You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng *KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

_Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai, godiya ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa
mai komai da ya ba mu aron rai da lafiyar da mu ka kawo wannan lokacin da rai da
lafiya. Ina roƙon Allah yadda ya bani ikon fara rubutu littafin nan lafiya da
aminci Allah ya sa na gama lafiya, Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani
al’umma baki ɗaya, ya Allah kar ya bani ikon rubutu ɓarna ko abinda ya saɓa addinin
mu amin._

_Wannan labari mai suna KIRAN RABO ƙirƙirarre ne, ban yi shi dan wani ko wata ba,
in ya yi kama da labarinki ko labarinka ayi haƙuri rashin sani ne._

_Ban yarda a canja min labari zuwa wata siga daban ba, ban amince a juya min labari
zuwa wata fuska ba ba tare da izini ba!._

*SHIMFIƊA.*

_*Hausawa suna cewa da mutuwa, aure da arzuƙi ƴan uwan juna ne. Ni kam na ce a haɗa
da RABO domin shima yana daga cikin waɗanan ukun. RABO in ya yi kira ko kana cikin
mahaifiyar ka sai ka amsa shi ka fito duniya. KIRAN RABO ya kan canja ƙaddara daga
baƙa zuwa fara, KIRAN RABO ya kan mayar da wasa ya zama gaske, KIRAN RABO yana
mayar da abinda ba zai yu ba ya zama mai yuwa. Wani yana shigowa rayuwar wani dan
ya zama silar amsa KIRAN RABON sa, wani yana fita daga rayuwar wani dan hakan ya
zama silar amsa KIRAN RABON SA. Ya ake gane rabo ya yi kira? Ba a ganewa, sai bayan
Allah ya yi ikon sa a kai ake fahimtar daman can kiran rabon ka amsa. Ana amsa
KIRAN RABO a lokacin da ba a san an amsa shi ba, ba a jin kiran da kunne balle a
kasa kunne a nutsu dan a saurari lokacin da rabo yake kiran ka. Kamar yadda bawa ba
ya sanin lokacin da mutuwar sa, lokacin auren sa, lokacin da ƙaddara ta kira shi
haka ba a sanin lokacin da RABO yake kira sai dai ka tsinci kan ka a lokacin da ka
amsa. KIRAN RABO lokaci ne dashi kamar dai yadda mutuwa take da lokaci!.*_

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

*Book 1*
*P 01*


_"Tsinanne ɗan iska, a haka zaka ƙare rayuwarka. Yara duk sun zama ɓata gari saboda
rashin kulawar iyaye"._
_"Ka daina furta irin wannan maganar don Allah, in kana aibata yaran wasu kamar na
ka ka ke aikabata. Mun haifa mu ma, don Allah ka daina ba hali ne mai kyau ba."_

Numfashi ta sauke tunawa da abinda ya wuce a shekarun baya, sai yanzu take fahimtar
illar da take cikin irin wannan kalamai da iyaye suke yiwa yaran da ba nasu ba. Sai
yanzu take fahimtar dalilin mahaifitarta da a kullum take kwaɓar mahaifinsu ga
barin aibata ƴaƴan wasu da yake yi. Tabbas yanzu ta fahimta tunda gashi reshe ya
juye da mujiya.

A zaune take a ƙaramar harabar gidan akan sallaya babba mai girma. Ita da wani
mutum ne a zaune amma gabaɗaya hankalin ta baya tare da shi ta tafi tunanin abinda
ya wuce saboda abin ya zo akan gaɓar da zata yi tunanin ne. Kallon farko zaka yi
musu ka fahimci zaman taɗi suke yi kamar yadda samari da ƴan mata ke yi, ko yadda
zawarawa suke yi.
A yadda take kallon sa yana magana zaka tabbatar da kalaman da yake faɗa basu yi
mata daɗi ba sam, fuskarta mai yawan fara'a ta canja gabaɗaya ta cushe waje ɗaya
saboda yadda kalaman suke sosa mata rai. Shima kallon ta yake yi cikin ƙarfin
guiwar sanar da ita saƙon da yake zuciyarsa, domin abinda yake ransa kenan kuma shi
yake faɗa kuma ya zama dole ta sani.

Babbar mace ce matashiya wacce a a shekaru zata kai shekaru talatin da biyar a
duniya, fara ce irin haske mai ja kaɗan, tana da haske sosai da manyan idanu masu
haske da ɗaukar hankali lokaci guda. Tana da dogon hancin da ya ƙarawa fuskarta
kyau. Kai tsaye in ka kalle ta baza kace ta kai shekarun da take kai ba saboda
ƙaramin jiki ne da ita, sannan ga madaidaicin kyaunta da yake ɗaukar hankali har ba
a fahimtar shekarun ta saboda hakan.

Jin Muktar ya gama maganar tasa sai tayi murmushin yaƙe wanda ake kira da yafi kuka
ciwo ta kalli wanda yake zaune kusa da ita cikin murya mai sanyi ta ce, "Abinda ka
ke tunani kaima a kaina kenan?." Yayi murmushi ya ce, "abu ne a bayyane ai Aysha.
Ke kin san da gaske nake ina so na aure ki, amma maganar da take yawo a kan ki bana
tunanin iyayena zasu amince da auren ki. Shiyasa na zo ayi ta ta ƙare kawai."

"Yanzu zuwa kayi ka ce min ka fasa aure na kenan?" Ta tambaya tana kallon sa. Duk
da ba yau aka saba ba, amma yanayin yadda yake magana yana bata mamaki.
"Kusan Hakan." Ta girgiza kai ta ta ce, "to ka tashi ka koma ta inda ka biyo, saƙon
da ka ke son isar min ka isar sai ka je ko?."

Ya bi fuskar ta da kallo ya ce, "ki yi haƙuri ba daga ni bane, in magana tayi yawa
akan mutum ko kana son alaƙa dashi dole ka dakata. Na so auren ki amma zancen nan
ya zaga ko ina. Har da masu cewa shiyasa baki aure ba saboda duk abinda miji yake
yiwa matar sa ƙanin ki OMAR yana yi miki."

Ta rantse ido cikin ɗacin kalmar ta ce, "kar ka sake magana akan ƙanina, kaje tunda
dai ka fasa ai shikenan ko?." Ta faɗa cikin rashin damuwa dan ta saba indai fasa
aurenta ne. Yayi dariyar rainin hankali ya ce, "Daman an ce bakya son laifinsa,
daman an sanar dani ko me za a ce baza ki taɓa ganin laifinsa ba, ke lallai ga mai
ɗan uwa. Taƙadarin yaron da ya adabi mutanen Kano gabaɗaya, wai shi ki ke jin
haushi dan an faɗi magana a kansa saboda kawai ɗan adam baya son gaskiya."

"Ka gama!?."

Ita dashi a tare suka juya zuwa inda suka ji anyi maganar zuciyar ko wannen su ta
buga a take. Wara idanu tayi ganin wanda idanunta suke gani dan gabɗaya bata so
yazo ya riski maganar ba, shikenan yanzu ƙaramin abu zai koma gingimeme a wajansa.

Yana zaune akan ɗan tudun ƙofar gidan ya harɗe ƙafafunsa, ga ƙatuwar wuƙa a
hannunsa yana shafa ta a hankali yana kallon ƙasa kamar ba shine ya yi maganar ba.
Juyo idon sa yayi ya watsa masa wani kallon da ya saka gaban Muktar ya faɗi nan
take ya shiga hankalinsa. Wani irin kallon raini da ƙasƙanci yake yi masa yana
taune laɓɓansa cikin ɓacin rai. Wuƙar ya fara wasawa a jikin ƙaramin dutse da yake
kai a nutse cikin salon mugunta.

Saurayi ne wanda a shekaru bai wuce talatin ba, kallo ɗaya zaka yi masa ka shaida
kamar da ya ke yi da Aisha, duk da kyuansa ya fi fitowa akan nata amma suna kama
sai dai banbacin halitta ta mace da namiji. Dogo ne mai cikar zati da kuma
kyakykyawar halitta, kallon farko zaka yi masa ka shaida kwarjininsa, dan lokaci
ɗaya zai cika maka idanu tsoronsa zai mamaye maka zuciya har ya kai mutum ga sauke
idanu ƙasa. Namiji ne wanda ake kira na miji, ƙaƙƙarfa kuma mai jikin ƙarafafa, sai
ka rantse da Allah Aisha ƙanwarsa ce saboda gabaɗaya ya zama shine yayan itace
ƙanwar. Yana da haske sosai, fuskarsa tana da haske irin sosai ɗin nan, yanayin
rigar da take jikinsa ƙarama ce zaka hango fatar jikinsa da ta kasance fara tas har
tafi fuskarsa haske.

Yana da manyan idanu sosai wanda ake kira kwala-kwala masu ban tsoro, idanunsa
zagayayyu ne masu girma, in ya wara su yana magana kamar zasu fito saboda girman
su. Kallo ɗaya in ka yiwa idanunsa baza ka so ka sake kallon idon ba musamman in
ransa a ɓace ya ke. Yana da hanci amma ba irin mai tsayin nan sosai ba kuma ba
gajere ba ne, yana da zagayye cikakken baƙin gashi a fuskarsa, wanda suka ɓoye
ƙuruciyar sa suka bayyanar da kwarjini a tare dashi.

Yana da kwantaccen gashi a kansa wanda ya tara, in ka kalli gashin lokaci ɗaya zaka
fassara shi a gashin buzaye ko fulani, dan yadda ya ke a kwance baƙi zai saka ka
tabbatar ba gashin hausawa ba ne. Yana da yalwar gashin gira irin wacce take a
cushe gata baƙa sosai. Haka fuskar sa itama a cike take da gashi mai yawa wanda
kana gani ka san baya samun gyara yadda ya kamata.

OMAR kenan! wanda ake yiwa laƙabi da DAMISA wasu kuma su ce MADUGU, wasu
kuma ce JAN WUYA.

Ɗan daba ne lamba ɗaya, ɗan daba ne mai lasisi wanda ya samu goyan baya daga iyayen
ƙasar wato ƴan siyasa. Duk da dabancin ta sa mai tsari yake yi amma yana daga cikin
ƴan dabar da ake matuƙar tsoron su a faɗin Kano. Kaf yankin ƙofar nasarawa shine
shugaba, babu wani ɗan daba da zai aikata ba daidai ba a wannan area sai Damisa ya
sani. Kuma saboda shine kawai ake jin tsoron yin faɗa a arear saboda in ya tashi
ɗaukar fansa bai iya ba, shiyasa ba a cika koda sace-sace a unguwar ba saboda ya
zama kamar kura da nama ya shigo zai kama. A shekarun baya ya yi faɗace-faɗace duk
da bai taɓa kisa ba amma ya yi ƙanin kisa, a yanzu ne ya canja tsari da salon
dabancin shiyasa wasu mutanen suke gani kamar ba ɗan daban gaske bane.

Aisha da take zaune ganin Muktar ya firgita da ganin ƙanin nata cikin bada umarni
ta ce, "Omar ka tashi ka shiga gida babu ruwan ka." Jin abinda Yayar ta sa ta ce
sai ya miƙe tsaye yana kallon ta, shigowa ciki yayi sosai yayi kamar zai wuce ta
kawai ya ɗuka ya damƙi wuyan Muktar ya miƙar dashi tsaye.

Nan take jikinsa ya soma, yana kallom Omar yana karkarwa dan daman an faɗa masa
Omar indai akan Yayarsa ne babu abinda bazai yi ba. Omar ya kalli cikin idonsa
cikin dakakkiyar muryarsa irin ta jarumai mazajen gaske ya ce, "maimaita abinda ka
faɗa mata naji." Jikin Muktar rawa yake yi sosai, ji yake kamar ya yi fitsari
saboda tsoro ya kasa furta komai saboda tashin hankali.

Aisha da take tsaye itama t ce, "Omar meye haka ne? Ka sake shi!?" Ta faɗa cikin
ɗaga murya. A fusace ya kalle ta ya ce, "DIDI ki matsa baya, babu abinda zai hana
ban farka bakin wannan mutumin ba. Nan gaba na ga da wanne bakin zai furta irin
abinda ya ce yanzu" ya dawo da kallon sa ga Muktar shi ya ce, "Tunda ya tako har
cikin gidan mu babu abinda zai hana ban ɗauki mataki a kansa ba. Ko na datse masa
harshe, ko na farka cikinsa."

"Wayyo Allah na shiga uku!. Aisha don girman Allah ki taimake ni, ki ce ya ƙyale
ni, ki taimaka min kar......" maganar da ta maƙale saboda wuƙar da ya kawo kusa da
wuyan sa ya ce, "kana cigaba da magana wallahi sai dai uwar ka ta haifo wani."

Ɗif ya yi ya kulle bakinsa da jikinsa yana karkarwa sosai nan da nan hawaye suka
fara ambaliyya daga idanunsa saboda tsoro. Didi ta ƙaraso wajan ta riƙe hannunsa ta
ce, "Omar ka ƙyale shi ya tafi na ce ko?."

"Bazan ƙyale shi ba. Ba shi yana da zarrar zuwa har gidan nan yake cewa ya fasa
aurenki ba?
Inda iya wannn kalmar ya faɗa da sauƙi, amma har magana mara daɗi ya faɗa a kanki.
Didi ko duniya ce zata taru yau babu abinda zai hana ban farka cikin mutumin nan
ba."
"To ba ni aka faɗawa magnar ba ina ruwan ka...? Malam ka cika shi ya tafi bana son
wannan ɗabi'ar" Ta faɗa da ƙarfi tana son cire hannun Omar daga wuyan Muktar amma
ta kasa.

Kallon Muktar ɗin ya yi da yake hawaye kamar ƙaramin yaro jikinsa na rawa sosai ya
ce, "ka ci albarkacin ta a yau ka sha, amma kar ka sake idanuna ya sake ganin
fuskar ka, In kayi wannan gangancin zaka yi dana sanin zuwan ka duniya." Kai yake
ɗaga kamar ƙadangare saboda tsoro Omar ya ce, "baka da baki!?." Yadda yayi maganar
cikin tsawa ya ake firgita shi ya ce, "na....ji....ka yi....ha...ku....ri."

Omar ya cika masa wuya ya kalle shi ya ce, "durƙusa ka bata haƙuri." Babu ɓata
Lokaci ya zube a ƙasa ya ce, "Ki yi haƙuri Aisha, na tuba ki yafe min." A fusace
Omar ya ce, "sunan ta ka ke faɗa kai tsaye babu girmamawa? Sa'ar ka ce?." Jiki na
karkarwa Muktar ya ce, "ki yi haƙuri Mama, Allah ya wuci zuciyarki."

"Haifar ka tayi da zaka ce mata Mama!?" Ya sake faɗa yana cakumar rigarsa. Muktar
ya fashe da kuka mai sauti ya ce, "Ki yi haƙuri Anty, ki yi haƙuri don Allah." Omar
ya sake shi ya nuna masa ƙofa ya ce, "bar nan." Ai bai sake magana ba ya fita a
guje ko takalman sa bai ɗauka ba saboda tsoro.

Omar ya kalli inda Didi take ganin bata wajan ya san ta shiga gida ya kalli yaransa
da suke ƙofar gida ya ce, "duk ranar da ya shigo area nan kar ya fita da lafiya."
Dukkan su suka haɗa biki suka ce, "An gama Damisa, a fito Lafiya Magudu uban
matsiyata." Ya jiyo idanunsa masu ban tsoro ya kalle su ya ce, "Zaku iya wucewa
anjima sai ku zo" yana gama faɗa ya shiga gida yana jin su suna amsawa.

Yana shiga tsakar gidan Didi ta tare shi ta ce, "Omar me yasa ka ke min
haka ne? Omar me yasa ka ke son saka min ciwo ne wai?." Zai yi magana ta ɗaga masa
hannu ta ce, "kar ka ce komai sai na baka dama. Ya ka ke so nayi ne? Me ka ke so ka
zama ne Omar? Yau gabaɗaya satin ka biyu da fitowa daga prison bayan ka shafe kwana
goma a ciki, so ka ke ka kuma komawa ne?."

"Didi...." Ta katse shi ta ce, "ba wani Didi, babu wani Didi kar ka ƙarasa. Omar me
ka ke son zama ne don girman Allah? Ɗan ta'adda ka ke so ka zama ko me? A gaban
idona ka dinga zancen zaka farkawa wani ciki?."

"Duk abinda ya faɗa miki naji, in ya fasa auren ki ya faɗa cikin magana mai daɗi
mana sai ya faɗa da wulaƙanci?. Na rantse da girman Allah ba dan ke ba sai na yiwa
bakinsa illa."

"To waye zai aure ni bayan kowa tsoron ka yake ji? Da irin wannan dabi'ar taka ka
ke so na yi aure Omar?. Wanne iyaye ne zasu amince ɗansu ya aure ni bayan ina da
ƙani irin ka?." Ganin idon Yayar tasa ya fara kuka da hawaye sai ya lumshe idanunsa
ya buɗe ya kalle ta ya ce, "Didi don ina so ki yi aure ba haka yana nufin zan juri
ko wacce kalma a kanki ba, Wallahi ko waye yayi ƙoƙarin ɓata miki rai shima sai
nasa da na danginsa ya ɓaci."

Didi ta ce, "waye yace maka raina ya ɓaci?Gaskiya ya faɗa Omar kowa a unguwar nan
kallon da suke min kenan. Ban taɓa aure ba muna zaune da kai a gida ɗaya gani suke
kamar ni da kai wani abun mu ke aikatawa mara kyau shiyasa rashin auren baya
damuna. Shekaran jiya matar Alhaji Yusuf ni da ita ta faɗa min ido cikin ido. Kaga
na damu...? Ban damu ba saboda ni na san ba haka bane, suna yiwa abun kallon baibai
ne, kuma babu wanda ya isa ya ce zamana da kai a gidan nan akwai haramci, sai dai
su yi tunanin banza su daina. Aurena kuma lokaci ne kawai bai yi ba."

Bai yi magana ba kallon ta yake yana kuma hakaito kamannin matar da ta ambata a
idanunsa yaji ta ce, "kowa tsoron zuwa ya ce zai aure ni yake yi saboda kai Omar,
kaf ƙofar nasarawa da kewaye tsoronka suke ji iya kallon idanunka ma tsorota su
yake yi balle ka yi musu magana. A haka ka ke cewa burin ka nayi aure?."

Ya sauke numfashi yana kallon ta kafin ya dafa kafaɗarta ya ce, "Didi lokaci ne
kawai bai yi ba, in yayi zaki yi aure. Kawai bazan yarda ki auri ɗan kutmar uba
bane, dan ko kina auren nasa ya raina miki hankali ni mai iya ganin bayan sa ne."

Ta cire hannunsa daga kafaɗarta ta ce, "Omar ka daina furta wannan kalmar, ka daina
cewa zaka ga bayan mutum don Allah ka daina."

Leɓensa ya ciza ya kalle ta ya ce, "Didi kamar uwa ki ke a wajena, in na kira ki da
uwata ban yi laifi ba. Ina so ki sani babu wani ƙato ɗan ƙatuwa da ya isa ya ɗaga
miki yatsa ban karya shi ba, kuma shi wannan da ya fita na ƙyale shi ne yanzu
saboda ke amma ai zamu haɗu ko da sanayya ko da ganganci. Itama matar Yusuf ɗin
zamu gauraya" yana faɗa ya juya ya shiga wata ƙofa da take farko a cikin gidan.

Idanu ta wara waje jin abinda ya ce cikin ɗaga murya ta ce, "Omar kar ka yiwa matar
nan komai fa, matar aure ce kar ka sake ka yi wannan gangancin!." Bata ji maganar
sa ba daman ta san bazai ce komai ba.

Waje ta samu ta zauna tayi tagumi hawaye na sakkowa daga idanunta. Tana matuƙar son
ƙaninta Omar, tana matuƙar ji dashi bata so taga wani abun ya same shi. Amma Omar
ya wuce tunanin mai tunani, duk yadda ka ke tunanin rashin jin Omar ya wuce haka.
Baya ji tun yana yaro, baya bari in aka ɓata masa tun bai kai haka. Yana da zafi
sosai, iya kallon idanun Omar zai saka ka firgice balle ka buɗe bakinsa ko ya yi
maka barazana.

Kaf unguwar tsoron sa ake ji ko almajiri baya iya shigowa gidan yayi bara saboda
dashi. Babu maƙociyar da take shigowa gidan saboda shi, baya ɗaukar raini kuma
yason munafurci da gulma. Bashi da ɓoye-ɓoye kuma girman ka baya hana shi magana,
shiyasa gidan kullum shiru sai Didi kawai ita kaɗai saboda kowa tsoron sa yake ji
ba a iya zuwa. In kaga mutane a gidan to tabbas baƙi ne, shima haka zai ta cin
magani yana zare musu idanu dan ya tsani ya ga anyi baƙo ko baƙuwa.

Hawaye taji yana share mata sai ta kalle shi bayan ya canja kaya zuwa ƙananun kaya
ya tsuguna a gabanta ya ce, "duk wanda ya zama silar zubar hawayen ki sai na zama
silar zubar jini a jikinsa, Didi kin san bana kisa, ban taɓa kashe rai ba. Amma
akan hawayenki zan iya farke maƙworagon ko waye" ya faɗa yana wara idanunsa yana
kallon ta.

Murmushi kawai tayi ta miƙe tsaye ta ce, "baza ka ci abinci ba?." Shima ya tashi
tsaye yayi yana kallon ta ya ce, "Zamu zo anjima dasu goje mu ci, yanzu zan je na
dawo."
"Ina zaka je?."
"Wani ɗan aiki zan je nayi."
"Wanne aiki ne?." Ya kalli idanunta ya ɗauke kai dan baya yi mata ƙarya kuma shi
baya ɓoye mata komai na sa. Ya ce, "mutanen Yakasai ne suka ƙwacewa wani na mu waya
sannan suka kashe shi, Ke kin san sai naje mun zauna dasu."

Ta girgiza kai tace, "don Allah Omar...." Ya dakatar da ita ta hanyar faɗim, "Didi
sai na je fa, amma nayi miki alƙawari bazan yi faɗa ba indai ba sune suka so hakan
ba. Magana kawai zamu je mu yi domin na ja musu kunne akuyar su ta kiyayi ramata."

Kallon sa take yi bata ce komai ba shima haka kafin ya ja baya ya ɗauke idanunsa
daga kanta ya ce, "Zan dawo yanzu Didi." Yana faɗa ya fita cikin takunsa na ƙasaita
ya bar ta a tsaye tana kallon sa.

Hawaye ta share ta ɗaga kai sama bayan ta ɗaga hannu ta ce, "Ya Allah ka kiyaye
min marayanka, Allah ka kare shi. Ya Allah ka sassauta masa wannan zuciyar da yake
fama da ita, ya Allah ka cire masa son wannan ɗabi'ar daga zuciyarsa." Ido ta share
tare da sauke ajiyar zuciya ta shiga falo.


•••••••••
*ABUJA*
*SENATOR SAGIR SANI SHATIMA RESIDENT.*

Senator Sagir shine Sanatan Kano ta tsakiya mai ci yanzu, wayeyen mutum ne mai
ilimi da kuma son ilimin boko. Kaf ma'aikata gidan sa daga masu degree sai masu
master, daƙyar ake samu ya ɗauki mai kwalin diploma aiki, saboda a ganin mai wannan
matakin karatu jahili ne bai san komai ba, shi kuma yana ganin aiki da wanda bashi
da ilimi ba ya haifar da komai sai dana sani. Kaf masu aikin gidan mata da zama sun
iya english, in suna turanci ba ka ce masu aiki ba ne saboda haka ne tsarin mai
gidan. Ya raina wanda bashi da ilimin boko, yana kuma ganin wanda bashi da ilimin
boko babu inda zai je a rayuwa sai dai ka ƙare a bara.

Ba ya mu'amala da wanda ba shi da ilimin boko, in kuwa ya yi to ta zama dole kuma
sai dai a ɓangaren siyasa. Bai damu da ilimin addinin ka ba, shi dai indai kana da
na boko ko kafiri ne kai ka fiye masa musulmi.

Matar shi ɗaya tal wacce yake so kamar rai, yana da yara guda uku. Nabil, Narma sai
Najwa.

Babban falo ne mai kyau da tsari, kai da ka kalli falon ka san na manya
mutane ne na na ƙananun mutane ba, ya tsaru iya tsaruwa duk da babu tarkace a cikin
sa. Yanayin tsarin sa zai saka ka tabbatar da falon ba na ƙananun mutane bane ba.
Wata kyakykawar budurwa ce fara tas a zaune a falon, sanye take da riga iya guiwa
kanta babu ɗankwali hakan sai ya bayyanar da yalwar sumar da take da ita. Tana da
kyau wanda a kallo ɗaya zaka fahimta saboda kyawun halittar da Allah ya yi mata.

Barr Narma Sagir Sani shatima kenan wacce ake yiwa laƙabi da Barr Nass. Second born
a wajan Senator Sagir, ƴar kimanin shekaru ashirin da shida. Bata da ƙiba daga sama
amma Allah ya yi mata baiwar ƙira mai kyau daga ƙasa, tana baiwar sura wacce in ka
kalla za ka so ka sake kallo saboda yadda ta tsaru. Barr Nass manager director ce a
ɗaya daga cikin kamfanin mahaifin ta. Sananniya a social media musamman a instagram
da X.

"Daddy Ina so zan shiga Kano next week" ta furta cikin muryarta irin ta ƴan
gayu ƴaƴan Daddy da Mummy.

Kallon ta ya yi a lokacin ta kai abinci bakinta ya ce, "me ake yi a Kano?." Ta ɗan
yi farrr da idanu wanda hakan ya zamar mata jiki ta ce, "arewa24 sun yi inviting
ɗina then..akwai bikin friend ɗina Samra kamar ma ka san Dad ɗin ta. Bashir na
Gwaggo ne babanta."

Dad ya kalle ta yana girgiza kai ya ce, "yes, i knew him. But, how many days are
you planing to spend in Kano?." Ta ajjiye spoon ɗin hannunta ta ce, "Uhumm two to
three weeks. At least two weeks." Daddy ya girgiza kai bayan ya haɗe fuska ya kalle
ta sosai ya ce, "Narma!." Jin yadda ya kira sunan ta sai ta kalle shi ta ce, "Dad."
"You know i don't want you to go to Kano, right?."
"Yes dad, but it's necessary. And dad I'm not a little gril fa, I know what I'm
doing. Zan iya kare kaina daga duk abinda ka ke gudu, so just calm down." Kallon ta
yake yi kafin ya kalli wacce take zaune a gefe sa ya ce, "Kina Jin abinda take cewa
baza ki yi magana ba?."

Mum ta kalle shi ta ce, "wannan maganar tsakanin ku ne babu ruwana a ciki. Ta faɗa
min batun zuwa Kano nace sai ta jira umarninka."
Dad ya kalle ta ya ce, "Narma kin san abinda ya faru last a zuwan ki kano ko? An yi
attacking ɗinki kin tuna wannan? Ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu bamu san meye
ya faru ba."

"Yes Dad ban manta ba, amma hakan ba zai saka na daina zuwa Kano saboda wanda ban
san su ba." Dad ya bita da kallo kafin ya ce, "well, I will think about this."
Kamar zatayi kuka ta ce, "Dad don Allah kar ka ce bazan je ba."
"I'm not saying that, but sai nayi tunani."
"Okay, thank you" ta faɗa tana tashi ta hau sama tana danna waya.

Senator ya bi ta da kallo bayan ta wuce ya kalli Maman ta ya ce, "Kina ganin ya
kamata na barta ta je Kano?." Mum ta ce, "yeah ka barta mana, na san Samra ƙawarta
ce sosai bai kamata ace bata je ba. Sai ka bata security su kula da ita." Ya
girgiza kai ya ce, "Okay zan san abinda zan yi" ya faɗa yana tashi shima ya saman
yana tunani. Anya zai iya barin Narma taje Kano? Garin da aka kusa hallaka masa ƴar
da yafi ƙauna a duk duniya?. Ko da zai bari taje sai ya haɗa ta da wanda yake
tunanin zai kular masa da ita sosai.

Narma ce ta sakko cikin shirin fita, sanye take silk adire kalar ja wanda aka yi
masa ɗinki mai ɗaukar hankali. Gabaɗaya ya bi jikinta ya kwanta yana bayyanar da
zallar surar da take jikinta, hatta bra ta da saka ana ganin shatin

Please Login or Register in order to submit comment