You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[8/11, 4:52 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*
*NA*
*AISHA GALADIMA*
*DEDICATED TO*
*HASSAN ATK*
*Tukuici*
Ga
*BATUL ADAM JATTAKO*
*HAJ MARYAM SAKATARIYA*
Bissimillahi Rahamani raheem
*PG 1*
zaune take a cikin dakin nasu Tana shafa powder a kyakyawar fuskar ta bayan ta
kammala ta dauki lipstick ta shafa a madaidaitan labbanta ta dauko turarenta meena
me sayyayan kamshi ta shafa daga nan ta kara kallon madubi tana ma kanta murmushi
se ta Mike tsaye ta nufi wardrobe din kayanta ta fiddo gogaggun uniform dinta ta
saka kalar purple and white daga can waje naji wata murya ta na fadar "Amal mun fa
yi latti ki fito mu tafi ko na wucewa ta dan bazaki sani shan na jaki ba,
Shiru tayi bata amsa ta ba har se da ta dago labulen dakin Tana kallonta tace "
Amal mun fa yi latti ki fito mu tafi" .
Ta shi tayi ta dauko Jakarta tana murmushi Tana "yi hakuri Ramla ai na shirya yau
da wuri zamuje ko?"
fitowa sukayi gwanin sha'awa duk da uniform din nasu ya tsufa amma saboda kula da
wanki da guga da suke sha farat daya baza ka ce tsoffin kaya bane suna fitowa suka
nufi wani madaidaicin kitchen wata matsakaiciyar mace zaune akan kujera tsuggune
tana suyar kosai ga bokitin kunu a gefenta duk'awa sukayi suna fadar "umma ina
kwana"
tace "lafiya lau har kun shirya?
Suka ce eh tazuba ma kowa kunun a karamin kofi da kosai a plate ta Mika musu
Da sauri sauri suka gama suka wuce saboda har takwas ta wuce
Suna tafe suna tunanin haduwarsu da malam bala
Har suka isa bakin makarantar suna sauri suna shiga kuwa suka tarar da shi rike da
bulala me baki biyu a hannu
Tuni Amal ta fara fidda kwallah!!!
*IN NAGA RUWAN COMMENT INCI GABA*
*DAGA AL 'KALAMIN AISHA GALADIMA*
[8/12, 7:51 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*
*NA*
*AISHA GALADIMA*
*DEDICATED TO*
*HASSAN ATK*
*DUBUN GAISUWA*
*GA*
*HUSSAIN ATK*
*PG 2*
Ai ko Basu tsira ba se da malam bala ya sauke masu bulala biyar biyar sannan suka
wuce aji............
➿➿➿➿
Wani cikkaken saurayi ne ya fito daga wani gida yana rufe kofar gida da key duk da
gidajen wurin kusan kamarsu daya kamar estate ne daga bayansa wani kyakyawan
saurayi yana fadar "captain kayi sauri fa oga jiranmu yake yace mu same sa a office
juyowa yayi yace "to 'Dan kanzagi muta fi ko duk kabi ka cika min kunne mutafi "
dariya dayan yayi yace nine Dan kanzagi farouk?
Murmushi ya masa ya ce eh din suka jera suka shiga mota daya suka fita se da suka
fito asalin gate din na kula da barrack ne na sojoji motar ta hau titi da kyau tana
sharara, gudu adai dai lokacin tashin 'yan makaranta
Ji kake kuuuuuuuuuuuu!
ya taka wani irin burki wanda yawancin yaran dake kan hanyar duk se da su ka juyo
saboda karar da ta dauki hankulan mutane
Tuni Amal ta sulale kasa Dan tayi tunani motar ta kanta zata bi ta wuce
Tuni farouk ya fito A fusa ce yayi tsaye yana kallon yarinyar data sulale kasa
Duk da kuwa motar bata buge ta ba
Ita kam Amal jin shiru yasa ta ta bude ido a hankali tana kara zare su ta mi'ke
tsaye bata kula
da Wanda yake bayanta ba
Se da taji an fizgo hannunta an jiyo da ita da karfi kafin ta gama dawowa se
saukar mari taji a kucinta tuni tayi sumar wucin gadi a wajen..............
*Yawan comment yawan typing*😀😀😀
[8/12, 12:40 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*
*NA*
*AISHA*
*GALADIMA*
*DEDICATED TO*
*HASSAN ATKA*
*ALKHAIRIN ALLAH YA KAI GARE KU HAR GADON BACCI*
*MUM KHADY*
*RALEEYA*
*TEEMA DIMPLE*
*PG3*
Ramla da sauri ta karaso wurin ta kama hannun Amal
Tana jijjigata ta na fadar "Amal baki dai ji ciwo ba ko" ?
Tuni hawaye sun fara anbaliya a fuskar Amal
A daidai lokacin khaleel ya kara so wurin be bi takan farouk bama ya matsa kusa da
Ramla
"Bata ji ciwo ba ko?
"Eh ba ta ji ciwo ba"
Cewar Ramla
Ya mai da dubansa gun Amal yace "kanwata Dan Allah ki dinga kallon gabanki idan
kina kan titi ko hanya kin ji ko"
Ta daga masa kanta
Yace "good girl"
Sannan" kiyi hakuri da Marin da abokina ya miki ya ji
haushin abun da kika yi duk da be kyauta ba kinji
Ita dai Amal sheshshekar kukanta kawai take!
Ramla ce tace" ba komai mun gode ai laifinta ne da ta hau titi bata kallon gabanta
"
Tuni farouk ya shige motar ya barsu nan tsaye
Koda khalel ya juyo se dai yaga wayam ya shige mota tafiya yyi shima ya shiga motar
yana fadar "Amma dai gaskya farouk baka da kirki yarinyar da ka kusa turewa a mota
ita ce har ka samu damar daga hannu ka mara"
Ko kulasa farouk be yi ba ya ja motar suka yi gaba...................
Amal kam ai har suka isa gida Tana kuka ga fuskar ta yi suntum abu ga farar fata
sannan ga Marin da Tasha
Suna shiga ummah na fitowa da ga daki Ai ko Amal da gudu ta fada kanta Tana kuka!
Umma dagota tayi Tana "lafiya me ya same ki"?
Ai ko se ta Kara gunjin kukanta!
Se umma ta maida kallonta ga Ramla da ke cire sandal a kafarta
"Ke Ramla me ya sameta"?
Ramla tace"mota ce ta tashi kadeta tunda Kullum ita ce tafiya bata kallon gabanta
ai ko me motar da kyar ma ya taka burki yana ko fitowa shine ya mareta "
Umma tureta tayi daga jikinta tace" wuce ki bani wuri dama wannan shashancin naki
na in kina tafiya ba kya kallon gabanki baki Dena ba ko"?
"Ai ya min daidai dama Dan karan duka ya miki a hanyar gobe ki sake ki gani , wuce
ki cire uniform kuyi sallah"
Da gudu ta shige daki Tana ci gaba da kukanta! ..........
¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶
To suma har suka je suka dawo duk maganar da khaleel yake masa share sa yayi , yana
shigowa falonsa ya zube akan doguwar gujera yana lumshe idanunsa
Sautin karar wayarsa ne ya dawo dashi daga baccin da ya fara fizgarsa
Ganin Wanda yake kiransa yasa shi aza mar zauna wa tare da daukar wayar ya kara a
kunne
"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikumu salamu" aka fada daga dayan bangaren
"Abbana ka wuni lafiya" cewar farouk
"Lafiya lau babana ya aikin naka"?
"Lafiya lau Abbah ya ummina da Al'ameen?
"Lafiya lau suke yaushe zaka zo gida ina son ganinka tunda muna gari daya Amma ka
koma zama barrack se ka kwana biyu ba mu saka a ido ba
"Insha'Allah yau gida zan kwana Abbana" ya kare maganar yana murmushi
"To yayi se ka zo
Waiwaye...............
Comments dinku shi ze kara min karfin gwiwa😀😀
[8/12, 8:11 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*
*Na*
*AISHA GALADIMA*
*DEDICATED TO*
*HASSAN ATK*
_wannan shafin_ _nakune 'yan uwa Rabin jiki_
*Hauwa Galadima*
*Maryam Galadima*
*PG 4*
*Waiwaye*
_______________________________________
Malam Isma'il Dan Asalin jihar bauchi ne a wani gari da ake kira kwankiyal, a
karamar hukumar Darazo local government ,
Su biyu iyayensu suka haifa , Lawal shine babba,sannan Isma'il
Malam musa shine mahaifin su , hajjo maryo ita ce mahaifiyar su bafulata na ce ta
usuli ,mahaifin su kuma babarbare ne
Iyayen nasu basu wani jima da su ba suka kwanta dama !
Se rikon su ya koma hannun baffansu Awalu, daga nan ya ci gaba da kulawa da su ,
har lawal ya girma ya kai kimanin shekara 20 daga lokacin ya fara tafiya kano yana
kasuwanci 'yan gongon da ake yi
Allah yasanya albarka a cikin neman nasa ,haka yake dawowa gidan baffansa da kayan
masarufi iri iri Wanda hakan yakan farantawa baffan sa Rai , Isma'il shima a
lokacin ya fara zama saurayi inda yafi maida hankalinsa a karatun Arabi sosai yayi
zurfi a karatun nasa .
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah
Lawal har ya auri 'yar gidan baffansa mai suna hafsatu inda ya dauke ta suka koma
kano a can ya nemi haya a
Unguwa ukku suka zauna
Ba jimawa sunje ganin gida suka dawo tare da Isma'il a kano inda shima yake biyar
yayan nasa wurin sana'arsa duk ze fita
Har shima sana'ar ta karbe shi yana tafiye tafiye mussaman zuwa kaduna saboda
harkar tafi ja a can
Amarya hafsatu a lokacin ta samu karuwar Danda ranar suna yaro yaci suna Abubakar
sadiq murna a wurin lawal da Isma'il ba ta kwatantuwa mussaman Isma'il da Koda
yaushe indai ba wurin aiki ya je ba yana nanike da yaron .......
Bayan shekara biyar , a lokacin sadiq ya girma har ya shiga makaranta, adai dai
lokacin Isma'il ya bijiro da maganar aurensa inda ya samu wadda yake so me suna
Maryam , Maryam bafillatanar gombe ce tazo ziyara gidan 'yan uwa a kano suka hadu
da Isma'il ,inda suka fara soyayyar su me tsafta .
Ba jimawa manya suka shiga maganar,
ba'a wani jima ba aka sha biki ,shima a kano suka fara zama daga nan kuma ya dauki
matarsa suka koma kaduna bayan yayi sallama da yayan nasa ,
Dalilin komawar Isma'il kaduna, shine kasuwancin da suke na gongon a lokacin a
kaduna yafi akan kano, saboda kano din mutane masuyin sana'ar basu da adadi se ya
zama kasuwar taja baya
A gugurje bayan shekara biyu da auren Isma'il , maryam ta haifi santaleliyar 'yar
ta me kama da mahaifinta, ranar suna na zagayowa a ka rada mata Ramlat , haka taci
gaba da jegonta suna kula da 'yar su Ramlat
Bayan shekara ukku sannan fa ta sake haihuwar mace fara tas wannan kam duk
mahaifiyar ta ta biyo murna wurin wannan A hali ba'a magana
Mutanen kano ma sunzo aka sha biki
Tunda suka zo sadiq yake rike da jaririyar da ta ci suna Amal ,yaki bari kowa ya
karbe ta
Se ta fara kuka yake bayar da ita Tasha nono
Wannan kenan..........
_Comments dinku_ _shi ze kara min karfin gwiwa_😀
[8/13, 8:29 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞
*NA*
*AISHA GALADIMA*
*DEDICATED TO*
*HASSAN ATK*
*PG 5*
____________________
Koda su lawal su kai Shirin komawa kano bayan suna, fafur sadiq ya tubure cewar
baze koma ba se dai abarsa wurin Amal
Se da mahaifin nasa ya jawo sa kusa da shi yace "ka fasa zama Dan sandan da kake so
ka zama ne?"
Se yace" A'a Abba ban fasa ba"
Yace "to ka yarda mu koma kano har se ka zama Dan sanda se kazo ka ga kanwar ka
lokacin ta girma ,kuma zata ji dadi in ta ga ka zama Dan sandan"
Da murmushi akan fuskar sa yace "Abba na yadda mu tafi"
Malam Isma'il da Maryam dai suna gefe suna murmushi da jin dadin yadda sadiq ya
damu da Amal
Ai ko se da ya matso kusa da Maryam yace "umma a sake bani ita na rike kafin mu
tafi ta ko Mika masa ita ya karba
Se ya kara bakinsa a kunnenta yana mata magana su kansu ba suji me yace ba 😀
Iyayan nasu suna ta kallo nai suna murmushi to a haka dai suka samu suka musu
sallama suka kama hanyar kano...
To tun daga wannan lokacin da suka tafi sadiq be sake zuwa kaduna ba a ce warshi se
ya zama Dan sanda😀
Bayan wasu shekaru sadiq ya girma ya zama cikakken namiji burin nan nasa na son ya
zama Dan sanda ya cika yana matsayin inspector..
A gidan malam Isma'il yara sun girma Ramla anzama 'yan mata Tana s s 3 a secondary
school ita kuma Amal Tana j s s 3
Tun bayan haihuwar Amal, Maryam hai huwa ta tsaya mata cak!
Duk wadannan shekarun da'aka dauka su Amal ko sunje kano basu haduwa da sadiq
lokacin yana makaranta daga baya ma su ka rage zuwa saboda makaranta. Da suke zuwa
Arabi da boko
To kuma ita Amal tun suna 'yan matasa Allah ya Dora mata tsoron Dan sanda, ko kuma
duk wani da zata gani da bindiga,
Kasancewar suna kallon yadda 'yan sanda keyi a cikin films
Tun uwayen na daukar abunta wasa har suka zo suka bar daukar sa wasa,
Akwai wani lokaci da take 10years 'yan sanda suka shigo unguwarsu , suku ma suna
waje suna wasa,
Se jiniyar motar 'yan sanda suka ji ai ko ta buga kara!
Tana nuna ma Ramla motar 'yan sandan da ta tsaya kusa da su
Se Ramla tace" ta shi mutafi gida" ta ji shiru , se da ta juyo taga yarinya ta
mimmike ai ko da gudu ta shiga gida
Abbah !! Ummah!!
Da sauri malam Isma'il ya fito yana fadar "lafiya Ramla?"
Se waje take nuna masa da hannu ,
Da sauri ya fita wajen ya isko Amal kwance a kasa ,
Koda ya tabata bata tumfashi ya dauke ta suka shiga gida
Ya shimfideta akan tabarma ya nufi randa ya debo ruwa yazo yana ta shafa mata a
fuska
Tayi kusan minti biyar sannan ta farfado,
Nan ne fa malam yake tambayar Ramla "me ya faru Wai?"
Nan take sanar da shi "saboda taga 'yan sanda ne"
Da shi da umma suka kalli junansu fuskokin su cike da damuwa...
____________________
*Cigaban labari*
Tafe yake cikin mota ya kunna kira'ar shaikh sudai Abdurrahaman yana saurare ya na
kuma biyar karatun nasa a cikin suratul Anfal
Unguwar Rimi ya shiga da motar tasa har iso wani katafaren gida ya Danna hon mai
gadi ya wangale masa gate ya shige da motar sa
Se da ya daidai ta parking dinsa ya fito
Se ga mai gadin ya tafo a cikin uniform dinsa yana
fadar" wellcome sir"
Daga masa hannu kawai yayi ya nufi cikin gidan
Wani kyakyawan falo ne ya shigo se tashin kamshi yake
Ba kowa a falon Dan haka se ya haura saman bene
Yayi sallama a wani daki aka amsa ya shiga
Wata kyakyawar mace ce zaune bisa dadduma ga alamu kamar sallah ta kammala ya zo ya
zauna kusa da ita
"Ummina barka da yamma"
Abunda ya fada kenan
.daga mishi kai tayi kawai Tana lazimi ne
Lura da hakan da yayi yasa yace "bari naje na watsa ruwa ummi "
Yasa kai ya fita.....................
[8/13, 6:04 PM] Aysha Galadima: 🌸🌸🌸💞💞💞
*ANYI GUDUN GARA*
*NA*
*AISHA GALADIMA*
*DEDICATED TO*
*HASSAN ATK*
*PG 6*
________________________________________
Koda ya shiga dakin sa toilet ya wuce yayi kusan 30minutes, sannan ya fito daure da
towel a kugunsa da kuma karami yana goge kansa ,
Captain Umar farouk irin cikkakkun mazan nan ne masu Kira da cikar halitta , dogo
ne wankan tarwada, me dauke da doguwar fuska hade da dogon hancinsa, yana da
madaidai tan idanuwa ,hade da karamin bakinsa, gabansa a bude yake Wanda da'an gani
ansan ma'abocin motsa jikin sane 6packs dinsa a fili suke ,se dai bai cika kiba ba
kirar da yake da ita ne yasa farat daya baza'a Kira sa siriri ba...
Da sauri sauri ya gama Shirin sa ya sanya kana nan kaya ya fito ,
Kasa ya sauko ya nufi dinning table ya fara bude warmers din abincin da ke kan
table , da kansa ya zuba abincin ya zauna ya fara ci ,
Ummi ce ta sauko ta nemi daya daga cikin kujerin falon ta zauna
Yana kammalawa ya taso yazo gefenta ya zauna yana fadar"ummina"
Ta juyar da fuskarta gefe ,hannun ya kama ya rike "say something please my
happiness"
Se sannan ta juyo ta kallesa ta Dan sassauto da tsuke fuskarta da tayi
Tace " Babana me yasa Kullum se an neme ka kake dawowa gida bayan kasan daga kai se
Al'amin a gidannan?"
"Ummi Ayyukane suka min yawa shiyasa Amma kiyi hakuri yanzu gida zan dinga
kwana ,ina cin abincin ummina me dadi" ya kare maganar yana murmushi
Ita ma murmushin tayi
Ya jingina kansa a gefen kafadarta
Ture shi ta fara yi Tana fadar "dagani kar Al'amin ya shigo ya gan ka haka"
"A'a ummina nine fa wanda kika fi ji da shi a cikin ranki fa"
Ture shi tayi ta Mike Tana fadar "marar ta ido dagani Kullum ka girma baka San ka
girma
Siriryar dariya yayyi yana fadar "ummi ina little bro Banga sa ba tun da nazo"
"Ai kuwa be dade da fita ba yanzunnan zaka gansa "
Kiran sallar magrib da'aka kirane yasa duk sukan Mike sh ya nufi masallaci ita ma
ummi ta wuce sama
____________________
Inspector sadiq lawal ya fito cikin uniform dinsa da ya karbe sa yayi kyau sosai a
ciki
Falon gidan nasu ya nufa wow komai na falon ya canza da gani sun Kara samun cigaba
a Rayuwa
Wata 'yar matashiyar budurwa ce zaune Tana kallo tv ,hankalinta ya dauku bataji
sallamar da yayi ba
Se da taji yana" ke husna ba ki zuwa school yau ne"
Ya fafa cikin tsawa firgigit ta dawo hayyacinta
"Yaya sadiq Ina kwana" ta fada
Yace "da ban kwana ba zaki ganni wuce kiyi Shirin makaranta ko na Saba Miki"
A hankali ta raba ta gefenshi ta wuce Tana gode ma Allah da be dake ta ba!
Tana wucewa mahaifiyar tasu ta fito yana ganinta ya duka yana fadar
"Ummah Ina kwana anstashi lafiya?"
"Lafiya lau dan nan"
Ba ta fadar sunansa saboda alkunya irin ta fulani lol😀
"Zan tafi wurin aiki ne dama"
Tace "to Allah ya taimaka"
Yace "Ameen"
Se ga husna ta fito cikin Shirin makaranta ,dama shi ke kai ta sallama kawai tama
umma suka yi ma umma suka fito
Motar shi ya nufa ya bude ya shiga ita ma ta bude dayan bangaren ta shiga
Ya tayar suka fita se da suka danyi nisa a tafiyar ya juyo ya kalleta ai ko suka
hada ido ta sauke idonta kasa
"Kina jina ko idan na Kara kama ki kina kallo lokacin makaranta jikinki ne ze fa da
Miki ,shashar yarinya"
Husna daga kai kawai,jin dadinta daya yau be mareta ba
Saboda yaya sadiq badai saurin fushi ba
Arzikinta daya Dan ma umma na taka mai burki akanta da Allah dai yasan irin
hukuncin daze dinga mata
A haka dai har ta samu ya sauke ya bata 500 tayi godiya ta wuce shima ya wucewar
sa aikin gabansa
Husna kanwace a wurin Sadiq Dan itace autarsu tunda ba wasu bayan ta kusan sa'ani
ne da amal
____________________
Malam Isma'il ne yayi sallama a gidansa da gudu husna ta fito daga daki Tana "oyoyo
Abbah"
Tana zuwa ta karbi ledar hannunsa
Ramla dai ruwa ta debo mai a kofi ta Mika masa ya karba ya Sha
Lokacin umma ta fito bayan gida Tana masa sannu da zuwan
"Malam yau Naga ka dawo da wuri"
Cewar ummah
"Eh dama kayan cefanen gobe ne na kawo dazu yaya lawal ya kirani ,yake sanar Dani
gobe zasu zo gaba dayansu sunyi hutun mako su koma"
Ai ko nan suka shiga murna zuwan nasu mussaman Amal da ke son haduwa da husna
Ramla ce tace "Abbah Amma bada yaya sadiq za'a zo ba ko?"
"Dashi za'a zo Mana "
Cewar Abba
Ta sake cewa
Amma Abba bashi ne Dan sanda ba?"
"Shine Mana"
Ai ko Amal murna ta koma ciki
"Abba Dan Allah kace kar ya zo shi"
Ta kare maganar da hawaye duk kallo suka bita da shi
Umma ce ta katse shirun da cewa "ke ban son shashanci anki ace kar ya zo din"
Ai ko se hawaye sharr!!
Ta shige dakinsu Tana kuka! .....................
_Comment
Share
[8/14, 8:00 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*
*NA*
*AISHA GALADIMA*
*DEDICATED TO*
*HASSAN ATK*
*PG 7-8*
_______________________________________
Umma ce tace "yarinya kina da aiki babba a gabanki kuwa"
Abba ne yace"nifa lamarin yarinyar nan ya fara bani tsoro, irin wannan tsoron Dan
sanda da take yayi yawa fa"
"Ai kuwa dama ta bari ,saboda auren ta da sadiq tamkar anyi an gama ne, tunda kasan
alkawarin da kayi da yaya lawal"
Abba shiru yayi be sake cewa komai ba yace "bari na koma kasuwa"
"Allah ya kiyaye" cewar ummah
Ya tashi ya wuce ummah kitchen ta wucewar ta
Ramla dakin nasu ta shiga har lokacin Amal kuka take se taji duk jikinta yayi sanyi
Tana tausayin 'yar uwarta ,ta kuma ji firar da su Abba suka yi, tasan duk Amal taji
labarin cewar zata auri yaya Sadiq, Allah dai yasan halin da zata shiga
Matsawa tayi kusa da'ita ta dago kanta ,ta sa hannu Tana goge mata hawayen da take
yi.
"Haba lovely sis miye abun kuka da zaki zauna kina ta kuka irin haka, ai se ki
janyowa kanki rashin lafiya"
Fadar Ramla
Ajiyar zuciya Amal ta sauke ta kalli 'yar uwar ta da idanun ta da sukayi jajir
saboda kuka , tace
"Aunty kinsan fa bani son Dan sanda fa da masu bindigogi ,Amma shine su Abba zasu
gayyatosu suzo gidan nan Allah dai yasan wadanda ze kashe idan yazo gidan nan ni na
tsane shi tun kafin yazo gidannan, dama ya mutu a hanyar zuwa
Da sauri Ramla ta rufe mata Baki Tana fadar"Amal Ashe Baki da hankali yaya Sadiq
din kike ma fatan mutuwa, Dan gidan kawu lawal ne fa na kano Wanda yake muna
aikan kaya na sallah ko Azumi ,koma ba su ba har kayan kwaliyya da kyalekyali haka
yake aiko Mana da su fa ,yaya Sadiq kuma shine babban yaronsa fa kuma shine yayan
husna fa kike so ya mutu?"
Se Amal tayi kwalkwal da idanu tace " to wa yace shi ya zama Dan sanda?"
"To ba aikin sa bane, sannan ba su kashe mutane kamar yadda kike tunani fa se masu
laifi suke kamawa
Dauke labulan dakin akayi "wake kashe mutane?"
Duk suka zare idanuwa 😳
Ummah ce ta dago labulen ,da sauri Ramla tace "labarin wani film muke "
se tace"to ku tashi ga Kiran sallar Azahar can Ana yi kuyi sallah"
Duk suka Mike suka fita
________________________________________
Se dare wurin dinner ya hadu da Abban nasa bayan sun kammala dinner ne yace yana
da magana da shi, tsam ya Mike ya nufi dakinsa , shima farouk biyar bayansa yayi
zuwa dakin
Da sallama ya shiga ya nemi kasan carpet ya zauna
Se da Abba yayi gyaran murya ya fara da "babana na Kira ka ne saboda akwai
muhimmiyar da nake so nayi da kai, farouk ya Kara sunar da kansa kasa, "
Alhamdulillah duk abunda uwaye ya ka mata Suma 'ya'yan su duk na maka, har an kai
matsayin da ka mallaki duk abubuwan da ya kamata se dai Abu daya da har yanzu Banga
Alamar kana da niyyar yi ba, shine aure tun Ina ma mahaifiyar ka magana akan ko
taji kana zancen se ta cemin A'a , Dan haka Naga ya kamata nama magana da Kaina
naji ta bakin ka"
Farouk ya dau kusan sakan 10 be ce komi ba se can yace " Abba Insha'Allah na kusa
yi"
"Ka kusa yi yaushe?"
Cewar Abba
"Bada jimawa ba "
Farouk ya bashi Amsa
"To yayi zan ci gaba da tsumayen amsar taka , to ya wurin aikin naka ba dai wata
matsala ko?"
"Eh Abba ba matsalar komai"
"To yayi Allah ya maka Albarka ta shi kaje"
"Amin nagode Abba"
Ya sa kai
Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500