You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
Downloaded From https://tknovels.com.ng [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/EZyeAwHEGGhJz1pRBmmale
NAGA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★𝒫𝒶ℊℯ 3
Da k’yar Umma Ta runtse idonta ta furta “Innalillahi wa inna ilaihirraji’una…” wasu
hawaye na zubo mata. Abba cikin k’arfin hali ya saki kansa da ya ji ya masa wani
irin duum ya furta “Uban me kika masa ya sake ki”
Ban amsa ba illa damk’e hannun Mami da na yi a cikin nata hannun cikin tashin
hankali kaf jikina rawa kawai yake yi.
“Kin ga ko Fateemah abinda nake gaya miki, wannan shagawab’atan da kike yi ba hanya
bace mai b’illewa, ga shi nan yanzu abin da ta janyowa mana ba mamaki bata kai
budurcinta gidan Miji ba”
Umma ta furta cikin wata irin karyayyiyar murya da ta bayyana karyewar zuciyarta.
Mami a kufule ta furta “To hasashenki bai zama gaskiya ba, tunda ga shi a rubuce ya
furta da kansa bai d’ora mata idda ba, idan kuwa haka ne ta ya zai san bata kai
wani budurci ba? Kawai dai butulcin y’ay’a maza zai nuna muku.”
Abba ya saka hannu ya wafce takardar da take hannun Mamin idanunsa ya zuba akan
gajeran rubutun mai saka dubban bak’in ciki a zuciya. Ya lumshe idonsa bayan ya
tabbatar da abinda Mamin ta fa’da. Wani irin bak’in ciki ne yake nuk’urk’usar
zuciyarsa don har yana jin wata irin suka a zuciyar tasa. Ya lumshe idonsa yana
tunanin Halaccin da Ustaz Ahmad zai yi masa kenan? Duk da k’ank’antar y’arsa ya
cireta a makaranta ya ba shi aurenta shine yau daga tarewarta ya saketa?
Ya d’ago idanunsa jajur yana kallona ya furta “To me kika masa ya sake ki Aysha?
Don kalmar bakomai ba zan yarda da ita ba ko duk jikina kunne ne.”
Na runtse idona ina sake jin takaicin Ahmad a raina. Ji dai yadda ya sanya iyayena
b’acin rai. Umma da Mamina hawaye suke. Shi kuma Abba nasa idanun ya tara hawayen
sai dai ba su kai ga zubowa ba. Amma bakinsa har rawa yake. “Wallahi Abba ba abinda
na masa, ka kirasa ka tambayesa ka ji idan baka yarda da ni ba…” “kira kam Ai ya
zama dole….” Ya fa’da yana mik’ewa ya fice daga parlorn yana danna wayarsa fuskarsa
a murtuke. Umma kallo guda ta mana ni da Mami itama ta mik’e ta shige d’akin Abba.
Ni na san a lokacin ji take kamar zuciyarta ta fito don tsananin b’acin rai.
Mami na ta dafa ni tana furta “Share hawayen ki Aysha, ni na san ba abinda kika
masa. Iskancine kawai da kuma nunawa mutane isa, ba su suka nuna masa sha d’in wata
tsiya ba ce. Kwanta abinki ki yi barci don na san jiyan ba wani isashshen barci
kika samu ba. Bari na je na samu dandazon munafukancan y’an saka ido na san me Zan
gaya musu.
Daga haka itama ta mik’e ta fice tana d’an murmushi tana cije bakinta ha’de da
k’wafa duka lokaci guda.
Lumshe idona na yi wasu hawaye suna zubo min. Na saka hannu na share hawayen ina
sake tsinewa Ahmad a zuciyata.
Madadin barci tunanin rayuwata ne ya dawo min daki-daki cikin kwanyata girmana
k’iruciyata da ha’duwata da Ahmad da zan ce a yanzu ha’duwar tamu ta zame min
mummunar k’addarar da zan ce da ina da iko da na koma baya na goge ta tas daga
cikin shagon rayuwata…..
★★★
Alhaji Imam Khalil shi ne sunan mahaifina, da kowa ya san shi. Asalin sunan
Abdurrahman ne, amma sakamakon ya ci sunan kakansa ne yasa ake ce masa Imam.
Mahaifina su biyu ne kacal a wajen iyayensa, daga shi sai k’anwarsa Dije, da muke
kira Umma Dije, sun taso cikin tsananin soyayyar Iyayensu game da kulawa.
Kasancewar mahaifinsa babban malami hakan ya sa ba su ingantacciyar tarbiyya, don
duk wanda ya ha’da da su dole ne ya yaba da nutsuwarsu, da hankalinsu. Mahaifina
tun yana shekara ashirin da uku aka masa auren fari, da Ummana Sa’adatu, y’ar
k’anin Babansa wanda da kansu suka k’ulla soyayyarsu, kuma kowa ya yi tsananin
murna da farin ciki da hakan ta kasance. Abbana da Ummana sun yi zaman aminci, ta
yadda suke ganin girman junansu, suka kuma gina rayuwar aurensu da soyayya mai
tsafta da babu algus a cikinta.
A shekara ta biyu da aurensu ne Umma ta ta samu cikin Yaya Muhammad, bayan shi aka
haifi Yaya Sadik, sai Yaya Umar, sai Yaya Usman, lokacin da aka haifi Yaya Usman
babu da’dewa Abba na ya auro Fateema Mami na, haifaffiyar fulanin yola. Su kuwa su
Abbana fulanin potiskum ne.
Tunda Mami ta shigo gidan ta fuskanci Umma na bata kishi da ita matsayin k’anwarta
ta d’auketa, sai itama ta zubar da shawara da zugar k’awaye itama ta kwantar da
kanta suke zaune lafiya.
Shekararta d’aya a gidan, Umma ta sake haifo Yaya Ali ita
Kuma ko b’atan wata bata yi ba tunda ta zo gidan. Bayan shekara d’aya da rabi sai
Umma ta sake samun ciki ta haifo Yaya Hamza. A kansa ne Umma ta ce ta bawa Mami shi
duniya da lahira lokacin da ta tabbatar da shigar cikina bayan wata uku da
haihuwarsa. Sai dai me? Wani ikon Allah yana komawa hannun Mami da wata d’aya
Ubangigji ya karb’i ransa.
Mami ta shiga damuwa sosai, don haka Umma ta ce ta kwantar da hankalinta tana
haihuwa zata bata abinda ta haifa. Tunda likitoci sun tabbatar Mami ita da haihuwa
sai wani ikon Allah.
Cikin farin ciki ta dubi Umma na ta ce “Ko mace ce?” Umma ta ‘d’aga kai duk da a
k’asan ranta tana jin Anya zata iya bada y’a mace, tunda abu ne da take mafarkin
son samunsa saboda duka yaranta maza ne. Shima Abba ya sha furta mata duk sanda ta
haifi Mace zata sha gatan da baa tab’a yiwa wani a gidan ba.
Lokacin da aka tabbatarwa Umma da ta haihu kuma mace ta ce da ni ta ji hankalinta
ya tashi matuk’a, ta kuma yi dana sanin furtawa Mami bada kyautar abinda ke
cikinta. Sai dai ba yarda ta iya ba zata iya kallon idon Mami ta ce ta janye
kyautar ta ba. Ga likitoci sun tabbatar mata ya zama dole ta hak’ura da haihuwa in
dai tana son lafiyarta ta ‘dore.
Don haka ranar suna Umma ta ce ta bawa Mami ni. Ba wanda bai dinga mata kallon
mamaki ba. Mami kuwa tsabar murna rungume Umma ta yi tana hawayen farin ciki. Ba
wanda bai fa’di wautar Umma ba sai dai ta saka yatsa ta toshe kunnenta ta kuma
kulle duk wata k’ofa da y’an gulma zasu mata tasiri. Ta mik’awa Mami ni ta ce “Na
bar miki ita Fateema duniya da lahira shayar da ita kawai zan dinga yi.” Mami ta
rungumeni tsam a k’irjinta cikin tsabar farin ciki tana yi mata godiya don da gaske
ta ji da’din kyautar.
Mami da kanta ta saka min suna Nana Ayshatu, Saboda ta da’de tana son sunan. Ba
wanda ya k’i amincewa tsakanin Umma da Abba duk da su ma cikin su kowa nada sunan
da yake burin saka min. Amma suka amince da Ayshatu da Umma ta saka min.
Ta mayar da ni hannunta, sai dai idan ina son Nono ta kai ni na sha wajen Umma da
daddare kuwa k’arfi da yaji ta mayar da madara ce abincina don ba zata yarda na
dinga kwana a wajen Umma ba.
A farkon shekaruna na taso cikin matuk’ar shagwab’a da sangarta, Don Mami bata son
ko fa’da a min balle duka yanzu duk girmanka zata maka rashin
Mutunci. Ana min magana zata ce a k’yaleni yarinya ce, Ko Umma da take yawan
tsawatar min sai da suka yi tashin hankalin da ta tattara ni ta watsar ta daina yi
min fa’da. Ta ce min sai dai kawai a koda yaushe bakinta cikin yi min addu’a take.
Idan kuma ta faki ido ko idan Mami bata nan tas take wanke ni da fa’da. Wani
lokacin nasiha.
Tun ina yarinya ban saba saka manyan kaya ba sai k’ananan kaya don haka na tashi
kamar y’ar turawa, musamman ina da hasken fulani da gashi mai tsayi. Ina da tsiwa
ta gasken gaske da rashin kunya don haka yayyena ke cin Uba na. Adon gashi Mami
take min sosai a wannan shekarun duk inda na shiga sai an yaba ni. Mami cikin jin
da’di da farin ciki Zata ce “Tubarkallah, maye ya ci kansa kurwar AYSHA ya fi gaban
ci.”
Umma da taga na yi shekara goma cikin kwantar da murya ta dinga bawa Mami shawarar
a dinga saka min kayan hausawa ko na saba da su. Amma Mami ta yi funfurunfus ta k’i
har ma ta fa’dawa Umman maganar da ta tsaya mata a rai cewa ta yi “Umma kada wata
rana fa ki ce zaki karb’e AYSHA a wajena, don naga kamar kina tantama da tarbiyyar
da nake bata?” Hankali tash Umma ta dinga bata hak’uri tana furta “Ba nufi na kenan
ba Fatima, amma Allah ya baki hak’uri In sha Allah ba zan sake magana akan abinda
ya shafi AYSHA ba.” “Ya dai fi.” Mami ta fa’da fuskarta a ha’de ta kuma ja hannuna
muka bar wajen. Tun daga ranar bata sake magana ba. Su Yaya Muhammad ne ma basa
gani su k’yale su kuwa Mami wankesu take tas.
A makaranta na taso da hazak’a da wata irin kwanya mai d’auke karatu duk girmansa.
Ina shekara goma na sauke Alkur’ani. Shekara sha d’aya kuwa ina Js One.
Sanda na shekara sha biyu ne, ba zan manta ranar da komai ya sauya a gidan mu ba.
Aka wayi gari Mami na ta tattara duk wasu kayan sawata ta rabar da su. Na sha kuka
a ranar don ina matuk’ar son kaya na. Bata kulani ba ta dai ja ni mun fita. Kasuwa
muka shiga ta dinga siya min atamfofi da laces da yadin Hijabai. Da after dress
masu kyau. Muka biya wajen tailor ta saka ya auna ni don a yi min d’inki. Ta kuma
ce masa urgent take so.
Tun a shagon ta saka min d’aya daga cikin dogayen hijabs d’in da aka d’inka min. Ta
Kuma saka sabon nik’ab. Farin ciki ne ya cika zuciyata don ni kaina ina son yin
shigar da dinga suturce jikina musamman tuni na gano
Na fara shiga sahun y’an matanci.
Muka dawo gida. Umma da su Yaya suna zaune suka bi mu da kallo baki sake, don kuwa
na d’age Nik’ab d’in ina kallonsu ina murmushi. Mami itama dariya take tana bin su
da kallo. “Lokaci ya yi da AYSHA zata dinga suturce jikinta ba don komai ba sabida
bana son wani ya min shigar sauri. AYSHA ba zata yi aure ba sai ta yi masters, don
haka har fuskarta ban amince ta bayyanata a waje wani ya gani ba……”
Ga duk mai son bibiyar littafin nan don Allah ya shiga link d’in nan don ba lallai
na jure yawon tafiya group group yin posting ba. Abin da yawa Nagode…🤗
★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NAGA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 1★
Wannan page kacokam d’insa sadaukarwa ne ga members na MIKIYA WRITERS…
★★★★★★★★★★★★★★
Yau ne k’arshen shagalin da ake gudanarwa a ranakun bikin aurena, yau ne dinner
party wacce aka shirya ta ta mata zalla a Amani Event center.
Ban ha’da dinner ta da maza ba kasancewar daga ni har angon ustazai da bama son
gurb’ata bikinmu da abubuwan da suka sab’awa shari’a da Addinin musulunci. Neman
albarkar auren kawai muke ba neman suna a duniyar social media ba, don haka bikin
nawa ya zama kamar lami miya ba nama saboda rashin warwasawa da na k’i bari y’an
mata su yi. Asalima ko ki’da baa saka ba sai ranar kamu ne ma aka saka ki’dan
k’warya shima na hana kowa ya yi vedio gudun ya’da b’arna a bayan k’asa. Hakan da
na yi ya burge mutane da dama yayin da wasu suke ganin tsabar iyayine da son a sani
ba wai addini ba. Ban da mu ba don na san Allah da zuciya yake aiki. Kuma mahaifina
ya yi farin ciki da hakan sosai musamman ganin k’ank’antar shekaruna bai saka na
ajiye addini da koyarwar Manzon Allah ba.
Hankalina gaba d’aya ba ya wajen dinnerr duk da ina tsintar wa’azin da Malama
Zainab Jafar take yi a wajen Dinnerr ka’dan-ka’dan. Farin cikin da nake ciki ne ya
yi min yawa sanin cewa yau zan angwance da masoyina wanda nake mafarkin kasancewa
matarsa a koda yaushe. Ji nake kamar na jawo lokaci a tashi daga dinnerr ko ma koma
gida mu je mu shirya a sada ni da gidan Mijina wanda nake matuk’ar d’oki shauk’i da
son gani. Tabbas fuskata kawai zaka kalla ka tabbatar da zakwa’din da zuciyata take
ciki.
Duk da gefe guda na zuciyar tawa a sanyaye yake da kuma rauni wanda zan iya cewa
ina jin sa har k’asan raina ba na komai ba ne sai na rabuwa da gidan mu da Ahalin
da suke cikinsa. Ina son iyayena kamar yarda zuciyata bata son rabuwa da Yayyena
maza da na kasance mace k’wal a cikinsu.
Ashe ban sani ba wayo a kai min daga wajen Dinnerr zaa kai ni gidan Mijina ba don
komai ba sai don an san yanayin shak’uwata da Abbu a lokacin rabuwarmu tabbas sai
mun saka jama’a kuka, musamman kuma kada Yayyena maza suji labari.
Mamana da Mamina suna wajen su sun halarci wajen Dinnerr don haka bayan tashi daga
dinnerr suka zame suma ban sake ganinsu ba sai jin hannun Aunty Sharifa na yi tana
fa’din “Tashi Aysha mu je daga nan sai gidan Mijinki kuma shikkenan Aysha ta
girma.” Sai sannan zuciyata ta sake tsinkewa fargaba ta shige ni sanin cewa da na
yi daga nan sai gidan Mijina shikkenan ana nufin na yi sallama da iyayena? Idanuna
na zubawa Aunty Sharifa murya a raunane na ce “Mami na fa..” “Mami ta tafi gida
Aysha ba zata iya ganin kukan ki ba..” Jikina ne ya yi sanyi don tun safiyar ranar
na lura da rashin walwalar Mami duk da k’ok’arin dannewa da take, amma hakan bai
b’uya a cikin k’wayar idanunta da suka tara ruwa ba. Ni na san Mami bata son wannan
auren don dai ba yarda zata yi ne a matsayin ta na marik’iyata kawai kuma kishiyar
uwa ba wacce ta haife ni ba. Shi yasa bata da damar da zata nuna hakan.
Wata ajiyar zuciya na saki da na hango Mamina na tahowa fuskarta d’auke da damuwa
sai dai tana k’ok’arin dannewa wajen sakin murmushi ta iso wajen. Ta zare hannuna
daga na cikin Aunty Sharifa ta maye da nata ta ja ni ba tare da ta yi magana ba
muka wuce. Hakan da mutane suka gani yasa suka biyo mu wasu da yawa a wajen Mamina
ta burgesu yayin da wasu na san ba mamaki abinda ta yi d’in su kira shi da iyayi.
Mamina da kanta ta shigar da ni d’akin aurena, hannuna damk’e cikin nata tana gaya
min addu’oin da zan yi a cikin kunne na. Na lumshe ido ina fa’dar addu’ar da duk da
na iya ta a yau saboda raunin zuciya sai na ji ta b’ace min b’at. Lokacin tafiya na
yi wani kuka ya kufecewa Mami ta rungumeni ina kuka tana kuka da k’yar mutane suka
lallashemu aka samu aka b’anb’are Mami daga jikina aka fita da ita. Kukan na sake
ruhshewa dashi ba wanda ya yi mamaki don an san shak’uwar da take tsakaninmu da
Mamina.
Haka ina ji ina gani kowa ya tafi daga gidan aka bar ni ni ka’dai kamar mayya. Sai
sannan fargaba ta sake shiga jikina saboda ina da tsoro musamman na san gidan
babban gaske ne. Tun ina saka ran shigowar ango har na saduda na yaye mayafin dake
jikina zuciyata cike da mamakin ko me ya hanashi shigowa haka. Har na d’au wayata
zan kira shi sai na ji ina jin kunya kada ya ce har na matsu da ganinsa na kira shi
don haka sai na mayar da wayar kawai na ajiye na cigaba da kewaye d’akin da idona,
wani irin farin ciki ya ratsani ganin irin namijin k’ok’arin da iyayena suka yi don
su fitar da ni kunya.
Sai sha biyun dare sannan na dinga jin takunsa kamar daga corridor hakan yasa na yi
saurin jan mayafi na na suturce jikina.
Daga jin yarda yanayin bugun zuciyata ya sauya na san shi ya shigo jikina kuma ya
ba ni ni yake kallo, amma ko me ya hana shi k’arasawa inda nake. Ta cikin mayafi na
dinga lek’ashi sanye yake cikin wata irin Alkyabba mai kyau da santsi kalar blue
black da ta amshi farar fatarsa. Saman jallabiyar Alkyabba ce golden kamar yarda
dai ya saba shigarsa a kullun yauma hakan ne. Kansa da hula mai shegen kyan tsiya
wacce hausawa suke cewa Tashi ka fiye naci sai dai wannan mai tsadar ce. Tuni
d’akin ya baje da wani irin k’amshin turaruka da ya danne nawa da na wutan da aka
saka a d’akin. Kana jin k’amshin turaren zaka san mai tsada ne na masifa…
Sai da na kai idona kan fuskarsa sannan gaba na ya yi wani irin fa’duwa ganin yarda
fuskarsa take a ha’de murtuk kamar bai tab’a dariya ba. Kamar ba Ustazuna mai yawan
fara’a ba. Me zai saka ya ha’de rai a wannan daren da yafi ni zakwad’in zuwansa?
Duk da dama ba ma’abocin dariya da k’yakyatawa bane amma ma’abocin murmushi ne don
ya ce dariya na rage imanin Mumini.
Ganin ya fara taku zuwa inda nake yasa na sake jan mayafi na k’udundune fuskata don
ban shirya amsa sunan mara kunya a wajen Ustazuna ba.
Yanayin takunsa yanayin yarda bugun zuciyata ke sauyawa da k’arfin gaske don na san
dai ba mamaki yau Ustaz ya kai min runguma abinda muka da’de muna mafarki don da
gani har shi na san mun yi dauriya…
“AYSHA!” Ya fa’da cikin jarumar muryarsa da take bayyana kasantuwarsa Namijin
gaske..
Mamaki ne ya kusan kasheni jin a yau ya ambaci sunana gatsau ba wani sakayawa kamar
yarda ya saba kira na da “Eesha ko ya ce Aysha ta..” Duk da haka ban yi nawar
d’agowa ba na zuba masa ido ina kallon yarda yake kallona fuskarsa a ha’de ya mik’a
min takardar hannunsa tabbas yanayinsa ya firgita ni…
“Ungo wannan.” Ya fa’da da wata irin shak’akkiyar murya, yana d’auke kallonsa daga
gani na. Leda ce ya mik’a min. Daga haka ya juya ya fice a zatona zuwa zai yi
shirya ya dawo. Duk da zuciyarta na gaya min akwai matsala ba haka Ustazuna ya
kamata ya tare ni ba ni da nayi zaton runguma da kyakykyawan kiss da na da’de ina
mafarki…. Ko dai na masa wani laifi ne da ban sani ba?
Ajiyar zuciya na saki ina jan ledar da sauri. K’amshin kazar Yahuza suya ya dake ni
da Ice cream masu sanyi. Jikina har rawa yake don idan ban manta ba rabona da
abinci tun safiyar ranar don haka kawai sai na samu kai na da fara cin kazar na sha
ice cream d’in. Na saka hannu na jawo leda zan d’au lemo idona ya kai kan wata
farar enveloped. A zatona mantawa ya yi don haka ban ma bu’de ba na ajiye a gefe
ina jan kwalin exotic na fara d’addaka shi a cikina. Na tattare kayan idona ya sake
sauka kan enveloped da a bayansa na ga sunana b’aro b’aro. AYSHA IMAM KHALIL…
murmushi na saki ina tunanin ko wata kyauta Ustaz d’in ya bani don haka na jawo da
sauri na farke enveloped d’in da yake ta zuba k’amshin turarensa.
𝒜𝓈𝓈𝒶𝓁𝒶𝓂𝓊 𝒶𝓁𝒶𝒾𝓀𝓊𝓂.... 𝒩𝒾 𝒜𝒽𝓂𝒶𝒹 𝒮𝓊𝓁𝒶𝒾𝓂𝒶𝓃 𝒮𝒶ℯℯ𝒹 𝓃𝒶 𝓈𝒶𝓀𝒾 𝓂𝒶𝓉𝒶𝓉𝒶
𝒜𝓎𝓈𝒽𝒶 ℐ𝓂𝒶𝓂 𝒦𝒽𝒶𝓁𝒾𝓁 𝓈𝒶𝓀𝒾 𝒹𝒶𝓎𝒶 𝒷𝒶𝓉𝒶 𝒹𝒶 𝒾𝒹𝒹𝒶𝓉𝒶 𝒾𝒹𝒶𝓃 𝓉𝒶 𝓈𝒶𝓂𝓊 𝓂𝒾𝒿𝒾
𝓉𝒶 𝓎𝒾 𝒶𝓊𝓇ℯ......
Kasa k’arasawa na yi saboda yarda na ji numfashi na yana neman d’aukewa na dinga
ware ido ina jin zuciyata na wani irin bugu..
Tabbas NAGA RAYUWA Me yake shirin faruwa da ni ne? Saki a daren aurena daren da
muke d’oki da zakwa’din zuwansa ni da mijina ya da’de yana gaya min yana jiran
ranar da zai rungumeni dtazo saboda kiyeye dokar Ubangiji. Me na yiwa Ustazuna ya
sake ni? Na shiga uku!! Haka na furta a zuciyata..
To fa! ko me AYSHA ta yiwa Ustaz Ahmad ya zabga mata saki a daren aurenta? Duka
yana cikin littafin NAGA RAYUWA da zai dinga zuwa muku daga Alk’alamin…..
ℯ★
✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NAGA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 2.
✍🏽
★
…..
Kuka ne sosai ya kufce min, irin kukan nan da kake jin d’acinsa har k’asan ranka.
Kuka mai sauti da Amon muryar karaya a cikinsa. Me Na masa? Shine tambayar da nake
wa kaina na kuma kasa lalubo amsar. Abinda zuciyata take gaya min nake k’aryatawa
ko nak’i ko na so dole ne na gasagata zuciyar tawa dole Butulcin d’a namiji ne ya
biyo ta kai na. Ko kuma ya yi haka ne don ya gwada mizanin soyayyarsa a zuciyata.
Amma ya rasa ta hanyar da zai gwada sai ta kalmar saki? Kai abinda kamar wuya Ustaz
da wayonsa ba zai yi wasa da saki ba Halak d’in da ya san Allah baya so, kuma idan
aka aikata shi ar’ashi tana girgiza. Dole ba don na so ba na amince da shawarar da
zuciyata take ba ni, na danganawa sashensa na je na tambayeshi abinda ke faruwa…
Tsam na mik’e na shiga laliben sashennasa, kasancewata bak’uwa a gidan bai saka na
sha wahalar gane k’ofar sashen nasa ba. Daga can corridor tsakanin k’ofar da zata
kai ka nawa sashen. A hankali na tura k’ofar na shiga. Shiru babban parlorn nasa
baka jin k’arar komai sai na A.c da take ta aiki ba ji ba gani. Fitulun wajen ma a
kashe suke. Karatun k’ur’ani ne kawai yake tashi a parlourn cikin k’ira’ar shureim.
Na gama zagaye parlorn da idona ban gan shi ba, don haka na isa k’ofa guda da take
parlorn da na tabbatar nan ne d’akin nasa.
Yana zaune a gefen gadon daga k’asa saman sallaya ya kifa kansa a jikin gadon. Jin
motsina ya saka shi d’aga kai. Wata irin fa’duwar gaba ce ta same ni ganin yarda
idanunsa suka ka’da suka yi jawur kamar gaurashi. Idan ba idanu na ne suka min gizo
ba sai naga kamar hawaye ne a kwance a k’asan idanun. Mayar da idonsa ya yi ya
lumshe bai sake kallona ba alamu sun nuna baya son gani na.
Zuciyata a jagule tana wani irin bugu da k’arfin gaske na k’arasa wajensa. Zama na
yi a gefen gadon murya cike da rauni na furta “Ustazuna, wata takarda na gani a
cikin kayan da ka kawo, zuciyata ta kasa amincewa hannunka ne ya rubuta ta. Ban
kuma fahimceka ba.”
Shiru kamar ba zai amsa ba, idanun dai still a lumshe daga inda nake ina ganin
yarda k’irjinsa yake bugu. “Ustaz, magana fa nake.” “Taki ce.” Ya fa’da muryarsa a
shak’e. Ido na waro ina furta “Saki Ustaz!” Ya bu’de idon nasa ya nutsasu cikin
nawa, a hankali ya d’aga lab’b’ansa kamar baya so ya furta “K’warai kuwa AYSHA, don
haka ki tabbata kin fice kin daga gida k’arfe bakwai na safe….”
Ina daga zaunen na dinga jin wani irin jiri yana d’ibana. “Ko zan san dalili?”
Wannan karan madadin amsa min mik’ewa ya yi yana zabga tsaki ya furta “Ban sani
ba…” Shiru na yi na lumshe idona ina hak’ilo da yak’i da b’acin ran da yake son
dannen numfashi. “Tashi ki fita zan rufe k’ofata..” Ya furta yana nuna min k’ofa..
Ya fa’da yana juya min baya… Jikina a salub’e na mik’e ina jin kamar k’afarta wa ba
Zata iya d’aukata ba saboda rawar da jikina yake yi na zallar tashin hankali. Da
k’yar na ja jiki na isa bak’in k’ofar daidai lokacin da na jiyo ina kallon Ustaz
ina cije leb’ena shima kallon nawa yake hawaye ba zuba daga idonsa. Na ja k’ofar da
k’arfin gaske na fice daga d’akin.
Zuciyata har Tafasa take saboda tsananin b’acin rai. Na zauna a gefen gadona ina
mayar da numfashi tabbas Uztaz ya cuceni a shekaruna sha takwas kacal ya mayar da
ni k’aramar bazawara? Shin halaccin da zai yiwa Iyayena kenan? Tabbas ya amsa
sunansa Butulu? Yanzu me Zan je na ce a gidan mu? Ya rasa irin sakin da zai yi min
sai irin wannan na tozarci da wulak’anci saki a ranar aurenka daren amarcinka? Yaya
mutane za su yiwa abin fassara? Dole ne a jefa min ayar tambaya musamman kowa da ya
san Ustaz ya san Babban Malami na da ake watsa tafseer d’insa a gidajen sunna na
t.v. Babban Malami ne da gwamnatin k’asa baki d’aya take ji da shi duk da dai ba
wani shekaru ne da shi ba ba zai wuce shekaru 32 ba.
Toilet na shiga bayan da zuciyata ta tabbatar min ba ni da wanda zan fuskanta a
wannan gab’ar sai Ubangiji. Don haka na yi alwala na fito na tada sallah akan
daddumar da Abba ya bani d’azu da safe ita da Alk’ur’ani da Riga da Hijab na sallah
farare tas har da carbi da wani turare mai k’amshin gaske, yana furta “AYSHA, kin
ga
Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500