gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading AUREN MANUFA Bayan Aure by 💝 Chapter 1 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng 







[04/11 11:33] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣0⃣
Cikin dare yau ma na farka na ganshi yana tilawar karatun alkur'ani irin na jiya sai wajan asuba naga ya idar da karatun yana bisa kujera waya naji yana yi amma maganar kasa kasa zuciya duk wanda ya bi mata sai ta kaishi ta baro shi saboda sai zuciyata ta mini kila da Fa'izansa yake waya, tun da sam bana jin abinda yake fada. Kuka na shiga yi daga kwancen amma ban bari sautinsa ya bayyana ba don kada ya san shi nake wa kuka. Dole inyi kuka saboda wannan wulakanci ne na karshe ace kana kwance da matarka ta aure cikin daki daya amma ka kwana kana hirar soyayya da wata. Ni nasan bai san ido na biyu ba da ya tsinke hirar tasu. Da na gaji da ganin wayar da yake yi bansan me yake fada ba sai nayi alamun da zai zaci ko zan farka so nake hirar ta kare saboda juriyata ta kusa karewa (Allah sarki rashin sani) motsi na yi bisa gadon nayi juyi na gyara kwanciya duk da dakin babu haske so sai amma ina kallonsa motsina sai yasa bi gadon da kallon amma bai daina wayar ba hakan ma ya isa yasa in gane bada mace yake waya ba tunda da mace ce da yaga haka da sai ya kashi wayar amma ni ban gane ba sai ma na dada kuluwa ni a dole ya wulakanta ne ya tozarta ni.
[04/11 11:34] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣1⃣
Da asuba da ya tashe ne inyi sallah sai yaga idona a kumbure sunyi ja sai yasha jinin jikinsa ya tambaye ne, me ya sami idonki? Ko baki sami yin bacci ne idanun ki suka kumbura? nace, nayi bacci ashashshe kafin dai in kwanta ne wani abu ya fada mini a ido na dauka idan nayi bacci na tashe zai da yi min zafi sheni suka kumbura saboda na murzasu. Zuwa anjima idan basu daina zafi ba sai muje asibiti je kiyi sallah bari inje masalaci. Harara na bi bayansa da shi saida ya fice sannan naja tsaki nace, dube shi don Allah kamar wanda ya damu dani, Alhalin shi ya haddasawa idanuna kumbura. Dana koma daki ma tambayoyi hajja ta rufe ni dasu itama amsa iri daya da wadda naba Ya Faruk na gaya mata. Nayi wanka ina zaune da dan tawul iya rabin cinyoyi ina shafa mai sai kawai naji sallah mar mutun ban ankara ba na ya shigo duk saina daburce gashi hajja bata dakin tafi ta sa turan wuta a falon nasan ya ganta shi yasa baijira an amsa masa salama ba ya shigo. Jikina rawa yayi na yayamo zani na daura ina lura dashi yadda yabi cinyoyi na da kallo, amma da ya ga mun hada ido sai yayi saurin dauki kansa shi a dole bisa tsautsayi ya kalleni. Na dauki wani karamin hijabi nasa saida na gama kidi mata sannan ya dube ne yace, da ma zan dan fita ne shine nace bari in gani idan idon bai daina ciwo ba saimu wuce asibitin. Nace, na wanke shi da ruwan dumi da gishire ya daina ciwo. Yace okey to Allah ya sawake ni zan fita amma yanzu zan dawo. Nace, to a dawo lafiya. Fita zaiyi baki yi masa abin karyawa ba? nace, fita zaiyi amma yace ba zai dade ba yanzu zai dawo. Tace, sai ki kokarta ki shiga kicin kiyi masa abinda zai ci kin girki sai yana saye zuciyar miji bale ida mace ta iya nau'o'in girki sai kiga duk inda yaje sai ya dawo yaci abincinta in tafiyar kwanace ta kamashi da kyar zaki ga yana iya cin abincin otal sai ki bada himma wajen iya girki da tsaf tace shi don na lura mijinki sarkin tsaftani dan gayu. Ni dai ban yiwa hajja musu ba amma nasan ko nayi girkii da wuya wannan sarkin iya yin zaici tunda tun asali baya cin abu
[04/11 11:34] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣2⃣
Asali ma baya cin abu idan muka yi amma ban san yanzu ba nayi shirina tsaf kamar zani wata shahararriyar unguwa sannan na nufi kicin din don in game ya kamata inyi masa stord din da aka shake mana da kayan abinci na bude na duba na ga kayan abinci ne shakare ni ban ma san yadda zamu yida suba sai dai rabawa dangi. Na farke buhun fulawa na debi kadan dai dai yadda zata ishemu na debo kwai wadatace sannan na dawo kicin din (meat puffs) zanyi mana na zuba filawar a cikin wata container ta silver sannan na fasa kwan akai nayi ta bugawa sannan na zuba ruwa na cigaba da bugawa dama tun shiga ta kicin din na wanke nama na dora a wuta saina duba naga ya dahu saina sauke na kwashe shi na dauko abin nika nama na nika shi sai na juye a cikin bugaggiyar fulawa da kwai din nan na nika albasa da atarugu sannan na zuba a ciki sai nasa curry tyme da magi sai gishiri kadan sai nayi ta cakudawa ya hadu so sai sannan na dora mai a wuta na fara soyawa nan da nan gidan ya dau kamshi. Ina tunanin Ya Faruk ya kusa dawowa shi yasa sai na dama masa koko na zuba a wani jug mai rike zafi saboda su Ifty sun gaya mini yawanci abin karyarmansa kenan. Naje na shirya dinning table din mu tsaf na goge ko ina sai kyalli yake yi abin kaga gilas nayi haka ne don kada sarkin tsaftar yaga gurin da kura. Na dauki namu na wuce dakina dashi. Hajja santi ta dinga zubawa wai wannan abunda na soya soyen zan dinga yi zan kwace mata miji. Muna cikin dariya sai gashi ya dawo ya dan leko yayiwa hajja sannu ya fita. Ta dube ne tace, tashi ki bishi ki bashi abincin nasa, kullun ana koyawa mutum abu bazai dauka ba. Lafiya na dauka na nade jikina zan fita tace, bana ce idan zaki gurin mijinki daina nade jikiba? Shifa ya halasta yaga komai naki. Nace idan naje dakinsa ina cirewa amma yanzu kinga kayan jikina sun matseni zaki iya ganin muna zaune a falon yayi baki maza shi yasa nake rufe jikina shima yace gara in dinga yin haka. Kaji karya yau shema ya bita kan lamarina balle ya san me nake yi'ni dai ina yin haka saboda bana son ya ga.
[04/11 11:35] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣3⃣
Kaji karya yau shema ya bita kan lamarina balle ya san me nake yi ni dai ina yin haka saboda bana son ya ga kamar don inja hankalin sa nake sa matsatsun kaya shi yasa nake boye jikina. Ina fita na ganshi a falo ya harde a doguwar kujera (3 seater) da mutuniyar tasa yana sana'ar wato (daily trust) ita yake karantawa ina jin ma ita ya fita sayowa. Na matsa daf da shi nace, ga abin (break fast) dinka can bisa (dinning) ya dube ni yace, I am sorry ina azumi ai ban san zaki yi ba dana gaya miki da baki wahalda kan ki ba. Raina ya sosu haka kurum hajja ta sani sai cusa kai nake yi gurin mutum amma shi sai gwalene yaki yi ya zanyi bari dai hajjan ta gama kwana bakwanta ta tafi idan yace haka zai cigaba dayi mini to bazan jure ba yana yin zamanmu zai canza zan kama kaina kuma ni na san ba wani azumin da yakeyi in ma yana yi to don kada yaci abinci nane ya tsiri azumin. Na daure nace, shike nan dare me za'ayi maka na buda baki? Yace kada ki damu bana cin abinci mai nauyi da dare tea kawai zan sha. Nayi jima rama nace lallai wannan mutumin dani yake zance wato har yanzu yana tunanin ban gama kaiwa matsayin da zanyi abinci yaci ba kenan shike nan nasan yadda zanyi muje zuwa. Na juya abina na koma daki hajja tace, har ya kamala cin abincin? wai azumi yake, tace, ai ya wuce wai zai yi miki karya ne? nace, ba wani azumin da yake yi kin san shi sarkin tsafta kila gani yake ban iya girki ba ko bani da tsatfa tunda haka yake mana a gidansu idan mamata samu yin girki in dai ya san shi mu muka yi baya ci ni ina ruwa na cikin sa ya cuta. Hajja ta rufeni da fada waidon me zance haka bayan ta gama fadan kuma ta koma yi mini nasiha.
[04/11 11:35] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣4⃣ Daren yau da yake na san abinda na shirya shi yasa da nayi wanka nayi shirin baccina banjira tace in tafi ba nayi mata saida safe na fice inaji tana cewa, ko kefa ashe dai kin san abin da ya kamata dama shakiyanci ne. Ni kam nasha alwashin insha Allahu na bar kara zuwa dakinsa kwana don bazan iya jurar wulakanci tunda ai bashi da lokacina daga sallah sai karatun qur'ani yake yi maimakon idan ya gama ya nuna kullawarsa a gare ne a'a gara yakarasa daren da yin waya shi yasa zan barshi koma da wace ce wayar gara in barsu inbai gani baya saki jikinsa su soye da kyau. Dakunan da aka gyara na saukan baki na shige gadon gyararre babu abinda babu saina kashe fitila mai haske na kunna bacci nayi addu'o'ina sannan nayi kwanciyata lakadan ba fargabar komai, bacci nayi mai isata saboda ko sallar nafila da ya kamata in tashi inyi Allah bai bani ikon farkawa ba, a dalilin duk dare bana samin yin bacci da rana kuma baki ba shakatawa sai dare yayi shi yasa har na so in makara don sai biyar da rabi na tashi.
[04/11 11:35] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣5⃣
Ina dar da salla a dakin da na kwana sai na baro dakin don kada Ya Faruk ya dawo masallaci ya leka can dakina yaga bai ganni ba kada kuma ya tambaye ni labari yasha bam bam da kuwa na shiga uku da fadan hajja kila ma tace sai ta gayawa mome ko dadi ni kuma tsorona Allah tsorona laifin da za'aje ace musu muyi wa mijina kada suga ba'aje ko ina ba na fara ruguza biyayyar da na basu tabbacin nayi musu, koda abubuwa zasu canza yadda na lura da take takensa shima yafi son sai hajja ta bar gidanmu nima nafison kada muyi komai da zata fahimci zamanmu na yan marina ne. Ina shiga dakin na isketa bisa sallaya bance mata komai ba kawai saina warware lafayar jikina na haye gado na shige cikin bargo ba bacci zanyi ba amma dai ina so in kwanta ne kawai. Ban dade da kwanciya ba hajja ta tashi daga abin sallar ta koma bisa kujera ta zauna na yaye bargo nazo na gaisheta ina shirin mikewa inje in sake kwanciya saiga wanda nake tsoron kada ya shigo dakin ganni da matsatsunriga da wando yayi sallama ya shigo dakin baccin nawa da sauri na koma nayi zaman cin tuwo a gaban hajja kallo daya yayi mini yayi saurin maida ganinsa gurin hajja yana gaisheta suna gama gaisawa nima na gaisheshi ya wani kasheni da idanu yana kare mini kallo banda matsatstsun kayan dake jikina ma kaina babu kallabi ga kana nan kitso na sun watsu a gadon bayana babu inda idanunsa basu karade da kallo a jikina ba ni kuma duk saina muzanta inaso in tashi amma kafafuna sun gaza motsi dole na hakura na zauna. Ya tsaida idanunsa cikin nawa yace, yaya kika kwana da idon naga yau basu yi ja ba? Gabana ya fadi Allah yasa kada ya tona mini asiri ya nuna cewa ban kwana a gurinshi ba. Nayi saurin cewa, sunyi sauki.
[04/11 11:36] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣6⃣
a takaice don bana son inja maganar da tsawo. Ya mike yace wa hajja, zanje in kwanta saina fito zuwa anjima. A raina nace, ai dole kaje ka kwanta kayi ramuwar bacci tunda an kwana ana waya da masoyiyya. Kamar yaji abinda nace sai naga ya dan kalleni yana wani miskilin murmushi. Bayansa nabi kamar yadda hajja tace inje inji me yake sona karin kumallo dan wulakancin nawa yau ma sai yace mini yana azumi saboda bakin cikin gwalene da yake yiko gayawa hajja abinda yace banyi ba kawai saina haye gado na kwanta sai ta tambayeni bazaki shiga kicin din bane kika kwanta? nace yace yau ma yana azumi kowa zai nuna ma walittaka da takawa oho? inaji hajja tana nanatawa "azumi". Allah ya bada lada. Ita naga ta soma zargin wani abu tunda naga damuwa karara a fuskarta. Ta tambaye ni, ba a gurinsa kika kwana bane naji yana tambayarki ya kika kwana da ido? na yi saurin cewa, can na kwana ina idar da sallah da naga bai dawo masalaci ba shine na taho daki. Tace nifa da kika ganni nan zaune ba zaman haka kawai nake bana zauna ne don in saki a hanya in kwaba miki idan kinyi ba dai dai ba bana son bayan na bar gidan nan mijinki ya kawo karar kinyi masa wani abu badai dai ba shi yasa tun yanzu nake sonki tafi yarda komanki cikin tsarin addini kiyi abinda zaki faranta ran mijinki ki tsaya masa arai kamar kafumar kusa a bango daga yanzu bana sonki baro gurinsa da wuri har sai inshi ne yace ki taho kuma da yace baya cin abu mai nauyi da dare ba zai yiwu ke ki kyale shi yayi azumi yayi buda baki da zallan ruwan tea ba yau ki shiga kicin ki hada masa duk wani abu da kika sani mara nauyi, kada ki kara kyaleshi ya dawwama da shan tea. Bin hajja nayi da to saboda na san duk yadda na fahimtar da ita mijina murdadde ne ba zata gane ba tunda nariga nasan halinsa tun kafin muyi aure yana da wuyar a canza masa ra'ayi.
[04/11 11:36] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣7⃣
Bai dawo gida ba tunda ya fita bayan la'asar sai ana kiran sallar magriba muka ji hon motarsa hajja ta dubeni tace, ga mijinki can sai ki shiga kicin ki dauki abun sha mai sanyi ki tare shida shi, idan ya dawo sallah sai ki gabatar masa da abubuwan da kika tanadar masa ki zaunar dashi cikin hira da kissa ki nuna ko dan yaya ne yaci da yawa indai girkin yayi dadi maza tashi kije. Na shiga kicin na dauki madarar holandia mai sanyi sai juice 5 a live na hada sannan na nufi dakinsa harya dauro alwala ya fito zai je masallaci ya tareni ya amshi kayan hannuna yace, masallaci zanje bani holandian din da na zuba nace, zanje inyi sallah ne. yace jiya me ya hana ki zuwa taya ne kwana? idan nazo me zanyi maka bayan kana da me taya ka debe kewa a waya. A zucci na fadi haka amma sai a fili na ce, baccine ya dauke ni ban sani ba shi yasa. Yace, to yau kizo. Ya mika mini kufin cikin sauri ya wuce massalaci ni ma barin dakin nayi na koma nawa dakin. Allah yasa ban zuba abinda hajja ta matsa inyi masa ba saboda na san bazai ci ba sai dai aba almajirai shi yasa na shirya kuloli babu komai a ciki bisa dinning don kada hajja tace ban bi umarninta ba ai kuwada nace ga abincinsa can sai cewa yayi inyi hakuri tea kawai zaisha ban nuna masa naji haushi ba amma yadda ya bukaci inzo taya shi kwana sai na fanshe haushi na anan naki zuwa dakina na jiya can na kwana ma yau. Ranar hajja zata tafi ranar kwananta na bakwai tun safe nake mata kuka nace ni dai bazata tafi ba inba haka ba idan ta tafi nima zan biyota gidan. Ta dinga lallashi na tamkar yarinyar goye, kina da hankali ne zaki ce biyo ni haba Hanifa ya zaki tada hankalinki dubi yadda yaron nan yake nan nan dake indai yana gida aikinsa kenan ya leko yaga ya kike kulawa dai dai gwargwado yana yi miki to me kika rasa?. Kiyi hakuri idan an kwana biyu zanzo in sake duba ku sannan baga waya basai mu dinga magana duk abinda ya shige miki duhu idan baki kirani a waya ki tambayeni ni kawarki ce.
[04/11 11:37] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣8⃣
25: Ko kin daina kawancen dani? dole nayi dariya hajjama tayi dariya tace, yauwa haka nake so"
Faruk ne da kansa kai hajja acan ya iske Ya Saif suka fito tare da yake Ya Saif bai koma ba hutun karshen shekara yazo. Suna hanyar zuwa gidanmu ne Ya Saif ya watsowa Ya Faruk tambayar da ta kwana bakwai tana kwakular wadda ada ya kanne bazai yi taba amma yanzu kalaman da yaji hajja na fada na yadda su Faruk da matarsa ke zaune lafiya a dalilin bin umarnin iyayensu da suka yi sai ya tsinke ya tuno ranar da aka zo aka ce wai Hanifa ta kai budurcinta yaga ana ta murna da dafe dafen abinci to wai ko aminina sa ya karya alkawarin daya daukar masa ne ya canza MANUFAR Aurensa da Hanifan. Damuwa karara ta bayyana a fuskarsa ya daure yace, Friend ko ka san tun kwana bakwai da suka wuce da aka cewa wai Hanifa ta kai budurcenta naga ana ta shagula fargaba ta dameni ina tunanin ko ka kasa rike alkawarin da kayi mini ne? dariya Faruk yayi ya dan dubi Saif sannan ya maida hankalinsa gurin tukin da yake yi yace Deen kenan kana tunanin zan iya karya alkawarin dana daukarwa nagartacen amini kamar ka? Gaskiya banyi tunanin zaka kawo faruwar hakan da gaske a zuciyarka ba kana son in rantse maka sannan kayar da dani? Saif yayi saurin girgiza kai yace, wallahi na yarda da kai babu haufi a aminta karmu amma (how comes) ka shirya (plan) din faruwar hakan gaskiya kashigar da iyayen mu so sai.
[04/11 11:38] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣9⃣
Faruk yayi murmushi, ya gaya masa yadda yayi ya shirya hakan tare da goyan bayan Hafina suka shirya komai ya kara da cewa itama na lura taji dadi da nayi haka don har yanzu na lura bani a gabanta balle taji haushi banbata hakinta ba haba ni wannan yarinyar ai tayi mini kadan duk ranar da naje mata da bukata ai ina sai buzunta don zata ji jiki sam ma ba zata iyada lafiyyaye kamar ne ba yadda take yar lange lange koda yake tana da fadi ta kasanta amma ina she is too young nafi karfinta bazata iya dauketa ba. Dariya sosai Saif yayi yace, ashe Allah ya taimaki yar kanwata data gane kurinta nine nan fansarta kana nan kana azumin da nasan kana yi na kare kai daga sha'awa? yace inayi babu fashi amma kasan sarai daci ance sheyaki kawo jin yinwa ko? To ni ban danganta bukatata a tare da ita ba inda nakai tawa daban shi yasa ko jikina ban damuba koda a bargo daya zamu kwana. Ya Saif dai shiru yayi amma abin nasa shi cikin kokwanto saboda bakowane lafiyyen namiji bane zai iya abin da Faruk ya fada saboda Hanifa tana da abubuwa masu daukar hankalin da namiji inba wanda yakai zuciyarsa nesa ba gaskiya babu wanda zai iya kauda idonsa a kanta balle shi Faruk da yake mijinta take matsayin matarsa mallakinsa halak malak anya zai iya boye sha'awarsa a kanta? Saurin kawar da hakan Ya Saif yayi a zuciyarsa don baya fatan abinda zuciyarsa take yawan ayyana masa ya zamo gaskiya wata rana sun iso gidanmu suka tarar gidan tsit bana babban falonmu Faruk ya haye dakinsa na sama bai dade baya fito ya iske Saif ya tasa T.V. agaba labaran CNN yake kalla har Faruk ya zauna sai ya dube shi yace, na san tana can dakinta tana bacci don na lura sarkin bacci ce.
[04/11 11:38] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 4⃣0⃣
Ba da san ransa ya nufo dakina ba saboda yanzu tunda hajja ta shige idan mun hadu a falo shike nan ma tambayi lafiyar juna idan kuma bamu hadu ba to a sauka lafiya don baya son abin da zai sa ya zubda girman sa a guri nashi yasa ya sha alwashin jan ajiosa. (kunjifa jama'a mijine zai jawa matarsa aji)
Bana falo na can kudune bisa gado ina aikin kuka sai kira'ar Jabir dake tashi adakin don kukan da nake ba mai sauti bane hawaye ne zalla ina kokawa kaina ne shin wace irin rayuwa zan fuskanta yanzu a gidan nan da ba hajja? Wulakanci ne daina san sun shirya dakonsa kwando kwando tunda koda hajja tana nan aboye Faruk yake mini gashin kuma yana gasa mini gyada a tafin hannu a gaban hajja ne yake nuna kulawarsa a kaina tunda ko abincinda take da ina dafa masa tsawon kwana bakwai bai taba ci ba kosau daya itace dai take ganin kamar yana ci wannan ma kadai wani nau'in wulakanci ne ka dafa domin mijinka amma yace baya ci.
Kaina yazo ya tsaya ya kira sunana na dago ido na da suka yi ja na amsa, na'am. Yace ai har yanzu kukan kike ye? Lallai aiki ya ganki. Ki taso ku gaisa da Deen. Na kwantar da kaina nace, ba zan iya zuwa ba jiri nake ji ka gaishe shi. Ko sannu baice mini ba ya juya ya fice abinsa wannan halin ko in kula daya nuna mini ya kara tunzira zuciya ta lallai yanzu ne zan tabbatar da an kawo ni gidan mijin da baya sona yanzu ne zan soma zaman hakuri da zaman hadiyar duk wani nau'in wulakanci da zai yi mini.
Yunwa Ya Saif yake ji lokacin shi ya sa da Faruk ya koma yace masa ina bacci sai yace ya bashi abinci dana na dafa yaci ya dube shi yace, Kaima ka san bana cin girkin yara ka shiga kicin din ka duba kila ka sami wani abu. Saif ya tashi da saurin sa ya nufi kicin din saboda yayi kewar cin girkina mai dadi fiye da na matarsa shi idan da halima kullum nan zai dinga zuwa yana cin abinci na tunda shi aminin nasa ba yaci. Ya duba cikin wata warmer ya iske nayi (cream macaroni cheese) sai turiri take yi ga dadin kamshi na tashi dana dafa naci ne yayi mini yawa shi ne na ajiye.
[04/11 11:40] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 4⃣1⃣
Wanda dana dafa naci ne yayi mini yawa shi ne na ajiye ko zanyi baki idan ba wanda yazo in ba mai gadinmu ya zauna a (3 seater) kusa da amininsa ya janyo (center table) ya dora warner din sannan ya bude ya soma zuba abincin ya cewa, ko in zuba dakai wallahi girkin yayi dadi baka ji kamshin dadi na tashi ba? Faruk ya wani ya tsina fuska yana duban abincin yace, kai dai da kaga zaka ci bismilla ni a koshe nake. Ya dai fadi haka ne kawai amma kallon abincin da yayi sai yaji miyansa ya tsirga da alamun abincin zaiyi dadi amma bazai iya zubar da ajinsa ya ci ba gara dai yaci gaba da cin na (El kanemi Restaurant) ya fiye masa. Ya Saif ci yake yana zuba santi hardai ya kare yace, kai tunda baka ci ni zan dinga zuwa inaci madadinka. Faruk yace, idan ta tashi bacci sai kadawo anjima ka gaya mata don ni bazan iya wannan zubda girman ba kaima ka sani sai tayi zaton kila nine zan dinga ci muka hada baki da kai alhalin na gaya mata in don ni ta daina wahalar dafa abinci dani. To kai aikin me matarka take yi? ko ba zaka ci nata bane koda yake tana da lalura ko nine ita bazan iya baka hada ta da kaya kuma kace dole sai ta yi maka abinci kaci. Yayi dariya ba ita ta kawo kanta ba kuma bai hana idan Allah ya rabata da wannan gobe mata dawo ba. Suk tintsire da dariya suka tafa Faruk yace, amma kai dan iska ne ka dai bi a hankali niba ruwa na. Tun daga wannan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment