google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group

WHATSAPP NO:+2349030159301






[3/1, 6:29 AM] Hayat: ________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_




*🤦🏽‍♀️ZAMANINMU🤦🏽‍♀️.*
_(HATTARA YAMMATA)_





*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*



*Wannan littafi kirkirarran labari ne, Banyishi dan cin zarafin wani ko wata ba.Nayi ne dan fadakarwa, ilimintarwa tare da nishadantarwa.idan yayi daidai da rayuwarka/ki to arashi ne.*

__*GODIYA*__
INA GODIYA GA ALLAH (S W A) DAYA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTATI,ALLAH KARA DADIN TSIRA GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S A W),DA ALAYENSA DA SAHABBAN AMEEN.


__~GARGADI~__
~BANYARDA~ ~WANI~ ~KO~ ~WATA~ ~YA~ ~JUYAMAN~ ~LITTAFI~ ~BA~ ~TARE~ ~DA~ ~AMINCEWA~ ~TA~ ~BA~, ~A~ ~KIYAYE.~

*SADAUKARWA*__
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI GA MAHAIFANA,
*MALAMA* *AMINA* *IDRIS*
*MALAM* *IDRIS* *BALAH* *MAI* *GORO*
ALLAH YAYIMAKA RAHAMA AMEEN.


*Ina Mika godiyata gareki* *uwar room KHADIJAH ADAM IDRIS* *(shalelen kainuwa)Allah yabar zuminci ameen.*
*God bless you my Aunty.*


بسم الله الرحمن الرحيم.




🅿️1

📝Yanayi ne na lokacin sanyi, garin yayi lif ba iska a keyi sosei ba amma yanayi ne mai dadi, domin sanyin baya ratsa jiki sosei.

Wata hadadiyar mota Naga tayi parking a harabar shagalinku 🏨 hotel , sai da a ka dau wurin 5 minute kamin naga an bude marfin motar tare da zuro kafa daya waje anan na gano kafar mace ce,saboda takalmin dana gani Mai tsiini sosei.


Harta fito daga motar waya takeyi,duk da banajin me take fada amma da alama tanajin dadin wayar,saboda irin smile din da yake kan fiskarta.

Doguwa ce sosei duk da takalmin kafarta ya Kara taimakawa wajan fitar da tsawonta,kananan kayane ajikinta bakin juns tare da farar tesheet ta dora bakar afterdress budadda tasa dan siririn mayafi akanta sai red din hand bag kalar takalminta duk da bana ganin fuskata sosei amma kirar jikinta Yana da kyau,domin bata da kiba Kuma ba ramammiya ce ba.


Rufe marfin motar tayi,ta nufi kofar da zata sadata da cikin hotel din.sai a sannan ta daina wayar tana tafiya a slow kaman wadda tasha wani abu.

A reseption ta tsaya, ta fara magana da Wanda yake akan kanta,ga dukkan alamu daki zata Kama saboda Naga ta ciro kudi daga cikin Jakarta ta mika,an bata keys tare da recite,saman matakalar benen dake baran hagu Naga ta nufa,,tabi wani dan sukuroto Mai tsayi,tana ta wuce dakuna daidai daki no 101 ta tsaya tare da sanya key jikin kofar ta bude...

Iska Naga ta firzar da ga bakinta,ta cilla jakar kan kujerar falon tare da cire dan gyalen data yane kanta da shi...

Tayi rigingine bisa doguwar kujera,hawaye nagani sunabin gefen fuskarta, wayarta ta dau Kara ta duba tare da cillar da ita kasan kafet.

Ta firta"BAZAN IYA BA" da karfi,ni kaina ta tsorata ni danjin karajin da tayi, ta Kara rushewa da kuka sosei.akalla ta dau tsawon 20 minutes tana kukannan,sai da ta gaji Dan kanta ta tashi ta dauki karamin galenta tana kokarin rufe kanta.

Bedroom din ta shiga ta nufi hanyar toilet bakin kofar ta tsaya Naga tayi addu'a ta shiga,fuskarta ta wanke tare da kuskure bakinta ta fito.


Tana dawowa falo wayanta ta Kara daukar Kara a karo na 2, dauka tayi ta kalli screen din wayan,da sauri ta furta na shiga uku hannunta daya akan kirjinta!!!

Oh my God !!!! Yaya Yasir yake kirana ? tayi saurin saka wayan a Jakarta tare da sanya takalminta cikin sauri ta fita daga dakin zuwa reseption,ta ce pls helf me ina sauri zan tafi ka rife rooms din ankirani yanzu emergency . Ya ce okey madam.

Cikin sauri kaman zata kifa ta bude motar ta shiga tare da Bata wuta tayi hanyar gida. tafiyar 5 minute ta kaita bakin gate din BARHIM masu gadin wurin Naga sun taso da uniforms a jikinsu Mai shigen kalar na sojoji, dayan ya ce " barka da dawowa madam. ta zuge gilas din motar ta ce " ka ga yaya YASIR ya dawo??? Eh hajiya ya shigo bada jimawa ba,, ok,

Dayan ya budemata gate ta shiga ciki da gudu tayi tafiya Mai dan nisa,ta wuce gidaje sosei Naga tayi horn a bakin wani gate milk color Mai gadin ya leko tare da ce wa "barka da zuwa hajiya.

'Yauwa baba'

"Ya budemata gate'

Ta samu wuri kusa da wata mota kirar benz,tayi parking.

Addu'a ta farayi kamin ta bude motar ta nufi hanyar shiga babban falon gidan .


A hankali ta daga coteing din falon tare da yin sallama kasa kasa idan ba kana kusa da ita sosei ba lallai ne kaji me ta ce ba, ba kowa a falon sai Karan fanka da sanyin A C da yake kadawa.

A hanakali ta sauke boyayyar ajiyar zuciya,tare da furta Alhamdlillah ta cire takalmin kafarta ta rike a hannuta.

Sadaf-Sadaf take tafiya ta nufi hanyar dakinta, anufinta na San ganin ta shige ba tare da tayi karo da kowa ba..

Da karfi ta ji ance "" DA GA INA KIKE MUNAFIKA"???

Ta tsorata sosei domin da zaka tsaga jikinta mawuyaci ne ka samu jini a ciki,,

bata juyo ba stel tananan tsaye kaman status.

Sai ji tayi alamar mutum Yana matsowa inda take,hakan yasa tayi kokarin rugawa domin tasan haduwarsu bazatayi kyau ba..
Tsalle daya yayi ya damkota, hakan yasa ta buga uban kara,saurin toshemata bakin yayi da tafin hannunsa,ya tsayar da ita da kafafunta tana sadda kanta kasa saboda bata so taga wannan idanun nashi masu Kama Dana mage.

ta tabbatar da sun hada ido ya gama kashemata jiki .

Ya ce "munafika dole kike sinne Kai saboda kin dawo da ga yawan banza shi ne zaki rinka sinnewa kaman wata mutuniyar kirki?,to yau sai kin fadamin daga gidan uban wa kike??.

Dan danan jikita yahau karkarwa Dan tasan yanzu yana iya dukanta.

Idona na runtse sosei,a hankali na furta SORRY.

Yatsun hannunshu ya sanya ya kamo habata ya kurawa fiskata ido sosei yaga ta Kara kyau a Yan kwanakin da yayi bai ganta ba,hawaye ya gani sun fara gangarowa ta kasan idannunta.

zuciyarshi ya ji ta fara yimashi zafi, ji yake kaman ya sanya harshe ya lashe,Amma yasan bazai iya ba saboda Yana kyankyaminta.

Dole ya Kama girmanshi kada yarinyarnan ta rainashi ..sakinta yayi tare da juyawa ya ce "kamin na dawo da ga masallaci ki gyaraman dakina yanzu"..ya fita da ga falon gaba daya.

Ajiyar zuciya na sauke da karfi,Nima na juya da gudu zuwa dakina .

Habata na taba daidai inda ya rike da hannunshi ,ji nake kaman yanzune ya rike wurin,na furta' mugu Allah ya taimakeni yau bai dukeni ba.MOMY naji tana kwalaman Kira a falo.

Na fito na durkusa
Kusa da kafafunta ,'momy gani.'

"Yaushe kika dawo"?

'Tun dazu na shigo',


Lokacin kina daki na shigo.'

"To yi sauri ki Kara gyarama yayanku part dinshi kamin ya dawo da ga masallaci" , 'tau MOMY daman ya fadaman dana shigo'

"Tau Allah yayimaki albarka"
Amen MOMYNA,na wuce part dinshi ina mita ni kadai.

Saboda zalinci saina gama Kannan inyi sallah,inaji ina gani lokacin sallah yayi,mugu kawai shi ai ya tafi yayi tashi ni Kuma ko oho?

Da haka na shiga, ba komai falon sai wani sanyi daya ratsa jikina alamun A C a kunne take.

Wurin kwas yake,hakanan nadan karayin goge-goge saboda kura .na wanke toilet tare da canza Bedsheedt na kunna turaran kanshi a dakin Dana toilet.

Na faffesa Air freshener,na zo kan miro ina gyara kayan da suke a Kai Naga wani dan karamin saban freim Mai kyau da rubutu manya da kanana a jiki, da ga sama an rubuta"" I REALLY LOVE YOU MY BEAUTIFUL DAMSEL"" da Manyan baki.
A tsakiyar freim din anyi zanan ❤️ a jikinshi an rubuta MY BEBYNAH.

Da ga kasanshi Kuma an rubuta "I NEVER FORGET YOU MY BEAUTIFUL DAMSEL "...

Dogon tsaki naja tare da furta "wannan ko wa ce banza ce zata so wannan Mai fuskar irin ta mugaye??

kafadata guda na dage alamar ko a jikina.
Na ajeshi tare da karasa aikina na fita lokacin tuni an idar da sallar mangari ba.

Komawata dakina wanka na shiga ,bayan na shirya nayi sallah tare da Addu'ar Allah yasa wannan mugun ya tafi gobe Kona samu sukuni.

Bayan sallar isha'i ina kokarin kwanciya naji cikina Yana kugi alamar Yana bukatar abinci.

Nasan ina fita zan ganshi a falo,gwamma kawai nasha moltina da donot na kwanta,hakan kukwa nayi na dauko wayana da take cikin jaka kirar kamfanin iPhone 7.

Sai a sannan Naga irin missed call din da Hasan yaman da Texs guda biyu


Na duba texs din farko kamar haka :haba bebyna kin yiman alkawari Amma nayita kiranki baki daga wayana ba?? Why zaki yiman haka bayan kinsan yanda na ke kwadayin na ga na kasance tare da ke?

Mtsssss na ja tsaki,shi wannan banzan matsalarshi kenan? to bazaka Kara ganina ba tunda zalimu ya zo,nasan bazai bari ko bakin gate naje ba ballantana cikin gari .

Nomber shi na Kira bugu 2 ana 3 yayi picking,ajiyar zuciya naji ya sauke, ya ce haba bebynah miyasa kike yiman haka? Eh?

Saida na danyi shiru kaman ina nazarin magananshi,kamin na ce 'wallahi Kai matsalata da Kai kenan' karinka yiman uziri Mana, kasan bada yin kaina nayi haka ba.

"Tau miyasa nayi ta Kiran wayanki Bakiyi picking ba"?

'wallahi ina zuwa Yaya YASIR ya kirani' Kuma na fadama duk lokacin daya kirani nasan ya shigo gari saboda ni yake fara tambaya daya diro garin KATSINA.

"Nifa wallahi bebynah wannan yayan naki bana sanshi Yana takuramaki"

'to ya zanyi sweety ? Ni kaina banaso Yana zauwa,idan ya tafi ji nake kaman karya dawo .

"Hmmm Allah ya kyauta"

Na amsa da 'Ameen'

Daganan mukaci gaba da firarmu ta soyayya,Yana furtaman kalamai masu dadi .

Da haka mukayi sallama, tare da yin agender zamu Kara haduwa idan Yaya YASIR ya tafi .

Na dauro Arwallah tareda yin addu'o'in kwanciya bacci na kwanta.


A bangaran Yaya YASIR kuwa bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i .

Darect part dinshi ya nufa Yana shiga gaba daya yaji falon yadau kanshi Mai dadi Wanda ya hade da iskan fanka dana A C hakan yasa yaji har idanunshi rufewa sukeyi basoda dadi .

A ranshi ya ce "wannan yarinya badai tsafta ba komai nata na dabanne.

Sauri yayi ya shirya cikin kananun kaya marassa nauyi ya nufi cikin gidan.

MOMY ya iske a falo tana kallon sunna tv,sai NUSAIBA tayi bacci akan cinyarta.

Yayi sallama tare da zama kasan kafet din kusa da kafafunta.

Ya ce "MOMY ina yini"
'lafiya Lau magaji' ya aiki?
"Aiki alhamdlillah MOMY"

"To Masha Allah,Allah ya taimaka"

'Amen'

"Momy kawo na Kai yarinyarnan daki kada tasa kafafuwanki suyi sanyi"

"A a kyaketa magaji' kada ta tashi, dakyar na samu tayi baccinnan yau rigimar takeji tunda aka daukota daga islamiyya ta hanani na huta"
"Jeka kan darning ka ci abincinka"

Tom momy ' ya nufi wurin cin abinci

MOMY ta ce "itama wannan dayar yar rigimar yau Bata fito dinner ba yanzu kuwa nasan tayi bacci"

Murmushi yayi Dan yasan *FARRAH* take nufi .

A hankali ya furta yar "rigimar *YASIR* "

Yaci gaba da zuba abincinshi,tuwon shinkafa ne miyar danyar kubewa taji naman sa da man shanu.

Saida ya idar ya daurayo hannunshi da bakinshi.

Sannan ya ce MOMY bari naje zan Dan karasa wasu ayyuka kamin na kwanta.

"Tau MAGAJI Allah ya tsahemu lafiya"

"Amen MOMY".

Yana kaunar MOMY sosei ,saboda yadda take bashi kulawa ga shi bai tabaji ta ambaci sunanshi ba, saboda shi ne da na farko a maza cikin familyn su duk Wanda suka girmeshi Mata ne.

Bayan ya koma part dinshi ya danyi wasu ayyuka a sistem dinshi kamin yayi Shirin bacci

*ASUBA TA GARI FARRAH & YASIR*

~DAGA~ ~ALKALAMIN~ ~AUTAH~.

*FOR* *COMMENT*
*OR* *CORRECTION* *08162385196*..
[3/1, 6:29 AM] Hayat: ________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_




*🤦🏽‍♀️ZAMANINMU🤦🏽‍♀️.*
_(HATTARA YAMMATA)_





*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*



*Wannan littafi kirkirarran labari ne, Banyishi dan cin zarafin wani ko wata ba.Nayi ne dan fadakarwa, ilimintarwa tare da nishadantarwa.idan yayi daidai da rayuwarka/ki to arashi ne.*

__*GODIYA*__
INA GODIYA GA ALLAH (S W A) DAYA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTATI,ALLAH KARA DADIN TSIRA GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S A W),DA ALAYENSA DA SAHABBAN AMEEN.


__~GARGADI~__
~BANYARDA~ ~WANI~ ~KO~ ~WATA~ ~YA~ ~JUYAMAN~ ~LITTAFI~ ~BA~ ~TARE~ ~DA~ ~AMINCEWA~ ~TA~ ~BA~, ~A~ ~KIYAYE~

*SADAUKARWA*

*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI GA MAHAIFANA* *MALAMA* *AMINA* *IDRIS*
*MALAM* *IDRIS* *BALAH* *MAI* *GORO* ALLAH YAYIMAKA RAHAMA AMEEN.


*Ina Mika godiyata garekitNUSHURZani KHADIJAH ADAM IDRIS* *(shalelen kainuwa)Allah yabar zuminci ameen.*
*God bless you my Aunty.*


بسم الله الرحمن الرحيم.




🅿️2

📝
Kiran sallar asubar farko akan kunnan FARRAH, tayi addu'ar tashi da ga bacci(ALLAHUMMA AHAYANA BA'AD MA AMAUTINA WA'ILAIHIN NUSHUR)
Ta tofa a tafin hannunta tare da shafawa a fuskarta zuwa kafafunta.

"Tasan yau aiki ne zata sha kaman me?" Gwamma ta fara da wuri.

Arwallah ta dauro ta shimfida prayermate,tare da dora Zan akan kayan baccinta,ta tayar da sallar nafila.

Bayan an tayar da sallah a masallaci,itama ta gabatar da tata,tayi sauran azikar dinta da addu'o'in safiya.

Ta nufi dakin MOMY,tayi knocking a bakin kofar.

MOMY ta ce "shigo".

Akan prayermate na taddata da qur'ani a hannunta tana tilawa.

Na durkuwa bisa kafet din dakin.
MOMY "Ina kwana"

"Lafiya Lau FARRAH"
"Jiya da daddare baki fito denner ba"?

"Eh wallahi MOMY na ji gajiya ne shiyasa nasha molt na kwanta".

"Tau kije ki fara aiki dukda yau weekend ne"

"Tau" MOMY na nufi kiching.

Cikin ikon Allah karfe 6:40 am na fara,Amma zuwa 8:00 am na gama hada soyayyar doya ,nayi yar miya ta danyun kayan miya.na hadamasu ruwan zafi a placks Wanda yaji danyar citta da kaninfari.

Kiching din na fara gyarawa fes,nakai kayan Kan dinning table.

Na Kara gyara falon,tare da kunna bunner ta turaren wuta,na nufi dakina Nima domin na shirya.

Sauri nakeyi na gyara gashina saboda Naga har karfe 10:01 yayi.

"Lallai na bata time ga rashin baccin safe,ni nasan na bani tunda wannan jalimun ya zo sai a slow.

Jinayi kaman motsin mutum a dakin,sosai na tsorata dukda safiya ce,na fara waige-waige sai Naga kaman mutum ya fita da ga dakin.

Nabi bayanshi da sauri banganshi ba saboda ya riga ya baceman.

Hakan yasa na karasa falon da gudu MOMY na hango a dinning table na fada kanta Ina mayar da numfashi dakyar.

"Ke lafiya kike neman kayar da ni"

Wallahi MOMY motsin mutum a dakina,na bani kada ya cutar da ni.

"Yi hakuri kin tsorata ne,Amma ba kowa a gidannan sai mu kadai".....

Sallamar shi ta katsemana maganar da mukeyi.

MOMY ta amsa sallamar .

Yana kokarin zama ya ce "MOMY Ina kwana"?

"Lafiya lau magaji"
Ya sanyi -sanyi ?

"Alhamdlillah sanyi ya fara wucewa".

"Ke lafiya kin fito Kai ba dankwali"??

"Ko ni zan gaisheki"? Yayi maganar tare da zuba mata manyan idanunshi .

Kokarin tashi nakeyi MOMY ta rikeni,ta na ce wa "kayimata hakuri a rude take wai motsi ta ji a dakinta shi ne ta fito da gudu"

"A boye ya sauke ajiyar zuciya ba tareda ya bari sun gani ba" a zuciyarshi ya ce "Allah ya taimakeni bata ganni ba yau da naji kunya"

"MOMY kyaleta tsoro ne kawai da ita"

"Ai na fadamata ta daina wannan tsoron ki rinka yawan addu'a duk lokacin da kikaji motsin kinji ko" tana gogeman hawayen fuskata.

Tau MOMY wallahi inayin addu'a.

"Jeki dauko dankwalinki ki zo muyi breakfast kinji"

Na tashi Ina kokarin sanya bant a kaina,na nufi dakina.

Bayanta yabi da kallo Yana mamakin yanda take juya hips kaman wata uwar mata.

A zuciyarshi ya ce "Dole inyi kokarin komawa gobe kamin DADY ya dawo".

Dawowarta ta zubama kowa abincinshi a lokacin NUSAIBA itama ta fito.

Sukaci gaba da yin breakfast .

Suna idarwa ya ce "BEBY daukoman key din motarki"

Ehm ...ah... YAYA wallahi

na fara inda-inda alamar Banda gaskiya. Da kyar na tattara sauran kalaman bakina,saboda yanda ya tsareni da ido.

MOMY na ganin haka ta kama hannun NUSAIBA suka koma falo .

Kara tsurewa nayi kafin nayi magana ya Kara ce wa "na Baki 2 minutes ki kawoman key din yanzu"

Cikin sanyin jiki na nufi daki,

Yabi bayanta da kallo kaman wani tsohon maye🤣🤣😜 ..

MOMY duk tana hangosu dukda Bata jin me yake cemata ta ga dai ta zunburi baki.
Tayi murmushi irin nasu na manya ta ce "MAGAJI kenen zanso inga karshen game dinnan.

Ina kawowa na doramashi Kan dinning din na ce "ga shi"Ina turo Baki.

Dauka yayi ,yayi hanyar fita ba tare daya kulani ba.

Ya ce" MOMY bari inje Goruba road wurin su UMMAH"

"Tau saika dawo Allah kiyaye"

Ya amsa da "Amin"

Nafi 3 minutes a tsaye saboda takaici daya isheni.

A raina na ce "wallahi wannan mutumin ya gama da ni Amma DADY zai dawo saina fadamashi".

MOMY ta ce "FARRAH zo nan"

Na karasa falon,kwantawa nayi jikinta na Dora kaina bisa cinyarta Ina turo baki.

Ta ce "FARRAH kiji tsoran Allah a duk inda kike,kada kiga bama ganinki ki ce zakiyi abida kika ga dama,tau ki sani Allah Yana ganinki.
Kinga dai auntynki HUSNAH lafiya Lau muka rabu da ita,dukda akwai banbancin ZAMANI a tsakaninku, Amma dan Allah Ina rokonki kada ki biyema rudin ZAMANINNAN ki zubar da tarbiyar da mukayimaki..

Ta dora da "YAYANKI Yana kaunarki shiyasa zakiga kaman yana takuramaki sai nan gaba zaki gane abinda yake nufi".

Nidai Ina jinta banyi magana ba saboda haushinshi nake ji.

A raina na ce "Shi idan ya tafi Abuja wa yasan me yake aikatawa",Amma idan yazonan sai ya rinka kalar muminai dan ace shi mutumin kirki ne.

Ai yanzu wannan ZAMANINAMU sai dai addu'a da fatan Allah ya Kara shiryamu..


"Maganar NUSAIBA ta dawo da ni da ga dogon tunannin dana Lula

Aunty FARRAH yaushe zamu je G R A,inaso inga khairat?


"Bansaniba uwar Yan gulma,bakina kallo wannan mugun ya amsheman key din motar ba ko hakuri Baki tsaya bashi ba.sai yanzu zaki dameni na kaimata rankwashi a kanta nayi dakina da gudu.

MOMY "ta ce Allah ya shiryamanke"yi hakuri AUTAH ta zonan ta rungumeta yarinya tana gunjin kuka.


Wayata na dauka saman mirror na bude whatsapp dina.

BILKISU ABBAS Naga tayiman magana nayimata replay tare da Jan tsaki,na ce "wallahi BILKISU kudai kun shiga uku kuna biyema zamani kuna abinda kukaga dama ko?

Ta ce "kedai FARRAH sakarai ce kina takura rayuwarki kinki bari kiji dadin rayuwa".kinga da ace ni ce ke Ai wlh da anga sharholiya,ga ki da kyau ga kudi Kuna da akwai Amma kina abu kaman wata yar kauye wannan ZAMANINAMU sai ana kara'in holewa 🤣.

"Nifa wallahi BILKISU bazaki gane ba ne,banaso diyana su aikata abinda na aikata wataran shiyasa Kuma ko yanzu saida MOMY tayiman nasiha mai shiga jiki".

Kuma kinsan wani abu ?

BILKISU : a a saikin fada.

"Duk lokacin danayi yunkurin hada wannan connection din sai ansamu matala".

BILKISU; Karki damu zan hadamaki Mai zafi akwai wani abokin Mubarak tun last time daya ganmu a school duk yabi ya dameni akan maganarki,Amma zanyimashi magana karki damu kawata gwamma kema ki shigo layi a dama dake 🤣🤣.

Ke nifa tsoro nake ji 😔🙄.

Karki wani damu dakin zama yar hannu shikenan.

Tau ba matsala zamu karayin magana,Amma sai idan zalimu ya tafi 😔.

Don't worry 🤣 kawata saina jiki.

Da ga haka na ajiye wayan tare da gyara kwanciyata Dan inaso nadanyi bacci kamin karfe 1 tayi.





✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

~DAGA~ ~ALKALAMIN~ ~AUTAH~.

*FOR* *COMMENT*
*OR* *CORRECTION* *08162385196*..
[3/1, 6:29 AM] Hayat: ________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_




*🤦🏽‍♀️ZAMANINMU🤦🏽‍♀️.*
_(HATTARA YANMATA)_





*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*



*Wannan littafi kirkirarran labari ne, Banyishi dan cin zarafin wani ko wata ba.Nayi ne dan fadakarwa, ilimintarwa tare da nishadantarwa.idan yayi daidai da rayuwarka/ki to arashi ne.*

__*GODIYA*__
INA GODIYA GA ALLAH (S W A) DAYA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTATI,ALLAH KARA DADIN TSIRA GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S A W),DA ALAYENSA DA SAHABBAN AMEEN.


__~GARGADI~__
~BANYARDA~ ~WANI~ ~KO~ ~WATA~ ~YA~ ~JUYAMAN~ ~LITTAFI~ ~BA~ ~TARE~ ~DA~ ~AMINCEWA~ ~TA~ ~BA~, ~A~ ~KIYAYE.~

*SADAUKARWA*__
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI GA MAHAIFANA,
*MALAMA* *AMINA* *IDRIS*
*MALAM* *IDRIS* *BALAH* *MAI* *GORO*
ALLAH YAYIMAKA RAHAMA AMEEN.


*Ina Mika godiyata gareki* *uwar room KHADIJAH ADAM IDRIS* *(shalelen kainuwa)Allah yabar zuminci ameen.*
*God bless you my Aunty.*


*INA* *JINJINAR* *BANGIRMA*
*AUNTY* *HAUWA* *TARE* *DA* *DOCTOR* *MARYAMA* *ALLAH* *YABAR* *ZUMINCI* 💋💋
BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM

Bayan kowace sallar farilla mu rinka karanta wanna addu'ar kafa goma.

HASBIYALLAHU LA'ILAHAILLAHUWA ALAIHI TAWAKAKKALTU WAHUWA RABBUL ARSHIL AZIM.

*INA* *JINJINA* *YAN* *GROUP* *DINA*
My zee
Hauwa sani
Safiya Muhammad
Hajjo
Maman ilham
Beby
Nagode da addu'arku Allah ya saka da alkhairi Ammafa ku Kara yawan comment 🤣🤣🤣

Fiddausi umar (maman intisar) yasin haryanzu Banga comment dinki ba 😔🙄.


*NOT* *EDITING* 🤗

بسم الله الرحمن الرحيم


🅿️4
📝 Farrah ita ce bata farka da ga baccin daya dauketa ba sai misalin karfe 1:35,tayi mamakin yanda tayi nisa a baccin.

Plant shues ta saka a kafarata ta nufi kicin da sauri danta dora girkin rana.

Momy ta tadda a kiching din

Please Login or Register in order to submit comment