gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading GONAR SHARRI Inda Mugunta Ta Yi Gida by BILLY S FARI Chapter 1 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ÿþ"[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*"

*³AN TAGWAYE BIYAR*

(Batch C)

NA

*BILLY S FARI*

Da

*HAJJA CE*

Areewabook@billysfari

Page 1..

"Tunda ta nufo cikin parlorn gabaki Waya hancinsa ya sha™o masa lafiyayyun ™amshin turarukanta masu matukar daWi, gabaki Waya sai yaji tamkar bai shafa nashi turarukan ba saboda yadda nata ya yi bala'in yin tasiri a gabaki Waya wajan. Zaune Alhaji Sha'aban Sada yake akan 2seater hannunsa ri™e da wayarsa yana dannawa wanda shigowarta yasa shi Wago kansa yana kare mata kallo mai cike da soyayya. Kyakkyawar mace ´ar gayu da kuma ™walisa da kallo Waya zaka yimata kasan don abun duniya ya tattara gareta, Murmushi suka sakarwa juna a lokacin da ta gama ™arasowa inda yake yana Wan matsawa can gefe alamar tazo kusa dashi ta zauna. Wani kallo tayi masa wanda yasa shi sakin ™awataccen murmushi tare da maida kansa yana kallon side table Win da ya janyo zuwa gabansa wanda yake cike da tarin dukiya akai da alama amfani zai yi dasu. Zama Hajja Maimoon tayi tare da rungume shi tana kwantar da kanta saman kafaWarsa cikin kulawa, hannunsa ta kamo cike da hikima da soyayya tana matsa su cikin nata. Sumbatar hannun tayi kafin ta Wan Wago kai ta kalleshi tana yatsina fuska kamar"

shagwaSa take faWin.

"""Ya Habiby shine ka gudo nan ko?"" Murmushi Alhaji Sha'aban Sada ya yi yana dawo da kallonsa gareta, ta lumshe ido zuciyarta cike da tunanin mai zai yi da uban kuWin nan haka dake gabansa? Matse hannunsu da ya yi ne yasa ta dawowa cikin hayyacinta. Cike da sanin yakamata domin Alhaji Sha'aban mutum ne da yasan kansa yasan kuma mutunci da karama na"

iyalinsa yake faWin.

"""Nan na taho ina jiran Irfaan ya ™araso."" Murmushi ta saki tana sake kallan uban kuWin dake gabansu, bataki a bar mata su ba gabaki Waya dan tsab zata iya Satar dasu a yau Win nan ba tare da ta jinkirta ba, tana mamakin yadda mijin nata yake da uban arziki amma kuma baya sakar mata su tayi yadda takeso. Sai dai duk abinda take bu™ata yana batashi, takan tuna maganar"

™awarta da take cewa.

"_""Kinsan fa ´an kasuwa basu sakarwa matansu kuWi haka kawai dole sai da dalili, ki dinga yi"

"masa dabara kina kwakular rabonki idan ba haka ba babu abinda zaki tara a tare dashi.""_"

"Murmushi ta sakeyi zuciyarta cike da tunanin yadda zata fisge rabonta kafin ta bari a fitar da su daga gidan. Yadda ta sauke numfashi a saitin kunnansa sai da yasanya Alhaji Sha'aban lumshe idanunsa yana jin wani irin abu a jikinsa zummm. Ta lura da yanayin da ya shiga dan haka ta sakar masa hannayensa tana jingina bayanta jikin kujerar da suke, da tsantsar kulawa take"

masa magana.

"""Ya Habiby yauma aikin ladan za'a yi kenan?"" Yace,"

"""Wannan aikin na wajibi ne Hajiya za'a kaiwa."" Wani abu mai zafi ne ya daki cikin zuciyarta dama tun kafin ya faWa tasan cewa Hajiyarsa za'a kaiwa, haushi da bakin ciki suka cika mata zuciya. A duniyar nan tana matukar kishi da matar nan saboda irin kulawar da Alhaji Sha'aban yake bawa Hajiyarsa a wajan Hajja Maimoon tayi yawa, gabaki Waya idanunta kullewa sukeyi ta manta da matsayin matar a wajan mijin nata. Shi kuma baya haWa komai da mahaifiyarsa dan wani irin girma da soyayya mai matukar burgewa ce tsakanin su. Kasa haWiye bakin cikin nata"

"tayi, sai dai bata yi magana ta yadda zai gano akwai wani bad thing a maganarta ba tace."

"""Ya Habiby kenan, Allah ya rabaka da Hajiya lafiya. Kana ji da ita matukar ji dan ni kam ban taSa ganin namiji irinka mai ji da mahaifiyarsa ba. Amma Ya Habiby sai naga kamar kana cikawa Hajiya kuWi bayan kuma baka barta da rashin ci ko sha ko sutura ba, ni sai naga kamar kuWin da kike aika mata dashi is too much, kasan kuma ba wai ita ke amfani dasu ba."" Tayi shiru tana fatan samun nasarar maganganunta suyi tasiri a gurinsa. Sai da ya juyo ya kalleta tare da sanya tausassun hannayensa ya kamota zuwa jikinsa yana sake sha™ar ™amahinta da yake"

saukar masa da wata irin kasala yake faWin.

"""Basu yi yawa ba Madam, waWannan ba komai bane da zan bawa Hajiyata, duk wani abunda zan bata bazan iya biyanta da abubuwan da tayi min ba. Za'a kai mata idan tace sunyi kaWan Madam dole zan ™ara mata saboda komenene na zama a yanzu itace mutum ta farko da ta bani gudummawa ba tare da gajiyawa ko gori ba."" Tunda ya furta idan Hajiya ta nemi ™arin wasu kuWin akan wannan na gabanta da za'a akaiwa Hajiyan, gabaki Waya hankalin Hajja Maimoon ya sake tashi. ˜an™ance idanuwa ta shiga yi tana jin zuciyarta tamkar zata fito. Karan hancinta taji"

yaja tare da sumbatar saman hannunta da yake ri™e dashi yana cewa.

"""Ko duka arzikin da Allah ya yi min Hajiya tace na bar mata su zan bata babu gaddama bare kuma Sata rai."" Duk yadda Hajja Maimoon take jin kamar zata mutu saboda yadda yake nuna"

"kamar mahaifiyarsa tafi ta, sai kawai ta daure sosai tana sake shige masa take cewa."

"""Masha Allah haka ake so ai Ya Habiby."" Tayi shiru bata ™arasa abinda ke ranta ba saboda tana son tayi amfani da damar itama ya wawuro wani abun a cikin kuWin ya bata. Ta buWe baki zatayi magana Irfaan ya fara knocking, Alhaji Sha'aban ya Wan saisaita kansa yana kallan ™ofar tare da bada izinin a shigo. Cikin girmamawa ya gaishe su suka amsa Hajja Maimoon sai hararasa takeyi tana mi™ewa tsaye, zuwan Irfaan tasan ba zata samu ko naira biyar ba, idan kuma an"

bata Irfaan yana komawa gida zai gayawa mahaifiyarsu. Ficewa tayi bayan ta ™udiri aniyar

karSar nata dan ba zata taSa hakura ba.

"Iya karfin ta take amfani tana dirzar tiles Win dake jikin bangon bathroom Win, gabaki Waya ta haWa zufa tana yi hawaye masu zafi suna gangarowa saman fuskarta. Sai da ta tabbatar da cewa ya fita yadda duk bala'i ba za'a iya dawo da ita baya ba sai idan suna son kuma bata wahala, sannan ta saka bayan hannunta tana sharce gumin da yake tsatso mata a saman goshinta."

Handshower ta janyo bayan ta kunna ruwa ya fito ta shiga Wauraye tiles Win kafin ta sake Wakko sosan da ruwan da ta haWa kumfar taje tana sake dirzar cikin standard jacuzzi Win wanda yake fari ™al dashi. Yadda taji an buWe ™ofar an shigo ne yasa ta juyowa a firgice dan ba ™aramin tsora taji ba. Wani kallo da take yi mata ne yasa ta sauke kanta ™asa tana jin wani irin tashin hankali yana shigarta dan bata san laifin da za'a ce tayi ba yanzu. Cike da wulakanci

da ™askanci take kallonta tana sake ™arewa bathroom Win kallo.

"""Yauma sai da kika sa na taso ko? Wai Jauhar me yasa baki da tunani ne na tashi da wuri kiyi mana abunda yakamata? Mtwww dallah can ki Wauraye zan shigo nayi wanka ´ar ™auye kawai."" Tana gama maganar ta juya tana banko ™ofar. Da kallo Jauhar tabi Suhana wacce zata iya cewa kaf cikin yaran gidan tafi su saukin kai a hakan. Sauri tayi ta shiga wankewa tana sake wanke sink da shower tare da duk abin ya dace a wanke a cikin SanWakin. Sai da ta gama sannan ta Wakko towel Win da ake goge bathroom Win nan ma ta goge ko'ina ta saka bathroom freshener. Sai da ta kusan fitowa daga ciki tana ri™e da handle Win ™ofar ta sake kallon ko'ina, ita kanta sai da tayi murmushi ganin ya yi kyau sannan ta rufe. Jikinta ciwo yake sosai burinta ta zauna ta huta, kallon gadaje guda ukun dake jere a cikin Wakin tayi tana kallan masu yin bacci akai. Ina ma ace itama tana da gatan ta zata ganta tana bacci so compartable koda ba a irin wannan gidan ba. Jiki babu karfi taje zata fita harta murWa handle taji an kirata da sigar da tafi"

tsana wato.

"""Ke..!"" Ras kirjin Jauhar ya wani irin bugawa, zuciyarta ta harba tamkar zata yo waje. Ta daWe tana kokawa da numfashinta yadda zata samu karfin zuciyar da zata jurewa abinda wacce ta kiratan zata yi mata. A hankali ta juyo tana kallon wacce take kwance a kan gadon tsakiya,"

yadda take haka ta juyo ta ganta bata motsa ba idanunta kawai ta buWe.

"""Zoki yi min tausa jikina ciwo yake mun."" Jannat ta faWa tana sake maida idanunta a hankali ta rufe tamkar ba ita tayi maganar ba tana sake bajewa akan ™awataccen gadon nata. Hawaye Jauhar taji sun zubo mata wanda tana da tabbacin na bakin ciki ne, a girme tasan ta girmi Jannata dan ta bata shekaru biyu suna gidan akaiwa Jannat birthday Win 12 da 13years ita kuma yanzu haka 15years take dashi. Amma yadda ta rainata take kuma wahalar da ita tare da kyamatarta kaf gidan babu mai yi mata kalar na Jannat Win. ˜arasawa tayi wajan gadon tasa"

hannunta akan ™afafuwan Jannat Win zata fara matsa mata kawai taji tana.

"""Ahhh."" Tare da Wagowa ta hankaWa Jauhar Win. Gabaki Waya tayi baya ta faWa ™eyarta ta buge da gadon Suhana. A gigice Jannat ta shiga cukuikuyewa a duvert tana sake sakin ihu tamkar wata"

wacce take ganin abin tsoro.

"""Menene wai Jannat? Me tayi miki?"" Sohana ta shiga tambayarta ganin yadda ta gigice. Kafin"

tayi magana Hajja Maimoon ta shigo cikin Wakin.

"""Meya faru?"" Ta tambaya tana nufar Jannat dake takure. Jikinta ta janyo ta a ruWe tana"

"duddubawa ko zataga wani abun, ganin babu komai yasa ta sake tambaya."

"""Jannat menene?"" Cikin kuka Jannat ta fara magana."

"""Gatacen daga cewa ta matsa min ™afafuwa na kawai tazo tana shafa min ruwan hannunta, gashi hannun da mugun sanyi."" Ta ™arasa faWa tana shigewa jikin Hajja Maimoon wacce tsabar Sacin rai har kamanninta sun soma canzawa. Furucin Jannat yasa Jauhar saurin kallon inda suke zaune tana ware idanuwa jin sharrin da Jannat keyi mata. Yadda taga Hajja Maimoon ta Wora Jannat a jikinta tana lallashi ne yasa Jauhar kasa yin magana sai hawaye da yake zubowa daga idanunta tasan yau kam ta shiga uku saboda ta saka shalelen gidan kuka. Suhana ce ta dafe kirji tana yin wulli da duvert Winta, sakkowa tayi daga kan gadonta ta nufi inda Jauhar ke du™e a ™asa ta fisgota da karfi. Jauhar ta kalli Hajja Maimoon dan ganin reaction Win ta, ga mamakin ta sai taga ta Wauke kai tana kwantar da Jannat a hankali tamkar wata kwai da ba'a"

fatan ya samu matsala.

"""Gaya mana muji aiki kika zo ko kuma kashe mana ´ar uwa? Kinsan ai tana fama da limoniya shine kika zo zaki ™arasa ta ko?"" Ko kafin Jauhar tace wani abun tuni taji an wanke fuskarta da wani gigitacen mari wanda yasa ta manta da kanta na tsawon sakanni. Muryar Hajja Maimoon"

ce ta dawo da ita cikin duniya da kuma hayyacinta inda taji tana cewa.

"""Da alama bakin cikin ganinsu kike yi ko?"" Kuka ya kwacewa Jauhar tayi saurin toshe bakinta"

da tafukan hannunta tana girgiza kai.

"""˜arya kikeyi shegiya mayyar yarinya, to ina faWa maki idanunki ya fita daga kan mutanan gidan nan domin su ba watsatsu bane ba kamar ke dan nasan ke kanki kinga alamar hakan. Idan kuwa kika sake Satawa wani rai a gidan nan ina tausaya miki Jauhar domin sai na lahira ya fiki jin daWi. Kije kiyi warming hannunki sannan kizo ki mata abinda takeso kafin kiga Sacin raina, ™azama kawai."" Ta faWa tana yi mata kallo mai cike da tsana. GabaWaya tazame mata kadangare bakin tulu ta rasa yadda zatayi da ita, Banda kaddara ita kam bataga dalilin da zai sa taci gaba da ganin yarinyar nan a cikin gidanta ba. Da gudu Jauhar ta fice daga Wakin, kitchen ta shiga tare da fashewa da wani irin kuka mai sosa zuciya. Gudun kada ta sake janyowa kanta yasa tayi saurin ™arasawa ta kunna cooker gas, jikinta yana rawa bata dena kukan ba ta fara gasa hannunta, saboda hankalinta baya jikinta yasa ko zafin wutar bataji, kalmar watsattsiya yafi komai taSa mata zuciya. Sam bataji motsi ba sai ji tayi an saukar da hannunta daga wajan wutar, tayi saurin Wago fuska tana Wora jajayen idanunta akan fuskarsa. Waigawa tayi ta kalli ™ofar shigowa ganin babu kowa yasa tayi saurin dur™usawa har ™asa tana gaishe dashi."

Kallanta yake cike da mamakinta kafin ya mi™a mata hannu alamar ta bashi nata ya Wago da ita

amma taki yadda.

"""Bakya tsoron ki ™one?"" Taji ya faWa cikin tattausar muryarsa."

"""Ina son busar da hannu na ne."" Jauhar ta faWa tana fatan ya fita daga kitchen Win kafin azo a ganshi a ciki. Kallanta ya yi sosai yana son ya gano wani abun a tattare da ita. Ganin zai bawa"

kansa wahala yasa shi janye hannun yana zuba su cikin aljihunansa.

"""Aikin gidan nan ya miki yawa ke kaWai Jauhar."" Ya faWa cike da nuna kulawarsa agareta. Lumshe ido tayi tana jin muryarsa tana ratsa mata cikin kai, tunani ta shigayi ina ma ace yana da iko akanta tasan tabbas zai kaita duniyar da tafi ta yaran gidan nan, sai dai sanin hakan"

"bazai faru ba yasa tayi saurin mi™ewa dan kada tayi laifi, bata kalleshi ba kanta yana ™asa tace."

"""Zanje na ™arasa aiki."" Tana faWa ta juya zata fita Suhana da ta shigo kitchen Win ganin wanda yake"

ciki yasa ta saki murmushi tana ™arasawa wajansa.

"""Uncle Irfaan."" Tausassar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya Wauke idanuwansa daga kan Jauhar"

da yabi da kallo har ta fice yana cewa Suhana.

"""Doughter kin taso baccin?"""

"""Eh Uncle Irfaan Ina kwana?"""

"""Lafiya kalau ina sarkin rigimar gidannan Jannat?"""

Ya™are zancen yana ficewa daga kitchen Win ba tare daya tsaya jiran jin amsa daga gareta ba.

#A heart touching story #Gonar Sharri..

#Hajja ce #Billy s Fari #³an Tagwaye

"[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*"

*³AN TAGWAYE BIYAR*

(Batch C)

NA

*BILLY S FARI*

Da

*HAJJA CE*

Arewabooks@billysfari.

Page 2..

"Da sauri Jauhar ta nufi cikin Wakin tana gudan karta sakeyin wani laifin, sai dai duk da hakan sai da ta tarar da wani Sacin ran dan tana shiga ta tarar da Hajja Maimoon tana yiwa Jannat tausa da kanta sai wani shafa mata gashi take tana yi mata hira. Nan da nan Jauhar taji wani abu ya taso mata tun daga ™asan zuciyarta har saman harshenta, tsayawa kawai tayi tana kallon su kuka na shirin zuwa mata. Idan tace zuciyarta bata sosu ba tabbas tayi ™arya, tana son ganin itama ana treating Winta kamar yadda ake yiwa ´a´a sai dai bata da wannan gatan, gatan ta Waya shine ta zauna a gidan nan taci gaba da bauta kamar yadda ta taso tun tana ´ar ™aramar yarinya. Da sauri ta ™arasa wajan ta dur™usa saitin kafafun Jannat tana ™o™arin yin abinda aka umarce ta,"

jikinta yana kyarma zuciyarya na rawa tace.

"""Mommy kawo naci gaba da yi mata."" Hajja Maimoon ta watsa mata wani banzan kallo ranta a"

matukar Sace tace.

"""Menace miki akan kirana Mommy?"" Tasa hannu ta sha™u wuyan Jauhar kamar zata kasheta dan ta tsani taji itama ta kirata da Mommy ji takeyi kamar ta kasheta. Jauhar ta shiga kakarin amai tana kuma ™o™arin kwacewa amma ta kasa. Hajja Maimoon kamar zata haWiye zuciya"

"tsabar Sacin rai da yarinyar ke sakata ta, da kallon ki shiga taitayinki ta bita tana faWin."

"""Idan na sake jin wannan ™azamin bakin naki ya kuma kirana da Mommy sai na fasa shi, sannan ki tashi kije kitchen Jannat zata wainar fulawa ta man gyaWa."" Jauhar ta mike jiki babu kwari tana haWiye kukan da yake neman kwace mata. Idan tace bata nadamar zama tare da mutanan gidan nan tayi ™arya, ji takeyi gwara rayuwar da ta baro dan ko babu komai wahalar da take sha a nan bata kai tacan ba. Kafin zuwanta gidan takan samu hutu tayi bacci da sauran wasu abubuwan na rayuwarta da takeyi. Amma nan ta rasa a wane situation zata saka kanta. Sohana ce tare da Uncle Irfaan a tsaye bakin kitchen Win hakan yasa ta kasa ™arasawa, bata da matsala da Irfaan amma idan taje zata ratsa su tasan tabbas sai Sohana tayi mata abinda zai taSa mata zuwa. Gefe guda kuma tsoran kar lokacin kiranta ta kawo wainar ya yi take, idan tace bata gama ba case, idan tane farawarta kenan shime ya zama case. Irfaan yana hangota ya kirata ta isa wajan cikin sanyin jiki. Shi fa yana mamakin yadda yarinyar take gidan nan amma bata gaba bata baya kullum jiya iyau, idan ya lura ma kamar kayanta kala uku ne dan sune zagaka tana ta sakawa. Sai da ta ™araso wajan ta durkusa har kasa kanta yana kallan tiles Win"

"dake malale a wajan, ji tayi yana yiwa Sohana magana."

"""Wai babu kayan da zaku iya bawa Jauhar ne a cikin naku?"" Kallonta Sohana tayi kafin tace,"

"""Mommy ce take kyauta da tsofaffin kayanmu idan muka cire."""

"""To me yasa ba'a bata? Gida bai ™oshi ba za'a kai waje? Ko kece bakya so Jauhar?"" Yayi maganar yana kallon Jauhar da har lokacin kanta ke ™asa. Da sauri ta girgiza masa kai, ita"

"gaba Waya wannan tsare tan da yayi ba ™aramin Waga mata hankali yake yi ba, sam zuciyarya"

"taki nutsuwa a wajan bare har ta fahimci irin karamcin da Irfaan Win yake shirin yi mata. Ganin kamar uzuri takeson yi a kitchen Win yasa ya bata hanyar da zata wuce, Jauhar tami™e jiki a sanyaye ta shige cikin kitchen Win ta soma haWa kayan haWin wainar fulawa Win wacce gabaki Waya hankalinta yana kan ganin ta shiga ta fara. Shi kuma palour suka nemi waje suka zauna da Sohana suna cigaba da firarsu wanda ko mintuna goma ba'a yi ba ta ™walawa Jauhar Win da har ta soma soya wainar fulawar kira. Da sauri Jauhar tafito ta™araso wajen tana Wan sinne kai take"

cewa.

"""Gani."" Ba tare da Sohana takalleta ba tace,"

"""Ki wanko mana fruit ki kawo mana ni da Uncle."" Jin wani aikin take son bata yasa kirjin Jauhar ya shiga bugawa, ta rasa me suka Wauketa tamkar wata inji kowa ya tashi bata aiki sai ya rufe ido ya kasa hango wanda takeyi a lokacin. Duk da tasan abinda zata furta bai zama lallai a karSi"

"uzurin nata ba, duk da hakan ta daure tace,"

"""Amma Jannat nake soyawa wainar fulawa kada ta ™one, bari na Wan ™arasa sai na wanko"

"nakawo maku."" Da sauri Suhana tayi mata wani mugun kallo tace,"

"""Mene? Ni zan saki aiki ki tsaya kawomun excuse? Ke wace? har kin isa Jauhar?"""

"""Kiyi ha™uri."" Jauhar tafaWa tana juyawa tabar wajen. Suhana ta bita da tsaki ranta a Sace. Kallonta"

"Uncle Irfaan yai yace,"

"""Sohana me yasa ke bazaki tashi kije ki wanko fruit Win kisha ba idan kina ra'ayin sha? ko ni kinji"

"nace miki inada ra'ayi ne? Wai neyasa bazaku ji tausayin yarinyar nan ba Sohana? Ko kun manta kuma mata ne za'a iya yi muku duk abinda kuka yimata ko yiwa ´a´an ku?."""

"""Tufar da yawun bakinka Irfaan, in sha Allah hakan bazata faru ga yarana ba, ko ka manta ba matsayinsu Waya da ita ba? Sannan kuma bazasu taSa zama Waya ba saboda su suna da gata."" Irfan yajiyo muryar Hajja Maimoon dake sakkowa daga stairs ri™e da hannun Jannat, Hajja Maimoon na faWa ta bayansa. Juyowa yai yana kallonsu fuskarsa ba yabo ba fallasa har suka ™arasa sakkowa daga stairs Win suka ™araso cikin palourn, Jannat ta taho da sauri tana shigewa"

"jikinsa tana faWin,"

"""Uncle Irfaan welcome yaushe kazo ban sani ba?"" Sai da ya saki murmushi yana ri™e da ita yake"

"cewa,"

"""Taya zaki sani kina can kina zubawa Mommynki sangarta, kar dai nace sai yanzu kika tashi daga baccin?"" Dariya ta sakar masa tare da kallon Mommy dake zaune ta Wora ™afa Waya akan Waya tana wurgawa Irfaan Win wani mugun kallo mai cike da tsana wanda ba kowa ne zai iya"

fahimtar hakan ba.

"""Mommy wai yanzu na tashi?"" Jannat tafaWa aWan shagwaSe tana turo baki. Murmushi Mommy"

"ta saki tana cewa,"

"""˜yale Uncle kin riga kowa tashi a gidan nan ciki kuwa har dashi."" Dai-dai lokacin Jauhar tafito Wauke da wani kyakkyawan tray daya ™awatu da kalar gold sai ™yalli yakeyi da fruit aciki ta kawo gaban Suhana ta ajiye ta juya gabanta na wani irin faWuwa ganin Mommy da Jannat a wajen"

"kasancewar bata kammala aikin da suka saka ta ba,"

"""Ke!"" Taji Muryar Jannat tafaWa cikin tsiwa. Jauhar tayi saurin rufe idanuwanta Sacin rai yana sake"

"wanzuwa cikin zuciyarta,"

"""Ina wainar fulawata baki soya mun ba ko?"" Sanin Mommy na wajan, sannan Sohana ma tana"

nan yasa Jauhar sanyaya murya tace.

"""Kiyi ha™uri saura kaWan na™arasa."" Jauhar tabata amsa cikin marairaicewa tamkar mai yin"

"magana da babba lokacin datake juyowa. Kuka Jannat ta saka tana buga ™afafuwan ta nufi wajen Mommyn tasu tana cewa,"

"""Mommy zan mutu yunwa fa nake ji."" Wata uwar tsawa Mommyn ta dakawa Jauhar da tayi"

"tsaye tana kallon ikon Allah. Hajja Maimoon ranta a Sace tare da jan Jannat ajiki take cewa,"

"""Uwar me kika tsaya yi da bazaki je ki ™arasa ba yanzunnan ki kawo mata?"" Sum-sum Jauhar"

"taja ™afafuwanta tabar wajen tana share ™wallor da suka zubo mata, Mommy tayi tsaki tana cewa,"

"""Shashashar yarinya kawai, sorry my Baby yanzunan zata kawo miki kici kinji ko?"" Ta™arasa"

"zancen tana Wago fuskar Jannat Win tana share mata ™wallar da ta fara Sata mata fuska. ³ar ajiyar zuciya Irfan ya sauke tare da kallon Mommy yace,"

"""Abunda yaran nan naki sukeyi yayi yawa fa, ke Sohana ina jin ke kika sata aiki amma kina ji anayi mata faWa bazaki iya faWar ke kika sa ta ajiye aikin da aka sakata ba tayi naki?"" Yayi"

maganar yana kallon Sohana da take turo baki.

"""Look Irfaan koma meye yakamata tasan aikinta da yadda zata iya aiwatar da kowane aka sata cikin lokaci, zata zauna gidan ubansu ne tana ci da sha mai kyau taki yimusu abinda suke bu™ata? Impossible dole takoyi yin komai in time yadda ake bu™ata koda kuwa duk yaran gidan sun sakata yin wani abun."" Mamaki ya kusa kashe Irfaan jin abinda matar Yayan nashi take"

faWa. Cike da Waurewar kai na kalaman ta yake cewa.

"""Amma aikin ne naga kamar yayi mata yawa, suma mata ne is good ace suna koyar yin wasu abubuwan da kansu ba tare da anyi musu ba."" Ran Hajja Maimoon ya soma Saci da yadda"

"Irfaan ke nuna mata kamar bata iya wasu abubuwan ba, cike da isa da kuma iko take cewa."

"""Me kake so kace min ne Irfaan? Nabar yaran nawa marayun Allah su shiga kitchen saboda ita?"

Na kalli Habiby da wace fuska kenan bayan ga wacce ke aikin? Impossible wallahi dole

"kafahimci wutsiyar ra™umi tayi nesa da ™asa domin akwai tarin banbanci sosai tsakaninsu da ita."""

"""Allah ya kyauta, amma hakan ba so bane, dan na tabbata idan mahaifiyarsu na raye wannan"

"iskancin baza suyi ba kuma ta Waure musu ™ugun yin rashin mutunci."""

"Irfan yafaWa yana jin ba daWi aransa tare da mi™ewa tsaye, hakan yayi daidai da fitowar Jauhar Wauke da tray data Wora plate Win wainar fulawa akai tare da yaji agefe da kayan miya da albasa data yayyanka akai. Cike da tausayinta yabita da kallo har ta ajiye plate Win akan side table ta janyoshi zuwa gaban Jannat dake zaune kusa da Hajja Maimoon Win da kalaman Irfan Win suka gama ™ona mata zuciya ta cika tayi fam kamar zata fashe. Yana ™o™arin fita muryarta ta dakatar"

"dashi da take cewa,"

"""Me kace Irfan? Da mahaifiyarsu na raye kenan so kake ka nuna musu duk abinda nake musu"

"bana sonsu tunda bani na haifesu ba?."" Kamar ba zai waigo ba sai yaji yana so ya bata amsa, dan haka ya Wan juyo yana kallanta yadda zatafi fahimtarsa yace,"

"""Ko Waya ban faWi haka ba, yadda kike kula dasu tare da basu gata nasan zai yi wahala yaya yasamu matar da zatayi musu hakan, sannan kar hakan yasa kiri™a mantawa da cewa ´a´a mata ne su kuma gidan wani zasu je, bawai ki Waure musu ™ugun ba ana wulakanta yarinya tare da bautar da ita sai wacce a girme sun girmeta idan aka Wauke Jannat."" Sallamar Yayan nasa Alhaji Sha'aban daya shigo cikin palourn yasa yakasa ™arasa maganarsa haWe da Wan rissinar dakai yana yi masa sannu da shigowa. Kukan da yaji Hajja Maimoon tafashe dashi ya sashi kasa amsa gaisuwar Wan uwan nasa tare da ™arasawa ciki wajenta da sauri ya janyota zuwa"

"jikinsa yana kallon Irfan Win yake cewa,"

"""Irfaan meke faruwa? Me akayi take kuka haka?"" Har Irfaan ya buWe baki zaiyi magana yaji"

"Jannat na cewa,"

"""Dady Uncle ne yasa Mommy kuka wai ba itace ta haife mu ba shi yasa

Please Login or Register in order to submit comment