google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng  _*🌻ABBA NE🌻*_

Hakkin Mallakar

_*Sarat Alk'asum ( Maman Nusaiba)*_



_*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*_


Ina godiya ga rabbis-samawati daya bani ikon rubuta wannan labarin, ina fatan yadda na daura Alk'alami na lafiya na saukeshi lafiya, Allah ka bani ikon rubuta abinda zai anfani Al'ummar Annabin mu Manzo (s.a.w.), Allah ka karemu da karewarka ya rabbi ka bamu zaman lafiya a kasashen mu baki daya, ya rabbi ka k'ara mana ilimi da fasaha da fikira da basira, Allah ka daukaka dukkan wani Marubuci/Marubuciya, ya Rabbi ka k'arawa Marubuta Yan Uwana daukaka da basira.

Wannan littafin na kune akan N 300 only kacal, kada ku bari a baku labari ga masu son labari su tuntubeni ta WhatsApp number na 👉🏻+966577675904 .


بسم الله الرحمن الرحيم


0️⃣1️⃣

*NIGER 🇳🇪*


Tafiya suke cikin mota dukkan su suna hira cikin nishad'i yayin da na hango wani Yaro kyakyawa wanda bazai wuce shekara 13 years ba yayi shuru yana jinsu"Wata kyakyawar Mata ce gefenshi wanda baza ta wuce shekara 30 ba hannunshi cikin nata tana murzawa a hankali lokaci zuwa lokaci tana kallon shi. Cen gaba wanda yake driving d'in ne ya d'an juyo fuskar shi dauke da murmishi shima bazai wuce shekara
40 ba" Yace Khalil ya dai naga ka wani had'e rai? Ko baka son zuwa Nigeria ne? Sake had'e rai Yaron yayi baice komai ba, sai bud'e k'ofar hanci yake. Tsohuwar dake gefen Baban nashi ce tace" Kai Khalilu dan butar Uwaka wajan dangin nawa ne baka son muje? To baka isa ka hana muyi zuminci ba koda yake ai kayo gadon Uwarka Salma shiyasa, nidai ba ruwa yo to in ba kin dangi ba Yaron nan tinda ka shigo motar nan sai wani cin magani kake. Ato nidai baka isa ka hana muje Nigeria ba wajan Yan Uwana ba, wannan idan ka girma an shiga uku a gidan nan, dan na lura mugu za'ayi Babba ma ba karami ba....
Murmishi Khalil yayi yace" Abba wai ni mugu ne inji Inna? Murmishi Abban nashi yayi yace" A'a Khalil tsokanar ka take kaji.. Inna ta rik'e baki tace yau ni naga jaraba ido da ido, kenan kai Umaru baza ka mishi fad'a ba ya rage bak'in hali sai kace wai tsokanar shi nake? To shikenan na dena magana babu ruwana idan D'anku ya zama munafiki, yo in banda rashin son gaskiya irin naka Umaru sai kace tsokanar shi nake, nifa da Bakori naji ance ka fad'i wannan maganar sai nace anyi k'arya.. to sai kuma gashi naji da kunne na, idan mukaje Bakori bazan sake zuwa inda kuke ba...
Abba yayi murmishi yace to yi hak'uri Inna zaneshi zanyi ma tinda har baya so aje Nigeria zuminci. Gyara zama tayi tace Yauwa yanzu naji bayani. Gudu sosai Abba keyi ganin Yamma nayi burinshi kawai subar dajin da suka shiga mai duhuwa. Kiiiiii Abba yaja burkin mota yana fad'in Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un, Inna Y'an fashi gasu cen a gaban mu. A matuk'ar razane Inna ta kama hannun Abba tace mu fita kafin suzo mu gudu. Da sauri Abba ya fito Khalil da Maman shi suma suka fito hankali a tashe. Motocin dake gaban nasu wanda Yan fashin suka tsare su suka hana suga fitar da su Abba. Wani rami Abba ya gani guda biyu Y'an madaidaita, kallon Inna yayi yace" Salma kama Inna ku shiga nan, kai kuma Khalil zo mu shiga nan.. da sauri Salma da Inna suka shiga cikin Ramin nan suna k'yarma" Abba da ya dauko wata jaka daga mota ya kwanta ruf da ciki, ganin haka yasa shima Khalil ya kwanta. Cikin azama Abba ya zarge jakar sai ga bindigogi har guda uku gefe guda kuma wata k'aramar jaka ce a ciki. Abba ya kalli Khalil da shima shi yake kallo yace" Khalil ka zauna anan amshi wannan duk wanda kaga yayo nan sai kasa hannun ka anan ka danna to zaka harbeshi.. Khalil ya soma kuka ya rik'e hannun Abba gam yace Abba kada kaje zasu kashe ka kamar yadda suka kashe min Y'an Uwana, kuma waďancen ma k'ila sun kashe su. Rufe mishi baki Abba yayi yace" Kul naga kayi kuka Yarona ka zama Jarumi a duk inda zaka kasance, kada ka bari wani yaga rauninka" San nan ka rik'e bindigar nan nasan ka iya harbawa tinda na koya maka dama saboda halin rayuwa. Girgiza kai Khalil yayi sai kuma yayi saurin goge hawayenshi nan da nan yaji wani kwarin gwiwa yazo mishi" ya gyara kwanciyar shi yace" Abba na dena. Murmushin k'arfin hali Abba yayi yace" Zanje ko ni ko su, nayi alkawari zan kare kasata bazan tab'a zuba idanu ina ganin ana zalinci nayi shuri ba, wannan hakkina ne k'are duk wanda yake dan kasata" Yana fad'in haka ya ciro da waya irin na Police ya soma magana cikin halin damuwa, yace" Hello Bonsoir Sir Shaf ďeta Umar mai Nasara ke magana dajin iyaka tsakanin mu da Nigeria a turo min da Sojoji mota uku. Daga cikin wayar aka amsa mishi da to yanzu yanzun nan za'a tura maka su ko kuma zamu turo maka da Sojojin sama. ABBA ya amsa da to Sir merci beaucoup" Bai tsaya yin komai ba ya nufi inda suka tara mutanen. Cikin sanďa ya shake wani dake kusan shi ya rife mishi baki alburushi ya sakar mishi a cikin shi nan take ya mutu" cikin Azama ya isa ga d'ayan shima ya kashe shi da haka ya kashe mutum hud'u duk basu ankara ba... Yana saita wani ne ya juyo, da sauri yayi baya yana fitar numfashi babu abinda kunnen shi yake juyo mishi sai kara da kururwar mutanen da suka tsare da alama kashe wasun su ne sukeyi. A guje ya koma inda ya bari Khalil yana huci, kallon Khalil yake yace Yarona bazan bari su k'ara kashe kowa ba zan fanshe su, na tabbata ni suke nema. Duk da Khalil Yaro ne amma yana da hankalin gane inda magana ta dosa,cikin kidima yace" Abba to da me zaka fanshe su? Ka bari Sojojin su iso tinda kayi waya dasu. Girgiza kai Abba yayi yace" No kafin suzo sun kashe su kuma har da Yaran goye da tsofaffi bazan iya bari ta dalilina a kashe rayuka ba. Rike shi Khalil yayi yace" A'a nidai don Allah Abba kada kaje. Zame hannun shi yayi ya sake kira Shugaban nasu akan sun tafo ne" Ogan nashi ke sheda mishi ai suna cikin tafiya mai ya k'are amma za'a kawo musu , su kuma Sojojin sama ba'a samu matuki ba saboda yau sunje gida hutu, shima yana d'aya daga cikin matuk'an jirgin. Abba ya k'ara shiga tashin hankali fiye da wanda yake ciki" Yana huci yace" Khalil zan baka umarni zaka bi? Khalil yace eh Abba zanbi...cikin yanayin damuwa da kuna kallon bankana ya shafa kan Khalil yace Allah ya maka albarka" Ameen Abba cewar Khalil da ya kagara yaji umarnin da Abban nashi zai bashi. Bud'e jakar Abba yayi ya fito da wata takarda guda uku ya mik'awa Khalil yace" Wannan ko bayan ba raina ka bari sai ka girma ka mallaki hankalin kanka ka karanta da kyau, kuma duk abinda na rubuta ka aiwatar. Jinjina kai Khalil yayi dan ya ma kasa magana. Abba ya dauko Bom guda uku ya daura a jikin shi, ya kalli Khalil yace maza zo muje. A matuk'ar tsorace Khalil yace Ab...Abba bom ne fa kasa" Had'e rai Abba yayi yace Bana son duguwar magana Khalil. Cen kusa dasu Abba ya tsayar da Khalil ya kalleshi da kyau yace" Khalil ka kula da Maman ka da Mahaifiyata, rai na fansa ne ga k'asa ta zan yaki kowa akan kare hakkin dan Adam" shi dai Khalil kallon Mahaifin nashi yake ba ko k'iftawa. Abba yace" Idan na isa cen zan kirga daga daya zuwa biyar da nace ka harbo to kayi haka kana jina da kyau? Ai tuni Khalil yasaki futsari yace" Abba bazan iya wannan abun ba taya zaka ce na harbe ka,idan nayi haka fa mutuwa zakayi , so kake mu tashi ba kai ne? Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Abba ya maidasu dan karfafawa yaron nashi,yace" Nina saka kuma da kayi ka koma cen wajan Maman ka ka bata du abinda na baka" Matsowa yayi kusan kunnen shi ya soma mishi magana cikin kunnen. Bayan ya gama ne ya juya zai tafi Khalil yace" Abba na zanyi duk abinda kace" Ya fad'a murya a sarke. Murmishi kawai Abba yayi yace Nagode d'ana san nan yayi saurin nufar su.

Abba na isa cikin d'aga murya yace" Ku dakata! Ba dai ni kuke nema ba to gani. Kwashewa da dariya sukayi suna nuna Abba da bindiga sukace, Ashe da gaske kana kishin Al'ummar ka? Cikin rashin tsoro Abba yace Ka tab'a gani Soja yaji tsoro? Ko kaji ance maka Umar yana tsoron irinku? Babban cikin su ne yace" Ai dama da niya muka kama wannan mutanen nasan Y'an k'asar ku ne kuma ko ka b'oye idan kaga muna musu fiďar Rago zaka fito. Abba yace" Ai na san Mutum biyu ne zasu turo ku, idan har raina kuka so to ku saki wannan bayin Allah suyi tafiyarsu ni kuma gani ku kasheni. Dariya suka saka suna nunashi da hannu suna fad'in shege Soja yaga uwar bari. Tuni suka saki wannan mutanen dama Babbar mota ce kowa ya shiga , wanda aka harba suka hada da su a guje direban yabar wajan kowa bin Abba da kallon taysayi yake. Khalil dake cen gefe ya b'oye a cikin wani rami dake kusan su, sai hawaye yake yi, kallon su yake d'aya bayan d'aya. Ji yayi Abba na fad'in" D'aya Biyu Uku had'u biyar wuta! Ya fad'a da karfi. Cikin hanzari Khalil ya harbi bom din da Abba ya d'ago a hannun shi,tuni bom din suka tashi da wuta. A guje Khalil ya nufi ramin da su Inna suke ya fad'a yana k'yarma. Cen yaji takun mutane suna ina Matar tashi take ne? To ku shiga mu duba har Yaron nashi Oga yace mu kashe su" Jin haka yasa Salma ta kunshe bakinta tana kuka kafin suyi wani motsi sai ji sukayi ana fad'in" Maza ku fito yanzun nan.. jiki na rawa suka fito" Babban cikin su yace" Hajiya zabi biyu zamu baki ko mu miki faďe a gaban idanun Uwar Mijinki da D'anki ko kuma mu kashe Danki da Uwar Mijin ki sai ki zabi guda... zazzaro idanu Salma tayi cikin matuk'ar tashin hankali tace" Don Girman Allah kuyi hakuri karku kashe min Yarona, ni na yarda ku kasheni ku barsu su a raye.. wani zazzafan mari taji ya sauka a kan kuncin ta, Khalil daya zaburo d'aya daga cikinsu yasa gindin bindiga ya kwada mishi a kai tuni ya zube a k'asa sumamme" Inna ganin wannan bala'in yasa itama ta suma.. Salma kuka take kamar ranta zai fita sai rokon su take amma sai dariya ma suka mata" d'ayan cikinsu ne ya janye mayafin jikinta yana lashe baki yace" Kai gaskiya dan iskan Sojan nan ashe yana da kayan alatu" dariya suka sa suna janta kiii a k'asa tana kuka.. Babban cikin su ne ya kama rigarta ya keta suka sa dariya, Ita kuma Salma da ta jigata sai kare jikinta take da hannu tana k'yarma. Cikin muryar kuka tace Azzalumai Insha Allah D'ana ne zai kawo karshen ku , kun kashe min Miji.. dariya suka sanya Babban cikin su yace" Yau zaki ga zalinci ganin idanun ki kai ku bankare min ita.. kuka take tana ja da baya tana girgiza kai dan maganar ma ta gagareta. Cikin rashin Imani ko wanne saida ya mata faďe sun kai biyar" suka jata suka jefa a mota. Babban cikinsu yace" Su Babawo sun mutu a hanyar bom din nan ,shi Sojan nan ya dauka mu duka ne. Dariya suka kuma sawa suka ja motar su a guje... Khalil tin lokacin da Maman shi ta kwalla k'ara ya dawo daga sumar da yayi amma rashin karfin ya hana shi tashi, jini ke ta zuba ta kanshi bai san sanda ya kuma sumewa ba, sai farkawa yayi ya ganshi a Asibiti. Kallon gefe yayi yaga Inna ansa mata karin ruwa d'ayan gefen kuma K'anen Abban shi ne da Matar shi tsaye a kanshi. Sannu suke jera mishi amma baice musu komai ba har Doctor yazo. Bayan ya gama auna shi ne yace To alhamdulillahi Kwakwalwar shi bata samu matsalar komai ba zaku iya zuwa gida nan da yamma. K'anen Abba yace mungode Allah yau wata d'aya muna jiran tashin sa sai gashi ya tashi, Allah ya jikan Salma da Yaya Umar.. kallon su yake kamar ya samu TV wata d'aya yake maimaitawa aranshi kenan wata yayi baisan indakanshi yake ba? Wasu zafafan hawayene ke zarya kan kuncin shi. Inna na farkawa ta ringa kuka tana basu labarin abinda ta gani kafin ta suma, suma din kuka suke suna bata hak'uri.
Da yamma Aka basu sallama suka dawo Gida inda aka kai Khalil dakin shi.


_*BAYAN SHEKARA GOMA*_


_*FARCE AÉRIENNE*_ babban Office d'in Sojojin sama wadda take a garin Niamey Niger" Sojoji ne sunfi dari uku jere kowa ya k'ame a inda yake, hannayen su rike yake da manya manyan bindigogi yayinda kafafuwan su sanye yake cikin bak'in takalmi mai tsaki har zuwa kusan gwiwarsu, ko wanne daga gaban rigarshi an sanya sunan shi dana Mahaifin shi.. Ogan su ne ya soma jawabi kamar haka: Alhamdulillah Masha Allah yau ne kuka gama tirenin da ake koya muku, dan haka sakamako ya fito kuma mutum biyu ne suka samu sakamako mai kyau a wannan shekarar. Shuru kowa yayi dan kowa so yake yaji sunan shi. Ogan nasu ya yace Wanda sukaci wannan Jarabawar ba kowa bane sai _*Ibrahim Khalil Umar mai Nasara*_ da kuma _*Abulkareem Yusuf mai Nasara*_ sune wanda suka ci a wannan shekarar congratulations muna tayaku murna. Khalil d'aya lumshe idanun shi tin lokacin da aka soma bayani jin an kira sunan shi ya bud'e idanu da sauri" Abdul dake kusanshi suka rungume juna cikin tsananin farin ciki. Ogan nasu yace su bishi ciki za'a canja musu Kaki, san nan ya sallami kowa su kuma su Khalil suka bishi. Suna zuwa babu bata lokaci aka dauki kake sabo dal aka basu izinin su sanya" wani waje suka shiga inda suka sanya kayan. Ogan nasu na murmushi ya mike ya sanyawa Kahlil taurari guda uku a ko wani kan k'afar shi, ya sanya mishi hular san nan yaja da baya yana murmishi. Sara mishi Khalil yayi ya kame " Kallon jikin kakin nayi naga an saka *General Khalil Umar mai Nasara*. Shima Abdul sanya mishi nashi akayi inda shi kuma nashi taurari biyu ne wato kenan Khalil ne gaba dashi, shima kasan an sanya sunan shi a jiki. Ogan su ya sara musu ya basu hannu suka zauna ya shiga yi musu bayani akan abinda ya shafi tukin jirgin sama da komai duk da sun iya amma ya kara musu haske akai. Suna tashi a tare shi da Abdul suka nufo gida ranasu fess Abdul sai murna yake, yayinda Khalil ke kissuma abubuwa daban-daban a cikin zuciyarshi, idan ba lura kayi ba baza ka tab'a gane yana cikin farin cikin ba. Suna isowa cikin takunshi na kasaita ya fito sai yanzu na k'are mishi kallo, fari ne amma ba har cen ba, dogo ne kakkarfan gaske fuskarshi dauke da saje wanda ya k'awata fuskartashi, yana da kyau dai-dai misali.. Cikin parlon suka nufa bakin su dauke da sallama" Mamy dake zaune a parlon taci ado na kece reni da fara'ar ta ta amsa musu. Abdul Baki yayi rufuwa yace Mamy munci jarabawar nan fa kuma Khalil shine Oga na. Da sauri Mamy ta mik'e ta rungume Kahlil dake tsaye yana kallon su" Cikin murna tace Alhamdulillah na tayaka murna Yarona duk da bana son aikin nan amma ya zanyi da kai tinda kace zakayi. Murmishi yayi cikin zazzakar muryarshi yace" Merci beaucoup Mamy na. Sakeshi tayi ta rungume Abdul" Bayan sun zauna ne ta kawo musu abinci. Khalil loma uku yayi ya mik'e yana yamutsa" Cike da damuwa Mamy tace Kai fa dad'ina da kai kenan baka son cin abinci. Murmishi yayi sai yace zan sha tea Mamy. Mamy tace OK bari na hado ma san nan ta nufi kitchen. Shi kuwa Abdul sai sunbatu yake yana fad'in, Ai kaji Alkur'an cin abincina zanyi" Sai kuma ya d'ago ganin Khalil ya nufo d'akin shi, yace Kai ina Inna wai take? Ko ci kanka Khalil baice mishi ba ya shige d'akin shi.....

Washe gari Khalil da Abdul suka shirya zuwa Office Mamy nata musu Addu'a, su kuma suna amsawa da Ameen. Koda suka isa tuni an shirya musu komai, Suna isowa jirgi suka shiga Ogansu ya basu wata takarda yace" Khalil wannan da kunje Maradi a babbar Office zaku kai wannan nayi magana dasu . Jinjina kai kawai Khalil yayi dan shi bai saba yin magana dayawa ba. Hannu aka basu nan Suka soma tafiya kafin daga bisani suka lula sararin samaniya. Koda suka isa Maradi sakon suka bada, bayan wani lokaci aka had'a su da wasu Sojojin sai lokacin aka sanar musu da wani daji zasu je inda wasu Y'an ta'adda ke buya sukashe su. Da to suka amsa Suna Sarawa Ogan nasu kafin duk suka shiga jiragen suka lula sararin samaniya. Yak'i sosai akayi da Y'an Ta'addar nan kafin suka samu nasarar kashe su wanda basu kashe ba kuma suka kamo su suna shirin guduwa.. Sai dare kafin suka dawo Garin Niamey a matuk'ar gajiye suka iso gida. Cikin k'ank'anin lokaci A garin Niamey dama sauran karuruwa suka san da general Khalil Umar mai nasara....


Zaune suke a parlo Mamy da Baba Abdul sai Khalil, Sako yaji ya shigo wayarshi, kamar bazai dauka ba sai kuma ya duba" Da sauri ya mik'e yana fad'in Abul maza muje Oga na Kiran gaggawa ankai hari an dauke mutane, kazo muje kafin suyi nisa sun tafi da mutane. A hanzarce Abdul ya mik'e suka nufi d'aki" Masufi minti uku ba sai gasu cikin kayan Sojoji bindigogi a ko wani gefen su. Mamy tuni har ta soma hawaye ta musu Addu'a, Baba na ta ce mata tayi hakuri. Kallonshi Tayi tace Haba don Allah Yaran nan tinda suka samu aikin nan bama zaman minti talatin dasu a gidan nan sai ace zasu je Kasar Ghana gobe ace gasu ce a Agades gaskiya ni inda za'abi ta tawa da sun hak'ura da aikin nan.. Baba yayi murmishi yace Ki bar maganar ma dan Khalil bazai yarda ba. Su Khalil na fita babu inda suka zarce sai dajin dake cen bayan gari da nisa sosai" Computer dake hannun su na nuna musu inda suke Khalil nata sharara gudu. A bakin dajin suka paka motar su, suka kutsa kai ciki dajin sai bishiyoyi sai ka janye zaka ga gaban ka. Gudu sukaji a bayansu, da sauri suka juyo sai sukaga wata mata da ciki tana tunkaro su" Da sauri suka tare ta ganin ta durkushe a kasa ta rik'e cikin dake jikinta. Cikin mawuyacin hali ta d'ago tana kallon su wani mugun ciwo ne ya zo mata ba shiri ta damki Hannun Khalil ta rike gam......






_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[12/09, 12:03] MAMAN NUSAIBA CE: _*🌻ABBA NE 🌻*_






Hakkin Mallakar

_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_



_JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION_


_Littafin na kud'i ne only N 300, my WhatsApp number 👉🏻+966577675904 _



بسم الله الرحمن الرحيم

0️⃣2️⃣


Ta damki Hannun Khalil ta rike gam sai juya kanta take alamar haihuwa ce zatayi" Cikin Azama Abdul yace Khalil maza kayi lungu da ita haihuwa zatayi ka taimake ta. Khalil da duk ta gama bashi tausayi ya sunkuce ta ya ringa kutsawa cikin dajin dan ya samu inda zai b'oye ta" Gindin wata bishiya ya samu mai inuwa kuma inba lura kayi ba baza ka san akwai mutum a wajan ba, aje ta yayi yana huci ya kama hannayen ta yace Ki daure kinji baiwar Allah zan kaiki gidan ki .D'ago da rinannun idanunta tayi ta zuba su a kanshi tana girgiza mishi kai, cikin sarkewar murya tace" A'a kada ka mayar dani dan ba nan garin muke ba, Mijina sun bishi yayi cikin daji bansan a wani hali yake ba" Zata sake magana taji wani azababben ciwo wanda ya lumka na baya" Sake damkar hannun Khalil tayi tana salati Ganin haka yasa Khalil cire rawanin shi daya naďa a kanshi ya lulluba mata a jikin ta.. idanunshi ya rufe yana jin zuciyarshi na mugun bugawa da sauri sauri" Kamar daga sama yaji kukan Jariri ta sauri ya bud'e idanu yaga Jaririya a k'asa tana tsala kuka. Rasa yanda zaiyi da Babyn yayi shi bai san yadda ake yanke cibiya ba gashi ba wani a kusan shi. Matar ce ta sauke wani wahalallan numfashi ta bud'e idanu duk da ciwon da take ji ta kalli Khalil tace" Kana da reza ko wuka mai kaifi. Cikin rawar murya Khalil yace" Eh akwai reza yasa hannu a aljihunshi ya fito da rezar sabuwa dal ya mika mata... Amsa tayi ta mike daga durkushen da take ta dauki wannan mayafin na Khalil ta aje a gefe" Yankewa Jaririyar cibiya tayi hawaye na zirya kan kuncinta. Daukan Jaririyar tayi ta lullubeta da mayafin ta d'ago kai ta kalli Khalil wanda shima ita yake kallo. Cikin raunatacciyar murya tace Soja ga Y'ata na baka ita halak malak, ka rike min bisa amana idan ta girma kace mata Maman ta na matuk'ar k'aunarta. Na baka ita kyauta har abada ta zama Yarka daga yanzu ka amshe ta mana" Ta fad'a tana murmishi mai had'e da hawaye.. hannun Khalil na rawa ya amshi Jaririyar ya rungume ta tsam a jikin shi, nan da nan yaji k'aunar Jaririyar na ratsashi, cikin damuwa ya kalli Matar yace" Anty na miki Alk'awarin zan rik'e Yarinyar nan da amana, amma ya sunan ki? Kanta k'asa tace" Ni Sunana Zulaihat Don girman Allah ka tafi ni nasan kwanana ya k'are anan zan mutu, kuje kar su kashe min Jaririya ta.. Khalil yace No ki tashi muje duk da ina jin takun tafiyar su amma baza su ganmu ba. A'a kada kace haka Soja karka damu

Please Login or Register in order to submit comment