You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyu a jikinta batare daya shirya ba. Ɗaya a gadon bayanta ɗaya akanta da ɗan kwalin ya fita. Sai dai akwai kitso ƙanana da suka mata ƙyau cikku dan tana son cikku sosai. Itama Nurse ɗin zaburowa tai kamar zata tare Nimrah ɗin duk da taga a jikinsa take amma da yake neman uwawun zama take itama sai tazo nuna bajinta.
Received at 10:47 AM     Yanzun ma kallo irin na ɗazun yay mata, dole ta dakata da gudu tana kai hannu ta sosa ƙeya tana jan jikinta baya. Shima daya tabbatar wannan yanayin zai iya saka cutuwa, a karo na farko ya furzar da iska yana shafa kan nata, ƙasa-ƙasa ya furta, “It's okay Babie” sai kuma ya kamata slowly ya maida saman gadon ya zaunar. Taƙi sakin hannunta dake zagaye da ƙugunsa, dole ya kai nasa hannun da kansa ya janye natan. Kuka ta sake fashewa da shi tana ƙoƙarin sake cusa kanta a jikinsa. Bai bari tayi hakan ba ya kai zaune kusa da ita. Sai kawai ta sake faɗa masa a jiki tana cukuykuye kan nata dai..........✍️
     
[14/02, 7:48 am] null: KIƊA A RUWA 3

8

.........Nurse data fahimci yanayin Nimrah ɗin cike da son birge shi ta zabura tana faɗin, “Yallaɓai bari na sanar da Doctor, dan kam akwai matsala a firgice take. Dama Doctor tayi magana ɗazun data farka akan ALLAH yasa kada ta shiga yanayin...”
       Yanda bai tanka ba a ɗazun yanzu ma hakan ne. Itama bata jira amsar tashi ba ta fice a hanzarce. Ai ko babu jimawa sai gasu sun shigo. Har yanzu kuma Nimrah ta hanashi ko motsi tsabar yanda ta cukuykuye sa. Dan zuwa yanzu gaba ɗaya rabin jikinta akan nashi yake. Cikin lallashi Doctor tai magana tana kamo hannunta. Amma sai ta fisge tana fashewa da kuka da sambatu irin na tabbacin bata cikin hayyacinta...
        Doctor ta rasa yanda zatai aikinta saboda yanda take jikinsa. Gashi maganar duniya Nimrah taƙi ɗagowa....
         “Miye matsalar?”.
   Dada ya faɗa yana ɗan kallon likitar a karo na farko. Sai kuma ya janye idanun nasa duk a lokaci guda. Itama ba iya kallonsa take ba, dan haka ta fara masa bayani yanda zai fahimta...... Da ga ƙarshe ta ce, “Yanzu akwai allurar dazan mata, in sha ALLAHU ƴan mintuna ne nutsuwarta zata dawo, dan har yanzu abinda ya faru bai bar brain ɗinta bane gaba ɗaya. Rashin tabbacin zata tsinta kanta a hakan yasa ban mata allurar ba tun ɗazu.”
       Bai ce komai ba, sai dai ya gamsu da bayanin nata, dan haka ya kama Nimrah da kansa ya ɗagota sosai. Tana mutsu-mutsu da son ƙwacewa dai akai allurar. Kusan a tare shi da Doctor suka sauke ajiyar zuciya bayan wasu mintina ganin Nimrah ta fara nutsuwa. Sai dai shi a ciki yay tashi, doctor kuma a bayyane. Knocking ƙofar da akai ya saka Nurse da Doctor kallon wajen, sai kuma Nurse ɗin taje ta duba. Dabo ne ɗauke da kaya, bayan sun gaisa ya miƙa mata kayan, ya ɗauki sauran ya nufi ɗakin Imran.
      Itama bayan ta ajiye kayan inda ya dace doctor ta bata umarnin gogema Nimrah jikinta dake sake ɗaukar zafi. Miƙewa Dada yay abinsa, dan tun da akai allurar ya kwantar da Nimrah gefensa yanzu ba'a jikinsa take ba. Sai da ya maida ƙofar ya rufe Nurse ɗin dake binsa da kallo ta ƙasan ido ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana nufar Nimrah. Murmushi Doctor tayi, sai ma taji Nurse ɗin ta bata tausayi...

÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷

Wani wawan birki Malam Buba yaja yana waro idanun mamaki ganin wanda ke ƙoƙarin tsaida shi. Duk da ya rufe fuska da handkachiff ga p-cap hakan bai hana shi gane shi ba. Wuff Dagger ya buɗe motar kuwa ya shigo. Ya furzar da iska mai nauyi yana janye handkachiff ɗin daya rufe fuska da shi...
       “Amma Oga wannan gangancine da mu duka zai iya sakamu a haɗari. Mizai sa kazo har nan anguwar, gari da haske kuma irin haka?”.
       Harara Dagger ya jefama Malam Buba kafin ya janye handkachiff ɗin da yake goge fuska yana gyara zama. “To faɗa min ya kake so nayi Mole? Tun randa ka kirani an ɗauke Nimrah ka sake nemana? Tsabar rashin mutunci ma waya ka kashe min gaba ɗaya. Jiya da shekaran jiya duk naje gidanka ance baka dawo ba. Sai da na kira Ari akan ya bincika min tunda na tabbatar bazai rasa huɗɗa da wani a gidan ba ya tabbatar min kana nan anan ma kake kwana. Mole mi kake nufi? Mi kake shiryawa? Ko Nimrah na hannunka?”.
        “Amma Oga wannan wace irin magana ce? Kasan dai duk wuya bazan ci amanarka ba, duk abinda zakaga nayi ina da dalili na, ko bakazo ba zan zo na kawo maka dukkan bayanai. Na farko dai kwana a gidan nima a gareni tilas ne, dan yarinyar nan Ruƙayya ce babu lafiya, sai kuma wajen jiyyarta ɗayar matar waɗannan ƙannen nasa ta faɗi akan ciki sai ta akai mata tiyata aka riro jaririn. Hakan yasa inata kai kawo na jigilar kai abinci da abubuwa. Sannan wlhy hankalina ba'a kwance yake ba, ina nane da su ko zanji bayanin an sami Uwa dan har yanzu mutumin nan bai sake dawowa gidan ba daga shi har Imran....”
         “Amma ba waya ya kamata ka kashe min ba, tunda nima ina buƙatar son jin abinda ke faruwa ko.”
Received at 10:47 AM
3 people reacted with     “Itama fa wayar ba kashewa nai ba oga. Wannan wawan Sanda ɗin ne ya ara ya shiga bayi saboda fitilar bayin ta lalace shine ya tsumbulata a ruwa, yanzu haka inda zan kai gyara nake nema”.
           “Mtsowww!”.
      Dagger yaja tsaki. Sai kuma ya miƙa masa hannu da faɗin, “Bani wayar.”
    Ba musu Malam Buba ya cirota ya bashi, Dagger ya ɗan jujjuyata a hannunsa sai kuma ya saka a aljihu. Wata ƙarama ya ciro ya bashi. “Ga wannan, daga yanzu na dinga sanin halin da ake ciki”.
       “Amma Oga ya batun Nimrah? Wlhy abin ya fara bani tsoro.”
    “Nima a tsoracen nake, dan itace rayuwata. Amma ina kan bibiyar iyayen yaron can da suka daka a makaranta satin daya gabata”.
       “Tsohon shugaban ƙasa fa naji ance”.
    “Eh su. Dan ina zarginsu gaskiya. Musamman matarsa bata da mutunci daman.”
       “To amma ta yaya Oga?”.
Wata dariya Dagger ya kece da ita. Sannan ya ce, “Humm Mole har yanzu kanka a tukunya yake kai kam. Baka san waye Dagger ba a ƙasar nan. Kodan kai kana ganina arhar banza ne. To bara kaji, wannan damar ina baka ita ne saboda Nimrah. Za kuma ka iya samun fiye da hakan. Kai dai bari na aureta”.
      Harga ALLAH sai da ƙirjin Malam Buba ya jijjiga. Har ya kasa dannewa cikin suɓutar baki ya furta, “Aure Oga?”.
         “Eh mana, ko bazaka bani ba?”.
    Dagger ya faɗa cikin tsatstsareshi da idanu. Yawu mai kauri Malam Buba ya haɗiya, zuciyarsa kuwa wani irin dukan take yi. Cikin rawar baki ya ce, “Ba..b...ba haka nake nufi ba Oga. Kawai dai naga ita ƴa take a wajen ka”.
      “A'a a wajenka dai, dan kai ka haifa. Ni masoyiya ce, kuma uwar ƴaƴana. Sai dai idan baka son bani”
     Yawu mai ƙauri Malam Buba ya sake haɗewa. “Oga ai kaima mai aurama wani ce. Kawai dai kasan ance wannan mutumin yana au.....”
      Cikin katseshi Dagger ya ce, “Oh kai harma ka ɗauki wannan auren aure? Shi jakin wace ƙasa ce zai aure ta babu iyayenta. Sannan ma wannan tsohon da aƙalla ma zai iya girmarka ne bakinka ke iya jinginawa da ƴarka. Jibeshi mutum a murɗe kamar ɗan damben turawa, dan ni banga abinda ya rage ba a zaman prison ɗin shiyyasa bamma yarda a can yake shekara takwas ba......”
      Sam Malam Buba ba jin Dagger yake ba a yanzu. Dan tsakani da ALLAH hankalinsa ya tashi. Ai koda rayuwa ta maidashi haka baya fatan yarsa ɗaya tilo ta auri mutum irin Dagger da babu sbinda ya sani a rayuwarsa sai mugunta da kisan kai. Ga neman mata kamar ɗan bunsuru. Tabbas baya ƙaunar Zak-Shadow, kuma ko zai rasa ransa wannan auren bazai bari ya tabbata ba akan ƴarsa. Amma kuma bazai so Dagger ya maye gurbin Zak-Shadow ɗin ba a rayuwar Nimrah. Dole ne yayi wani motsi a wannan gaɓar, kuɗin nan da su Oga suka bashi gida zai nema ya saya a wata ƙasa cikin maƙwaftan ƙasashen nan, ya ɗauke ƴarsa ya maida can, ya sama mata ma'aikata masu kula da ita, ya biya mata ta cigaba da karatunta har ta samu miji irin wanda yake fata a gareta amma ba Dagger da Zak-Shadow ba.....
      “Wai tunanin mi kake yi?”.
   Dagger ya faɗa cikin tsawa-tsawa. Ajiyar zuciya Mole ya sauke yana girgiza kansa. “Ba komai Oga, babbar damuwata kawai ina ta shiga? Waye ya ɗauke ta? Saboda mi ya ɗauke tan?”.
         “Karka damu zata dawo. Yanzu haka su Ayu nakan aikin nemanta. Bari naje yau inada meeting dasu oga aiki zai fara da zafinsa saboda kayan aiki sun iso, duk halin da ake ciki dai na dinga sani. Kaima kuma ka zama cikin shiri, idan ta kama kazo dole zaka zo”.
      Kai Mole ya jinjina masa. Daga haka sukai sallama ya fita a motar anata kiran sallar magrib shi kuma yaja motar ya ƙarasa gida. Dan dama daga asibiti yake yakai abinci. Sai da ya dakata wata mota da Malam Almu ya buɗe ma gate ɗin ta fito sannan ya shige, har yay parking idanunsa akan Nabeeha dake komawa ɓangarenta da alama motar data fita baƙinta ne.....

°°°°°°°°°°°°°°
   °°°°°°°°°°°°°°°

       Kusan mintina ashirin Nurse ɗin ta ɗauka tana gogema Nimrah da barci ya ɗauka jiki. Ta canja mata kayan da aka sako marasa nauyi. Dan simple doguwar riga ce sai hula. Tana ƙoƙarin saka mata hular ne ta buɗe idanun ta da sukai jazur tana yamutsa fuska. Hannu takai ta dafe kan.
Received at 10:47 AmDan haka Nurse ɗin ta dakata daga saka mata hular tana tambayarta kanta na ciwo ne?. Kan ta jinjina mata tana lumshe idanu, a lokacin Dada ya sake dawowa ɗakin.
       Tunda ya iso gaban gadon Nimrah ta buɗe idannunta a kansa, sai kuma tai narai-narai da su hawaye na taruwa a ciki. Cikin muryarta dake fita ƙasa sosai ta ce, “Dada kaina”.
    Bai wani jita da ƙyau ba, sai dai a motsin lips ɗinta ya fahimci abinda take faɗa. Maimakon zama a kujerar gaban gadon sai ya zauna a bakin gadon kusa da ita sosai, bayan hannunsa ya kai saman goshin nata. A dai-dai lokacin Nurse ɗin ta fito daga bayi hannunta ɗauke da ƙaramar tasa da ruwa a ciki, sai towel ɗin data goge mata jiki data ɗaurayo. Cikin in-ina take sanar masa zata sake saka mata towel a kanta. Hannu kawai ya miƙa mata alamar ta bashi, ai ko da hanzarin ta ta matso towel ɗin daga ruwan ta miƙa masa. Amsa yay batare daya kalleta ba, ya janye hannun Nimrah data riƙe kan ya ɗora towel ɗina. Sosai ta sauke ajiyar zuciya, tana mai ɗora hannunta akan nashi da yake ɗan daddana towel ɗin. Idanun su ne suka shige cikin na juna a hankali. Tai saurin janye nata tana rufesu. Shi ko ya cigaba da kallon fuskarta da tai fayau..........✍️
Received at 10:47 AM

9


..........Ita dai Nurse nata kallonsu kamar ta samu television, sai in ya cire towel ɗin ya miƙa mata ta sake jiƙashi da ruwa ta matse ta miƙa masa. Sai da sukai haka sau kusan uku ya tabbatar zafin kan ma ya sauka sannan ya barta. Badan Nurse ɗin taso ba ta shige ta fita. Shi kuma ya fara ƙoƙarin haɗa tea. Sai da ya kammala a karo na farko yay mata magana. Idanunta dake rufe ta buɗe, sai kuma ta janye ganin ita yake kallo, ga hannunsa ɗaya ya miƙa mata alamar ta kama. (Sun ɗaura miki aure da wani a gidan tun kina 7years, sunyi hakan ne kuma dan cimma burinsu akan ki da mu. Babu shakka a yanzu kuma zasu fara aiwatar da bukatarsu a kanki. Sai ki lura, ki kuma fahimce su musamman shi tun kafin yay miki illa, ki yaƙe shi tun kafin ya karasa kassara mu ahalinki. Dan yana da wayo, bazai taɓa nuna miki saɓanin abinda yake so ki sani akansa ba. Mun baki assignment kuma ki nema sanin wanda suka aura miki idan kin koma.....) Waɗan nan zantukan ne keta dawo mata acikin kai. Ƙirjinta ya sake bugawa sakamakon dawowar hirar Dada Da Daddy Imran da taji kalmar aure suma a bakinsu. Mi hakan ke nufi? Wa aka aura ma ita ne? Waye mijin nata?. Bata da mai bata wannan amso shin a yanzu, dan haka ta zubama hannun nasa idanu har kusan mintina biyu. Ita bata kama ba, ita bata tashi bisa umarnin daya bata ba.
       Dada dake kallonta cike da nazarin yanayin nata yay ɗan gyaran muryar data sakata yin firgigit, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana risinar da idanun nata. Zuwa yanzu ta ɗan ji daɗin jikinta saboda goge matan da akayi, daddafawa tai ta tashi kawai batare data kama hannun nasa ba. Shima bai ce da ita komai ba ya miƙa mata tea ɗin kawai. Maimakon ta amsa sai ta fara magana cikin rawar murya...
        “Dada! Dan ALLAH zan je wajen Mammah.”
     “Ni zan cinyeki ne anan?”.
  Yanda yay maganar kai tsaye yana danna waya ya sata saurin girgiza kai. Sai ga hawaye sharrr. Hannunta ɗaya takai tana sharewa. Hakan yasa shi ɗan dubanta, sai kuma ya janye idanun a lokaci guda. “Kisha ga magani da safe zaki je”.
        Kamar wadda bata gane yaren nasa ba ta ce, “Wajen Mammah ɗin?”.
    Yanzu kam gaba ɗaya ya ɗago yana kallonta sosai. Da sauri ta janye nata idanun data wara a kansa ta fara shan tea ɗin. Sai faman sauke ajiyar zuciya take a jajjare. Bata sake gigin kallon inda yake ba dan yaƙi ɗauke idanunsa a kanta harta shanye tea ɗin tas. Sai ga zufa na wanke mata jiki alamar ƙoshi...
          “Zaki ci abincin?”.
     Da sauri ta girgiza masa kanta. Shima sai kawai ya jawo ledar maganin nata da robar ruwa. Duk yanda suka rubuta haka ya bata, tana gama sha ta zame zata kwanta...
        “Tashi zaune”.
     Ya faɗa cikin umarni. Ba haka taso ba, amma bazata iya masa musu ba duk da itama dai kwanciyar ta isheta daman. Da kansa ya gyara mata filo ta jingina. Knocking ƙofar da akai ya saka Dada bada umarnin shigowa. Faro ne, dan haka Nimrah dake lullumshe idanu ta buɗe su da ƙyau tana gaishe shi. Ya amsa mata da kulawa yana tambayar jikinta. Tace masa da sauƙi. Hankalinsa ya maida kan Dada yana magana. Sai kawai Dadan ya miƙe alamar yafi son suyi maganar a waje. Dole Faro ya take masa baya suka fitan. Nimrah ta bisu da idanu abu na tsaya mata a maƙoshi. Dan taso maganar da Faro ɗin ya fara ayita a gabanta ƙwarai da gaske. Amma yanda Dadan yayi sai maganar mutanen can ta sake samun gurbin tasiri a zuciyarta.
     Fin mintuna talatin da fitar tasu, tun tana saƙe-saƙe har barci ya fara ɗibarta a hakan. Koda Dada ya dawo bataji motsinsa ba. Shima daya ƙaraso ya ɗan zuba mata idanu daga tsayen da yake, kafin ya duƙo kanta a nutsensa cikin rashin gaggawa ya fara gyara mata kwanciya. Ya rufa mata bargo zai janye jikinsa caraf ta riƙe hannunsa kawai ta juya kwanciyarta ta kwantar da fuskarta akan tafin. Da wani irin ƙarfi ta sauke ajiyar zuciya. Shi sai abin nata ma yaso bashi dariya. Amma sai ya gimtse yana kallon kyakkyawan fuskarta da hannun nasa. Kaɗan yay ƙoƙarin janye wa ta sake cikukukyesu ta matse har tsintsiyar hannun na kwanciya a ƙirjinta. Hakan ya saka shi kaiwa zaune dole.
Received at 10:47A ransa kam ayyanawa yake (Yarinyar nan tana da son tada zaune tsaye fa) a fili kam lips kawai ya ɗan damtse da haƙori. Vibration da wayarsa keyi ya tilasta masa buɗe idanunsa dake rufe. Dole yay amfani da hannunsa na haggu. Ganin Mammah ya sashi ɗagawa.
     Yanda yay sallama muryarsa a ƙurya gashi tana shaƙewa ya saka Mammah faɗin, “Lafiya dai?”.
        Gefen fuskar Nimrah ya ɗan zubama idanunsa da launinsu ya canja. Kamar Mammah na kallonsa ya girgiza kai kaɗan. “Ba komai Mammah. Har yanzu baki kwanta ba?”.
           “Yanzu dai nake shirin kwanciyar. Ina fatan dai kunci abincin ko?”.
       “Tasha tea tasha magani har tayi barci. Nima yanzu zanci. Dan ALLAH ki kwanta ki huta Mammah. In sha ALLAHU da safe da wuri zan kawo miki kayar ki”.
        Murmurshi Mammah tayi har yana iya jiyo sautinsa. Ta ce, “To ALLAH ya tashe mu lafiya. Kadai ci abincin kaima. Sannan kai mata addu'ar barci, dan ALLAH kada kai nisa da ita wani ya sake sace min ita”.
      Kaɗan ya rage yayi dariya. Ya dai daure ya murmusa kawai. Yana yanke kiran ƙasa-ƙasa ya furta, “Ni ai gashi nan tana neman sace ni idan ita wani bai sace miki ita ba Mammah.”
     Tamkar Nimrah ta jishi ne, tai juya kwanciyarta zuwa rigingine. Har yanzu dai hannun nasa bata saki ba, sai ma gyara shi tai akan ƙirjinta ta rungume sosai kamar wadda ta samu filo. A yanzu kam ya fahimci dukan zai masa yawa. Dan an kai wani matsaya ne na ga mari ga tsinka jaka. Ba arziƙi yay dabarar janye hannunsa, zata warto ya warce abinsa yana miƙewa. Yafi ganewa ƴar nesa-nesa, in ba haka ba za'ayi ja ya faɗo ja ya ɗauka ne a asibitin mutane....

      =============

      Gaba ɗaya ran Nabeeha a dagule yake. Ta rasa inda zata tsoma ranta taji sanyi. Ga Ismat tayi tafiyarta saboda taji haushi ta bata shawara taƙi ɗauka. Ko yanzu datai ma wata ƙawarta rakiya da tazo wai tayata murnar dawowar Dada sai da ta sake tambayar maigadi yace ƴan gidan har yanzu suna asibiti babu wanda ya dawo.
      Haka ta zauna ta zabga tagumi komai baya mata daɗi. Kewarsa take ji mai tsanani, so take ta ganshi cikin idanunta ta tabbatar gaskiya ne ya dawo. So take ta jita a cikin jikinsa kota samu nutsuwar shekara takwas da rabi data rasa. Amma sai ƙwalelen ɓoye kansa yake a gareta. Shin har yanzu yana fushi da ita ne? Miyasa bai nemeta ba? A tunaninta yana fitowa ita zai so fara gani duk duniyar nan. Amma sai taji saɓanin haka. Miyasa Haysam zai mata haka? Shifa ya mata laifi mai girma... Kiran daya shigo mata ne ya katse tunaninta. Ta sauke ajiyar zuciya tana ɗaukar wayar ganin Momy ce.
      “Momy wlhy har yanzu fa bai dawo gidan ba. Suma kuma duk suna asibiti wai”.
      Ta ɗan yi shiru alamar sauraren ɗayan ɓangaren.
    “Ni gaskiya bana son zuwa asibitin, ai saina koma warin magani”.
           “Shi ke nan naji Momy zanje goben”.
      Bayan katsewar kiran ta harari wayar tana ƙunƙuni. Dan zuwa yanzu ta fara fahimtar akwai abinda Momy ke nema ne. Inba haka ba har itace ke mata faɗa akan ƴan uwan Haysam. Bayan da itace ke zugata ma akansu. Baki ta taɓe tana miƙewa ta wuce bedroom, dama a falo take.....
     
      
<%><%><%><%><%>

         Barcinta yay nauyi sosai ta yanda yake jin saukar numfashinta na sauka a hankali. Dan haka ya sakama ƙofar key ya cire kayansa domin yin wanka. Dan gaba ɗaya a takure yake, kayan sun damesa ainun. A hakan ma ya canja su daga kakin da akai gumurzu a jejin can. Wanka ya fara gabatarwa yayo alwala. Koda ya fito jallabiyar da Dabo ya sayo masa ya saka, yay shafa'i da wutri sannan yay zaman shan tea da abinci kaɗan dan yunwa yake ji sosai. Duk da yanda ya cisa kaɗan sai da yaji ya takura, dan shi ƙa'idarsa baya wuce 8 na dare baici abinci ba. Amma gashi yau har kusan 12 ma ake magana. Yanayin takurar da abincin yay masa ya sashi buɗe ɗakin ya fita, ɗakin Imran ya leƙa, shima barci yake akwai kuma Yusuf a tare da shi. Sai kawai ya dawo wajen Nimrah. A cikin ɗakin ya gabatar da push-up da shi kansa bai san adadi ba, dan mintina kawai ya saita, suna cika ya miƙe yana sauke numfashi, a kujera ya zauna yasha ruwa, sannan ya kwantar da jikinsa ya lumshe idanunsa.
Received at 10:47Sai da jikinsa ya daidaita ya ɗauka laptop ya fara sana'ar tasa, duk da dai akan aiki ne...
      Kusan 1:am Nimrah ta farka a firgice har tana neman faɗowa a gado. Cikin zafin nama ya miƙe ya tareta, gaba ɗaya zufa ta jiƙeta, ga jikinta na rawa tana sambatu. Dole ya sakata a jikinsa ya rungume ta ya fara mata addu'a. Ƙafafunsa ne suka fara dayi, dole ya zame ya zauna a gadon jiyyar tata, har lokacin kuma tana a jikinsa. Ƙoƙarin kwantar da ita yay amma ta ƙanƙamesa har tana ƙunƙunin kuka a cikin barci. Babu yanda ya iya dole ya barta, sai ma zama daya gyara ya sakata a tsakanin ƙafafunsa shi kuma ya jingina da filo. Kanta na saman jikinsa ta zagaye cikinsa da hannayensa duk biyu. Hakan yasa numfashinsa ke sauka a saman cikinsa..........✍️
Received at 10:47 AM
[14/02, 9:15 am] Abue Saleh: 10

........Iska yaɗan furzar kawai ya ɗauki laptop ɗinsa ya cigaba da aikinsa. Shima zuwa 1:47am idanunsa suka fara yajin barci. Dole ya rufe Laptop ɗin ya zama a hankali ya kwanta a gadon duk da ya musu kaɗan, sai dai ya tabbatar yace zai tashi wata sabuwar futinarce kuma. Dan shi kam lamarin Nimrah da rigimarta sun fara fin ƙarfinsa. Aiko kamar abinda take jira kenan. Mutuniyar ku sai aka sake gyara kwanciya a jikin Dada ɗare-ɗare.
         Addu'a yayta ambata duk wadda tazo bakinsa. Har ALLAH ya taimaka tarzomar dake neman turniƙewa ta lafa cikin amincin ALLAH, daga haka shima barcin yay gaba dashi saboda yana jinsa sosai. Kiran sallar farko ya farka, baya buƙatar farkawarta taga a yanda suke kwance, dan haka cikin dabara ya zameta a jikinsa ya kwantar da ita a tsakiyar gadon yana gyara mata blanket shi kuma ya sauka. Duk yanda yaso tashi kasawa yay, sai da ya jinkirta zaune a bakin gadon hannunsa ɗaya dafe da kansa, ɗayan riƙe da cikinsa daya ƙulle masa tamau, ya ja mintuna a haka har ya ɗan sarara sannan ya miƙe zuwa bayi. Bayan wasu mintina ya fito yana goge kansa zuwa wuya alamar jiƙashi yayi, dan jallabiyar jikinsa ma ta nuna hakan kasancewarta coffee color. Sauri-sauri ya ƙarasa kimtsawa ya tafi masallacin cikin asibitin....

Kan Nimrah neman tarwatsewa yayi da mamakin ganin alamar fa Dada a ɗakin ya kwana. Duk da sai da ya dawo salla massalaci ya tashe ta. Daga yanda take zaune a bakin gado ta zubama ƙasan farar jallabiyar jikinsa idanu. Dan ba itace a jikinsa jiya da daddare ba.
      Gyaran muryar da yay ya saka ta ɗagowa gaba ɗaya ta kallesa. Sai kuma tai saurin kauda idanun nata dan shima ita yake kallo. Miƙewa tai kamar wadda ƙwai ya fashe ma a ciki ta nufi toilet dake a cikin ɗakin. Dan ɗaki ne guda da gado guda biyu kacal, komai na buƙata akwai a cikinsa har fright. Abinda ya bata mamaki ɗayan gadon babu alamar an kwanta akai, shiyyasa taketa wasiwasin a ina to ya kwana shi? Badai a zaune a kujerar nan ba?. Bata da mai bata wannan amsar, dan haka ta fito a bayin, daga

Please Login or Register in order to submit comment