You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Nwasne Kwasnen
RUFAIDA M. UMAR
a mike tsaye da sauri tamkar wani spring ne ya harba ni a Nkujerar da na ke a zaune, kirjina ya buga da karfi kamar
yana shirin buſewa, alamun tsoro da fargaba suka bayyana kuru-kuru a fuskata Na dubi Asma'u da niyyar neman tabbaci akan abinda ta fada, to amma sai harshena ya gaza furta komai, sakamakon yawun bakina da ya kafe gaba daya. Sai da nayi fama
na tsahon lokąci kafin na kai ga samun damar yin tambayar.
" Wai gaskiya ki ke fada min ko kuma almara?" Ta girgiza kai cikin takaici " Karimah kin sani ko da ina yi
miki wasa ba zan yi miki irin wannan ba"
Tana gama tabbbatar min na dora hannu aka na fashe da
kuka, ina mai yin kururuwa a kan lamarin mai hargitsa zuciya.
Ganin haka ya sanya Asma'u mikewa tsaye, hannuna ta kama gami
da kokarin zaunar da ni " zauna ki ji Karimah wannan ba shi ne mataki abin dauka ba"
Na yi karfin halin zama tare da ita, duk kuwa da cewa har
yanzu ban daina kukan ba. Kokarin tana fara magana ya zo daidai
da lokacin da kofar dakin ta yi duhu, dalilin da ya sanya mu
waiwayawa gaba daya. Abdul ne a tsaye yana kallonmu, fuskarsa
na mai nuni da bukatarsa akan abin da ke faruwa.
"Yauwa! Shi kenan ma shigo ka ji" Asma'u kenan ta ke
gayyatarsa.
Ya sulalo zuwa cikin dakin a hankali, sannan ya nemi waje a
gefena ya zauna.
" Abdul wani babban al'amari ne ya ke tasowa, matar ka
Jimmai me ka sani dangane da ita?"
Fuskarsa ta yi nuni ga rashin ga ne inda tambayar ta nufa, bai
tsaya iya haka ba har sai da ya kai ga furtawa " Asma'u ban ga ne
tambayarki ba"
"Ma'ana an yi maka wani bayani dangane da wani abu da ya
shafi lafiyarta?"
Ya girgiza kai " babu wani bayani da aka yi min irin
wannan" ト
3
"Ai kuwa an ha'ince ka, ha'inci ba dan karami ba, watskila
kuma sakayya sai dai ta Allah. Jimmai tana da kwayoyin H.I.V.
me haddasa kanjamau"
Da sauri ya mike irin mikewar da na yi dazu, ya zazzzare
idanu gami da sunkuyowa " What? H.I.V ?"
Ta gyada kai " Kwarai kuwa, ni tabbatau ce ba zatau ba"
Ko kalma daya bai kara furtawa ba, ficewa ya yi da duk
iya gaggawar da zai iya. Asma'u ta yi kira, tayi kira ina! Lamarin
ya zama tamkar ana kiran kurma. Ta juyo gare ni a lokacin da na
ke kalace ragowar kukana.
" Karimah sai dai ace Allah ya kiyaye, domin kuwa ku duka
kuna iya kamuwa. Na tabbata Abdul ya yi zirga-zirga a tsakaninku
sau da dama, wanda hakan daya ne daga hanyoyin da ke yada ta"
Na yi shiru gami da yin tagumi, hawaye kuma ya ci gaba da
sululu a kumatuna. Asma'u ta mike tsaye " Karimah ni ya kamata
na tafi, na san yanzu mai gidana ya kusa dawowa, amma ki
shaidawa Abdul ku gaggauta zuwa a aunaku. Ina dai zaton yanzu
can wajen Jimman ya nufa, zai kuma samu abinda na fada din
haka ya ke, ke ma kin ga sai ki kara tabbatarwa"
Ban iya cewa komai ba, ta ci gaba " Kin ga fa ta'aziyya na zo
yi miki, amma wannan tashin hankalin ya shagaltar da ni, to Allah
ya jikan Hamidah, ya kuma maye mu ku da wadansu"
tafi
Da kyar na iya cewa " Amin"
Ita kuma sai ta nufi waje, takalminta ta sa gami da fadin "na
Na bita da "ki gaida gida"

Abdul ya shigo har falo ba tare da sallama ba, da kallonsa
na tabbatar da cewa mai afkuwa ta afku. Ya cusa hannayensa biyu
cikin aljihun wando, yayin da fararen idanunsa suka kada su ka yi
ja. Da kallona ya kawar da kansa, ya fada kan kujera kamar wanda
ya bugu.
Na yi karfin halin tasowa na dawo kusa da shi, na fara
tambayarsa abin da na san amsarsa.
Abdul ya ya aka yi?"
Ya dan waiwaye ni daga bisani ya kawar da kansa " rabu
da ni Karimah, ni nan na tsani kai na, a halin yanzu mutuwa ita ce
mafi cancanta da ni, ban ga amfanin rayuwar mutum iri na ba,
shashashan da bai damu da kiyaye kansa ba, ballantana ya kiyaye
wani, ba zan yi musu ba in har likita yace kwakwalwata iri daya
ce da ta jaki"
Na fashe da kuka " Abdul ka dai na fadin haka, ka amince
cewa Allah ne me kaddara komai"
" Dakata Karimah! Tinkaho da cewa Allah ne mai kaddara
komai ba zai hana mutum yin taka tsantsan ba, dubi fa yanda na
kwaso Sakinah a baya, don dakikanci da rashin tunani na kuma
kwaso Jimmai, ba kuma komai ne matsala ba illa rashin nazari. Da
ina nazari da haka duk ba ta faru ba. Ko da yake Jimmai ina ganin
kamar gida ne, ashe a gidan ma aka yi rufa-rufa"
Na sa gefen zani na na share-hawaye " babu komai Abdul
haka Allah ya hukunta, koma me ya faru haka ya so, bari na kawo
maka ruwa ka sha"
Ya kura min ido tsahon lokaci " wai ke Karimah ba za ki yi
min tawaye ba? ba ki lura da irin hadarin da na dora rayuwarki
akai ba? Ai ya kamata ace na ba ki haushi"
Na girgiza kai " ni babu wani haushi da ka ba ni, ban kuma ga
abın da za ka yi ka ba nì haushi ba. Idan ma na dauki cutar a
Yawon banza na dauko tan e ? ai ina ce a zaman aure ne?"
Ya jinjina kai " Eh! lallai Karimah ba zan sa ran a sami
vanzu da komai ya gama kure min ba. Ni dai fata na daya Allah ya
sallakar da ke, in ya so ni komai ta fanjama fanjam! Da na
ısallake, da na kamu duk daya, ko ma me ne ne ni na jawowa kai
na, umarnin Ma'aikin Allah (S.A.W) na saбa, na ke auro mata
domin tsarin halittarsu, gashi nan sakamakon da ya bayyana ya
afku a kai na, in ma na yi wasa ba haramta min kyawun kawai aka
yi ba, har azabtar da ni za a yi da shi. Wace azaba ta wuce ka wayi
gari da cutar kanjamau, surutan jama'a ma azaba ce, kafin ma ayi
batun jiki magayi"
***
Na yi iya yi na akan Abdul ya dan ci wani abu, amma ya ki,
hatta jiya da dare haka ya kwanta. Na fuskanci hankalinsa ya tashi
gaba daya. Ya dube ni bayan da ni na gama karyawa "je ki ki
shirya mu tafi wajen bincike"
Na iso kusa da shi na zauna "Abdul babu wani bincike da za
mu je, domin kuwa ba zai amfana mana komai ba, sai dai ma ya
tayar mana da hankali. Amma idan muka manta da batunsa shi
kenan, sai mu yi zaman mu cikin kwanciyar hankali"
Ya girgiza kai "ban yarda da shawararki ba. Binciken zai yi
mana amfani, domin kuwa sai an bincika zan san matakin da ya
kamata na dauka, idan duk mun haye na kai kara, idan duk mun
kamu ma na kai kara, amma idan ki ka tsallake ni na kamu sai na
yi shiru na kuma sallame ki baki alaikum. Hakan zai taimaka miki
samun mijin aure da wuri, domin kuwa in har aka san ina dauke da
cutar, to kuwa ke da samun wani mijin sai dai a can, domin ban
taba ganin wadda cutar ta kashe mijinta ba ta auru, duk kyawunta
kuma ko 'yar wace ce ita"
Na zura masa ido har ya gama, sannan na kara matsawa kusa
da shi " to bari ka ji Abdul wallahi kar ma ka kuskura ka jarraba
saki na, ni nan babu inda zani koma me ya faru zama na daram.
Kuma irin zaman da ka san mu na yi a baya, ka nemi hakkokinka
daga gare ni nima ka ba ni nawa"
Ya zura min ido " kin san kuwa abin da ki ke fada Karimah ?
sai ki zauna da ni alhali ni ina da cutar ke kuma lafiyarki kalau?"
"Kwarai da gaske, me zai hana ni za ma? Ni ai ko dar ba zan ji ba,
cuta da lafiya ai duk na Allah ne"
Ya jinjina kai " Eh! Lallai amma ke daban ce Karimah,
kuma na yi shirme da na azabtar da ke a baya, da na san haka za ki
yi min halacci ko canza fuska ba zan yi ba, sai dai na makaro tun
da me afkuwa ta aſku, amma ina neman gafararki"
" Abinda ya wuce ya wuce Abdul kama dai na tuno da shi.
kuma ni ban ga laifinka ba, laifi na yi ka horar da ni"
Ya kada kai " Shi kenan tashi ki shirya din mu tafi" Na marairaice" ni fa na fada maka babu inda za ni, me ne ne amfanin karbo takardar da za ta zame min tashin hankali, ka fara
cewa in menene-menene saki na za ka yi, to ai sai a bar shi baka dai san ko me ciki ba, ballantana ka sake ni din"
Ya yi murmushi " kar ki damu da wasa na ke yi miki, ke ma kin
san ba zan iya rabuwa da ke ba, ko kin manta abinda na taba rubutawa ne mutu ka raba aurena da ke"
Wani dadi ya cika raina na fada jikinsa nan da nan " ko kai fa Abdul amma da duk ka bi ka tsorata ni"
Ya rike ni kam-kam gami da wasa da maballan rigata "sai ki fitar da tsoron, jarraba ki na ke yi dama. To tashi ki shirya din mu tafi"
Na kara gyara kwanciyata " to bari na dan huta don Allah, domin na gaji"
"Gama hutawar minti goma sha biyar dai ai ya isa" Sai na kudundune gami da rufe idona, aniyata dai na mantar da Abdul maganar tafiya wajen bincike, bayan da na ji aniyar da ya ke da ita"
"Karimah" Ya kira suna na
"Na'am" Na amsa ba tare da na bude ido ba
"ba dai barci za ki yi min anan ba?"
Na márairaice "kai don Allah Abdul yau na fara barci a kan cinyarka? Ko dai ka fara gajiya da ni ne na tashi?" "A'a kwanta, ni ban gaji da ke ba, amma da duk abinda za ki yi ki kammala a cikin minti goma sha biyar, da sun cika zan tashe ki"
Na yi shiru na rabu da shi, haka ya kasance rike da ni tsahon lokaci, alhali kuma ba barcin na ke yi ba. Ya tayar da ni zaune bayan da mintunan da ya diba min suka cika " to sai ki tashi ki shiryo"
Babu yanda na iya, sai na je na shiryo din. Muka fito daga
gidan a tare, a cikin mu babu wani mai kuzari. Muka hau motarsa,
muku rankaya. Babu wata tazara mai yawa daga unguwar da muke
zuwa cibiyar da mu ka je, hakan ya sanya ba mu bata lokaci mai
yawa ba.
Da fitar mu daga mota muka nufi ginin cibiyar. Zirga-zirgar
jama'a a wajen bai kai na asibiti ba, mai yiwuwa hakan yana da
nasaba da karancin masu fama da matsalar cutar Kanjamau.
Cikin nutsuwa muka fara nazarin ofishin da ya kamata mu
shiga. Ba mu sha wahala ba wajen ganewa, sai muka nufi wajen
kai tsaye. Tamkar a asibiti, shi ma ofishin ba a rufe ya ke ba, hakan
ya ba mu damar hango mutanen da ke ciki. Mai ofishin ne gami da
wata mata suna hira ne, hirar da ke cike da. , alamun
da suke tabbatar da cewa ba matsalar cuta gare ta ba, mai yiwuwa
ma ita kanta tana aiki a cibiyar ne.
Abdul ne ya kwankwasa musu kofa, abin da ya juyo da
hankulan mutanen biyu. To amma juyowar ta su sai ta farar da
wani abu, fuskar Abdul ce ta murtuke, ya kuma fara kokarin
dawowa baya. Cikin gaggawa na yi nazarin fuskokin mutanen
biyu, nufi na shi ne zakulo wanda Abdul ya 6ata rai saboda shi.
Lamarin bai boyu gare ni ba, fuskar matar ce ta canza nan da nan,
abin da ya tabbatar min cewa ita ce abokiyar fadan mijina. Ya
janye ni daga wajen zuwa gaba. Bayan wasu 'yan taku kadan, sai
ya tsaya gami da fuskanta ta "dakata karyar can ta fito tukunna"
" karya " na maimaita sunan da ya kira ta da shi. Lallai gabar ta kai
gaba, to wai ma wacece ita? Tambayar da na ke shirin yi
masa kenan, matar ta fito. Abdul ya sake binta da kallon da yafi na
da kaifi. Daga bisani ya jinjina kai gami da cizon lebe, ya sake jana
zuwa komawa ga ofishin.
Mutumin da muka tarar a ciki yana fara'a sosai ya tare mu
cikin girmamawa, sannan ya nemi jin abinda ke tafe da mu. Abdul
ne ya yi masa bayani gamsasshe, sai ya rubuta mana takarda gami
da tura mu Laboratory domin a yi mana gwaje-gwaje. Ba mu sami
matsala ta fuskar komai ba, illa sakamakon da aka ce sai gobe. Sai
mu ka yi aniyar komawa gida. Sa'in da muka wuce ofishin da
muka fara shiga, matar ta sake dawowa, tuni ma sun sake kulla hirarsu da mai ofishin, sai dai su suka jiyo, mu dai bukatar mu ta biya.
A mota na tambayi Abdul zancen matar, ban sami amsar da
na nema bu. Na sake matsawa, abin da ya sanya shi
duba na" Karimah don Allah ki yi min hakuri, tuna matar kawai
kan sanya na ji kamar zuciyata ta tarwatse"
Dole na hakura na rabu da shi, ba tare da na ji abinda na ke
son ji ba.
***
Gari ya waye sarai, wanda hakan shi ya baiwa mutane damar
shiga hada-hada, amma fa banda mijina, wanda tun shekaran jiya
ya rasa sukuni. A jiya bai fita kasuwa ba, yau ma kuma da alamar
haka nan.
Na tashi daga kan kujerar da na ke a zaune, zuwa ga zama a
kusa da shi. A hankali na runtse hannunsa a nawa " Abdul yau ma
ba zaka fita kasuwa ba?"
Girgiza kai ya yi, ba tare da ya dube ni ba" Karimah idan ki
ka ga na fita kasuwa to na sami tabbaci ne akan cewa lafiyarki
kalau, to sannan ne za ki ga na shiga walwala"
Na gyara zama " idan lafiyarmu kalau za ka ce Abdul"
Karkada yatsa ya yi " ba ta kaina na ke ba Karimah, rashin
sanin halin da ki ke ciki ne, ya sanya ni kasa walwala, bari ma ki
ga na je na karbo sakamako"
Na rirrike shi " Abdul babu inda zaka, ina ji a jikina cewa
sakamakon nan ba zai zama alheri gare ni ba"
Ya kalle ni gami da yin murmushi "Haba Karimah me yasa
ki ke karaya ne? babu abin da zai faru"
Sai ya sabule hannunsa a hankali. Na bi shi da kallo, sa'ar da
ya ke kokarin ficewa. Tausayinsa da na ke ji ya karu a zuciya ta. A
tsayin yini biyu duk ya sakwarkwace, hawaye ya biyo kumatuna.
9
Fitar Abdul ta ba ni damar fadawa tunane-tunane. Kokari na
shi ne zakulo sakamakon da za a samu a kowanne daya daga halin
da za mu iya samun kanmu. Abin dai a bayyane ya ke, in dai mun
haye rayuwar farin ciki za mu shiga. Na kuma tabbata Abdul zai
rinka taka-tsantsan a duk lokaci da zai karo aure. Idan kuwa duk
mun kamu, to lallai za mu karashe ragowar rayuwarmu cikin
takaici. Kallon kyama da tsana ma da mutane za su rinka yi mana
ya isa tashin hankali. Na tabbata za mu rasa ko wane irin sukuni da
mutum zai so samun kansa a ciki.
Idan kuwa lamarin ya zama na haye Abdul kuma ya kamu, to anan
za a sha kallo. Na tabbata Abdul zai yi kokarin saki na kamar
yanda ya fara furtawa, sai dai ni kumą babu inda za ni, mutuwa се
kadai ta isa ta fitar da ni daga gidan mijma.
Ina cikin wannan tunani Abdul ya dawo. Tun daga soro ya
kwalla min kira, na fito daga falo da sauri. Fara'ar da na ga ni a
fuskarsa ma ta ishe ni albishir. Shi kansa sai ya yi kokarin sanar da
ni da baki.
"come on Karimah, nothing is wrong (Karimah babu abinda ya ke
ba daidai ba)"
A guje na karasa inda ya ke, ban 6ata lokaci ba wajen
shigewa, muhalin da ya yi min a kirjinsa, shi kuma sai ya rufe da
ni. Na ma rasa yanda zan kwatanta farin cikin da ke raina, baki na
kuwa ya gaza dakatawa da dariya. Hannunsa ya fara zarya a cikin
kaina, abin da ya sanya ni kara lafewa a kirjinsa sosai. Na fara
magana cikin wata murya mai kama da rada. " Abdul dadi zai
kashe ni"
Ya girgiza kai "dadi baya kisa Karimah, da dadi zai yi kisa da
babu maraba tsakaninsa da wuya"
Farin cikin da ke raina ya ci gaba da karuwa, abin da ya
tilastawa hawayen murna fitowa. Abdul ya sa hannu ya share min "
hari kuka Karimah yayin bakin ciki a ke yinsa, lokacin farin ciki
kuwa sai murmushi da dariya"
10
Na kara lafewa a jikin mijina " Abdul farin cikin da ya tsaya
ga sanya dariya bai cika farin ciki ba, idan farin ciki ya amsa
sunansa ai sai kuka"
Ya gyada kai "kin yi gaskiya, mu koma falo ko?"
Mu ka dunguma falo makale da juna. Da shigar mu ya
zauna akan kujera, sannan ya zaunar da ni a cinyarsa. Na kewaya
hannuna a wuyansa " Abdul wai yaya ka ji a ranka?"
Ya yi min belt da hannayensa biyu "Karimah na ji abinda ya
fi karfin farin ciki ko kuma dadi, ni dai ban san yanda zan kira
abinda na ji ba, ke kuma yaya ki ka ji ?"
"Na ji abinda ya nunka naka dubu"
"Kai! Kai!! Kai!!! Dubu fa ki ka ce? ina laifin ma ki ce kin ji rabin
nawa"
Duk mu ka yi dariya. Ya warware hannayensa " Karimah juyo
nan ki ga ni "
Sai na juyo mu ka yi fuska da fuska da shi, har yanzu kuwa ina
zaune ne akan cinyarsa, mu ka yiwa juna belt gaba daya.
Ya fara magana a hankali " Karimah yanzu kin ga wata sabuwar
rayuwa za mu shiga, saboda haka mu yi clearing din abin da ya
wuce a baya. Ina so ki yafe min duk wani abu da na taba yi miki a
halin sani ko kuskure"
Na jingina goshina da nasa " Abdul ba ma abin da ya wuce ba,
hatta wanda zai zo gaba na yafe maka"
"godiya na ke yi masoyiya ta, ni ma na yi kamar yanda ki ka fada"
***
Karfe taran dare daidai muka kammala hira, abinda ya rage
mana shi ne tafiya mahallin barci. Na dubi Abdul da ke shirin bin
tsayin daguwar kujera " Abdul me za ka yi anan kuma?"
Yayi dan jinjirin tsaki " anan zan kwanta Karimah, wani
maganin majina na sha, ina ganin nan zai fi yi min kusa da bayi"
11
Na tsaya kikam, murna ta ta koma ciki, ni da ada na so mu
more farin cikinmu ta hanyar farantawa juna, shi kuma ga inda ya
ke shirin bugewa. To amma babu yanda na iya tunda larura ce, sai
na nufi daki " to sai da safe"
ummm sai da safe"
Sa'ar da na tashi da safe, tuni Abdul har ya yi wanka, abin
ya yi matukar ba ni mamaki, Ban iya barin abin a raina ba, sai da
na tambaye shi. "Abdul wannan irin sammakon wanka fa da ka yi,
kana shirin zuwa unguwa ne?"
Ya yi murmushi " daurin aure za ni, jiya farin ciki ne ya
mantar da ni shaida miki"
Na yi murmushi ni ma " to ai lamarin ne akwai faranta rai"
Ya gayyato ni ga zuwa a kusa da shi, da zama na ya dora
hannunsa a kafada ta, sannan ya sa daya hannun ya juyo fuskata,
muka kurawa juna idanu. Nice na fara kawar da idona " yaya aka
yi ne Abdul?"
Ya yi murmushi "so na ke yi na yi nazarin fuskarki, ina so ne
zuciyata ta kara amincewa dari bisa dari cewa babu fuskar da ta
kai ta tsari, hakan zai kara nisanta ni da tunanin auro wata matar
bayan ke"
Sai ya kara kura min idanu. Na yi karfin halin kallonsa ido da
ido, abin da ya sanya shi yin murmshi, sai na sake rumtse idona.
Ya ci gaba " Karimah zan so ki yi min alfarma na sumbaci
fuskar nan ta ki sau biyar yanzu-yanzu"
Na yi murmushi " ka yi duk yanda ka so Abdul, ka tuna fa
sunkutukum dina mallakinka се "
Ya sumbaci wuraren da suka fi kayatar da shi, sannan ya
mike tsaye rike da hannuna " zo ki raka ni mota"
ba?"
Na kalle shi cike da mamaki " ba dai tafiya zaka yi babu kari
"karki da mu, akwai abokina da zan biyawa ne, ina jin tsoron
kar ya tsaya jirana, amma ki adana min nawa shayin a flask"
Na mike " to shikenan mu je na raka kan"
19
Muka nufo hanyar waje, kafada da kafada mu ke tafiya da shi, abinda ya tunatar da ni farkon amarcina, babu ranar banza kullum sai na raka shi mota"
Cikin wannan halin muka fito waje, sannan muka taka zuwa
inda motar ta ke a ajiye. Na sa hannu na bude masa, sannan па
dube shi cikin murmushi "bisimillah yallabai"
a
A hankali ya sulale zuwa ga zama akan kujera, ya kamo
hannuna ya rike " Karimah ina mai tunatar da ke komai
rayuwata, kasancewa tare da ke shi ne cikar farin cikina, ina ma
ce za mu kasance tare dindindin, sai dai kash! Inda haduwa ta bi
rabuwa ma nan take saka kafarta"
a
Babu zato sai na ga ya fara hawaye. Na sunkuya zuwa ga
kusantar fuskarsa " Abdul me kuma ya kawo wannan
maganganun? Kana nema ka tayar min da hankali"
"kar ki da mu Karimah, shi mutum a kullum ana so ya rinka
tuna makomar al'amuransa ne, hakan ya kan taimaka masa wajen yin taka tsantsan a rayuwa"
"to na ji amma dai yi shiru haka, ka bari har ka je ka dawo,
na yi tanadin abinda zan faranta ranka"
"ba sai kin fada ba, na sani a kullum kina cikin irin wannan
tanadin, amma yau sai dai ki yi hakuri ba lallai ne na dawo ba, ina
sa ran daga can zan zarce"
Na zare idanu " ka zarce ina?"
Yayi murmushi " kasuwa mana, kin san
ma kawa na je kasuwa"
ba
"ni ma na fi so ka tafi, kwananka biyu fa baka je ba, bari dai
na daina 6ata maka lokaci," Sai na janye jikina gami da rufe kofar
a hankali.
Ya dube ni " to haka zaki bar ni na tafi babu ko wani abu da
zan rinka tunawa?"
Na yi murmushi gami da sunkuyawa ta tagar motar, hakan ya bani damar kewaya hannaye na a wuyansa, sai na sunbaci
kumatunsa na hagu da dama, na kara janye jikina gami da fara daga ma

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment