You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
tana rokona nayafemata nayakuri da sauransu, but I was strong, shegiyar halitta ce Hassana, ga bakin rai, ga taurin kai da bakin zuciya, yau wai har nine take koroma warning........" nan yashiga bama Attajiri labarin abinda yafaru, saida yagama tsaf Attajiri yace "karka karaya, koma wani kalan wulakanci ne kai doubling dinshi kana mata, sannu sannu zata fara kuka tana rokonka yafiya, yanzu dai mubar zancen Hassana, Yaya Saudat kaji dadinta kuwa" dan shiru yayi saikuma ya yatsine fuska yace "ba laifi amman ba kaman Hassana ba, Hassana daban ce wlh, ni inda zata kwantar dakanta tazo tana kuka tana rokona da wlh na sadu da ita, nai kewan kasanta sosai, wajen dabanne kawai bazaka gane abinda nake fadiba" dariya duk sukayi, Attajiri yace "bari kaji xancen Hassana yadena damunka, mata fa biyu gareka yanzu kana gamawa da Saudat zakaje dakin budurwa dazaka bare dakanka daga leda kaci kai nak, koda ta tafi gidansu karka kuskura kabita zata dawo da kanta kaman yanda tadawo dafarko, sanan kama manta da ita, duk randa kasami chance kana gasamata wulakanci dazaisa tadinga hawaye zata baka hakuri, ai wlh kayafemata ahaka batare daka ciremata wanan girman kanba kaci baya nagayamaka, kaci baya" nan yacigaba da bashi shawarwari na banza.......
Da kyar ta lallaba takoma dakinta tai salla sanan ta tashi taja key motarta da wayanta, ko kadan bamata gani da kyau kanta wani irin bugawa yake kaman mutuwa ma zatayi, lallabawa tayi tana dafa bango tafito tasauko kasa sanan tafito compound, direban Alhaji kadai tagani a compound yana wanke sauran motocin Alhaji, yanayin yanda yaganta yasa dasauri yazo wajenta yace "Hajiya bakida lafiya ne"? Kasamagana tayi tabashi key dinta kawai tace "gidan.....mu" dasauri yakarbi key yana kallonta saikuma yadan kama gefen hannunta yace "sannu muje ki shiga mota" har mota yakaita yasata sanan yashiga gaba yaja, yasan gidansu hakan yasa yadauki hanya yakaita harchan gidansu.
Horn yayi agaban gidansu saida gateman yafito yaduba sanan yakoma da sauri yabude musu gate din, suka shiga ciki yay parking sanan yace "Hajiya mun iso" shirun dayaji yasa da sauri yawaiga baya, kaman ma sandarewa tayi tana zaune inda take a sume bata numfashi wani irin bude kofa yayi yafito saikuma yay ihu sosai yace "help, Hajiya ba lafiya" dasauri mai gadin yazo wajen dayaga yanda Hajiya take saiyawani irin famfala damugun gudu yay flat dinsu, ko one minute ba'a yiba saiga Mahaifinta wani black beauty magidanci kakkyawa yana sanye da suit kaman yashirya zai fita aiki ne, gefenshi kuma mazane manya guda biyu saiga Maman su (step Mum) tafito dasauri itama, suna zuwa wajen motan babanta yafara kai hannu yatabata saikuma yajuyo yakalli yaron dake bayanshi direct yace "Mustapha zoka dubata" matsama yaron yayi yazo yadubata, sanan yakalli dan uwanshi Hydar yace "mukaita ciki" daukanta sukayi Mama tafara salati tace "maiya sami Hassana, kai direba maiya sameta? Nan yafada musu yanda yaganta daharma yadauko ta. Afalon Mama yakaita suka kwantar da ita tareda ciremata hijab, dukansu sai kallon yanda tarame suke sanan yayan nata yafita da sauri yadauko medical kit dinshi yazo bp ta yafara dubawa kawai saiya saki salati, Baba da Mama dake kanshi sukace "meya faru Mustapha"? Baice musu komiba yashiga hada wata allura sanan yakama hannunta yamata a vein saikuma yamata daya a bumbum sanan yasauke ijiyan zuciya yakalli Baba yace "Baba kaga yanda jininta yahau kuwa wlh tana gab da samin paralyze, meke damunta hakane?" Fashewa da kuka Mama tayi tace "tunda naga yarnan kwanakin baya nasan bata hayyacinta, Hassana menene meke damunki? Har Hussaina nakira nacemata takirata taji ko kalau take" duk tsayawa sukai akanta suna kallo sai gashi chan tadanyi motsi dasauri Baba yazauna agefenta dan yanason yaranshi ba kadanba, kanta yashafa yace "Yan Biyu" dan haka yake kiransu tun suna yara, bude idanunta tayi ahankali ta kalleshi saikuma tafashe musu dakuka sosai dayasa jikin kowa yay sanyi. "Kinci abinci"? Baba yatambayeta ahankali, girgizamai kai tayi hakan yasa ya kalli Hydar yace "kawomata shayi da chips" dasauri yafice baiwani jimaba yadawo da shayi mai kauri da chips da egg, Da Mama da Baba ne suka dagota atare sanan yadauki tea yabata takarba kai tea bakinta tayi takurbi kadan saikuma tasake fashewa da kuka ahankali tace "Baba kaima kasan tun ina yarinya am a strong girl, Baba alot are happening agidana, I thought I can handle it alone, maybe matsalan daga nine, nafara zuwa ganin therapist, I did everything cus I want the marriage to work sabida su Khalil da Khalid, but I've heard enough........." tana kuka tasanar dasu daga farko har karshen abinda yake faruwa batare data musu karya ko dayaba, nan fa Baba yafara, Baba wani irin mutum ne dako kadan baiso yaji wani d'a namiji ya wulakantamai yarshi, shifa kafin ma yabaka auren yarshi zai gayamaka idan kagaji da y'ata kadawomin da abata gida batare daka cutarmin da itaba yarana sune rayuwana sune komi nawa, dakaci zalunsu gwara kaci nawa. Shi Baba yamafi iyaye mata supporting yaranshi, cikin fushi sosai yafara masifa yana kallon su Mustapha yace "angaya mishi banson y'ata ne dazai wulakantamin ita haka harda maran min ya? Koyazaci nagaji da itane eh Mustapha? Shi waye waye ubanshi waye kuma yadaure mishi gindi anan Nigeria dazai daga hannunshi yabugi y'ata" yanda Baba yahau zazzaga bala'i bil hakki yasa sai suka shiga bashi hakuri da kyar yay shiru sanan yajuyo ya kalli Hassana dake kuka sosai, yace "stop crying, karki kara kuka sabida shi" share hawayenta tayi tass tana haki, sanan yatashi yace "nabaki 24hrs ki yanke decision din dakikeso kinason cigaba da zamadashi ko bakiso" sanan yajuya yakalli Mustapha yace "zaka tafi da ita asibiti ne ko zaka mata treatment anan"? Ahankali yace "zanje nasayo magunguna anan zan mata" gyadakai Baba yayi yace "tom" saikuma yacigaba da masifa yace "koku su Mustapha ban yarda ku wulakanta matan kuba, ba'a rayuwa haka, yaza ayai ku dauko yara daga gatan iyayensu ku auro saiku kawosu kuna wulakanta su kun zaci iyayensu basa sonsu ne eh? Koko basuda gatane? Idan kaji bakason mace ta gundureka ka tsaneta karabu da ita baka wulakantata kana azabtar da ita ba, inna dinna yusrun, shi addininmu fa mai sauki ne, wlh bazan lamunta ba, zaisan yatabamin y'a" yasakai yafice daga dakin fuuuu yaran suka bishi.
Ahankali Mama takama hannunta tarike tana shafawa tana kallon yanda take kuka saikuma ta girgizamata kai cikeda taysayinta tace "I want you to think this through yar albarka, ke kikasan mijinki, banda haka aure is not do or die, any decision dakika daura, we will support you, kece ke zama da mijinki bamu iyayenki ba, dan haka kiyi tunani mai kyau kinji" gyadamata kai tayi ahankali saikuma tadago kanta tarungume Mama sosai tace "nagode Mama" girgizamata kai tayi tace "karki karamin godiya gabaki dayanku yaranane, Allah yamuku albarka, mezakici naje nadafa miki dakaina" ahankali tace "tuwo damiyan kubewa danye" maidata tayi ta kwantar tace "tom shikenan bari naje" ta tashi tafita daga dakin itama.
Wuraren 12 Mustapha yadawo yashiga mata treatment sanan aka kawo mata tuwonta taci sosai sai bacci, dukansu tabasu tausayi, koda ta tashi da yamma taji dadin jikinta sosai aka sake kawo mata wani abincin batawani ci dayawa ba amman ciwon yaragu sai kanta dake kwankwasa haka suka cigaba da managing lafiyanta.
Bai dawo gidanba sai da magrib, yana shigowa Saudat tafesamai gulma da already direban shima yafara fadamai komi, dudda yaji wani iri amman ko ajikinshi yace bazai kiraba yacigaba da more amarcin shi dudda bini bini tana fadomai arai amman yaki kira.
Bayan kwana uku!
Tana zaune afalon Mama taji sauki sosai Mama na mata tsifa Baba ya aiko Hydar yakirata, gabanta saida yafadi amman tadaure tadauki mayafi tayafa sanan takalli Mama tace "Mama zoki rakani please" Mama bata misaba ta tashi sukai falon Baba, wanda daga Baba sai yayyinta aciki, wuri tasamu tazauna akasa sanan tace "gani Baba" gyaran murya yayi yace "Yan biyu dafarko nabaki 24hrs saikuma dan kaina nakara lokaci, nabari kika sami sauki dan kisamu ki kara tunani da kyau, dan haka inaso ki gayamin gaskiyan komi dake ranki dakuma hukuncin dakika yanke" shiru tayi nadan lokaci saikuma ahankali kanta nakasa tace "Baba kowace diya mace da abinda takeso takuma ke bida agidan aurenta, ni awajena kudi ko yawan dukiya bashine dadin aure awajena ba, kwanciyan hankali, farin ciki, kulawa, dakuma lokacin iyali shine aure awajena, wanda dukansu narasa, Baba Baban Khalid baya sona, bantaba ciwon kai yatambayeni ya jikinba, idanma ina ciwo idan inada sa'a shine zai kwana agidan yaraba daki dani, that's ranan da yan mutuncin shi kenan kenan, idan kuma basanan barin gidan yake yaafi hotel shi baison kamshim mai ciwo, bai damu dayanake ba kokuma yaya nakare, Baba idan zan fadi na buge na kurje agabanshi sannu bazaicemin ba balle ya tashi ya taimakamin natashi, baya kirana, bayida lokacina, Baba bai damu daniba, halayen dayake nunamin ire iren haka da gwaleni dayakeyi yasa I grew out of love for him, Baba, Mama ku iyayena ne idan namuku karya bazanma Allah ba, amman wlh harga Allah Allah yana ganin zuciyata banason Baban su Khalid yanzu ko kadan sabida yanda yake wulakantani, bakuma yaune nadena sonshi ba tunda dadewa, amman nacigaba da zama dashi ina kyautatamai sabida murayu tare kobadan komiba sabida yaranmu, amman at this junction bazan iyaba, yara nakowane kulansu da rayuwansu na hannun Allah ne baniba, shida yabanisu yasan yanda zaiyi dasu, kuma bama kananu bane dazan dinga tsoroba, kuma ko babu komi zan iyama Babansu shaida daya! Itace yanason yaranshi bazai taba wulakantamin su ba, Baba inason karaba aurena dashi bazan iya cigaba dazama dashi ba, zuciyata tagaji dakomi, kayakuri Baba wanan itace iyakan gaskiyata" tunda tafara maganan dakin yay shiru harta gama sanan Baba ya gyadakai ya kalli yaranshi maza yace "ina fatan kun dauki darasi daga maganan kanwarku" dukansu gyadamai kai yayi, Baba yace "wani zubin bakudi ne komiba, mace dakuka ganta anan tanada rauni, mace tafison mijin dazai sota damijin dazai bata kudi, kudi ba komi bane awajen wasu matan, kabama mace time, attention da care kaga yanda zata soka sama da komi, kardan kunzo kunyi kudi kufara wulakanta matanku, mata sun kashi gida biyu ne, akwai mai jure komi kome zaka mata taita jurewa tana shanyewa tana hakura, akwai kuma wacce bazata iyaba data tsaya jurewa tana shanyewa gwara tabarka which is kanwarku dinan dakuke gani, and I am so proud of her, I am so proud of you Yan biyu, Allah yamiki albarka, this shows kodayau zan mutu inada yarinyar dat can take care of herself, ta tsayawa kanta, Nothing beat peace of mind, bazan taba advising koyarda batawaba ta tsaya namiji yabata hawan jini yakasheta abanza yakaita lahira ba No" yabuga kujera yace "mace abuce mai rauni, ana bukata asota ne akuma kulada ita ba'a wulakantata ba, take care of your women mata deserve love, care, and attention, Allah yamuku albarka gabaki daya, kotu zata nemi Baban su Khalid, bayan an raba auren zan baki kudi ki kara expanding business naki, settle down mutuwan aure bashine end of the world ba hasalima is Nothing, kawai ki dage da addu'a sanan kizama mai yawan tsoron Allah kinajina" gyadamai kai tayi, yay murmushi yace "tashi kitafi kinji" tashi tayi ahankali saikuma tajuyo ta kalli Baban nata, batasan lokacin dataje da gudu ta tsugunna gaban kujeran dayake kawai tasa kanta aguiwanshi tahau kukaba sosai, tace "Baba u are the best father in this world, thank you Baba" dagokanta yayi yakai hannunshi yasharenata hawayen kaman wata karaman yarinya yace "I don't take my children for granted, babu wanda ya isa yabanzantar min da my girls, oya dena kukan ya isa haka, kome kikeso ki gayawa mamanki gatanan, ranan visiting din su Khalid kuma zaki kiga yaranki ki musu shopping okay" gyadamai kai tayi yace "to tashi kitafi" tashi tayi ahankali tawuce tatafi duk suka bitada kallo cikeda tausayi dakuma so, Baba ya kalli Hydar yace "start with the procedures, akaimai sallama yau yau dinnan" gyadamaikai yayi yatashi yafita feeling so proud of his Dad, Mahaifinsu wani irin kalan mutumne, tun suna yara yake koyamusu always respect women, mata abin tausayine, abin atausayamusu ne, sanan akuladasu alallashesu, idan kaduba kagani zakaga nafarko daga hakarkarinmu maza aka yosu, to akanme zaku wulakanta su, Baba kan yawan cemusu Annabin mu yariga ya kwatoma mata yancinsu dan haka dole mu daraja su, mu tausayamusu kodan hayayyafomana dasuke yi, Baba always say never hit a woman, Baba nada wani irin believe inhar ka kulada mace, kasota, kabata attention to wlh zata bika kaman kamata magani bazaka taba samin problem da itaba, murmushi kawai yayi yashiga mota yaja zuwa Shari'a court.
"Baby kibarni natafi wajen aiki mana, naji to zan sayomiki idan zan dawo" yay maganan yana washe baki yafito daga dakin Baby da gudunshi kaman wani dan yaro yasauko kasa yana gyara necktie dinshi sanan yabude kofa yafita compound, tsaye yaga direbanshi jikin mota, yana ganinshi yazube akasa cikeda girmamawa yace "barkada fitowa Alhaji" saukowa yayi daga matattakala yace "barka" tashi direban yayi yana ciro wata envelop daga Aljihunshi yace "Alhaji yanzun nan wani yace daga shari'a court yake yabani wanan jakarwasikan waina baka" jin sunan kotu yasa ya kalli wasikan da ake mikamai yasa hannu ya karba sanan ya yage yabude yashiga karantawa sosai gabanshi yawani irin fadi dum!!! Ahankali yamaida wasikan ya linke sanan yashiga mota yazauna direba yarufe yadawo gaba yazauna yakunna motar, ahankali Baban Khalid yace "kaini wajen Attajiri" jan motan yayi suka dauki hanya tafiyan kusan 40min sukayi sukakai building din, baima jira direba yabude maiba ya sauko yay sama,
Bude kofan office din Attajiri yayi hankali tashi, Attajiri dake zaune kan kujera ganinshi yasa yatashi dasauri yace "kai Ango lpy" ko magana kasawa yayi ya wurgamai envelop din dahar take faduwa kasa da sauri ya tsugunna yadauka yana kallonta yace "menene kuma wanan" folding hannu Baban Khalid yayi akirji ya jingina da bango da kyar muryanshi ya iya fitowa yace "see for yourself" hakan yasa Attajiri ya zura hannu yazaro takardan sanan ya warware yashiga karantawa duk Baban Khalid nakallonshi, saida yagama sanan ya dukunkune takardan ya yar sanan ya kalli Baban Khalid dahar lokacin yana rungume da hannayenshi yana kallonshi yace "yanzu daman wasikan nanne yasa duk hankalinka yatashi saikace ana tuhumanka da sata"? Cikin yanayi na damuwa sosai yace "toya kakeso nayi? This wasn't part of the plan, plan din was nasa kanta ya sauko kasa, tabini tana shanye duk wulakantatan dazanyi not this, ni ai banso narabu da Hassana, itace mahaifiyar yarana yaza'ayi mu rabu, what will I tell my sons"? Tunda yake maganan Attajiri ke kallonshi saida yagama tsaf Attajiri yace "kai wlh kaji kunya, kabama maza kunya wlh, tirrr, kai wlh gaula nema Gwamnati, yanzu sabida kai bakada hankali matarda ta rainaka, takeda girman kai takasa saukomaka ka takata shine yanzu danta aikomaka da sammacin kotu dukka tsure haka? Wlh inda ace yanzu zataga yanda hankalinka yatashi saita zamar dakai zaninta kadawo mata woman wrapper" cikeda wani irin damuwa ya lumshe ido yama kasa magana, hakan yasa Attajiri dayasaki baki yana kallonshi yace "kai wai daman haka kakeson Hassanan nan?" Dan bude idanunshi dasukai ja kadan yayi ya kalli Attajiri saikuma yay shiru yamaida idanun yarufe su, wani shegen tsaki Attajiri yaja yace "ahhhhh iyayenmu sunyi gaskiya daman ance macen dakecin uban namiji ita yafiso, yanzu sabida kai sokone jibi yanda su Saudat ke sonka suke binka kaman kaine rayuwansu amman hasana dabata darajaka kakeso har hankalinka yake tashi akansu haka" cikin wani irin yanayi yabude ido yace "kadena comparing su Saudat da Hassana, wlh ko kadan banji dadin Saudat ba, she is not even sweet, gata so loose, Hassana dabanne acikin mata, zakinta da dadinta yasa kaga all my life da ita banma taba sha'awan kara aure ba, sabida full mace ce Hassana, bana iya 2night ban saduda itaba, akwai wani kalan natsuwa danakeji atattare da ita da banjishi jikin Saudat ba kuma ko jikin yarinyar ma nasan bazan jishiba, kai kasan da yaya nake surviving wanan fadan damukeyi da itane? Har addu'a nake ta gayyato yan uwanta suzo suyi bikona sabida nasamu nasami natsuwa da ita amman taki, ni wlh bantaba hararo rabuwa da itaba, banmasan tayaya zan fara rayuwa babu itaba" cikedajin haushinshi Attajiri yace "aisaikaje to kabata hakuri ku shirya" dasauri yakalli Attajiri yace "never! Ubanta yay kadan wlh naje nabata hakuri, nidai kawai kafadamin yaya zamuyi mu shawo kan al'amarin nan" yay maganan yana dawowa kujeran dake facing na Attajiri yazauna sanan yasauke ijiyan zuciya yace "tell me what to do"?
Wani irin ijiyan zuciya Attajiri yasauke, yace "nifa inada plan bawai banida shi bane, kuma my plan is the best one inhar kanason Hassana to succumb to you" dasauri yace "mezanyi dazaisa tai succumb to me"? Yay maganan jikinshi har rawa yake yakosa yaji amsan da Attajiri zai bayar, ido da ido Attajiri ke kallonshi sanan yace "ka saketa!" Wani irin komawa da kujeran dayakekai baya yayi kujeran yawani karkace saigashi akasa, tsabagen shock ma kasa tashi yayi daga kasan sai kallon Attajiri yake kalman kasaketa namai yawo a brain, ganin haka yasa Attajiri ya gyadamai kai cikeda kokarin son gamardashi yace "hear me out, tashi kazauna dan solid plan ne wanan plan din, tashi tashi kaga" tashi yayi ahankali yadaga kujeran sanan yazauna yana kallon Attajiri din kirjinshi na dukan biyar biyar, murmushi Attajiri yayi yace "common calm down, don't you trust me, wanan shine surest plan ina gayamaka kashirya ji" gyadamaikai yayi yama jasa magana, Attajiri yace "yauwa, kaga kariga kabata Hassana in such a way matarnan bazata taba iya zama dawani namiji ba, to gayamin waye yakaika kudi yanzu amasu shekarunka? Kabama matarnan kudi, gidan hutu, jin dadin duniya, ka lalatata da jin dadi towani namiji awanan zamanin zata samu dazai mata haka? Forget wanan kotun takaikane sabida idan kazo kanemi sulhu alkali ya shiryaku kadauketa ku koma gida, amman bahaka zakiyiba kai" duk wanan maganan da Attajiri yake idanunshi kyam akanshi, murmushi Attajiri yayi yace "idan kasaketa nanne all her ego and pride will completely shatter, zata rushe da kuka tazo tana rokonka kayakuri, kasan yanda mata keson zama da uban yayansu kuwa? Kaikuma alokacin zakamata shakara kafin ka koramata sharuddan maidata dakinta zata yarda da gudu sanan kudawo daidai" wani irin kallon yadan soma natsuwa yakema Attajiri sanan yace "to saki nawa zan mata"? "Biyu zaka danna mata, ukuma dan sabida idan kamata saitai wani aure zata iya dawomaka inda bahakaba daka dannamata ukun duka yanda hankalinta zai tashi tahaukace, but nevertheless saki zaka danna mata ai kadai gane" wani irin murmushi yayi cikeda jin dadi, ganin haka yasa Attajiri yace "kawo kunnenka kaji nafadamaka yanda zaka mata sakin" dasauri yamikamai kunnenshi, nan Attajiri yashigamai whispering abubuwa saichan dukansu biyun suka kwashe da dariya kaman bashine yanzun nan hankalinshi yake atasheba, Attajiri yace "Allah kaimu gobe, wanka zaka zuba na kece raini bugaggiyar mahaujaciyar gizna zaka zuba babban riga kafasa kotun nan tayanda koshi alkalin yaganka saiya girgiza, ni zanma rakaka, sabida tafara kuka inje ingayamata taje tabaka hakuri ka komarda ita dakinta kaikuma saikai mota kajirani, kai amara mutuncin Alhaji fa zaka shiga kotun" dasauri yana dariya yace "kaida kasan komi trust me" suka shiga dariya, Attajiri yace "inada meeting eleven kaga takusa" dasauri yatashi yace "nima bari natafi" gaisawa sukayi sanan yawuce yafice, shikuma Attajiri yashiga kwashe kwashen takardu, saida yaji yarufo kofanshi sanan yadago yakalli kofan tareda haderai kaman bashi ke murmushiba yace "just watch and see yanda zaka rasa komi naka right before your eyes, meanwhile Saudat da Maryam na nasu aikin agida nikuma ina nawa daganan Bakori kenan" saiyawani kece da dariya, sanan yace "har yanzu baka gama sanin kan duniyanci ba, sai randa zakaga na auro Hassana matarka, company ka kuma yadawo nawa zakasan cewa kayi kuskure babba dani" wani irin dariya yakarayi sanan yawuce yafita daga office dinshi.
_Bari nai amfani da wanan daman namuku tallan clases din danakeyi na matan aure kadai mai suna EROTIC IDEAS, na wanan October._
_Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._
_Duk ranan Alhamis munayin program mai suna MARRIAGE LIFESTYLE, wato ZAMANTAKEWAN AURE, inda nakema mata lectures kan yanda ake zama da miji dakuma dabarun zama da miji, ranan jumma'a kuma muna program din damuke kirada TALK & HEAL wato yi magana ka warke, inda matan aure zasu gayamana matsalolin dasuke fuskanta agidajen mazajen su, zasu iya turamin ta pc idan basuson asansu nisainai forwarding group mu taimaka musu da shawarwari dakuma dabarun dazasubi su magance wanan matsalolin, sai ranan asabar shine ranan LECTURES, inda zan dauki darasi dake dauke da dombin ilimi abu wanda ya dace mata su iya dangane da aurensu, mu koya musu ayi magana akai sosai, sai ranan Lahadi zamuyi lectures akan ilimin daya danganci yanda zaki gamsar da mijinki sanan ki gamsar da kanki, kisaka mijinki ihu agado yana kururuwa yana sambatu, mukoyar dake yanda zakiyi spicing up sexlife dinki, and yanda zaki dinga rayuwa da mijinki kullum kaman sababbin aure._
_Idan kinason shiga wanan group din zaki turo 2000 to 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din, wata daya ne group din, idan kinason ki cigaba da zama duk wata dubu dayane 1000 ne subscription, sababbin zuwa kuma new member zakiyi register is 2k ne, don karin bayani zaki iya tuntubata a number ta 07012181461_
M Shakur ❤️
Dayake karfe goma ne za'a shiga shari'ar su tun 9:30 duka itada family member ta na court din, tana sanye dawata Oman black Abaya mai bala'in kyau, tana tareda Mama dakuma Hussainanta dasukenan kamanninsu daya da jiya itama ta diro daga Dubai dan she needs to support her sister, saikuma su Baba da Hydar dake wani waje daban har lokacin babu Baban Khalid, karfe goma daidai aka shiga dasu cikin kotu kowa ya zazzauna akai shiru Hussaina takama hannunta tarike ganin duktai wani iri ahankali tace "calm down we are all here with you Hassana" gyadama sister kai tayi tana kakalo murmushi daidai lokacin Alkali ya shigo kotu aka tattashi saida ya zauna sanan aka zazzauna, akai shiru itadai sai tsoron rashin ganinshi take, daya daga cikin ma'aikatan kotune yatashi yabama alkali wani file sanan yajuyo yace "ayau shadaya ga watan Augusta zamuji karane tsakanin Hajiya Hassana dakuma Alhaji Alhassan Bakori, inda Hajiya Hassana ta kawo karan mijinta wanan kotun mai adalcine bisa wayan nan dalilan, bai damu da lafiyanta ba, baya kaunarta, yana wulakantata sanan abinharyakai ga yafara daura hannunshi ajikinta da sunan duka, inda tanaso alkali yaduba wanan lamarin sanan ya sauwake mata yaraba aurenta da Alhaji Alhassan Bakori, yanzudai zamu fara da kiran Hajiya Hassana datazo ta tsaya anan".
Rawa jikinta yafara hakan yasa Hussaina takama hannunta gamgam tace "hey take a deep breath calm down kinji, Allah natare dake" lumshe ido tayi sanan tabude ahankali tareda karanto addu'a sanan taji wani karfi da dakewa yazo mata ahankali ta mike tsaye sanan tafito looking so damn beautiful and matured, tawuce ta tsaya a inda aka nunamata ta tsaya.
Mutumin yacigaba yace "saikuma Alhaji Alhassan Bakori shima ina kiranshi dayazo nan ya tsaya" shiru akayi Hydar da Mustapha suka juya suna duba kotun koyazo amman babushi, sake kiranshi mutumin yayi. "Alhaji Alhassan Bakori" daidai lokacin Baban Khalid yawani danno kanshi cikin kotun yana sanye dawata mahaukaciyar gizna fara da saida takashema mutane ido, sai zuba kamshi yake idan kaganshi zaka dauke president ne, bayanshi kuma Attajiri ne shima yaci gayu sosai yasami waje yazauna kusada Baba yana gaidashi shikuma Baban Khalid yawuce gaba inda akace yatsaya, yana tsayawa yawani kalli Hassana dake tsaye awajenta sanan cikin daga murya da rashin mutunci yace "ke har kin kisa ki kawo karan Alhaji Alhassan Bakori kotu" jikake kotun yay tsit, mutumin dake kiran sunansu yace "Alhaji kayi shiru koma menene Alkali yanzu zai fara shari'a sanan zai bama kowa daga cikinku chance yay magana"
Ko takan mutumin baibiba yana kallonta still, yace "bari kiji nafi karfin ki kawoni kotu kitonamin asiri, Hassana kisani cewa ni Alhaji Alhassan Bakori nasakeki saki biyu!" Jikake tsit, wasu irin hot hawaye taji sun zubomata daga idanu data kasa controlling, sanan yawani tura hannu a Aljihu yaciro envelope