gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading FUREN BADO Soyayya Cikin Ƙaya by ZAINAB IDRIS MAKAWA Chapter 1 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng NOV/12/2025.

ZEE MAKAWA NOVELS

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

5- SARAUTAR MATA500

6- MURICCIN KAN DUTSE... 500

7- BAHAGON RAYUWA 500

8- KANIN AJALI 500

9- LOKACIN MUKE 500

10- MIJIN BUZUWA 500

11- SARKA...500

12- ABU CIKIN DUHU 500

13- ANA DARA... 500

14- KARAN DAFI... 500

15- TUMFAFIYA... 1000

16- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

17- JA YA FADO JA YA... 1000

18- MURFIN JALLO 1000

19- HAWAYEN KADA 1000

20- FUREN BADO 1000

Account No.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2254380105

ZENETH BANK

PHONE NO.

08036959257

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI KANKI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI"

"A WAJENKI GOBE KIYAMA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

"DON ALLAH IDAN KINSAN BAKI BIYA BA KIBAR MIN KAYANA TUN A DUJIYA,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Assalamu alaikum yan uwa zan fara da duban yanayi ayadda tarihi yazo zan iya cewa tun nineties

rayuwan arewan mu ya tabatbare ga baki daya da soja ya karfi mulki kuma sai abin ya danyi dama.

"Dawowan siyasa a kasan gaba daya arewa ta juye da akidar nasara da yahudanci muka aro al,adun"

daba namu ba muka yafawa a kawunan mu .

"Cikin wanan al,adun abu mafi muni a yanzu shine ragamar aurataiya ya koma ga iyayye mata a baya"

ance namiji shine komai ga iyalinsa komai talaucinsa kuwa.

Amma a yanzu wayewan da boko yazo muna dashi a kasa yasa abin ya juya mace ce cefane sai namiji

ya mikawa mace kudi da sunan ayi girki ba tare da yasan nawa zata kashe a wajen girkin nan ba ?

A yanzu sai mace ce zata dauki yara takaisu neman ilimi ya Allah na boko kona arabiya saidai mai dan

tausayi ko karfi ya miko kudin da zata hada taje ayiwa yaro register.

A yanzu idan yara sun kimtsu mace uwa a gida ta jajirce da taimakon ubangiji har hakan zai faru

sabanin da a baya da ko tari namiji yayi alaman zai shigo gidansa daga mata har yara suke natsuwa cikin second kafin ya karaso gida ya koma tankar babu numfashi a cikinsa.

A yanzu ankai saidai maigida ya wanke yan tufainsa ya shaye yasa a goge ya fita fes dashi alhali gida na

can da yunwa da bakin cikin iyali.

A yanzu anakai karnin da wasu mazan ko aci ko kada aci wanan ba damuwansu bane idan ma ke mace

bakiyi dubara kin girka ba sai hakan ya kawo fitina a tsakaninki da miji.

Mata yakai lokacin da miji na daki a kwance yana barcin safe kona rana mace zata fita neman abinda

iyali zasuci shi yana kwance cikin damuwa.

A takaice an kai an wuce don a yanzu abinci ke ce mace kudin makaranta saidai ku raba idan kin samu

asibiti kece tarbiyan gaba daya kece idan kinyi wanan kin taimaki diyan da kika haifa .

Wata macen ba iya diyan data haifa ba harda tarkacen maigida itace ke daukan nauyisu shi mijin bai

damu ba.

A wasu gidan masu dan hali abinda dama don ana zaman fifty fifty da zuna ki bada rabi ta bada rabi ki

ya dauki abinci danye ki dauki kayan miya icce dasu mai omo sabulu da sauransu.

Allah sarki uwayen mu mata a zamaninku iyayyenku sun rike mutuncinsu na mazaje sun zama zakuna a

gidanjensu sun baku tarbiyan da iyayyen yanzu suka kasa baiwa diyansu ?

Sun baku ilimi mai inganci mai amfani a gareku amma boko da zamani tare da mutuwar zuciya a yau

ubannen mu maza suna sakaci da nauyi da amanan da suka daukowa kansu na aurenku har ku haifemu.

Akance Allah ya kauda ranan yabo koda kuwa kana rayene sai an yabeka to nidai Hindu nace Allah ya

jikan baba buhari da rahamansa dattijon arziki dattijon albarka daya so yaga arewa ta koma irin da ba mutuwan zuciya ga maza ko mata amma Allah ba nufa ya karasa cinma manufarshi ba lokaci yayi halinsa.

Da mutanen arewa zasu cire girman kan amfani da kalman Ok a rayuwansu kalman data dasa muna

fadin rai kalman data dasa fankama da takama a zukatan mutane wanda yayi boko da wanda baiyi ba .

Kowa a yanzu fadin rai ya hana ayi aikin karfi a samu kudin duban iyali ana zaune a takama da boko ko

jiran tsamanin aikin gwaunati har mutuwan zuciya ya samu mutum .

Wanda ya samu bai godiya da hakan jira yake yakai gaba tako wani ya Allah kasa mugane gaskiya

gaskiya mu koma hanyar gaskiya irin da muke a baya watau Noma da kiyo da fatauci da kamun kifi

wanzanci kiri da dillanci saye da sayarwa da sauran wai a yanzu wanan madogaran namu su aka koma ana kyama sai kiga dan gado yana gudun da kunyar ace gadon gidansu noma ko kiyo ko da sauransu.

Wanda wanan rayuwan a yanzu yake haifar da abubuwa da dama ga iyali wanda mu bamu fahintar

silan wanan abin zakiga maigida ya koma iyali basu tsoronshi.

Ya yar uwa mai karatu zakiji zance da farko kamar shirme nake koro maki a yanzu wanda saikin natsu

zaki fahinci zancena dutsene don in bai faru a gid'an auren ki ba yana faruwa a gidan yar uwa in babu matsalan gidan yar uwa yana faruwa a gidan makwabta mafi kusa idan babu a makwabta haka yana

faruwa ga wata yar uwa musluma yar arewa mace yar uwarki.

Sai mu duba sakacin nan nawaye shin mu matanne da sakacin tun farko ko mazaje amma

"ummul,aba,isin zancen ya faro daga karatun zamani da muka dauka yafina Allah muhinmanci yanzu ga dan adam ni dai sai ince shine mafarin zancen ?"

Duk wanan tunanen ina yinsa ne ta dalilin ganin yadda mahaifiyarmu Dije take faman wahalan rayuwa

a kan mu.

Zan iya cewa dashi na bude ido nagansu a hakan cikin babban gidanmu da zaki iya kira da gidan gandu.

Irin gidan da kaka da uwayen miji da yayyun minji da kowa nasa suna gidan a zaune a waje daya gidane

dakan koma kamar wani unguwa.

Amma duk da kowa yayi kokarin saya nashi lungun ya kare daga hango dan uwa a cikin gidan don rage

saka ido.

Wanda hakan bai hana tsegumi ko sanin halin dana wancan lungun suke ciki ba wanda dan abu kadan

"zai rikida ya zamo babba dama ance babban gida babban bala,i."

A yadda muke jin labari ga manyan mu ance gidan namu tun kakan kakan mu ake cikinsa wanda a

lokacin duniya na madara ya mallaki wanan wajen wanda shima kusan gadarshi yayi.

"Ya dora dayiwa zuri,an baya baki da cewa wajen zai ish,i zuriansa nagaba har bayan ransu su mahaifan"

mu ke nan ake nufi.

Sai gashi kuwa duk wanda ya taso zaiyi aure da inda zai tsaga yayi nasa ginan har ya koma kamar sun

raba gidan zaure zaure na iyayye a tsakaninsu.

Duk da wanan tsarin nagidan akwai hadin kai a tsakanin mazauna wanan gidan duk da dan akasin hali

da ake samu daga wasu daga cikin gidan .

"Dakan nuna ra,ayi na son kai wajem mata ko diya hakan bai zama wani babban baraza ga mazauna"

gidan ba kamar yadda yake abin sabo garemu yan arewa antoso a mafi yawan gidaje an samu iyayye ko kakani a tare ana zumunci wanda har gobe zumunci na cikin abinda malam bahaushe yake dauka da muhinmanci.

"Wanda wanan abin yake tafiya da addini da kuma al,ada a wasu wuraren a cikin arewan nan zakiga"

gidan ma hade yake da musulmai da kuma wasu daba musulmai ba amma ana zumunci hakana ta jini a tsakani ba nuna kyamar juna a tsakani.

Wanda hakan ba karamin kai zuciya nesa wanda suka fito irin wanan gidajen sukeyi da juna ba don dai

"a zauna lafiya a tsakanin al,umma."

"Duk da wani lokaci akan samu dan sabani amma saboda al,ada ta malam bahaushe hakan yasa yana"

cijewa da daurewa tare da kawar da kai a zauna lafiya da yan uwa.

Mu namu gidan kan gaskiya bamu samu irin wanan gamin gambiza din ba don Allah yayi gaba daya

jinin mu tsbatattacene mun fito daga tsatsa zalla addini na islama gaba da bayan mu.

"Illa akasi dai bambancin ra,ayi na zama shine kawai abin hari a tsakani yau ayi dadi gobe fitina don zaki"

samu ba miji daya ba ba kuma lungu daya ba amma ba zaman lafiya da mutanen gida.

Saboda wata sai a dauki karan tsamgwama a sakawa wata ba gaira ba dalili har abin yaso ya shafi

mazajen gidan wani lokaci.

A irin gidajen nan zaki samu kan wacan hade da wacan tare suke kitsa munakisa waccen zata dauko

gulman kishiya takaiwa abokiyar shirinta.

Ita kuma zata dauka takaiwa wace suke tare tana ganin abokiyar cin mushentace ba zata iya boye mata

komai ba a duniya ai sai kiji cikin kwana biyu zance yana yawo a tsakani kowa da irin abinda zai fassara zancen dashi.

A karshe wanan zancen zai dawo kunnen ke da kika dauki sirin kika fita dashi amma a birkice an gyara

zancen an birikitashi an masa kwaskwarima don aji dadin saurare.

A karshe fitina sai ya barke ya zama masifa inda wani lokacin sai mazan gida sun shiga an gyaro zancen

ayi zama mai kama da yar tsure inda a karshe ake gano munufaka zakiji ana wance ai karku bari wance taji zancen nan.

Amma a irin gidajen nan idan kin kasance mai baki ga masifa ga cin mutunci zakiga kowa tsoronki yake

ji kome kikayi za a iya daga maki kafa a barki .

Wacce bata da baki mai hakkuri mai rashin son hayaniya itakan wanan tatakan kowace wani lokaci har

yaran gida sai suso kawo maki raini don kin kasance mai hakkuri akan komai.

Irin wanan sahun mahaifiyar mu take duk da gida gudane yana da wuya kiga ta shiga wani part din a

gidan koda yaushe kika shigo tana lungunmu a zaune zaki sameta tana tsabgoginta nagida.

Duk da hakan bata tsira daga kaidin cikin gida ba idan wani abin ya hadata da wani yanzune zakiji ana

jefo magana wanda bai dace ba a gareta.

Balle innan mu data kasance mai tarin diya mata a dakinta don har suna suke kiranta dashi a gidan da

uwar yan mata don saida ta jera mata hudu rairan

kafin ta samu tankonsu da kyat dayazo a na biyar.

Wanda har an fara mata shagube akan cikinshi ana fadan maganan banza ta yadda zata tunzura a

samu kafar yi mata tonon asiri da kazallah da aka dade ana tarawa wanda ake jira fada ya hada ai mata nune dashi don kawai taji haushi.

Idan ban manta ba fadansu inna Hafasatu uwargidan baba Adamu akan ruwa lokacin wuyan ruwa yan

famfo sunyi yajin aiki a lokacin sai ake farwa dan rijiyan dake a tsakar gidan kakan mu wanda akace yayi shekara da shekuru a wajen saidai ana gyaransa lokaci lokaci yasa bai fada ba ko ya lalace.

Mama ta riga inna hafsatu isowa bakin rijiyan don saika tsaya ruwan ya dan taru a rijiyan ka kwalfe

dole wanda yazo bayanka ya jira idan ka kwalfe sai ya saka nashi jiron shima a lokacin.

Irin wanan lokaci da kasa ke kafewa ba karamin wuyan ruwa akeyi a garin ba zakiga mutane suna bin

duk inda aka san za a samu ruwa aje neman ruwan amfani a gida.

To cikin irin hakane mama ta aje kaya tana gefe inna hafsatu tana isowa da kayanta kawai ta kawar wa

mama din da kaya ta soma jan ruwan a cikin izzigili.

Haba hafsatu naga dai kinga jiron nan nina sakashi ai amma kinzo kin kawar min da kaya gefe tun dazun

nake jiran ruwan nan a nan ?

Don ganin kuna diba dazun yasa bari sai yanzu nazo in dan samu in dora muna girki zakice bada ita

mama ke magana ba taci gaba da diba tana waka a cikon haibaici irin na barmani coge da suke yayi.

Ranan mama ta kasa hakkuri don haka tace da ita saukin abindai kowa abu dayane ya kawoshi gidan

nan badon an fishi ba ?

Sai lokacim inna ta jiyo dama jira takeyi ta sauka tayi wani shewa tana fadin aure dai ansan wanda aka

auro ba wanda akaiwa cushe ba don halitta ?

A hakan dai ake zaune damu kuma ba nan ko inna ta hau bakinta ta soma zagin mahaifiyarmu ta uwa

ta uba tana mata kazafi da tonon asiri .

Abinda matan gidan ke nema ke nan dama aji kyasham a taru ana kallo da saurare wani lokacin a saye

fadan wani lokaci kuma ayi shiru ana daukan darasi daga bakin wanda ya iya fadan magana.

Ance fadan wanda bai hayani ba kyau tana kaiwa kan iyayyen mama ba ayi aune ba sai gani kawai

akayi mama ta cire inna sama ta nake a kasa tana kai mata duka duk aka zubar da dan ruwan data diba din kowa ya rasa.

Wanan abin daya faru ya kawo sanadin kariyan hannun inna hafsatu daya wanda ta jima tana jinya

akanshi .

Sanadiyar hakan suke kiran mahaifiyar mu da mai kashi guda sai zaman nasu ya kara baci sosai ko maza

a lokacin abin yaso ya shafa saida tsohon gidan ya tarasu yace bai son ya kara ganin hakan a tsakaninsu.

Inda yabawa mai gaskiya gaskiyanshi yakuma hadasu yaja masu kunne akan rigima tun lokacin mama ta

"samu sa,ida daga wani abin izzigili da ake mata a gidan."

"Saidai abinda ba,a rasa ba can ya shiga tsakaninsu din a tsaya ai fadan fatan baki balle ita mama yana"

da wuya kaji bakinta da wata a gidan suna jidali.

Muko yayan mama hattara da zagi da yaba magana a siffan mu ba bakon abu bane a garemu wanda

har mun saba da hakan wajen matan gidan wanan yasa yana da wuya mu shiga cikin yara yan uwan mu kiga muna irin wasan nan da ake hadewa anayi a gida da yara yan uwan mu.

Tsabtan mu ba bai barin haka don dole idan kana zaune da mama ka koyi tsabta komai wuyan ruwa da

akeyi fes zaki gan mu ba datti a jikinmu.

Ga zuwa karatu boko da arabiya ba wasa kuma alhamdullahi Allah ya bamu kokarin karatu gwagwado

muna gane abinda muke dauka din daga ko wani bangare.

Wanan yana cikin tsegumin da yan gidan mu sukeyi akan mama damu din wai mama tana mayar da

diya kamar diyan gwal kamar mu mukafi kowa a gidan.

Da ace mama tayi ilimi mai zurfine da basu san inda kaudinta zai tsaya ba saukin abin dai an fita asali

da ilimin duk abinda take takama dashi gidan andai fita.

Bata damuwa da zancensu illa iyaka dai diyanta da aiyukanta datasawa gaba shine gabanta.

A wani shekara da kan gidan yaso rabuwa shekaran da baba Audu ya tayar da fitina akan a raba gado

abawa kowa a nasa sunkai lokacin da zasuci gashin kansu suma amma an rike abu ana jidali kanshi ba mai iko sai ace sai abinda baba Alu yace shiya gaji da wanan abin gaskiya.

"Abinka da babban gida ashe akwai masu ra,ayin hakan a gidan sai kai ya rabu biyu wasu suka goyi"

bayan baba Audu din wasu kuma suna tare da tsofin gidan.

Dake juya gidan yadda aka taso anayi tun farko abu wasa wasa har yakai hukuma sun shigo zancen .

Ganin da baba Aliyu yayi abin zaikai ga tonon asirine yasa yace ba sai anyi haka ba a zauna a sulhunta a

zamanin shi insha Allahu ba za a samu baraka ba shida diyan yan uwanshi.

Kai gado masiface gaskiya wanda baka zato ko tsamani saiya fitoma da tsigar dabaka zata ba gareshi.

"Don abin harda matan gida da sukazo aure yaso tabawa a lokacin an koma ba,a magana da wanan"

lungun da wancan idan aji mazajen sun samu matsala da juna a wajen zaman da akeyi sai gaba da gori dake yawo a tsakar gidan.

Zance wanan rabon yayiwa mutane da yawa dadi a cikin gidan inda wasu suka samu cigaba daga hakan

wasu kuma suna ganin an kwaresu anyi masu zalunci a ganinsu .

Zance mahaifin mu na cikin wanda suka samu cigaba wajen rabon inda ya tashi da nashi kason dana

kannensa da mahaifisu ya riga rasuwa ya barsu suma daga baya suka dinga binshi guda guda harsu ukku duka daki daya.

Dole wajem kasu aka ware da nasu aka hadawa mahaifinmu shi kadai donshi keda gadon yan uwan

nasa a lokacin.

Sai hakan yaiwa yan uba kuma zafi suka koma ganin laifin mahaifin namu da baba Aliyu da yai wanan

rabon haka don me baba ba zaice ya yafe na yan uwan nashi da basu da rai ba za a hada harda nasu a bashi ?

Baba Aliyu yake fadin maraye abin tausayine a wajenku inga tunane ku kun fishi karfi kun fishi samun

abu dakin ku don dan wanan nashi kuma saiya tsone maku ido yanzu.

Filin gida sam baba bai taba ba yabar abinshi kamar yadda kowa ya bari amma yasaida wani gona da

suka samu a cab wani kauye .

Shi yaje ya sayar yazo ya tayar da sabbin gina a bangaren nashi inda ya kewaye iya abinda Allah ya

tsaga rabonshi acikin gadon .

Aka tayar da sabbin dakuna wasu mama da abokiyar zamanta sai ga bamgaren mu ya koma na zamani

lokaci guda muma anshigo yayi a bangaren mu .

Sauran kudi ya saka a kasuwancinshi yana juyawa sannu a hankali abubuwa suka fara budawa a part

din mu din don munfi kowa zama a karamin shiya a gidan hakana iyayyenmu suke zaune a cikin gidan.

Ba shi kadai ba yawancinsu a wanan shekaran gaskiya an dama sosai don anji dadin rayuwa da abinda

aka samu din.

"Inda labari ya baza gari kamar yadda akewa ko wani ahali idan irin haka ya faru ga zuri,a irin sai"

tsegumi ya biyo baya da jin haushin juna.

Nan baba Audu kan mijinsu inna hafsatu daya kawo fitinan rabon gado dama shi wayayyene idonsa

bude yake don bai zauna gida ba tun yana karami ya koma inda ya fito wajem neman kudinshi.

Daga haka Allah ya taimaka aka danji wani saukin rayuwa a gidan don dama nawai mazan suna kwance

bane don basu so rashin nayine kawai da basu dashi lokacin.

Har ya kawo dole matan sun mike suke tallabe da gida suna daukan nauyin komai daya kamata ace

maza ke dauka a gida.

"Amma halin rayuwa irin na malam bahaushe da kuma abin gado tun ba,aje ko ina ba na wasu ya soma"

tabarbarewa aka fara komawa gidan jiya da matayesu.

Shiko baba Audu da zai dawo gari da tsaraba ya dawowa su inna hafsatu don ko ya auro masu wata yar

sokoto da ake kira da karima .

Shigowan inna karima gidan namu yazowa yan gidan da sabon sallo tare da sauyin yanayi da dama .

"Don inna karima irin matan nan ne masu budaden ido da wayewa kai ance ma,aikaciyar gwaunatine ita"

a can jaharsu din na sokoto.

Ranan anyi tashin hankali sosai a gidan mu bazan manta ba ranan daren wani babban sallah dayazone

yazo da ita a matsayin matarshi .

Dama ana rade radin cewa yana da aure a can ashe har mata tayi haihuwa biyu iyayyen mu maza sun

sani saboda fitinan inna hafsatune kowa bai fada mata ba don gudun fitina.

Inna hafsatu yar gidace ita hakama kishiryata itama duk auren gida baba Audu yayi duka matanshi sai

inna karimace yanzu bare a cikinsu

Ga yadda abin nasu yake sun kasance diyan mace da diyan namiji a wajen kakanin sai kuma kishi ya

hadasu a waje daya tunda baba Audu ya aurosu ya hada a waje daya.

Ita inna hafsatu itace amarya itace zumuncinsu yafi karfi da baba Audu don iyeyyensu don yan cikin

gidane inda abokiyar zaman ta inna laraba uwargidan baba Audu din take zaman tobashiya garesu duka ita tazamo yar wani gida ke nan amma ta fannin uwa yar gidance ita ma.

A sanadin inna balarabane mama bata shiri da inna don suna tare da inna balaraba sosai ita haka take

kamar innan mu bata da son hayaniya ita sosai.

Dan biyewa junan da sukeyi tsakaninsu shine itama inna hafsatu ta hade kai da amaryan inna din suna

iskanci irin na kissa don a cusgunawa gwaggo balaraba.

Kamar yadda mama take da diya mata haka gwaggo balaraba take da yara mata biyu sune manya a

bangaren baba Audu din ita inna hausatu itace tazo ta fara haihuwan bamiji a gidanshi.

Inda dama shine dalilin shigowan ita gwaggo hafsatu din don baba yace bai son diya matashi a

rayuwanshi.

Wanan yasa ta kara daukan girman kai da izgilanci ta muzantawa gwaggo balaraba da sunan wasa har

raini mai tsanani ya shiga tsakaninsu daga baya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/14, 2:45 PM] Mmn Bibo:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Misalin karfe dayan rana yayin da gidan ya rage hayaniya ko wani part sakamakon duk yaran gidan sun

watse zuwa daukan karatu a makarantunin da suke.

Akwai masu zuwa makarantar kudi haka masu zuwa ta gwaunati a cikinsu harda yaran Dije cikin masu

karatu a makarantar gwaunati din .

Kuma Alhamdullahi ba za ace an barsu baya ba don gwargwado akwai ilimin da ganewa a garesu haka

suke fama da challege irin na yayan dake ji da kansu da wa yanda ake gani ba kowa bane.

Salma ce ta shigo gidan da sauri tana hakki tashige dakin mahaifiyarsu mama hau fadin haba Salma ni

dakin tureni ai wanan gudan kamar na ceton rai ?

Daga can inda suke zaune a gindin inuwa inna Asiya ke tambaya ke salma ke kedawa haka a guje

kamar kinga wani mugun abu ?

Ai kema kin sani bai wuce ta fita ba komai a jikinta wani ya ganta ya darkakota a cikin yayyunsu basa

jin magana ance su daina fita ba dankwali ko riga a jiki tunda kullum ana masu fadan fita hakan.

Daki uwar ta koma inda ta hangota can karshen gado ta boye ta soma fadin haba dai Salma baki

tsoron ki fadi ki fasa baki ko ki karye ?

Duba fa yadda kika shigo din nan a guje haka da kadan kin kayar dani a kofa ?

Mama yaya na gani tafe shine na gudu kada yayi min irin dukan da yaiwa yaya ranan don baije

makaranta ba kuma ban saka hula akaina ba nafita.

Tsuki maman taja tana fadin kin faye shirme salma wallahi don kawai ya ganki sai ya dokeki ai yasan ku

baku soma karatun boko ba har yanzu.

Sallamanshi sukaji a tsakar gidan yana gaisawa da abokan zaman mama inda ya dora da fadin wacece

nagani ta gudu yanzu ta shigo gidan nan me takeyi a gida bataje boko ba yau ?

"Saida mama ta soma gaidashi cike da fara,a fuskanta take fadin salmace fa kasan aisu basu fara bokon"

"ba har yanzu ita da sa,id ne munyi munyi malam ya saka muna su bokon abin ya gagara har yanzu."

Amma ai sin girma ya kamata ace sun fara karatu yanzu don Allah a sakasu su dinga bin yan uwansu

zuwa makaranta mana mama ?

Insha Allahu zamuyi kokarin hakan Ahmad an dawo lafiya ya amsa da lafiya kalau mama min sameku

lafiya ya gida kuma dasu baba da sauran yara ?

Wallahi duk kalau muke Ahmad an karasa karatun ke nan koda saura take tambayanshi tana jin

abokiyar

Please Login or Register in order to submit comment