You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
yana mai daka masa tsawa yace"tabbas yanzu zan ganar dakai kuren ka zan hallaka kuma na tafi da ZOBEN SHIRI, domin sanin wane ne ya aiko mu gareka ya huce tunanin ka.
Kafin ya gama furucinshi, dakarun sun zare makamansu sunyi ɗauki izuwa kan hubairu, suna ihu da kururuwa mai firgitar DANDAZON MAYAKA a filin daga,
Shi kuwa ya tare su aka fara ɗauki badaɗi, duka ɓangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance.
Wohoho! Maza gumbar dutse, haƙika inda babu ƙasa nan ne ake gardamar komowa.
Nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, ihun mazaje haɗe hargagi ya cika dodon kunne.
Sai da aka shafe tsawon rabin Sa'a da daƙiƙa talatin ana wannan artabu babu sassauci.
Nanfa dukkan bangarorin biyu suka fara gane kuren su, shi hubairu ya cika da mamakin yadda dakarun ke da zafin naman sa yakasa samun nasarar hallaka su.
Su kuwa suna al'ajabi ne bisa ganin cewa duk yawan su ya tashi a banza, halitta ɗaya ta zamemusu alaƙaƙai.
Lokacin da Sa'a ɗaya ta shuɗe ne ana wannan fafatawa,wani daga cikin mayakan ya sulala ta bayan hubairu ya makashi ƙoatar takobin sa, saboda raɗaɗin da hubairu yaji, bai san sa'adda ya kurma ihu ba.
Kafin yayi wani yunƙuri badakaren ya sake dankara mashi wawan sara a gadon bayan shi,take in da ya sareshin ya haddasa wani lafcecen rauni jini ya kama feshi yana tsartuwa.
Hubairu ya sake kurma ihu karo na biyu ya sulale ƙasa magashiyan yana nishin wahala,
Kawai sai wannan garjejen kato ya zare wani zabgeegen al'amudi a damtsen shi ya taka da kafafunshi har izuwa in da yake kwance, sannan ya ɗaya ɗaga al'amudin domin ya tarwatsa ƙoƙon kan Hubairu.
Kwatsam bazato babu tsammani sai sauran dakarun suka ji shugaban su ya tsandara ihu, ya sulale ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba.
Al'amarin daya firgita su kenan suka ja da baya domin suga wane ne yayi kisan, ai kuwa sai suka akayi arba da wata bakuwar jaruma
Sanye da fararen tufafi masu yalwa, ta rufe fuskar ta da siɗin rawani, hannunta rike da wata ƙasaitacciyar kwari da baka.
A sannanne dakarun suka fahimci cewa Jarumar tayi amfani da kibiyoyin ta wajen hallaka shugaban nasu, don Allah sai jikinsu Yakama tsuma yana kyarma saboda matuƙar fushi sukayi jarumar ƙawanya,
Wani daga cikin jaruman ya kurma wawan ihu yayi ɗauki kan jarumar yakaimata wani wawan sara a wuya, Cikin wani irin baƙin zafin nama ta sanya bakanta ta kare harin sannan ta daki badakaren a kirji.
Take ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba, cikin zafin nama jarumar ta buɗe baki ta karanti waɗansu kalmomi da ita kaɗai tasan me take furtawa , ta tsugunna ƙasa ta tofa a bisa raunin dake gadon bayan Jarumi Hibairu,
Take raunin ya warke sumul, adai dai lokacin da hubairu ya miƙe tsaye cikin ƙoshin lafiya, yana mai ƙura wa ɓakuwar jarumar idanu ko ƙiftawa ba yayi.
Yana mai tambayar kansa a cikin ranshi yana cewa shin wacece wannan bakuwar jaruma, kuma mene ne dalilin daya sanya ta ceci rayuwata, shin ko kuwa jaruma Amirat ce tayi badda-kama, amma kuma ai Amirat na cikin jinyar rashin lafiya yaushe ta samu lafiya.
Amsar tambayar da hubairu yakasa bawa kanshi kenan, adai-dai da dakarun suka kammala yi musu ƙawanya.
A na cikin wannan hali ne kwatsam sai aka hango wadansu dakaru na daban kuma mabanbanta na fitowa daga kowace kusurwa a birnin,waɗansu akan dakwai wasu a ƙafa.
Lokacin da suka kammala bayyana asannanne hubairu ya lura dacewa ba wasu bane ke jagorancin mayaƙan ba face Sarki shaibat da sarkin yaƙi abu-Damraz.
Yayin da dakarun suka yi arba da mai girma shaibat sai suka dare a tsakiyarsu suka bayar da wata hanya da mutum zai iya hucewa.
Sannu a hankali Sarki shaibat na ratsa tsakanin kafaɗun dakarun har ya bayyana daf inda Hibairu da baƙuwar jaruma take.
Tsawon daƙiƙa hamsin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne sarki shaibat ya dubi hubairu yayi gyaran murya cikin matukar fushi fuskar shi har gyatsine take yi yace"yakai Babban abokin gaba na har abada hubairu ibn Shabbaru kayi sani cewa haƙiƙa kana da tsanin sa'a da rabo da har ka iya tsalle ke tarkona, ka sani cewa a halin yanzu bazaka tsira da rayuwarka ba, domin ka maimaita laifin da mahaifinka Barde Shabbaru yayi mini.
Yanzu abinda nake bukata kawai shine ka miƙo mini zoben sihirin cikin ruwan sanyi, kafin sarki shaibat ya gama rufe bakin shi sai akaji wata murya taɓa cewa "Haƙika nine nafi cancanta daya mallaki zoben sihiri face domin kuwa sai a yanzu ne na gano cewa ashe ma aikin banza nake yi dana ɓata lokaci wajen mallakar dukiyar gasar GOGA SHA FAMA.
Cike da matuƙar al'ajabi sarki shaibat, hubairu,baƙuwar jaruma suka waiga domin suga wanda yake wannan furuci, yayin da suka yi arba dashi sai suka yi turus!.
Ba wani ne bane face Sarki Baddadul-ulƙas shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro tamkar wani ifritu,hannun shi na hagu rike da wani irin makami na haske, na hagun kuwa rike da sarƙa ta wuta, wani dattijo ne ɗauke da jikin sarƙar ta ɗaure sassan jikinshi, ba wani ba ne dattijon ba face Barde Shabbaru mahaifin sarkin sadaukai Hibairu.
Sa'adda hubairu yayi arba da halin da mahaifishi ke ciki, bai san sa'adda kwalla ta cika Mashi idanu.
Sarki Baddadul-ulƙas ya bushe da dariyar mugunta sannan ya murtuke fuska ya ɗorawa dacewa "Binciken dana gudanar bisa halarar tsafina ya tabbatar mini dacewa duk wanda yake tare da zoben sihiri zai mulki duniya, domin, zai iya lalata dukkan sirrikan tsafin dake duniya, domin dukkan makarin tsafin dake duniya na jikinshi, yakai Hubairu kayi sani cewa, a halin yanzu mallaka mini zoben sihiri domin kuwa hakan ne zai sanya na cire mahaifin ka daga wannan kangin bauta, idan kuwa kayi kunnen uwar shegu dani yanzu zan hallakashi a gaban idanun ka kuma na kashe na mallaki zoben cikin ruwan sanyi.
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Baddadul-ulƙas sai hawaye suka zubo daga idanun hubairu yaji tausayin mahaifin shi ya sake kama shi, kawai sai ya sanya hannu na dama akwai na hagu zai cire zoben sihiri ya
Da nufin ya miƙa wa Baddadul-ulƙas, amma sai baƙuwar jarumar ya dakatar dashi ta hanyar buɗar baki ta fara magana a karo na farko cikin Daddaɗar Murya tace"yakai sarkin sadaukai kayi sani cewa a yau ne zaka tabbata jarumi Ɗan baiwa, amma hakan bazai cika ba face ka rushe zaluncin wadannan sarakuna biyu, Baddadul-ulƙas da shaibat
Da ma dukkan zaluncin dake ɗoran ƙasa,
Ta hanyar amfani da wannan zobe.
Ka sani cewa damƙa shi ga sarki Baddadul-ulƙas tamakar ka damƙa rayuwarka da sauran al'ummar duniya cikin rayuwa da mutuwa, shin yanzu kana da tabbacin cewa sarki Baddadul-ulƙas bazai ci amanar ka ba idan ka mallaka ma shi zoben?.
Koda jin wannan jawabi haɗi da tambaya daga bakin baƙuwar budurwar sai Hibairu ya mayar da zoben bisa ɗan yatsanshi,
Shi kuwa sarki Baddadul-ulƙas sai ya bushe da dariyar mugunta ya dubi baƙuwar jarumar cikin tsakanin fushi yace"yake wannan jarumar ɓoye haƙiƙa kin tafka babban kuskure da kika shiga gonar da ba taki ba.
Yanzu nan zan ganar dake kuren ki, yana gama faɗin hakan sai kawai cilla sarƙar da dake hannun sa izuwa sama,take Barde Shabbaru dake ɗaure da sarƙar yayi sama tamkar an janye shi da ƙugiya ya tsaya a cikin iska, sannan Baddadul-ulƙas ya ɗaga wannan makami na haske dake hannun shi ya ruga izuwa kan baƙuwar jarumar yana ihu da kururuwar mai firgitarwa
Koda ganin hakan sai mai girma shaibat ya zare wata sharbebiyar takobi a damtsen shi ya kurma Wawan ihu yayi ɗauki kan Hubairu sarkin sadaukai.
Ana haɗuwa akayi karon batta ƙarfe, nan fa GWARAZAN JIYAn suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da jarumtaka irin ta zaratan Jarumai.
Lokacin da GWARAZAN JIYA huɗu, sarkin sadaukai,mai girma shaibat, Baddadul-ulƙas da baƙuwar jaruma suka ruguntsume da azababban yaƙi.
Sai suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare- hare cikin matuƙar zafin nama juriya da jarumtaka irin ta zaratan Jarumai.
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan Manyan giwaye suka fito filin daga, dole kananan dabbobi su zamo yan kallo, hakan ya faru ga sauran dakarun koda sukaga shuwagabannin su sun kacame da azababban yaƙi sai suka zamo yan kallo.
Kyan faɗa akwana ana yi inji masu iya magana, sai ɓangarorin huɗu suka shafe tsawon rabin Sa'a da daƙiƙa talatin Suna ɗauki ba daɗi ta hanyar kaiwa juna miyagun hare-hare tamkar waɗansu ifritai.
Duk sa'adda sarki Baddadul-ulƙas ya kaiwa naƙuwar jaruma sara da makamin dake hannun sa idan ya haɗu da takobin ta sai kaji sun fitar da sautin ƙara ƙal! Ƙal, kuma tartsatsin wuta ya tashi,
Sa'adda Baddadul-ulƙas yaga cewa ya kasa samun nasara akan baƙiwar jaruma sai ya fusata ainun kuma ya faɗa izuwa kogin tunani,
Abu na farko daya faɗo mashi a rai shine, shin mene ne dalilin da yasa sanya ya kasa samun nasara akan jarumar duk da cewar a zahiri ya fita karfin damtse da salon yaƙi, abu na biyu shine haƙiƙa idan yayi jinkirin kawar da ita sarki shaibat ya samu nasara akan Hibairu to zai riga shi mallakar zoben sihiri
Lokacin da Baddadul-ulƙas yazo nan a tunanin shi sai kawai ya zage damtse yana cigaba da kaiwa naƙuwar jaruma sara da suka cikin ɓakin zafin nama, amma sai wani tunanin da ya faɗo mashi shine anya kuwa wannan ba jaruma Amirat ba da ta fafata yaƙi da hubairu a gasar GOGA SHA FAMA ba, amma idan kuwa har ita ce ɗin akwai babbar damuwa domin kuwa komai zai iya kasance, domin binciken da na gudanar bisa halarar tsafina ya tabbatar mini dacewa da sani Amirat ta faɗi wannan gasa domin hubairu ya samu nasara.
Lokacin da ya sake zuwa nan azancenshi sai zuciyar shi ta buga da karfi, amma saboda ƙi faɗi irin ta hamshakan sarakai sai ya bar abin a ranshi.
Abangaren mai girma shaibat da sarkin sadaukai kuwa sun wanzu suna kaiwa juna sara da suka babu sassauci. Ga duk wanda ke kallon yadda artabun ke wakana zai fahimci cewa mai girma shaibat ya nunkashi a karfin damtse sau huɗu.
Abinda ke ceton hubairu shine naci da zafin nama, amma badan hakan ba da tuni shaibat ya samu nasara akan shi.
Lokacin da kowannen su yaga cewa yakasa samun nasara sai ya faɗa izuwa kogin tunani domin samun mafita.
Abu na farko daya faɗo sarki shaibat shin yaza'ayi ace gwarzon mayaƙi kamar shi ya kasa samun nasara akan Hibairu, yaushe aka samu wani hatsabibin jarumi a wannan nahiya dazai fishi karfin damtse, ko kuwa zarginshi ya tabbata na cewa hubairu ya ƙarɓi addinin Musulunci ne ,haƙiƙa idan kuwa haka ne akwai baban matsala akoda yaushe zan iya kunyata domin ma'abota addinin Musulunci hatsabiban mutane ne da babu su a wannan duniya baki ɗaya, haƙiƙa wajibi ne na ƙara zage damtse.
Aɓangaren hubairu kuwa abinda ya faɗo mashi a rai shine shin ya akayi yana tare da zoben sihirin shi amma ya gaza samun nasara akan shaibat, abu na biyu daya faɗo mashi a rai ne matsawar kana son kayi nasara, wajibi ne ka kayi amfani da waɗannan kalmomi na jaruma Amirat waɗanda ka karanta su har ka samu nasarar lashe gasar GOGA SHA FAMA.
Lokacin da dukkan suka zo nan a tunanin su sai suka canza salon faɗansu, sarki shaibat na karanta muhimman sirrikan tsafi a ranshi,
Hubairu kuma ambaton sunayen Ubangijin jaruma Amirat a cikin ranshi.
Gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya canza dole rawa ma ta canza, faruwar hakan keda wuya sai hubairu ya fara samun nasara akan shaibat, duk sa'adda sarki shaibat ya kai mashi hari idan ya kare kafin ya sake mayar da martani, hubairu ya soka mashi mashinshi a wani ɓari a jikinshi jini ya kwatanta.
Abinda shaibat bai sani ba shine bakomai ya sanya sihirin shi yaƙi yin tasiri ba sai domin zoben sihirin hubairu bazai bari nashi na yayi tasiri ba.
Kamar yadda ya wakana abangaren su hubairu,haka al'amarin yakasance ga su Baddadul-ulƙas, a inda baƙuwar jaruma ta fara samun nasara akan shi har takai ga cewa baya iya mayar da martani ya shiga yin amfani da sihiri amma sai ya zamana ya tashi abanza domin kuwa duk sihirin daya turawa jarumar da ya doshi inda take sai su zama hayaƙi su ɓace ɓat.
Ana cikin wannan yaƙi ne mai girma shaibat ya shammaci hubairu ya gabza mashi naushi a ciki, saboda karfin naushin sai da ya yayi sama tamkar an jashi da ƙugiya amma ya daɗo ƙasa yana mai amai na jini lokacin daya dunga birgima aƙasa yana mai dafe cikinshi saboda yadda yake murɗamshi.
Koda samun wannan nasara sai shaibat ya suri mashin hubairu daya faɗi can gefe guda ya taka dakyar har izuwa inda yake ya ɗaga Mashin domin ya caka akan saitin zuciyar hubairu, yana mai yi mashi murmushin mugunta.
Al'amarin daya sanya hankalin baƙuwar jaruma ya dugunzuma ainun kenan ta juya domin kaiwa hubairu ɗauki, kafin tayi taku biyu Baddadul-ulƙas ya sammace ta ya maka mata wani makami a tsakiyar kanta, take ta sulale ƙasa sumammiya babu alamun numfashi a tare da ita.
Kwatsam bazato babu tsammani sai a kaga waɗansu zaratan kibbau sun dira akan gadon bayan sarki shaibat sun faso ta ƙirjinshi jini ya dunga kwaranya yana tsartuwa tamkar an buɗe kan fanfo.
Al'amarin daya sanya shaibat ya saki makamin dake hannun shi kenan, ya kurma wawan ihu yana mai durkushewa ƙasa domin yaga wanda ya harbeshin.
Ai kuwa sai ya yi arba da ita ba wata bace face jaruma Amirat zaune a bisa kan wani matashin aljani,zaune a gefen ta na dama wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa tagaban kwatance, waɗansu tawagar aljanu marasa adadi na biye da ita cikin shigar yaƙi tamkar masu shirin yaƙar duniya, suna saukowa daga sararin samaniya.
Nan fa kowa dake wajen ya shiga da matukar al'ajabi, musamman jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI dake kwance a ƙasa magashiyan
Shi kuwa sarki Baddadul-ulƙas saboda ya matuƙar al'ajabin ya manta da baƙuwar jaruma da ya sumar ya ɗaga kanshi sama yana ƙarewa Jaruma Amira kallo cikin tashin hankali,yana mai tambayar kanshi a cikin ranshi yana mai cewa "shin kenan baƙuwar jarumar da nake fafatawa da ita ba ita ce Amirat ba, yaushe Amirat ta samu lafiya, sannan a ina ta ɗauko wannan tawagar aljanu da idanu basu taɓa ganin irin su ba.
Amsar tambayayin daya kasa bawa kanshi kenan.
Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga sarkin sadaukai Hibairu ya miƙe tsaye zumbur cikin koshin lafiya ya suri waɗansu takubba biyu ya ɗora akan wuyan sarkin shaibat ya tsinke mashi kai, kan yayi fitar burgu,jini ya dunga feshi yana kwaranya, ganagar jikin ta faɗi ƙasa rikici! .
Kaico! Haƙiƙa kafirci rayuwar banza ce, ina da ace mutum yana tsaye a wannan waje zai ga yadda gawar mai girma shaibat ta wulakanta kwance a ƙasa, dole yayiwa Allah godiya bisa ganin yadda Allah ya kawo karshen azzalumi.
Cikin wani irin baƙin zafin nama HUBAIRU ya daga tsalle sama, sai gashi yana taka kawunan dakarun dake tsaye a wajen tamkar yana tafiya a turba, cikin abinda bai gaza daƙiƙa goma ya dira a dai-dai saitin in da sarki Baddadul-ulƙas ke tsaye tun a saman ya kai mashi wani wawan sara a kafaɗar shi.
Bisa sa'a sai gashi ya sare hannun shi ɗaya, Baddadul-ulƙas ya kurma ihu lokacin da jini ke feshi daga dungulmin hanuun.
Cikin ɓakar zuciya Baddadul-ulƙas ya sanya hannun sa ɗayan ya kaiwa hubairu naushi a fuska.
Cikin zafin nama HUBAIRU ya wurƙila ya zamewa harin ya sake sanya takobin shi ya sare ɗayan hannun, Baddadul-ulƙas ya sake kurma ihu ya durkusa kasa bisa gwiwoyinshi, haka dai hubairu ya shiga sare gaɓoɓin Baddadul-ulƙas ɗaya bayan ɗaya, duk sa'adda ya sarewa wata gaɓar sai sarkar tsafin data ɗaure mahaifinshi Barde Shabbaru ta ɓace ɓat.
Lokacin da yazamana cewa kai ne kawai ya rage da gangar jiki a tare da Baddadul-ulƙas sai Barde Shabbaru ya faɗo ƙasa daga sararin samaniya babu komai na sarkar tsafin a tare dashi, kuma a dai-dai wannan lokaci ne tawagar su saurayi Hizmal suka iso wajen filin fafatawar tare da dabbobin hubairu, kuma jaruma Amirat da tawagar aljanun dake biye da ita suka sauka a turba.
Sa'adda su Hizmal suka ga gawar mai girma shaibat a ƙasa, kuma suka yi arba da sarki Baddadul-ulƙas cikin mummunan yanayin dake tsakanin Rayuwa da mutuwa, sai suka cika da matukar mamaki da farin ciki.
A bangaren Dabbobin hubairu kuwa koda sukayi arbda da Baddadul-ulƙas sai kawai suka afka masa suka shiga yaga sassan jikin shi kafin wani lokaci babu wani abu na jikinshi da basu cinye ba face kans hi.
Kaico! Haƙiƙa mutuwar azzalumai ba ta da daɗin kallo, yanzu dai gashi duk kasaita da dukiya, sihiri gami da jarumtaka da sarki Baddadul-ulƙas ke takama dashi sun zamo a banza yayi mutuwar wulakanci, wacce dabbobi ne ma marasa daraja suka kashe shi wanda shi bai ɗauki rai na ɗan adam a bakin komai ba.
Cikin matukar kwaɗuwa hubairu ya durƙusa a gaban baƙuwar jaruma domin yaga a wane hali take ciki, amma sai yaji taja dogon Gwauron numfashi ta miƙe tsaye cikin koshin lafiya, dai dai lokacin da jaruma Amirat ta iso inda take tsaye suka rungume juna cikin matuƙar farin ciki, koda ganin sai hubairu ya riga izuwa inda mahaifinshi yake tsaye suka rungume juna suna masu fashewa da kukan farin ciki.
A sannanne gumbiya Zarifa dake tare Amirat ta hango mahaifinta sarki uslaim don haka sai ta ruga gareshi suka rungume juna suna masu zubar da hawayen farin cikin sake saduwa da juna,
Ashe shi ma aljani Marhutul-Azab ya lura cewa wanɗannan tawagar aljanu da ke tare da Amirat ba wasu ba ne face zuri'arshi dake bukatar jarumi Hibairu ya ceto su daga fadar sarkin bokayen Duniya, kawai sai ya ruga garesu cikin farin cikin saduwa da juna.
Bayan komai ya samu lafawa kuma jama'ar gari sun taru a wajen lokacin alfijir ya keto sai jaruma Amirat ta shiga yiwa jama'a bayanin yadda akayi ta samu nasarar zuwa fadar sarkin bokayen Duniya a cikin sa'o'i kaɗan har ta ceto rayuwar gimbiya Zarifa yar sarki uslaim tare da zuri'ar aljani Marhutul-Azab da ruhukansu dake ajiye a cikin akwatun shiri, tun daga farko har ƙarshe ta zayyanewa jama'a.
Sa'adda jama'a suka ji wannan bajinta gami da karfin Ubangijin halitta sai suka kara cika da mamaki da imani da Allah (SWT).
Jarumi Hibairu da mahaifinshi Shabbaru ne suka fara ƙarbar kalmar shahada a hannun Amirat, sannan jaruma sunaila, Hizmal, Abidatul-auliya,Nuwairat,yaro Humair makaho, matsafi shubairu, budurwa Nihla,sarki shazwan da tawagar bokayen shi,gimbiya, boka ƙarzum, aljani Darmanu tare da tawagar aljani Marhutul-Azab sai dukkan jama'ar gari da suka bayyana a wajen,
A wannan waje ne wani abu ya faru domin kuwa bayan sarauniya Abidatul-auliya da masoyinta matsafi shubairu sun faɗi kalmar shahada nan take suka ji wannan cutar kuturta dake tsagin jikin su ta daina yi musu ciwo yayin da suka duba kuwa sai suka ga babu komai tamkar cutar bata taɓa wanzuwa ba, yaro Humair makaho kuwa shi sai yaga idanunshi yana iya ganin kowa alamar ya samu lafiya.
Nan fa suka ji sun ƙara imani da ubangijin musulunci.
Kashe gari tun da duku-dukun safiya fadar margayi shaibat ta cika ta batse da jama'a babu masaka tsinke domin yin naɗin sarautar hubairu sarkin sadaukai tare da ɗaurin aurenshi da Budurwa Nihla, sarauniya Nuwairat, jaruma Amirat da gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat tare gumbiya Rumaisat yar sarki shuraih,tare naɗin wazirin shi sarkin yaƙi abu-Damraz bayan shima ya karbi addinin Musulunci,
Saurayi Hizmal suka zai auri jaruma sunaila da baƙuwar jaruma ba wata bace wannan baƙuwar jaruma ba face amrita wacce suka kasance Hassana da Husaini ga jaruma Amirat, lokacin da fuskar ta ta bayyana a fili sai da kowa ya cika matuƙar al'ajabi bisa ganin yadda kamannin baƙuwar suka zo ɗaya sak da na Amirat tamkar an tsaga kara.
Sarki shazwan kuwa zai auri gimbiya yar uwa ga jaruma sunaila,
Sarauniya Abidatul-auliya kuwa da matsafi shubairu masoyin ta.
Sarki Hamza mahaifin jaruma Amirat ne ya zamo waliyin amaren, wani hadimin shi mai suna Salman kuwa ya zamo waliyin angwaye.
Bayan anyi shagin ɗaurin aure da naɗin sarauta dukiyar da za'a bawa hubairu ta nasarar cinye gasar GOGA SHA FAMA kuwa sai yayi umarni aka dunga rabawa talakawan gari tare bawa dukkanin bayin kurkuku da aka 'yan tasu.
Haƙiƙa anyi gagarumin shagalin da ba'a taɓa yin kamar shi ba iya Tsawon wanzuwar birnin madinatul-shaja'a, domin kowa ya wadata da arziki mai tarin yawa.
Bayan mako guda ne da faruwar hakan sai sarki Hubairu yayi umarni ga waɗannan aljanu yan uwan aljani Marhutul-Azab suka ɗauki Sarauniya Abidatul-auliya da angwanto, sunaila da nata aka kai su izuwa kasashen su,
A inda matsafi shubairu yazama sabon Sarkin birin Tehran,saurayi Hizmal kuwa yazamo sabon sarkin birin Baitul-mausul, bayan ya warkar da sarki ishwar mahaifin jaruma sunaila daga lalurar dake damunshi bisa ikon Ubangijin musulmi batare da anyi amfani da tsumin tsafin dake fadar sarki bokayen Duniya ba , yarima ubaiyu ya zama wazirinshi, yarima zaiyum kuwa ya zama shugaban majalissar sarki bayan sun karɓi addinin Musulunci, kuma suka janye gabar dake tsakanin su da yar uwar su jaruma sunaila.
Sarki shazwan da amaryar shi Gimbiya Hushriba yar uwata ga sunaila suka kasance cikin aminci,
Lokacin da aljani Darmanu ya ɗauki sarki uslaim, boka ƙarzum da gimbiya Zarifa bai zame ko ina sai tsakiyar birnin baharen ya sauka a turba,
Nan fa farin ciki ya kama jama'ar bisa dawowar gimbiya Zarifa da sarki, kuma a wannan rana aka ɗaura auren boka ƙarzum da gimbiya Zarifa
Sarki Hamza mahaifin jaruma Amirat ya koma izuwa birnin madinatul-salam bayan ya aika da malaman addini izuwa dukkan kasashen daban-daban.
Yaro Humair makaho ya ci gaba da kasance tare da sarki Hubairu, daga wannan rana hasken musulmi ya mamaye ko ina a duniya, a kawo KARSHEN ZALUNCI da azzalumai, adalci ya cigaba da wanzuwa.