You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
tareta badon haka ba fad'uwa 'kasi zatayi.
Lokaci guda idon Mommy ya 'kakkafe ta dafe 'kirjin ta tana shure-shure ciwon zuciyar ta ta tashi,
Ayush ta tsorita sosai da ganin haka da kyar ta iya d'ago Mommy suka fita daga d'akin
Falo ta nufa tana zuwa ta tarar da bodyguards duk sunyi cirko cirko kowa yaji jiki sai ajiyar zuciya suke sau'kewa
Da sauri sukayi kan mommy
'Daya daga cikin bodyguard ne ya d'aga mommy cakk yayi waje duk sauran ma binsa sukayi a baya
Motor suka shiga gaba d'ayansu
Motor biyu suka d'auka
Biyu suka shiga d'ayan motor and order car shima mutum biyu a ciki,
Kafin one minute sunbar harabar gidan, iya Ayush da mai gadi kawai aka bari a gidan, da sauri Ayush ta nufi gurin mai gadi tana fad'in "Ina zasu Kai ta?"
In short amsa mai gadi ya bata "Asibity" yana fad'an hakan ya shige cikin d'akinsa zallar tsoro ne a tattare dashi...
"Anya kuwa ba Aljanu a cikin d'akin nan? Junaid kuma? Uma ta ta6a bani labarinta akan Junaid, a'a ba wannan Junaid bane, to aina Zan samu Junaid d'in da Uma take so na taimake shi??
Waye wannan Junaid d'in? Innalillahi wa ina'ilaihi raju'un shi na gani acikin mafarki na idon sa kamar na namun daji,
A'a sharrin mafarki ne bashi bane......
Haka ta rin'ka sa'ke-sa'ke a raanta!...
*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️
*FREE* *BOOK*
👇👇👇👇👇👇👇👇
🐅 *MATAR* *DAMISA* 🐅
(the wife of tiger)
*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK* *ONE*
*PAGE* ➡️23 to 24.
Tana cikin nazarin duniya kamar wacce aka zabure ta tayi cikin falo da gudu kamar wanda taga abun tsoro, daga nan ta haura upstairs ta shige d'akin Junaid, da sauri taje gabansa ta tsaya tana ajiyar zuciya! Still a yanda ta barshi anan ta dawo ta same shi, lokaci guda taji wani irin tausayinsa ya kamata ta wani 6angaren kuma tarin tsanar sa ne acikin kwayar idanunta, bata kaunar ganin fuskar shi sunkuyar da kanta 'kasi tayi tana tariyo lokacin da ya buge mata mahaifiya da kalar wulakancin da ya yi mata itama yaso ya rabata da duniyar a lokacin, zazzafar hawaye ne yake gangaro mata ta d'ago da manya- manyan idanuwanta wad'anda sukayi jawur lokaci guda, kallon tsana takeyi mishi tana maganar zuci "saboda mahaifiya ta zan taimakeka, ba don haka ba ba abunda zaisa na ceci rayuwarka a halin yanzu sai dai ka hallaka! Allah yasa ka mutu" a halin yanzu mutuwar Junaid shine farin cikin Ayushh.
Rufe idonta tayi sosai ta d'ago da hannayenta biyu zata jawo shi, wani irin murya ne mai ban tsoro ya daki dodon kunnen ta
"KEE AYUSH KADA KI KUSKURA KI TA6A SHI, UMARNI NAKE BAKI, KAR KI KARYA MUN DOKATA, YANA CIKIN HUQUBA TA" tan fa ta bara jin kukan namun daji dana mujiyoyi 🦉 cikin firgici da tsananin tsoro yasa ta rungumi Junaid ta 'kan'kame shi cikin rashin sani,
(Ita da ake bata dokar kada ta ta6ashi amma tsananin tsoro yasa ta rungume shi gaba d'aya) dogon numfashi yajaa tare da d'ago kansa sama ya bud'e jajayen idanuwansa wad'anda suka canza launi tsabar azaba, wani irin sanyi yaji a cikin zuciyar shi kamar wanda aka watsa masa ruwan sanyi, sakin shi akayi daga sama ya tafo luuuu ya fad'a kan Ayush atare suka fad'o 'kasan lallausar carpet 'Kara Ayush tayi saboda jin yanda Junaid ya fad'o akan ta ga ciwon breast d'inta da ya fame mata shi!
Shi kuwa sai 'Kara narkewa yake ya 'kara 'kan'kameta, shi yasan kalar nutsuwar dayake samu daga gareta ba tare da yasan ko ita wacece ba, haka yake maida numfashi sama-sama!
Guri kuwa yayi tsitt ba alamar motsi sai numfashin da suke ja a tare.
(Ayush itace samun nutsuwar Junaid, itace kuma samuwar warakar sa indai ta samu rauninsa wanda yake jikinta, in har ta kusanci yanda Junaid yake to babu wani abun cutarwar da zai sameshi, a yanzun mah itace ta ceceshi daga azabar da ake gana masa, domin suma kansu Aljanun tsoronta suke,
Ita d'in dai itace AYANAR JUNAID 🧚♀️🧚♀️ ).
Dakyarr Ayush ta tattaro iya 'karfinta ta ture Junaid gefe tana mai da numfashi duk ya kashe mata jiki, ta d'ago zata mi'ke ta nufi yanda yake kwance da rarrafe ta Isa waro ido waje tayi tana 'kare shi da kallo abun mamaki duk ciwon dake jikinsa babu shi, jikinsa ya koma normal kamar bashi ne wanda akaita azabtarwa ba babu tabo ko 'kurzune d'aya sai tarin gargasar dake kwance saman kirjinsa,
Abun ba karamin bata mamaki yayi ba aranta take fad'in "Anya ba Aljani bane, nashiga uku nayi gamo" a tsorace taja da baya zata gudu yayi caraf ya ri'ke hannun ta, a hankali yake bud'e idanuwansa yana ganin Dishi-dishi har idon ya washe nan ya sau'ke kyawawan idanuwansa akan ta idon ya washe ya komo fari soll, a hankali yake lumshe ido still hannunsa yana ri'ke da nata a hankali yake motsa 'karamin bakin shi murya Ciki-ciki yake fad'in "Wace ce ke?" Murya na kakkarwa tace "Ni ni ni ni" ta rasa mai zata ce tsabar tsoro kuma lokaci guda yayi mata kwarjini ga wani shakkar sa datake ji! Tana cikin motsa baki ba tare da yasan mai take fad'i ba ya katsar da ita "please can you carry me to go inside bathroom?"
Yayi maganar da harshen turanci, waro Manya-manyan idanuwanta tayi waje tana binsa da kallo, seriously taji abunda ya ce! Duk da batayi karatun boko ba amma ta iya turanci sosai ta koya agurin mahaifiyarta domin Umanta sai data zo Nigeria sannan ta koyi Hausa amma yarenta daga Ghananci sai turanci ta kuma iya yaren French, haka itama Ayush duk ta iya yaren sai dai yaren mahaifinta ne bata iya ba wato fulatanci.......
Ita dai bazata iya maida masa da amsa ba sai dai tayi magana da zuciyarta "How comes Zan iya d'agaka kana nam gardi da Kai, amma sai dai kyakykyawa ne mutumin" tana cikin maganar zuci taji ya ri'kota zai tashi ai tunin ta fad'a jikin shi 'karfinsa ya ninka nata sau goma 😄
Shima komawa yayi ya kwanta yana binta da kallo, d'agowa tayi a hankali suna fuskantar juna, numfashin su yana dukan na juna, ido cikin ido suke kallon juna! Dakyar Ayush ta iya cewa "you're a strong man, I can't....... Kasa 'karisa maganar tayi sakamakon Breast d'inta dake mata ciwo ga wani feeling da yake shirin kawo mata ziyara duk ya kashe mata jiki shi kuwa babu wani abunda yake ji babu sha'awa a ransa an gusar masa da shi,
Gaba d'aya jikinsa ne yake masa ciwo, shi bai San meya faru dashi ba a tunaninsa duk abunda ya faru dashi mafarki ne saboda ya duba jikinsa babu alamar ciwo...
"I need to bath, please d'agani mana ko na zama gadon kwanciyarki ne" yana magana ne a lokacin da yake shirin tashi...
A kunya ce Ayush ta tashi daga kansa, ita dalilin dayasa ta cigaba da kwanciya masa rad'ad'inda Nononta keyi mata ne yasa ta kifar da kanta saman kirjinsa hakan yasa yayi mata magana.
Tashi yayi yana tafiya a hankali zuciyarsa kuwa cike tam da tambayoyi "shin meya same ni haka bana jin dad'in jikina, and than who is dis girl? And what she her doing inside my room in dis midnight?? still ni da nake kwance on my bed meya kaini 'kasa?". Haka ya shige cikin toilet yana wannan tunanin!
Itama tashi tayi tana maganar zuci "tabbas wannan shine ya sha'ke mun wuya bayan ya buge mun mahaifiya da mota, Anya kuwa yanada lafiya kuwa, Ina tantama akansa wannan ba mutum bane, na ganshi a wani mummunan hali yanzu kuma Gashi lafiyarsa klau ba ciwo a jikin shi Anya ba mafarki nake yi ba..? Shin meye silar faruwar haka..? A lokacin da ya raunana mun breast nabar d'akin normal amma kuma bayar faruwar haka meya faru..? Zanyi bincike akan wannan al'amarin......"
Nufan hanyar fita tayi taji an tsayar da ita "where are you going....?"
Waiwayowa tayi da sauri ta kalle shi fuskarsa a d'aure ba annuri yana d'aure da towel a kunkumin shi alamun ya watsa ruwa ne a jikinsa..
Nufan wurin da take tsaye yayi har sai da 'karaso gurin da take GAF to GAF suna fuskantar juna ya ri'ke kunkumin sa yana mata kallon tuhuma,
Ganin kallon yayi yawa yasa ta sunkuyar da kanta 'kasa tana kallon carpet, hannu yasa ya tallafo ha6arta suna fuskantar juna ya ce "who are you...?"
Shuru tayi batace komai ba sai siraran hawayen da ya gangaro mata.
Sakin fuskarta yayi yana fad'in "can't took to me..? Okay have a seat" ya nuna mata bakin gado, ya koma gaban mirrow yana Milka jikinsa da cream mai shegen 'kamshi! Ayush zama tayi a bakin gadon kamar yanda ya umarce ta tana ta sa'ke-sa'ke a raanta cewa "yanzu kenam yana nufin ya manta da fuskata..? Ya manta da matar da ya d'auki raanta...?" Lokaci guda kuwa taji kamar ta sha'ke shi ta baya.. Tana bin duk surar jikinsa da kallo "gaskiya yana da 'kirar jiki mai kyau, ga tsayi ga fad'i ga d'aurarran jiki ga kuma gargasa ta ko ina a kwance luff-luf gwanin sha'awa sai dai kuma shi baya yabon mace kamar yanda mace take yabonsa bcox baya ra'ayin mace kwata-kwata, bai ta6a jin son mace ko sha'awarta ba haka yake zaune daga gida sai gida ko aiki baya zuwa yanzu....
Ayush fah ta kafa idonta akan Junaid bata San lokacin da take sauwa murmushi ba,
Shi kuwa gaba d'aya ya tsargu da kallon da takeyi mishi , ransa a 6ace ya juyo gareta akaci rashin sa'a jikin mirrow ya Kama towel d'in dake d'aure dashi ya zame gashi bayan towel babu komai a jikinsa .
Ayush tana ganin haka ta zaro ido waje wani irin ihu tayi tabi saman gadon yaraff ta fad'i sumammiya taga abunda bata ta6a gani ba tinda uwatta ta haifeta....... Shi kuwa ihun datayi ne yasa ya bita da kallo bai bi takan towel d'in ba haka ya tsaya zigidirrr yana kallon Ayush wacce ta suma akan gadonsa........
*TO* *BE* *CONTINUE* *INSHA* *ALLAH*
*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️
*FREE* *BOOK*
🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)
*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK* *ONE*
*PAGE* 25 to 26.
Tsaki yaja ya nufi yanda jerin kayan baccin sa yake ko sauraronta baiyi ba, haka yake taku tsindir ba kaya a jikinsa ga towel kuma a yashe a 'kasa, Riga da wando ya zaro marasa nauyi sleeping dress milk colour ya sanya su a jikinsa ba 'karamin kyau kayan sukayi masa ba, sai hasken sa ya Kara bayyana!
Ya feffeshe jikinsa da turare mai sanyaya zuciya, yana kammalawa ya nufi hanyar fita zai dubo mommyn sa kamar wanda aka dakatar da shi ya tsaya cak sannan ya dubi clock dake manne a jikin bango 3:30 fasa fita yayi a bayyanai yace "nasan kinyi bacci yanzu, rest in peace my Mom" juyawa yayi ya nufi gurin bed d'insa yabi ta gefen Ayush ya kwanta, jawota yayi close him ya kashe light d'in d'akin sannan yaja musu mayafi rungumarta yayi suna fuskantar juna, da haka har bacci yayi awun gaba da shi! Itama Ayush daga suma ta wuce da yin bacci,
Asubar fari anata 'kiraye- kirayen sallah dai dain lokacin wayar Junaid ya hau ringing
Juye-juye Ayush ta Fara yi tana mur'tsika ido tana 'ko'karin bud'e idonta taji an 'kan'kameta juyar da kanta tayi tana fuskantar Junaid Wanda numfashin su yake gaurayuwa, a firgice ta zaro ido waje ga tsananin tsoro da ya bayyana akan fuskar ta, a hankali take janye jikin ta daga nasa har ta samu ta zame kanta tana maida numfashi tare da dafe kan kirjinta tana kallon kyakykyawar fuskarsa shi kuwa sai sharar baccin sa yake lokaci guda tasau murmushi har saida dimple d'inta ya bayyano, haka kawai take jin nutsuwa a tattare da ita..
Wayarsa ce ta sake ringing a Karo na biyu, idonta na kan wayar batada niyar picking har sai da ya kusan katsewa sannan takai hannun ta kan wayar, Doctor Hasheem taga an rubuta picking tayi ta Kara akan kunnen ta tana sauraron Wanda ya Kira "Hello Captain Junaid, mahaifiyarka tana cikin mawuyancin hali sunanka kawai take ta ambato, please kazo yanzu har saita ganka kafin mu iya magance matsalar ta....! Shuru yaji anyi ba amsa, ya sake cewa "Hello Captain Junaid kana jina kuwa...?" Katse wayar Ayush tayi ba tare da ta amsa masa ba, wani irin kuka ne mai cin rai yazo mata, tana cikin kukan taji wani 'kiran ya sake shugowa wayar da sauri ta katse 'kiran tayi switch up d'in wayar gaba d'aya ba tareda tasan Ina ta danna ba domin Ayush ko keypad bata iyaba balle wannan 'katuwar waya 'kirar iPhone 11. Bud'e wardrobe tayi ta tusa wayar cikin kayansa ta katse wayar ne saboda kar ya Kai mata naushi kumadu, tayi waje da gudu tana toshe bakinta da hannayenta kuka ne yaso ku6uce mata....
Bedroom d'insu ta nufa tana shiga ciki ta doku a saman gado, lokaci guda ta fashe da kuka tana fad'in "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, mahaifiyata ta tafi ta barni itama wacce take kula dani tana kwance rai a hannun Allah, Allah ka taimake ni ka bawa Auntyna lafiya, idan ta mutu bansan Ina zan sa kaina ba, wayyo niii"...
Bayan ta gama kukanta mai isanta ta tashi ta shige toilet jiki ba 'kwari Alwala tayi sannan ta tsayar da sallah tare da lafulfuli, Addu'o'i ta shiga karantowa tayi Addu'a a mahaifiyarta tare da nema mata gafarar ubangiji sannan tayiwa momin Junaid Addu'ar nema mata lafiya...
Junaid yana kwance yanaji har an shiga sallah yanaso ya tashi yayi sallah amma dai dai lokacin aka shagaltar dashi da wani mafarki mai ban tsoro da kuma firgici....!
Gashi a cikin tsakiyar ruwan da bashi da iyaka, crocodiles ne sun kai goma suka nufo shi a cikin ruwan nan, yanata gudu a cikin ruwan ya kasa isowa karshen ruwan su kuwa sunyi daf dashi suna bud'e manya-manyan bakinan su, wani 'karamin jirgin ruwane yazo ya tsaya ta gabanshi sai dai jirgin ya d'anyi nesa da shi wata kyakykyawar Yarinya ce mai sanye da fararen kaya dogi da suman gashin ta har gadon bayanta yarinyar farace soll ta ware hannayenta biyu tana fad'in "Junaid taho, kazo gareni don ka tsira da rayuwarka...."
Tsayawa yayi cakk a cikin ruwan yana kallon kyakykyawar yarinyar dake masa magana, zazza'kar muryarta ne ya sake dukan dodon kunnensa "JUNAIDDDDD ka kula bayanka" kafin ya ankara har sun kawo masa hari, "JUNAIIDD ga wannan, ta cillo masa wata doguwar tokobi mai she'ki irinta sarakuna.
Hannunsa yakai ya cafko wu'kar kafin yakai musu sara har sun rufa mishi 'kasin ruwa suka lumar da shi.
"Junaaiidddd" yarinyar ce ta kwalla mishi 'Kira sannan ta ce "karka bari suyi Nasara akan ka, ka zamo jarumi na gaske, kayi ya'ki dasu kamar yanda kake a filin dagaaa...... Bata 'karisa maganar ba taga jini duk ya malale ruwan, fashewa tayi da kuka tana fad'in "why! Why!! Why!!! Meyasa zaka bar ma'kiya suyi Nasara akan ka Junaiid.."
Ji tayi an ri'ke jirgin da sauri ta le'ka 'kasin ruwan
Junaid ta gani ya d'ago da kansa duk ruwa ta ko Ina a jikinsa, kallon juna suka tsayayi murmushi yasau mata itama ta mayar masa da martani
Mi'ka mata hannu yayi ta ri'ko shi d'aya hannun kuma yana ri'ke da takobin nan ya haura cikin jirgin still bai daina kallonta ba itama idonta akansa
Daga bisani ya soma motsa lips d'insa zaiyi magana tayi saurin katse shi ta d'ora yatsanta akan lips d'inta "Shhhhhhh 🤫🤫 you wanted to ask me who I'm again...?"
Abun ya d'aure mishi Kai a ransa yace "wace ce wannan" kamar tasan abunda zai tambayeta kenam!
Murmushi tayi ta kanne masa ido d'aya 6atttt ta 6ace masa, a firgice ya mi'ke tsaye yana waiwaye baiga kowa ba....
Firgitt ya tashi daga baccin da yake duk gumi ya wanke masa jiki duk da A.C dake d'akin
Yana furta "Laa'ilaha ilalla, Muhammadu rasulullah S.A.W"
Agogo ya kalla 8:30 waro ido waje yayi "A'Uzubillahi Mina shaid'anin rajin, sallar Asuba has already pass" a gaggauce ya tashi ya shige toilet yayo alwala ya tsayar da sallah...........
Mommy kuwa tana kwance a gadon asibiti tana 'kiran sunan Junaid har numfashin ta ya d'age cak oxygen aka sanya mata domin da sauran bugun zuciyar,
Likitoci sunyi ta 'kiran wayar Junaid switch up daga farko ya shiga amma daga karshe kuma switch, bodyguards kuwa suna kawo mommy hospital suka fece Junaid yafi karfinsu zai iya hallaka su wata Rana.
Doctor Hasheem har gidan yaje dubo Junaid saidai an'ki bud'e gate, shima mai gadi yana kwance zazza6i mai zafi ya rufeshi ko kwakkwarar motsi baya iya yi, hakan yasa Doctor Hasheem juyawa yayi tunanin babu kowa a gidan, shima kanshi ya shiga damuwa ganin Doctor Fateemah a wannan halin
Yana
Book Chapters
Chapter 5
Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500