You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
shigo ciki.
Hakan ne ke faruwa don yan uwan mu idan su zo daga kauye sun kan kebe damu suna tambayan mu irin rayuwan da muke ciki a nan din.
Bamu kan boye masu komai mukan fada masu duk irin kokarin da akeyi damu a nan din sai su juya maganan da ana cutar mu ne ana cin amanan mu don wai da kudin mahaifin mu ai ake muna komai da ake muna na rayuwa.
Tun ban daukan wanan maganan a raina har maganan ya fara tasiri a zuciyana wani hutu mun dawo ne muka samu an kawo kayan lefen da mahaifin mu yakai kaduna wai yanzu kayan ya zama na magada.
Don haka suka dawo wa yan uwan mahaifin mu da kayan sai da muka kwana biyu da dawowa ne aka fitar muna da kayan baba kabiru ya kasa muna aka cire lwa umma nata kason a cikin kayan don ita ma tana da gadon kayan.
Kurciya ke damun mu a lokacin sai murna muke mun samu kayan banza baba kabiru ya biya kudin dinki aka shiga dinka muna kayan bai dauki komai ba a ciki.
Sai matar sa anty ne muka cirewa turmi daya da man shafi daga ciki sauran mu muka dinka abin mu muna sakawa mu a dole ga yan mata a lokacin ba abinda ya damay mu.
Hura ma baba kabiru wutan da mukayi akan muna son zuwa kauye muyi hutu ne yasa ya barmu muka tafi kauyen wanda ni da biyu na tafi don ina son ganin jamil a lokacin wanda yanzu tsakanin mu sai wasika don bamu amfani da waya.
Wanan zuwa kauyen da mukayi ne aka fara zuga mu kan iyayyen namu yan uwan mahaifin mu dake kula da alamarin mu tankar iyayyen mu na raye.
Don suna iyakar kokarin su damu a lokacin wani dan wan mahaifin mu ne da mahaifin shi ya riga namu rasuwa ya fara tun kara na da maganan.
Yace bayan mun gaisa ashe kun zo garin nace eh mun zo shekaran jiya sai yake cewa wai yaya zancen dukiyan ku ne har yanzu shiru.
Nace wallahi bamu san komai ba akai don su baba ne ke da maganan a hannun su yake fadin ba naji ance an sai da motar marigayi din ba da gidan shi na Abuja .
Wanan gidan da Alhaji kabiru ke ginawa yanzu ance da dukiyan ku ne yake gina sa ai maganan ya bani mamaki kwarai ban gaskanta maganan ba sai da jamil yazo muna hira ya kara fito min da wanan zancen na yarda.
A lokacin naso in tayar da hankalina sosai na kebe da yan uwana ina fada masu halin da ake ciki sai baffa kanina ke fadin shima yaji wanan zancen sai dai ba yadda zamuyi yajzu don mu din ai kanana ne ga maganan .
Amma an bashi shawara idan lokaci yayi ai dole za a fitar muna da dukiyan mu ne don haka mu bar zancen har mu tasa tukun na .
Da wanan shawaran muka bar maganan iya mu don summaiya kanwa ta cewa tayi dani wai da nake magana kan dukiyan mahaifin mu ni ban ganin irin kokarin da kanin mahaifin namu yake damu ne.
Maganan ta ya ban haushi sosai nake fadin kin ji nace baya kokari da mune ko kin ji na fadi wani abu ne mara kyau akan zancen.
Maganan yaso ya zama muna fada a tsakanin mu sai da na taushi zuciyana don kada wani yaji mu muna magana akan zancen ai muna wani fassara na daban.
Wanda ni zancen dukiyan ba wai ya damay ni bane sosai don maganganun mutane ne a kai har zancen ya fara tasiri a raina yanzu.
Munyi hutun mu lafiya mun dawo inda bamuyi wani dadewa ba muka fara shirin komawa makaranta.
A daren da zamu koma ne baba kabiru ya kiramu a falon shi yake fada muna sunyi shawara da yan uwan shi sun sayar da gidan mu na Abuja sun saya muna wani a nan garin don nan din yafi kusa da gida.
Don haka yan haya ke cikin gidan za a dinga karban kudin haya ana muna abinda ya dace damu.
Mukai mashi godiya bayan ya gama muna bayani ya fada muna zamu iya zuwa idan mun dawo muga gidan da ko yan uwan mu maza su tafi su gani.
Wanan maganan ya kara kwantar muna da hankalin mu summaiya ke fadin kun gani nace daku abi sannu don ban sa baba zai iya muna hakan ba da ake fadi.
Gashi mahaifin mu ashe duk takardun shi sunan baba kabiru ne a ciki sai nawa dana baffa daya saka magadan shi.
Mun koma makaranta zuciyar mu ba wani zargi ko tunanen komai a ciki don yadda mutane ke zuzuta zancen kan mahaifin mu yabar dukiya mai yawa sai bamuyi tunanen a ina dukiyan yake ba wanda mu bamu san dashi ba.
Bamuyi kuma la,akari da irin samun da baba kabiru yake yi ba don shi din yanzu shahararen dan siya sa ne da ake damawa dashi sosai.
Ga kokarin da yake muna wanda mu bamu gani a lokacin don ma iyalin shi suna da hakuri da hangen nesa ne yasa basu damuwa da irin yadda yake gwada muna banbanci a tsakanin mu da nasa iyalan.
Don kirikiri zai muna abu bai ma diyan cikin shi ba kuma basu damuwa da hakan da yake muna din sai dai duk da haka mutane masu hana ruwa gudu suna nuna muna ai cutar mu akeyi kawai.
Matsin da shamsiya ke muna na mu gudu daga gidan na baba kabiru ne yayi yawa ganin bamu gudu ba yasa ranan muka wayi gari babu shamsiya ta tattara kayan ta ta gudu daga gidan baba kabiru din.
Wanda hakan ya batawa baba rai sosai har yakai ga kiran wayan mahaifinta yana tambayan shi sai cewa yayi eh tana nan gida ai ta iso da yamman nan yace to ku barta a gurin ku don dai ni nasan gidana banda yunwar komai a tare dani.
Maganan yaso hada zumunci fada don mahaifin nata na rufe ido ya goyi bayan yar shi ya mance da irin halarcin da akai muna din a gidan kanin nasa.
A wani yammaci jamil ya kawo min ziyara yana saye a cikin dinkin shada da hula ya fito dan bahaushe shi sak sai dan glass din daya kafa a fuskan shi.
Na fito na samay shi tsaye a waje yana jiran fitowa na lokacin yana gani na ya sakar min wani dan murmushi mai laushe yana a fuskan shi na jin dadin ganina a lokacin.
Dadin ganin shi naji a lokacin ban san lokacin dana mayar mai da murmushin ba na karaso da sallama na gurin ina mashi sannu da zuwa.
Ya amsa min da yar fara,a a fuskan shi tare da fadin gani dai na biyo ki don yanzu naga alaman kin samu wasu anan kin fara mantawa dani.
Na dan ji zafin maganan a raina don ban ci wanan maganan ba a gare shi idan yayi duba ga yadda nake samun matsi a kan shi a gida akanshi gurin umma don tabi ta bata zancen shi ta ko ina.
Gashi idan na tuna shi sai naji kamar nima in gudu yadda shamsiya ta gudu daga gidan baba kabiru din duk a kan shi.
Sai dai ba zan iya yin hakan ga baba kabiru ba don ya nuna muna duk wani kauna daya dace a duniya dashi da matan shi.
Naja dogon nunfashi tare da fadin wanan zaton kake mun kuma yanzu duk irin halaracin da nake nunawa akan ka yace.
Kin san garin yafi namu matasa wayayu na sani ko wani ke son min yankan baya akan ki wanan dadewa da kika yi bamu hadu ba ya fara sani a shakun soyayyan mu.
Murmushi nayi a raina ina kallon shi dayasan kewan shi na hanani sakat a raina da bai fada min wanan maganan ba tunanen sa yana hanani jin dadin zaman garin.
Sai dai a fili nace bayan ajiyan zuciya ban yarda da uzurin ka ba jamil don da ka damu dani yadda kake fadin wani nisane a tsakanin mu da zai hanaka zuwa nan din kai.
Yanisa yana murmushi yace kin san abu ga mara hali yanzun ma da kin san yarda nazo nan din dakin tausaya min.
Nayi walwal da ido nace da fatan dai ba wani rikici ka jefa kanka ba don kazo nan din ya girgiza kai tare da fadin ko daya wallahi.
Mun dauki lokaci har baba kabiru ya dawo ya samay mu a gurin na dauka zai min fada sai naga babu wani alaman baci rai a tare dashi dana shigo.
Bayan tafiyan shi ne zuciyana ta shiga garari akan sa ashe duk yadda nake daukan shi a raina yafi hakan damuwa dani don irin dadan kalaman daya shimfida min ya tafi.
Alhamdullahi na gama karatuna lafiya inda na samu kyautar jam daga hukumar makarantar da nake ciki mu uku muka samu wanan kyautar a shekaran.
Zuwa lokacin tsakanina da jamil soyayya ne mai karfi wanda har lokacin umma na saman bakin ta akan bazan aure shi ba ko bayan ranta ne kuwa don ba zata hada zuria da irin gidan su ba.
Ban damuwa da maganan ta don yanzu akai back din da ban tsoron ta na fahinci ita din kakace a wurina ba uwa ba sai dai akwai shakku da tsoron ta a raina.
Don Allah kuyi hakkuri wanan ma da kyat na samu caji na dan rubuta shi don kuna raina da fatan zakuyi min afuwan kan hakan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:50 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼♂️ KANIN AJALI 🙆🏼♂️
1️⃣1️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Tunda na gama karatuna ina gida zaune sai dai ina gamawa summaiya tace ba zata koma boarding ba ita ma sai dai tayi jeka ka dawo a gida.
Son da baba kabiru ke muna ne yasa bai mata fadan haka ba ya nema mata makarantar jeka ka dawo ta fara zuwa anan cikin garin.
Gashi mun dinke sosai da jamil don yanzu shima a cikin gari yake zama gidan wani abokin aikin mahaifin shi don ya samu saukin kebewan mu a ko wani lokaci ya bukata.
Da damana yayi zai koma gida ne muka kitsa akan nima in koma kauye na kwana biyu na yarda da hakan bayan tafiyan shi nima na tsiri son zuwa gida wurin umma kamar yadda nace a gida.
Baba bai hanani ba don saukin kai irin nasa nan na shirya nayiwa kauye diran ba zata da farkon zuwa na naji rashin dadin garin don da yan uwana muka saba zuwa wanan karon kuma ni kadaice nazo.
Sai daga baya na dan fara sake jikina a lokacin duk wata sa,a ta acikin dangin mu tayi aure nima don karatun da nake ne ba ai min ba na sani.
Sannu a hankali na fara sajewa da su nan na yanke shawara na fara sana,a don kudin kashin da ke kokarin yi min tsaye a garin .
Da taimakon yar mahaifiyar mu na samu jarin dana fara sana,a dashi a garin inda naje birni na saro kuloli da sauran kaya na bukatan mata.
Sai dana kwana biyu a gurin yan uwana sai dai ban yarda na zo da kayan gidan baba kabiru an gani ba don kada yayi min fada kan hakan na gama masu kwana biyu tare da gama sayen duk wani abinda nake bukata na juya zuwa gida.
Sai dai da farko naji kunyan yin talla don bantaba ba a rayuwana sai gani dauke da kaya buuuu a kaina ina shiga gidajen kauyokan mu dama ke waye ina tallatawa.
Allah a cikin ikon sa yasa ma sana,an tawa albarka sai gashi dan lokaci kadan nayi suna sosai don bayan kuloli har turamay nake sayarwa kuma.
Cikin dan lokaci kan kani nayi arziki da bai faduwa da wanan sana,an da nakeyi inda baba kabiru ya samu labari ya zo takanas ta kano har kauyen ya gana da umma akan barina da sukayi ina wanan ssna,an kamar mara gata a gari.
Sai umma tace ni naga zan iya banda rashin gata abinda na zabawa kaina ke nan bai min magana ba ya koma da bacin rai don mahaifiyar su, ta hanashi yi min fada.
Kudi na hada yakai dubu dari biyu jamil yazo gurina muna hira nake bashi labari yake fadin sai in samu wani sana an in dora a kai da riban nawa.
Ya dan jima gurina muna hira daya koma gida ya kasa zaune ya kasa kwance yana tunanen wanan kudin dana bashi labarin na mallaka a yanzu.
Washe gari bayan la,asar na dawo daga talla sai gashi nayi mamakin zuwan shi don ba lokacin zuwan shi bane kenan.
Bayan mun gaisa ne yake fadin dama wani shawarane yazo min dashi shine dalilin ganin shi da nayi a wanan lokacin.
Nace wani shawara ke nan yace eh gani yayi yanzu dai shi baida wani sana,an da yake yi mai zai hana shima ya fara sana,a da zaiyi saurin kawo muna kudi don mu samu mu fara shirin auren mu nan da dan lokaci kadan.
Don ni gashi sana,an ya karbeni da farawa na tara wanan uban kudin idan mun hada hannu sai abin yayi auki mu kashe mu birne ba wanda yasan tsakanin mu.
Nace ba tare da nayi wani tunane ba kana ganin haka zai fi muna yace kwarai kuwa don karuwan mune gaba daya.
Nace yanzu kai may kake ganin zakayi wanda zamu samu karuwa haka da sauri ya gyara tsayuwa da kyau yace dani shawaran dana yanke shine in dinga shiga birni ina sayo mai na fetur da gas ina shigowa dashi nan kinga babu mai wanan sana,an ai anan ko ga kuma masaya na dayawa .
Nace wanan shawaran yayi daidai gaskiya kaga a dan lokaci kankani zamu samu mu hada abinda muke so ke na yace shi ya gani shima.
Batare da jin wani darrr ba nace ya je da dare idan yazo zan fito mai da kudin don yanzu idon mutane yayi yawa a kan mu.
Ya gama min dadin bakin shi daya iya ya na shiga gida don jamil a gurin iya dadin baki baida tsara a kauyen mu nan da jin dadi na na shiga gida.
Sai ga umma na gyaran gurin da take kiyon awakanta ta dago tana fadin yanzu muka gama maganan ki da babakin yushau nake fada mai riban da kika samu da sana,an ki .
Shine ya kawo shawaran mai zai hana a sayo maki shanu a turke maki har lokacin da dabbobi zasuyi tsada a sayar nace ya bari ki shigo muyi shawara dake.
Fuska na bata tare da fadin kash umma baki fada min wanan maganan da wuri ba yanzu fitan nan da nayi har na bada sakon a saro min kaya don ni ba zan samu zuwa ba wanan satin da kaina.
Kuma gashi har mai sakon ya wuce ko fuska ta sauya tare da fadin Allah yasa haka shine alheri nace amin nayi saurin wuce guri don naga kamar bata yarda da magana ba a lokacin.
Don idan zan sari kaya da kaina nake zuwa in sari duk abinda nake so in dawo don ko gidan baba kabiru sai inyi shiga goma ban leka su ba duk ko da cewa tan uwana suna gidan.
Sai idan naga dama nakan dan leka su a gurguje in fito duk zuwa da zanyi sai anty tayi min korafin yadda na mayar da kaina wata gaja saboda da neman duniya ina karamar yarinya dani haka.
Takan ce arziki na Allah ne ko nayi ko banyi ba idan lokacin arzikina yazo Allah zai bani ne gama mu da kudin mahaifin mu ake saka ran fitowan shi a ko wani lokaci zamu iya samun abin mu.
Wanan fadan da takan min nakan ji zafin shi don ina fanin tana min hassada ga samun da taga inayi ne a yanzu ga zugin Jamil dake shiga kaina kan in raba yan uwana da can din ma gurin su anty din.
Ga maganganun da wasu dangin mu yan hana ruwa gudu da sukan min kan dukiyan mahaifin mu wai su baba kabiru sun karbe sun cinye su da iyalin su.
Maganan yanzu da nasan kudi sosai ya zauna min a raina sai nake ganin haka din ne don su ko yaushe yanzu a cikin wadatata suke don basu rashi sam.
Dare yayi jamil yazo na fito da kudin zuwa gurin shi muna gaisawa yake fadin to yaya ina can ina Allah Allah kar gimbiyar tawa ta canza shawara don nasan idan umma ta sani zancen ta baci.
Nayi murmushi tare da fadin ina zan bari umma ta san wanan zancen kaiko sai dai ina shiga dazun ta tare ni da zancen wai in kawo kudin a sawo min saniya da kudin.
Da sauri yace sa may injin baki bata ba dai nace gasu tare dani yanzun haka ban yarda na bata ba don karya nayi mata kan cewa nabada sakon su a saro min kaya ai.
Yayi wani irin shu,umin dariya tare da fadin da kyau ta wurina ita umma may tasani kan kudi yanzu su burin su ke nan idan mutum ya dan samu kudi ace wai yasai abin kiwo dashi.
Nace ai ni ba zan yarda da wanan shawaran nata ba ga kudi ina ganin inda zamu samu karuwa wani zancen kiwo ake yanzu kuma da za a zo a girke a gida karshen tama ba wani riba a ciki.
Na kawo kudin dana kulle a cikin bakin leda na mika mai yana rawan jiki ya karba tare da fadin gobe asubanci zanyi don in samu in dawo da wuri kin ga har rumfa na kafa dazun bayan rabuwan mu dake inda zan fara sana,an tawa.
Bai dade ba yace zai tafi don ya samu barci issashe don asubancin da zaiyi a gobe din mukayi sallama dashi ya tafi na koma ciki cike da murnan wanan shawaran da jamil din ya kawo muna.
Don ina ganin zai ma fini samun riba a yadda ake cinikin man fetur da gas a kauyu kan mu don masu noman rani dake amfani da injin da sauran abubuwan bukata don rashin wutan lantarki da muke dashi a garin.
Washe gari sabo da murna ban fita talla ba barci na nayi sosai a gida sai zuwa sha daya da umma ta jini shiru ne ta leko dakin mu tana fadin.
Yar kabiru yau nace ba fita tallan kayan ne ko hutu kikeyi ne haka na bude idona da kyar tare da fadin umma yau hutu nake yi don ba wasu kaya da yawa a tare dani sosai.
Takai dubanta gurin da nake aje kayan tana fadin lalaikan kaya sun fada sosai wallahi kila zuwa gobe sakon ki ya iso ai kinga sai ki fita da tushe.
Sai zuwa a zahar na fito na debi ruwa na watsa ma jikina na nemi abinda zanci don tun safe ban ci wani abin kirki a cikina ba don dauki da nakeyi jira kawai nakeyi inji ance ga jamil can ya bude rumfar shi ai.
Sai dai har yamma banji komai ba yasa na dan fito na fita nabi ta wurin har lijacin ba jamil babu labarin shi a garin sai zuwa gab da magariba ne nake jin labari wai an tare jamil a hanya ko may ko may ban karasa jin maganan ba don faduwan da gabana yayi a lokacin.
Fita nayi a gagauce don in tabbatar da zancen da nake ji nan nake ganin mutane gungu gungu kin san abu ga kauye basu iya samun magana ba.
Yana kuka shabe shabe wai an tare shi a hanyan shi na zuwa birni sayan mai an kwace kudin an mashi dukan tsiya ko mashin din don sunga tsofo ne suka barshi dashi don ko sun dauka basu dauki komai ba don wahalanta.
Jikina yayi sanyi nadai gode ma Allah da suka barmin shi da rai suka tsaya ga kudin kawai basu taba lafiyan shi ba sai dai ban yarda na nuna wani abinda zai kara tayar mashi da hankali ba a wanda yake ciki.
Sai da dare muka samu kebewa dashi yake ban labarin abinda ya samay shi din inda hankalina yayi matukar tashi sosai na daiyi wa Allah godiya da ya dawo min dashi lafiya a lokacin.
Satin shi daya sai gashi yazo min wai zai yi tafiya wani abokin baban shi yaji labarin abinda ya samay shi yace yazo ya taimaka mashi.
Nayi murnan jin hakan sosai mukai sallama ya tafi akan washe gari zai tafi amsa kiran abokin mahaifin nasa a can birni.
Abinda ban sani ba ashe kudina zai shiga birni yasha garalin shi dasu don abinda ya faru yana barin yankin kauyen mu da jarkokin daya dauka na sawo mai na bat da kama dayayi ya watsar dasu a hanya a cikin jeji.
Ya shiga gari ya yi sayayan yadudukan shi na maza dasu takalma da sauran abin da yake da burin bukata a rayuwan shi.
Sune ya koma ta karbi dinkunan shi ya karasa kashe kudin daya saura a hannun shi don rashin tausayi da imani da bai dashi.
Nabi ruwa nabi iska na bi rana da sanyi na samo su rana daya jamil ya zo yaci amana ta ranan ko barci ban yi ba sai faman sakawa da kwancewa nake a raina.
Ina kallon kayan sana,ata da dan abinda ya rage min a ciki wanda basu taka kara sin karya ba a lokacin wanan abin har zazzabin dole ya ja min sai da nayi jinya akan hakan.
Bayan kamar sati uku ina dan bubugawa har tiren sana,an ya dan fara dagowa kaya ya fara samuwa min ga kuma kewan shi dake damuna a lokacin don tunda ya tafi ban samu labarin shi ba.
Kwatsam sai gashi ya dawo garin kowa sai da ya girgiza da ganin canzawan da yayi a dan kankanin lokaci ya murje yayi kiba ga shiga ta alfarma da yakeyi kamar ba dan kauyen mu ba.
Ban dai san inda umma taji rabarin ai nice na bashi kudin da yake karyan sun zube ba sai ji nayi tana fada tana fadin dama wanda baiji bari ba yaji hoho gashi yanzu ya fara nuna maki irin gidan su mayaudara.
Na fada maki ki rabu da yaron nan ba dan arziki bane da yake ke mai taurin kan tsiya ne kika dauki kudi kika bashi ya shiga birni yasha garalin shi dashi.
Yar nan kina arziki kuwa da wanan yaron da kika lakanta dama na fada maki ko mutuwa nayi sai na taso maku fatalwa idan kika ce wanan shegen yaron zaki nacewa.
Yanzun dai ga magana ta nan ya fara fitowa fili ai ya yaudare ki ya raba ki da komai naki sai kamay kamay da ya barki kina yi a gari yanzu.
Gabana ne ki faduwa don jin abinda umma take fada sai dai ni yace min abokin mahaifin shi ne ta bashi kudi ai yace ya sai kaya ya kuma koma karatu idan yana son ci gaba.
Sai dai yaga ni banci