru, ba wai na yi da wata manufa ba, kawai gwadaki zan yi”
“Miye hujjarka na gwada ni toh?”
Ya sauke ajiyar zuciya ya cire facing cap din dake kansa.
“Noor gaskiya tun a lokacin da na fara ganinki a shopping mall, kin burge ni, natsuwarki kyaunki, farinki da kuma yadda kike da rashin jiki komai na ki yayi min, sai dai an samu akasi a lokacin kina tare da mijinki, sai dai damuwar da na sake yi dake bayan mutuwar mijinki a gidanmu, ya sake motso min da burina akanki, kin ga sanadi sai Allah yasa Alhaji ya auro mahaifiyarku gashi yanzu har ina magana dake, wata kila da ba zan ma san mijinki ya mutu ba”
Na kalleshi kawai domin ban gama fahimtarsa ba.
“Noor ba zan boye miki ba, ina son ki kuma ina son na aureki idan har Allah ya kaddara, kuma ni ba da wasa na zo ba, bana ma son a bata lokaci, har ga Allah ni dai kin yi min, ina son mace irinki kuma daman ina da burin kara aure saboda inda nake aiki ni kadai nake zaune a can matata kuma tana nan tare da yara, na kan dauki wata hudu uku ban zo ba, mahaifiyata ma tana son na kara aure amman dai ban ga wanda ta yi Sai a yanzu da na hadu da ke, babu wanda ta sace min zuciya ba sai ke”
Na nuna kaina.
“So na?”
“Eh, kuma idan kika bani dama zan tabbatar miki da gaske nake iyaye za su shiga maganar da yardar Allah, already ma na yi maganar ki da Mama, amman dai ban fada mata kudirina akanki ba tukuna”
“Ni ba aure zan yi ba yanxu, yaushe ma mijina ya rasu da zan sake yin aure?”
“Ke yarinya ce, karki cutar da kanki kuma ki cutar da masu kaunarki ki ce ba zaki yi aure ba sai nan gaba, wata kila nan gaba babu wanda zai kalle ki ya yi sha'awar aurenki komai yana da limit Noor, zai fi kyau dai ki yi shawara”
“Toh zan yi shawara”
Ita ce kawai amsar da na bashi na juyo ina tafiya, har na shiga gida ban juya na kalli inda yake ba. Ina shiga gidan na samu Baba a gida sai ya rufe ni da fadan batar da bokitan da na yi, Allah ya shiga lamarin dai be doke ni ba.
“Kuma gidan uban waye kika fito yanzu?”
“Gurin neman kayan na fito, kuma ban gansu ba”
Na fake da hakan domin ba ni da wata hanyar wanke kaina.
“To su kuma kudin da kika bata a ina kika samu?”
“Alhaji ne ya ba ni ranar da muka je gidan ni da Yaya gurin bankwana”
“Wane Alhaji”
“Mijin Mama”
Baba ya bude baki
“Har dubu goma?”
“Eh yace na hau Napep”
“Yanka kai yake ne ko kuma minene? Allah yasa ba jininki zai sha ba, dubu goma a take?”
“Mai kudi ne sosai Baba, gidan ma kowa da bangarensa”
Mtscheeeeeeee yaja dogon tsaki ya nufi gurin da buta take ya dauka ya shiga bandaki. Ni kuma na nufi dakinmu na shiga na zauna, ina tunawa da Mama ba san zaman gidan Baba be da dadi a gareta da mu, amman duk da haka ina jin kewarta kuma ina jin babu dadi idan na tuna a gidan wani take rayuwa a yanzu ba gidan mahaifinmu ba.
Kamar an kare ni haka hankali ya tattara ya koma gurin zancen da na ji na auren da Zafeer zai yi, ko yana sonta kamar ni ko kuma dai shi ma zai aureta ne kamar yadda na auri Hafiz ba dan ina son shi ba. Ya yake a yanzu? Ya sauya rayuwa ya cireni a zuciyarsa ko kuma ina ciki? Tunaninsa ne ya karkato da ni na tuna da wunin yau dan karamin lokacin da Kareem ya ba ni kuma ya saurare ni ya yarda da zance.
“Allah ka yafe masa ka yaye masa damuwarsa kuma ka bashi abun da yake nema, macen da yake so Allah kasa ta so shi, yana da kirki sosai”
Har cikin zuciyata nake da masa addu'ar da kuma fatan dacewa da rayuwar da yake ta mafarki. Tun daga lokacin ban sake saka Kareem idona ba, shi ma be sake ganina ba, daman baya zuwa nemana sai da dalili yanzu kuma babu wannan dalilin, amman addu'ata tana tare da shi a kullum. Zuciyata kuma ta ki bari na huta da tunanin Zafeer da rayuwarsa, sai na yi ta hasashen irin zaman auren da zai yi da Amaryarsa she turn to be my enemy a yanzu.
Duk bayan kwana daya biyu sai Abdull ya zo gidanmu ya saka sallamo ni, a duk lokacin da yayi min sallama sai na fito mu gaisa ya ba ni tsaba ya tafi, tun ina kin karba har na saba idan ya ba ni dole na karba na shiga da shi gida. Kuma sai na lura Umma har farinciki take da zuwansa saboda baya zuwa hannu sake, yana yawan fada min labari akan rayuwarsa tsarinsa irin zamantakewar da yake da iyalinsa da kuma wanda zai yi idan ya aure.
Ni dai saurarensa kawai nake idan ya tambaye ni sai na ce masa har yanzu ina tunani ne ban gama yanke shawara ba. Ni da shi kuma muka taki sa'a duk zuwan da yake ba taba haduwa da Baba ba, ni kuma be taba zuwa ko aikowa kirana na Baba yana nan ballle ya tambaye ni alakata da shi.
It's Friday again ina zaune ina wanke wanke Baba ya fito da shirin na masallaci, farar shadda ce jikinsa da babbar riga sai hula da yake gyara tsayuwarta a kansa, kusa da ni ya karaso ya tsaya ina ganin haka na san akwai abun da zai fada, ko dai na yi wani abun ba daidai ba ya rufe da fada da zagi ko kuma umarni ne ga yin wani abun ko hani.
“Nooriya”
“Na'am Baba”
Na amsa ina jefa kwano a ruwan kumfa, sannan na juyo na kalleshi.
“Ko kina da wanda kike so?”
Na yi shiru na sauke kai kasa ina jin abun wani kala, domin be taba min irin wannan tambayar ba.
Na dauki lokaci a haka ina ta sake saken me zan fada, na yi karya na amsa ina da shi alhalin babu shi a yanzu? Ko kuma na fadi gaskiya na ce babu din?
“Toh na dai baki lokaci ki yi shawara nan da kwana biyu, idan akwai wanda kike so, to sai ki gabatar kar na gabatar miki ace na sake yin karan tsaye, idan kuma babu to ina son na hadaki da ďan yar'uwata Ridwan mahaifiyarsa ta yi min magana, kuma shi ma yayi min magana da kansa, amman Anty Larai tace sai idan babu kowa, zan tafi masallaci sai na dawo”
Na hade yawu da karfi na daga kai ina kallonsa har ya fice na kasa ce masa Allah ya tsare ko a dawo lafiya, Ridwan kuma? Wane irin Ridwan mutum mai mata biyu da yara tara ga kuma suruka duk a gida daya, gidan da ba wadatacce ba? A ciki zai aje ni ko kuma dabam? Ina ma zan iya zama da Ridwan. Gaba daya sai kasala ta kama ni tunanin ma na rasa wane zan yi.
Haka dai
Book Chapters
Chapter 30
Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54