google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a little danunki bata da ja domin ita kanta tasan tabbas a irin kukan datai dole za’a gane ba “tabbas nayi kuka umma amman acikin mafarki .”umma bata mutsa mata ba amman tasan ba’a mafarki bane azahiri tayi kuka amamn tunda ta zabi ta fad’a haka shikenan “na had’a mana tea mai dadi bari naje na kawo miki jirani ina zuwa .”umma ta mike ta nufi kitchen inda maryama tabi bayanta da kallo mai tattare da tsantsar qauna tana zaune umma ta fito ta dawo gabanta ta tsaya tana mika mata cup din tea “ga naki tea tasa hannunta ta kar’ba cike da girmamawa tace “na gode sosai ummata umma ta kai nata cup din baki ta kur’ba tana cewa kai tea din nan yayi dadi sosai hakan yasa maryama ta kai nata cup din bakinta ta soma kur’ba tana lumshe ido “gsky ne umma yayi dadi kuma ya sha bambam da sauran tea “kuma kinga bashi da wata wahalar yi ba idan zaki yi ki samu kanufari,lipton tafarnuwa mint leave da gayen nahna’a shikenan ina son ki koya dan bamu san wani irin mutun zaki aura ba, idan allah yasa mai yawon sha tea ne shikenan sai ki dinga masa irinsa” kai umma duk maganarki bata wuce ta aure nifa ynzu ba aure bane agabana kamar yadda na sha fad’a miki burina a yanzu mu bar gidan nan “nasani amman kibi komai ahankali” umma ta fad’a tana dubanta a natse kafin ahankali ta cigaba da magana ina son ki bani aron hankalinki jin haka yasa zuciyar maryama ta fara tsinkewa ina son nayi miki magana akan wani abu zuciyarta ce ta cigaba da tsinkewa yayinda ilahirin jikinta ya d’auki rawa babu shiri ta ajiye cup din hannunta ta tsura mata ido “muryarta a sanyaye tace “ina sauraronki umma “ina son Kiyi aure maryama bazan so ki cigaba da rayuwa haka ba wani irin ajiyar zuciya ta sauke mai qarfin saka makon ba abinda tayi tunanin bane “ muddin ban baki shawa rar kiyi aure ba lallai ban cika mai adalci ba ,aure yana daraja kuma zai kareki daga dukkanin wata matseefa “in sha allahu zanyi umma amman ba yznu ba dan ahalin yanzu babu wanda yace yana son maryamarki ko da yake kin dai san maryamarki da bakinjini .”ta fad’a tana dan murmushi “.


“ni maryamata bata da wani bakinjini kisa niyya sai Allah ya taimakemu ,shikenan umma naji bari na wuce aiki lokaci na tafiya .”har tayi taku biyu ta kira sunanta “maryama !ta tsaya cak batare data juyo ba ki tsaya bari naje na kawo miki custard lokacin data juya alokacin maryama ta juyo tana duba agogon hannunta, lokaci ya soma tafiya umma bata wani jima ba ta fito hannuta rike da wasu flaks guda biyu kanana
ta miko mata daya maryama ta kar’ba tana murmushin jin dadi “kai gaksy umma kina ji dani shiyasa nake sonki fiyye da komai kamra Kinsan kwana biyu nayi missing custard dinki ai shiyasa nayi miki dan nasan kina so ga naki ,wannan d’aya kuma na mai gidanki “what !”
Maryama ta furta da karfi jikinta har rawa yake tsabar rudewa “umma wa kenan kike magana akai wa custard ?wa kuwa bayan mai gidanki mr ata shi zaki kaiwa nasan bai ta’ba shan custard irinsa ba “what !” wai mr..”mr ata kike nufi ?ta fad’a murayarta na rawa me zai yi da wani custard umma?” ke kike tunanin mai zai yi dashi ke dai ki kai masa ki gani “murmushi maryama tayi tana cewa “amman dai umma da wasa kike ko ?” idan ba haka ba ta yaya zan kai wa mr ata custard?”


“to ke mai yasa kike mamaki ke dai nace ki kai masa kuma kice inji mamanki “no no umma karki damu kanki wallahi baki san waye wannna mutumin ba shiyasa ,mutumin da bashi da bambamci da hawainiya mutunin da zuciyarsa bata da bambamci data dutse kai zuciyarsa tafi ta dutse karfi mutumin da babu abinda yasani sai wulakanci da tozarci shine mutumin da kike tuannin na kaiwa custard?” ina bazan iya ba umma ba,” tsaya maryama ina son ki fahimceni kema na rasa gane kanki wata rana kice mutumin kirki ne wata rana ki canza magana ,ni wanne zan dauka aciki maryama tai shiru kawai cikin tsnanin damuwa dan tasa aiki ja umma take son bata ,duk abinda kike fad’a akansa ni dai abu daya nasani zuciyata tana son shi a haka duk rashin kirkinsa shine yayi nasarar dawo miki da farinciki da walwalarki dan haka ki amsa ki masa idan na isa dake idan kuma ban isa dake ba nasani.” lumshe idanu maryama tayi “.
“na fahimceki umma amman walalhi mutum ne shi mai wuyar shaani”nasani !wallahi umma da wahala ya karba ki fahimceni ba wai ina jayayya dake bane halinsa nasani “nace miki zai amsa ki kar’ba to ni yanzu idan na kai masa mai zance masa ?”
tai maganar tana dafe goshinta umma tace “ bazanki bin umarnina bane ?”babu shiri maryama tasa hannu ta kar’ba “yauwa sai kin dawo Allah ya tsareki “ ahankali ta juya ta bar bangaren da sauri inda ta bar umma tsaye tana kallonta “maryama kenan bazaki gane abinda wannna mutuminn yake nufi dake ba sai nan gaba kin kasa fahimtar mai yasa ya damu dake, me yasa yake yawon fushi akanki ,mai yasa ya damu matukar sai kinyi aiki akarkashinsa ,ni dai nayi imani akwai wani abu acikin ransa akanki, koma dai menene Allah kasa mu dace Allah yayi miki kyakkywan zabi mafi alkairi arayuwarki da addininki.”



Ahankali maryama ta shigo ma’aikatan tana gyara zaman jakar dake kafad’anta tare da rike qaramin jakar da umma ta sako mata flaks ciki duk ilahirin jikinta yayi wani iri yayinda zuciyarta ke cike da tsannain fargaba “maryama ki sanyawa jikinki jarumta sannan ki karkafa zuciyarki, yanayin yadda kike damun kanki akan abinda bai kai ya kawo ba, yanayin ne damuwa zata miki yawa.”
ki samu natsuwa ba dole sai kin bashi sakon umma ba zaki iya bawa wani ya shanye a madadinsa tana tafiya tana zance zuci a natse ta shiga office dinsu ta gaishe da mutanen data iske ,sai dai babu wanda ya amasa mata bare ya kalli inda take, sai yusura kad’ai ta amsa mata sa’banin jiya tana kallonta cike da tsananin tausayi da mamakinta dan har lokacin bata daina mamakin hotunan jiya da’aka tura masu ba .”


Maryama tana tsaye madam some ta shigo ta wuce ta gabanta tana kallonta tana zance zuci tare da nazarin maryma har a wannan lokacin zuciyarta bata bar mamakin mami da dalilin da yasa ta tambayeta tsakanin maryama da mr ata ba ,da kuma dalilin mr ata na cewa lallai ta tabbatar maryama ta shiga motarta kuma lallai ta kaita har unguwar su “amsarki itace mr ata yana tsananin son maryama haka ma mahaifiyarsa ta fahimci irin son da yake mata shi yasa ta kiraki jiya domin ta tabbatar
Numfashi ta sauke adaidai lokacin da maryama tace “good morning ma !” madam some ta amsa mata ,inda maryama ta samu waje ta zauna ta ciro littafinta tana dubawa sai dai bata fahimtar komai “maryama bai kamata kiki bin umarnin umma ba ,meye aciki ki kai masa idan ya kar’ba fine idan bai kar’ba shikenan sai ki bawa wani amamn idan kika ki bashi idan kin koma gida ta rutsaki me zakice mata?” ko idan tace ki rantse me zaki ce ?”.
shiru tai kawai tana tunanin yadda zatayi bayan wasu mintuna ta mike ta nufi office dinsa bata iske madam some a mazauninta ba dan haka ta soma qoqarin shiga ta ajiye masa ta kama gabanta inda ahankali madam some ta kai hannu ta dafata da sauri ta juyo jikinta na wani irin rawa lafiyarki maryama me kikeyi ?sorry ma ta fad’a bakinta da jikinta na rawa kina bukatar wani abu ne ?no ..”no ma .”meye wannan rike a hannunki ?”amm daman mamana ce tayi wa mr ata custard tace na kawo masa .”
nan take gaban madam some ya bada rasa haka ma sultana dake tsaye a bayansu dan tana hankalce da duk wani motsin maryama “kutumar uba can .”sultana ta furta tana cewa” lallai ma yarinyar nan yayinda madam some tace “shikenan kije ki fara aikinki kafin yazo dan har yanzu bai qaraso ba tukun, jiki a sanyaye ta juya bayanta da zumar komawa office tana gama juyawa taga sultana tsaye tana jifanta da wani rikitaccen kallo wanda yasa hantar cikinta kad’awa bata ce mata Uhm ba bare uhm uhm hakan nan yau kallon nata ya saukar mata da mummunar fargaba mai tsanani.”sultana ta cigaba da aika mata da mugayen kallo mai had’e da harara.”




Maryama na tsaye cikin tashin hankali da tsananin fargaba sai gashi ya shigo ya iskesu tsaye “good morning sir”. ta furta da sauri qirjinta na bugawa “morning “!kawai yace tare da kallon inda madam some take yace some kije ki fad,awa duk wanda aka turawa hotunan nan su goge kuma muddin ya fita nayi bincike na gano wanda ya fitar dashi qarshen aikinsa yazo bayan na d’auki mataki akansa” okay sir yana gama fad’ar haka ya shige office dinsa yayinda maryama ta sauke numfashi tana mai Jin farinciki ta koma office da sauri sultana itama ta juya ta shiga wani office ta samu waje ta zauna tana tunanin matakin da zasu d’auka akan maryama.”


Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye acikin office din tana tunanin yadda zatayi ta bashi sakon umma tayi taku d’aya biyu sai kuma ta tsaya gabdaya ma’aikatan dake office din suka bita da kallo sultana da hankalin ta ke kan maryama tai murmu shi yayinda maryama ke sake sake “ naje na bashi yanzu ne ko kuma na bari zuwa anjima na kai masa tana kallonsa ya fito yana kiran sunan some “yes sir “! ta amsa masa dashi yayi mata magana a can kasan makoshi sannnan ya fice da idanu maryama ta bishi dashi tana sauke wani wahallen numfashi ,sultana ta kasa hakuri ta mike ta shigo office din da maryama take ta tsaya adaidai gefenta “ban ta’ba ganin yar talakawar dake shishigi irin naki ba ,wama yasan me aka zuba masa cikin custard din da ake son ya sha dan naga duk hankalinki baya jikinki alamun rashin gasky? .



maryama ta dago kanta ta kalleta da mamaki sai dai bata ce mata komai ba ta maida hankalinta akan aikinta tana zance zuci ,”da Kinsan da yaya na taho da custard din nan da bakice haka ba ,any way ma mai zai sa ayi wa mr ata wani abu mai ake nema agurinsa kawai dai kyatatawa ce irin ta umma ba komai bane”idan kuma son shi kike yi gara kiyi maza ki ciresa aranki dan yafi karfin aurenki ,sai dai ya more kuruciyarki kamar yadda muka gani a hotunan wama yasan me ya faru a tsakaninku dan a yadda nake kallonki zaki iya aikata fiyye da zina “subhallah maryama ta furta a fili tana kallonta da kwayar idanunta da suka soma canza kala tsabar bacin rai “mai yasa sultana zaki fad’a min haka ?”wallahi Allah shine shidata akan hotuna nan kuma nasan duk abinda zan fad’a bazaa ta’ba yarda dani ba amman kije na barki da Allah daman dashi kawai zaki barni dan babu abinda zaki iya min munafuka kawai “dan Allah sultana bana son tashin hankali ki barni naji da damuwata maryama ta fad’a qirjinta na Dylan uku uku gbdy taji sauran natsuwar dake jikinta ta kau mussaman a yanzu tafi Jin bugun zuciyarta yana qaruwa
duk baqaqen maganganun sultana maryama bata tankata ba ta shareta ta cigaba da aikinta sai dai zuciyarta ke mata wani irin zafi kusan mintuna talatin maryama na zaune tana aikinta batare data kalli kowa acikin office dinsu ba haka zalika bata ga dawowar mr ata ba har lokacin break yayi.”
ta ciro flaks dinta ta d’aura akan table ta soma shan custard din tana cikin sha wayarta ta soma vabriting alamun kira ta ciro ta duba sunan umma ta gani yana yawo a scren din wayar ta d’aga tana cewa “hello umma nah daga bangaren umma tace “hello maryamata ya kike ya aiki.”? “alhamdulillah umma!” kin bawa mai gidan custard din kuwa ?”
”amm umm ban bashi ba nasan kunya kike ji da tsoro Kiyi qoqari ki cire tsoron nan ki bashi kinji diyata zan ji dadi idan kika bashi sannan zanyi farinciki idan ya kar’ba ya sha.” “In sha allahu umma zanyi qoqarin na bashi yanzu ma dai baya nan tun dazu daya shigo ya fita banga dawowarsa ba amman da zarar ya dawo zan bashi tana cikin magana sai gashi ya dawo tace “yauwa gashi nan ma amman wallahi umma tsoro nake ji ban san yadda zai dubi abun ba bana son yayi react kamar cutar dashi zanyi .”


“karki damu maryama bana jin zai yi tunanin wani abu kije ki bashi “to umma kin sha naki ne Eh umma shi nake sha okay yayi sai kin dawo “ya rab ka taimakeni ban san yadda zanyi na bashi custard din nan ba gashi yau da alamun akwai rashin mutunci atare dashi kar naje ya sauke min ruwan balai tana cikin wannan halin yazo ya tsaya akanta “maryama”! yes sir !”ta amsa da haka tana qoqarin rufe flak’s din gabanta ta mike tsaye “ance kin kawo min wani abu me kika kawo min ?..”


“uhm ..” no sir bani bace daman umma ummata ce .”ki natsu ki yi min magana ta yadda zan fahimta “daman me ..”?daman ummata ce tayi maka tace na kawo maka “.ta fad’a jikinta da zuciyarta na karkarwa hakan yasa tayi saurin tsarke hannu wanta waje d’aya domin taimakawa gangar jikinta samun sausauci idanunshi ya tsura mata ta cikin farin glas din dake manne da kwayar idanunshi yana kallonta kmr zai cinyeta ,kafin ahankali ya ciro hannunsa d’aya cikin aljihun wondonsa yana kallonta yace “me ta baki ki kawo min ?da sauri ta ciro flaks din ta miko masa jikinta na sake d’aukar rawa, ya cire dayan hannunsa dake cikin wondo ya amsa ya bude flaks din data mika masa yayinda ta tsaya a tsorace tana kallonsa tare da jiran rashin mutuncin da zai mata .”


yana gama budewa ya tsaya shiru yana kallon abinda Ke ciki yayinda ta cigaba da kallonsa a matukar tsorace muryarsa a kasalance yace“meye wannan ? ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi masu matukar tsoratarwa” kayi hakuri sir ummana ce tace na kawo maka .”numfashi ya sauke tare da cewa “yakayi tasan ina matukar son fruit custard kallonsa tayi da sauri tana jin wani irin sanyi a zuciyarta wanda bai tsaya iya zuciyarta ba har ganganr jikinta take jinsa wani sanyayen dadi ne ya mamayeta” kana matukar son fruit custard ?”ya gyada mata kai kawai tare da yin shiru ya rufe flaks din ya juya har yayi taku d’aya sai kuma ya tsaya rike da flaks din “kice wa mum na gode sosai” kenan zaka sha? ya juyo tare da lumshe mata tsumammun idanunshi bana shan abun hannun kowa bayan mahaifiyata da some amman zan sha saboda mahaifiyarki ce tace ki kawo min ,”kuma kace nace mata ka gode?” meye damuwarki dan nace na gode ?ya fad’a yana hura mata hanci tace” babu “!


maryama ta waiga waje taga babu mai zuwa dan Allah Allah take ya fita ya barta kar wani ya gansu bare sultana”
”maryama kina mamaki dan na kar’bi abun hannunki” ta gyada masa kai alamun eh “ina mamaki ne sir dan na ma fad’a mata bazaka kar’ba ba saboda behavior’s dinka sai gashi ka kar’ba babu mai saka abu babu mai hanaka babu wanda kake iya yiwa godiya sai gashi kayi wa ummata,kasan wani abun ?”yayi shiru kawai yana kallon bakinta da take magana dashi daga gida har office nasan duk dabi’a daya kake yi dan allah ka canza wannan dabiar taka kowa tsoronka yake ji “.sannan kuma na gode sosai da kace kowa ya goge hotu nanmu hakan ya rage min tarin radadi da nake ji duk da ya zubar min da kimata agurin abokan aikina ,sun zargeni Akan laifin da ban aikata ba kuma suna min kallon banza gabadaya bana cikin sukuni da kwanciyar hankali ina jin kamar na bar aikina domin bazan iya jurar irin kallon kaskanci da tozarcin da suke min ba ta qarasa maganar muryarta na rawa “ban san me zan cigaba da cewa ba amman naji dadi sosai dakasa suka goge ta fad’a tana d’ago idanunta dake cike da ruwan hawaye .”


Shiru sukai daga ita shi kafin ahankali ta d’ago idanunta nan take idanunsu ya tsarke cikin juna ,ido cikin ido suke kallon kwayar idanun juna suna cikin wannan yanayin sai ga sauran ma’akatan sun shigo da sauri maryama ta d’auke kwayar idanunta acikin nashi ta maida wani bangaren turus sukayi suna kallonsu daya bayan daya kallo daya yayi masu kowannen su ya kama gabansa madam some ta shigo itama kallo daya tayi masu ta d’auke idanunta ta wuce a natse ya soma tafiya rike da flaks din hannunsa cike da jin haushin abinda sukai mata yana zance zuci baku sani bane,akanta zan iya korar kowa acikinku, amman zan d’auki mataki akai dan babu wanda ya isa ya tozarta min rayuwata.”



Bayan wasu mintuna ya bude kofar office dinsa da qarfi ya fito yana waya ya isa a gaban madam some tare da cire wayar a kunnensa ya nuna mata hotunansu shi da maryama “ kinsa sun goge hotunan nan ko kuwa ?”yes sir sun goge ya qara taku daya ya isa inda take zaune yana cewa “zan yiwa kowaye ya tura maku hotunmu rashin mutunci domin ba maryama ake son tozarta wa ba ni ake son tozartawa ko ba haba,” haka ne sir wannan abu ba wai da gaske bane nan ya shiga kora mata dalilin da yasa hakan ta faru batare da yasan ma yana mata bayani ba yana dasa aya tace “I will explain everything to them sir “ bana bukatar some amman na rantse da girman allah bazan d’agawa kowaye kafa ba kuma zan yi komai akan duk wanda zai ciwa maryama mutunci acikin ma’aikatar nan ya qarasa fad’ar haka a tsawa ce kallonsa take cike da tsananin tsora da mamaki yana gama fadar ya wuceta ya shiga office dinsu maryama sakamakon hangosu da yayi suna tautaunawa a tsakaninsu sun ware maryama .”



shiru kowannensu yayi alokacin da suka gansa “why everybody quiet?a tsawace ya tambayesu yana had’e rai fiyye yadda yake yi “oh ashe kunyi shiru ne saboda kunsan cewar ni ne shugaba anan ba .”?ai bai kamata kunyi shiru ba ku cigaba da tautaunawa ko bakuna tautaunawar ne akan abinda ya faru tsakanina da maryama ba ? daya bayan daya ya kira sunansu tare da cewa ku cigaba da tautaunawar mana “speak up let me hear you “. “wato kun d’aukemu amatsayin mazinacita ba?shiru sukai gabad’aya sai yusura ce ta samu damar cewar “kayi hakuri sir ai bazamu ta’ba fad’ar abu makamancin haka ba,dan mun san bazaka ta’ba aika haka ba .”taya kuke tunanin bazan iya aikata haka abu makamancin haka da maryama ba ?ai ni mutun bane kamar kowa kuma zan iya “! a matukar tsorace suke kallonsa yayinda mryama ta kasa d’ago idanuta ta kallesa a tun sanda ya soma magana iska mai zafi ya fesar daga bakinsa ya cigaba da magana kusani babu wanda ake jin tsoronsa anan ,saboda daku da ma’aikatan nan abun ikona ne sannan yadda naga dama zanyi daku kuma ko barin aiki kukayi nan sai naga dama zan baku damar yin aiki da kowani ma’aikatan amman bazan nuna maku qarfin ikona ba ,abinda nake son kusani maryama ba mazinaciya bace, ba yar iska bace, hassalima ta fiku kamewa da natsuwa dasanin ya kamata.”


cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa maryama ta d’ago idanunta tana kallonsa tana sauke naunayen ajiyar zuciya zan iya korar kowa acikin kamfanin nan na zauna daita kad’ai ,sannan da zaa tara min duk matan duniya wad’an da zan sheida ita kadai zan cire wani sabon mamaki ya bayyana akan fuskarsu maryama maryama mutuniyar kirki ce and she have especial talent yayi maganar tare da matsowa kusa daita sosai, ban dauka zaku iya mata wannan tunanin ba domin kuwa nayi imani da itace wani acikinku ya samu kanshi cikin halin data tsinci kanta tabbas bazata so taga ya wulakanta ba ,kuma bazaa ta’ba hade kai daita dan a musgunawa wani ba .”
shiru sukai gabad’aya farko tunani ya kamata kuyi mai yasa maryama ta rungumeni mai ya faru daita ba wai ku dauki wannan damar ba dan kuyi mata wulakacin ko kuci mata matunci ko tozarci ba ,kallonsa kawai maryama take babu abinda yake faru haka kawai batare da dalili ba ,kuma nasan kusan haka dan ku ba yara bane ni mai yasa baku canza min ba ,ko dan ita ta kasance mace ne shiyasa kuke jin haushinta har kuje bleming dinta ?ai ni ma yakama kuyi bleming dina kamar yadda kuke bleming dinta . kallosa kawai maryama takeyi har bata son kifta idanunta.”




Mmn Sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.



Page 44


maryama na kwance lamo duk abun duniya ya isheta ahankali ta soma jiyo sautin magana daga parlour’n umma ta yun kura ta mike tsaye daga kwance da take ta soma taku cike da natsuwa tana kusanto parlour’n tana sake jiyo abinda suke tautaunawa akai “na gode maku sosai da yadda kuka mutuntani ,kuka nuna min cewar ina da darajar da zan nemi alfarma a wajenku kuyi min,na gode sosai allah kuma ya shirya mana zuria ,”
babu komai dan wallahi kin wuce haka a wajenmu dan data shegiyar yarinyar nan ce ko uwarta da wallahi komai za’ayi sai kowa acikin dangi yaga wad’an hotun , bama iya nan kawai zai tsaya ba dan hatta jama’ar unguwar nan sai sun gani , duk wani mai ganinta da kima ya daina ganita dashi amman taci darajarki”.inji cewar aunty hasana “na gode sosai sai dai hasana kisani duk abinda kikawa maryama kasani kanki kika yiwa saboda idan sunan maryama ya lalace dole za’a zageki saboda jininki “a’a aunty karki had’ani da wannan mara kunyar yarinyar da bata san ciwon kanta ba .”a qalla sun d’auki mintuna sama da shabiyar suna tautaunawa.” maryama ta fito gbdy daga d’akinta adaidai lokacin da umma ta kar’bi duka hotunan hannunsu ta had’esu waje d’aya su kuma suka mike suka nufi kofar fita ,inda umma ta shiga kitchen ta d’auko ashana duk maryama tana tsaye tana kallonta ta fito ta nufi hanyar kofar baya da alamun kona hotunan zatayi .”bayan wasu mintunan ta dawo inda tayi turus sakamakon ganin maryama tsaye dan kwanaki uku kenan rabon data sanyata acikin kwayar idanunta bata ce mata komai ba ta sake shigewa kitchen ta soma qoqarin d’aura girki .”



Jin motsin umma yayi yawa a kitchen yasa maryama ta fahimci wani aiki take dan haka ta taka ahankali ta shiga a bakin kofar kitchen din ta tsaya tana kallon bayan umma dake wanke tukunya ,numfashi ta sauke ahankali sannan ta soma taku ahankali har ta qaraso cikin kitchen din sosai ta tsaya a gafenta tana cewa “umma sannu da aiki “yauwa !kawai ta amsa mata atakaice kana ta cigaba da abinda take bayan ta gama ta zagaya ta gefenta ta d’aura tukuyar akan gas jikin maryama a sanyaye ta d’auki wuka

Please Login or Register in order to submit comment