You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
Downloaded From https://arewanovels.com KAR TASAN KAR
JIGO: AMANAR ƘAWANCE
GROUP: 11
[8/3, 4:17 PM] Gimbiya wrt: *KAR TASAN KAR*
(Qawatace)
*littafin Gasa ne masoya na 2021 dan Allah in kin karanta ki share*
*GROUP 11*
*Jigo “AMANAR QAWANCE”*
Na Gimbeeya (MSS1LOVE)
*Part 1*
Da sauri tafito daga wankan datake tana goge kanta da towel direct wajen wayarta ta nufa saboda ringing d’in datakeyi tin tana band’aki ganin sunan my mom yafito yasata saurin d’agawa cikin girmamawa ga mahaifiyarta tace “mom ina wankane wlhy inajin ringing kina kirana am srry,kuna lapia??”
Momy cikin zaquwa tabawa ‘yarta labarin daya d’agamata hnkl tace “ai ba batun lapia meemah (Amina)kinsan kwa wa babanki ze aura???”
Tace “mom waidama daddy aure yakeshirin qarawa “
Tace “ke dallah ba aurenba kinsan wa ze aura???”
Meemah tace “a a momy sekin fad’a”
Tace “tom aminiyarki aysher wacce kullum bakida zance se nata ta hannun damanki ita ze aura wlhy ashe har ankai kud’i da sa rana wata 2 yanxu hakanma anci wata 1 da kwanaki “
Dafe qirji tai kamar tana gaban momyn nata tace “are u serious momy aysher dai besty ta???momy anyakwa da gsk ne wlhy besty bazatamin hakaba “
Momy tace”sekuma kiyi daga majiya me tushe naji wannan zancen,Dan naji daga bakin wacce bazatamin qaryaba “
Itadai meemah mamakine yakamata dan ita haryanxun bata yardaba d’azun su gama chart da besty suna shirin bikinta ita da DR tana shirin fitar da anko amatsayinta na aminiya ace wai daddy nata zata aura kai da sake,muryar momy ce ta katsemata tinaninta “ke meemarh dole musan abunyi dan baze yiwu ba wannan abin kunya dacin amana dole musan abunyi “
Tace “wlhy momy niharyanxu ina kokwanto besty fa DR zata aura kuma fa nizamma fito da anko,inhakane kenan nice amara abikin yiwa uwata kishiya?
Momy tace “ah toh ke kikasani dan tacemiki DR sunansa tagayamiki kuma ubanki ma ai doctor ne a boko “
Dogon numfashi taja kafin tace “momy bani mintina kad’an zan kiraki “
Tace”tom”
Safa da marwa meemah tafara ad’akin ta inda duk kwakwalwarta ta kulle batasan ta ina zata faraba,inda gaskene kuwa besty ta gama ci mata mutunci,zata had’a shinfid’a d’aya da ubanta cafff.
Wayarta ta d’akko tafara dialing layin besty seda tai ringing uwa bazata d’agaba sekuma ta d’aga cikin voice d’in bacci aysher ke magana,
“Hello besty kintashene abaccina wlhy ina mafarkin DR baki kyautaba “
Meemah tace “ayyaeh srry besty,besty nikam natambayeki “
Tace “inaji “
“Waye DR dazaki aura “
Tace “banganeba wayeshi kuma ???shine future hubby d’ina “
Meemarh tace “nasani ai ma ana meye sunansa?
Numfasawa tai kamar bazata fad’iba sekuma tace “sunansa Yusif ya akayine “
Gabantane yace rasss jin sunan dadynta da sauri tace “aysher dady na zaki aura???
Wata ‘yar dariya aysher tai tace “dadynki kuma kina nufin mahaifinki amma wlhy besty kin mugun rainan wayo to ni DR d’ina saurayine abuna ina ni ina auren dady shifa mahaifinane “
Wata ajiyar zuciya tasauke tace “hmmm dama nima nasan bahaka bane akwai amana ai ko amafarki haka baze yiwuba “
Aysher tace “gsky kam wannan labari se dai ko afilm,hhhhh wayaga aysher ta auri uban bestynta “
Tace “kinfara ko kinga banson zulaya yanzu de kihau online nazab’o mana anko kiduba material d’in dinner da atamfar kamun kiga “
Aysher tace “laaaa besty bangayamikiba ai ba dinner se kamu daza ai kawai agida “
Meemah tace “au haba kice angonnaki uztaz ne “
Tace “ehmn kituron ta kamun sena tura group namu sugani “
Tace “ok “
Nan sukai sallama meemah ta samu nutsuwa saboda tasan hakanma bame yiwubane,kawai dai munafukaine suke so su dora momynta awata hanya dan su samu shiga,nan take kira momy tagayamata yasukai da aysher itama tasamu nutsuwa tace “to watak’ila sunane yazo d’aya “
Itama meemarh tace “hakane kam “
.................
To bikifa nata matsowa meemarh se uban shiri take zatai bikin aminiya wajen kaya kala biyar ta d’inka shikansa mijinta seda yay sabon d’inki na d’aurin aure.kullum kuwa cikin waya da aysher suke wajen tsare tsaren biki.
*RANA BATA K’ARYA SE DAI UWAR D’IYA TAJI KUNYA YAU SAURA KWANA UKU DAURIN AURE*
Invitation card na d’aurin aure keta yawo dan har group d’insu meemah seda aka tura,su hajiya meemah anyi busy wajen tailor don tasamu d’inkunanta shiyasa ko online bata hawa,haka itama momyn meemarh taga katin daurin aure amma batasan cikakken sunan aysher ba shiyasa bata wani kai hankalintaba.
Ranar kamu su meemah agidansu aysher tayini akai biki aka rakashe tasha rawa kai kace budurwace haka d’anta areef ma yaci gayu se dare tabar gidansu aysher inda sukai sallama zataje gidansu takwana washe gari d’aurin aure tadawo dan itama dadyntane wai ze qara aure duk da momy tahana kowane shege zuwarmata gida wai da sunan biki.
Haka sukai sallama da aysher inda tanunamata cewa ya akai dadynta ze qara aure duk shekarun dasukai da momy.
Meemarh tace “hmmm maza kenan barsu da abinda sukeso nidai se gobe naga dare ma seyi yake ga farouq yazo d’aukana yana mota yana jirana “
Aysher tace “tom ngd besty Allah huta gajiya “
Meemah tace “bazaki zo ku gaisaba?”
Tace “kai nagaji wlhy kigaisheshi kice in yanayi yacanja ai baza amanta da zamanin dayawuceba “
Jimmm meemarh tai dan bata gane Hausarba ahakadai suka sallama meemarh ta taho gidansu.
................
Zaune suke da momynta inda momy takalleta tace “aibadan ansan ba fuskaba da yanxu ‘yan kauye suncikan gida waisu sunzo biki “
Meemarh tace “wlhy daddy yajamana magana kamarshi dan Allah dan annabi wai aure budurwarma kuma haba!!!”
Momy ta gyad’a kai tace “hmm yazami to aikin gama yariga yagama ,tinda bawanda ya isa yadakatardashi kinsan halinsa kinga ni katin d’aurin aurenma dan kunyama ban rababa “
Drower ta bedsite d’inta tajanyo ta d’ebo katinannan.
Meemarh take kwance mik’ewa tai tana ummah nagani ni wlhy ma ko katin banganiba,mik’omata tai.
Mitsike idonta takumayi ganin sunan Aisha ibrahim jingau cikin kad’uwa tace “momy wannan ai aysher ce “
Momy zaro ido tai tace “wai bestynki ??
Tace “itafa wlhy aisha ibrahim jingau sunan tane “
Momy tace “aidama wlhy jikina yabani nasan wacce tagayamin bazatamin qaryaba kika dage cewa ba ita bace aigashinan yanxu kuwa lokaci yak’uremana “
Hawayene suka fara fitowa daga idon meemarh lallai aysher tamayar da ita sakarya duk shagalin bikin dasuke ashe na ubantane Allah wadaran ta,hawayene yaci gaba da zuba a idonta tama rasa mezatace.
Momy ce tace “kingafa kuka bashine maganiba faruwa tafaru aiseda nagayamiki kika qaryata “
Wayarta meemah ta d’auka zuciyarta namata zafi tafara kiran besty kira wajen nawa batai picking ba se a na biyar d’in qanwarta suhaima tad’aga tace “wlhy wayar bata hannunta “
Meemah tace “to kikamata wayar yanxu meemah cea “
Suhaima tace “aiba agida takwanaba yanxu dare yayi kuma sedai dasafe “
Cikin takaici meemah takashe wayar yacce taga rana haka taga dare.tana ta saka da warwara aranta.
*to misalin k’arfe 11:30 na safe aka d’aura auren aysher ibrahim jingau da Alh yusif Ahmad shattima*
Momy da meemah sunyi tsuru ad’aki dan kwa yau bayacce momy zatai abokan alh yusif suncika gidan haka bayacce sukai sunagani masu aiki suna takaimusu abinci fa alh yusif baki har kunne,itako meemah ko ruwa tinsafe takasa sha sekiran wayar besty take dan areef ma nata kuka taqi saurarenshi se momy keis rainonshi.
Kiran besty neis yafara shigowa wayarta da sauri tad’aga tana “wlhy kinji kuny aysher kinci amanar Qawancenmu Allah ya isa tsakanina dake aysher kin yaudareni ubana shizaki aura “
Dariya aysher tai me isarta kafin tace “Au wai dama babankine????to koma shine aiba haramumbane,yanxude and’aura koba komi niyanxu uwarkice ba kowane magana yakamata kigayanba “
Wasu zafafan hawayene suka zubowa meemah tace “Allah yatsare kizama uwata munafuka matsiyaciya kinyi asara aysher “
Da sauri aysher tadakatar da ita tace “Dani dake aga wayay asara karki manta KAR TASAN KAR ke bance kinji kunyaba seni aidama ance inharshe yafurta besan maganar daza ajuyarmasaba kuma ramuwar gayya tafi tagayya zafi zaki iya tina waye farouq awajena???zaki iya tina meke tsakanina dashi ,naji ni iya auren ubanki nai amma ban tarwatsamiki farincikinkiba ban saki amasifa irin wacce kika saniba “
Meemah matuwar zaune tai tafara hango rayuwarsu abaya.
Menene asalin labari ??????
[8/3, 4:18 PM] Gimbiya wrt: *KAR TASAN KAR*
(Qawatace)
Part 2
Asalin labari!
Rana d’aya aka kaisu senior secondary school me suna gifted science academy,tin ranar zuwansu school aka had’asu sit d’aya, aysher Allah yayita dason mutane shiyasa cikin qanqanin lokaci suka saba ,dan ko break suka fito tare suke siyayya itakuma meemarh batada rowa abunta bairufemata idoba, haka dai suke zamansu cikin qaunar junansu dan in d’aya batazo ba school d’in bataiwa d’aya dad’i haka ba wacce ke buyewa d’aya sirrinta har kwatance ake dasu.
Haka in driver aysher yazo d’aukatan haka ze d’aukesu yafara kai meemarh unguwarsu sannan yazarce da aysher dayake hanyarsu d’aya ita meemarh tana sharad’a phase 1 itakuma aysher suna NDC quarters abunsu gwanin sha awa.
Kwanci tashi ba wuya ahaka har suka zo SS 3 sunyi matuqar shaquwa dan meemarh itace headgirl itakuma aysher assistance headgirl ,aysher sau 3 ta tab’a zuwa gidansu meemah shima taje duba tane sekuma dazasu unguwa ,dan dukansu ba afiya barinsu fitaba amma meemah tana d’an zuwa gidansu aysher ba laifi dan maman aysher ma aikaciyace shiyasa in meemarh tana free takan tambayi momy dayake momy tasan yacce suke bata hanata haka zasu yini susha hira.
To yau ranar tafarko dasuka fara jarabawar waec d’insu ,bayan sunfito daga exam ne aysher tasamu meemarh tace “besty da story fah “
Cikin zaquwa dason labari meemarh tace “wayyo bani nasha “
Tace “meemah mafarkina ze zama gsky addu ata takarb’o meemarh irin mijin danakeso nahad’u dashi”
Tsalle meemah tai tai hugging nata tana “da gsk besty???dama za asamu irin mijin da kikeso kyakkyawa fari dogo d’angayu kuma lawyer??”
Tace “wlhy nima nayi mamaki har irin aikin danakeso kuma kinsanme sunanma irin wanda nakeso omar amma farouq ake cemai “
“Kai!!!yau dad’e ai celebration congratulations besty saura ni wlhy naji dad’i”
Aysher tace “aini yanxu yarinya nacanja ra ayi candy to marriage dan wlhy bazan bari farouq ya subuceminba “
Tace “da gskynki wlhy yanxu yaushe zanga angonnamu “
Cikin farinciki tace “ in aka tashima shize zo yakaimu gida “
Meemarh tace “tom”
———————
Abakin gate d’in school nasu barrister farouq yay parking yana jiran qarasowarta,can yahangeta tare da qawartata,qarasowa sukai nan yazuge glass d’in motor yace “ ah ya exam naga alama kungaji “
Aysher tace”ehwlhy ga qawata kuma aminiyata meemah”
Nan suka gaisa cikin fara’a.
Harda tsokana yana “aminiyarmu shiga mutafi”
Meemarh kuwa tama rasa mezatace dan duk yacce aysher ke misaltamata shi yawuce gsky guy d’in ajin farkone sema kaji muryarshi.
Aysher ce tadawo da ita daga tinanin datake tace “shigaba muje “
Gaba aysher tazauna meemah nabayansu ahanya farouq seyabon Qawance su yake har cewa yay suna kama duk da baifiya surutuba amma se jansu da magana yake,dariya sukai gaba d’ayansu nan aka ajjiye meemah suka zarce.
Dare yayi dare idon meemah kiriiii lips d’in farouq take tinani dakuma maganrshi wata zuciyar na kwab’arta tana “haba meemah karkiyi haka bestynki fa kidaurewa zuciyarki “
Wata kuma tana “to semeyene abunda zuciyarki takeso kibata dan wlhy ko mutuwa zan iyayi akan nasamu farouq “
“To ya aysher zatai bayan kinsan mafarkintane farouq “
Aranta tace “ohooo mata “
To saura paper 2 sugama kullum ayshe cikin labarin farouq take hakan yasa meemah kuma qaunarsa gashi ko siyayya zai harda meemah yake had’awa,aysher ce takalli meemarh tace “meemah wlhy farouq yazama rayuwata kinga arana inbangashiba senaji uwa zanmutu wlhy gsky innarasa farouq mutuwa zan “
Meemah tagwalo ido “mutuwafa kikace ?caff toyanxu yaushe ze turo?”
Aysher tace “eh yace damungama exam ze turo kuma beso asa rana meyawa 3month haka “
Gaban meemahne yace dummmmm lallai tanaji tana gani zata rasa masoyinta 1 wanda take matuwar so cafff ,azahiri kuwa setace “wow naji dad’i amma ,besty takusa zama amarya “
Aysher tace “kema wlhy kifito dashi inbahaka ba har na haihu nabarki “
Tace “besty soon nima zakiga nawa “
Tommm Alhamdulillah sungama exam ranar final meemah tai iya qoqarinta ta d’auki number farouq awayar aysher batare data saniba.
————————
*farouq ana gab da rasa rai wlhy zan mutu farouq kaceci rayuwata karka barni na haukace asonka farouq inban rayu dakaiba to bawani amfani arayuwa saboda narasa jin dadina*
Text message d’in dayashigo wayarsa kenan cikin mamaki yaduba yana wannan wace?? nan yabi number dakira ba ai picking ba,haka text din safe daban narana daban gashi inyakira number ba adauka.
To safiyar lahadi aka anshi kud’in zancen aysher daga wajen farouq dubu d’ari yakai,aysher tai murna sosai dan aminiyarta tafarakira tagayamata.
“Besty wai da gsk kike ko da wasa?”
Abinda meemah tafad’a kenan aysher tace “nataba miki wasa irin wannan kuma sa rana wata uku “
Kiiiitttt meemah takashe wayar itakuma aysher atinaninta charge natane yaqare shiyasa batakuma kiraba.
Abu fa yaqi ci yaqi cinyewa meemah harda zazzabi ga text message data damu dayi mishi ,yaukam dayakira bata d’agaba seyamata message
*haba kekam meyasa kike b’oye kanki yakamata kibayyana wace ke text d’innan ya isheni kinasama kanki damuwa bayanni nakai kud’in aurema *
Reply tamai da *eh nasani sanin hakannema yasani tinanin nasha poison nahuta*
Dasauri yay reply *auzubillah meyay zafi haka wace ke plx*
*idan nagayama wace ni kai alqawarin zaka soni???*
Yace “gsky bazan alqawari ba dannakai kud’in auren wata “
Tace “nasani amma koda nalokaci 1 ne “
Yace “shikkenan wace “
Tace “zan kiraka mi magana”
Daga haka call yafara shigowa da sauri yay pick yanajin muryar yafara tinanin ina yasanta.
Yace “ehumm inaji “
Cikin shehseqar kuka tace “nice meemah aminiyar aysher wacce zaka aura wlhy farouq tin ran danafara ganinka naji bazan iya rayuwa bakaiba”
Jiyay kansa yay nauyi danma namijine yace “whattt !!!!! Meemah are u crazy????
Tace “eh indai akankane nahaukace farouq dan Allah ka saurareni plx wlhy sonka nake “
Yace “amma kinji kunya wlhy kinci amanar qawance “
Tace “eh naji bayacce zanyine “
Kitttt yakashe wayarsa,fashewa tai da kuka sosai.ita yanxu tashirya karb’ar komeye akan farouq.
B’angaren farouq kuwa hankalinsa atashe yake mamakine yacika zuciyarsa ganin yacce aysher take da meemah lallai ba amana ko kunyarsa batajiba yanaciki tinaninnane kiran aysher yashigo cikin kulawa yad’aga yana “mrs farouq ko nace ayshfa (aysha da farouq)yacce friend naki suke fad’i ya kike?“
Tace “hmmmm baby kenan kasanme wlhy inaso mi maganane dakai “
Yace “inaji “
Tace “kaga bikinnan ba dayawa akasa lokaciba dama inaso nagayamane kayan fitar bikina inaso kamana komi tare da meeemah ma ana iri d’aya “
Farouq ne aranshi yace” Allah sarki aysher bakisan me meemah keshirin yimikiba amma nayi alqawari bazan sanar dakeba saboda bazan biyemataba kuma bazanso qawanceku ya lalaceva azahiri kuwa seyace “kinga dear nifa ke kad’ai zan aura why zanyi jigilar ta gsky banda kud’i bazan iyamataba “
Mamakine yakamata ganin da shiyake cewa ai ranar bikinsu komi iri daya yakamata suyi dan meemah ma ! aikamar amarya zata zama saboda amintarsu,cewa tai “baby kai kake fad’in haka da bakinka ?meemah fa nake nufi meemah yusif qawata kaifa kk cewa komai tare yakamata muyi”
Dakatar da ita yay yana “look aysher kibar mgnr meemah nan plx qawa qawace amma abun yayi yawa nizan fita office ma se anjima zankiraki “
Kafin tace komi ya kashe wayar.
Mamakine yacika aysher.
————————-
Tom barrister farouq zaune yake a office nashi dan anjima yanada wata shari ar dazeyi hakan yasashi binciken hujjojin da ya ajjiye ze gabatar gaban kotu “
Salolar office d’ince tafara ringing da sauri yad’aga “yallabai kayi bakuwa “
Yace “ta iya shigowa “
Meemah ce wurjan wurjan tana shigowa tazube aqasa gwiwarta biyu aqasa tana “farouq dan Allah dan Annabi wlhy zan mutu farouq kai kad’ai nakeso farouq katausayamin “kuka take kamar ranta zaifita.
Hakan yasa tabashi tausayi sakkowa yay daga kujerar dayake kai yay facing nata yace “meemah d’ago ki kalleni “
Jajayen idanunta ta daga dasuka kumbura takalleshi, yace “meemah son dakike min bakai rabin wanda aysher keminba burinki kawai kika sani kinsan halin dazata shiga in ban aureta ba dan haka kifidda hakan aranki kinjiko “
Kuka take sosai tana rokonsa amma kwakwata takasa shawo kanshi bud’e jakarta tai tad’akko kwalbar poison tace “farouq wlhy inbaka amshi soyayyataba senasha poison namutu nahuta “
Asheqeqe yakalleta yace “wannan ruwankine kin mutu kafira “atinaninshi bazata tab’a sha ba”
Juyowar daze yaga takafa kwalbar abaki tasha azabure yafusge amma hakan be hana shigar wani cikintaba cikin d’imuwa yafara meemah bakida hankaline meye hakan “
Ina tini tafara kwarewa idonta yay wuri wuri yay ja se kakari take jibbbb tazube ajikinshi azabure ya tallafota yana meemah dan Allah karki kashe kanki karnazama sanadiyar mutuwarki meemah zan aureki dan Allah tashi ganin ko alamun motsi batayi yasa yasureta se asibiti,ba jimawa akabata gudummawa. likitan yasamu yace “tana lapia ko?’
Yace”eh bawani matsala kawai dai tana sa damuwa aranta dahar takusa shafar lapiarta kadaina barin matarka tana shiga kunci kaji “
Gwalolo yay jin yace matarsa lallaima ‘cewa yay “ok dr zan iya shiga nadubata yace “eh “
Akwance yaganta amma idonta abude kallonta yay yace “yajiki “
Tace”da sauki farouq dan Allah zaka aureni “?
Goge hawayen idonta yay yace “meemah zan aureki kuma ba b’ata lokaci “
Zimbir tamiqe tana “Alhamdulillah wayyo ni meemarh amma yazakai da aysher?”
Yace “meemah aurenki ceton rayuwarkinai dan haka zanbata hakuri nace auren zumunci za amana dama ke ‘yar uwatace bansaniba seda iyayenmu suka had’a aurenmu “
Tace “d’an uwa kuma wannan mgnr aibazata d’auki hankaliba kuma ace bamusan junaba asake “
Yace “no haka za abarshi nasan duk wuya daga qarshe zatasan ba ‘yan uwabane mu alokacin aikingama yariga yagama “
Murmushin nasara meemah tai,bajimawa aka sallemata hargida yakai ta tanashiga tabuga tsalle tana “”momy shawararki tayi wlhy yad’auka poison nasha hauka nake zan kasha kaina baisan nan vitamin c bane naruwa aciki”
Dariya momy tayi tace “ ‘yata tilo tarasa abun datakeso aibaze yiwuba“
—————-
Akwana biyu farouq yatura gidansu meemah tare da kudin zance dana sadaki yakai, harda lefen daya had’awa aysher,Allah sarki aysher kuwa tanacan tana lissafin bikinta ,itadai takasa ganewa meemah kullum insuna maganar biki setace batada lapia inta warke sayi.
Farouq kuwa iyayen aysher yasamu yace”dan Allah suyi hakuri dadynshine yace auren zumunci zemasa kuma bayacce ze dan haka yajanye kuma kud’in zancema yabarmusu “
Ai ranar da aysher taji zancennan seda tasuma saboda tsanin son datakewa farouq shikkenan farincikita yaruguje dakyar momy tashawo kanta da ‘yan uwanta suka numamata bafa shikad’aine namijiba.
Haka meemah ma tazo gidansu aysher tana kuka sosai ,akai akai tafad’i meke faruwa taqi dakyar ‘yan gidan suka shawo kanta sannan tace musu “wlhy zata gudu tabar gidansu ancuceta anaso acuci qawance su “
Aysher tace “wai lapia “
Meemah rungumeta tai tana “besty wai dady ne yahada aurena da d’an uncle dinsa dake abuja dazama kinsan waye besty mijinki farouq wlhy besty nigwara namutu dana aure burinki “
Kowa seda yagirgiza awajen kafin daga bisani suafara lallashin meemah da tayi hakuri taiwa mahaifinta biyayya,aysher ma tace “haba besty dani dake duk d’ayane ninaji dad’ima dayakasance kece karki damu shima may be baisan ke bace shima iyayensa sunmishi mata sukace ashe kece“
Meemah yini tai agidan tana tamusu bariki abincima seda umman aysher tasata agaba taci,dazata tafi aysher duk kayan gyaran jikinta tabata tace tacigaba da amfani dashi.
Tom aysher tayi kuka tayi kuka .daga lokacin da farouq sukai aure da meemah bata sake kula wani saurayiba haka taita rayuwa dan bazata samu makamancin farouq ba,bayan haihuwar meemah data haifi areef asannan aysher tagane cewa duk shirin film suka mata bawani ‘yan uwa taji zafi sosai amma bata nunawa meemah tagane abunda suaka gaya mataba abaya,tabar abun aranta.
Bazata tab’a mantawa daranar da suka had’u da alhaji yusif awajen shopping ba tasanshi amma shibai santaba, lokacin da tagaisheshi yakyalla ido akanta, haka yajira tagama shopping tafito ,da tayi niyar tagayamai yacce akai tasanshi ganin ya kyasa da ita yasa taqi fadamai cewa qawar meemah ce ‘yarsa haka yay drop nata agida ,nan suka fara syya koba komi tarage rad’ad’in dazuciyarta keyi.
Wannan kenan.
Cigaban labari
——————
To misalin qarfe tara nadare ‘yan kai amarya sukacika gidan Alh yusif dayake part biyune ,a d’aya part d’in akasata meemah kwa baqinciki uwa tai hauka ashe haka aysher taji,gaskiya son zuciya baiba dama ance son zuciya b’acinta gaskiya tamata ramuwar gayya.
Bayan kowa yawatse ne ,alh yusif yad’auki aysher suka tafi part d’in momy inda yatarar da momy azaune, farouq kuma yana d’auke da areef yana jiran fitowar meemah dan sutafi gida ahaka alhaji yusif da aysher suka samesu.
Ido biyu sukai da farouq da aysher nan kwakwalwarsa tafara tinomasa rayuwarsa tabaya gaskiya yayi rashi ganin yacce aysher taqara kyau hannunnan yasha lalle,mazauni alh yusif yamata nuni dashi ,nan ta zauna ad’aya daga kujerun falon,zama tai yayinda farouq kegaishe da dady cikin fara a ya amsa sannan yace “ga auntyn kama baku gaisaba“
Adiririce farouq yace “ina yini aunty “
D’an kallon alh yusif tai tace “ alh wannan ma d’ankane?”
Yace “a a mijin ‘yatane meemah kinsan ai ita kad’ai nake da “
Tace “au Allah sarkee lapia lau Allah yayi albarka “
Takaicine yacika momy dan tasan kar tasan kar abunda sukawa aysher,gashi alh se rawar kai yake da ita.meemah na sakkowa daga bene tayi turus ganinsu afalon momy ,dady ne yace”yawwa meemah kema sakko ga second mom naki ku gaisa “
Ido fal kwallah takalleta tace “sannu barkanki da zuwa auntynmu “
Murmushi aysher tai tace “mashallah alh ‘yarka meemah akwai hankali “
Washe baki alh yusif yay kafin yagabatar da addu ‘a dakuma nasiha inda ya jadaddawa aysher taiwa hajiya jamila biyayya (momy)itama kuma momy tariqeta hannu biyu.bayacce momy ta iya saboda tana tsoron Alh tasaki fuska suka gaisaa da aysher harda cemata tasaki jikinta nan gidan mijintane.
Itama aysher cike da girmamawa tacewa momy “nagode sosai hjy inshallah nima zan kiyaye daidai gwargwado “
Murna alh yusif yay sosai kafin yasa farouq yasha fa musu addu’a,daga bisani ya umarci meemah tarakata part d’inta ze hau sama yasakko inda momy tabi bayanshi ,ita kuma meemah ta tafi rakata daidai bakin part d’in ,meemah ta tsaya takalli aysher tace “aysher ni dake mumzama tamkar hanta da jini amma son zuciya yasa na rusa ginin amanar qawancenmu tabbas yanzu nafahimci zafin dakikaji aysher munci amanar qawancenmu munrusashi dukanmu munwa kanmu KWAR TU KWAR kuma nice sila yanxu kam bayacce na iya dole acema mijin iya baba konaso ko naqi yanxu kinzama uwa agareni ,kigafarceni aysher wlhy son zuciya yakaini narabaki da farincikinki dan Allah karki amfani da damar hakan ki ci zarafin mahaifiyata don rama abinda naimiki “
Dafata aysher tai tace”meemah kenan ba komi ,yawuce dama wani baze auri matar waniba ,kuma ni na auri mahaifinkine ba saboda abunda kikayiminba kaddarace tahad’amu dan haka bazan wa momy rashin kunya kowani abunba ,zaman aure nazo ,kawaidai da yanemi soyayyata ban qi karb’aba ,saboda wai qawancen dake tsakanina dakea saboda nima baki dubi hakanba kika take ,kika aure mijin da zan aura ,kikabi son zuciyarki nima shiyasa nabi nawa namiki KAR TASAN KAR amma komi yawuce “
Hugging d’inta meemah tai tana kuka tace “ngd aunty aysher qaddarace tazomana da haka “
Aysher tace “meemah kijanye aunty nan fa “
Tace “wlhy nibanzan janyeba dole na girmamaki kamar yacce kike girmama mahaifiyata kuma kinzama matar babana “
Hugging d’in juna sukai kafin si sallama,toh amota farouq yakecewa “gaskiyane alqawarin Allah baya canjawa abinda kai se ammaka kuma wlhy nibanga laifintaba “
Yatsina fuska meemah tai tace “plx farouq komi yawucefa dan Allah ainasan meyafaru”
Dariya farouq yay yace “kinyi wufffff da mijinta ita kuma tayi wuffff da ubanki “
Meemah tace “ubanmu dai “
Atare sukai dariya....
To Alhamdulillah anan nakawo qarshen labarina dan Allah kwimin share fans plx karku manta littafin gasane taku gimbeeya
Downloaded From https://arewanovels.com