google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ta fad'a tana balle mishi mab'allin rigar, rufe idanu yayi ita kuma ta gama ta cire mai riga har ta cikin duka ta cire. Kyakyawar fatar jikin shi ce ta bayana Rufaida ta sauke ajiyar zuciya tana kallon shi ,da hanzari ta dauko ruwan ta sanya towel d'in ta shiga goge mishi jiki. Tana gamawa tace" Abie saura wandon za'a cire na wanke ma kafafuwan ka kalli yadda sukayi baki" Da sauri ya zabura cikin rawar baki yace" Wando kuma Daughter ki barshi kawai zan iya zuwa toilet sai na canja kayan. Kuka tasa tana fad'in" Abie kaji fa duk warin dauďa kake amma kace baza a goge ma jiki ba, nidai ka tsaya na gama ko na shirya ka" Sake da baki yake kallon ta maimaita maganarta yake yana cewa" ko kin shiryani kamar wani Baby?.. wayo ya mata yace" Ki kawo ruwan ki wanke kafata kawai ya wadatar nama ji sauki sosai" Ruwan ta kawo kusan k'afarshi ta shiga gogewa sai cika take tana batsewa wai ya hana ta gyara shi.. shi kam murmishi yayi yana kallon ta har ta gama" Kaya ta dauko mishi masu kyau ta sanya mishi rigar ta aje wandon tace" Bari na wanke toilet kafin na fito ka gama" To yace mata tana shiga yayi sauri ya tashi a hankali ya kimtsa ya dawo ya zauna. Bayan ta fito ta ringa murna Abie d'in nata ya samu lafiya" Kama shi tayi suka fita Palo... zaune suke a gaban Boka sun nutsu kamar wasu wanda ake yiwa nasiha mai ratsa jiki" D'agowa Bokan yayi ya kallesu da jajan idanun shi sai kuma ya kece da dariya dajin na amsa sautin muryarshi. Had'e rai yayi yace" Alhaji Babba meya kawo ku? Cikin rawar Muryar Alhaji Kabeer yace" Muna so a kashe General ne da wannan Yarinyar, kai duka ahalinshi ma duk a kashe su mu dena ganin irin su a Duniya.. Dariya Bokan yayi yace" Bari mu gani, Wata kwarya ya janyo ya soma tsubbace tsubbacenshi ,sai ga ruwa sake fad'in wani kalmomi yayi sai ga Khalil ya bayyana zaune a Masallaci yana jan tasbaha" Boka ya d'ago yace ku lek'a ku gani. Lekawa sukayi suka ga Khalil a cikin kwayar, Cikin jin tsanarshi Alhaji Sammani yace" Shine Boka a kashe shi tinda mu mun k'asa kashe dan iskan Yaron nan mai taurin kan tsiya.. Boka ya bud'e k'ofar hanci yace" Bazai tab'a yiyuwa ba a kashe shi. Da mamaki suke kallon Boka su da sukazo ya share musu hawaye amma yana wata magana" Alhaji Mati yace" Boka kamar yaya kace bazai yiyuba? Dariya Boka yayi yace" Wannan Yaron da kuke gani yana tare da sanya albarkan Al'umman gari da wanda suke rikeshi, kuma kullum Kakarshi sai ta mishi Addu'a neman tsari ga irin ku" Ya fad'a yana sake yin wata dariya. Jinjina kai sukayi Alhaji Kabeer yace To Diyar tashi fa? Shafe photon Khalil Boka yayi ya kawo na Ashma tana kwance tana bacci Inna na gefen ta. Dariyar basawa yayi yace" Za'a iya yiwa wannan wani abun amma fa baza a iya kashe ta ba.. Da sauri Alhaji Mati yace A maidata mummuna kowa yake k'yamatarta" Boka ya zaro manyan idanun shi yace Bazai yiyuba ba ku dai fad'i wani abun. Shikenan a hauka tata kawai nan ma Boka yace bazai yiyuba ba" Alhaji Mati ne yace To Boka ake firgitata kawai kaga sai a dauka ta haukace " Dan Jim Boka yayi sai kuma ya dauko wani ruwa ya watsa a saitin fuskar Ashma dake bacci, gani sukayi ta dan motsa sai kuma taci gaba da baccin ta...

Murmishi sukayi Alhaji Sammani yace Yanzu ba abinda Za'a yiwa Khalil din boka a dai bduba? Boka yace Kuje bayan sati biyu ku dawo lokacin na samu wata hanyar" Cike da farin ciki suka tashi har zasu tafi Alhaji Kabeer yace Kai munyi mantuwa ,Boka D'an mu yana son wannan Yarinyar a cire mishi sonta muna so ya kashe ta da hannun shi" Sake dubawa yayi yace" Shima bazai yiyuba ba na raba soyayyar da yake mata saboda ba daga sama ta fado mishi ba so na gaskiya yake mata, maza ku tafi La'anannun Allah sai bayan sati biyu ku dawo. Juyawa sukayi suka bar dajin kowa na ta saka da warwara...

A guje ta fito harabar gidan kanta ba dan kwali ,wata Mata ce ke binta da dorinar, tana fad'in" Ni zaki kunyata Sanjina? Duk jin dad'in da kike yi a gidan nan shine ki rasa wa za kice kina so sai General Khalil to yau saina kashe ki kowa ma ya huta, har kina da abinda General zai kalla a jikin ki yace yana sonki bari ki gani.. Wata sandar karfe ta dauko ta shiga maka mata tana cewa" Ni zakici amana Sanjina Musulmi zaki ce kina so Shi wanda muka Zaba mikin uban waye zai aureshi iyee? Kuka sosai Sanjina keyi tana fad'in Mama kayi hankuri nidai shi nake so shima yana sona" wani wawan Mari Maman nata ta sauke mata akan kuncin ta wanda yasa taga wucewar taurari. Janta da ringayi tana ci gaba da dukan ta har bakin k'ofar waje ta kawo ta, hankada ta tayi tana huci ta koma ciki" Jakar kayanta ta dauko mata a jefo mata tana cewa" Kije cen gidan su sai ku zauna indai shi kikeso ba mu ba ke karki kuskura kizo inda muke kinji na fad'a miki.. Hak'ura ta shiga bata amma Maman nata tace Sam baza ta yi ba daga karshe ma Yaran Unguwar ta kira tace su Kora ta har sai tabar Unguwar gaba d'aya" Su kuwa Yara sun samu abinda sukeso tuni suka ringa jifanta suna tile ta da k'asa. A hankali take tafiya tana kuka yaran na binta har ta kusan zuwa karshen layin gidan su san nan suka kyaleta. Zama tayi a gindin wata bishiya tuna wayarta yasa ta duba ta kuwayi sa'a Maman nata ta hado mata da ita.. number Khalil ta dannawa kira, yana dauka ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma rai. Khalil dake zaune yana shan iska ya d'aga kiran nata jin kukan ta ne yasa Yace" Hello Sanjina kina jina? Lafiya kike kuka ? Waye ya tab'a ki? K'arawa Kukanta Volume tayi da k'yar ta iya cewa" Mama. ....








_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[12/09, 12:03] MAMAN NUSAIBA CE: _*🌻ABBA NE 🌻*_










Hakkin Mallakar

_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_


_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_



_*Littafin na kud'i ne only N300 ku harzarta ku mallaki naku my WhatsApp number 👉🏻+966599791573*_



بسم الله الرحمن الرحيم

0️⃣9️⃣


Da hanzari Khalil ya mik'e ya shiga ciki daret dakinshi ya nufa hankalinshi a tare" zama yayi yana jin sautin kukan nata yace" Mama kika ce fa Sanjina? Ko wani abun ne ya faru da ita? Girgiza kai tayi kamar yana kallonta cikin zafin abinda Maman nata tayi mata tace" Ta koreni daga gida tace bani ba ita karna kuskura nace su suka haifeni" Zaro idanu Yayi yace" Ita Maman ta fadi haka? To me kika mata.. Nidai kazo ka daukeni zan zauna dakai saboda kai ta koreni tace ni ba Y'arta bace" Khalil ya saki baki yana jin maganar ta Sanjina kamar daga sama, baki na rawa yace" Saboda ni kuma Sanjina? To me nayi ni kuma? Nidai kazo yanzu ma ina zaune a waje kila ma ta karya min hannu kazo don Allah zan iya mutuwa in baka zo ba" Ta fad'a tana sake sakin kuka. Mik'ewa Khalil yayi da sauri yace Gani nan amma ina ne Unguwar taku? Goge hawayen ta tayi tace *Tanko pomp* ina karshen layi fita daga Unguwar" To shikenan gani nan zuwa yanzu, kashe kiran yayi ya mik'e da sauri ya fito. Dakin Abdul ya nufa ko sallama babu ya shiga yace" Zo mu tafi" Abdul bai musa ba ya dauka ko wani ne zasu je kamowa dan haka ya sanya kakin shi riga baka wandon kuma na Sojoji har da daukan bindiga ya sanya a kugunshi saboda tsaro suka fito. Ashma data fito tana kuka ganin su yasa tayi saurin isa gareshi ta fad'a jikin Khalil tace" Abbana! Kakkarfar ajiyar ya sauke har sai da Abdul yaji ya kwashe da dariya, lumshe idanu yayi yace My princess lafiya kike kuka? k'ank'ame shi tayi tana ci gaba da kuka tace" To ba kai bane ka shareni, shine jiya ko kazo ka min Addu'a ma. Fesar da iska yayi ya banbareta daga jikinshi yace" Naji na dena fushin ki bari da na dawo sai nazo muyi magana zan kawo miki wani abu wanda kikeso sosai. Murmishi tayi tace To Abba Allah ya tsare hanya, Allah ya kare min kai Abbana" Cikin jin dad'i yace Ameen sai mun dawo" Abdul yace To lalle Princess wato ni baki ganni ba ma ko? Yar dariya tayi taje ta bashi runguma tana cewa" Papi ai bazan manta da kai ba sai kun dawo. Dariya yayi yace" Tam shikenan, fita sukayi Sojoji harabar gidan suka taso suna sara mishi" Hannu yake mik'a musu suna musabaha yana tambayar lafiyarsu, su kuma suna amsawa da lafiya" wani acikinsu yace" Yallabai ina zamu tafi? Unguwar Tanko pomp zamuje amma ba sai kun bimu ba wani abu ne zamu dauko mu dawo yanzu. Jinjina kai direban yayi yaja da baya ya mik'awa Captain Abdul key d'in motar su kuma suka shiga ciki, ba bata lokaci suka fita daga gidan..


Hisham yau jiki yayi sauki yana jin zai iya zuwa Asibiti da kuzarinshi ya shirya cikin k'ananan kaya ya feshe jikinshi da turare san nan ya fito zuwa parlo.. Rufaida ce ta tareshi tana murmishi tace" Good Morning Abie na" Shafa kanta yayi yace Morning daughter how are you? Yar dariya tayi tace Am fine Abie how are you feeling now? Alhamdulillahi am OK fa yanzu ma zan wuce Hospital ne kici abinci sosai kuma idan kinje Makaranta banda jan fad'a kinji ko" Ya fad'a yana zama.. Itama zaman tayi tace" To Abie bari na kawo maka abincin naka kayi breakfast,mik'ewa tayi taje ta hado mai abincin ta dawo kusa dashi a kan center table dake kusanshi ta aje itama ta zauna. Bismillah yayi ya dauko kamar zai kai bamin shi sai ya nufi nata" B'ata fuska tayi tace Abie kar fa kayi latti kaci abinci. Had'e rai yayi yace" Bana son muso kin sani ai" Bud'e bakin tayi ya shiga bata tana cin tana yamutsa fuska kamar tana cin sabulu. Sai da ya tabbatar ta koshi san nan shima ya soma ci ai kuwa tace ita zata bashi, gyara zama yayi ta shiga bashi sai da ya koshi ya janye kanshi yana fad'in" Alhamdulillah. Ammi ce ta fito cikin shigar ta ta alfarma tana ganin Hisham tace" To My Son jiki yayi sauki kenan har za'a fita aiki? Murmishi yayi ya tashi yazo ya bata runguma yace" Barka da fitowa Ammi na da fatan kin tashi lafiya? Murmishi tayi tace" Alhamdulillah ita kuma wannan sai yanzu takecin abinci? Ta fad'a tana nuna Rufaida. turo baki tayi tace" Dama Ammi ai baki so naci abunci yadda nakeso. Tab'e baki tayi tace" Ni da kici da karki ci matsalarki ce ba tawa ba ehhe, in banda ma shi Uban naki daya sangarta ki katuwa dake har sai ya zauna yana baki abinci a baki kamar wata babyn roba. Dariya sukayi Hisham yace na wuce, Allah ya tsare hanya suka mishi Rufaida ta bishi har bakin mota. Cikin sakalci ta soma dira kafa tana cewa" Abie to me zaka kawo min? Kallon yayi ,shi kam wani lokacin Yar nan tashi kamar mai aljanu lokaci d'aya sai ta rikice, wani lokacin kuma tayi abun masu hankali" Jinjina kai yayi yace zan dawo miki da ice cream shikenan? Tsalle tayi ta rungume shi tace" much love you Abie na saika dawo" Murmishi yayi kawai yaja motar ya fice...

Su Khalil na isa Unguwar ya kira ta tana d'agawa tasa kuka tace" Kazo ne kaga wasu ne suka tsareni yan giya ne sun hanani na wuce" Baki na rawa yace A dai-dai ina kike? Kwatance ta mishi san nan ta kashe kiran" Yan mayen dake kewaye da ita wani yace" Baby wai ina zaki je ne? Harara ta watsa mishi yace Ina ruwanka dani ku bani waje na wuce nace" Dariya suka sanya cikin maye suke cewa Ai baki isaba Yarinya tare zamu tafi. Wani da yayo kusan ta hankaďa shi tayi ta kwasa a guje, binta sukayi suma ita kuwa sosai take gudu tana kuka.. Khalil ya hango wata na gudu da sauri yace" Tsaya Abdul gata cen! Tsayawa sukayi ya fito da sauri kallon ta yake ganin yadda take gudu suna binta" Da sauri ya nufeta, kamar daga Sama Sanjina ta ganshi k'arawa gudunta wuta tayi har ta iso suka had'e da sauri ta fad'a jikinshi tana kuka. Rungume ta yayi yace" Okay yi shuru yanzu zamu tafi gida kinji Ashma na gida" Dena kukan tayi sai sauke ajiyar zuciya tayi.. Murmushi Abdul yayi sai kuma ya zaro bindigar shi ya harba yace" Duk wanda ya motsa zan tashi kanshi da alburusai. Cak suka tsaya suna zare idanu , agaba ya sanya su yace Muje Y'an iska lalatattu kawai, kuna shaye-shaye kuna bata D'iyan mutane, yau zaku gane baku da wayo" Wayarshi dake kan kafadar shi ya ciro ya danna wasu number ya soma fad'in" kuzo nan Unguwar Tanko pomp mota daya ta isa kuyo sauri" Yana gama fad'in haka ya maida wayar inda take.. Khalil da k'yar ya rabata da jikinshi yace" Muje mota. Kunya ce ta kama ta ganin abinda ta aikata tace Kayi hak'uri ban san na rungume ka ba. Murmishi yayi yace Ba komai ai nasan bakya hayyacinki muje" Motar suka shiga Abdul kuma na tsare da Y'an kwaya a gefen hanya.. suna nan sai ga Yaransu sun iso babu b'ata lokaci suka kwashesu suka wuce Office d'in Sojijo...

Tin kafin suje gida Khalil ya kira Baba ya fad'a mai zaizo da bakuwa" Ba komai Baba yace san nan ya kashe kiran.. suna isowa daret parlo suka shiga Sanjina na bayan Khalil duk jikin ta rawa yake bata san ko Iyayen Khalil d'in zasu amshe ta ba.. duk suna zaune a parlo Mamy ta mik'e ta kamo hannun Sanjina ganin duk shatin bulala ne yasa tace" Subhanallahi Yarinya meya sameki? Bata iya amsawa ba sai kallon Khalil take da shima ita yake kallo" Ashma data fito daga dakin Inna tana kunbura baki idanun ta suka sauka akan Sanjina, da sauri ta iso ta rungume ta tana cewa" Anty Sanjina dama Abbana kece zai kawo min? Murmishi tayi tace Eh nice ya kike ya karatu? Lafiya lau tace tana dariya...

Khalil yace" Am Sanjina ko zaki iya fad'a mana abinda ya faru har Mama ta miki dukan? Fashewa tayi ta kuka sosai,Mamy na rarrashin ta sai da tayi mai isarta san nan ta d'ago, ta soma cewa" Lokacin da mukayi canjan numéro dana dawo gida ina ta murna yau na ganka kuma har ka bani numéro d'in ka" Muna ta waya da kai har kace kana sona tinda ina son Ashma zaka aureni duk da ni ba Musulma bace" Ranar kasa bacci nayi saboda farin ciki ban fad'awa kowa ba mukaci gaba da magana, to jiya ne na samu na fad'a mata nifa kai nake so bana son wanda suke son aura min.. Mama ta min kallon banza tace" Amma Sanjina baki da hankali mutumin da ko hamshakin mai kudi zai ganshi sai da k'yar taya har kika ganshi kuma yace zai aureki? Ni ba wannan ba ma kin san dai ba abu daya muke bautawa ba, to ba ke bashi.. ina jin haka hankali na ya tashi na kwana ina kuka yau ina zaune kawai naga tashigo d'akina ta rufeni da duka, tace saina ce bana sonka ,ni kuma nace tayi hak'uri ta barni ina sonka shine ta ringa dukana har ta farfasa min jiki, daga karshe ma waje ta turoni da kayana kuma tace sai dai nazo gidan ku na zauna tinda kai nakeso, daga yau ko a hanya na ganta kar nace ita ta haifeni. Hakan ma bai mata ba ta sanya yara sukayi ta bina suna watso min k'asa" Ta karashe maganar tana sanya wani sabon kukan... Inna ta dauki salati tana fad'in" Muhammadu rasulullahi salallahu alaihi wasallam ni Indo, Kai amma Allah ya tsinewa halin wannan uwar taki yo ita haka ake rayuwa dan ba Addinin ku d'aya ba sai tace baza ki aureshi ba? To zan ga Uban da zai hana wannan auren ,kai Yusufa kuna fita masallaci da kun gama Sallah a daura auren Khalilu da wannan Yarinyar. Ajiyar zuciya Baba ya sauke yace" To Inna amma zamu je mu bawa Iyayen ta hak'uri su bamu auren ta shikenan" Inna tayi mitsin-mitsin da idanu tace" Kaima dai Yusufa kamar wani Yaro wani lokacin, to bari na kira Musalle yazo sai ya daura musu auren" Khalil yace Inna bafa gaggawa akeyi ba Baba zaije ya nema min auren ta ba wai maidata za'ayi ba.. Mik'ewa Inna tayi ta kama hannun Sanjina tace" Dan Butar Uwaka yau nakeso a daura auren nan ko min dare, kuma ka kira Likita ya dubata wannan hannun nata kila ta karye ma, sai kawai Inna ta rushe da kuka tana fad'in" Wannan Uwar taki Allah ya tsine mata sau ďai-ďai har sau dubu, kamar bata san ciwon Haihuwa ba to ki rabu da ita wata rana zata zo ta nemeki a lokacin zan nuna mata nima tacacciyar marar mutumci ce" Tana gama fad'in haka ta damki hannun Sanjina ta jata suka yi dakin ta..

Jiki a sanyaye Khalil ya nufi d'akin shi, da sauri Ashma ta bi bayanshi tana goge kwalla....








_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[12/09, 12:03] MAMAN NUSAIBA CE: _*🌻ABBA NE 🌻*_





_Hakkin Mallakar_

_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_



_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_



_*Littafin na kud'i ne only N300, my WhatsApp number 👉🏻 +966599791573*_


بسم الله الرحمن الرحيم


1️⃣0️⃣

A bakin k'ofar ta tsaya tana kallon shi kamar yau ta fara ganinshi, Juyowa yayi sai ya ganta a bakin k'ofa hararar ta yayi yace" To ki koma tinda baza ki shigo ba. Murmishi tayi ta taka zuwa inda yake,tana isowa ta kama hannayen shi duka biyun tana murmishi tace" Abbana! Murmishi ya subce mishi yace Na'am my Princess d'ina" hannun shi ta daura akan fuskarta tana kallon shi cikin idanu, Ganin hakan yasa ya gane mai take nufi" Jan hannun ta yayi suka zauna bakin gado ya janyo ta ya rungume yana shafa kanta. Lumshe idanu take tana k'ara lafewa a jikinshi dan ba k'aramin nutsuwa take ji ba in yana mata haka, shiyasa ko tayi kuka sai tazo wajan Abban nata ya mata haka" A hankali ta bud'e idanunta karaf suka sarke dana juna, Kallon kallo suke tsakanin su kusan ten minutes kamar baza su dena ba, ita ta fara janye idanun ta ta koma ta kwanta akan cinyarshi tana murmishi. Kuncinta yaja yace" My Princess d'ina ya ya akayi? Naga wannan bakin naki mai shegen surutu yana motsi da alama akwai abinda zaki fad'a min ne? Tashi tayi zaune kanta a k'asa tace" Abbana ka aureta Don Allah kaji" Ta fad'a tana zubar da hawaye. Girgiza mata kai yake yace Kin san abinda bana son gani a wajan ki zubar hawayen ki ko? Ki dena kukan muyi magana. Da sauri ta goge hawayen ta gyara zama tace Abbana ka auri Anty Sanjina kaji, ina sonta sosai tana da kirki kuma bata shigar banza duk da ita ba Musulma bace, amma Wallahi yadda take suturta jikinta wata Musulmar bazata yi hakan ba, ka aure ta kila ko nan gaba Allah yasa mu dace da babban rabo ta Musulinta, san nan ta haifa min K'ane ko K'anwa nima na samu D'an Uwa. Idanu ya zuba mata jin abinda take fad'a, dan murmishi yayi yace" Princess wani lokacin kamar babba kike in kina wata maganar ,wai wa yake koya miki irin wannan maganganun? Dariya tayi tana jan kuncin shi tace" Kawai daga ciki take fitowa Abba, kasan cikina yana da magana sosai daga nan take zuwa baki ni kuma sai na fad'a. Dariya yayi yana jijjiga ta yace" Eh lalle fa daga ciki take fitowa hakan yayi, zamuje gidansu a bamu auren ta daga yau anan za take zama . Yatsunta ta sanya a baki tana tsotsa tace" Abba za'ayi shagali ko? A'a babu abinda Za'ayi kedai kije waje gani nan fita zanyi wanka" Jinjina kài tayi ta mik'e ta nufi k'ofa,har taje bakin k'ofar ta juyo tace Abbana! murmishi kawai ya mata" sab'a baki tayi kamar zatayi kuka tace" Je t'aime" Murmishi yayi yace" I really love you so much my princess d'in Abban ta, Y'ar gatan Abba da Inna da kuma Papi din ta. Da sauri ta dawo ta rungume shi tana dariya tace" Abba inason koyon English kaji" Shafa kanta yayi yace ai da anyi conje de vacance shikenan in zaku koma za'a fara koya muku English. Tsalle tayi tace Kai naji dad'i to Allah ya kaimu da rai da lafiya,Ameen yace san nan ta wuce.. Yana ganin ta fita yaje ya kulle k'ofar zama yayi ba zato ba tsammani yaji hawaye na zuba daga idanun shi, gogewa yayi yana janyo wata loka dake kasan gadon ya bud'e, photon Iyayenshi ya rungume ya shiga yin kuka kamar wani karamin Yaro sai cewa yake" Abbana Umma na ina kewarku fiye da tunanin ku, ina fatan kuna cikin rahamar Ubangiji" Sai da yayi mai isarshi ya mik'e ya shiga toilet. Yana fitowa dama tuni su Baba na jiranshi shi da Abdul da Daddy Musa wanda bai jima da zuwa gidan ba, kai tsaye wucewa sukayi Masallaci...

Mansoor na zaune sun sakashi a tsakiya suna fad'a mishi abinda Boka ya fad'a musu, sai dariya suke. Alhaji Sammani yace" Dan iskan Sojan nan tinda baza mu iya mishi komai ba ta wannan hanyar sai kawai mu yiwa ita Y'ar tashi Ubanta ya Jaya mata shiga tarkon mu" Dariya suka kuma sanyawa har da tafawa a tsakanin su. K'uri Mansoor ya musu yana bud'e baki kamar wani sakarai, kauda mamakin yayi dan yasan kad'an daga cikin aikin mugayen Iyayen nashi ne ,sun kashe ma bare haukatawa ko maida mutum nakasashe, gyaran murya yayi yace" Am Daddy nace ba ita Ashma mai kukace ayi mata? Murmishi Alhaji Kabeer yayi yace" Munce Boka yake firgitata take fita a guje ana kamota, kaga daga nan zaka samu damar dauke ta ko. Tinda shi Uban nata ya gagare mu to mu koma kan makusancin shi da haka zamu ga bayanshi " Dam gaban Mansoor ya buga cikin rawar baki yace To yanzu yaushe ne maganin zai fara aiki?

To meye na gaggawa Mansoor? Yanzu Boka ya kirani yace Nan da wani lokaci zata soma shi kuma Ko ta halin Yaya sai mun san yadda zamu illata mishi rayuwa ba dai mu yake son kurewa ba.. dafe kai yayi yana binsu da kallo mik'ewa yayi a fusace kamar zai dake su yace" To Alkur'an idan kuka sanya Matata ta haukace nima nasan hanyar gidan Boka wanda ma ku baku sani ba, sai naje nasa a haukata ku kuma kusan zan iya aikatawa" Ya fad'a yana naushin bango san nan ya wuce fuu yana masifa har parlo ya iso Mommyn shi na zaune

Please Login or Register in order to submit comment