google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da rashin sanin dalilinta nayin hakan Amma koma dai meyene ya fahimta batason Kamal yasani...

Shima hakanan yasamu kansa da sakin murmushin yaqe na Dole Yana cewa,

Ok Allah ya qaro sauqi.

Kallon saheeb da zuciya tagama kashesa yayi ta gefen Ido yaga yanda kafeta da idanuwansa dasukai mugun kadawa sabd 6acin Rai yayi saurin dafasa cikin qasa qasa da murya yace,

Please danne 6acin ranka and Let's go from here sbd wannan qanin naka karya fahimci wani Abu sbd inaga bai kamata wani yasan komaiba gameda wannan alamarin harsai mun gama bincike mun San komai.

Rintse idanuwa yayi cikin wani irin zafin zuciya kafin ya bu'de ya saukesu akanta
Ta qaqalo wani hadadden murmushi ta sakar Masa gabanta na dagargajewa cikin zuciyarta tana cewa,

Anano kin mutu...

Juyawa yayi yabar room 'din zayyan yabi bayansa Dan kuwa tagama kwashesu da mugun mamaki...

Suna fita ta juyo ta kalli Kamal ta juya zata shige toilet Dan tattaro nutsuwa kozata samu ta iya fuskantar Kamal din shima taji ya fixgota da qarfi ahasale tareda jefata gado saura qiris ta fa'da Kan abdul tayi saurin 'dagowa ta kallesa cikin zafin zuciya ya nunata da yatsa cikin tsananin masifa yace,

What was that bastard trying to do.....

Bansaniba"""""ta fa'da da qarfi ya shaqota da qarfi Yana cewa,

Ohhh wato har idonki ya bu'de kinfara mayarmin da magana you ingreat bitch,
Tell me what is going on between you two idiots,
Are you having a secret affa....

Qwacewa tayi da qarfi tana shafa wuyanta tana tari sbd ba qaramar shaqa yayi mataba.

Wani mugun kallo take binsa dashi na tsana da takaici tace,

He is far morethan you tako Ina Dan haka ba laifi bane Dan nayi mu'amala dashiba sbd yafika sanin darajar mace.....

Kanta yayo tayi saurin kaucewa zata gudu ya damqo gashinta dake cikin 'dankwali cikin azaba tafara qoqarin qwacewa tana cewa,

Kaga babban kalar banbancinka dashi sbd he will never hurt a woman and....

Shut up bitch,,,,barima nafada Miki wani Abu dabaki saniba
Babu shegen daya Isa yasoki idan baniba Dan kuwa duk Wanda yayi gangancin hakan wallahi sainayi Masa mummunan illarda harke saita shafa,
Ke tawace nikadai
Bazaki so kowaba saini
Duk Wanda kikayi gangancin so saikinyi Dana sani...when I said kowa
I mean kowa ciki harda kwartonki saheeb...

Wurgi yayi da ita yafice afusace kamar zai daki iska..

Wani irin kuka tasaki ahankali zuciyarta na tsananin quna,

Kuka take sosai Dan kuwa tasan tana cikin masifar dabatasan yazata fidda kantaba daga taimako Abu yazamar Mata qaddara mummuna Dan kuwa dayanzu tana tareda iyayenta tana cigaba da karatu Amma qadda ta jefota cikin wa'innan mutanen Daba imani ko tausayi a zuciyarsu ga Kamal nason zamar Mata wani bala'in na musamman.

Adaren kwana tayi kukan tausayin rayuwarta data juye ta yamutse Mata takeyi Dan kuwa shawarar guduwa takeyi Amma abin mamakinta 6angare 'daya na zuciyarta jitake bazata iya tafiyaba su Kamal su cutatar da saheeb Dan kuwa jitake zuciyarta kamar bazata iya daukar hakanba...

Guraren asuba ta farka a firgice sbd mafarkin datayi da mahaifiyar abdulshakur duk da har cikin mafarkin bataga fuskarta Abu 'daya ta ringa maimaita Mata,,,,

Ke haske ce arayuwar masoyana abdulshakurs,,,,
Ina roqonki daki tsaya aduk inda kike ki Hana cuta kamar yanda Kika Hana a hallakani da cikina har Allah yabani ikon haihuwarsa,,,,,
Anano ke haskece kizamo jaruma Mai tsayawa akan maqiyanki.........

Dafe goshinta tayi gabanta na fa'duwa sbd kanta gabaki daya a qulle yake musamman Yanzu datayi wannan mafarkin...

Toilet tashiga tayo alwala tazo tayi sallah ta roqi Allah yabata sa'a da qwarin gwiwa akan wannan yaqin dazata fara Dan kuwa tayanke shawarar tsaya tsayin daka akan bazata ta6a Bari su mum asee su ta6a saheeb ba to Amma why all the risks..?ta tambayi kanta tana qara daga hannu sama tace,

Ya Allah karka Bari zuciyata takamu dason.....shiru tayi sbd tsananta fa'duwa da gabanta yayi Dan kuwa kaman she's too late..


Qarfe goma na safe aka sallamesu suka shigo napep suka dawo gida tun a gate tasan da tsaron gidan ya ninku cikin ranta tace,

Duk abanza Dan kuwa bala'in na ciki anrufe gidan dashi Amma gaf nake da hanka'dosu kodan na nemawa kaina yanci daga wulaqancin Kamal.

Suna shiga harabar gidan Yana fitowa zai shiga mota tareda abba..
Ha'duwa idanuwansu sukayi tayi saurin 'dauke Kai tana gaida Abba dayake tambayar gwaggo jiki abdulshakur duk da wani saninsa sosai yayiba.

Tunda tadawo asibiti saidatayi kwana biyar bataje aiki bangaren mum asee ba Sai yau da mum din ta Aiko kiranta zata aiketa
ta shirya cikin doguwar rigar atampa ta fito ta nufi part din

Ba kowa apalon saita nufi bedroom'din mum asee Kai tsaye Dan Jin aiken...

Zaune take bakin gado Kamal na zaune a sofa fuskarnan a ha'de.

Akwai wasu mahimman takardu dasuke 'daukeda bayanin wani shahararen number one wanted criminals gang da akai shekaru ana fafutukar son cafkewa Amma ba'a samu dama ba Sai yanxu kuma takardun da information na komai akan case din Yana hannun saheeb cikin laptop dinsa ya adana komai......

Tsaki yaja cikin takaici yace,

Toni meye nawa da wannan shirmen.....

Cikin baqin ciki da tsawa ta katsesa da cewa,

Allah ya tsinewa rashin haquri da daqiqanci tareda toshewar qwaqwalwa irin taka Kamal Dan wlh ni gani nake ba cikina kafitoba......

Please karfi fara mum coz yanzu zuciyata akusa take bazan iya juran wa'innan zantukan nakiba....

A hasale yakurah data fito toilet din mum tace,

Kaidai kaji haushi Kamal Yaya Kamal kullum saika.....

Shut up mumu'''''ya katseta Yana cikin zafin rai Dan tarigada tagama rainasa.

Cikin qunar Rai mum asee tace,

To jakai idan Kun gama saina cigaba da bayani tunda narigada na haifi sokaye kowa na haihuwar abin arziki Banda ni.

Kamal sonake kaje ka Sato Mana laptop dinsa da takardun yanda zamu Samar Masa da muguwar matsala gurin aikinsa Dan kuwa ba tantama rufesa zasu.....

No mum""""yafada yana matsowa kusada ita sbd wani mugun tunani daya shigesa..

Bazamu dauke takardunba information din komai na operation din zamu watsa a internet kafin gobe ya baza duniya Kuma kafin goben sojoji ba adadi zasu rasa rayuwarsu ta dalilin farmakin ba zata da gang din zasu kawo musu idan suka samu information din
Fadamin me kike tunanin zai samu saheeb da shikadai information din komai yake hannunsa after all da account dinsa zamu tura....
The poor bastard will end up in hell....

Da wani irin mamaki mum asee ke kallonsa kafin tace,

Nasan jinina dake yawo ajikinka bazai zamo aikin banzaba
Said yanzu nasan na haifi abin qwarai...
Murmushin farin ciki tasaki tana qara jinjina alamarin Dan kuwa ba tantama saheeb bazai gani da kyauba agurin aikinsa barema yanda hukuncin sojoji yake da mummunan tsanani.


Baya takoma tareda sharce gumin daya gama jiqata ga bugawa da zuciyarta takeyi da sauri,,,,
Bazan iya da mutanen Nan ba sbd abubuwansu sun fara wuce qwaqwalwata.

Juyawa tayi da sauri hartana tuntu6e tabar sashen.
Tana zuwa daki takasa zama takasa tsayi itadai gwaggo Banda harara ba abinda take binta dashi sbd ganin kamar hankali haryanzu baigama shigartaba.


Qarfe biyar motocinsa suka shigo gidan ya nufi part dinsa,
A Palo kurtun soldier dake biyedashi daukeda jakar takardunsa da laptop ya ajiye tareda juyawa ya fice ya turo qofar.
bedroom dinsa ya nufa Kai tsaye ya tube tareda fadawa toilet yayo wanka Yafito daureda towel ya shirya cikin black trousers da ash shirt data fito da qaqqarfan muscles dinsa na majiya qarfin soldiers ya fito Palo ya dauko robar power horse a fridge yasha ya dauki jakar yakai bedroom dinsa yafito yanufi masallaci sbd Kiran magrib da aka fara.


Ana sallar magrib ta fito daga part dinsu mum asee jikinta duk a sanyaye sbd har lokacin batasan abinyiba Dan maganar gskia batasan yazatayiba ta Hana wannan Shirin faruwa.

Harabar gidan ba kowa duk sun shiga masallaci soldiers biyu ne kawai zaune agurin gate Suma Dan dai christians ne...

Part din saheeb din takalla Sai kuwa taga kamar wani yashige qofar palon tareda rufowa..

Binsa tayi cikin rashin sanin abinyi ta murda kofar saitaji yasaka key taciki gabanta ya yanke ya Fadi da sauri ta zagaya ta qofar palonsu tafada bu'de qofar kicin dinsa taji arufe taduba bataga key ajikiba ta nufi 'daki da sauri gurin gwaggo saita tarar tana sallah,,,

Dafe goshinta tayi cikin damuwa kafin tahau nemansa cikin sauri...

Jitake kamar zata zauce haka ta birkita dakin kafin idanuwanta suka sauka akan qaramar fridge din dakin da sauri ta wartosa ta fito.

Daqyar ta bu'de qofar tashiga kicin din cikin sanda tashigo palon tana sako qafa palon taji anbude qofar palon anshigo
Zayyan ne agaba Kuma akanta idanuwansa suka fara sauka tayi saurin komawa baya da sauri gabanta na fa'duwa da tsanani.

Sake kallon qofar zayyan yayi Yana son tabbarda ita yagani din Amma baisake ganintaba.

Saheeb kuwa samun guri yayi ya zauna Yana fara korowa zayyan bayanin gobe tun qarfe 6 zasu bar gari.

Sai bayan dasukai sallar Isha kafin zayyan ya wuce gida shikuma yashiga gurinsu mum yaci abinci ka'dan yadawo yayi Shirin kwanciya ya kwanta.


Anano kuwa jitayi hankalinta Yana tashi gabanta na tsananta fa'duwa tayi sallah daqyar tareda yiwa saheeb addua Dan kuwa tayi alqawarin itace kawai abinda zata iya yimasa daga yanzu ta Kama kanta da abinda ba ruwanta.




Qarfe biyar shida saura duk yagama shirinsa tsaf cikin wandon uniform dinsa da takalmansa baisaka rigarba farar shirt yasaka Yana cikin 'daura agogo Kiran zayyan yashigo wayarsa kafin ya 'daga akai knocking qofarsa ya 'daga wayar tareda nufar qofar Yana bu'dewa yaga soldiers sun zagaye harabar gidan da bindigoginsu
Cikin tsananin mamaki yake kallonsu ya bu'de Baki yace..........




Vote
Comment
Share
[9/21, 7:55 PM] Aysha Galadima: *_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_




*22*
Wat""""yace cikeda mamaki...

Babban cikin wa'inda aka Aiko Wanda shima tuni hassadar saheeb da baqin cikin cigaban daya fisa samu har zamowarsa babban kanal major yasa yakejin tsananin tsanarsa ya matso cikin wani shu'umin murmushi dabawanda zai gane yace,

Sorry sir but we have the strict order to arrest you.....

Wani kallo ya watsa Masa da big white oily eyes nasa Nan take ya diririce yace,

Sorry sir.

Baikoba cikiba ya fito yabiyosu kusan soldiers talatin Nan take yasan koma menene to babba ne.

Abba da Kamal taredasu mum asee ne suka fito hankulansu amatuqar tashe musamman ma mum asee da tuni ta qanqamesa tareda fashewa da kuka tana cewa,

Nashiga uku ni aseeya mezan gani?
Saheeb fadamin menene?
Meyake faruwa?
Please son talk to me....

Abba ma bayanin yakejiran yayi musu Amma Sam ko magana yakasayi saima idanuwansa dasuka ka'da jajir zuciyarsa na wani irin ra'dadi...

Kamal kuwa yakura ya kashewa Ido daya suka saki murmushi.

Tunda tayi sallar asuba tana zaune Kan sallayar Bata tashiba hakanan takejin tsananin fa'duwar gaba da damuwa..

Hayaniya tafara juyowa sama sama ta miqe tsaye tareda wuce gwaggo dake kwance tana Jan minsharin bacci bayan tayi sallar asuba.

Cak ta tsaya zuciyarta na bugawa da sauri nantake taji kamar jiri zai zubar da ita tayi saurin yin zaman Yan bori a qasa Dan kuwa abinda idanuwanta suka gani yanxu ya tabbatarda aikinsu mum asee yaci...

Hawaye ne suka tsinke Mata lokacinda taqura Masa Ido ko baifadaba ta hango tsananin damuwa da tashin hankali tareda bacin ran dayake ciki....

Sake 6allewa hawayenta sukayi Yana 'dagowa zai wuce idanuwansu suka hadu ta qura Masa Ido cikin hawaye shima bai dauke nasa kanba Saida wayarsa dake aljihu tayi qara ya juya ya nufi motocinsu dake waje Dan kuwa ko nasa anhana yashiga Sai Wadda akazo arresting nasa dasu.

Kasa motsi tayi agurin har aka wuce dashi ta juya cikin wani irin nauyin zuciya takoma 'daki ta zube bakin gado tareda sakin kuka Mai cin zuciya ahankali.....
Abinda takeji azuciyarta yafi qarfin tausayi,
Jitakeyi zuciyarta na Mata zafin dabazata iya jure ganin saheeb ahaka,

Sabon kuka tasaki Dan kuwa zuciyarta batayi Mata adalcin kamuwa da wannan muguwar soyayyarba dabatada qarshe me kyau,,
Meyasa zuciyarta koyaushe Bata iya za6en masoyaba,,,,

Duk yanda taso daina kukan ta Nemo mafita kasawa tayi
Hawayenta sun kasa tsayawa ta miqe cikin Dan sauri sbd zayyan daya fa'do Mata arai tasan shika'dai zata iya fadawa gaskia...to Amma yakamata na yarda dashi shima kuwa tunda Naga duk nakusada saheeb din ne ke farautar dukiyarsa da rayuwarsa.....

Kallonta gwaggo lokacinda ta tashi taga fuskarta tayi mummunan kumbura tai jajir.....

Jitayi jikinta yayi sanyi Dan ita alamarin Anano yafara Bata tsoro ta miqe tsaye tashiga toilet ta wanko fuskarta da bakinta tadawo ta zauna kusada ananon tareda kallonta cikin tsananin kulawa tace,

Anano indai da gaske kike bakyason Nan din banga amfanin zamanmuba saimu koma gidan tunda can kikeso Amma wannan alamarin yafara bani tsoro gabaki 'daya kin hargitse bakya cikin nutsuwa da walwala duk kwanakinan.......

Sabbin hawaye ne suka gangaro Mata Bata damu data gogeba tace,
Gwaggo zuciyata na zafi,,jinake kamar zuciyata zatabar qirjina ra'dadin datake ciki...

Kallon tausayawa gwaggo tayi Mata sbd 'daukar ciwon zuciya take da gaske tashafo kanta tace,

Allah ya yaye Miki yakawo Miki sauqi Anano.

Amin tace daqyar tana sunkuyar da kanta sbd zuwan wasu sabbin hawayen Sai kawai ta miqe tabar dakin Dan kukan nata ba tsayawa zaiyiba gwara taje tayisa ko ra'dadin zuciyarta ya ragu.

Tana fitowa nufi hanyar gefen part'din saheeb inda gym dinsa yake cikin wani mugun yanayi taji fixgota tareda 'daga hannu zai sharara Mata Mari
Ta rintse ido batareda ta motsaba Dan kuwa tasan zai zargi hakan kodan ganin daya Mata jiyan a palon saheeb din.

Sauke hannunsa yayi tareda yarfewa cikin tsananin fushi da 6acin Rai idanuwansa har wani ruwa suke tarowa sbd 6acin Rai ya kalleta da jajayen idanuwansa yace,

Koki fadamin ubanda kikewa aiki Kona daureki nakaiki headquarter inda zakifi Jin da'din magana..

Cikin tsinkewar zuciya ta kallesa hawaye nabin fuskarta ta bu'de baki cikin sanyin murya tace,

Bani nayiba.....'dauketa da lafiyayyan Mari yayi sbd yakasa tankwarar zuciyarsa Kuma tabbas Babu abin zargi akan wannan abin Sai ita Dan kuwa saheeb nacan tuni aka rufesa a 'dakin qanqara duk bayan 30min Sai anmasa shock sbd kawai yayi admitting laifinsa shi munafikin sojane Yana tareda 6arayi....

'dagowa tayi ta kallesa da idanuwanta dasuka ka'da sukai jajir ga gefen bakinta daya fashe sbd Marin tace,

Ka dakeni,kasa a 'daureni,kayimin azaba Zan cigaba da maimaita maka bani nayiba sbd banyiba...
Kuka tasaki tana cigaba da cewa,

Kana tunanin Dana iya computer dazan bar hakan tafarune?

Wani kallo ya watso Mata sbd dai maganarta tasake tabbar Masa da koba ita tayiba tasan ya akayi hakan ta faru.
Baisan meyasa zuciyarsa keson tayarda da itaba duk da kuwa ita din ba abin yardabace.

Cikin qunar Rai da fushi yace,

Ok then idan bake kikayiba then prove yourself..

Rintse idanuwanta tayi hawayenta nacigaba da zubowa tace,

Wallahi bani bace....

Cikin wata gigitacciyar tsawa yace,

Then who is it bitch.... talk coz am loosing my patience hia..

Girgixa Masa Kai tayi ahankali tana sake zubo da hawaye..

Cikin zafin Rai da takaici yakallleta ganin taurin kanta yace,

Ok then zanmiki yanda zakifi ganewa....

Palon saheeb ya nufa tareda zuwa har bedroom ya dauko laptop dinsa tareda wayarsa daya yafito ya fizgi hijabinta yafara janta tana tana kuka yakaita motarsa ya jefa but yarufe yajata Bai tsaya ko'ina ba Sai barrack.

Budeta yayi yakuma jawota Nan take akayi ciki da ita zuwa lokacin tuni hawayenta suka qafe jikinta ba inda baya rawa hankalinta yayi mummunan tashi...

Office din general major ya nufa cikin girmamawa ya Sara Masa.

Cikin kulawa general major Muhammad tukur Garba ya zare medical glass dinsa yakalli zayyan yace,

Zayyan hope kasamo evidence din dakace coz we're running out of time within 24 hours idan Babu wani prove nabashine yayiba he will be sentence to dead...

Sir I have the prove sbd yarinyar gidansuce ta 'dauki laptop din taje tana wani Abu da ita so she mistakenly send it...

Wat...? do you expect me to go the headquarter nabasu wannan bayanin...

Where is the girl?

She's here with me sir..

Let's go and see her...yafada tareda miqewa..

Zaune take a wani dakin horo an 'daureta Kan kujera tareda kunna wani mugun kwai daya masifar kashe Mata idanuwa jitake kamar idanuwanta zasu zazzage Banda ko hawaye basa iya fitowa sbd dasun nufato fitowa saisu bushe sbd azabar Kwan da haskensa.

Qare Mata kallo general major muh'd yayi cikin mamaki yace,

Zayyan are you sure of wat you're saying..?

Yes sir yace,.

Kashe qwan akayi ta rintse idanuwa da qarfi Dan kuwa ta daina ganin komai tasaki wani razanannen ihu tana Dan kuwa ta tabbatarda tadaina gani Koda zata gani kuwa ba Yan kwanakin nanba.

Cikin wata irin muryar ban tsoro general major ya daka Mata tsawa tareda sake maimata Mata abinda zayyan yafada..

Tsit tayi cikin wani sabon tashin hankalin Dan kuwa Sai yanxu tagane dalilin kawota Nan kenan ita zasu maqalawa laifin..

Ganin yanayinta yasa zayyan matsowa da niyar walwaleta qasa qasa gurin kunnenta yace,

Is better kice keki daukar Masa laptop by mistake Kika tura internet coz kina qaryatawa saheeb zai iya rasa rayuwarsa nidake Kuma zamu iya qare shekarunmu a prison sbd already munriga munshiga cikin zancen so better be careful.



#vote
#comment
#share
[9/21, 7:56 PM] Aysha Galadima: *_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_




*24*
Tana ganin ya shige ta kalli zayyan tace,

Nagode Zan shiga ciki.

Siyayyar dayayo Mata ya fitar tareda miqa Mata manyan ledojin takallesa zatai magana yace,

Apologies and thank you......

Girgixa Masa Kai tayi zatai magana yarigata da cewa,

For Allah's sake karkiyi magana ki karba..

Kar6a tayi tareda godiya ta juya tabar gurin yabita da kallo zuciyarsa na kar6ar abinda ke shigarsa akanta duk da dai yanason magana da ita sosai akan abubuwan dasuka faru Amma yabari saita warware duk da dai zuciyarsa na hararo Masa wani alamari acikin zuciyarta gameda saheeb.


Washe gari Inna da ciwon Kai Mai tsanani ta tashi tun Daren jiyanma take fama dashi..
Tana tashi ta Mike ta nufi hanyar fita Anano dake gyarawa abdul lullu6i takalleta tace,

Gwaggo Ina Kuma zakije?

Karin safiya Zan dorawa saheeb Kinga shima ba lafiyarne dashiba.

Keda bakida lafiya gwaggo kiyi zamanki zanyi Miki aikin.

Idanuwanta dabasu gama hucewaba gwaggo takalla zatayi magana takatseta....

Zan iya gwaggo zoki huta.

Miqewa tayi ta nufi kicin din gabanta na fa'duwa...
Cikin qanqanin lokaci ta ha'da Masa breakfast lafiyayye tarasa yazatayii tashiga palonsa takai masa.

Rintse idanuwa tayi tareda sauke numfashi ta dauka ta bu'de qofar palon ahankali tashigo.

Tsaye yake bakin fridge na dining area din ya Ciro Power horse zaisha kayan baccine black ajikinsa Sai suka qara fito da hasken fatarsa sosai....

Cak ta tsaya jikinta na'dan rawa sbd Sam batayi tsammanin ganinsaba kallo daya tamasa tayi saurin 'dauke idanuwanta cikin nasa tareda saurin qarasowa ta aje zata juya suka qara hada ido ya dauke Kai tareda tsuke fuska

Komawa tayi ta 'dauko sauran abincin tadawo wannan karon yabar gurin Yakoma tsakiyar palon ya zauna Kan kujera.

Sake hada idanu sukayi murya na rawa tace,

Ina kwana?

'daga power horse din hannunsa yayi yakai baki baiko kalli inda takeba bare ya amsa.

Harara ta watsa Masa tareda turo baki Aiko Sai Akan idonsa
Wani kallo yasako Mata zai dako Mata tsawa tun kafin maganar ta fito ta fice da sauri tana cewa,

Ni kullum da masifaffi Allah ke hadani hunnn.
Tun safen kamalu keson ganinta ta lafe cikin daki raqi fitowa yayita Aiko asabe tayi biris taqi zuwa

Sai Da yamma zayyan yazo ya Aiko kiranta tafito cikin doguwar Rigar blue atampa da qaramin hijab.

Kallonta yayi cikin kulawa suka gaisa tareda Yar fira sama sama ya wuce part 'din saheeb.

Part din mum asee ta wuce Dan dubo asabe dataita zaryar dubata kwana biyun.

Tana shiga taji an fixgota da qarfi tareda jefota tsakiyar palon saidata bugi centr table gefen bakinta ya fashe ta 'dago da sauri taga Kamal yana wani irin huci kamar zai buga ya sake damqo gashinta dake cikin hijab da qarfi cikin 6acin Rai yace,

You ingreat bitch so nawa Zan fa'da Miki Babu shegen dazaki kula bayan ni Amma kinqi ji
Bakisan rufa Miki asiri ne zanyiba na taimaka muku keda that bastard thing you called son
Ke bandama qaddara mezanyi dake da bastard son dinki.....

Cikin baqin ciki da hasala ta katsesa tareda miqewa tsaye tace,

Karka qara Kiran yarona da shege sbd ba shege bane Dan haka ka janye tausayi da taimakonmu dazakayi ka rufa Mana asiri sbd har abada bana buqatar taimako ko tausayawa daga gareka afterall Mena sama yaci bare yaba na qasa,,,
Karka Kuma Kiran sunansa sbd inason abuna ahaka duk da Yana shege Zan iyayin komai akansa Dan kuwa dakasan yanda nasamesa naci wuya akansa na yafe gatana sunana mutumcina da iyayena akansa nazo Nan nasan zaka tabbatarda idan nace maka Zan iya komai akansa zaka yarda Dan haka karka Kuma shiga rayuwata da yarona bakasan wacece Anano ba
Yaron dakake Kira bastard yafika Dan kuwa Bai dauko halayen shegunba ko 'daya saima Kaine kakeda kaf halayensu harma.......

Hannu ya 'daga a zafafe zai wanketa da Mari mum asee ta riqe hannunsa tanabin Anano da wani irin kallo Dan dama tana palon zaune itada Kamal kafin ananon tashigo....

Lallai dama ance 'dan iska na qauye...ta fa'da cikin zuciyarta
Taji zafin maganganun ananon sosai Amma qarfin zuciyarta da iya fitsararta tareda son datace tanayiwa shegen 'danta zatai komai dominsa su zatayi amfani dasu tayi amfani da ananon ta jefi tsuntsu biyu da dutsi daya,,,ta cimma burinta,,ta wargaza ananon bayan ta sheqa shegen danta lahira..

Murmushi tasakarwa ananon bayan ta sauke hannun Kamal tareda cewa,

Bakada hankaline zaka daki mace
Kai kullum cikin zafin Rai da rashin hakuri..fice kaban guri mutumin banxa kawai.

Kallon mamaki yabi mum din dashi tamasa alamar ya wuce
Ya wuce Yana qwafa kamar zai tashi sama.

Kamo hannun ananon tayi suka zauna a kujera ta kalleta tace,

Karki saka alamarin Kamal arai haka yake kamar Mai shaqar cocaine.

Mamakine yakama Anano ganin yanda mum asee ta sakar Mata tasan akwai abunda zata qulla
koma meyene zatabita yanda takeso.

Murmushim yaqe tayi tana goge gefen bakinta da tissue dinta mum asee din ta miqo Mata tace,

Bakomai aina Saba da halinshi zuwa yanxu.

Mamakin Anano mum asee tasakeyi ganin yanda take Kai tsaye tayi murmushin mugunta tace shege baqauye...kafin ta fuskanci ananon dakyau tace,

Kince kinason 'danki,,,bakyayi Masa sha'awar kyakkyawar rayuwar hutu da ingantaccen ilmi da Jin da'din rayuwa..

Kallon mamaki Anano tayiwa mum asee

Mum asee tace,
Eh sbd naji kince zakiyi komai akansa..

Ina Masa addua da fatar hakan...

To idan nace Miki ga damafa Wadda zakiyi arziki 'danki yayi sunan Mai arziki hakama akiraki da uwar 'dan Mai arziki
'danki yayi kyakkyawar rayuwa yasamu ingantaccen ilmi...

Zaro idanuwa Anano tayi
mum asee tasaki wani shi'umin murmushi tana cewa,

Yes idan har Zaki iya tsayawa kice saheeb shine uban 'dan shegenki,
Ki tsaya kice shine yamiki cikinsa Kika haifesa.....

Miqewa tsaye tayi da sauri tsoronta na fitowa qarara Dan Bata ta6a kawo wannan shine abinda mum asee zata fa'daba..

Zaunar da ita mum asee tayi tace,

Kar kiji tsoron kowa idanhar Zaki iya nizan tsaya Miki akomai.

Tana kallon tsakiyar idanuwan mum asee 'din cikin tsananin mamaki tace,

Meyasa zance 'dana 'dansa ne...?

Sbd samun cikakken iko akan dukiyarsa...

To ai a musulunce 'dan shege baida gadon ubansa...

Ba wannan Zaki dubaba yanxu cigaban 'danki da naki Zaki Duba.

'dana bazai ta6a samun iko daga dukiyarsa ba Dan ance 'dansane tunda ba aurene atsakaninmu ba..

Aurenki zaiyi.....

Miqewa tasake yi cikin tsananin mamaki da fa'duwar gaba da zancen yasata.

Muryarta na rawa tace,

Ta Yaya?

Ta nice Zan saka ubansa yasashi aurenki Dole sbd yayi Miki ciki kin haihu...

Cikin 'daga murya takatseta da cewa,

Duk menene dalilin dazaisa ayi hakan.

Murmushi tasaki tareda miqewa tana kallon ananon da tuni zufa yafara jiqata sbd tashin hankali tace,

Dalilin hakan shine Ina buqatar takardu ahannunsa Kuma bazan ta6a samunsuba Dole saita hanyar matarsa.....

Girgixa Kai Anano tayi idanuwanta na cikowa da hawaye murya na rawa tace,

Bazan iya ba..

Zaki iya.

Bazan iyaba ki aura Masa yakurah.

Dole Sai kece zakiyi sbd 'dankine zai Zama dalilin auren.

Bazan iyaba"""ta fa'da hawayen idanuwanta na gangarowa sbd mum asee tafara wuce tunaninta.

Janyota tayi da qarfi tareda cewa,

Dolene kiyi idanba hakaba Zaki 'dauki gawar shegen 'danki da gwaggonki a hannunki Dan bazakiji sirrina abanza ba.....ta bu'de qofa ta hankadata waje da qarfi ta kife a qasa.

Qafafun mutum tagani agabanta ta 'dago da sauri gabanta na fa'duwa tayi Ido biyu da zayyan fuskarsa ta ka'da tayi jajir..
Miqewa tayi jiki asanyaye tareda sunkuyar dakai zata wuce ya sha gabanta tareda nuna Mata hanyar gym room 'din saheeb da hannu fuska.

Ganin yanayinsa ba sauqi yasa ta nufi inda yake nuna Mata Dan tsoron karta Kuma Shan azabar dazata sakata rasa idanuwanta.

Suna shiga ya rufe qofar tareda zaunawa Kan wani machine ya dafe kansa idanuwansa na qara canzawa...

Rakubewa tayi cikin tsoro duk da itama tana cikin tashin hankalin.

'dagowa yayi ya kalleta ciki wani irin yanayi yace,

Me saheeb yayi muku arayuwa dakuka za6i Zama masu farautar dukiyarsa da rayuwarsa....

Girgixa Masa kai tayi cikin sanyin murya tace,

Qaddaratace takawoni Nan Kuma nasan qaddara zata daukeni daga Nan din sbd na fado cikin mutanen daban ta6a ganiba arayuwa,,,,,

Qaddarar taimako ita tarabani da komai nawa harna kasance cikin wannan mummunan halin...

Kuka tasaki ahankali tana cewa,

Tabbas zasu kashe gwaggo da abdul matuqar banyi abinda sukaceba sbd nasan zasu iya fiyeda hakan Dan sunsha yi.

Kallonta yayi tereda matsowa ya fuskanceta yace,

Tabbas tun farko nayi zargin cikin gidannan basa qaunar saheeb sbd abubuwa da dama Amma bantaba tunanin hakanba...

Cikin qureta da Ido yace,

Waye yasa abisu Abba last time?

Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta Dan batason

Please Login or Register in order to submit comment