You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

G matarka a kusa ''insha Allah gobe
zandawo'' tana fadar haka ta mike tajuya ta futa'' kuka Habib ya saka tare da rufe
idonsa gam kamar wanda yaga fatalwa, itako saliha ganin haka yasa ta karasa gabansa
tace'' honey ga abinci kabude idonka nabaka abaki.......

Me?" Yayi saurin bude ido yana kallonta akidime'' abaki fa'' gaskiya yarinyar nan
kinga makwanci na'' dan uwar....... Wani yunkuri saliha tayi tare da juya kwayar
idonta ta zuba masa idanunta manyamanya tana kallonsa'' a rude habib yace'' ranki
shi dade meyayi zafi haka?" Ina zaki naga kinmiki da sauri'' haba ke kuwa zauna
kada ki gaji da tsaywa''murmushin gefan fuska saliha tayi tace'' bazan zauna ba,
jiranake ka karasa zagarmin uwa tukunna dan naga alamar bakasan darajar iyayeba''
tabe fuska Habib yayi kamar zaiyi'' kuka yace'' wallahi Ni ba zaginki zanba'' taya
za,ay ace na zagar miki iyaye sai kace bansan darajar suba'' haba amarsu ta, kimin
rai dan Allah kada ki sake wujijjigani a sama karki manta Ni mijinki nefa'' ya zaki
dinga dagani sama kamar wani dan baby'' dan Allah kiyi hakuri'' nasan matata saliha
ce ,kuma ''yar islamiyya me tarbiyya''zaki iya min uzuri Please my wife kada kiki
yafewa mijinki'' uhm lumshe ido ta danyi ta bude sannan taja dogon numfashi'' a
ranta tana cewa'' inama ace Habib duk wadannan maganganun da yake fada har cikin
zuciyar sa'' daidai kash bahaka bane'' tasan tsorone kawai ''duk da batasan abin da
ya faru da mijin nataba har ya gigice haka'' abu daya zata iya tunowa shine'' dukan
da yayi mata ...



SAFIYYA
Umma dan Allah kiyi hakuri'' ki daina sawa kanki damuwa akan abin da ya faru''
wallhi nayi hakane domin na nemawa Xulaiha yanci '' umma kema kinsan bazan taba
mantawa da abin da ya faruba''muddum Xulaiha jini nace''kuna dugon jininta na
gudana a jikina sai na nemarmata ''yanci, insha Allah sai ruhin ''yar,uwata yasamu
salama akan zaluncin da Habib ya aykata'' mata, tana fadar haka ta fashe da kuka''
umma ce tace, amma Safiyya ina tunanin abin da kikai biki kyau taba, Meyasa zaki
saka saliha a cikin Bala'i tun kafin saliha tasan Habib Xulaiha tasanshi haka nima
na sanshi'' mugun mutum ne, bazaki iya dashiba ,abin da nakeso dake shine'' ki
hakura da daukar fansar nan Allah zai saka mata'' shi ubangiji''baya bacci aduk
inda yake yana gani kuma ya naji'' nasan cewa da ,ace Xulaiha tana raye bazata taba
bari kice zaki dau fansa ba'' no umma Xulaiha kalmarta ta karshe kafin kalmar
shahada'' ita kada na bar jininta ya tafi abanza'' kada na bar wulakantata da akai
ya zama ba,a sauki matakiba'' tace tana so wanan abin ya zama zina ga
''yanbaya.....


Pege17


Bazaka ci abincin bane''uhm dan Allah kada kisaka min guba aciki saliha wallhi
nayi nadama'' au wai tunani kakeyi zan iya kasheka ''uhm Ni ba irinka 蓳 aci,,
tunyanxu har kafara tsoron mutuwa'' bekamata kafin ga jin tsoron taba, sabi da a
hannunka mutuwar dan adam ba komai bane'' wani drum Habib yaji gaban sa ya fadi
jikinsa ya fara rawa''tinani ya tafi saka makon tino wadda tataba fadamasa irin
wann kalmar arayuwarsa'' bagama tinaninba ya tsinkayo Muryar saliha tana cewa''
Habib muddum digon jinina yana gudana ajikin ''yan,uwan bana nadama donka kasheni''
daga lokacin nan ina bukatar kafara irga ranakun mutuwarka'' arazane Habib ya bude
ido yana cewa innalillahi nashiga uku'' no''no'' karya ne''hakan bazai taba faruwa
ba, kallonshi saliha tai tace'' menene yafaru honey'' shima zuba mata ido yayi
cikin mamaki yace'' saliha wai bake kikayi magna bane''?"nikuma a,a Ni bance komai
ba me kagani'' atsorace yashiga waige waige yana duba gefe da gefansa'' kozai ganta
amma ina babu wan da yake gani sai dai saliha kawai'' idonsa ya runtse tare da
budesu'' saiga sababin hawaye sun zubo masa'' masu zafi, sai kuma ya saki murmushi
yace'' Xulaiha........


What'' bangane ba Habib wacece Xulaiha?" Uhm yayi murmushi ya kauda kai'' nace
kafadamin wace Xulaiha da har kake fadar sunanta a gabana bayan Ni ina matsayin
matarka, ko kunya ta ma bakaji kake fadar sunan mace a gabana''tafada cikin masifa
tana hura hanci''

# Habib kam mikewa zaune yayi ya tsura mata ido sannan yace'' saliha zan fadamiki
wacece ita amma badan ina jin tsoron ki ba'' sai dai kiji irin halayen mace ta
gari'' me kana nufin Ni bata gari bace ba?"a,a ba haka nake nufiba'' abin da nake
nufi Xulaiha ta fita daban daga cikin mata'' duk da ba,a san dan aljanna ba''bamu
san dan wutaba''amma ina kwatata zaton Xulaiha ''yar aljaninace, hawayen da yake
tare wane suka karasa zubowa akan kuncinsa'' amma duk da haka be tsaya da magana ba
yace'' Xulaiha ta kasance macece mai tsananin son iba da, ga kirki ga nutsuwa''
baruwan ta dakowa'' tun da Xulaiha take bazaki tabajin ance ga abokin fadanta ba''
Xulaiha tana tsananin sona don sai nace miki tun da nake a duniya babu macan da
tataba sona kamar yadda Xulaiha tasoni'' Xulaiha ta kasance ''yace ga murugayi ado
Ahamad zubar wan da akafi sani da ado'' shahararren dan kasuwa me jida kudi'' kaf
nahiyar afrika'' mahaifina yana da tarin dukiya amma bekai mahaifin Xulaiha kudida
mulki ba''amma duk da haka Xulaiha bata yi la,akari da kudinsuba kawai soyayyata
take bukata'' sai dai kash naci amanar ta'' tabbas bazan taba iya mantawa da
Xulaiha arayuwa taba ''aduk lokacin da karar agogo ta buga daidai da second zuwa
minti 24 awas zuciya ta bugawa take, a kullum a tsorace nake bani da burin da
yawuce na sake saka Xulaiha a idona'' ina son na nuna mata kalar soyayyar da zuciya
ta take mata'' sai dai lokacin ya kuremin Xulaiha ta min nisan da bazan taba iya
taddo taba....awayen idon sa ya share yace'' bazan cigaba da miki bayanin wacece
ita ba'' ....

Meyasa bazaka bani complete din labarin ba',Meyasa kake boyemin abubuwa, gaba
kidaya ka tashi ka daure min kai'' narasa inda ka dosa''Kuma gashi kakasa fadamin
ina Xulaiha take a halin yanzu?"

Bazan fadamiki wacece itaba'' dakuma abin da yafaru da ita ba, domin wanan sirri na
ne''kingane....

Murmushi saliha tai tace'' okay bazan tilasta kaba, amma kasani komai wuya duk
rintsi abin da kake boyewa zai fito fili'' sanan asirinka zai tonu anan zan ji ko
wacece ita...


Me ''kewai mekike nufi dani, kidai turoki akaine domin kisan ko ita wace, hhhhhh
a,a kokadan Ni ba turoni akaiba'' ya ka tsorata ne bayan Ni kace karuwa ce bani da
wani mahimmanci a rayuwarka ''nifa ''yar matsiya tace, mezai hadani da budurwar ka
tafada tare da kashe masa ido Daya'' arazane Habib ya kalleta'' yace budurwa ta
kuma''yaushe nacemiki ita budurwa tace, ke kifadan gaskiya ke wacece?" Hhhhhh Ni
mutum ce me daraja kamar kowa'' ina fatan kagane tana gama fadar haka ta mike ta
barshi a gurin ta shiga ban 蓷 aki ta dauro alwala''


Tana shiga Habib ya janyo wayarsa ''ya danna wata number wadda akayi save da F. J.
X, bugu daya aka dauka , ko sallama babu aka fara magana, akace'' Ranka yadade''
dawata matsalar ne?" Habib ne yace'' babbama kuwa kana inane?" Ina Jigawa ''
haryanzu ban kammala wanna aykinba, domin yarannan'' fa sun yi wuyar gani'' uhm
kanaji ko F.J.X inso ka tambayar min ''yayan ado Ahmad zubar nawane , sannan
inason ganin hotunansu a yanzu'' kai Ranka yadade akwai kurafa'' sojoji da ''yansan
da nemana suke'' yanzuma wata mafaka nasamu na buya''kafin na bar garin ,idan nace
zan tsaya tambayar ''yayan ado kamani za,ayi''kaga kuma asirin mu zai tonu.....


馃Turkashi gaba kidaya kaina ya kulle'' barasa inda abin ga ya dosa'' wacece''
Xulaiha?"




MAR'ATUSSALIHA


Pege 18


Tana shiga Habib ya janyo wayarsa ''ya danna wata number wadda akayi save da F. J.
X, bugu daya aka dauka , ko sallama babu aka fara magana, akace'' Ranka yadade''
dawata matsalar ne?" Habib ne yace'' babbama kuwa kana inane?" Ina Jigawa ''
haryanzu ban kammala wanna aykinba, domin yarannan'' fa sun yi wuyar gani'' uhm
kanaji ko F.J.X inso ka tambayar min ''yayan ado Ahmad zubar nawane , sannan
inason ganin hotunansu a yanzu'' kai Ranka yadade akwai kurafa'' sojoji da ''yansan
da nemana suke'' yanzuma wata mafaka nasamu na buya''kafin na bar garin ,idan nace
zan tsaya tambayar ''yayan ado kamani za,ayi''kaga kuma asirin mu zai tonu.....
Babu damuwa insha Allah zanyi kokari''okay ya katse wayar tare da sakar ajiyar
zuciya ,ya taune lebe''dai dai lokacin saliha'' ta fito daga toilet ta kara so inda
yake tana sakar masa murmushi' shikuwa kau da kai yayi tare da runtse idon sa yana
ji ajikinsa kamar wani abu zai faru dashi muddum yacigaba da jintsoron saliha''
tabbas Yakamata na nemi mafita ,yafada a cikin zuciyar sa.


India.....


Zaune yake a kan kujera 3ster hannunsa dauke da computer ya na dan dannawa a nutse
yana yatsine fuska kamar Wada aka yiwa dole sanye yake da riga tishet da bakin
turoza na maza iya guywa gabaki daya ragowar gangar jikinsa a waje'' gawani gashi
kwantacce da ya kwanta s jikin 茩 afarsa abin sha,awa ''juneid jiyayi kamar an
tsikareshi da sauri ta mike ya nufi kofar fita'' tare da bawa ''yan aykinsa umarni
su kullo gidan su biyoshi'' babu musu suka fito sannan suka shiga mota'' basu tsaya
a ko inaba sai filingirgi'' fitowa sukayi sannan suka nufi bakin wani jirgi me kyau
da tsari Wada aka tanada dominsu'' shiga sukayi suka tsaya cak'' kamar sakago''
shikuma juneid ya zauna a kan kujera yayi shiru kamar me tunanin wani abu gashi ya
kurawa hundin jirgin ido''..

Jirgi ne ya tashi suka fara keta hazo suna tafita ,akalla saida sukayi kwana 1 a
hanya sannan suka isa garin Katsina..



19


Wayar sa ya dauka ya Shiga contact ya danna wata numba da akayi save da my
dad ,dialling din number ya shiga yi bugu daya akayi aka dauka tare da cewa,
Asssalamu alaikum, wa,alaikumussalam dady Ina good morning, morning my son "Ina
fatan dai kana lafiya ko ,lafiya kalua dada amma Daman Ina airport ne inason azo a
daukeni , airport?Wai yanxu maganar da muke dakai kana Nigeria ?eh dady Ina jira ,
okay yanxunan ko zanturo a daukeka , okay Dad think you.

Dady Yana kashe wayar ya shiga sanar wa da hajiya fateema isowar juneid ,Nan take
tashiga murna Tana cewa,najidadin hakan sosai Allah ya iso dashi lafiya yanxu waye
zaka tura ya dakkoshi ,kadai San Habib bashi da lafiya yau dinan aka sallameshi
daga asbiti ,uhm ba Habib ne zai jeba anisa ce satané,anisa Kuma ?ta sake tambayar
sa ,eh anisa inason tun daga yanxu sufara fahimtar zunansu ,ko za a samu ya amince
ya aureta" uhm momy tayi ajiyar xuciya tare da shakar dogon numfashi tace to Allah
ya sa adace dagan Kuma tamike tanufi kicin domin shiryawa juneid kayan makulashe,
shiko dady .ameen yafada tare da kwallawa anisa Kira,


Anisa ko da tunda sukayi fada da hajiya Adama tacire hannunta daga kan ta,ta hado
kayanta tadawo gidan su habib ,kullum Tana zaune adaki it's kadai batada ayki sai
kuka .


Yauma kamar kallum Tana zaune Tana aykin kukan tajiyo muryar dady Yana
kiranta ,dasauri ta tashi daga kwanciyar da ta, ta goge hawayen fuskarta ,ta Mike
jiki a sanyaye tanufi kofar fita ,wadda zata sadata da babban falon gidan,...


Dasallama dauke a bakinta tace assalamualaikum, Amin wa, alaikumussalam dady ya
amsa tare da sakar mata murmushi yace ,Anisa karaso mana ,karasawa tayi ta durkusa
akasa tare dacewa barkanka da wanan lokacin ,naji kakirani, eh Daman sonake kije
airport ki dakko yayanki juneid,yau ya iso Nigeria,

Washe Baki Anisa tai tare dacewa Tom dady ,Tana fadar haka ta Mike da sauri ta
shige dakinta, ta sauya kaya ,masu kyau ,sanan ta dau Kee ta nufi parking space,ta
shiga mota ta dauki hanyar airport,


Tana Isa ta yi parking ta fito, ta dudduba amma Bata ga inda yakeba, wani ma aikaci
taga Yana doso inda take ,dakamar bazata saurareshi ba sai dai tatsaya har ya
karaso ,Yana zuwa yace, ranki shidade ,kije yallabai Yana jiranki a wancan
jirgin ,shikadaine yace ki karasa ki taho dashi.

Yana gama fadar hakan bejira amsar da anisa zata bashiba ya bar gurin,

Itako Anisa tsaki taja tare dacewa lallaima wanna Dan rainin hankalin, wato ma irin
iskancin dayake a India shizaice zaimana anan kut to ma idan naje mezan masa, to ko
goyoshi zan ,goyo Kuma saikace yaro tafada tare dajan wani tsakin tace bara dai
naje naga mezan masa, takawa tashiga yi anutse harta Isa bakin matattakalar jirgin
ta fara takawa har tashiga, can ta hangosa a zaune idanunsa alumshe ya Dora kafa
daya kandaya, karasawa tai tayi tsaye akansa batare da tace komai ba, gaba kidaya
tabi ta susuce tama rasa mexata cemasa sabi da tsabar yarikitata ,tabbas tayarda da
kanta tasan juneid ba tsarar aurenta bane, shiko juneid magna yasomayi tare da bude
jajayen dabbansa yace ke baki iya sallama bane, haba wa ay Anisa Kara rikicewa tai
ganin yadda dimple dinsa suka lotsa abin gwanin Sha,awa ,tsawa yadaka mata tare
dacewa bamagana nake mikiba ,Nan danan Anisa ta dawo cikin hayyacinta tace am naam
na am mekace Tana magana Tana sosa Kai, dasauri tafara magana bakinta Yana rawa
tace Yaya Ina kwana, banza yamata tare da tashi ya futo ya barta atsaye Baki asake
Tana binsa da kallo, ...


Har juneid ya kurewa ganinta ya shiga mota tana tsaye Tana bin hanyar da kallo,
harsai da ma,ai kacin gurin yamata magana yace ta fito, tunna ta fito da sauri
tanufi mota ,tna zuwa tagansa agidan baya ,babu yadda ta iya haka tashiga ta zauna
a gaba tafara tuki ,suka dauki hanyar zuwa gida......


20...


Tom tafiya sukeyi Basu tsayaba har suka Isa bakin katafaren get din sake manne
ajikingidan alhaji alhassan wato mahaifin juneid,. Hown sukayiwa megadin gidan
cikin hanzari ya shiga bude musu get din gidan tare da yimusu sannu dazuwa, Anisa
ce kawai ta amsa shiko juneid kawai kai yadaga masa suka huce, parking spece ,
parking din motar Anisa tayi ,batare da tacewa juneid komai ba tabude murfin motar
ta fito, fitowarta kenan saiga ma,aikatan juneid sun karaso sunyi hown anbude musu,
suna shiga sukayi parking din wata jibgegiyar mota kirar kasar America, fitowa suka
shigayi daya bayan daya suna kamewa atsaye daya daga cikinsu me ya nufi motar da
juneid yake ya bude kofar tare da sa hannu ya fito dashi,sann ya daukeshi
cak ,badireshi a ko Ina ba sai a babban falon gidansu ,inda momy da dady suke zaune
suna jiran karasowar sa, anisa kam tsayawatai tama kallon ikon allah daga bisani
kuma ta bi bayansu cikin falon.


Dashigarsu dady da momy suka tashi tsaye ganin yadda katan mutum ya dakko juneid
kamar wani karamin yaro ,dasauri dady yace subahanallahi Yana ga kadakko
shi ,meyasameshi? Yafada a tsorace, batare da mutumin yace komai ba ya karasa ya
ajiye juneid a kan kujera sann ya tsaya cak a gaban juneid,kallonsa juneid yayi
tare da cewa jaka iya tafiya,babu musu ya juya ya fita "shikuma juneid ta shi yayi
ya karasa gaban dadynsa tare da durkusawa yace good morning my sweet dad Ina fatan
dai nasameku lafiya,shiko dad Baki da hanci yasaka Yana kallon ikon Allah ,daga
bisani kuma yace "au Daman Wai iskancine irin naku na yaran zamani ,kalau kake
amma kasa wancen jibgegen mutumin me kama da samudawa ya dakkoka ,dariya juneid
yayi wadda ta karamasa kyau da kwarjini yace au dad kenan dashi kadai kagani
guduwa zakai,dariya dad yayi yace"wlh guduwa xanyi ace inban da rashin mutunci irin
na yan bana bakwai inakai Ina wancan basamuden, sai kace wani jariri kull
kakiyayeni Junaid, uhm alhji kenan Ay su yarannan dasun ji kudi ya zauna sai
sutsiri iskanci kala'kala ,shidai juneid bece komai ba saima kallon momynsa da
yayi yace mom nayi missing dinki sosai amma kafin Nan inajin yunwa, dariya momy tai
sannan tace to ay gashican tun dazu ya kamma la Kai yake jira, okay ya fada tare da
cewa bari nafara watsa ruwa tukkuna don garin naku akwai zafi ,Ina fatan dai an
gyramin bedroom Dina, daga masa kai mom tai ,sannan ta koma ta zauna, Tana zama
saiga daya daga cikin ma,aikatan juneid ya shigo ma,ana dai wan da zai kaishi
bedroom, Yana zuwa ya da hannu ya daga juneid cak tare da hayewa matattakalar benen
dashi juwa bedroom din sa, . Baba dayansu wadan da suke falon Bin su kawai sukai da
kallo ,momy kam harda salati Tana cewa, yanxu juneid wankanma yimaka za,ai oh ni
fateema wannan Wace iriyar Al,adace....


Itako Anisa tun da Takoma dakin ta taketa faman kaiwa da komowa, tana ta tinanin
mafarkin da iyayenta suke kan cewar juneid zan aureta, ita dai tasan ko giyar wake
Tasha bazata hada kanta da juneid ba sabi da tasan nagaba yayi gaba nabaya sai
lanari Junaid ba ajinta bane Dan duk yadda take fasalta yanayinsa to ya huce
haka....


Bayan juneid yayi wanka Yana zaune a gefan bed dinsa ana samasa kaya, sai ga
wayarsa ta hau ruri , wazai gani doctor devit ne,Kira na farko juneid ya dauka
tare da yin sallama yace" assalamualaikum, doctor daga can bangaran doctor ya amsa
da Amin wa alaikumussalam, sir Daman wannan Mara lafiyar da take kwance a asbitin
muce ... Dasauri juneid ya katseshi dacewa doctor kardai kace min yarinyar Nan ta
mutu, no bahaka nake nufiba inason nace maka jikin nata Yana Dan samun sauki,
musamman ma bangaren tabin kwakwalwar da tasamu, okay godiya nake doctor to amma ya
maganar feyden da aka matafa dasauki dai ko, eh sir dasauki sosai Dan har ayki ma
munyi mata okay Tom ba damuwa ,yanzu Ina Nigeria naje gida katsina indan nadawo zan
shigo okay sir thank Yana gama fadar hakan ya kashe wayar...

Juneid kam fadawa yayi dogon tunani akan wannan Maralafiyar tasa tabbas idan ya ga
ma hada hujjoji akan wannan yarinyar ,indai Al,amarinnan gaskiya ne babu makawa
saiya kwatar mata hakkinta ......


*********************************Am saliha zoki taimaka ki bani ruwannan
nasha,wallahi na gaji daker nake iya tashi, babu musu saliha ta Mike ta dakko masa
ruwan ta bashi , sannan ta koma ta zauna tace ,Allah sarki Ashe zaka iya Shan abin
da kazama karuwa ta dakko ,shidai Habib bece mata komai ba saima kallon ta dayake,
domin shikadai yasan rin abin da ya tama idan yasamu lafiya akan saliha, murmushi
yasakar mata tare da cewa ,saliha naji dad yace ya juneid ya dawo gashi inason zuwa
na ganshi sai dai daker nake iya tashi, salihace ta kalleshi tace ay kam dai
yakamata, sai ka bari ka warke ko kajira yazo har gidannan...




****Umma yakamata kije gidan saliha kigano mana lafiyar ta, kimanta da komai
ni nasan ayadda kike ayanzu Habib bazai taba iya ganekiba ,uhm baxaki ganeba
safiyya har yanzu ke yarinyace ,ninasan menake tinawa idan naga yaronnan, Kay umma
kenan gaba kidaya hankalina ba a kwance yake ba ,bamusan a halin da saliha takeba a
yanxu, kitaimaka kije, a,a safiyya ke kije ki dubata, umma idan naje komai zai
lalace Dole idan habib yaganni zai gane shirinmu akanshi, bazai ganeba safiyya
inason kije kigano mana, idan kin tashi tafiya kisaka nikaf kinji, Tom shikkenan
umma INSHA ALLAH xanyi hakan.....


....... WASHEGARI .....


ALHAMDULILLAH duka duka anan nakawo karshe wannan book mesuna MAR'ATUSSALIHA book 1
Sai mun hadu acikin littafi na 2 wan da shine zamu fada cikin cakwakiyar
littafi ,dagan Kuma sai book 3 wan da ashine zan warwaremuku komai idan ubangiji
yabani aron rai da lokaci littafi MAR'ATUSSALIHA n'a 3 paid ne 400, kacal gaduk me
bukatar fara biya tun yanzu ga account number 2478578665 zanth Bank hindatu
Yusuf ,sai atura shaidar biya ta wannan layin 09166764540, gamasu tura mana katin
waya sai a tura ta wannan number 09166764540 MTNngd

Daga taku har kullum HAFSAT UMAR DANGORO yar mutan bakin rafee

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment