You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basu wuri.... "

Ta fadi hakan tare da janyo hannun Zuwairah suka bar dakin,Zuzu sae dariya take tana cewa"Kai Ash gaskia baki da dama,wato yanxu sae da kika kirashi shi yazo ya saka mata kayan kenan ko? "

? Ash tace"Ai rabu da ita,dani take zancen,idan tasan wata ai bata san wata ba,dole gyad'a tayi mai,idan taki kuwa tasha matsa......... "

Ni kuwa binsu nayi da ido da baki bud'e kamar wata shashasha har suka fice,kafin na tsaya wani dogon tunani naji an doko sallama wanda nake tunanin babu tantama ango nawa ne.

? ? Tuni gabana ya hau dukan uku-uku,rud'ewa nayi nama rasa abinda xanyi da kuma inda xan saka kaina. Mik'ewa tsaye nayi tare da gyara saman hijab dina wacce ta Anty Hajaar ce na ara.

Sae dana baiwa kofa baya sannan na k'arba masa sallamarsa,kai tsaye naji ya shigo yana furta"Amincin Allah da albarkarsa su tabbata agareki amaryar Mahmood..... "

? ? Kunnuwana ne suka dauki kuwwar maganarsa,ji nake kamar na tab'a jin wannan muryar awani wuri,dakyar na danne wannan tunanin nawa tare da furta"Gareka kaima wanda ya yakice farin cikina har yaci nasara aka aura masa ni..... "

Ina gama fad'ar hakan naji wasu hawaye masu dumi sun ziraro min saman kunci har ina ji suna diga ak'asa.Shi kuwa sautin murmushinsa kawai naji,kana yace"Subhanallah! ah ina kika tab'a jin wani masoyi meh matuk'ar qaunar masoyiyarsa ya rabata da farin cikinta? A'ah sae de mah dada tsundumata cikinsa da zeyi..... "

K'ok'arin magana nake,sae kawai naji yayi saurin taran numfashina"Gimbiya pls safe the discussion for later,yanxu zuwa nayi na rokeki da pls ki rufamin asiri nasan sam bamu k'yauta muku da bamu sanar daku xancen reception da wuri ba sae akurarren lokaci,don Allah amaryata amana afuwa,ki taimaka ki rufa wa angon naki asiri ki halarci reception din nan,pls kada kisa naji k'unya agun abokaina don su suka shirya abin......... "

?? Afusace nace"Nasan tabbas an fad'a maka cewar bana jindadi,kuma yanxu ka nuna min cewar baka damu da rashin lafiyar matarka ba,ta k'unyar abokanka kake right? toh bari kaji,agaskia babu inda zani naje na kwaso sanyi abanza na janyowa kaina farawa daga square one ta rashin lafiyar ba......... "

? ? "Fadima Zahra banfa sanki da Kafiya da taurin kai ba,haka kuma ban sanki da tsiwa da rashin kunya ba,infact ko bah kece da laifi ba,kina da saurin bada haquri,then why all diz all of a sudden changes? "

Gabana ne ya tsananta faduwar gaba,ah iya tsawon rayuwata nasan mutum d'aya ne ke gaya min wannan kalaman da bawan Allahn nan ya fad'a kuma shine *ENGR.MAHMOOD*.

Yana yawan cewa"Kai sister inlaw ni dai halayyarki sun mugun min,sam baki da hayaniya,baki da girman kai,komanki da sanyi kike yinsa,abinda yafi birgeni dake shine saurin bada haquri koda kuwa ba kece keda laifi ba.... "

? ?? For the very first time na samu kaina da son yin ido hudu da *Mijin Kaddarata* (another name for the novel).

Sannu ahankali na juyo da kaina xuwa gareshi.Fes! na sauke rinannun idanuwana akan fuskarsa.Hasken lanta din dakin ne ya bani damar k'arewa handsome face dinsa kallo.

? ?? Shock!startled!astonished!Amazed!.... and any other type of surprise mood u could think of,duk na shigesu alokaci daya ah sa'ilin da idanuwana da nashi suka gauraye cikin na juna.....

Kun san wah nake gani agabana??.......... =???

? A/N
Hahaha! amaryar Nakowa maida wuk'ar,duk mun riga da mun sani kece kurum aka bari cikin duhu,yanxu tambayar itace "Taya zamar auranku ze kasance? " mun fa k'osa mu gani.

? ? ?? *Hey! Hafnan's freaking fans! wai atunaninku family house za'a sauketa?? Haba its too early to start separating fight mana,atleast biko let dem enjoy their first night tukun Koya kukace? Lol

? ? ? Pls ur comments & votes are getting down,I need like 100votes before I move on,lol juz kidding amma nasan inda zan kamaku ai.....!!

? ? *IT'S YOUR LADY HAFNAN*=???
*=???SHIN SO DAYA NE?=???*

? ? ?? *INTELLIGENT WRITER'S? ? ? ? ?? ASSOCIATION*

? ? ?? *{Onward together}*
? ?? *{ we give the reader's of ours the? ? ? ? best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE =?? HEART TOUCHING d' TEARS OF SORROWS =?-? CURDLES =?
? GIGGLES =?? AND MARRIAGE THINK =???'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*'

? ? ? ? ? *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*

? ? ?? *WATPADD:HAFNANCY=???*

? ? ? ? ? *IG:Hafsy___mustee*

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ('('('

? ? _*Jinjina gareku my slay queens,my surporters,I started diz novel kamar wasa,na fara first babi sae kuma na dakata naki cigabawa,wa'ennan qawayen nawa sune suka bani gwarin gwiwan cigabawa wanda har muka Kai inda muke ayau,gashi ayau na kammala littafin *SHIN SO DAYA NE?*tare da taimakon abokan arziki masu son cigabana,don haka gabaki daya wannan littafin na sadaukar dashi agareku my lovely squad*_

?? _**Ayusher Shafi'i=???*_
_**Zatifah,marubuciyar 'Neelam'*_
? _**Nafisatouh unique=?Q?*_
? _**Sorphiyyerh Sorphie=?\?*_
? _**Maryam 'yar fillo=???*_
? _**Fatymerh Zahra _**Queen deeyana=???*_

? ? ? _*Thank you all for your support,I love you all so very much irin sosan nan,am assuring you all dat ana mugun tare har abada juz lyk magnet da qarfe '=?L?*_

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? =???=???

*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*

? ? ? ? ?? *
? ? ? *=??=??=??=??=??=?O?*

? ? Bayan Mahmood ya kammala waya da Momi,cike da tashin hankali ya dubi Fadima wacce tayi matashi da kanta asaman cinyarsa,itama hankalinta tashe ganin yanayin mijinta ya sauya ah sa'ilin da yake waya.

"Dear nah what happened? Wani ne ya mutu?" na fada cike da fargabar amsar da ze biyo baya.

Murmushin leb'en baki kawai yayi yace"Momi ce ta k'irani take fada min cewar Mubarak ya dawo don haka mu hanzarta xuwa kano yanxun nan kuwa,so Zahmood tashi muje ayita ta kare da zazzafin nama........"

Ya fadi hakan tare da mikar da kanta,ya tashi tsaye.Ni kuwa duk wani na'ura meh aiki ajikina ya tsaya cak!,alokaci daya naji duk wani kuzari dake jikina ya kau,idan ka kasa kunnuwa kuma kana iya jiyo yadda xuciyata ke bugawa da sauri da sauri non-stop.

? ?? Har ya kusa shiga dakinsa sae jikinsa ya bashi cewar bata biye dashi,da sauri ya waigo,tana nan de inda ya barta,sae binsa take da kallo,kwayar idanuwan nan nata dauke suke da tsantsar tashin hankali.Jikinsa ne yayi sanyi qalau,Sam baya son ganinsu cikin tashin hankali haka,amma kuma toya ya iya?dolene dama su fuskanceta koba jima koba dade,kuma insha Allahu daga yau za'ayi ta ta k'are don ba tsoron Mubarak din yake ba.

? ? Sannu ahankali ya taka xuwa gareta,ya tsugunna tare da dafe gwiwowinta don zaune take saman kujera.

? ? ?? "Zahmood dear nah...... " ya fadi hakan cikin wani irin siga ta salon soyayya.

Ni kuwa kamar dama jira nake ya fadi hakan,sae kawai na rusa masa kuka meh daga hankali.beyi yunkurin hanata ba,seda tayi meh isarta don kanta tayi shiru ta koma 'yar shesshek'a.Can ya janyota ta fado jikinsa,ya lalubo lips dinta ya shiga tsotsarsa don kawai ya dan rage mata damuwar data shiga ciki.

?? Nima din biye masa nayi cuz I can't hold it back,bazan iya jurewa ba.saida yayi meh isarsa sannan ya cikani,ya riko hannuna tare da mik'ewa yana fadin"Oya let's go..... "

Kokarin magana nake sae naga yayi saurin sanya 'yar yatsarsa saman lips dina,yace"Shhhhhh! Zahmood don't say anything again,Idan har kina sona then ki taho mu tafi muje ayita ta kare yau...... "

?? Runtse idanuwa nayi ba tare da furta komai ba,banyi aune ba kawai naji ya kinkimeni yayi daki dani,shida kansa ya saka min kaya,don ada daga ni sae wata yar shimi da bone shot ce,shi kuwa threequarter da kuma singlet.ya dan shirya mana wasu kayan acikin wata 'yar karamar akwati wai zamuyi weekend gaba daya ne acan,dayake yau jumma'a ce.Nide jinsa kawai nake da kuma binsa da kallo don gabaki daya hankalina baya jikina.Cikin kankanin lokaci muka kama hanya bayan na k'ira Umma nace mata mun tafi weekend kano,fatar alheri kawai ta mana.

? ?? ***
_*('KANO('*_

? ? Mubeen da Usee,sae kuma Hanan ne kadai xaune afalo,sunyi shiru kamar wasu kurame,Hanan ce kurum ke 'yar shesshekarta.Daya da daya matan ke shigowa?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ahargitse cikin kuma tashin hankali,kowacce Idan ta shigo sama-sama take gayar dashi sannan ta nufi dakin Momi.Ganin kowacce na shigowa fuska sam babu annuri akai yasa hankalin Mubeen tashiwa.'Yar wasar da suke da yayarsa Meema akodayaushe yau babu ita,hasalima sama-sama ta gaishesa kana ta wuce dakin uwarta da sauri-sauri.

?? Akalla yanxu an shafe kusan mintuna talatin kenan da zamarsa anan wurin yana jiran momi,amma shiru-shiru taki fitowa suyi maganar datace zasuyi,sae ganin yan'uwansa mata dake ta shigowa yake wanda hakan ya bashi tabbacin lallai an buga an sanar musu da dawowarsa ne shine suka taso suka zo,kuma yanayinsu ya tabbatar masa da cewar lallai babu lafiya,dakwai abinda ke kasa wanda suke tsoron gaya masa Kai tsaye.ya yanke shawarar k'ara mata wasu mintuna talatin din,wanda ze kama 1hr kenan,Idan har kuwa 1hr din ya cika kuma bata fito ba,toh kuwa shi zeje ya sameta ta gaya masa abinda ke faruwa.

? ? shesshek'ar da Hanan keyi sosae ya soma isarsa,afusace ya dubi inda take yace"Wai zaki yiwa mutane shiru ne ko kuwa? Kin de san arayuwata na tsani kananan koke-koken banza ba tare da dalili bako?tukunna mah de meh aka miki kike kuka? Huh gaya man? "

At once ta tsaida shesshek'ar,ta shiga jifarsa da kallon mamakin wannan sauyawarsa daga dawowa wai kuma duk akan Fadima wacce bema san cewar wansa ya aureta ba,yanxu muddin ya sani kuwa toh abin ze ninka wannan ninkin ba ninkin kuwa,wani dan marayan kuka ne taji yana nemar kubce mata don ita arayuwarta ta tsani ganin Mijinta cikin tashin hankali.

?? Murmushin leb'en baki kurum ya sakar mata ganin tana shirin sakin wani kukan,shi kansa yasan he's harsh on her wanda har ya lura mamakin hakan take,he juz have to act so don Momi ta tsorata da yanayinsa har ta bari ya auri Zahransa.

? ? "Jiddanah pls stop crying lyk little Jasmin owkay?" Ya fadi hakan cikin muryar lallashi.

Gyad'a masa kai tayi da sauri-sauri tamk'ar wata 'yar yarinya,alokaci daya ta hadiye kukan.

? ?? Kallonsa ya dauke daga gareta ya maida xuwa ga Usee wanda ya rafka uban tagumi da dukkan hannayensa,yayi nisa sosae cikin tunani don ko abinda Mubeen ya gayawa Hanan beji ba.

"Lil fada min,anyi mutuwa ne shine kuka kasa fada min sae inda-inda kuke tayi?huh?"

?? Wannan tambayar ta Mubeen shine ya dawo da Usee cikin hayyacinsa,gabansa ne yaji ya bada rasss!,axuciyarsa yace"Ina ganin dama mutuwar ce akayi da zefi sauki akan wannan tashin hankalin da ake shirin fuskanta..... "

Kafin yakai ga bashi amsa sae ganinsu Baba Mu'azzam sukayi da matarsa da kuma goggo Ladidi wacce ya biya ya daukota sun fado dakin hankali tashe,hijab din goggo ladidi mah bata sakashi dede ba.Abin kamar hadin baki sae gasu Momi dasu Meema suma sun fito don sunga shigowarsu cikin gidan ta window.

?? Yanayinsu ya saka hankalin Mubeen kara tashiwa akan nada,sama-sama ya gaishesu suka amsa masa,kana kowa ya samu wuri ya zauna.

? ? "Toh kode wani ya mutun ne? Ina brother Mahmood yake?tunda abin yaga na taron dangi ne,toh Ina shi yake?" Tambayar da xuciyarsa tayi masa kenan,kafin ya sake yin wani tunani yaji kawai Baba ya katse masa hanxari.

? ? "Mubarak ina son ka bani aron hankalinka da kuma tunaninka anan,ina son ka natsu ka saurari jawabina...... "

Ji yayi gabansa ya yanke ya fadi,amma se ya daure yace"Na ara maka su duka Abba.... "

? ? Yace"Madallah nagode,wato Mubarak tabbas kowanni dan'adam akwai irin jarabawar da Allah ubangiji madaukakin sarki yake yi masa domin gwada cikar imaninsa,ba kuma dan Allahn shi be sani bane yayi masa wannan jarabawar,a'ah Allah yasan komai,se de shi Allah yana yin jarabawar ne domin mu da bamu san abinda ze faru nan gaba ba.Haka kuma Allah madaukakin sarki yana yin jarabawar ne domin k'arama bawa da kuma kaishi wani matsayin da ayyukansa na ibada baze kaishi ba har abada,amma ta wannan jarabawar,idan bawa ya cinyesa,sae akaishi matsayin da ayyukansa be isa ya kaishi ba,wannan jarabawar fa dolece,don Allah madaukakin sarki yana cewa acikin alqur'aninsa meh girma acikin suratul Ankabut,yace_*"tsammaninsu su mutane suce sunyi imani abarsu haka kawai ba tare da an jarabcesu ba? (Allah yace:Lallai na jarabci wa'enda suke gabanninsu domin asan masu imani na gaskia,acikin imaninsu sukayi imani da gaskia,tsakaninsu da mahaliccinsu duk tsanani basu juya baya).Kuma lallai Allah yasan wa'enda sukayi k'arya,abaki cewa sukayi sunyi imani da Allah,amma axukatansu k'aryace suke yi,idan sunga musifa sae su juya baya suna masu kuka,Alhalin manzon Allah(SAW) yace mana yana daga cikin imani yarda da kaddara meh k'yau ko mara k'yau don duk daga Allah suke)......"*_

?? Dakatawa yayi yana duban Mubarak wanda ya nutsu sosae yana sauraren jawabinsa,kuma ya lura duk jikinsa asanyaye yake,kila zece wai meh tsohon nan yake shirin gaya min ne da har yake min wannan tunatarwar?

Goggo Ladidi itace ta soma nata jawabin"wato sae ka yarda da kaddara meh k'yau ko mara k'yau,ka yarda da cewar duk abinda ya sameka daga Allah ne,asannan ne zaka zamo mumini meh imani,toh ni Kam nace,idan har komai ya zama daga Allah ne,meh k'yau ko mara k'yau,meh dadi da mara dadi,kuka da dariya,samu da kuma rashi,nasara da kuma akasinta,toh kuwa komai abin godewa ne,abin karba ne sannan kuma abin alfahari ne,sae mu amsheshi muyi farin ciki,muyi godiya ga Allah,sae mu amsa k'iran Allah(SWT) da manzonsa(SAW),muyi haquri mu kuma sallama mu mika duka lamuranmu ga Allah madaukakin sarki,Yah Allah ka bamu ikon cinye duk wani jarabawar da zaka mana,da wanda kake mana da kuma wanda kayi mana,ka temakemu karmu fadi jarabawar don alfarman gwaninka annabi Muhammad........ "

?? Gabaki daya kowa ya amsa da"Sallallahu alaihi wa sallam.... "

? ? ahankali Mubeen ya budi baki ya soma magana"Abba wai duk meya kawo wannan tunatarwar ne?ku fada min ko wani nawa ne ya rasu shine kuke tunanin idan har kuka gaya min toh ina iya tada hankalina shine kukayi tunanin kwara ku soma da min tunatarwa?Yah Mahmood ne ko kuwa Zahrata? "

?? Babu wanda beji gabansa ya fadi ba jin cewar direct ya ambaci sunayen culprits din nasa,shiru akayi na tsawon wani lokaci,shi kuwa ya baza kunnuwa yana bin kowa da kallo daya bayan daya,yana meh jiran yaji wani ya budi baki ya bashi amsar tambayarsa.

?? Runtse idanuwansa yayi yana meh tunano abinda Hanan ta gaya masa dazu,maganar tata ce take masa kuwwa akunne,ji yake kamar yanxu take masa maganar.

? ? _*"Haba mijin hauwa'u yanxu har xuwa wannan lokacin baka cire Zahra aranka ba?aganina ya kamata ka shafeta acikin rayuwarka because I think Zahra ta maka nisa ba kadan ba........"*_

?? Karde hakan na nufin Zahra ta jima da mutuwa shine ta gaya masa hakan?kode dalilin daya saka dan'uwan nasa yake ta raina masa hankali kenan har kuma ya dena daga k'iransa kawai don kada atada masa hankali ko ya shiga cikin wani hali?

? ? **
Seda muka soma biyawa gidanmu muka ajje akwatinmu sannan muka kamo hanya xuwa family house.seda kuma Mahmood yayi da gaske kafin ya samu na shiga gidan,ganin ransa ya soma bacewa ne ya saka kawai nayi shahada muka shige.

? ? Gabana ne ya hau dukan chalugude asa'ilin da muka kusanto entrance door.Cak! na tsaya,naki gaba haka kuma naki baya,Mahmood ne ya juyo yana dubana,yace"Zahmood yadai?"

? ? "Dear nah am not ready to face Mubeen,idan na shiga ince masa meh?ni matar wansa ce? Wallahi I can't........ "

Axuciye yace"Shikenan Fadima tunda ban isa na saki abu kiyi ba,ba damuwa kina iya yin duk abinda ranki ya keso...... " ya shige ciki abinsa ya barta nan tsaye.
? ? ?
? ? Da hanxari na take masa baya,adaidai lokacin kuma Mubeen ya bude idanuwansa yana fadin"No! No! No!!! Fadima Zahra tana nan araye bata mutu ba....... "

Kowa ya bishi da kallon mamaki jin furucin daya fito daga bakinsa,jin shigowar mutane ne ya maida hankulansu ga kofar shigowa.

?? Babu wanda beji gabansa ya tsananta faduwa ba ah sa'ilin da kallonsa ya sauka kan halittun da suka shigo.Zumbur! Mubeen ya mik'e ya nufesu,cike da farin ciki yake fadin"I knew it,wallahi na fada zahrata bazata tab'a tafiya ta barni yanxu ba........ "

? ?? Rungumar Mahmood yayi yana murna,yace"Brother an k'ira an fada maka na dawo shine kayi min wannan big surprise din ta hanyar kawo min my Zahra ko?tank u very much amma meyasa ka dena daga call dina Idan na k'ira? "

Shi kuwa Mahmood wani uban d'aci ne yaji aransa ah sa'ilin da mubeen ya k'ira Zahmood dinsa da 'Zahransa',ai yanxu Fadima tasa ce shi d'aya.

?? "Brother say something mana,wai meyasa Kowa ya maidani mahaukaci ne?tun dazu naketa tambaya amma Kowa ya maidani shashasha,wai meke faruwa ne da har ake b'oye min?"

Cikashi yayi ya nufi Fadima wacce take tsaye bayan Mahmood dukkan ilahirin jikinsa rawa yake tamkar wacce ake kad'awa gangi.

? ? "Zahrata nasan ke kadaice zaki iya fada min abinda ke faruwa,sabida irin son da kike min shi ze saka bazaki iya b'oye min komai ba,so now tell min wat's happening? "

? ? ? ? Baba shine ya taso ya kamo hannun Mubeen ya mai dashi mazauninsa yace"Mubarak zauna ayi magana ta fahimta... "

Ya dubi inda su Mahmood ke tsaye yace"Mahmooda kuma kuzo ku sami wuri ku zauna...... " suka bi umarninsa.

? ? Baba ne yake gayawa Mubarak cewar ai gashi-gashi,be bari ya k'arashe ya mik'e zumbur!,idanuwansa sun canza launi xuwa pure hot red,ya dubi inda Mahmood ke zaune yace"Mahmood kaci amanata,ashe dama komawarka Zaria sabida ka samu kusanci da budurwata ne?ashe duk wani taimakon da kake ta ikrarin zaka min kanka kake tayiwa?Haba shiyasa Jiddan Mubarak ta canza min,kwata-kwata Idan mukayi waya bana gane kanta,koda na dawo mah Kowa beyi murnar dawowata ba sae mah tashin hankalin dana lura kowa ya shiga,atunaninku ni Mubarak ban yadda da kaddara bane ko menene da har za'a tara min mutane ana kuma min nasihu? Toh ku sani na yadda da ita,na yadda cewar abinda Allah ya rubuta cewar ba naka bane tofa komin tsiya bazaka tab'a samunsa ba,ni tun farko mah da'ace ka nuna min cewar kana son Zahra,toh wallahi ina iya bar maka ita sabida nima ina son naga kayi aure Yah Mahmood.......... " shiru yayi jin wani irin azababban ciwon kan dake nemar masa sallama.

?? Duk jikin kowa awurin seda yayi la'asar,masu hawaye nayi,masu shesshek'a suma ba'a barsu abaya ba,sosae Mahmood yayi dana sanin biyewa son xuciya,ahankali ya soma magana"Brother haqiqa ban k'yauta ba dana biyewa son xuciya,cin amana yana daga cikin halayen munafurci,cin amana yana daga cikin abubuwan da suke tauye imanin mutum,cin amana yana daga cikin abubuwan da suke qasqantar da darajar mutum awajen Allah,cin amana yana sanya mutum yayi baqin jini acikin al'umma,haka kuma zalika cin amana yana zama sanadiyyar dulmiyar da mutum acikin wutar jahannama.......... "

?? Mubarak baze iya jure ganin dan'uwansa na suffanta kansa da wa'ennan zantukan ba,da sauri ya isa inda Mahmood din yake ya rungumesa"No brother pls stop it,ka dena suffanta kanka da wa'ennan zantukan naka da babu dadin ji,wallahi ni baka ci amanata ba,dama can haka Allah ya rubuta cewar kai din Mijin Fadima ne bani ba,kawai ya tsara cewar ta sanadiyyata ce zaku had'e,come on brother wallahi ni na yadda da kaddara,dadina ayanxu kayi aure kamar yadda muka jima munata mafarkin faruwar hakan,and am assuring u dat Fadima Zahra will make a good home for you....... "

?? Kamar hadin baki,kowa ya dau tafi da hamdala ga ubangiji,basu taba tunanin cewar komai zaizo musu da sauqi haka ba.(ni kaina Hafnan da fans dina mun dauka za'a yi yakin duniya ta uku ne kafin adaidaita,sae gashi Mubeen ya tabbatar mana da cewar shi din cikakken Mumini ne meh yadda da kaddara meh k'yau ko mara k'yau).

?? Baba ya sake nasiha meh ratsa xuciya da gangar jiki,haka goggo Ladidi,da Mami da kuma Momi kowa seda ya tofa albarkacin bakinsa,daga bisani aka nemi gafarar juna da k'yau,sannan kowa ya watse.Washeqari seda muka sake cimma Mubarak agidansa,dayake aranar ya tattara iyalinsa suka koma gidansu,muka sake nemar gafararsa da k'yau,yace mana"Haba Yaya wannan wani irin abu ne?Nace maka wallahi baka min laifin komai ba,haka Allah ya tsara abinsa tun fil'azal,yanxu Idan nayi wani tashin hankali hakan na nufin ni din ban cika mumini meh kuma imani ba,tunda har na kasa yadda da kaddara,ina son ka sanya aranka cewar Fadima dama can ba tawa bace,Kila babu alheri ne acikin aurena da ita,da'ace na nace saina aureta,Kila bayan auran musifu kala-kala su kunno kai,don haka ni nama yi farin ciki da ban auretan ba,kaine alherinta shiyasa Allah ya hadaku,fatana ayanzu Allah ya yaye min sonta axuciya..... "

?? Haka muka baro gidan jikinmu asanyaye.Kwananmu biyu muka dawo Zaria.Bayan kwana biyu kuma Mahmood ya kaini ganin gida,toh agaban Mahmood dinne na fayyace musu abinda yayi ta faruwa.

? ? "Ikon! Allah kenan,dama haka Allah ya tsara abinsa,Allah ya dada baku zaman lfy.... " shine abinda Abba da Umma suka fada.

Su Ash dasu Leedar kowa mah yayi matuqar mamaki da farin cikin ganin komai yazo da sauqi.Suma suka qara mana addu'ar samun zaman lfy.

***
_*BAYAN WATANNI BIYU*_

Hanan ta sauka lafiya tare da taimakon Mubarak,da kanta ta haihu wannan k'aron lfy qalau kuwa sabida ba k'aramin kulawace ta samu awannan cikin ba,sannan kuma addu'a baya faduwa Allah ya qarbi koke-kokensu ya sanya ta sauka lfy.Qatoton baby meh kosasshiyar lafiya ta haifo,yaro kamar Mubeen yayi kaki ya tofar.Ana gobe suna,Mahmood ya kaini kano,ah family house na kwana,washeqari da sassafe muka dunguma xuwa gidan suna,su Umma sun min kara ba kadan ba,ita,Ash,su Lubna da kuma Suhaima wanda Leedar ne ya bata izini suka zo.Ranar suna yaro yaci sunan Mahaifinsu Mubeen wato *MUSTAPHA*,se aka sakaya ana k'iranshi da *IRFAN*.,bayan kwana biyar da yin suna,Hanan ta shirya ta tafi maiduguri wajen iyayenta don kam ta dade bata je ba.se bayan 40days ta komo Kano.

? ? ?? ***
_*AFTER NINE MONTHS*_

? ?? Allah ya saukeni lafiya,yayi min baiwar da ba kowacce 'ya mace yake yiwa ba,wato haihuwar ya'ya uku atake.Mahmood ya rasa inda zesa kansa don murna,tuni ya saka aka yada agidajen radio.Har kukan murna seda yayi,shi meh son 'ya'ya kamar meh sai gashi tashin farko Allah ya azurtashi da 'yan uku,maza biyu da mace daya,mazan duka suna matukar kama ne dashi,hasken fatata ce kawai suka dauka,macen ne kawai take kama dani kamar an tsaga kara an k'arya.Mahmood yayi barin naira da kuma rarraba kyaututtuka ah haihuwar 'yan uku,ni kuwa k'yautar wata sabuwar dalleliyar motace ya min,yanxu motocina sun zama biyu kenan,ga tasa daya ban,sannan kuma da nawa da nake hawa alokacin ina budurwa wanda Abba ne ya saka aka kawo min ita alokacin mun dawo daga kano sabo-sabon amarcina.

?? Ranar suna,yara suka ci sunan,baba mu'azzam ana k'iransa da Hassan,dayan kuma sunan Abbana aka saka masa wato Sa'ad,ana k'iransa da Hussain,macen kuma Zaynab aka saka mata,ana kiranta da Afra.Bayan suna na kira Ash na mika mata tsohuwar motata kyauta ko don zirga-zirgar school.Har kuka seda tayi min don murna,tana ta godiya da shima triplets albarqa.

? ? ? ****
Rayuwa ta mik'a,Mahmood na musamman ya samo min 'yan aikin da zasu dunga kula da triplets,har makaranta suke bina se su tsaya awaje harna fito lectures,sannan na karbesu na basu mama.watanninsu hudu-hudu da haihuwa amma idan ka gansu zakace sun kai 9months ne sabida yadda sukai bulbul dasu da wani irin k'yau sabida wadatacciyar kulawa da suke samu daga iyayensu da kakanninsu,kai infact kowa nason 'yan ukuna,babu wanda ze gansu beyi sha'awarsu ba.

? ? ?? Abangaren Mubeen kuwa,tuni ya manta da batun wata Zahra don Hanan ta zage damtse akan nada tana nuna masa tsantsar soyayya da kuma kulawa wanda ya zarce nada.wani irin soyayyace yake wa Hauwa'u Jiddah ayanxu wanda ko kadan beji hakan ba alokacin da yake tare da Zahra.Anan ya gane kuma ya tabbatar wa Kansa da cewar lallai _*SO_* na hakikanin gaskiya kwara _*DAYA_* ce tak!.kuma shi yakewa Hanan dinsa.

? ? ? Bangaren Suhaileedar suma ba'a barsu abaya ba don rayuwar auransu mah abar kwatance ne,haihuwarta de shiru tukunna because planning sukai don ta samu nutsuwar karatunta wanda watanni kalilan ne ya rage mata ta kammala final year dinta.Tuni Leedar da Fresh suka soma bautar kasarsu ah federal high court dake nan zariar wadda justice ne ya shige musu gaba har suka Samu aka barsu anan,da zarar sun gama kuma zasuje law school na shekara guda ah Lagos before they will be call to

Please Login or Register in order to submit comment