gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading IG AJEEMAL Neman Mahaifi 1 & 2 By Oum AmReesh Chapter 9 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma sheda masu irin kaunar dasuke mata kamar ciki daya suka fito, kullum surutun su a school Nishan su,"

"se guraren magrib su Nisha suka nufi toilet yin wanka tareda alwala daya bayan daya, daga bisani masu yin sallah"

"sukatashi sukayi haramar alwala sukayi sallah wayanda suke fashi suna zaune suna danna wayoyinsu,"

"bayan ko yakammal ibadarsa yakuma yazauna, ganin haka yasa reeda tamike tafice, akokarinta nafita taci karo da"

"wacce suka kira domin tazu tamusu makeup, tareda mai tai maka mata agefenta tana rike da makeup kit a hanunta, nan tace musu sukarisa bari taje ta dawo,"

"jin haka yasa suka sakai suka nufi cikin bedroom din, ita kuwa reeda kitchen tanufa tayiwa barka magana kai musu"

"abun tabawa bedroom dinsu, nan baba Barka tasheda mata yanzu kowa, daga bisani reeda tajuya takoma ciki,"

"koda shigowar ta tasamu har anfarayiwa fadeela, nan itama tazauna dayar tashiga mata, Nisha kama tana daga"

"zaune saman bed suna hira da salma,"

"seda aka kammala wa fadeela, daga bisani Nisha tasakko aka shiga yimata, basu wani bata lokaciba abunka da"

"kwararro nan danan aka kammala musu duka,"

"fadeela ne tadauki kayanta tashige toilet domin tasa, because, dakin da mutane bazai yiyu su canza kayansuba,"

"ganin haka yasa reeda taja hanun Nisha suka nufi wani dakin domin canza kayansu suma, kuda isarsu dakin reeda ta"

"dauki nata kayan tayi toilet din cikin bedroom ne domin bawa Nisha daman shiryawa itama,"

"nan itama tashiga sari gan koda mamakinta dake kayan yashige , hakan nanufin takara gibane ko me, duk dacewa"

"shima telan bawai ya gwada taba bane ganinta kawai yayi,"

"kasan cewarsa kwararre shiyasa bai nemi gwadataba, gown din yadan matseta kadan, gaba daya shef dinta ya"

"bayyana masha Allah,"

"fareeda ne tafito idonta yasauka kan Nisha datayi tsaye tana kallon gown din jikinta, wow masha allah Nisha tsinkayi"

"muryan reeda, dagowa Nisha tayi tana kallon reeda data tsaya tana kallonta,"

"reeda matsowa tayi tana fadin,"" kai my lovely kiga yanda gown dinnan ta mashi jikinki kuwa gsky tamiki kyau sosai,"

"murmushi nisha tayi tana Fadin,"" nagode kema tamiki kyau ai, murmusawa reeda tayi tareda fadin,"" okay muje aima"

"dauri musamu mudanyi picture kafin motarcin dinner su suma zuwa,"

"ahankali Nisha take daga kafa, because yanda takejin kayan ya matseta dan haka setakeji kamar tsirara take, dan"

"gaba daya a tsarge take ita damuwartama karya barke mata cikin mutane aji kunya,"

"tundaga shigowar su nisha yan dakin suketa wow wow nikuwa nace,( baku suma wowba sema an kammala"

"kwaliyar,)"

"nan akashiga rangada musu dauri, kowacce da kallan daurinta, sunfito sunyi kyau dasu kai kace yan ukune masha"

"allah, gaba daya sae suka zama abun kallo, gani yanda suka fito sukayi kyau dasu kamar wasu taurari,"

"kuwa phone dinsa yadauka yashiga daukar su a photo, suna cikin daukar hutun ammi tashigo tana sanye cikin"

"kayaceccen shirnta mai kyau da ban shaawa sewani walwali take uwar angoba ,"

"masha allah abinda ammi tafadi kenan sanda idonta yasauka kan kyawawan taurarin yayanta 3 , ganinta da su"

"fadeela sukayi yasa sukayi kanta suna daga salfi,"

"seda tajira sungama daukan photon nasu daga bisani ammi taja hanun Nisha suna kokarin barin dakin, ganin haka"

"yasa su reeda fadin ,"" ammi ina kuma zakuje muna pictures , babu yanzun nan zata dawo,"

"Ammi na fadin haka taja nisha suka fita, upstairs ammi tanufa da Nisha, direct parlourn Daddy suka nufa yanda"

"manyan bakinta suke,"

"nan tashiga gabatar musu baby girl dinda take riko wacce ta basu labarin marainiyace, nan Nisha tashiga gaishesu"

"suka amsa cikin fara'a da sakin fiska, tareda mata fatan alkhari,"

"daga nan ammi tanufi bedroom dinta da Nisha, suna shiga tazaunar da Nisha saman sofa, tana fadin,""bari nazo,"

"juya ammi tayi tanufi bedside tabude tareda jawo wani kwalin kwaya, tanufo Nisha dashi,"

hanun Nisha taja tareda daura matar kwalin wayar iphone xr zaro ido Nisha tayi tana kallon kwalin wayar da ammi

"ta ajiye mata, daga bisani tamaida kallonta ga ammi, murmushi ammi tayi tana fadin,"""

"Kyautata agareki, na dade insu nabaki but nayi tunanin bari sekin fara zuwa school zaifi miki amfani, to, yau naga"

"ranace daya dace nabaki kema kidanyi walwala dashi, kuma naga kamar phone dinki ta dan tsufa bazakiyi wani walwala da ita sosaeba,"

"tsit tayi ganin Nisha ta sunkuya tana kokarin kuka, "" oh meyena kukan kuma kanasun bata kwalliyarki, ammi tafadi"

"tana tana tallafo ta tareda dan babuga bayanta alamar lallashi,"

"ammi nagode allah ubangiji yasaka miki da mafificin alkhari, narasa wani irin godiya zan miki, Nisha tafadi tana"

"sharce hawaye,"

"Nibanason wata godiya, kukan nakeso kibari, share hawayenta fiskarta tayi tana bin kwalin wayar da kallo, tana mai"

"jin dadi,"

"daga nan ammi taja janunta suka fito, daga nan suka rabu Nisha ammi ta koma parlourn Daddy Nisha tanufi"

"bedroom dinsu,"

"tana zuwa tashiga nunawa wasu salma da su fadeela kyautan waya da ammi tamata suka tayata murna, duk dasu"

"fadeela sunsan da zancen wayan su fada mata bane kwai sede taji surprised,"

"wuraren 8:30 motarcin angwaye suka shiga zarya cikin gdnsu kamal, manyan motoci na yayan manya, daga farkon"

"layi har kanshan layi,"

"dan haka masu haramar tafiya suka suma turoron shiga mota, already dangin amarya sunacan babban Hall din da"

aka kama dan gudanar da invent

"daga saman bene ta window su reeda suka lura da zuwan motocin dan haka , suka fara shirye shiryen fita, nan kowa"

"dake dakin yamike wasu suka fara fita, yarge daga Nisha se salma dasu fadeela, da fauzee, suma kokarin fitan suke"

"nan fareeda ta dauki handbags tazaro kudi tamikawa me makeup, taimusu godiya suka tafi, suma fitowa sukayi ,"

"tareda neman motar suna kokarin, shiga,"

"Su biyar ne kuma mutu hudene sukeda damar shiga motar because baza biyune agaba, mai driving se nagefensa,"

"fauzee ne tafara shiga daga bisani reeda tashige se fadeela tabi bayanta,"

"Nisha da salma tsayawa sukayi suna kallon juna, ganin haka Nisha ta kutsa salma ciki tana fadin,"" kishiga nibari na"

"shiga nabayanku, tana fadin haka tamayar musu dakofar tarufe,"

"su reeda sam basu ji dadiba suso sukasance atare, jin sunshiga mai driving din motar yayiwa motar key , nan"

"motocinda akwai mutane aciki suka suma tafi, ganin haka Nisha nufi wata rantsatsiya mota da nufin shiga,"

"budewa tayi mutum ukune ciki, hartasa kafa daniyar shiga taji anjawota da karfi, har seda tafara kokarin nemana"

"faduwa ,"

"daker Nisha ta daidaita tsayuwarta tana binta da kallo, bakowa bane da wannan aikin face raheela, tasha uban"

kwalliya yuwa aljana tana ta wani huci da kumburi

Khaleeseart Raeys

08105565439Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D8AO9ndEkrVIe0gZ1Q9GcP

IG AJEEMAL

Story and writing by Oum AmReesh

Free book

Page 21_22

gyara tsayuwa Nisha tayi tana cigaba da kallon raheela daga ita har zagada zagadan ham shakan matan guda biyu

"dake bayanta, """

"ina kike kokarin shiga heelah tafadi tana hararo Nisha, banganeba Nisha tafadi, dama bazaki ganeba, ina kikabar"

"aheel kike kokarin tafiya gayyar sudi, ban ganshiba nisha tafadi atakaice zuciyar ta na mata wani irin suya,"

to kisani ba inda zaki kije kinemu yaron nan because nasan ba inda zai shiga agdn nan se gurinki dan haka kikama

"hanya kiwuce kinemu munshi,"

"Nisha tariga tagane muguntan datakeson mata sutake kartaje wurin dinner nan, shiyasa take kokarin kawo wadan"

"nan zantukan,"

"but ita kuma tasa ranta azuwa wajan, dan haka cikin bacin rai Nisha tace, ,"" ni ban ganshiba kuma ba gurina yazoba,"

"kije kine mesa can inda yake, Nisha tafadi tareda kokarin matsawa tashige cikin motar,"

"cikin zafin nama da takaicin kalaman nisha agareta yasa raheela tafisgo Nisha tareda hankata baya dakarfi,"

"nan da nan Nisha tarintsa ido tareda sakin wani ihu tana neman faduwa, jin tafada jikin mutum yasa tayi saurin"

"gwalo ido tasauke kan goggo rabi da take tallafe da ita,"

"goggo rabi tsaida Nisha tayi ta tsaya dakatarta cak, daga bisani tayi kan raheela cikin bacin rai, tas kakeji tadauketa"

"da mari seda cingan dinda heelah keci yafado kasa,"

","" kaji min mutumiyar banza, yarinyar wofi, ni anya hankalinki daya kuwa, wannan wace irin bakar mugunta ne, kina"

"kokarin ilata yarinya, goggo rabi tafadi cikin fada da bacin rai,"

"goggo rabi juyawa tayi takalli Nisha daketa ta faman rau rau da ido tana shirin kuka,"

"matsawa goggo rabi tayi kusa da Nisha tareda janyuta jiki tana fadin,"" sorry karkiyi kuka kinjiko, tafadi tareda kokarin"

"kutsata cikin motar daza sushiga, daga bisani goggo rabi ma tashige,"

"nan da nan motacin biki suka suma yin reverse suna fita, daga compound din gdn because kowa yan biki angama"

"shiga,"

"Lallai fa haka fiskar ki tayi cheesepiet haka gdn nan da kowa zai iya bugu, friend din heelah tafadi tana tabe baki,"

"yayinda take sake kallon heelah tayi tsaye tana rike da kumatun ta, tana furzar da wani irin huci,"

tsabar takaici raheela takasa magana because irin wula kancin da goggo rabi tai mata sa hanu da tayi ta mareta

"agaban jiga jigan kawayenta,"

"Wani dugun kwafa tayi tareda ratsasu fuuuu tayi part dinta zuciyar ta na wani irin suya, ganin haka yasa suma kawan"

"nata suka rufa mata baya suka bita,"

"dinner da heelah bata samu zuwansa ba kenan,"

guri yayi guri taro yayi taro yan uwa da abokan arziki maza damata manya da yara ancika tam cikin babban Hall din

"dinda aka ta nada domin su,"

"Isuwarsu goggo rabi da Nisha kenan, nan sukashiga cikin hall din da sauran tawagar dasuke taredasu,"

Nisha tunda sukashiga se wul wul ga ido take tana kallon gurin irin kudinda aka narkawa wajan da kuma tsari da

"kyau da yayi,"

"Ahankali takebin wajan da kallo, idantane yasauka akan amarya nabilah da angonta kamal cikin kyakykyawar yanayi"

"tareda shiri mai daukan ido da hankali,"

"jitayi gaba daya wani abu yataba mata zuciya duk da itama batasan meyeba,"

"Jin anrungumuta yasa mind dinta yadawo jikinta, aheel ne rungume da ita yana washe mata baki, cikin murna da"

"daukin ganinshi yasa Nisha tadago shi tarun guneshi hade da masa wani cool kiss akuncinsa,"

"duk da tayi mamakin ganinshi anan saka makon mummyn da take nemansa, tambayar shi tashiga yi shida watso"

"nan, nan yasheda masa da grandma dinsa wato ammi, batakaiga sake maganba,"

Fareeda tazo taja janunta suka nufi inda suke zaune seat reeda tanunawa nisha nan tazauna tareda daura aheel

"acinyarta, gefe dasu kawayan nabilah yan rawar kai suna opposite da abokan kamal"

"goggo rabi dama tuni tashiga tawagar ammi tasamu guri tazauna,"

nanfa guri ya hargitse yakacame da nishadi

"daga abokan ango kama da amarya su fadeela anyi rawa kamar ba gobe, uwar amarya da ammin kamal se barin"

"dollars sukewa yayansu,"

"banda Nisha da salma dake zune suna kallo dama su ba gwanayen rawa bane,"

"anci ansha anyi rawa yanda yakamata anyi photo sosai, ango da amaryansa sun yanka cake sunbaiwa junansu,"

gefe guda kuwa wata matashiyar matace ke zaune daga daya daga cikin kujeran da su ammi ke zaune tana ta kokarin

"dealing wani nurmber amma shiru ba adaga ba,"

"ba kowa bace face mahaifiyar raheela Hajiya jumana, tana ta dealing numbern heelah yanata ringing but bata"

"daukaba, kuma tayi tsamanin ganita gurin dinner, but shiru haryanzu babu alamar zuwanta,"

"wani dan guntun tsaki taja tareda daukan handbag dinta tafice, but ba wanda yalura da fitarta, because ba wanda"

"hakalin sa ke gareta yana wajan bidirin da ake,"

"tana fita motarta tashige tareda yimata key tadau hanyar gdnsu reeda, sannu ahankali take tafiya harta karisu gdn a"

"gaggauce tayiwa hon, mai gadi yazo yabude mata geat tashigo tareda yin parking compound din gdn tafito tayi part din raheela cikin hanzari,"

"shiru parlourn yake se heelah data hango tana kwanta saman kafe kamar wata macecciya, cikin rudu da hanzari"

"takarisa gun raheela tana kiran sunanta,"

"muryan ummanta datajine yasa raheela ta mike daga kwanciyar da tayi still hanunta narike da kuncinta, nan da nan"

"raheela ta fashe da kuka tareda fadawa saman cinyar ummanta, """

"ke lafiyanki kuwa mai yasameki, hjy jumana ta tambaya, tana sake kallon ya daya tilonta, ganin ta rike da kumatun ta"

","

"ganin haka yasa ta matsar da hand din heelah daga kuncita, ganin yatsu biyar kwance kumatun ya daya tilonta yasa"

"ta waro ido tana fadin,"" kutumar uba , waya mike wannan aika aikar haka, fadamin wani shegenne,"

cikin sheshshekar kuka heelah tashiga bata labarin abunda yafaru tsakanita da nisha dakuma marin da goggo rabi tai

"mata agaban friend dinta, karya da gaskya duk ta hada tafadi,"

"wani zazzafan huci Hajiya jumana ta furzar tana fadin,"" lallai kuwa dama nasan arina yanda naga suke wani haba"

"haba da yarinyar, to sun tabo tsuliyar dodo yanzu akan wancen sha sha shan yarinyar har rabi ta iya daukan hanu tamareki?"

"wato bare yafi dan gd kenan, lallai zasu san sunshigo gunata musamman yarinyar nan , tunda ammi tazu tana wani"

"introducing dinta agurinmu, nidama tunda naga yarinyar bai ta kwanta min arai bane, kuma nasan bahaka banza tashigo gdn nan ba, harta samu karbuwa haka,"

"gashi ta dalilinta aka mari gudan jinina, to kuni da na haifeki yatsama ban taba gwada mikiba balle taba lafiyar"

"jikinki, hmmm ba komai tashi kizauna, umma tafadi,"

"seda suka zauna akujera, Hajiya jumana takalli heelah cikin tausayawa da takaici na marin ta da goggo rabi tayi,"

"janyuta tayi jikinta tana fadin,"" kiyi hakuri kikyalesu kuma kibarni dasu,"

"daga zuwar yarinya ana kokarin amayarmin da ya kamar ganga, nan gaba kuma bansan me zai faruba matsawar"

"wannan yarinyar tana gdn,"

"Ina mijin naki yake umma ta tambaya tana duban heelah, tashi tayi daga kwanciyar da tayi jikin umma tana"

"fadin,""baya nan yayi tafiya yau kwansa biyu,"

"Yaushe kenan zai dawo umma tasake tabaya, bansani because bai sanar da niba nikuma ban nemisaniba tunda bai"

"sanar daniba, heelah tafadi tana dan tura baki,"

"hmm wato de haryanzu yana nan da zafin kanshi da miskilanci, because bakida mahimmanci kinsan tafiyarshi da"

"dawowansa ne komai? umma tafadi,"

"nima bansaniba heelah tafadi atakaice, hmm yayi kyau wato kekuma ga shasha sha kizauna kina basa jiran daki da"

"yaronsa koh,"

"shiga agogo sarkin aiki ko bikin dan wansama baya gabasa, hmm zamu hadune, Hajiya jumana tafadi tareda mikewa"

"tana fadin,"""

"yanzude kitashi ki kimtsa nizan tafi zamuyi waya, daga nan tayi mata sallama tafita, tana fita tashiga motar ta"

"taimata key, maigadi yabude mata tasa kai tafice,"

"ban garan yan dinner kuwa guraren karfe 10:30 aka suma watsewa masu tafiya suka suma tafiya gdajensu, amarya"

"da kawaye da yan uwa tuni anwuce dasu gd jensu,"

"haka bangaren kamal yan uwa da abokan arziki kowa hankali ya tattara ya kuma gd,"

salma da fauzee da suran kawayan su fadeela tuni sunyi gaba because dama su basu wani dade wajanba suka tafi

"su fadeela motar kamal suka shiga , se motar dake tafe bayansu abokinsa md yana jansu ammi ,"

"sanu ahankali suke tafiya har allah yanufa suka iso, mai gadi yabude musu geat sukashigo tareda nufan compound"

"din gdn sukayi parking,"

"nan kowa yafo yanufi sashensu, because kowa yadibo gaji da bacci aidonshi,"

Kamal tsayawa yayi gun md seda sukayi sallama tareda yiwa md godiya har seda yaga fitanshi daga bisani shima

"yanufi nashi ban garan,"

Su Nisha suna shiga seda sukayi sallar isha dinda basuyiba daga bisani kowa yayi shiri cikin night dress daga bisani

"suka kwanta,"

"washe gari Friday da safe akashiga yin walima tareda saukan Allah Qur'ani mai girma, gd yasake cika da yan uwa da"

"abokan arziki,"

"bayan sakkowa daga sallahn jumma'a cikin masallaci aka daura auran KAMAL ABUBAKAR MUDIBBO BATURE, tareda"

"amaryarsa NABILAH MUHMMAD MODIBBO BATURE yan uwa da abokan arziki kowa ya samu halarta masallaci da aka daura auran ,"

"Da misalin karfe 4:30 motan angwaye suka shiga zarya gdnsu nabilah, domin daukota akaita gdnta na sunna,"

"goggo rabi da kanta tashiga ta dauko, tanata kukan rabuwa da mom dinta, mom nayi itama nabilah nayi haka suka"

"rabu abun ba Dadi, gwanin ban tausayi, nan aka kutsata cikin mota aka dauki hayar gdnsu kamal,"

"anan ban garan kamal aka sauketa tareda wasu kawayanta, masu dan debe mata kewa, duk da gdn yakasan ce ba"

"bakonta bane but yau setaji gdn yamata daban,"

"seta kasance tamkar bakowa, guraren magarib kawayeda suke tareda ita suka shiga yimata sallama suna watsewa"

"daya bayan daya, gashi parlourn ba kowa ita dayanta,"

"aban garan cikin gd kuwa nan ma gd yayi shiru duk yan barka kowa ya watse ya kama gd,"

"guraren karfe 8 su reeda zaune saman bed sunjeru kamar kifi gwan gwani suna latsa wayarsu, Nisha nadaga kwance"

"tana kallon picture dinsu da fadeela ta tura mata cikin new phone dinta,"

"goggo rabi ce tayi sallama tashigo tasamesu cikin yanayida sukeciki, jin mutsin shigowar goggo Rabi yasa suka"

"dakata da danne danne dasuke awayoyinsu, nisha kuwa ta tashi daga kwanciyar da take tazauna,"

"Goggo rabi, seda takallesu daya bayan daya daga bisani tasuma fadin, "" sako nazu nafada muku yayanku kamal yace"

"kunbar masa amarya ita kade, dan haka kubar duk abunda kuke kuje kutayata fira,"

Khaleeseart Raeys

08105565439 IG AJEEMAL

Story and writing by Oum AmReesh ( khaleeseart Raeys )

Free book

"Page 23, nabilah amarya tana can katafaren parlourn mijinta jikinta sanye cikin kayaceccen lulubi irin na amare,"

"sezuba kamshi take ,"

"Jin anbudu kofa hakan ya tabbatar mata da angonta kamal ne ya iso, dan haka cikin natsuwa tadago tana kallon"

"kofar domin ganin shigowar sa,"

"ga mamakinta setaga ashe su fadeela ne suka shigo daya nabin daya, bata kaiga karisa ganin shigowar su ba ,"

"nabilah tadukar da kai kasa tana sakin wani goron numfashi,"

"Amarya kina nan ke kadanki reeda tafadi tana tambayar nabilah yayinda take kokarin zama kusa da ita,"

"Gyada kai nabilah tayi tana murmushi batareda ta dago takallesu ba,har"

"friends din naki suntafi? nadauka zasu tsaya se ango yazo ae, fadeela tafadi tana yar dariya,"

"wannan karon nabilah dagowa tayi danufin magana , karaf idonta yasauka kan Nisha dake zaune takurawa guri guda"

"tana kallonsu,"

","

"Oh my God nabilah tafadi yayinda tamike tsaye tana kallon Nisha, itama Nisha mikewa tayi wacce duk taji jikinta yasuma bari, se yanzu idonta yayi tuzali dana nabilah,"

saka makon ko wajan dinner bawai ta ganetabane because irin ado da bride makeup datasha ba lallai tagane ainihin

"face din taba,"

"haka itama nabilah bata kula da Nisha wajan dinner ba because attention dinta baikai wajan Nisha ba, """

"meyakawo wannan stupid girl dinnan cikin gdn nan, ? nabilah tafadi tana kallon Nisha datayi tsaye hawaye na shirin"

"wanke mata face,"

""" Fareeda da fadeela sake baki sukayi suna kallon ikon Allah, but sun gagara cewa komai sun koma kasa gane meke"

"shirin faruwa, ahankali nabilah take matsawa kusa da Nisha tana kallon ta, duk da nisha tadan canza but hakan bazaisa nabilah tamance da face din yarinyar da tagansu tareda kamal gdn masaukin uncle dintaba,"

yarinyar da kamal harya iya daukan hanu ya wanke ta damari saboda tafita mahimmanci wani irin azabebben kishin

"yaturnike nabilah , because Allah yagani yanda take bala in son kamal da kuma kishinsa, tun ranar da idonta yagane mata Nisha da kamal sun kebanta hankalinta yakasa kwanciya takuma kasa mancewa da ranar,"

"Wani kukan kura nabilah tayi tareda yin hakan Nisha, Nisha naganin haka yasa tajuya da gudu tana kokarin fita daga"

"parlourn, aiko kafin tayi wani yunkuri nabilah ta janyo hand dinta takai hanu danufin marin face din Nisha, carab taji anrike hand dinta,"

"Kallon kamal tayi dake rike da hanunta yashiga tsakanisu da Nisha datayi kasa dakai tana sharce hawaye, gefensa"

"nadauke da md tareda muhaiseen dayazo tun farar safin da aka daura auran kamal,"

ganin yadan kamal ya rike hanunta gam yana binta da kallon cikin wata siga yasa nabilah tashiga kiciniyar kwace

"hand dinta danufi auwatar da abunda tayi niya because idonta yarufe,"

kamal kuwa yanda yaga nabilah na kokarin kaukawa dashi yasa cikin bacin rai yatureta gefe wanda hakan yasa

"tashiga tangal tagal tana neman faduwa, cikin hanzari kamal yarikota tareda daidaita mata tsayowa yana fadin,"" I'm sorry ba danufi nayiba, baikai ga karisa maganar ba nabilah tadukar dashi, tana fadin,"" ba hakurinka nakeda bukatan jiba , seda ta zame jikinta daga rikon dayayi mata daga bisani taja gefe guda tatsaya tana kallon Nisha tana fadin,"""

"meye dalilin zuwan yarinyar nan gdn nan, duk haduwar dakukeyi awaje ahakan bai wadatar ba seta biyoka har inda"

"kake tarabeka meye hadinka da ita da har take bibiyar rayuwarka haka, nabilah tafadi cikin kunar zuci, parlourn ne yadau shiro kamar bakowa cikinsa, su fadeela mamaki yagama cika kwakwalwarsu haka muhaiseen yakalli Nisha yakali nabilah gefe kuwa ya maida kallonsa ga kamal da nabeela ta tsaresa da ido, shimade yakasa gane inda"

"zantukansu ya dosa, shide yasan sanadin zaman yarinyar agdn kuma ya dade dajin labarin ta gurin reeda dakuma"

"goggo rabi wato mahaifiyar sa, md kuwa kai sunkuye because already dama yasan komai ,"

"kamal jan hanun nabilah yayi suka nufi sofa, zaunar da ita yayi shima kuma zaman yayi, kuma yiwa abokan tafiyarshi"

"md da muhaiseen tayin zama, yakuma kumarci su fadeela dasu zauna suma, banda Nisha datake tsaye kai sunkuye tana ta jan hanci,"" kizo kizauna kamal yafadi yana kallon Nisha datayi tsaye abun tausayi, gagara daga kafarta tayi shiyasa takasa matsawa tazauna, se reeda ne tamike daga zamar da tayi tanufi Nisha tareda rukota suka taho tazaunar da Nisha daga bisani itama tazauna, nabilah se bin Nisha take da wani mugun kallo, haka kamal shima Nishan yake kallo face dinta yayi jawur gwanin ban tausayi , daga bisani yamaida kallonsa ga nabilah da ta tsareshi da eyes, ahankali yasuma magana da cewa,"

niba abunda yake tsakani na da ita but bun dade da sanin juna hasalima akwai abubuwan da suka faru abaya wanda

"bawanda yasanda faruwanso,"

TUNABAYA***********

Wata kyakykyawar motar hadaddiya tsa daddiya write color takunna kai a million tana tasheka gudu bisa hanyar kan

"wata layi cikin wata anguwa, kai kace wanda yake tukin ba hankalisa yakeba,"

"Yammane lis gari yarufa yanayin gari na damuna, yayafine take diga dis dis, saka makon tsagaitawa da ruwa yayi,"

"Matasan yan matane guda biyu dake tafe suna tafiya suna fira , jikinsu sanye da inform hijab yarufe musu jiki kirib se dan sawayansu da ake hangowa cikin black socks, da alamar antashesu daga mkrnt suna kan hanyarsu takomawa gd,"

"duk da dan yayyafi dake hakan bai hanasu tafiya slowly yanda sukeba, da alama suna cikin nishadi a cikin firan"

"dasuke,"

"jin wani mahaukacin hon yasasu firgici yasa sukayi saurin watsewa junasu kowa yafara kokarin yin takansa, cikin"

"tsurita da rudu, daya tayi hanyar motar da take kokarin bi, jikake gauu, motar data tahu ta bugeta, duk da bawani bugeta yayi sosaeba because yalura da ita but yayi kokarin taka Burkin allah yariga da ya iko da tsautsayi yadan bugeta,"

"dasauri wacce suke tafiya tare tayi kan kawarta dake kwance tana duka salati tana kiran sunan ummynta , da Nisha"

"tana fadin tazu ta taimaka mata takaita gurin ummynta, wayyo namutuna, itama Nisha duka sallallami tashigayi , tana kiran sunan, salma"

"nanfa motar tafara yin reverse danufin cigaba da tafiya tabar gurin, oh my God meka aikata haka, kuma kake"

"kokarin tafiya kamar baka san kayiba? dayan yafadi yana kallon mai driving din, "" mekuwa nayi baka ganin ita tashigo gabana bawani bugeta nayibafa kawai tsoritace tayi tafadi, mai driving din yabashi amsa, yana kokarin cigaba da tafiya, cikin hazari dayan matashin ya taka Burkin motar tareda zare key yabude motar yafito, daga bisani yazagayo ya bude gdn gaba yafito da abokin tafiyar tasa, yatusa keyarsa zuwa ga gurinda yan yan matan ke tsugune

Please Login or Register in order to submit comment