You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
Downloaded From https://tknovels.com.ng *_PRINCE ISHMEL_*
*OUM HAIRAN*
*300 via 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank*
*Or 9031307566: Fauziyya Tasiu Umar Opay bank*
*WhatsApp number 09013718241
🔞FOR ADULTS ONLY
*1-2*
Buɗe manyan idanunsa da suka kada daga farare zuwa jajaye yayi kan TAJ, ya sauke ajiyar zuciya tare da dashi daga kwanciyar da yake tun farkon safiya gashi har duhun magrib ya fara shiga. Hannu yasa ya ɗauke gumin da sanyi A C ya gaza tsai dashi Yace.
TAJ bansan Jenny ta buɗe zuciyata ta ɗiga jininta ba sai bayan da abubuwa suka lalace, TAJ na tafka kuskuren da bansan ta ina zan fara Please help me TAJ wlh a yanzu sonta nakeyi ba sha'awarta nake ba".......
Kallon tuhuma TAJ yayi masa tare da zama kusa dashi Yace “Tun dawowarka daga England na fahimci akwai damuwar da take cin ranka saidai tunda baka sanar dani ba banji zan tambaye ka ba PRINCE ISHMEL meye asalin abinda yake damunka yake neman taɓa lafiyarka?" Miƙewa yayi tsaye ya fara zagaya ɗakin yana dukan tsakiyar hannunsa yace “Itace TAJ Jenny ita ne damuwar da take neman zautar da ruhina" rusunawa yayi gaban Taj ya riƙo hannunsa yace “Please ka bani mafita, na rusa rayuwata da hannuna bansan Jenny rayuwata bace sai bayan na tozarta ta na koreta daga rayuwata ina zan ganta ina zan fara neman ta ina ta tafi ta barni Taj wanne hali take ciki ita da cikina dake jikinta? Don Allah ki dawo Jen wlh na yarda cikin jikinki nawa ne baki taɓa sani wani namiji ba bayan Ni am believe Jennifer ki dawo Please....."
Mamaki tsoro da tunanin Abokin nasa ya zauce yasa Taj jijjigashi yace “Eshmel calm down mana wacece ita meye yasa ta zama damuwarka ka haƙura ka manta da ita mana haba don Allah nawa ka manta kafinta sai itane zata gagara mantuwa Ishmel wai itan me take dashi da sauran mata basu dashi meye yasa ka saki zuciyarka har tayi maka saƙa to wai ma a ina take da kakejin ciwonta yake damunka mace ko a daular Hindu take in mukaso sai mun amfana da ita itan me isa ka yarda ta baka ciwon kai?"
Komawa yayi ya zauna yana jan ajiyar zuciya me ƙarfi yace ba kamar kowacce mace take ba Ni nake faɗa maka wannan wlh tafisu komai duk da kasancewarta ba musulma ba inajinta saman mata musulmi na duniya gabaɗaya babban tashin hankalina abinda zata faɗa a gaba game da Musulmi bazai zama mai daɗi ba domin ba daɗin taji ba Taj nine musulmi ɗaya tal data fara sani a rayuwarta na shiga rayuwarta tun bataso har ta haƙura tasoni ta bani kanta don mafitar kaina badon tata ba Taj bantaɓa mu'amalantar Jenny ranta naso ba amma takan danne tayimin duk wani abu da zaisa na samu nutsuwa duk da wahalar da take sha wajen sex dani bata guduna da na nuna mata alama take kawo kanta. Amma hakan baisa na ɗaga mata ƙafa ba kan kuskure ɗaya tak da tayimin shima don kare lafiyarta ne nasani badon ta baƙantamin ba"
Taɓa ƙofar da aka fara ne ya sanyashi tashi ya shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa Taj ne ya sanar da Bafaden yaje yace da Mai martaba gasu nan. Hakance ta faru bayan ya fito ya shirya cikin shigarsa ta alfarma kasancewarsa cikakken Prince mai cikakken iko tunda ya fito ake watsa masa fure ana zuba masa kirari, tabbas isa Izza da iko da Ɗagawa da Miskilanci ya gama ƙarewa wajen Yarima Isma'il bayada sauƙi kuma baya shayin murje uban kowa, wannan yasa duk sanda ya dawo hutu wannan babbar masarauta take matuƙar shiga taitayinta domin Yanzun nan zaisa ayi maka azabar da a wannan rana tsaf zaka roƙi Allah ya ɗauki rayuwarka ka huta.
Kai tsaye gurin da yaga an parker manyan motocin suka nufa shida Taj ɗaya cikin kafuran motor ɗin suka shiga daidai lokacin aka bada umarnin tafiya suka sulali hanya cikin nutsuwa ake tafiyar jerin gwanon motocin dukka farare sunata ɗaukar idanun talakawa da haka suka isa wani babban guri sukayi parking kowa ya fito amma banda Isma'il yana zaune ya lula duniyar gajimare tunano farkon haɗuwarsa da Jenny kawai yakeyi lokaci zuwa lokaci yana fidda iska me huci.
Shidai Taj fita yayi don wakilci kamar yanda ya umarce shi gidan marayu ne musamman da Mai Martaba Ƙassim ya gina tun shekara goma sha biyar baya to yau ake aurar da wasu yammata cikin marayun shine dalilin zuwansu don halartar ɗaurin auren da King bazai samu halarta ba.
Sun ɗauki a ƙalla awanni uku a wannan gidan marayu sannan ne suka sami damar juyawa domin komawa gida, tunda suka taho kansa ke cikin cinyarsa har suka isa gida a haka yake saida Taj ya taɓashi sannan ya fita a wahalce ya nufi sashinsa an gyara masa shi kawai faɗawa yayi gadon tare da jan bargo ya ƙudundune yana rawar sanyi komai ya ƙwace masa tabbas dole cikin satin nan ya sake komawa England a karo na ba adadi ko Allah zaisa ya sami wani Information game da Jen tabbas ya haƙiƙance zuwa yanzu haƙƙin marainiyar Allah ne ya fara bibiyar rayuwarsa.
Gabansa ne ya faɗi wasu kalmominta suka fara dawo masa lokacin da yake fatali da kayanta bayan ya gama zane ta da belt ta zuba masa idanunta dake tsiyayar da hawaye tace “Banida kowa a duniya daya wucce ka kowa na shine ya damƙani a hannunka bayan ya tabbatar min kai Musulmi ne kuma musulmi basa zalunci Eshmel ka tabbatar min da cewa Musulmi basa zalunci kamar yanda Kenn ya sanar dani ta hanyar jin ƙai na da nunamin tausayinka gareni.
Me kake tunani game da gobe na bayan ka koreni daga sashinka a lokacin da nake tsananin buƙatar kulawarka Ishmel farin cikina ya ta'allaka da naka ne komai damuwar da nake ciki burina na ganka cikin farin ciki saboda ina maka kallon uwa uba kuma ɗan uwa sannan ina kallonka kallo irin na miji domin abinda na daɗe ina tanadin saboda miji na sallama shi gareka burika kawai naga ka tsarkaka ka daina mu'amala da kowacce mace Ishmel saboda Future naka ne saboda kaine duk da cewa hakan baisa nayi nasara ba amma ban fasa baka kaina a duk sanda ka buƙata ba nidai inaji a raina ko ba komi ka rage kula mata.
Ishmel karka wofintar dani a daidai wannan lokacin wlh dani da babynka muna tsananin buƙatarka babynka baya gajiya da ɗuminka idan ka barni na tafi ya zanyi...."
Duk da ƙarfin zuciyarsa bai hana shi fashewa da wani marayan kuka na tausayin kai ba kora na ba adadi da yake ƙalubalantar muguwar zuciyarsa mara tagomashin ɗigon tausayi a cikinta wai meye yasa ne anya kuwa shi mutum ne?" Sake ƙanƙame ƙirjinsa da yake masa zafi yayi ya rushe da kuka me sauti yana faɗin Jenn! Please Jennifer help me am dead in kika ƙi dawowa gareni wlh zan mutu babynmu zai taso irin rayuwar da kika taso Jenn meye yasa kika sallama min komai Ni na kasa sallama miki farin ciki ɗaya, kawai ɗaya tal. Da nayi miki da ba anan muke ba yanzu ina zan ganki Jenn don Allah ki tausayamin kizo gareni ko cikin mafarki ne zakiga na canza ba Eshmel ɗin da kika sani ba.
Nasan yanzu kin haifa min babyna me kama dani ki kawo shi ya ganni na gansa inason King don Allah Jenn ki yafe min nasan zuciyarki batada juriya game dani ƙarya nake bazan kasheki ba ki yarda dani daga yau zan fara faɗawa kowa nawa Inada Abraham ɗana ne na cikina daga jikin....
Rufe masa bakin da yaji anyi ne ya sanyashi buɗe ƙananun idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur ya zuba su kan Queen Wato mahaifiyarsa sai kawai ya tashi ya faɗa jikinta ya rungumeta yace “Please Mom kice ta dawo gareni wlh tallahi inasonta inason fetus ɗina kar ta bari ya taso da baƙin cikina Mom zan mutu Mom zuciyata zata fashe na kasa jurewa Jenn Mom Jenifer nake buƙata ita nakeson rayuwa da ita kiji ƙaina ki tausayamin Mom ita ce rayuwata tayimin komai ta sallama min komai ko zata sha wahala indai zanyi farin ciki to bata ganin wahalar burinta farin cikina Mom please kice wani abu mana ko kema kin daina sona ne...."
Numfashi ta sauke me nauyi ita dama tasan bayan tia akwai wata caca tun dawowar Ismail daga England ta fahimci akwai wani abu dake cin ransa amma dake miskili ne yaja bakinsa ya kulle sai rama yakeyi sai yau da abin yafi ƙarfin cikinsa sannan ne ya fita batare daya shirya fitarwa ba.
Miƙewa tayi da nufin ficewa domin kanta ya kulle tunanin ta ya kasa hasaso mata kalmar da zata furta akan wannan rikitaccen al'amari da Isma'il yazo mata dashi lamarin ya girmi tunaninta dole sai ta nutsu zata samu abin faɗa.
Ji tayi ya riƙo hannunta ta ɗago ta zuba idanunta cikin nasa ba ƙaramin firgita tayi da saƙon data gani a cikin idanunsa ba ta rikeshi da sauri tace.
“Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Isma'il kai meye hakan...." Kafin ta rufe bakinta yakai ƙasa ta fasa ƙara tana cewa jama'a ku kawo min ɗauki Yarima kai kuma soyayya ce ƙaddararka jama'a ko gidan babu kowa ne a taimaka min zan rasa shi akan mace....."
Tuni masu hidimar sashin suka cika parlourn hankalin kowa ya tashi domin iyakar saninsu Yariman nasu ba ma'abocin yawan lalura bane hassalima bai taɓa shiga irin wannan yanayin ba.
Fita akai dashi domin sadashi da babban asibitin dake cikin masarautar likitoci biyar ne a kansa domin ceton rayuwarsa, daƙyar suka samu ya dawo hayyaci Dr Nazar ya fita yana sharce gumi ya isa ga Queen dake zaune cikin damuwa yace.
“Allah ya taimake ki duk abinda ya damu Yarima gsky me girmane domin kuwa binciken farko ya nuna mana abun ya daɗe yana cin zuciyarsa sannan yana tsananin soyuwa ga abin wanda bazai iya cire shi a ransa ba kuma bazai iya control tamper ɗinsa akansa ba Queen indai zai yiwu a kusantashi da abin da yake muradi ko kuma a bashi madadi da zau cire masa kewar wancan saboda lallai zuciyarsa tana barazanar kamuwa da mugun ciwon da zai iya kaishi ƙarshen rayuwa!....."
Cikin ɗimuwa Queen ta kama kuka tana cewa da wacce ke kusa da ita “Kinji ko? Kinji abinda nake gudu ko Janah yanzu ina zan iya nemowa Baban karuwar da shi kansa bai san inda zai nemota ba, shiyasa tunda na fuskanci take taken Baban yarone miskili amma fitinanne bazai iya kare kansa daga mata ba, naketa ƙoƙarin naga yayi aure amma yaƙi kuma King ya Goya masa baya yanzu wa gari ya waya bamu ba? Janah yaje yayi zaman dadironsa da karuwa me tayi masa me tayi masa su suka sani wai abin takaicin har Ni Baban yake faɗawa yanason fetus ɗinsa yanzu yasan ma ta haihu ta kawo masa Abraham kar ya taso a irin rayuwar data taso!"
Dafata Janah tayi tace “Kiyi haƙuri yaya sharrin ƙadangarun bariki Prince ya haɗu dashi yanzu addu'a za'a dage masa da ita kawai Allah ya ƙwatoshi" kuka sosai takeyi tana cewa yanzu Ishaq dake basa ɗasawa da King ba gashi ƙalau yake zaune ba amma Isma'il shine shan giya shine neman mata yanzu gashi garin jaye jayensa ya janyowa kansa tsiya baki Janah taci gaba da bata har ta samu tayi shiru.
Zuwan King ne ya sanyasu tafiya bayan likita yayi masa bayanin komai sosai King ya shiga damuwa da jin zuciyar shalelen nasa tana neman taɓuwa ya zubansa idanu lokacin da yake buɗe nasa idon ya saukesu akan King matsawa yayi ya kamo hannunsa ya zauna kusa dashi Yace “Baban meye yasa ka cunkusawa zuciyarka damuwa da take neman ganin bayan numfashinka haka meye ya dame ka a duniya da kakasa maganceshi kuma ka kasa faɗa mana mu tayaka da addu'ar samun maganinsa?"
Kawar da kai yayi gefe tare da zame hannunsa daga na King, murmushi yayi ya miƙe yace “Ok na fahimta kayi hƙr komai yayi tsanani maganinsa Allah zamu tayaka da addu'a" da wannan shima King ya fice basu jima ba suka fito da likitan yan cike cikensa yayi ya bawa wani Bafade ya fita bai jima ba ya dawo da magungunan daidai lokacin shima Ishmel ya gama shiryawa ya riga su ficewa ma daga ɗakin ya nufi cikin gidan sarautar wani ɓangare ya nufa da yakan zauna don Hutawa da bawa zuciyarsa damar yin tunanin abubuwa shuɗaɗɗu masu muhimmanci a rayuwarsa ji yayi an dafashi ya sauke numfashi ƙamshin turaren kawai ya fallasa masa asirin wanda yake tsaye a kansa ƙaninsa ne Ishaq zama yayi kusa dashi Yace “Sorry Bro sai yanzu nake samun labari ashe Bakada lafiya amma ya jikin?" Lumshe idanunsa yayi Taj ya amsa da cewa “To da sauƙi kenan zaace kawai yana neman kashe kansa akan wata kafura saboda rashin mafaɗi....."
A fusace ya ɗagansa hannu ya miƙe yayi gaba abinsa duk maganar da sukeyi masa bai kulasu ba saida suka isa tsakiyar ɗakin baccin nasa sannan ya juyo ya kafesa da ido yace “Yafi sauƙi ka ɗaga hannunka ka kwaɗamin mari da ka aibata Jenn a gabana kai ko a bayan idona bazan yafe maka ba" ɗagowa Taj yayi da sauri cikin mugun mamaki karon farko da wani mummunan furuci ya shiga tsakaninsu kenan taɓ dole ya iya takunsa aminin nasa kuma ubangidansa da gaske yakeyi.
Juyawa yayi ya fice ya riga ya sani a yau dai ba sake kulashi Ishmel zaiyi ba hakan ce ta bashi ƙwarin gwiwar ficewa to shima bathroom ya shiga yayi wanka yayi sallolinsa ya ɗauki wata zazzafar Giya ƙaramar kwalba ya ɓalle ya shanye wai ko zaiji sauƙin abinda yakeji a ransa. To yadaiyi bacci shima me cike da mafarkai masu tada masa da hankali, zabura yayi ya miƙe baitaɓa mafarkin da ya nemi tafiya da ransa ba saboda firgici kamar wannan ajiyar zuciya kawai yake saki dafe da kansa da yake juya masa a haka ne kula da abincinsa ya shigo ya ishe shi ya rusuna yace “Abinci ya kammala Allah ya taimakeka ko da wani abu da kake buƙata?" A zahiri yana bukatar wani abu amma nauyin da harshensa yayi masa yasashi ɗagansa hannu miƙewa yayi ya fice shi kuma ya sake gyara kwanciya ya zubawa pop na ɗakin idanu abubuwa suna dawo masa kamar yanzu suke faruwa kamar bazasu ƙare ba yau gashi cikin bala'in da bazai taɓa iya fitar da kansa ba. Itace maganin ita kuma tayi masa nisa.
Zuffa ya share ya lumshe idanunsa farkon haɗuwarsa da ita tana dawo masa sabuwa kamar ya kunna video yana kallo.......
*_PRINCE ISHMEL_*
*OUM HAIRAN*
*500 via 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank*
*Or 9031307566: Fauziyya Tasiu Umar Opay bank*
*WhatsApp number 09013718241 / 09031307566*
🔞FOR ADULTS ONLY
3-4
ENGLAND
BIRMINGHAM State Yammacin ranar Lahadi ne mafiya yawan mutanen dake zaune a unguwar ta Alum Rock suna cikin gidajensu ne saboda yau ɗin ta kasance rana ce ta hutu ga daukacin ma'aikata wadda aka ware ta don samun damar zuwa gurin ibada.
Haka yake ga Jennifer wadda tun sanyin safiya ta shirya ta tabi grave na Mahaifiyarta Helina nan ne ta mayar gurin ibadarta a nan take bautar ta tanajin a ranta bata da wani abin bauta daya wucce mahaifiyarta.
Tsugunne take gaban kabarin tana rera wasu yan baitoci cikin sahihin turancinta na jini domin kuwa cikakkiyar baturiyar England ce kasancewar mahaifiyarta cikakkiyar yar ƙasa.
Miƙewa tayi tana share hawaye ta matsa daidai ƙirjin Mahaifiyar Tata ta kwanta saman tiles ɗin tana kuka me tsuma zuciya tana cewa “Miss ur Mom na rasa komai saboda rashinki tare dani tunda ke kinƙi dawowa gareni ki rokamin Yessu ya dawomin da ɗan uwana Kenny gareni rayuwar kaɗaici tayimin wahala Harvest ne yake daukemin kewa inason mutum a kusa dani Mom please kar kice a'a yau ma kinji!"
Murmushi tayi me ɗauke da hawaye tace “Yap naji a jikina kin amsa zaki faɗawa Masihu damuwata zan barki kamar yanda nayi miki alƙawari bazan dawo ba sai Sunday me kikeso na taho miki dashi?" Wata leda dake ajiye a gefe ta buɗe ta ɗauko wata flower me kyau ta saƙala saman wani kwando dake saman grave ɗin ta mike tana hawaye tana ja da baya tana ɗagawa kabarin mahaifiyar tata hannu.
Ji tayi ta daki wani abu ta baya tayi saurin juyawa tana faɗin “Ohh God bless sorry...." Wani tsalle tayi ta maƙalƙale mutumin data gani a tsaye tana shinshina shi ta tura hannunta cikin sumarsa ta fashe da kuka tace “Miss you bro ka tafi ka barni long time why?" Shima shigar da ita yayi jikinsa yace “Miss ur My love" kissing kuncinta yayi yaja hannunta ta zame ta sake tsugunnawa gaban grave ɗin tace “Double tnks My heart na daɗe ina faɗawa Masihu bai amsa ba sai gashi kina faɗa ya amsa na gode ki huta" tashi tayi ta sauke idanunta kan mutumin dake gefe da tunda ta juyo ta ganshi idanunsa a kanta amma ba tashi takeyi ba ta ɗan uwanta takeyi.
Har yanzu idanunsa akanta yake tare suka sauke ajiyar zuciya lokacin da Kenn ya kama hannunta ya kamo na Ishmel ya haɗasu yace “Friend ga love sis da ka daɗe kanajin labarinta inasonta fiye da yanda nakeson kaina itane rayuwata kuma amanata" jinjina kai yayi tare da ɗaga ɗayan hannunsa ya saka a bayanta ya janyota ya rungume wannan ba wani abu bane ga al'ada ta Bature itan ma bata ɗauke shi komai ba saidai banda Ishmel da ya tsinci duniyarsa da ɗaukar wani shorck da baitaɓa jin irinsa a rayuwarsa ba musamman lokacin daya ɗora haɓarsa saman gyararriyar sumarta me nauyi baƙa wulik kwanciya ta sakeyi a jikinsa ɗumin hannunsa daya riƙe ƙugunta yana zaga ilahirin jikinta.
Fuskantar bashi da niyyar sakinta ne yasata motsawa sai lokacin ya ankara da riƙon da yayi mata ya wucce seconds na al'ada ya sake ta tare da motsa bakinsa yace “Fine girl you are welcome!" Ƙasa tayi da kanta tace “Thank your" komawa tayi gurin ɗan uwanta ta kama hannunsa tana cewa “Ka manta dani 3 years Bro Meye yasa?" Shafa sumarsa yayi yaja hannunta suka fara fita daga maƙabartar yana cewa “Zan baki labari don kene My love alliance na Mom bazai riƙemu ba shiyasa na tafi nake karatuna kuma ina nema maki mafitar rayuwarki" kwantar da kanta tayi a kafaɗar sa har suka fita suka fara takawa kasancewar ba wani dogon nisa garesu ba.
Basu ba daɗe ba suka je ita ta buɗe musu gidan suka shiga babban gidane ginin turawa daya wadatu da bishiyoyi masu kyau sunyi covering gidan gabaɗaya.
Wata kofa ta buɗe suka shiga wani sihirtaccen ƙamshi ya daki hancinsu suka zube a kujera juice ta ɗauko musu da ruwa sai Snack ta ajiyewa baƙon a wani center table dake gabansa shima Kenn ta aje masa nasa ta miƙe da gudu ta haura sama ta buɗe wani ɗaki ta shiga ta ɗauko wata ƙatuwar Teddy ta dawo ta zauna tana kallon Teddyn nace “What cry Abraham why?" Ba Kenn ba hatta Ishmel abin ya bashi nishaɗi ya dubi Kenn daya daɗe da lura gabaɗaya hankalin Ishmel yana kan sistern nashi yace “Waye Haka?" Shafa kansa yayi yace “She name is My Dad" jinjina kai yayi yace “Ok yana ina ko shima ya mutu?" Girgiza kai yayi yanayin mode na face nasa ya canza ya miƙe yana cewa “Tun ina 11 years Jenn tana 1 year ya tafi ya barmu bai kuma waiwayarmu ba Mom ta hanamu nemansa gashi itama 4 years kenan da mutuwanta I think kamar ɗan ƙasarku ne Nigeria"
Bai kuma cewa komai ba Kenn ya haura sama shikam duk motsin da yarinyar zatayi idanunsa na kanta duk iskancinsa baya sha'awar yara ƙanana amma fah ya kwaɗaitu da wannan yarinya da bata wucce 18 years ba gabaɗaya batafi sa'ar ƙanwarsa Princess Jiddarh ba.
Yarinyar ta ƙeru sharp ɗinta ya fita ga ta tara kayan daɗi gata kalar da ya jima yana marari kalar Adamu ita ba fara ba kuma baka taɓa kiranta baƙa ba. Yamutsa gashin kansa yayi tare da lumshe idanunsa yana hasaso irin daɗin dake ƙunshe a boye jikin wannan tahalika tabbas shikam yaga guri zai gwada sa'arsa yasan akwai tarin damuwa ta kuɗi a kan Kenn kuma ya sani Kenn yana masifar son kuɗi fiye da komi a duniya domin Yanzun ma a cikin buƙatarsu yake, zaiyi amfani da damar yagani ko zai dace ya bashi babyn kawai ta koma gidansa rayuwarta anan da hatsari duk da cewa ƙasar turawa ba kamar ƙasashen Africa ba akwai tsoro sannan babu ruwan kowa da rayuwar kowa dole tana da yancin sai wanda ta amince zata bawa dama a kanta wannan doka ce idan kuwa tsautsayi yasa ka haike mata batare data amince ba to shakka babu zaka iya rasa mazantakarka matsawar takai kararka hukumar kare haƙƙin mata.
Fitowar Kenn ne yasashi miƙewa sukayi mata sallama suka fita da alƙawarin Kenn zai dawo su kwana tare suna fita ta tashi ta fara gyara parlourn bayan ta gama ta koma ɗakinta taci gaba da wasanta da Teddys ɗinta saida taji yunwa sannan ta shiga kitchen ta ɗauko waken gongoni da kifi shima na gongoni ta haɗasu guri guda ta ɗauko bread ta fara ci tana korawa da Youghurt saida ta ƙoshi ta kunna kallo tana zaune tana kallon wani korian Film bayan shuɗewar few Hours tayi wanka tana zaune daga ita sai wani wando iya cinya da wata riga bata rufe cibiyar ta ba ta ɗaure gashinta da wani band baƙi tayi kyau sosai abinka da ruwa biyu.
Chat takeyi da abokan karatunta rabin hankalinta akan kallon musamman lokacin da taga star na Film ɗin ya turmushe yarinyar cikin Film ɗin yanata lashe mata jiki gabaɗaya sai taji mode nata ya canza ta lafe a kujerar tanajin wani yanayi da ta kasa gane wanne iri ne bata rarrabewa Ita dai kawai tasan ya ƴan kwanakin nan indai zataga namiji yana lalubar mace sai taji duniyar ta ta hautsina tana zaune a haka taji an buɗe ƙofar an shigo ta ɗago idanunta dake lumshewa ta saukesu kan me shigowar Kenn ne still da abokinsa Ishmel yanayin Kenn ne ya bayyana mata akwai abinda yake damunsa.
Bai bata damar gama tunani ba ya matsa ya ɗagota yace “My love kin yarda dani?" Jinjina kai tayi tana lafewa a jikinsa yace “Ok kin amince Ni inasonki fiye da kaina?" Sake jinjina kai tayi tace “Amma kana tafiya ka barni da kewa kaɗaici yana damuna ina feelings me ɗauke mini kewa" murmushi yayi ya samu daidai gaɓar magana yace “Alr Yanzun zan kuma doguwar tafi zuwa American na samu wata contract ne Jenn cikin contract ɗin babu travel dole saidai ka zauna ka gama kuma at 5 years zanyi acan shine na yanke shawarar damƙaki hannun Abokina Ishmel...."
Da sauri ta ɗago idanunta ya ciko da ruwa tace “No Please Bro ka barni anan zanci gaba da rayuwa Ni kaɗai" girgiza mata kai yayi yace “Me kikejin tsoro Eshmel He is Muslim sunada amana addininsu ya hana su zalunci zai riƙeki kamar Ni ki saki jikinki dashi replacing nawa ne a gurinki zakiji daɗin rayuwa dashi fiye dani domin shi zai kawar miki da kowacce irin feel My sis please last chance kinji"
Rungumeshi tayi tace “Yeah Bro I trust to you Mom ta daɗe tana faɗamin babu mutane masu tausayi da Imani da gudun cutar da na ƙasansu kamar musulmi na yarda am believe bazai cutar dani ba ko?" Ta dubi Ishmel dake tsaye rungume da hannu soyayyar wa da ƙanwar tasa tana burgeshi tabbas zaiyi bakin ƙoƙari yaga ya kare haƙƙin addininsa a wajen kafuran nan duk da cewa yasan ta wani fannin bazai iya ba bashi da juriya a lamarin mace.
Miƙa mata hannu yayi ta saki Kenn ta nufoshi tana zuwa maimakon nufinsa na ta shiga jikinsa sai yaga ta rusuna ta dafa ƙafarsa tace “Na rantse da Allan Yessu Al Masihu zanyi maka biyayya fiye da wacce zanyiwa Bro domin shi dole nane kaikam jin ƙai ne na addininku yasa ka shigo rayuwata zanso farin cikinka koda zai zama ƙuncina a ɓoye dukkan abinda kazomin dashi zan karɓeshi komi wahalarsa saidai ina maka tuni da nauyin amana Ni banida kowa a yanzu duk duniya sai kai banida gatan daya wucce ka I promise zaka barni da ƴanci na bazaka taɓa yimin kallon baiwa ba?"
Maganar ta gigitashi baisan sanda yace “Baiwa? Not