gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KOMAI KYAN TAKALMI Farashin Soyayya by Sumayya Salihu Chapter 1 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [16/08, 6:16 a.m.] 👑Queen Sumy💍: 👠👠👠👠👠👠
👠👠👠
👠👠👠👠👠👠
👠👠👠


👠 _*KOMAI KYAN TAKALMI...*_👠


👢sai ya taka ƙasa👢


___✍🏻Written Story
By
*Sumayya Salihu*
👑 *Queen Sumy ce*


Daga marubuciyar👇🏻

1, *SAKAYYARMU CE!*
2, *WUTAR SO*
AND NOW
3, *KOMAI KYAN TAKALMI....*



*FREE PAGE* 1 ➡️ 2

___________________________________

🌈KAINUWA WRITTERS✍🏻ASSOCIATION
```{united we standa and suceede; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

______________________________



*_D̰̃Ṵ̃K̰̃K̰̃Ã̰Ñ̰ G̰̃Õ̰D̰̃Ḭ̃Ỹ̰Ã̰ T̰̃Ã̰ T̰̃Ã̰B̰̃B̰̃Ã̰T̰̃Ã̰ G̰̃Ã̰ Ã̰L̰̃L̰̃Ã̰H̰̃ Ṵ̃B̰̃Ã̰Ñ̰G̰̃Ḭ̃J̰̃Ḭ̃Ñ̰ H̰̃Ã̰L̰̃Ḭ̃T̰̃T̰̃Ṵ̃, T̰̃S̰̃Ḭ̃R̰̃Ã̰ D̰̃Ã̰ Ã̰M̰̃Ḭ̃Ñ̰C̰̃Ḭ̃Ñ̰ Ã̰L̰̃L̰̃Ã̰H̰̃ S̰̃Ṵ̃ T̰̃Ã̰B̰̃B̰̃Ã̰T̰̃Ã̰ G̰̃Ã̰ Ã̰Ñ̰Ñ̰Ã̰B̰̃Ḭ̃Ñ̰ R̰̃Ã̰H̰̃Ã̰M̰̃Ã̰ Ã̰Ñ̰Ñ̰Ã̰B̰̃Ḭ̃ M̰̃Ṵ̃H̰̃Ã̰M̰̃M̰̃Ã̰D̰̃ {S̰̃ Ã̰ W̰̃}, Ã̰L̰̃L̰̃Ã̰H̰̃ K̰̃Ã̰B̰̃Ã̰Ñ̰Ḭ̃ Ḭ̃K̰̃Õ̰Ñ̰ R̰̃Ṵ̃B̰̃Ṵ̃T̰̃Ã̰ W̰̃Ã̰Ñ̰Ñ̰Ã̰Ñ̰ L̰̃Ḭ̃T̰̃T̰̃Ã̰F̰̃Ḭ̃Ñ̰ L̰̃Ã̰F̰̃Ḭ̃Ỹ̰Ã̰ K̰̃Ṵ̃M̰̃Ã̰ K̰̃Ã̰B̰̃Ã̰Ñ̰Ḭ̃ Ḭ̃K̰̃Õ̰Ñ̰ G̰̃Ã̰M̰̃Ã̰ S̰̃H̰̃Ḭ̃ L̰̃Ã̰F̰̃Ḭ̃Ỹ̰Ã̰{Ã̰M̰̃Ḭ̃Ñ̰}._*


*Wannan littafin na kudi ne shi da WUTAR SO idan kana buk'atar duka biyu zaka biya naira #300 kacal idan kuma d'aya ka ke so zaka biya d'ari #200.*

Sai ku tuntub'eni ta wannan number
👉🏻08104986525


VIP zasu biya d'ari #400.


Wannan littafin yana d'auke da daddarussa da dama, yazo da tsarin sa na daban, yana d'auke da soyayya da kuma k'iyayya da tsantsar wulak'anci da kuma ladama, kuma akwai ilimantarwa nishad'antarwa, yan uwa kada ku sake abaku labari wannan littafi *KOMAI KYAN TAKALMI...* Ku garzayo domin siya dan koda kudinka sai da rabonka ku zo ku nemi naku dan jin me ke tafe dash. Allah ya bada ikon biya amin.


*Wannan k'agen labarine banyi shi dan cin zarafin wata/wani ba, ko da yayi dai-dai da rayuwarka to kayi hakuri*


*Ya Allah kakareni da rubuta shashan abinda bashi da kyau Allah ka nuna min yadda na rubuta shi lafiya in kareshi lafiya Amin*


*بسم الله الر حمن الر حيم*


🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐

*📖 ..........* *Tass! tass! tass!* Dr Bilal ya ɗauke Salma da azababben mari har sau ukku cikin zafin nama, wanda yasa ta ganin gilmawar taurari a cikin ƙwayar idonta.

Ya ce cikin d'aga murya " Stupid kawai, shashasha wawuya i hate you! i hate you! na tsane ki bana son ganin ki bana buk'atarki bana ƙaunarki wawuya donkey!.

A wahalce Salma tasa tafin hannunta ta dafe kuncinta inda ya d'alla mata mari dan jin wani irin azababen rad'ad'i yana jiyartar fuskarta, ta jiyo muryarsa yana fad'i cikin tsawa.


"Na ce bana sonki bana k'aunarki ko kin isa kisani na soki ne? Dube ki wata irin kucaka dake mezan yi dake ? Stupid dalla ki b'ace min da gani ko yanzu in b'alla ki a gurin mtwss"

Salma ta d'ago kai ta kalle sa da kyau har yanzu hannunta na dafe a kuncinta hawayen wahala suka ziryo a fuskarta.

Dr Bilal ya wurga mata uwar hararar da zaka ga tsatsar k'iyayya acikin idonsa, ya yi mata nuni da k'ofar fita "Get out in my room" ki fitar min a d'aki bana son na k'ara ganin kin shigo min gidana ki fita na ce ya k'arashe maganar cikin tsawa.

Salma sai da ta k'ara kallon sa idonta cike fam! da k'walla kafin tasa kai tabi hanyar k'ofa.

Sai da ta kai daf da k'ofar sannan ta tsaya cak! ba tare da ta juyo ba ta ce.

"Yaya Bilal" na gode da wannan wulak'ancin da kake mani na ji kuma na d'auka, tabbas na yarda da baka sona kuma ka tsaneni.


Tasa hannu ta goge k'wallar da ke biyowa a gefen kuncinta kafin ta ce.

"Yaya Bilal ka san da cewa ina maka so mai tsanani zuciyata ba wanda take muradin kasancewa sai kai ina matuk'ar k'aunarka,nasan na riga na fad'a kogin sonka wanda ban da tabbacin zan iya fitowa, sonka akoda yaushe yana ziyartar zuciyata ni nasan na fad'a tarkon k'aunarka wanda ba wanda zai iya ciremin shi sai kai, lallai tabbas nasan nayi nisa a sonka ba na jin wani kira"

Zanso ace nafi kowa matsayi a zuciyarka saboda inda tabbacin nafi kowa k'aunarka ina murna da murmushi zuciyata ta dade da bautuwa da tsananin zafin sonka tun ina zubarda hawaye har na kasa aune ka kawo d'auki ga zuciyar da ke cike da tsantsar begenka, zuciyar da bata san komai ba sai soyayarka, amince dani shi kad'aine sauran burina a rayuwa!.

Ta k'ara sa bayan tafin hannunta ta goge k'walla a karo na biyu, taci gaba da cewa cikin muryar tausayin kanta.

Yaya Billal kayarda dani zan zamo komai naka, na baka d'aya na biyu a gurbin zuciyata babu kamarka!.

Dan haka a shirye nake da d'aukar wahala wulak'anci daga gare ka in dai a kan sonka ne komai tsanani zafi wahala wallahi zan iya jurewa, saboda ina bala'in k'aunarka! ko ka soni ko ka k'ini ina tare da kai"


So tamkar k'urb'ar ruwan shayi yake mai tsananin zafi a Karon farko zaka kasance cikin shauk'in begen shi wanda daga bisani kuma zai k'ona maka harshe na tsawon lokacin da zaka shafe kana jiyar shi.



"Soyayyar da nake maka tamkar lafiya ce mai nisa dana farayinta wadda bata da lokacin yankewa har abada na san burina zai cika matsawar ina tare dakai domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samunka a matsayin miji uban 'ya 'yana ba, ina sonka fiye da gwal ko kud'i"


" Yaya Bilal kasan da cewa, Zuciya ta ta yi zurfi a k'aunar ka, na riga nayi nisa a sonka, rayuwata tana masifar buk'atarka, bana jin zuciya ta zata iya daina sonka"

" Idan har kaga na daina sonka to bana numfashi a doran k'asa"

" Yaya Bilal" ka san da cewa wallahi har duniyar nan ta nad'e ba zan tab'a daina sonka ba, ina sonka! ina sonka! ina matsanancin buk'atar ka a rayuwata....!


Dr Bilal hannu yasa da k'arfi ya toshe kunnuwansa dan jin kalamanta yake tamkar tana zuba masa ruwan zafi masu tsananin masifar zafi a cikin kunnuwansa ya ce cikin tsawa.


"Yaa isaa! Yaa isaaaa!!"

Ki dakata! haka na gaji da jin wad'an nan banzan kalamanki wad'an da har duniyar nan ta nad'e ba zasu tab'a tasiri a zuciyata ba, dan na tsanakiiiiii! bana k'aunarkiiiii!


Ki koya wa zuciyarki hakuri da juriya da kuma tawakkali saboda wanda take muradi baya k'aunarta.



Kuka mai tada rikar jikin mai saurare Salma ta rushe dashi dan jin kalamansa suna k'ona mata zuciya ji take tamkar yana d'ebo gaushi mai ci da wuta ya d'aura mata shi kan zuciyarta, da sauri tabar falon cike da kunci da tausayin kanta.

Ya ja dogon tsaki tamkar zai cire bakinsa yazuk'i iska ya fuzar, jijiyoyin kansa suka fito rad'a-rad'a kamar zaka sa hannu ka cirosu ya had'e girar sama da ta k'asa tamkar bai tab'a dariya ba.


Ya ce cikin tsanin b'acin rai "aikin banza aikin wofi me zanyi da ke? Me zan samu a cikin jikin ki? Me zan yi da macen da bata da aji? Wacce bata da zuciya, har ita ta isa ta sani na sonta dole?.


Duk a fadin duniyar nan ban ga mahalukin da ya isa ya sani na soki ba.

Ni duk 'yan matan duniyar nan aka tara su gurin d'aya ban ga wacce zan iya furta wa kalamar *_SO_* ba saboda na tsani mace a duk inda take!!!.


Mace komai kyanta ba zata tab'a burgeni ba, a rayuwata ban ji zan iya tsaya wa na yi soyayya da mace ba dan bana son raini, dama ai soyayya raini ce duk girman ajin da nake dashi haka kawai na tsaya wata macen banza ta raina ni.



Ya girgiza kai yana fad'a cikin d'aga murya sam! sam! bazai tab'a yuwuwa ba, mtswwww!
Ya k'ara jan tsaki a karo na biyu.

Sannan ya nufi bedroom d'in sa, ya shiga kai tsaye kayataccen bed din sa ya nufa da k'arfi ya fad'a a kwance dan hutawa, kansa ya d'aga sama yana kallon silin d'akin yasa hannunwan sa biyu ya dafe kansa, takaici da bak'in ciki ya ishe shi ya ji haushin abinda Salma ta fad'a masa.

Wai har ni *_DOCTOR BILAL_* dan tsabar raini zata dubeni ta furta wa kalmar *_SO_* Hmm! yarinya kin yi gangancin tsundumawa cikin kugin sona dan ko kad'an ba zakici nasara ba, sai dai wahala da kuma ladama.


Gyara kwanciyarsa ya yi gami da lumshe sexy eyes d'insa


Tunda ta fita a cikin d'akinsa bata tsaya ko ina ba sa paking lot ina ta ajiye motarta.



Har lokacin hawayene masu tsananin bala'in zafi suke kwaranya daga kusurwar idanuwanta.

Bud'e murfin motar ta yi gidan gabata zauna ta rufo k'ofar, zuciyarta na mata wani irin rad'ad'i wanda tun farkon rayuwarta bata tab'a jin irin k'onar zuciya ba irin yadda take ji, tana jin soyayar Dr Bilal tana k'ara ruruwa a cikin duk wata kusurwa ta jikinta.


k'wak'walwarta ce take tuna mata da bak'ak'en kalamansa wad'an take jin basu da bam-bamci da bak'in macijiji.


_"Stupid kawai shashasha wawuya i hate you! I hate you! na tsane ki bana buk'atarki bana k'aunarki wawuya donkey!"_


Da saurin gaske tasa tafin hunnayenta ta toshe kunnuwanta da take ji tamkar yanzu ne yake fad'a mata bak'ak'en kalamai masu zafi.


Ta d'aura kanta kan matashin kujerar fuskarta na kallon saman motar a hankali ta rufe idonta fuskar Dr Billal ce take gani a cikin k'ayar idonta, a hankali ta mutsa labban bakinta tasamu ta furta.

"Tabbas! dole Yaya Bilal ka wulak'anta 'yan mata saboda kai kyakyawane ko a cikin kyawawan mazaje kaina za'aba wa lamba d'aya, kuma ka had'a da kud'i ilimi kyau gata tsafta martaba!"


Ni kuma na riga da na san sonka shine k'addarar rayuwata!!!.

A hankali ta bud'e idonta ta goge zufar da take bin gefen fuskarta saboda wani irin zafi ta ji yana ratsata ta samu a wahalce ta furta.

"Yah Ubangiji kaine kake da ilimin gabu kaine mai sarrafa al'amurra ta yanda kaso, mai hadawa kuma kaine mai rabawa, Allah kaine ka d'aura mini son bawanka Bilal ya Allah kad'auke min son shi gaba d'aya k......kasa idar da furucin ta yi sakamakon wani kuka mai tsuma zuciya ya sub'uce mata.



Tasa tafin hannuta ta rufe fuskarta sai da ta yi kuka mai isarta babu mai rarrashinta.



<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<

*Annabi s a w yace:"wanda ya fad'i wannan addu'ar da asuba ko da yamma "Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wahuwa rabbul arshin azimi" sau bakwai, Allah ya isar masa duk wata damuwa ta duniya da lahira "Dan sinniyu ne ya ruwaito shi daga Abid-darda'i (RA)....*




*Allah kabamu ikon karatawa Allah kasa mu dace duniya da lahira amin*



kuci gaba da biyo ni my fans



kabiya dari biyu #200 kacal kayi karatun ka mai dad'i , yanzu aka fara labari.😎



Whatsapp no.
08104986525


*TAKU CE 👑QUEEN SUMY ✍🏻*
[16/08, 6:16 a.m.] 👑Queen Sumy💍: 👠👠👠👠👠👠
👠👠👠
👠👠👠👠👠👠
👠👠👠



👠 *_KOMAI KYAN TAKALMI...._*👠


👢Sai ya taka ƙasa👢




-----✍🏻Written Story
By
*Sumayya Salihu*
*👑Queen Sumy ce*


*1 SAKAYYARMU CE!*
*2 WUTAR SO*
*3 KOMAI KYAN TAKALMI..*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*


*_FREE PAGE_* 3 ➡️ 4


*wannan littafin na kuɗine shi da WUTAR SO duk mai buƙata nazo maku da farashi mai arha idan biyu ka ke so zaka biya naira ɗari ukku #300 kacal idan kuma guda ɗaya ka ke so zaka biya naira ɗari biyu #200.*



VIP zasu biya ɗari huɗu #400



Idan kuna buƙata ku tuntuɓeni ta wannan whatspp number
👉🏻08104986525

_Domin fad'a maku ta inda zaku biya sai asaku group d'in da nake posting d'insa,, ina k'aunarku masoyana a duk inda ku ke a fad'in duniyar nan Allah ya bar k'auna Amin_






🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐🎐



*📖.........* Salma taci kuka sosai, da ƙyar ta buɗe bakinta ta ce "Yah Ubangiji Allah ka tausaya wa rayuwata! Allah kaine ka jarabceni da soyayyar Bilal Allah kai sassauta mini soyayyar shi a zuciyata ka taimaki rayuwata..." wani sabon kuka ne ya suɓuce mata ta daɗe tana kuka daga bisani ta goge ƙwallah, sannan tasa wa motar key tun daga can take horn get man ɗin ya wangale mata get ɗin, ta ja motar ta fice daga gidan Dr Bilal cike da ƙunci da ɓacin rai.

Da gudu take jan motar ta ɗan yi yar tafiya mai nisa sannan ta isa wani makeken gida na gani da faɗa, tun daga nesa ta yi horn da sauri get man ya buɗe mata ta kurna kan motar ta shiga cikin gidan, mai gadi ya ɗaga mata hannu tare da cewa "Hajiya sannu da zuwa" horn kawai Salma ta yi masa alamar asawa.

A parking lot ta tsaida motar, ta daɗe a cikin motar saboda gaba ɗaya rayuwar duniya ta yi mata tsada hawayene ke ta sintiri a fuskarta, tana tausaya wa rayuwarta na faɗa wa *KUNGIN SO!* kuma wanda take tsananin muradi baya ƙaunarta kwata-kwata duk da dai ɗan uwanta ne na jini amma ya tsaneta.

Ta ce a ranta "to me nake aikatawa wanda Yaya Bilal ya tsana da har yake nuna min ƙiyayya haka sosai? " Ta tambayi kanta da kanta amma ta kasa gano amsar tambayarta.


A haka dai ta fita daga motar, tafiya take a hankali tamkar bata da lakka har ta isa wani part ta nufa a cikin gidan, a babban falon gidan ta isa ta zauna kujera 2 sitter ta ajiye wayarta da gyalenta tasa tafin hannu biyu ta dafe kanta dan yadda take jin yana sara mata tamkar ana daka mata guduma a ka.


Ta furta a sarari "Yah salam! Wanne irin so ne nake yi wa Dr Bilal? Soyayyar shi a koda yaushe ruruwa take a cikin ƙalbina! Zan yi murna da farin ciki idan Dr Bilal ya furta mani kalmar da tafi komai daɗi a dunayi ina sonki! "


Amma miyasa Dr Bilal ya bar harshensa ya rinjayi laɓɓansa suka buɗe bakinsa har ya iya furta kalmar da tafi komai ɗaci da zafi da raɗaɗi a cikin faɗin duniya! Wato na tsaneki!! Dr Bilal da kasan irin yadda masoya suke jin zafi a zuciyarsu idan aka furta kalmar tsana! "


Nasan ni da na riga na faɗa tarkon so kuma bazan iya fitowa ba, ina jin haushin kaina da har nabi son zuciya na kuma aminta da zuciyata har ta rinjayeni ta kaini ga faɗawa a cikin duniyar son Dr Bilal, duk da dai nasan waye Bilal? Amma na yarda da zuciyata" nan take ta rushe da kuka cike da jin haushin kanta, kafin ta ce.


"Miyasa zuciyata zaki bani wannan shawarar? Ina nadama sosai da har na yarda na bi ruɗin zuciya! Tabbas ni shaida ce akan Dr Bilal bai san meye *SO* ba, bai kuma san darajar *SO* ba! bai kuma san raɗaɗin *SO* ba! bai kuma san me a ke kira da *SO* bah! ba ka san halin da zuciya take shiga ba idan ta nemi abin da take so bata samu ba, tabbas! *SO* masifane sannan kuma *SO* bala'ine ni nasan na riga ta shiga taskun rayuwa ina son Dr Bilal so mai tsanin gaske kuma na rasa ya zan cire wannan so a zuciya!.


A gogon da ke manne a ƙayataccen bangon falon ta mai da dubanta inda yake dan ganin lokaci, karfe biyar har ta gota na yamma, ta ce a ranta "yau miyasa Mom bata dawo da wuri ba? Gashi har 5 " miƙewa ta yi ta ɗauki wayarta ta nufi wani ɗaki, har yanzu zuciyarta tana tafasa sosai tana duk yau bata jin daɗin rayuwarta komai ya yi mata ɗaci zuciyata sai zafi take mata sosai.


Ta shiga bedroom ɗinta ta zauna bakin gato ta rafka uban tagumi ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "zuciyata yanzu ta tabbatar min da Dr Bilal bai san haƙiƙanin asalin so ba, yana izgili sosai akan so, basan kuwa so bai san ƙaraba kuma so ba zai ragawa kowa ba, why some people are taking love as granted ? If u confront them with love they ignored it! Yaya Bilal har yanzu ya kasa fahimtar menene *SO* ? "


Salma ƙwallah ce fam a idonta ta rumtse idaniyanta hawayen ciki suka gangaro a fuskarta.




*ASALIN SU*

Alhaji Garbah haifaffen ɗan garin Kano state ne yana da matarsa guda ɗaya Ummulkhairi, ƴa ƴansu ukku a duniya, na farko Ahmad sai Abubakar, Nana Khadija.


Alhaji Ahmad Garbah minister kud'i ne *MINISTER OF FINANCE!* ya yi ƙwaurin suna a faɗin duniya, mutum ne kamili mai adalci da riko da gaskiya ya kuma san darajar ɗan adam bai cika zama nigeria yana zuwa ƙasashen waje da dama, kuma yana yawan zama Abuja iyalinsa kuma suna zaune a garin kano yana da mata biyu ɗaya a kano take zama ɗaya kuma tana Abuja.

Matarsa ta farko ita ce Hajiya Hindu! mace ce mai son dukiya da kuma son duniya bata da wani burin da ya wuce ta ga ta zama babbar mai kuɗi hakan yasa take sana'o'i siye da sayarwa har ƙasashen waje tana zuwa tana siyan kayan sana'a irin su sarƙoƙi, da ƴan kunne, awarwaro, na gold da azurfa, da kuma atamfofi da lesi da matirial, tsaidaddu, Hajiya Hindu ba abin da ta tsana a duniya kamar *TALAKKA!* ta tsani talakkawa kamar yadda ta tsani mutuwarta.


Hajiya Hindu tana da ƴa ƴa biyar, Bilal shi ne ɗan fari sai mai bi masa Abdurrahaman ana kiransa da Sudais sai twins mata Aslam da Ahlam sai ƙaramar su Fatima ana ƙiranta da Maamah.


Dr Bilal babban Doctor ne ya yi karatu a ƙasar waje a Dubai ya karantu sosai, ya dawo Abuja ya buɗe babban Hospital *SAWABAH CILINIC HOSPITAL* duk ya zuba Doctors da kuma Nursing ƙwararru a cikin asibitin, kuma a kano ma yana aiki a wani Hospital, Dr Bilal ƙwararran likita ne ya ƙware a fannin theater da kuma ƙarɓar haihuwa.

Dr Bilal yanzu yana da shekara 32 years amma har yanzu bai yi aure ba, dan ko soyayya ma ba ya yi ya kasance mutum ne mai son girma da kuma ji da kansa shi wani ne, baya son hayaniya, babban miskilin mutum ne, gashi Allah ya yi masa sura mai kyau kyakkyawan ne duk inda ku ke tunani a kyau to yakai, fari dogo yana da tsawo kuma yana da jiki amma ba sosai ba, ga cikar zati da kuma haiba, fuskarsa tana da ɗan tsawo hancinsa dogone kamar karas ɗan bakinsa madaidaici pink lips ne, irin kyan Dr Bilal baki ma bazai iya faɗa ba.



Shi bai damu da ƴan mata ba, saboda girman kansa baya iya jin zai so mace dan ya tsani raini a rayuwarsa shi ne yake ganin cewa ita soyayya raini ce irin yadda yake ganin namiji yana ɓautawa mace shi kuma baya iya jure hakan a rayuwarsa, kuma lafiyarsa ƙalau amma baya jin zai iya soyayya kuma gashi yana fama da yawan sha'awa, sai dai yasha lipton da lemon tsami idan ma har feeling ɗin ta damesa, iyayensa suna masa maganar aure amma sai ya ce bai shirya ba sai nan gaba, kasancewar ɗan gata ne shiyasa iyayensa suka zuba masa ido dan gudun ɓacin ransa, saboda yana da saurin fushi.



Shi dai aikinsa ne yasa a gaba, Allah ya yi masa arziƙi ya bashi dukiya amma bai damu da ya yi aure ba, abokanensa duk sun yi aure har da yara, ƴan mata kala-kala sun kawo maitarsu akan Dr Bilal amma basu yi nasara ba dan shi mace bata burgeshi hasalima haushi wasu matan suke bashi.


Sudais kuwa ƙaninsa mutum ne mai son jama'a da sanin darajar ɗan adam yana son wasa da dariya ga tausayin talakkawa, dan shi kam ya yi halin mahaifinsa sak, suna kama sosai, yanzu yana karatu a jami'a yana 300 level yana karanta mass communication, dan burinsa yaga ya zama cikakken ɗan jarida.

Sai kuma twins Aslam ita ce Hassana Ahlam ita ce Husaina, ƴan biyu ne masu kama da juna sosai komai nasu iri ɗaya ne, sai dai ita Aslam tafi Ahlam fari, Aslam yarinya ce wacce tayo halin mahaifiyarta sak, yarinya ce mai son kuɗi a rayuwarta da kuma son abin duniya, ita kuma Aslam bata damu da kowa ba sha'anin gabanta take sai dai ita kuma tana shan ƙwayoyin maye ba tare da iyayenta sun sani ba sai da kawai tawainiyar haihuwarta ce kaɗai tasani, ƴan mata ne budare suna da 22 years suna karatu a jami'ar bayero university kano, suna 100 level.

Ƙanwar su Maamah tana da 18 years, yanzu tana SS2 ita ma yarinya ce mai wulaƙanta mutane ga son ƙyalƙyalin duniya.


Matar Minister Ahmad ta biyu ita ce Saudat mace kamila mai nutsuwa da hankali da son addini tana farau-farau da jama'a ita kuma ma'aikaciyar banki ce, tana da yaranta biyu Saif da Ummita.



Alhaji Abubakar Garbah shi kuma ɗan kasuwane, yana da mata biyu sai dai yanzu basa tare da amaryarsa sun rabu, Hajiya Nauwara ita ce uwar gida tana da ƴa ƴa ukku, Aminatu sai Yazid, Zeenatu.


matarsa ta biyu ita ce Hajiya Kaltume tana da tilon ƴarta guda ɗaya Ummu-Salama yanzu shekara biyar da rabuwar aurensu ƙaddara ta gitta masu ta rabuwa da juna, dama ita ƴar garin Abuja ce dan can yan uwanta suke, Alhaji Abubakar ya saya mata babban gida da mota dan kawai ta zauna ta kula masa da ƴarsa, anan Abuja take zama har yanzu bata yi aure ba, Salma tana da 24 years dan har ta kammala karatunta ta fara aiki, ita bata yi aure ba duk da tana da maneman aurenta amma babu wanda ta ji tana sha'awar ta aura kamar Dr Bilal tun tana ƙarama zuciyarta take dakon son shi.



:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::


Wata yarinya ce zata kai kimanin shakaru 18 years ta shiga wani ɗan madaidaicin gida wanda daka kalli zubin gidan kai kasan gidan yaku bayine, da sallama ta shiga.


Wata matashiyar mace ce zata kai kimanin shekaru 40 years ita ce ta amsa mata sallamar tana zaune tsakar gidan kan tabarma ta miƙe ƙafafuwanta ta ɗaura tiren mai ɗauke da shinkafa ƴar hausa tana cire tsakkuwa.

Dai-dai kan tabarma ta isa ta zauna kan tabarmar tare da faɗin "wshhh! Kaii na gaji sosai" Ummah ta ɗago kai ta kalleta tare da cewa "sannu Raheelah kin dawo? Raheelah ta ce "Eh Ummah na dawo wallahi a ƙafa ma na dawo shiyasa ki ga na daɗe gashi har yamma ta kusa " Ummah ta ce " kai sannu Raheelah kin yi ƙoƙari sosai gashi wurin da ɗan nisa, ina fatar dai anyi nasara ko? " Ta faɗa cike da son jin abin da Raheelah zata ce.


Raheelat ta kalli Ummah kafin ta ce " Hmm! wallahi Ummah ko sisi ban samu a wurin uncle ba, kuma gaskiya Ummah wannan zuwa shine na ƙarshe bazan ƙara zuwa gidansa tun da ya nuna bai san darajarmu ba ni ƴarsa ce amma ya mai dani tamkar wata bare"


Ummah dai bata ce ko ƙala ba ta maida hankalinta ga gyaran shinkafar tana jin abin da Raheelah take cewa..





_Domin samun ci gaba littafi ka/ki biya naira d'ari #200 kacal,, Ta katin waya MTN ko ta account ku tuntubeni ta wannan Number_
_👉🏻08104986525 yan uwa kada ku sake abaku labarin wannan littafin *KOMAI KYAN TAKALMI....*_ _yanzu ma aka fara,, masu bukata ku hanzarta domin samun naku dan koda kudinka sai da rabonka_


*TAKU CE👑QUEEN SUMY✍🏻*

PLX comment and share
[16/08, 6:17 a.m.] 👑Queen Sumy💍: 👠👠👠👠👠👠
👠👠👠
👠👠👠👠👠👠
👠👠👠



👠 *_KOMAI KYAN TAKALMI...._*👠


👢Sai ya taka ƙasa👢




___✍🏻Written Story
By
*Sumayya Salihu*
*👑Queen Sumy ce*


Daga marubuciyar👇🏻
*1 SAKAYYARMU CE!*
*2 WUTAR SO*
AND NOW
*3 KOMAI KYAN TAKALMI...*






*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*


_*FREE PAGE*_ 5 ➡️ 6


*wannan littafin na kuɗine shi da WUTAR SO idan kuna buƙata nazo maku da arfa idan biyu ka ke so zaka biya naira ɗari ukku #300 kacal idan kuma guda ɗaya ka ke so zaka biya naira ɗari biyu #200.*



VIP zasu biya ɗari huɗu #400



Idan kuna buƙata ku tuntuɓeni ta wannan whatspp number
👉🏻08104986525

_Domin fad'a maku ta inda zaku turo kud'in,, ina k'aunarku masoyana duk inda ku ke a fad'in

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment