You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
tun daga nesa ta hangosu tsaye ahankali take tunkarar inda suke har ta karaso kusa dasu tana masu kallon rashin sani “cike da natsuwa tace “sannunku kune kuke neman maryama “? eh mune muke nemanki tayi mamakin yadda suka santa amman ita bata sansu ba “gani da fatan dai lafiya ?ta fad’a tana jin wani iri ajikinta dan gsky haka nan taji mutanen basu kwanta mata ba bugu da qari rashin sanin da batai masu ba mutun d’aya acikinsu yace “naga kin tsorata da ganinu ki kwantar da hankalinki mu din ba mugayen muaten bane bamu zo da niyyar cutar dake ba jikita a sanyaye tace “to amman kuyi sauri ki fad’a abinda ya kawo ku Ina son na koma ciki .”
tayi magnar tana juya bayanta sannan ta juyo domin ta fuskansu ai juyowarta keda wuya taji ta shaki wani abu , nan take taji tunanin kanta ya d’auke ya soma ganin jiri tana qoqarin yin kasa kallon dayan mutumin yayi yace “sa’bata aka fad’a muje nan take ya taro maryama ya sabata a kafa suka nufi bakin titi inda sukai parking din motar su da sauri dayan mutumin ya bud’e masa gidan baya ya kwantar daita tare da maida kofar suka rufe atare suka zagayo cikin sauri suka bud’e gaban mota suka fad’a suka bar unguwar .”
Mmn sudais
Downloaded From https://tknovels.com.ng
Book Chapters
Chapter 45