You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

DIMAUTA

08069524699

MUKHTAR
KWALISA
1

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

DIMAUTA
Haqqin mallaka (H) M. Kwalisa
Bugu na Farko 2008
Shekarar bugu:- 2022
Shekarar bugu na uku:- 2024

Domin ‘Ya ‘yana

Muhammad Arif Mukhtar
Aisha Mukhtar (Amra)
Halima Mukhtar (Amna)

GARGAI
Ba a aminta wani mutum, ko wani kamfani ya
sarafa wannan littafin wajen juya shi ta hanyar wasan
kwaikwayo ba tare da neman izinin marubucin ba.

2

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

DIMAUTA

Mukhtar Isah Kwalisa
3

R

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

DIMAUTA
ashin kwanciyar hankali duk ya damu al'umar wannan
karni, domin inin rashin imani da yawan hare-hare da ake
kai musu, ako wane lokaci a cikin zullumi su ke da shi
suke kwana da shi, kuma suke tashi, kowa ka kalla da
zullumi yake yawo a zuciyarsa, domin gudun kawo hari na
daga kasar kafiran da ta yadu ta girma, ta hanyar sanun
gawurtattun sadaukai.
Kasar Hamran kasa ce da take bin tafarkin addinin tsafi,
wanda duk shekara sukan yanka al'ummar mutane mabiya
addinin Musulunci ga wata kuba da ke tsakiyar garin,
Jinin ya kwarara zuwa cikinta. Kasar tana da sadaukai
masu juriya da tumbe a fagen daga, ba sa gajiyawa, kuma
suna sanun nasara ako wanne hari su ka kai, hakan ya sa
duk.kasashen duniya suka tsorata da Su.
A kowacce shekara suna kaiwa 'yan tsirarun kasashen
Musulmai hari, su kamo bayi da kuyangi, su shayar da
kubar jinin äl'umma Musulmi gareta. Sarki Shamal shi ne
sarkin kasar ta Hamran. ya kasance azzalumin sarki ne
ma'abocin zalunci, bai san tausayi ba, kuma ya tsani duk
wani Musulmi. Kamar yanda al'ada ta tsara duk shekara ya
kan fito yakin da nemo mutunen da za'a shayar da su ga
kubar, nan da kuma kamo bayi; don a bautar da su.

4

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Sarki Shamal ya fito daga cikin gidansa da shiga irin ta
yaki, ya yi tigijim, yasa sulke na bakin karfe, da hula
akansa, ita ma to baqin karfe hannunsa na dama wata
mahaukaciyar takobi ce, rantsatstsiya, an tsafeta Tarihin
takobin yana da yawa, don farkonta ta wani tsohon
sadauki A lokacin idan ka yi duba zuwa ga sarki sai ka
dauka wani shedanin aljani ne. don ya tabbatarwa da
mutunensa cewar, yakin na yau yana muhimmnci. Sarki
ya yi duba zuwa ga sadaukansa, ya ga yawan su sai dadi
ya lullubesa, domin ya san ko babu ko mai yawa su ko a
tarihin rayuwarsa bai taba hada runduna mai matukar
hatsari gami da zaratan da ke a cikinta don haka ya ji a
ransa duk kasar da suka tunkara sai sun murkushe Kasar
da za su dosa.
Boka Kazal ya gabato gaban sarki, ya yi gaisawa ya yi
shiga irin ta bokancisa Munanan kamaninsa sun bayyana
ya zama wani abun tsoro. A hannunsa jakar ce ta bokanci.,
shi ne kuma babban wazirin sarki
"Akwai nasara mai yawa a tafiyar, amman ina hora da
sarki da kada ka sake ka yarda ku yi fito-na-fito da
mutanen Kasar ta Jamir, domin matukar ka yi haka to, za
su karar da duk rundunarka, kuma su kama ka, a matsayin
ribatacce" Cewar boka Kanzal.
Sarki Shamal ya yi matukar mamaki da jin maganar
bokansa, don shi yanda yake tsammani a yanzu a duniya
babu Kasar da bata tsoronsa, domin irin tunbensa a fage
daga, don a yanda yake tsammani a yanzu duk duniya
babu sadauki kamarsa, don haka sai ya yi duba ga
bukan"Kai yanzu ka na ganin har akwai wani sadaukin da
zan ji tsoron fito-na-fito da su? Jin maganar ya sa wazirin,

5

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

kuma bokan sarki ya dube shi "Akwai wani sadauki a
garin wanda shi kadai gayya ne,hatsari ne ga rundunarmu,
kuma shi sadaukın shi kadai fitina ne kuma bala'i ga
rundunar mu kamar yadda ya bayyana gareni ya tarwatsa
duk rundun nan ta mu."
A fusace sarki ya juya ya dubi bokan na sa. Lokaci daya
idonsa ya kada ya yi ja, bakinsa ya soma fitar da kumfa,
fuskarsa ta kuma hadewa. Ya sa hannunsa ya fizgo bokan
nasa da hannu daya ya matso da shi kusa da fuskarsa, da
matukar fusata ya ce da shi.
"Wannan karan alkaluman sun gaya maka karya, na
tabbata babu rashin nasara a garemu, kuma ina maka
rantsuwa da kubar da muke bauta a gareta, da kakana na
goma da ke a cikinta a kwance, babu wanda zai wanzu a
garin face yana gafalalle, kuma na san kubar za ta ba mu
nasara." Ya ce da boka Kanzal. A lokaci daya ya sake shi
ya fadi kasa. Ko kallonsa sarki Shamal bai kuma yi ba ya
ja linzamin dokinsa suka nausa. Sadaukai sai iface-iface
suke yi, suna kaiwa iska sara da makamansu.
**
A Kasar Jarmi, sun kasance ma'abota tawali'u ga addinin
Musulunci, suna binsa sau-da-kafa, kuma suna masu
kyautayi ga addininsu. Sarkinsu adali ne, mai kyautatawa
talakawansa, suna da sadaukai masu tirjiya a fage fama,
basa tsoron mutuwa.Sadauki Kafilu ya kasance tsara ne a
cikin sadaukai,da ne ga wazirin garin, duk garin babu
wanda ya kai shi
sedaukantaka, don shi kadai yana tarwatsa gari guda,
yana da matukar kishin addinin Musulunci. Ya kuma tsani
duk makiyin addinin. Shi kadai yana fita garuruwa ya yi

6

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

wa'azi gare su, idan sun Ki karbar addinin sai ya yake su,
hakan shi ne ya riski sarki Shamal, ya ga gwara ya share
su daga doron kasa tun Suna 'yan mitsatsansu, ba su rayu
sun yi rassa ba,balle har su kawo barazana ga mulkinsa,
don ya taba karantawa a wani littati a cikin litttatan da
kakanin sa suka rubuta suka mutu suka bari. sun ce
musulunci zai girma ya tartsa duk wani addini, haKan ya
sa ya tasarwa kasar Jamir don murkusheta.
Bayan sun sami a Kalla wata daya suna tafiya, Sa rannan
suka karaso daidai garin na Jamir, ganin haka ya sa sarki
Shamal ya yi musu izini da su yi wa dawakan kaimi, su
abka musu, shi kuma da sauran wasu sadauka suka sauka a
bayan gari suka kala tantinansu,Rundunar kuma kaso biyu
suka yı dauki garin na Jamir a lokacin da suke a halin
barci.Sadaukan da sarki Shamal ya zaba suka wuce har
zuwa cikin garin. Suna zuwa suka bala kofar garin, suka
yo dauki kan gidan mutane, suna kashe su, suna kunawa
gidajen su wuta. Kafin lokaci kankani sun yiwa garin
muguwar barna, sun rushe gidaje da yawa, sun kashe
mutane da babu iyaka.
Sadauki Kafilu yana kwance a dakinsa ya ji ihun jama'a.
Ya fito da sauri yana zuwa ya tarad da hari aka kawo
musu, ya ga barnar da aka yi musu, sai zuciyarsa ta baci.
gashin jikinsa ya mimmike. A fusace ya koma cikin
gida ya soma shiga, ya Kimtsa. 'Yan lokuta ya fito a
haye akan ingarman dokinsa, ya yi shiga ya yi tigijim, ya
zam kamar wani shaidani. Ya rike wata sharbebiyar takobi
a hannunsa na dama, daya kuma hannun wani alamudu ne
na bakin Karfe. ya fito da matukar fusata.Ya nufi gida
sarki ya ga an ruguje shi. an kashe mutane. Ya ji ransa ya

7

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

kuma baci, ya tabbatar an mu su barna, don ya tabbata
maharan sun kashe sarkin na su Ya karkata ya nufi
gidansu. gidan waziri Ya tara da an tarwatsa shi an sama
sa wuta, ya ji wani abu ya tokare masa zuciya,ya tuna an
kashe masa iyaye kenan.Duk son da suke masa yanzu an
kashesu. Wani hawaye ya kwaranyo masa, ya ji zuciyar
sadaukantakarsa ta motsa, farin cikinsa ya kare, bakin ciki
ya mamaye masa ilahirin kirjinsa,ya kuna kai cikin gidan,
wuta tana cin gidan. A yashe ya ga mahaifīyarsa an mata
yankan rago. Da sauri ya mike ya haye dokinsa, ya juya ya
nufo waje, yana wani irin ihu da kururuwa, ya nufi sashen
da sadaukan suke.Juyo ihunsa ya sa suka juyo, suka
fuskance shi. ganin irin tahowar da ya yi mu su mutum
goma suka tare shi,amman minti kadan ya gama da su.
Ya kutsa cikinsu, ya soma saransu yana sukansu,yana
gabatar da su zuwa ga ajalinsu, baya barin kai face ya raba
shi da gangar jikinsa. Baya barin wani Kirji face ya bude
shi, ya dunga saukar musu da kofofin bala'i iri-iri
wanda ba su taba jin irin sa ba. Nan da nan ya kuntata
musu, ya zama kamar wani zaki a cikin garken shanu.
Sadauki Kafilu ya dunga sadar da su izuwa ga ajalinsu.
Kafin fitowar al'tmuru ya Karar da su, sai yan tsiraru.
Ganin haka ya sa suka juya da gudu, domin tsira da
rayuwarsu.Kafilu ya rufe musu baya, yana saransu, yana
bulala da duk wanda ya riska, yana dukan kawunan duk
mutumin da ya tara. Kwakwalwa ta yawaita, jini ya dunga
kwarara,
Kamar mayanka, mutuwa ta yi shawagi, gawarwaki suka
yawaita a wurin.

8

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

A Cikin sadaukan kimanin dubu biyu da kyar mutum
uku suka tsira, suma har bayan gari ya raka su. Ya tsaya a
kofar garin ya ja tunga.
Al'amudunsa da takobinsa sai digar da jini
Jikinsa duk a jike yake da Jini Ya koma kamar wani
shaidani, ya tsaya yana huci, yana mai Sauraron wani mai
karar kwana.Sadaukan guda uku suka komä da kyar, suka
gabata a gaban sarki a galabaice. Ganinsu ya sa sarki
Shamal ya a mike a fusace.
"Lafiya na ganku a haka a galabai ce?" Sadauki daya ya
sunkuyar da kansa kasa ya ce.
"Na rantse da kuba abin bauta a garemu, wani
shaidani ya sauka a garin ya yakemu, ya karar da
rundunar tamu, sai mu kadai muka tsira, don na tabbata
mutum bai isa ya yi yakin da muka gani ba." Jin maganar
ta harzuka zuciyar sarki Shamal.
"Karya kuke gafalallu, na rantse da kuba sai na kamo shi
na mayar da shi wulakantace, dan da kai na zan fita na
kamo shi yanzu nan.Sannan ya sa wuka ya fillewa sauran
sadaukan ukun
da suka kawo masa labarin kawuna.
"Ku bi sauran yan uwanku." Ya ce da gawarwakinsu.
Sannan ya fito a cikin shirin yaki, ya hau dokinsa ya shige
gaba, runduna ta rufa masa baya.
Suna karasowa bakin garin suka hangi sadauk Kufilu shi
daya a tsaye ya ja tunga. Sarki Shamal ya yi duba gare. ya
ganshi da Sifar Sadauki, to amman bai taba tsammanin
Kafilu zai iya ta'anati ga rundunar tasa ba, sai dai ko wani
shaidani saudauki ifiritu ne ya sauna.

9

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Da daga murya ya ce da sadauki Kafilu "Ki yi sani ya
kai wannan sadauki ma'abocin jajircewa. Sarki Shamal ya
gabato gareka, kuma yana neman da ka yarda makamanka
ka yi biyayya a gare shi, tun kafin ya saukar maka da
azabar irin ta yaki"Kafilu ya ji zuciyarsa ta harzuka, ya
tuna shi ne ya yi sanadin ya tarwatsa garin na su, ya kashe
iyayensa, kisa
mafi muni, don haka sai yake ganin fansa aka kawo
masa har gida Da zuciyar sadaukantaka ya ce da shi.
"Ka yi sani ya kai wannan sarki ma'abocin zallunci ka
tabowa kanka masifa da bala'i, kuma sai na yi maka Kisan
wulakanci, na je har kasur ka na tarwatsata, na rushe
gidajenta na farfasa ganuwarta, don haka maza bisa bisa
kanka."
Ya yi kånsu yana mai wujijiiga al'amudinsa. Ganin haka
ya sa sarki ya yi wa sadaukansa tsawa da su afka su yi
sukuwar sallah a kansa.Nan fa aka soma cin kasuwar
mutuwa, jini ya soma kwaranya. Duk wurin da ya sa gaba
sai ka ga gawarwaki a kwance. Ya dunga yakarsu da wata
zuciya kamar dutse Ganin sadaukanta irin ta Kafilu ya sa
sarkı Shamal ya
tsorata, kuma ya yarda da naganar bokansa, tabbas a
yanzu duk duiya babu sadauki kamar Kafilu.Kalin wani
lokaci gawarwaki sun yawaila. Kawuna sun barbazu,
dawakai sun wanzu ba mahayansu, ganin nau'in bala'i na
yaki da azabarsa yasa sadaukan sarki Shamal suka juya da
baya da zummar su tsere, da rayukansu, don suna ganin
sadaukı Kafilu kamar ba mutuba ne.

10

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Ganin aniyarsu yasa sadauki Kafilu ya Kara kaimi ya
kifu aka su, ya dunga gaggauta sadar da su zuwa ga
ajalinsu.
Hankalin sarki Shamal ya tashi. Ya yi tsawa ga
mutanensa, amman ina sun dimauce, ganin haka ya yi
dauki kan Kafilu da wata zuciya. Suka yi haduwa, sulke
ya gogi da sulke, damtse ya gogi da damtse,Makamansu
suka hadu wuri guda. Nan fa suka tiririniya, suna tirjiya,
suka dunga kaiwa junansu bugu da sara da suka.
Sarki Shamal ya samu Kafilu sadauki ne tsara.shima
haka Kafilu ya samu sarki Shamal, don tun da yake a
rayuwarsa bai taba gamo da sadauki kamar sarki Shamal
ba.Nan suka wanzu a cikin tintiriniya, Kasa ta duga
raurawa, suka dunga gwada wa junansu salo-salo na
yaki,sauran sadaukan da suka yi saura suka wanzu cikin
kallon nau'inkan fada.Can da Kafilu ya tuna abin da
wannan sarki ya aikata
masa, sai ransa ya kuma harzuka, don haka sai ya kuma
azama ya yi wa dokinsa kaimi, ya dunga kaiwa sarki
Shamal duka ta ko'ina, babu Kakkautawa, ya sauya salon
yaki irin wanda sarki Shamla bai taba ganin irin saba Nan
da nan ya gajiyar da shi, ya kuntattashi. Ganin haka Sai
sarki Shamal ya soma wasu sumbatu yana hamma,yana
damma, amman ina bai sami ikon karasa karato kalaman
tsafi ba
don ganin azabar da yake fuskanta ta
yakl.Sadauki Kafilu ganin ya dimauta sarki yasa ya kuma
azama akan sa ya kinfu da wata zuciya Kamar dutse, can
ya dauki nufashi sarki shamla ya zu ba masa wani sara a
tsakiyar kai hular dake kan ta tarwatse. Ya samu kan sarki
shamla, amman bata shiga Da can ciki ba domin rawanin

11

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

dake kasa, sarki Shanal yayı taga-taga ya zame daga kan
dokinsa ya fadi kasa, Kasa to tashi s sama,sabi da
garmansa Sadauki Kafilu ya matsa zuwa wurin ya kalli
Sarki shamal a wulakance yace dashi.
"A yanzu ka zamto gafalalle a gabana, kuma zan kasheka
na nufi garinka na kashe su, na rashe shi ya zamto kamar
ba'a taba yin shiba, kamar yauda ka aikata ga
kasarmu."Yana gama fada ya sama jujjuya al'amudun dake
hannunsa da zumar tarwatsa kan sarki Shamal. Tamkar
budar ido, wani katon maridin bakin aljani ya bayyana
Siffarsa abin tsoro, kafin Kafilu ya kai duka ga sarki
Shamal har aljanin ya sure shi. Kafilu ya daki daidai wurin
da kan sarki shamal yake, wurin ya zama wani rami.
Da bacin rai sadauki Kafilu ya juyo don ganin wanda ya
aikata masa hakan, amman ina har maridin aljanin ya sure
shi da dokinsa ya daga sama, ya tashi da su. Sannan ya
kalli wani fafadan dutse da ke wurin ya gwara sadauki
Kafilu da shi da dokinsa, nan take ya sume a
wurin,dokınsa kuma ya tarwatse.Maridin aljanin ya dauko
wani sassari na bakin Karfe
ya daure Kafilu a jiki, sannan ya kawo wani magani ya
zuba a wurin da aka jiwa sarki ciwo, kafin ya bace. ya bar
Kafilu a sume, a daure cikin sarKa. Ganin haka ya sa
tsirarun sadaukan suka yo dauki ga sarkinsu don
taimakonsa.
**
A haka suka shafe kwana da kwanaki suna tafiya
Kowanne sadauki ka kalla a matukar galabaice yake da
kyar suke iya tafiya Sadauki Kafilu yana daure a cikin
sarkoki. Ya yi matukar galabaita kwalkwalin da ke kansa

12

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

ya fita, hakan shi ne ya baiwa gashin kansa zubowa, wani
lokacin har ya rule
masa idanu, kana kallonsa za ka san yana cikin damuwa
da bakin ciki matukar.A haka har suka shafe kwanaki suna
tafiya. A safiyar
wata ranar suka isa zuwa kasar ta Hamran, tun daga suka
hango dafifin mutane, alamar sun fito taryarsu, kamar
yadda suka saba ga al'adar mutanen garin, domin boka
Kazal ya sanar da su zuwansu.
A haka su sarki Shainal suka karasa, Sadaukai janye da
Kafilu. Da zuwansu mutane suka dauki shewa da murna
dawowar sarkinsu, bayi suka soma watso furen fulawa.
mai taushin Kamshi ga sarkınsu. Kuyangi suka dunga
watsa turare na almiski mai dadin kamshi, sabanin
kowacce shekaara da idan sarki Shamal ya dawo daga
fagen fama ya kan dunga murna da dagawa jama'arsa
hannu, amman wannan karan fuskarsa a turbune
take.kuma sadaukai 'yan kalinan suka dawo, don a kashi
goma uku ne kawai suka dawo.
Wanda ba su ga yan uwansu ba. suka soma Kuka,domin
sun san an kashe su. wasu kuma suna mamakin yau sarki
da sadauki daya kawai ya dawo, don haka sai mutanen
garin m suka soma tsorata don ba su ga mutanen da za'a
yankawa kuba ba, Boka kanzil ya zo gaban sarki ya yi
gaisuwa yaSumbaci hannnunsa na dama, sannan ya kalle
shi ya shi.
"Sani cewar hankalın jama'arka ya yi tashi, don ba su
ganka tare da mutanen da za sha a shayar da kubab ba sai
sadaukı daya."Sarki ya ji maganar kamar wata suka a
zuciyar.don haka ya juyo da fusata ya kalli mutanen

13

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

nutsuwa, yana daga dokinsa cikin daga murya ya ce. "Ya
ku taron jama' ata."Su kuma suka ce, "Muna gaisuwa ga
sarkinmu. "
Sarki Shamal ya ji dadin haka, don haka sai ya ji ya
sauko daga fushin da yake yi.
"Ku yi sani cewar za ku yi mamakin ganina wannan
karon da sadauki guda daya. To ku yi sani wannan
sadaukin da kuke gani yafi mutum goma da nake zuwa da
su, yafi mutum dari, shi kadai jininsa daidai yake da na
mutum dubu, donin bala'i ne a duniya, masila ne, wanda
suka ga yakinsa za su labarta muku. Don haka ku kwantar
da hankalinku, nan da shekara goma ba mu ba neman wani
jini za mu dunga zuba kubarmu jinin wannan sadaukin
don na tabbata abin bautar mu zai yi matukar farin ciki da
haka."
Yana gamawa ya juya ya nufi hanyar da za ta kai shi
zuwa fada. Jama'a sai kallon sadauki Kafi suke, amman
gashin da ya zubo masa ya hana su ga fuskarsa.
Gimbiya Suhaila ta gabato gaban mahaifinta, da murna
ta tare shi ta kama hannunsa ta sumbata.Sarki Shamal ya
yi matukar murna da ganin yarsa guda daya, rabin ransa,
tauraruwar zuciyarsa, abin farin Cikinsa, wace ya jima bai
ganta ba Gimbiya Suhaila kyakkyawa ce, ta gani ta fada,
don a duk duniya a zamanin babu mai kyawuta, don ko
aljanu tasbaha suke da kyawunta, ya'yan sarakuna da
manyan attajirai na karmin sune suke mutuwa don sonta,
to amman tunaninta baya gare su, ita tafi son farauta.Tun
da take sau daya ta taba bude fuskarta mutanen Barin suka
ganta, a shekara sai da mutane suka dimauce,Suka dunga
sambatu, suka mance a gaban sarki suke, hakan shi ne ya

14

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

sa sarki ya ce ta dunga boye fuskarta Gimbiya Sunaila ta
kai duba zuwa ga Kafilu ta ganshi shi kadai ne a dare
cikin wasu irin' sarkoki bata taba ganin irin su ba. Don
girmansu, don ta tabbata idan aka ajiye su sadaukai goma
da kyar za su iya dagata,hakan ya bata mamaki ita ma, don
tun da take ta sa
duk shekara idan mahaifinta ya yi irin wannan fitar ya
kán dawo da Sadaukai kimanin dari, to amma wannan
karan da mutum daya ya dawo, don haka ta kasa daurewá
sai da ta tambayi mahaifinta. sarki ya kalleta cikin
murmushi hace mata.
"Kiyi sani cewar wannan sadaukin bala'I ne kuma
masifane ha mutane domin shi yafi mutum dubu"Jin haka
sai ta ji tana son ganin fuskar sadaukin,musamman da
yakë gäshi ya rufe masa idanuwaa Shin zan iya ganin
fuskarsa don ko gaba zan iya bada labarin sa; don nasän ba
žan iya karä ganinsa ba"Kwarai 'yatá"Da sauri 'sarki
Shämal ya ce då sadáuka."Kunawa yatä füskär
Kaskantäccèn nan"Gimbiya Suhaila ta gabata gàban
šadauki Kafilu,sadaukai suka janye gashinsá. Cikin tsäwa
suka ce da shi "daga fuskarka gimbiýa ta ganka"ko
kallonsu sadauki Kaflu bai yi ba, a haka ya ji wani kamshi
yä doki hancinsä,zuciyarsa ta soma bugawa don haka Sai
ya ji'yänä muradin" gänin' mai dudan turaren ma'abociyar
kamshi süka' yi musayar kallo da Gimbiya Suhaila
gabansa ya yanke ya fadi domin tunda take bata ganin
mutum mai kyawunsa ba,nan da nan taji begensa ya
mamaye mata zuciya. Ta kasa daurewa da kallonsa ta
cikin mayani sai da ta bude fuskarta. Ai ko da Kafilu ya
ganta sai ya kidime ya dimauce. Ya ce,

15

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Godiya ga sarki da ya kagi mai kyawu
kamarki."Gimbiya Suhaila ta ji maganar, ta ji wani dadi ya
mamaye mata zuciya da taushin murya ta ce da shi.
"Barka da zuwa ma'abocin kyawu da ya dimauta
Zuciyata."Tana gama fadar haka ta rufe fuskarta ta juya ta
nufi wurin da keken dokinta yake ta haye, aka ja aka tafi
da ita.Sadauki Kafilu aka tusa shi zuwa ga wata kurkuku
da ke cikin garin a matsayin ribatacce.
**
Fuskar Kafilu ta dunga bayyana a cikin idon gimbiya
Suhaila, wutar begensa ta dunga zabalbala mata zuciya, ta
kasa zaune ta kasa tsaye."Barka da zuwa ma'abociyar
kyawu da ya dimauta zuciya." Maganar Kafilu ta dunga
yawo a cikin zuciyarta.A yau kwana biyu kenan da kamo
Kafilu ta ganshi,amma har ta zabure ta rasa mafita, ta rasa
abin yi.Don haka ta kirawo wata kuyangarta 'yar kasar
Sin,ma'abociyar hikima da yawan tunani, hakan ya sa ta
zamto amintacciyar gimbiya Suhaila. Gimbiya Suhaila ta
labarta mata halin da take ciki.Jin maganar ya baiwa
kuyanga Zulza matukar mamaki, ta ji abin ya zamto mafi
girma a gareta.Ta yi duba zuwa ga Suhaila kallo na
nutsuwa ta ce da ita
"Lamuranki yana da matukar wuya da kuma hatsari,to
amma ki yi sani raina fansa ne a gareki ya shugabata."Ki
yi sani ya Zulza ina son sadakin nan, kuma zan iya shan
gidauniya, dominsa don haka bana shakar komai na daga
wani mutum, kuma na rantse da kuba duk wanda ya kawo
mini matsala ga lamarina sai na shayar da shi gidaniya ta
mutuwa." Jin maganarta ya girgiza zuciyar kuyanga Zulza,
ta yi shiru zuwa wani lokacı tana nazari, daga bisani sai ta

16

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

numfasa gami da fadin."Ina ganin tun da shugaba mai
gadin kurkuku, wato ma'ana Jal nake nufí ina ganin tun da
ya zamto ma'abocin son Rawa ta duniya, za ki iya kawata
zuciyarsa da dukiya,da nunawa za ki nutsar da shi a cikin
dukiya, na tabbata zai aminta da labarin mu." Cewar
kuyanga ZulzaGimbiya Suhaila ta ji matukar dadi, da
wannan shawara ta Zulza. Don haka sai ta soma yabo ga
kuyangar Zulza, tana kambamata da fadar hikimarta.
A wannan lokaci suka yi hawa tare da ita da
kuyangarta suka nuti gidan kurkukun. Suna zuwa fadawa
suka bude mta, ta shiga ta samu shugaban mai jiran
kurkukun Jal a zaune,yana ganinsu da gaggawà ya fadi ya
yi gaisuwa, cikin gimamawa. Sannan ya dakawa sadaukan
tsawa nan da nan suka samar da wajen zama ga
ginbiya,suka kawata wurin da abubuwan ci da na sha.ya
nisa Bayan an nutsa sosai sai kuyanga Zulza ta yi duba ga
Jal, duba na yaudara Nan da nan sai Jal ya
dinauce.kyawun Zulza ya dimauta shi, ganin haka sai
Zulza ta kudurce makirci a Zuciyarta.
"Ka yi sani ya kai Jal mun zo gareka tare da Gimbiya
don mu magance wata matsala da ta addabe mu, matsala ta
ta zamto sirri daga ni sai kai, sai gimbiya matukar za ka
dunga biya mana ita, to za ka samu dukiya." Jal jin an
ambaci dukiya sai yawonsa ya tsinke."Maza fade ta yake
Zulza ni kuma na gaggauta biya muku ita."Nan da nan
kuyanga Zulza ta sanar da shi lamarin.Jin maganar tasa Jal
ya yi wani tsalle gefe, gami da nannauyar ajiyar zuciya, ya
durkusa a gaban gimbiya ya ce."Ki yi mini rai ya
shugabata, don ba zan iya biya miki bukatar ba, don gwara
ki bukaci raina, na baki akan abin da kika bukata."

17

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Hankalin gimbiya Suhaila ya yi matuker tashi, jin
maganar. Hawaye ya soma kwarayo mata, ganin haka sai
kuyanga Zulza ta dubi Jal ta yi masa wani tattausan
murmushi. Sannan ta warware wani dauri da ke gabanta,
na'uin dukıya ya bayyana. Ko da Jal ya ga dukiyar sai
yawunsa ya tsinke ya dimauce.Ganin haka ya sa kuyanga
Zulza ta kuma yin murmushi.
"Mai ka gani za ka yarda mu ba ka duka duniyar
nan,kuma duk zuwa mu ba ka kaso makamancin wannan,
ko kuma mu tafí da ita mu nemi wani wanda zai iyà?"Jal
ya yi daraf ya damki duniyar. Ya ji to da gaske ba

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment