gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Rainon Yaro Book 1 Takun Farko Complete Hausa Novel by Hafsat Umar Dangoro Chapter 5 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Baby, wanda hawaye ke shirin gangarowa.

“Come with me.”



“Daddy... suna zargin—”



“I know. But your eyes are clean. That’s enough for me.”



Yana rike da hannunta suka bar wajen. Kowa ya zuba musu ido. Wasu suna mamaki, wasu suna harara, wasu kuwa suna jin haushi — amma MJ bai kalle su ba.


---

A GIDA…

Da dare, Baby na zaune kusa da MJ. Ya rike hannunta, yana goge mata hawaye da tawul.

“Idan duniya ta juya miki baya, ki kalli ni. I will always be your front.”



“But I don’t want to disgrace you, Daddy... suna cewa ni ban dace da kai ba…”



MJ ya dafa kanta, ya furta da nutsuwa:

“You don’t have to match me, Baby. You only have to match your truth. And I know your truth is pure.”



******
---

SARKI YAJI ABINDA YA FARU…

Da safe, MJ na shirin kai Baby makaranta, sai aka kira shi a fadar Sarki.

Sarki ya kalle shi da tsantsar basira:

“Abee... lokacin da yarinya ta fara fuskantar ƙiyayya, to zata fara girma da karfi. Amma ka san me ke cutar da mace da wuri? Idan ta dogara da soyayya kafin ta girma da zuciya.”



“Kayi hattara. Zuwaira da irinta... ba ƙiyayya suke ba — kishin rikonka suke.”



MJ ya ce:

“Zan kare Baby, ko da kuwa sai na hana zuciyata kwanciya. Tana min kamar wani bangare na rayuwa wanda babu wanda zai iya cike shi. Kayi hakuri Abba ammani bazan taba iya zuba ido ina kallon masu chutar da baby ban tsawatar musuba, da ace zuwaira zata Gane abin da zatai na sota, to ta kaunaci baby nikuma zan kaunace ta Amma bawai ta kulla mata sharriba" MJ Yana gama fadar haka ya bar cikin fadar gaba daya.

""""""""""""""""""🫂
Bayan dawowa daga makaranta, Baby ta zauna a gaban window tana kallon rana tana faduwa, tana rik'e da certificate ɗinta na zinariya, amma idanunta cike da tambayoyi da damuwa.

MJ ya zauna gefenta da cupcake a hannu, ya ce da dariya:

“You know what we do when the world frowns at us?”



Ta girgiza kai cikin rauni.

“We smile back. Amma ba dan muna jin dadi ba — sai don mu nuna musu we’re stronger than their hate.”



Baby ta kalle shi, sannan ta ce cikin hankali:

“Daddy… yaushe zan daina jin kamar bana cikin nasu? Kamar bana daga masarautar nan?”



MJ ya janye gashinta daga fuskarta, ya ce a hankali:

“Zaki daina, Baby. Lokacin da kike d'aukan kanki a matsayin tauraruwa, ba dutsen da zai iya hana ki haskaka.”

Gyda Kai kawai baby tayi hadi da rausayar da Kai ta Dora kanta a kan kafadar MJ Tana sauke ajiyar zuciya.


---***************

WATA SABUWA... MAHAIFIN ZUWAI RA YA DAWO MASAURAUTA DA ZAMA.

A lokacin da Baby ta fara samun karbuwa daga wasu malamai da manyan makaranta saboda kokarinta, sai mahaifin Zuwaira — Alhaji Faruq — ya shigo masarauta da korafi.

“Mai martaba Sarki, a yarda da za’a rika dora yarinya ba asalinta ba, bisa manyan mukamai a makaranta da masarauta? Wannan zai lalata tarbiyyar ‘ya’yanmu.”



Sarki Umar ya kalle shi, ya dan tsaya kafin ya ce:

“Ka tuna cewa ba jinin sarki ke sa mutum mutunci ba — halinsa da zuciyarsa ke gina shi.”



“Yarinyar da kake magana akai — Baby — na fi yarda da ita fiye da yawancin yaranmu da aka haifa da zinariya.”



Alhaji Faruq ya fita da jin haushi. Ya hadu da diyarsa Zuwaira a waje, ya ce:

“Idan baki hana wancan yarinyar nan taka kasa ba, to zan hana ki gado a gidana.”



Zuwaira ta dafe ƙirji da ɗan mugun murmushi.

“Don’t worry, Abba. She’ll taste salt without soup.”


Kai kawai abban ta ya daga ya ya juya ya tafi tabi bayansa da kallo.

---

Zuwaira da abokanta suka fara tsananta mugunta. Suna jefa Baby cikin gori a makaranta da gida. A wani lokaci har aka boye mata littafinta na jarabawa. Sai dai duk da haka, Baby ta ci gaba da samun matsayi na farko.

MJ na lura da komai. Wani dare ya kira Baby ya ce:

“Kinga... I won’t always be able to shield you. Amma zan koya miki yadda ake gina garkuwar zuciya. Ki tsaya da kafafunki, Baby. Don ba zaki iya gudu daga komai ba, watara na bazaki ganni ba dole ni ma zan mutu ,bazai zama kullum nine mai kareki ba.”



“I’ll try, Daddy. I’ll try…”




---

SHEKARUN GIRMA… KYAU NA BAYYANA

Baby ta ci gaba da girma. Yanzu tana da shekara goma sha bakwai 17 wayonta da kwarjinta na bayyana. Komai nata ya cika da ladabi da kamala. A makaranta, kowane yaro na kallonta fiye da sau biyu. Har wasu malamai sukan ce:

“Wannan yarinya, kamar Sarauniya ce da ba’a saka mata crown ba tukuna.”



Samari ‘yan masarauta, da yayansu masu kudi, sun fara aiko mata da notes da gifts, amma duk MJ yana karantawa kafin ta karanta.

Wani dare, MJ na goge mata kai yana mata kitso, sai ya hango wata love note daga ɗaya cikin yayansu Alhaji Faruq. Ya janye karyar murmushi, ya ce a hankali:

“Yanzu sun fara rubuta miki wasikun soyayya?”



“Na ce musu bana sha’awar soyayya. Ban san me soyayya take nufi ba. Ni dai ina da kai, kuma hakan ya ishe ni.”



MJ ya kalle ta. Idanunsa sun kada, amma da murmushin zuciya. Ya ce:

“That’s all I needed to hear tonight, Baby.”


🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺



A wani dare mai duhu da hazo, mahaifiyar Zuwaira — Hajiya Sa’adatu — ta ce da diyarta a sirrance:

“Zuwaira, idan da gaske kike son ki samu nasara, ki cire jin kai. Wannan yarinyar da kike bari tana daukar hankalin MJ? Kafin ki farka, zata dade a zuciyarsa fiye da rayuwar da kika yi tun kina cikina.”



Zuwaira ta dafe kirji. Zuciyarta cike da kishi da azaba. Ta ce:

“Mama, ban san lokacin da ya fara jin ta fiye da ni ba. Amma ina so na ga karshenta.”



Hajiya Sa’adatu ta saki murmushin mugunta.

“To sai mu kai sunansa da nata... gurin boka. Zamu juya duniya, zamu juya zuciyoyi idan kin amince.”



Murmushin mugunta zuwaira tayi tace" duk yadda kikace haka za ayi Momyna"
---


🕊️ RAINON YARO

Chapter 8










Washe gari da sassarfa suka shirya tsaba suka dauki hanyar zuwa wajen boka ,
a cikin wani daji mai duhun gaske — boka Malam Gado. Ya karɓi hoton MJ yana dariya cikin mugun sauti:

“Wannan saurayi, zuciyarsa cike take da tsarki da ƙauna. Amma zan shafa masa inuwa — yanda duk lokacin da yarinyar nan tazo kusa da shi, sai yaji haushi, kamar jini da toka.”



“Za ta shanye hawaye — ki shirya, domin daga yau, duniya za ta juyawa Baby baya.”



Malam Gado ya daga hayaki, ya fesa su akan hoton MJ da na Baby, sannan ya fadi wani zazzafan kalma:

“Zuciyarsa zata rufe... idonsa ba zai sake ganinta da ƙauna ba. Sai dai tsana. da baƙin ciki...”


Godiya sosai sukayiwa boka sanan suka aje tulinn kudin da sukazo da shi, sanan suka koma gida cike da tsantsar farinciki.

---

After two days 💍

Kwanaki biyu kacal bayan wannan dare, MJ ya dawo gida da fuskar da ba'a saba gani ba. Yana zaune a falo, Baby ta shigo da dariya a fuskarta tana dauke da wani zanen da ta yi a makaranta.

“Daddy, kaga na zana mu biyu... ka gani?”



MJ ya kalleta kamar wata ƙasa ce ke neman tsage masa fuska. Ya ce da ƙasƙanci:

“Na ce ki barni! Ki fita da wancan shashancin banzan naki!”



Baby ta tsaya cak, kamar wuta ta kone mata kafa. Hannunta na rawa, idanunta sun cika da mamaki.

“Daddy… me nayi maka?”



MJ ya miƙe da fushi, ya yi wurgi da zanen:

“Kin takurani! Kin dame ni! Ki fita ki barni!”



Baby ta fita daga falon tana kuka, zuciyarta na karaya, kanta na juyawa. Tun daga wannan rana, MJ ya daina mata kulawa. Ko kallonta baya yi. Kullum fuska tamkar yana kallon abinda yake ƙyama.


---****

A makaranta, ko da sauran yara suka fara ganin MJ yana guje mata, su ma suka fara tsanarta. Wasu sun fara mata dariya, wasu suna kiranta “marainiya mai bakin tabo.”

Har wasu malamai suka fara janye kulawarsu, suna nuna kyama da rashin yarda da ita. Duk da haka, Baby ta ci gaba da kokari.

Amma wata rana, bayan sun dawo daga makaranta, ta tsaya a bakin kofa, tana kallon MJ wanda ke zaune a falo ba tare da kallonta ba. Ta ce cikin muryar da ta ƙarye:

“Ka daina sona, Daddy?”



MJ bai ce komai ba. Ya cigaba da kallon TV, kamar bai ji komai ba.

Baby ta juya, tana tafiya cikin dare, hawayenta na gangarowa kamar ruwan sama, zuciyarta na faɗuwa, kamar bata san gaba ba.


---

" Wani mugun asiri na iya juyar da zuciya, amma soyayya ta gaskiya tana da darajar da ko bokaye ba za su iya murkushe ta ba Kai Anya asirine Kuwa" baby ta tambayi kanta har ta isa dakinta Daren dai yadda taga dare haka taga rana sabi da damuwa.



Baby ba ta da sauran kuzari. Duk safiyar da ta tashi, hawaye ne farkon kalmarta. Ba MJ ne ke tada ta zuwa makaranta ba. Ba MJ ne ke dakota ba. Ko lokacin da ta yi ciwon ciki a daren Juma'a, MJ ya zauna a dakin sa kamar ba komai ya faru ba.

Zuwaira kuwa sai shagwaba take a gaban MJ, tana kawo masa abinci, tana matsa masa kafafu, tana bin umarninsa da murmushi. Amma duk da haka, MJ bai taɓa nuna cewa yana sonta ba — sai dai a ce ya fi nuna mata kulawa fiye da yadda yake yi wa Baby yanzu.

Sai dai a fadar sarki, shiru ya mamaye zuciyoyi. Kowa yana mamakin sauyin MJ. Baby ta koma kamar ba a san da ita ba. Ko lokacin da sarki ya ganta zaune ita kaɗai a tsakar gida, yana jin wani irin zafi a zuciyarsa, amma sai ya janye. Ba zai nuna goyon baya a fili ba, domin ya sa sharadi... Dan a tunaninsa MJ Yana nuna ko in kula akan babyne domin tasaba da rashinsa watarana.


---

A DARAREN JIYA.

MJ na zaune a farfajiyar gida, yana shan iska. Wata rana baby ta taho a hankali da takunta mai nutsuwa. Cikin riga da siket na makaranta, kanta cike da damuwa da tambayoyi. Ta tsaya gaban sa.

“Daddy…” ta ce cikin ƙasa da murya. “Ni nayi wani abu ne da ya ɓata maka rai?”



MJ ya ɗago kai, yana kallonta kamar ba ya ganinta yadda yake ganinta da. Akwai ƙara da sanyi a idonsa — kamar ba zai iya amsa ba. Ya buɗe baki da ƙyar:

“Kada ki kirani da Daddy. Ni ba mahaifinki bane.”



Wannan kalmar tamkar sara mata aka yi da wuƙa. Baby ta runtse idonta, ta ce:

“To... to meye ni a wajenka?”



MJ ya ce da ƙarfi:

“Ke? Ke ba komai ba ce! Kawai nauyi ne da aka dora min! Ammani ban saniki ba, Naga mahaifina Yana hadani dake ,kuma Yana tambayata ke bayan ni ban sanki ba, ki fita daga rayuwa ta". Ya daka mata tsawa hadi da tasowa kamai zai dake ta.



Ta juyo da gudu, ta nufi ɗaki, tana kuka kamar rai zai fita. Amma bayan ta shiga, ta rushe da kuka a kan gado, tana faɗin:

“Ba haka Daddy yake ba. Ba haka ba… Yana sona, wallahi yana sona. Me ya faru da zuciyar sa?”




---

ZUWAIRA

A gefe guda, Zuwaira tana kallon wannan fadowar, tana murmushi da girgiza kai:

“Na gaya miki ba’a karɓar zuciyar da ba taka ba. MJ zai kasance nawa — ko da da kisa ne.”



Mahaifiyarta kuma ta ce:

“Ki kwantar da hankali. Boka yace duk wata ƙauna da MJ ke ji mata yanzu wuta ce. Sai dai kallo — babu tausayawa, babu kulawa.”




---

A DARAREN KWANA GOMA BAYAN HAKA…

Baby ta soma sauya hali. Tana shiru fiye da da. Bata sake dariya kamar da ba. Wani dare ta samu wata ƙaramar takarda, ta fara rubutu da tawada mai ɗumi da hawaye:

“Dear Daddy... Na san wani abu ya faru. Ban san menene ba. Amma zan yi hakuri. Zan bar komai cikin hannun Allah. Zan girma. Zan koya. Zan jira — har ranar da za ka sake kirana ‘yar zuciyarka.”



Ta ɗora takardar cikin litattafinta. Sannan ta kwanta da hawaye a idanu, amma zuciya mai fata.


*Sarki Umar*


Sarki Umar na zaune cikin dakin karatunsa. Ya buɗe wani tsohon littafi da aka buga a kasar Andalus shekaru da yawa da suka wuce. Amma ba littafin bane a ransa — zuciyarsa na nan wajen MJ da Baby.

“Wannan yarinya… tana da wani irin haske. Amma yanzu ina ganin hasken yana dusashewa.”



Ya kalli hoton mahaifiyar MJ da ke manne a bango. Sai ya furta:

“Halinki ne ke jikin MJ. Amma ko zuciyarki za ta iya jimre da wannan azaba da Baby ke ciki? Kenason kina son baby to Amma meyasa ?.. sarki yayi shiru yanajin kodai yaje yasamu mahaifiyar MJ ya ji ko ita tasan mai ya faru a tsakanin MJ da baby har ya daina sauraronta.




---

*School*

A makaranta, Baby ta fara zama mai nisa da mutane. Duk da tana da ilimi, tana samun matsayi a ajinsu, amma sunan MJ na bibiyar ta — wasu suna cewa "Meye tsakani su da MJ?" Wasu suna cewa "Ai tana jin girman kai tunda MJ yana goyonta da can."

Sai wata sabuwar daliba, Fareeda, ta matso gareta:

“Kinyi kyau yau, Baby. Amma kin yi shiru sosai. Kin san me? Ina jin kamar akwai abu da ya dame ki.”



Baby ta ɗan murmusa, ta ce:

“Babu komai.”



Amma Fareeda ta tsura mata ido.

“ba Komai? To me ya sa idan MJ ya wuce kusa da ke, kina runtse ido kamar ki ɓalle da kuka?”



Baby ta yi shiru. Amma zuciyarta na faɗin: “Kin ce komai… Amma kin fara fahimta.”


---

A GEFE GUDA… BOKA NA RIKE DA HOTON MJ A DAKIN DUHU

Boka ya kalli MJ da ido irin na sihiri. Yana kara tsafi da gumaka da turare.

“Ka fara mantawa da ita gaba ɗaya. Za ka iya ganin ta ba tare da ka ji komai ba. Amma… akwai hadari.”



MJ ya ce da murya mai sanyi:

“Hadari?”



Boka ya ce:

“Idan zuciyarka ta taɓa tuna ta... asirin zai rushe. Kuma... kai zaka ji ciwo fiye da kowa.”



MJ ya kalli ƙasa. Sai kawai ya furta:

“Na rasa yadda nake ji yanzu. Komai ba shi da amfani. Kamar ni ba ni ba ne.”

Murmushin boka kawai yayi yace "ai Daman bakai bane daga haka ya kara matse hoton MJ hadi da cigaba da tsafetsafen sa.


---

A DAREN WATA LITININ…

Baby na dakin karatu tana ɗan rubutu da yatsanta a jikin takarda. Ta rubuta:

"Rai kamar ruwa. Kuma ni kamar jirgi ne cikin wannan ruwa. Amma daddy... kai hasken fitilar da ke kan ruwan ne. Ko da baka ganina a yanzu, ina can. Ina jiranka."



Sai ta lumshe ido. Ta janyo rigarta, ta kwanta, tana mai jin numfashinta kamar wani zazzafan yaki a zuciya.


---

A FADAR MASARAUTA...

Sarki ya kira limamin fadar asirce.

“Ina jin akwai wani abu mara kyau da ke faruwa a gidan nan. Wani abu da ya shafi MJ da Baby. Ka je ka nemo gaskiya — amma cikin sirri. Kada kowa ya sani.”



Limamin ya ce da tausayi:

“Zan bi komai da addu’a da bincike. Idan akwai sihiri, insha Allahu za mu bankado shi.”


🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺


Baby na zaune a dakin ta, kanta a jingine jikin window, tana kallon sama mai taurari. Amma ba taurarin take kalla ba – zuciyarta na karayin kuka cikin shiru.

“Daddy... me na yi maka? Me ya sa ka barni da wannan shiru da yake cin zuciyata kamar wuta?”



Kukan da take shanye ya hana ta magana, amma zuciyarta tana karanta kalmomi da MJ ya taɓa faɗa mata:

“I will always protect you.”


“I promise, Daddy.”



Tayi shiru, sai kuma ta ɗago kai kamar wacce ta yanke shawara.

“Na fara fahimtar wani abu. Kuma zan bi saƙon zuciyata, komai za ta fitar min da shi.”




---

A MASALLACIN FADAR SARKI...

Limamin masarauta yana cikin masallaci yana karanta ayoyi cikin nutsuwa. Sai ga shi ya ɗago kai da mamaki.

“La hawla...! Akwai sihiri da aka nannade da wuta da ƙiyayya. Ba MJ bane ainihin laifinsa. Wani abu ne yana sarrafa zuciyarsa.”



Ya tashi da sauri, ya nufi fadar Sarki.


---

A FADAR ZUWAIRA...

Zuwaira na zaune da mahaifiyarta a dakin su. Mahaifiyarta tana girgiza kai tana hurawa boka turaren sa da suka boye a cikin ƙamshi.

“Idan har MJ ya ci gaba da mantawa da ita, sannu a hankali, za mu zama dole ga rayuwarsa.”



Zuwaira ta ƙara kwafa da wulakanci:

“Ai yanzu ma ya daina kulata sosai. Shi fa ba yadda na ke so yake ba — amma tunda ya daina kula da waccan, zan sami damar shiga zuciyarsa.”



Mahaifiyar ta ce:

“Amma ki kiyaye... idan sihiri ya kama zuciya sosai, ba zai san me zai so ba, balle wacce zai aura. Sahi dai gashi kamar shara.”




---

MJ A DAKINSA...

A dakin MJ, yana zaune yana karanta littafi. Amma ba ya gane me ke ciki. Sai kawai ya mike, ya kalli madubi. A cikin madubi, sai kawai yaga fuskar Baby — amma fuskar ba ta murmushi ba ce, ba kuma ta dariya ba. Fuskar da ta cika da tambaya da raɗaɗin jin ƙiyayya daga masoyi.

MJ ya zabura — zuciyarsa ta yi wani irin bugawa.

“Me ya ke faruwa dani?”



Yayi wani numfashi mai nauyi. Ya zauna. Ya ɗauki wayarsa — sai ya duba hotonta da ya taɓa ɗauka ranar da ta samu kyautar karatu a makaranta.

“Na manta da ke... Amma kuma... me yasa zanji wannan ciwon yanzu?”




---

SAFIYAR RANAR ASABAR...

Baby na zaune a lambun makaranta. Fareeda, abokiyarta, ta zo kusa da ita da takarda a hannu.

“Na samo miki bayanin wata tsohuwa da ke cire asiri a wajen gari. Akwai labarin cewa tana iya tantance wanda aka tsare da sihiri. Idan baki so kowa ya je — mu je mu duba da dare.”



Baby ta girgiza kai. Cikin ranta ta furta:

“Daddy... ko da ba ka gane ni yanzu ba... zan nemi hanyar da zan dawo da kai.”

Afili Kuma tace "nagode sosai kawata da taimakon ki a kaina duk da cewar ban fadamiki abin dayake damuna ba, sai da kikai duk yadda Zaki kika nemo abin da ke damuna, daskiya ke kawar kirkice.


---Misalin ƙarfe 9:00 na safe
Fareeda da Baby suka tsinci kansu a cikin wani daji mai zurfi, inda bishiyoyi suka lullube sararin sama, kuma iska ke busa kamar tana ɗauke da sirri. A tsakiyar dajin, wata tsohuwa ke zaune, idonta biyu kamar gilashi — masu tsananin haske da fahimta.

Tsohuwar ta kalli Baby tun daga nesa, sannan cikin sauti mai tsawa ta ce:

“Kin zo da zuciya mai tsarki. Amma zuciyar wanda kike ƙauna an nannade ta da igiyar asiri.”



Ta miƙa hannunta, ta ɗora shi a kan ƙirjin Baby, sai ta ce cikin sanyin murya mai zurfi:

“Na fahimci wanda ya aikata wannan asirin. Ya samo asali ne daga cikin masarautar ku. Amma akwai mafita — sai dai farashi mai tsanani.”



Baby ta share hawaye, ta kalle ta da karfin zuciya:

“Duk abin da ake bukata zan yi. Daddy na ya fi kowa cancanta da a dawo da shi. Ko rayuwata ne za a nema — zan bayar. Indai game da shi ne, na riga na yarda da sadaukarwa!”



Tsohuwar ta gyara zama, sannan ta ce da ƙaramin murmushi:

“To ki sani… kafin zuciyarsa ta warke, dole sai naki ta sha wahala.”



Idanun Baby suka zaro, cike da mamaki:

“Me kike nufi da haka? Kina nufin sai na sha wahala kafin a karya shirin da ke jikinsa?”



Tsohuwar ta gyada kai a hankali:

“Tabbas. Baby, ke wata sirri ce wadda Ubangiji ya ɓoye. Babu wanda ya san hakikanin komai a kanki sai mahaifinki, mahaifiyarki… da kuma kishiyar mahaifiyarki. Ita ce silar da ya mai da ke marainiya, mai rayuwa ba tare da asali ba.”



Baby ta ja da baya, zuciyarta na bugawa:

“Ke… kina nufin kin san wani abu game da ni?”



Tsohuwar ta murmusa kaɗan, tace:

“Ba shi ne ya kawoki nan ba. Kin zo ne domin ceton ran mahaifinki.”



Baby ta sunkuyar da kai, jiki a sanyaye:

“Menene zan yi, wanda zai dawo da shi cikin hayyacinsa?”



Tsohuwar ta ce:

“Ina so ki zauna a nan — ki zauna da ni har abada. Ki zama ɗiyata. Na jima ina jiranki… ke ce cikon mafarkina.”.........





🕊️ RAINON YARO

Chapter 9



Baby ta tsorata, amma da ta tuna da MJ da yadda yake mata ƙauna da kulawa, sai ta ce a hankali:

“Indai hakan zai dawo da daddyna, na amince.”



Fareeda ta yi saurin janyo ta gefe, cikin tashin hankali:

“Baby, ba ki da hankali ne? Idan kika zauna anan, burinki fa? Karatunki fa? Rayuwarki fa? Kina so ki lalata komai? Idan MJ ya dawo lafiya kuma ya tarar baki kusa da shi — zai mutu da damuwa! Ki tuna da hakan!”



Baby ta numfasa, ta ce cikin murya mai sanyi:

“Fareeda, kin san cewa sarki ya ce ba zai taɓa aurar da ni ga daddy ba. Na san babu aure tsakanina da shi. Amma ni ‘yace a wajensa. Koda na rayu da daddy, dole wata rana za a tura ni ga wani. To me zai hana in sadaukar da kaina domin wanda ya fi kowa kaunata? Ka da ki manta Fareeda ,cina, suturata, kulawata, rainona, wankin Kashi, wankin futsari, shayarwata, karatuna,tarbiya ta,komai da kika gani atattare Dani daddyne ya minsu, kinsan mene kadai bai min ba haihuwata, da Kuma haluttata a doron duniya, bazan ma fadamiki wannan maganar ba tunda bani da tabbacin cewar bashi ya haifeni ba,tun da har yanzu na kasa sanin waceceni, Indai har iya zamane zan zauna da ita har abada' muddum zan ceto zuciyar daddy"



Tsohuwar ta tashi a hankali, ta nufo Baby da sandarta tana nazarin zuciyarta kamar tana karantawa daga takarda.

“Zuciyarki kamar ruwa ce mai tsarki — amma idan aka zuba ƙashi a ciki, sai ta zama baki. A yau za ki yanke hukunci tsakanin zuciyar ki da zuciyar wanda ke kiran ki Baby.”



Fareeda ta tsaya gaba da Baby tana girgiza kai, idonta cike da ƙwarin gwiwa:

“Wallahi idan kika zauna anan, Baby, na rasa ke. Ya Mujahid ya rasa ke. Kin san yadda zuciyarsa ke karaya ko da yana cikin jama’a. Kin san yadda yake zaune da mugun burin ganin ke kina dariya?”



Baby ta sunkuyar da kai, hawayenta suna zuba kamar ruwan sama. Tana jin duniyar na juyawa — tsakanin soyayya da sadaukarwa, tsakanin burin zuciya da ƙaddara.

Tsohuwar ta sake magana, cikin sautin da ya haɗa tausayi da rinjaye:

“Zaki iya dawowa, amma sai kin cika sharuɗɗa. Sharadi na farko: har sai ran mahaifinki ya dawo cikin nutsuwa, ke ba za ki sake masa dariya ba. Sharadi na biyu: kowanne mutum da kika ƙauna sai ya jarrabtu da rashin ki.”



“Wannan ba fushin Allah bane — wannan ne fansar ƙaunar ki da amincin ki.”



Baby ta ɗago da idanu masu haske amma cike da hawaye. Ta ce da Fareeda cikin murya mai sanyi:

“Na san zan iya rasa komai — amma idan daddy ya daina shan wahala, zan iya jurewa.”



Fareeda ta rungume Baby da karfi, tana hawaye:

“Sai ki dawo, please. Ki dawo da daddyn mu. Amma ba ki da damar ɓata rayuwarki wajen fansar kowa. Ke har yanzu kina da mafarki, kina da burin karatu... kina da zuciya da ba a gama gane ta ba.”



Tsohuwar ta gyara zama, ta ɗauko ƙaramar ƙoƙo daga gefe, ta miƙa wa Baby:

“Ki sha wannan ruwan ganyen rai-dore. Zai karɓi wani ɓangare na farin cikin ki. Amma zai ƙara wa zuciyar MJ haske.”



“Zan sha,” Baby ta ce, tana girgiza kai da murya mai ƙarfi. “Na amince da ƙaddarata.”



Ta ɗauki ƙoƙon — ta kai bakin ta — ta lumshe ido... ta sha.

A can masarauta, MJ wanda ke zaune cikin daki, sai ya ji zuciyarsa ta buga... kamar wani abu na tashi daga barci cikin jikinsa. Ya ɗaga kansa da sauri:

“Baby...?”




MJ ya farka da kyar, kamar wanda aka farkar daga mafarki mai nauyi. Yana zaune a kan gado, yana kallon hannunsa — ya tsinci kansa cikin wani irin nauyi da ba ya iya fassara.

“What’s happening to me... why do I feel like I forgot something important?”



Ya mike, ya nufi mirror, sai idonsa ya sauka kan takardar gaisuwar Baby da ta rubuta masa shekara guda da ta wuce a ranar da ya kai ta bikin makaranta.
Ya ɗauke ta, yana karanta rubutun da bai taɓa dubawa ba kwanan nan:

"To the best Daddy in the world. You didn’t just raise me, you rescued me. I will never stop learning, I will never stop dreaming — because you showed me how to live."
— Your Baby Girl, fateema



MJ ya runtse ido. Kamar zuciyarsa tana harbi da wani sauti... Sai kuma ya furta:

“fateema...”



Zuciyarsa ta buga. Idanunsa suka cika da ruwa. Sai ya ji wani abu ya shiga tunaninsa kamar sauti yana bayyana:

“Ba duk wanda ke kusa da kai ne ke tare da kai ba.”




---

A CAN BANGAREN BABY...

Baby

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment