Downloaded From https://tknovels.com.ng MASARAUTAR MU! 4. SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com babbangoro2015@yahoo.com SADAUKARWA Ga 'yar uwar da muka rasa a TAKORITES. Allah ya jikan ki da rahma HASNA'U yasa aljannah ce makomar ki. Ya bamu guzurin tadda ke. Takorites bazamu taba mantawa da ke ba. Da zaman amincin da muka yi tare. Muna son ki Hasna. JINJINA Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. GARGADI Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, youtube, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali. MASARAUTAR MU 4 Saadatu na gyangyadi bisa dardumar da ta yi sallahr asubahi, kamshin turaren Yarima ya ziyarci hancinta wanda ya durkusa a gabanta kamar ita ce Yareemar shi subordinate. A hankali ta bude idanunta sai suka sauka cikin na Yareema. Wanda ke kallonta da dukkan kauna da soyayyar duniya cikin idanunsa. Sannan kwayar idanun sa sun nuna submissiveness wato karbar laifin da ya san ya yi. Ta maida idanunta ta lumshe don ba ta san me za ta ce masa ba, ya bata mata rai da yawa, har ba ta son ganinsa. Don jikin ta ya bata ko daga ina yake, to tare yake da Aisha-Sultana tunda ta ga fitar su tare. Ranar ta ta farko a gidan sa, ranar alfaharin kowacce amarya, ita nata angon ya tafi da matarsa hotel ne ko wane waje bata sani ba ko sallama bai yi mata ba, idan ta ce ba ta ji ciwon hakan ba hakika ta yi karya. Ita bazata ce kishi take ba amma taji ciwon abun a can kasan zuciyarta yadda bazata iya kwatantawa ba. Im sorry Princess!. Dr. Sageer ya fada cikin lallashi. Da karyayyar murya mara amo. Ba shi da kalaman kare kansa, so he admit kawai cewa ya yi laifi. Ya sake cewa, Im so sorry Saadahtouh, yanzu taso mu je mu yi sallama da su Fulani mu raka su filin jirgi sai mu dawo a yi min bulala goma sha biyar. Ai da jin haka ta yi maza ta mike ta nufi kofa batare da ta kalle shi ba, da ma da hijabinta jikinta. Yareema bai mike ba, ya ci gaba da durkuso a inda ta barshi. Sai ta ja ta tsaya daga bakin kofa tana kallonsa questionably. Ya lumshe mata shanyayyun idanunsa ya ce, Saadatuh, not even a good morning kiss? Saade ta juya masa baya cikin jin haushi, zuciyarta na tafasa, ita wane kiss ta iya? Meyasa bai samo can a wajen tubabbiyar baturiyar sa da ya dauka suka tafi hotel suka bar ta ba? Tana mai tambayar kanta wai dama ashe haka Uncle Yareema yake tana masa kallon salihi duk da abinda matar sa ke fade a kansa mafi muni? Daga sanda ya taso ya tako zuwa gaban ta, zuwa sanda ta ji saukar hannunsa ya zagaye bayan ta gabadaya ya rungume ta tsam-tsam, ba ta tantance ba. Im sorry Saadah, very sorry. Ban yi da niyya ba, uzuri ne mai karfi ya rike ni. Amma ko ina nake, cikin kowanne hali kina rai na Saadahtuh. Saade bata san yaya aka yi ba ta sunne kai cikin kirjin Yareema, zuciyar ta tayi wani irin sanyi da yadda Yareema ke lallashin ta, daga can kasan makoshin ta ta ce, Ni ai ban ce komai ba Yaya Yareema, ko ka ji na yi complaining? Na riga na san mijin wata aka aura min, don haka I should expect things like this. Don Allah mu bar zancen nan mu je wajen su Fulani. Sai hawaye. Wadanda tuntuni suke son samun damar zubowa, bata basu dama ba, sai yanzu da weakeness din ta na kishi ya nuna a cikin sautin furucin ta. Ya ce, Don zuwa za mu je, amma kafin nan he began to kiss her passionately, wani irin zazzafan kiss wanda ya sa Saadatu gigicewa da ficewa a hayyacin ta. Har yanzu ta kasa sabawa da sumbar Yareema Sageer mai tsirgawa har cikin ruhin ta, she always feels it strange a tare da ita. Sai da ya yi mai isarsa amma ko taya shi bata yi ba, sannan ya kama hannunta suka fito. Ya rasa kuma ta hanyar da zai bi ya goge laifin sa. A hotel din hilton sun samu Fulani da Maimartaba sun shirya, direban Yareema kuma ya debo su Fanna, don haka ba su bata lokaci ba kuma bata samu damar yin wata magana da Fulani ba sabida Askirama yana wajen, da ta yi mata korafin abinda Yareema yayi mata jiya; ya tafi ya bar ta ita kadai ranar ta ta farko a gidan sa (the first challenge), don haka basu bata lokaci ba suka wuce filin jirgin saman Nnamadi Azikwe. Ta hadiye bacin ran ta ita kadai. Da kyar Saadatu ta saki Fulani lokacin da jirginsu zai tashi, tana kuka Fanna na yi. Sai da suka ga tashin su Yareema ya kama hannunta suka koma gida, jikinsa a sanyaye don har zuwa lokacin Maimartaba ya ki sakar masa fuska. Kuma bai yarda sun yi musayar kowacce kalma ba har jirgin su ya tashi. Sannan Saade ma ta ki sakar masa fuska har yanzu fushi take. Suna shigowa gida ya janyo daya daga cikin jakunkunanta da ta dawo da su ya soma fidda mata kaya da kansa. Sai da ya fidda kala bakwai ya ce ta dauki duk abin da ta san za ta bukata na kwanaki bakwai, yana rike da kafadun ta bayan sun shiga dakin ya ce, Za a yi refurbishing gidan nan kafin ki fara zama a cikin sa. Zaa fidda komai dake ciki a kawo wanda Maimartaba ya yi miki ki tsara shi yadda ki ke so. Ita dai ba ta ce komai ba, ta gane so yake ya wanke laifinsa. Ko ina zai kai su kuma? Oho! Bai jira amsarta ba ya tafi nasa dakin don ya hada nasa kayan. Har ya janyo madaidaiciyar trolley ya fito zuwa dakinta Saadatu ba ta motsa daga inda ta ke ba. Da alama wanka ya kara yi ya canza kaya zuwa wani danyen yadin boyel fari kal mai shara-shara har tana iya hango singlet dinsa. Ya tsaida trolley din a kan tayoyinta ya karaso cikin dakin, cikin sanyin murya ya ce, Saadatuh mu je ko? Ta sunkuyar da kai hawaye na son zubowa, kewar Fulani, Fanna da Zarah ke damun ta. Yanzu kuma Dr. Sageer na cewa zai kwashe ta su yi wani wurin har tsayin kwana bakwai. Ni ba inda za ni, jibi za mu koma makaranta. Dr. Sageer ya harare ta, ya ce, Ko yanzu za ku koma ke ba za ki koma ba, gara tun wuri ki sani, da da yanzu ba daya ba ne, lokacin da babu nauyin kowa a kanki. So ki bi ni a hankali in na ga dama sai in soke karatun gabadaya. Hawayen da ta ke ta tattali kada su zubo suka zubo din. Ta mike cikin fushi ta dauki handbag dinta. Ba abin da ta dauka bayan ita, shi ya ja mata tata jakar suka fito. A cikin motar Yareema 4Maticsuke tafe, babu mai magana daga shi har Saade, tuki kawai yake cikin nutsuwa da kwarewa. Tun tana tsammanin cikin Abuja ne inda za su je din har ta ga ya kama hanyar barin gari. Mikakkiyar tafiya sosai suke yi akan titin Jos, uffan ba ta ce masa ba. In ma sayar da ita zai yi ya sayar, Fulani da Maimartaba su suka jawo mata. Sai wajejen azahar suka shiga garin Jos, ya nemi wajen sallar matafiya a gefen hanya wanda mata za su iya amfani da shi ya yi parking. Kwarai ta ke son shiga toilet don haka har ta riga shi fitowa. Sai da suka yi sallar azhar (kasaru) sannan suka sake daukar hanya. What do you want to eat? (Me ki ke so ki ci). Yareema ya tambayi Saade. Shiru ta yi masa kamar ba da ita yake magana ba. Ya yi kwafa ya ci gaba da tuki. Ya rasa gane inda ta sa gaba, in laifin da ya yi mata jiya ne ai ya ba ta hakuri, ya kuma karbi laifin sa. Yayi duk irin lallashin da ya kamata. Wannan shirun da ta ke masa yana ci masa rai. Ya ci gaba da tukinsa yana tunanin ta inda zai billo mata. A hanyar fita garin Jos ya tsaya ya saya musu gasasshen nama mai laushi, kuma mai yawa, ya hada musu da gorar ruwan swan mai sanyi, sannan suka sake daukar hanya. Ya bude naman ya ajiye a gefenta, kamshinsa ne ya tado mata da tsohuwar yunwa kuma da ma dai akan abinci ba ta iya filako. Don haka ta yi fuska abinta ta hau cin nama cikin yanga. Ta gefen ido Dr. Sageer ke kallonta yana murmushi, komai na Saade burge shi yake ba tun yau ba. Suna cikin tafiya wayarsa ta yi kara, da ya duba sunan Ya Gumsu ne. Sai da ya ji gabansa ya fadi, har fargaba yake magana ta sake hada su. In dai alkawarin da ya yi mata ne ai ya cika. Saade ido kawai ya zuba mata sai dan abin da baa rasa ba, wanda dan Adam ba shi da iko a kansa. Tsoro yake kada ta yi masa maganar Hajjaju shi ya sa da ya je mata sallama bai gaya mata tare da Saade zai taho ba. Amma ya san bai isa ya ki daga kiran mahaifiyarsa ba. Duk irin rigimar ta, wadda ta diga masa jinin haihuwa ta dauki cikin sa watanni tara ta haife shi cikin wani hali na kaka-ni-kayi ba tareda taimakon kowa ba. Don haka ya rage gudun motar ya amsa kiran Ya Gumsu da sallama cikin tsantsar ladabi. Ko amsawa ba ta yi ba ta jefo masa tambaya. Da gaske da yarinyar nan ka tafi Abuja? Yareema Sageer ya yi shiru cikin rashin sanin abin cewa. Ya Gumsu ta yi kwafa, cikin tsananin hushi ta ce, Watanni uku na ba ka ka zo a yi maganar auren ka da yar Sarkin Bauchi (Hajjaju) kuma watanni uku na ba ka ka sako mata yarta, idan ba haka ba ALLAH YA ISA haihuwarka da na yi, na sallama ka ga Bilkisu da yarta. Tana gama fadin hakan ta kashe wayarta. Yarima ya ja wani irin birki a tsakiyar titi, ji ka ke kuuuu! Saura kadan ya buga wa motar gabansa. Daga shi har Saade suka jirkito sannan suka koma mazauninsu daidai kasancewar duk da belt a jikinsu. Da sauri ya sa wa motocin bayansa signal, sannan a hankali ya sauka gefen titi, ya danna wani abu gilassai bakake (tinted) suka maye gurbin masu haske. Saadatu ba ta yi aune ba sai ji ta yi Yareema Sageer ya jawo ta jikinsa da karfi ya rungume ta, cikin kunnuwanta yake rada mata. Cikin kowanne hali kada ki rabu da ni Saadatuh! Shiru ta yi, bugun zuciyoyinsu na bugun kirjin juna. wani irin moment ne mai wuyar fassarawa ga Saade komai na Yareema ratsa ta yake har cikin kwakwalwa his gentle touches, his sexy voice, and everything da yake yi a yanzun. Kasa magana ta yi, domin gabadaya Yareema ya gama rikirkita duniyarta da zuciyarta cikin dan lokaci kalilan. Ta ga ba shi da niyyar ci gaba da tukin motar ga yamma na yi musu, ga shi ba ta san iya inda za su je ba, don haka ta janye gefe tana regaining consciousness. Lokacin ne ya ja motar suka ci gaba da tafiya. Amma sabanin lokacin tahowarsu ta lura wannan karon akwai babban abin da ke damunsa tun wayar da ya amsa. A hankali kuma barci ya dauke ta. Ba ta farka ba sai da suka shiga garin Bauchin Yakubu. Nan ma ta dauka masauki zai nema musu musamman tunda dare ya yi, amma sai ta ga ya kara nikar hanya. Ba ta so Yareema ya ji muryarta balle ya yi tunanin ko ta huce daga fushinta (sunan littafin Takori mai zuwa, NAHUCHE), shi ya sa ta yi masa shiru. Ba su dade suna tafiya ba ya karya kan motar suka hau titin da ta ga sign board dinsa zai kai mutum ne YANKARI GAME RESERVE. ****** Yankari game Reserve and Resort na nan a Wikki Camp. Yankari na daya daga cikin Nigerias Foremost Tourist attractions, ana kuma kiransa (home of wild life) saboda wadatar manyan namun jejin da ke cikinsa. A ciki akwai hotel domin maziyarta wato Marshall Suit a nan Yareema ya kama musu daki V.I.P Room. Kwarai attraction na Yankari ya dauke hankalinta har ta manta fushi ta ke da Yareema, duk da cewa dare ya yi musu amma koina haske yake da fitilu kamar rana. Ba ta san lokacin da ta dora hannunta a kan na Yareema ba, wanda ke bisa birkin mota. Uncle au? (ta toshe baki da ta tuna ya hana ta kiran sa Uncle) Prince, kwana za mu yi? Kwana nawa za mu yi a nan?The place is quite attractive and I like it. Mutane da yawa na kiransa Prince, musamman abokai, amma bai taba jin wanda ya fada with correct accentdawankakken harshe da makogaroirin Saade ba. Bai san sanda ya yi murmushi ba don ya ji dadin sunan da ta canza masan. Ya dube ta da gajiyayyun idanunsa irin na wanda ya sha tukin mota ya gaji, In kin yarda za ki yi min tausar tukin nan da na sha, kuma za ki ba ni baby in sa masa suna Dan Yankari, ko kwana nawa ki ke so mu yi sai mu yi abinmu, tunda babu mai jiran mu ko neman mu. Da sauri Saade ta kai tafukanta ta rufe fuskarta, kunya kamar ta yi ya ya, da ta san abin da zai fada kenan da ko kusa ba ta nuna shaawar wajen ba har ya gane ya nemi reward. Reward din da duka cikin biyun da ya ambata babu wanda ta ke jin za ta iya, don sosai ta ke ganin girman Yareema Sageer, ta kasa accepting reality na kasancewarsa miji a gare ta har zuwa yanzu. Har gobe kallon matsayinsa na baya ta ke masa (Uncle/Guardian) duk da he seldom kisses hera duk lokacin da ya bukaci hakan a kwanaki bakwan su tare, cikin siga mai nuna tsananin bukatuwar miji zuwa ga matarsa (physical urge). Suna shiga dakin nasu ko zama ba su kai ga yi ba Saade na ajiye handbag dinta akan kujera wayar Sultana ta shigo wayarsa. Bai ki amsawa ba, amma da ya daga wayar bai ce komai ba, sauraron ta yake yi. Sultana ta ce cikin fushi. Sageer ina ka shiga ne har yanzu ban ganka ba? Na dawo aiki tun dazu ga Uche baya gidan Ina inda ki ka aike ni tare da amaryata. Ke da ganina sai ranar da ki ka karbi addinin musuluci da gasken-gaske, sai kin tuba kin bar giya gabadaya, if not ki kama hanyar Korea ba ni da ranar dawowa. Wani ihu Aisha-Sultana ta saki a cikin wayar, You are lying you cant do this to me Sageer remember Im your Rose, wadda ta bar kasarta da addininta ta shigo wani saboda kai. Ya ce, sabida jiki na dai. Notbecauseofme, in sabida ni ne you can sacrifice everything for my sake, you will give me children. Abu daya nake dubawa da ya sa ban sake ki ba a jiya; mahaifi na baya barin saki. You hurt my father ko gaisuwa ta ya daina amsawa. Sultana ina yi miki sallama, na gaya miki in bazaki iya barin giya ba zaman mu ba zai taba dorewa ba, kin cire mahaifa ba da sanina ba, kin dauke ni kawai a matsayinsex slave ban yarda da wannan soyayyar taki ba. Na ba ki zabi, ko barin GIYA ko komawa Korea ne ko Amsterdam ke ki ka sani.... Yana gama fadin haka ya kashe wayar gabadaya ya ajiye ta gefen bed side-lamp. Saadatu tuni ta shige toilet da ta fahimci sensitive magana yake yi da matarsa. Ta yi wanka ta gasa jikinta sosai daga gajiyar zaman mota. Ba ta san me ya sa ya zabi su taho a mota ba tun daga Abuja har Bauchi. Daga baya ta lura cewa tukin mota is his hobby. Ko ba komai yana jinsa a privacy da Saade, ba tare da wani ya gifta a tsakaninsu ba, ko da kuwa ba za ta yi masa magana ba. Kafin ta fito ya yi musu odar abinci na alfarma, kayan da ta shiga da su da su ta fito a jikinta, sai tawul da ta rufo a kansu. Yareema ya shiga wanka wannan ya ba ta damar shiryawa a nutse. Amma maimakon ta sanya kayan barci sai ta dauko wata kakkaurar laffaya ta nannada ta dora a kai. Kai ka ce unguwa za ta tafi, ba ta yi wa fuskarta kwalliyar komai ba banda wet-lips da ta shafa kadan, amma ba karamin kyau ta yi ba. Ta daga ido ta dubi Yareema Sageer yana fitowa daga toilet ruwa yana yarari daga cikin gashin kansa. Bakin kyakkyawan Babarbare mai kama da Mai Askira. Tawul kawai ya daura zuwa gwiwoyinsa, ta hango wani ingarman physique chestna manyan maza wanda ya sanya ta ba shiri ta sunkuyar da kanta. Lokaci guda jikinta ya dauki rawa da makyarkyata lokacin da Yareema ya tako zuwa gabanta. Kamshin bathrobb din da ya yi amfani da shi na desire dunhill ya bakunci hancinta. Saadatu Hashim, tayi saurin sunkuyar da kan ta cikin neman taimakon Allah ganin irin kallon da Yarima ke mata. Kallo ne mai aika sakon kiran miji zuwa ga matar sa. Ya kira sunanta da wata siga da bai taba kiran ta da ita ba wanda hakan ya sa ta dago ido a hankali ta dube shi, idanun ta na ragaita, ya kama dukkan hannayenta ya mikar da ita tsaye, hannayensa sarke cikin nata. Ya ce, Saadatu hakurina ya gaza, na yi alkawarin da ba zan iya saukewa ba, Im so sorry Saadatu. Na daga kafar iya yadda zan iya, kuma na tabbatar kin samu tsarki, ki yarda ba zan cutar da ke ba, kuma ba zan hana ki karatunki ba, sannan zan bi hanyar da ba za ki samu ciki yanzu ba. Ki yi hakuri Saadatu, hakkina nake so na aure a daren yau ba sai gobe ba Saadatu, I promised you it will only be sweet, not hurting akwai barazanar da nake fuskanta wadda tasa dole zan tabbatar da aurena a yau. Saadatu ta soma kuka, Yaya Yareema ni ban shirya ba, na karanta a biology (reproduction) yana faruwa ne sanadin haka in na zo haihuwa mutuwa zan yi. Im only 19 years. Daga yadda jikin Yareema ke kyarma ta tabbatar yau ba ta da maceci sai Allah. Kalaman fatar bakin ta sun yi kadan su sa Yarima fasa abinda yayi niyya. Cikin wata sassanyar murya ya ce, Saadatu hakuri za ki yi, ni ma ban shirya hakan a yau ba, amma ba zan bari a raba ni da ke ba, dole in tabbatar da ke matsayin matata a daren yau. Iyayenmu har shekaru sha hudu ana musu aure, kuma suna haihuwa lafiya tambayi Fulani shekararta nawa sanda ta haife ki.. and he began from there... with very hot and irresistible kisses..Saadatu roko ta ke tana magiya, amma kamar tana kara zuga Yareema Sageer ne. To ka bari in ci abinci? Ta fada cikin ragaitacciyar murya jikin ta na kara karkarwa. Kafin kukan ya kwace mata gabadaya. Ya soma warware mata laffayar idanunsa ko buduwa ba sa yi, Abinci? Abinci fa ki ka ce Saadatu? Im sorry ki ba ni only two hours in ba haka ba zan cutu Saadatu. Da ta ga ba sarki sai Allah, sai ta mika lamarinta ga Allah. Hawaye na bilbila, in wuya ta yi wuya ta kira sunan Fulani, yau har Hanne da Raheema sun sha kira da neman taimako daga bakin Saade. So it was with every woman. Cikin awanni biyun da Yareema Sageer ya ambata, ya mayar da Saade cikakkiyar matarsa, wadda ko mutuwa ya yi sai ta yi masa idda. Bayan samun nutsuwarsa bai juya mata baya ba, rungume ta ya yi with utmost devotion and affection wanda baki ba zai iya fassarawa ba. Tunda yake biye-biyen matansa, farare, jajaye da bakake, da aure da ya yi na shekara da shekaru bai taba zama sexually satisfied irin yau ba. Rayuwarsa daga ranar ya tabbatar ta juya zuwa anotherdirection, zuwa sabuwar rayuwa wadda babu sauran sabon Allah a cikinta. Saade na kuka, Yareema na lallashi, ta rantse cikin daren nan sai ya maida ita Askira, bazata kuma zuwa gidan sa ba, ashe haka auren yake bata sani ba? Kuma ya rasa da wa zai yi sai ita kanwar sa da aka bashi amana don kawai ita ba Askirama ne ya haife ta ba? Kuma ta rantse sai ta gayawa Fulani komai. Wani abun in ta fada dariya Sageer yake amma a cikinsa, yadda ta ke a fusace din nan daren yau za ta iya kai duka, tunda cizo da yakushi ya sha su har ya gode Allah. Na ji duk abinda kika ce Saadatu, na ji ni dan ne, amma na Saadatu da Aisha-Sultana kadai, na amshi laifina ki yi hakuri ki yafe min, rayuwar will not besmooth ba tare da wannan din ba, baki ji ba yanzu duk wani tension da ke kaina ya fita, duk wata damuwa ta gushe, babu komai a rai da zuciya ta sai SAADATOUH,and I want to use this mediumin gaya miki tun daga karkashin zuciya ta cewa;I love you very- very muchhh!. Yadda ya furta kalaman na karshe har cikin ruhin Saade, ta ci gaba da kuka ba ta ce komai ba. Har ya je ya hada ruwa ya dawo ya dauke ta ya sanya a jacuzzi idanun Saade a rufe suke suna bulbular da hawaye. Idan wannan ita ce rayuwar diya mace hakika ta jinjina wa mata. Duk wani taimako da ya kamata miji maabocin kulawa ya nuna wa matarsa, Yareema Sageer ya nuna wa Saade daren yau. Abincin kuma da ya ce ta ci bayan sun kimtsa, cewa ta yi ba za ta ci ba, sanda ta ce zata ci ai bai saurare ta ba. Ya yi juyin duniya ta ki, sai kuka. A haka suka kwana, washegari ko waya bai kunna ba, tunda ya yi wanka ya tafi falo ya barta a dakin, ya kunna talabijin domin ya gaji da lallashin. Ko yaron goye nan ya ga Saa ya barta wajen kukan banza. SAADATU SAAR MATA!!! Yareema Sageer ya fada a fili, yana tuno kalaman Mai Askira. Za ta dauke kwadayinka a kan sauran mata tunda Bilkisu ce ta haife ta matan Baggara ne don manya aka halicce su. Murmushi ya yi yana jin kaunar mahaifinsa na kara ratsa shi. Sai kawai ya dauki wayarsa a gefe ya kira Maimartaba. Da kyar ya daga wayar tashi, sabida a ganinsa Sultana ta ci gaba da kafirci ne da sakacin Yareema. Ga shi an ce Da na kowa ne ba zai so ya sa shi sakinta ba. Amma Allah ya gani auren Aisha da Yareema ya fice masa a ka. Damuwarsa ita ce irin tarbiyyar da za a bai wa yaya idan Allah ya kawo. Ciki-ciki Mai Askira ya amsa gaisuwar Yarima, shi kuma excitedly yake bayyana masa dalilin kiransa da ya yi Godiya marar adadi da ba shi auren Saadatu, ya kuma yi alkawarin rike aurenta da daraja da amana har karshen rayuwarsa. A karshe ya dora da bada hakuri a kan Sultana, ya ce, ya dauki matakin kaurace mata har sai ta daina shan giya. Idan ba za ta iya dainawa ba ya ce ta tafi garinsu. Wannan hukunci ya sanyaya ran Askirama har ya sanya musu albarka, ya kuma ce ya saya wa Saadatu waya mahaifiyarta na cikin kewarta, ga shi ta bar wayarta a nan dakinta na Unguwar Fulani Bilkisu. Yareema ya ce, A nan inda muke ba za a samu waya ba, amma in mun koma Abujan zan saya mata. Mai Askira ya ce cikin tsokana. An bar kasar ke nan zuwa shahar asal (honeymoon)? Yareema ya yi murmushi cikin jin kunya yana shafa kai, ya ce, Aah Alanguburo muna cikin Nigeria. Na kawo ta ta ga dabbobi ne, a nan Yankari Game Reserve. Askirama ya yi dariya, idan yana magana da Sageer mantawa yake shi Sarki ne. He so much love him, zai iya komai don ya faranta masa ko da kuwa kara masa wata mace ne bayan Saade in dai har zai nutsu ya tsaya a kan matansa na aure. To a ga dabbobi da kyau. Ina gaida Giwayen Yankari. Dariya Yareema ya yi, sannan suka yi sallama cike da begen juna. Ya koma dakin, Saade na kwance har yanzu yadda ya barta abincin da aka kawo musu ko tabawa ba ta yi ba. Da ya duba sai ya ga bacci ne ya dauke ta, ga busasshen hawaye a fuskarta, ya tsugunna ya sumbaci goshinta, sannan ya hau kintsa kayansu da ya yi watsi da su a dakin daren jiya. Jinya sosai har ta kwanaki uku cif! Yareema ya yi ba shiga ba fita, ko kofar falo ta ki fitowa sai a rana ta uku ne ta yarda ta ci abinci ta koshi, amma a tsayin kwana uku oldenburger fresh milk kawai ta ke sha a Yankari. Ranar da ta dan soma walwala, Yareema bai yi kasa a gwiwa ba ya sake kalallame ta ya maimaita laifinsa. Sai dai wannan karon ita kanta ta san da bambanci. So sweet, so gentle. Kafin su bar Yankari cikin kwanaki bakwai Saade an zama manyan mata. Ta iya dauke wa mijinta Yareema Sageer Yusuf Askira lalurar da mata hudu ba za su iya dauke masa ba. Sun dinke sun zama miji da mata na haqiqa mafiya kusanci da juna, maabota soyayyar da biro ya yi kadan ya bayyana ta. Sai a na i-gobe za su tafi ne suka zaga wild life na cikin Yankari Resort, Saadatu ta ga dabbobi iri-iri a fili, wadanda sai a talabijin ta ke ganinsu. Ta baro Yankari with nostalgia, ta sanya zamanta na amarci na dan lokaci a Yankari cikin kundin tarihinta as the beginning of the beginning na kafuwar rayuwarta da maigidanta Yareema Sageer Yusuf Askira. ****** ABUJA Sun dawo Abuja ranar lahadi da yamma. Saade ta saki baki tana kallon yadda aka canza komai na gidan da ROYAL ONE. Duk abin da ke cikin gidan zubin na sarauta ne, sarauta ta zamani mai tafiya da boko. Ta karaso cikin main parlour tana latsa cushion din Royal Chairs din da suka yi wa dakin kawanya. Komai ya burge ta beyond her taste, beyond her expectation. Da Yareema ya ce za a yi refurbishing gidan ne shi ya sa suka tafi Yankari ba ta taba zaton gyaran zai kai kayatuwar haka ba. Once again, she simply fall in love with her humble abode (ta fada a matsananciyar soyayyar gidanta). Tunanin me ya kamata ta fara gyarawa ta tsaya yi. First of all zata gyara zaman kujerun. Su kalli juna madadin yadda aka ajiye su. Ta daga kai tana kallon hoton kyakkyawa Fulani Bilkisu cikin alkyabba da aka kafa mata a bangon gabas maso kudu na falon, ta saki murmushi ita kadai murmushin farin ciki. Ta matsa a hankali zuwa ga hoton, ta kai hannu ta shafi fuskar Fulani a hankali tana murmushi, lebbanta suka furta, Ina kewarki Fulani ba dan kadan ba. Ba ta san Yareema ya shigo jaye da trollies dinsu ba, yana tsaye daga bayan ta, ya ce, Me ki ka ce? Ta juya ta yi masa wani kallo na kasa-kasan ido, sannan ta zumburo dan bakinta gaba ta ce, Na ce ne Im missing her Prince, don Allah yaushe za mu je Askira? Dariya ya yi tare da mika mata kwalin wayar da ya sayo a hanya yana fadin, Ke da Askira sai na ga kina daga kafa da kyar, kina tafiya da kyar, sannan kina tashi da kyar. Ya karaso ya kama hannayenta ya sanya mata kwalin wayar, ya ce, Call your Mum, anytime. Har da dan tsallenta don farin ciki, ta makale a gefen kafadun Dr. Sageer ta na fadin, Na gode Prince. Dakin barcin Sultana na da nan ya kai mata kayan. Ya ja hannunta suka shiga dakin. Saade sai da ta rike numfashinta sakamakon ganin irin dankara-dankaran Royal furnitures da Maimartaba ya zuba mata. Wanda sai yayan sa su Ya Maira kadai zai iya yi wa. Hawayen farin ciki suka zubo mata, ba ta san sanda ta juya ta rungume Yareema Sageer ba. Ka taya ni godiya ga Alanguburo, Allah ya kara yawan rai, ya kara nisan kwana mai albarka. Ya gama yi min duk wani gata a rayuwa. Yareema ya rike ta sosai a cikin hannayensa, sannan ya ba ta kyakkyawar sumba saman idanunta. Yace. Nima ya gama min kowanne gata a rayuwa, tunda ya bani ke a lokaci mafi dacewa. When my heart was bewildered. Na kasa tunkarar ki in ce ina son ki, haka na kasa tunkarar kowa don ina ganin Im not good enough to have you. Bansan ni da ke wa Askirama ya fi so ba. Dariya ta yi ta zame daga cikin rikon sa, cikin jin dadin kalaman sa, aah Prince. Blood is thicker than water, ni ce ma yakamata in ce Im not good enough to haveyou, ni da ba yar kowa ba, ba yar sarau!. Yarima yayi saurin toshe mata baki da nasa in such a waythat hakan ya sa ta hadiye abinda ta yi niyyar fada cikin cikin ta, ya kuma kalubalance ta da cewa; watarana ruwan yana fin jinin kauri Saadatu. A daren ranar suna cin abinci yake cewa, Saadatu in na tafi na barki ke kadai a gidannan sai maaikata, babu matsala? Zan sake yin tafiya ta tsayin kwanaki uku. Da sauri Saade ta sake cokalin hannun ta, damuwa ta bayyana karara a kan kyakkyawar fuskarta. A dan zaman da suka yi tare a Yankari game reserve ta saba da Yareema Sageer fiye da tsammani, ya shiga zuciyar ta fiye da kintace. Tace tana son shi ma bata baki ne and is not enough to express the feelings Zuwa ina kuma Prince? Muryarta ta nuna tsantsar damuwar data fada.Yareema Sageer ya kamo hannunta ya dunkule cikin nasa, suka zauna a tare a gefen katafaren gadon Saaden, ya sassauta murya cikin lallashi, Its a promise ba zan wuce kwana ukun ba, zan kai Aisha-Sultana ganin gida ne. Wani abu ya zo ya tokare a kirjin Saade, wanda a nata sanin yafi komai zafi a zuciyar diya mace, a hankali ta janye jiki daga gare shi,sannan cikin karayar murya ta ce, A dawo lafiya!. Yareema ya sanya fuskarta cikin tafukansa, yana kallon fararen kwayar idanunta, ga mamakinsa idanunta sun cika taf! Da kwallah, kada dai Saadatu ta fara kishinsa? Babban burinsa kenan ta so shi irin yadda shi yake sonta. “Look at me Saadatu, na yi tafiya da ke mun yi kwanaki bakwai, ita ma tana da hakki a kaina, so ki yi hakuri in je in rakata, na yi miki alkawarin ba zan wuce. A hargitseSaadatu ta mike. Ka ji na ce wani abu ne Prince? Ko na ce Aunty Sultana ba ta da hakki a kanka? Ko me ye damuwata a ciki don ka dauki matarka kun tafi kun bar ni jiran gida? Ta juya masa baya a kokarin ta na boye hawayen ta. Yareema Sageer yana daga zaune yana kallonta ban da murmushi ba abin da yake yi. She never talked to him in this manner (cikin tsiwa). Saade ba ta ankara ba ta ji Dr. Sageer ya sure ta yana juyi da ita a tsakiyar dakin, kafin ya dire ta a tsakiyar gadon su ya koma samanta, ya dora mata dukkan nauyinsa gabadaya. Say it againba ki da damuwa don na dauki matata mun tafi Korea, to su wadannan hawayen kuma na mene ne, ya ya sunansu? Zan so kwarai in san maanar su. Saade ta runtse idonta hawayen na ci gaba da bulbula. Kamshin INVICTUS da ya riga ya kama Yareema ya soma hargitsa ta. Yana tada tsigogin jikin ta. A hankali Yareema ya soma kissing dinta from head to toe, lungu-lungu, sako-sako, kusfa-kusfa, kafin dan lokaci Saadatu ta fice a hayyacinta. Abin da ya biyo baya mai nauyi da girma ne da ya shallake tunaninsu. It was kind of gentle romance da ya gudana da hobbasar Yareema shi kadai, yayin da Saade ta sakar masa komai, gangar jiki, zuciya da ruhi, sai yadda ya ga damar sarrafa ta. Daren ya zamo cikin dararen tarihi a rayuwar amarcin ta, dare ne da daga Sageer har Saadatu, bazasu taba mantawa ba. Washegari suka yi shirin shiga makaranta. Saade ta yi tsaf cikin doguwar rigar atamfar chiganvy kalar pusher pink, ta yi lullubi da mayafi kalar kayanta wanda ya ciza sosai. Kallo daya Dr. Sageer ya yi mata yana shigowa dakin nata yana daura agogon hannunsa na danyar zurfa samfurin (Gucci) na maza, ya girgiza kai ya ce, Ai da sake. Ba ke ba fita da irin wadannan mayafan Saadatu, ko dai ki sa hijab ko ki koma gado ki nade ki kwanta. Saadatu ba ta kula shi ba, don ba wai ta huce daga fushin tafiyar da ya ce zai yi da matarsa ba ne, duk da duniyar soyayyar da ya dauke ta ya luluka ta daren jiya, yayi shawagi da ita a sararin samaniyar soyayya sky-blue mai haskaka zuciya da ruhi,still kishin hakan na makale a kasan zuciyar ta. Ya ce, reporting kawai zai je ya yi a ofis ya je gidanta ya dauke ta su wuce airport. Hijabin sallarta ta dauka ta saka akan atamfar jikin ta sannan ta biyo bayansa suka fito. Suna tafe a shimfidadden titin da zai shigar da kai cikin jamiar NTNU, a hankali Yareema ke jan motar tamkar ba ya so. Kwanakin nan da ya yi da Saade cikin rayuwarsa su ne kwanaki mafiya daraja da farin ciki da zai iya tunawa. Kwanaki ne da ba zai taba mantawa da su ba. Sannan kwanaki ne da suka bude sabon shafin tsaftatacciyar rayuwa da bai taba samun kansa a ciki ba. Sannan wadannan kwana ukun da zai yi ba tare da ita ba suna nufin komai. In ya ce komai yana nufin komai. Amma su kadai ne za su ba shi madauwamin kwanciyar hankali tare da Saade, ba zai iya hada rayuwarsa da ta kowace mace a yanzu bayan ita ba.(ASKIRAMA ya yi gaskiya). Aurensa da Sultana aure ne da bai san a rukunin da zai sanya shi ba. A yanzu ya gane kwanciyar hankalinsa da na Maimartaba shi ne kawai rabuwa da Sultana duk da Askirama bai furta hakan ba sabida principles din gidan sarautar Askira ya san abinda yafi so kenan. Don ya tabbata ba za ta taba yarda ta bar alcoholism ba. Ta fannin sa abubuwa sun dade da canzawa, ko yace suna kan canzawa, tun kafin shigowar Saade cikin rayuwar sa ya dade da nisantar zunuban sa. Abinda ba shi da tabbas a kai shine abinda gobe zata haifar. Amma ya dade yana tuba akan laifuffukan sa na baya. Tuban da Ubangiji yayi alkawarin karbar sa wato tuban da aka yi da niyyar bazaa sake komawa izuwa zunubin ba. Cikin matakan da ya dauka don kare kansa har da nesanta kansa da Dr. Ziyad. Ko Maimartaba bai gayawa ba, don ya san zai dakatar da shi ne daga hukuncin da ya yanke a kan Sultana, zai ce zai yarda da kowanne irin hukunci amma ban da rabuwar aure, sabida ba ya cikin aladar sarautar Askira. Shi kuma ya yi laakari da fadar Ubangiji (S.W.T) ne da ya ce, Na hore ku da auren abin da ya yi muku dadi daga daya-daya, biyu-biyu, uku-uku ko hurhudu. Amma in kun san ba za ku yi adalci ba, to ku zauna da guda daya. Shi kam ya tabbata bai iya yin kowanne adalci tsakanin Saadatu da Aisha-Sultana. Musuluncin da ta karba a yanzu ya gane don ya ba ta lasisin aurensa ne kawai, daga sanda ta same shi kuwa ta nade shi cikin tabarma ta jingine a gefe. Don haka ya amince wa ransa rabuwarsu ita ce mafi alkhairi. Har gaban department din su Saade ya shiga da motar, inda babu mai wucewa sai staff only. Yana tsayawa ta bude kofar za ta fice, cike da dokin shiga aji, ta yi kewar karatunta sosai, ta san abubuwa da yawa sun wuce ta, amma ta tabbata Said zai dora mata komai. Yarima ya rike hannunta tana shirin fita. Haah! Saadatu har murna ki ke zan tafi in ba ki fili ko? Ya fada da marainiyar murya, har cikin ransa yake jin rabuwar nan da zai yi da Saade har tsayin kwanaki uku. Kwarai bai yi karya ba tana murna da tafiyar sa ta wani fannin ko don kwarzaba irin tasa, ta san za ta samu hutu da nutsuwa na dan lokaci ta yi karatu sosai na abin da aka wuce ta. Amma in ta tuna da matarsa zai tafi sai ta ji gara ya zauna ya yi tumurmusar nata da ya tafi wajen mai jan kunnen tasa. Amma ko kashe ta zaa yi ba za ta iya gaya wa Yareema tunaninta ba. Ta san kuma da gaske ne kamar yadda ya ce matarsa ma na da hakki a kansa, ba don ita kadai aka halicce shi ba. Ba ta ankara ba ta ji hawaye sun zubo mata. A hankali ta ce, Ni ba murna nake ba, hasali ma I will really miss you. Cikin jin dadin kalaman ta Yareema ya mika mata hanky dinsa ya ce, To share hawayen, ki bar wayarki a kunne, zuwa asubahi in mun sauka zan kira ki. Me zan sayo miki? Kasar Korea ta Kudu za mu je ni da Sultana. Ta kasa sabawa da ambaton Sultana da yake yi, don ji ta ke kamar ya fi kowa iya fadar sunan. Wasu hawaye suka sake zubowa, wadanda ba ta san dalilinsu ba. Yareema ya sa hannunsa yana shafe mata hawayen da tafukansa sai a idanun Said da ke fitowa daga lecture hall. Dr. sageer ya gan shi ta karshen idon sa amma ita Saade bata lura da shi ba, da gayya ya kara rungumo Saade yana mata magana cikin kunnen ta. Zan iya tafiya? Ta tambaye shi bayan ya gama dauke mata hawayen fuskarta da tafukan hannun sa. ...Only if you give me a farewell kiss (za ki tafi ne only in kin ba ni sumbar bankwana). Wani irin murmushi ne ya subuce a siraran lebbanta, wanda Said bai taba gani a tare da ita ba. Ji ya yi kafafunsa na neman kasa daukarsa ya juya ya koma cikin aji da mugun sauri. Har yana cin tuntube a bakin kofa saura kadan ya kifa. Prince ka bar ni in tafi aji, ka ga malam ya shiga. Kuma nan kan hanya ne, mutane suna iya hango mu ko daga lecture hallne. Kin yi alkawarin in na dawo komai zai canza Saadatu? Za ki daina fushi da ni, za ki dinga gaya min duka bacin ranki? Zamu shimfida sabuwar rayuwa ta amana, soyayya da fahimtar juna? Da sauri Saade ta gyada kai. Yareema ya ratsa yatsunshi biyu cikin nata ya matse su sosai sannan ya sake su a hankali. Ta kasa dago ido ta dube shi, domin wata irin soyayyar Sageer da ta ji tana shigarta tana mamayeta a hankali. Ta bude kofar motar ta fice rungume da folder dinta. Ba ta waiwayo ba sai da ta kai kofar lecture hall dinsu. Har yanzu yana nan a inda ta bar shi, kanshi kwance bisa sitiyari, bai dauke ido a kanta ba. Ta sakar masa lallausar murmushi, sannan ta juya ta shige aji. Yau sai ta ji ta kasa zuwa ta zauna kusa da Said yadda suka saba, wanda ya tattara hankalinsa duka ya dora a kanta tana shigowa. Ta dauke kai ta nemi gefen wata kabila mace ta zauna. Mai miji kamar Yareema Sageer, ji ta yi ta daina son ganin kowanne namiji a duniya sai shi. Tafiyar da ya yi kuma tamkar ya tafi tare da ruhin ta ne. Gabadaya ta rasa kuzarinta da walwalarta. Malamin Baireshe ne, yana ta bayani a kan applied chemistry, Saadatu ba ta jin muryar kowa sai ta mijinta Yareema Sageer cikin kunnuwanta yana rada mata tausasan kalamansa. Har ya yi awanni biyunsa ya gama ko alifun ba ta rubuta ba. Said daga inda yake zaune ban da satar kallonta ba abin da yake yi, yana yi yana rubutu, ta yi wani mugun kyau, ta yi fresh da ita. Yana ta mamakin abin da idanunsa suka gane masa yana faruwa cikin motar Dr. Sageer Askira da kanwar tasa Saadatu. Ba ta taba yin kama da mutanen banza ba, yarinya ce mai tarbiyyar babban gida, amma anya abin da ya gani cikin idanunsu ita da Yayanta Dr. Askira bai yi kama da mashahuriyar soyayya ba? Soyayyar ma irin wadda ba ta taba faruwa sai da physical relationship a tsakani. Bayan fitar Malamin, Saade dole ta taso ta cimma Said a mazauninsa don ya ba ta notes din da ya wuce ta. Ta yi masa sallama, ta ce, Said kwana biyu? Ya daga ido ya dube ta a hankali, sai kuma ya dauke kai. Mamaki ya kama Saade. Said ba ka gane ni ba ne? Kawai sai ya tattara takardunsa ya bar gurin. Saade mamaki ya kashe ta a tsaye, ta bi bayansa yana fita daga theater din. Said! Said!! Ta daga murya tana kwala masa kira. Juyowa ya yi ya jefe ta da wani mugun kallo, sannan ya dakata har ta cimmasa. Suka yi kallon-kallo na yan sakanni kafin Saade ta tuna cewa ita yanzu matar aure ce, ta yi saurin kawar da idonta. What happened Said? Ina magana kamar ba ka san ni ba? Said ya rasa me zai ce mata, idanunsa sun kada sun yi jazir don kishi. Saade ta soma shaka, don ta tsani wulakanci. Ta kankance ido ta ce, In dai don notes dinka ne, ka rike abunka kada Allah ya sa ka ba ni, kada ka manta kanwar Dr. Sageer ce ni, zai karba min a hannun kowanne malami. Said ya yi murmushi mai ciwo, ya ce, Kwarai, na shaida hakan tunda kuwa kina ba shi reward a cikin mota, abin da ya fi notes ma zai karba miki. Kan Saade ya kulle, ta ce, Me ka ke nufi? Ya yi mata wani irin kallo zuciyarsa na zabalbala, ya ce. Kin ba ni mamaki Saadatu, ina miki kallon yarinyar kirki, mai hankali da tarbiyya, yar manyan mutane, yar babban gida, amma ashe kallon kitse nake wa rogo, duk abin da ya faru cikin motar da ta kawo ki tsakanin ki da wanda ki ka kira Yayanki na gani. Abin da ban sani ba shi ne, da gaske biological brother dinki ne ku ke aikata wannan assha? Saade ta kai yatsu ta toshe kunnuwanta ta juya da sauri ta bar wurin. Ba ta san me za ta ce masa ba, tunda ashe duk amincin da ke tsakaninsu ba zai iya shaidarta ba, zai iya yi mata mummunan zargi irin wannan. Ranta ya yi mugun baci, har ta ji ba ta bukatar fayyace masa gaskiyar ko wane ne Dr. Sageer a gare ta a yanzu. Ya je ya yi ta yi mata kallon yar shan minti a mota, damuwarsa ce. Daga yau ba za ta kuma shiga shirginsa ba. Ba su gama lectures ba sai yamma lis. Direbanta ya zo ya kai ta gida bisa umarnin Yareema. Ta fito daga motar goye da jakarta irinta yan sakandire (school bag), ta gaya masa gobe karfe takwas zai zo ya shiga da ita. Uche ta taras ya yo cefane himili guda yana shiga da su kitchen. Ta yi masa sannu, sannan ta ce daga yau ta hutashe shi girkin gidan, aikinsa ya koma share-share da goge-goge kafin ta dawo makaranta ya yi duk abin da zai yi ya gama ya wuce baskwata. Sai kuma cefane da aike da zai dinga yo wa lokaci zuwa lokaci. A ransa Uche ya ce, Tunda dai ba za ki sa a kore ni ba ai shi ke nan. A fili kuma ya ce, Yes Ma!. Don haka yana gama jera mata komai a firji da store ya bi ta kofar baya ya koma baskwata ya ci gaba da aikin fulawoyin gidan. Wanka ta yi, sannan tayi sallar magriba ta yi lazimi zuwa isha. Ta kawo sallar isha da shafaI da wutiri, sannan ta roki Allah ya sauki Yareema lafiya, Ya kuma dawo mata da shi lafiya. Ta koma kitchen ta hau aiki, ta gyara komai zuwa yadda ta ke so, ta ke buri tuntuni kitchen din ya kasance (da a ce nata ne). To shi Allah buwayi ne, gagara misali. Abin da ba ka taba zato ba ko tsammani ya riga ya rubuta shi cikin littafin kaddarorinka. Noodles kawai ta dafa guda daya ta shige daki, ta ci ta koshi sannan ta yi shirin kwanciya. Da asubah tana idar da sallah ta janyo wayarta da ta saka a caji ta kunna. Wayar ta cika taf da caji. Tana kunnawa kamar jira yake, sai ga kira daga international number. Saade na amsawa, tana jin muryar Yareema sai ta saka masa kuka. Prince yaushe za ka dawo? Jiya da kyar na yi barci, tsoro nake ji. Hankalinsa gabadaya ya tattara ya mika mata, ya ce, Ki yi hakuri Saadatu, mun sauka lafiya on transit a Amsterdam, yanzu za mu jau jirgin South Korea, insha Allahu jibi i-yanzu muna tare. Mun fara shirin tarbar mai sunan Maimartaba, da ni ki ke so ya yi kama ko da ke? Ba ta san sanda ta yi murmushi ba, ga hawaye shabe-shabe a idon ta. Ina gaida Aunty Sultana, ka gaya mata ni ban ce ina son mijinta ba aka aura min, ta daina fushi da ni. Yareema ya yi ajiyar zuciya, ya ce, In ki ka ce haka ba ki yi min adalci ba Saadatu, dukkanmu mun dade muna son juna, ba mu gane hakan ba ne har sai da Maimartaba ya ankarar da mu. In kuma da gaske ba ki sona din ne Saadatu, to gata ki gaya mata da bakinki. Ta girgiza kai da sauri kamar yana gabanta, ta ce, Yaya Yareema!!! (In exclamation). Ya ce, Yes, ki gaya mata da bakinki, sannan ne zan yarda cewa ba kya son nawa. Murmushi ya subuce mata, ta kawar da zancen da cewa. Karatu ya wuce ni da yawa, an yi min fintinkau, in ka dawo za ka koya min? Ya ce, Karatun namu ai kala-kala ne, wanne daga ciki? Ba ta gane hausarsa ba don haka ta ce, Courses din Applied Chemistry, inorganic, organic and petrochemistry. Tunda kai ka jawo aka wuce ni. Ta fada cikin shagwabar da ba ta san ta yi ba. Dr. Sageer ya yi ajiyar zuciya. Anya Saadatu za ki bar ni in yi kwanaki biyun nan? Gabadaya kin rikita min lissafi, na kasa zama lafiya cikin nutsuwa tun barowata makarantarku. Ke kawai nake son gani, ke kawai nake son ji a jikina. Ta kai tafin hannunta ta rufe ido kamar Yareema na ganinta, sannan ta ce, Kada in shiga lokacin Aunty Sultana. Prince sai ka dawo. Ta yi maza ta kashe wayar ta koma ta jingina bayanta jikin allon gado, ta lumshe idanunta. Ba abin da ta ke son gani a daidai wannan lokacin sai Yareema Sageer. Wayewar gari ke da wuya ta soma shirin shiga makaranta. Ba ta dade da zama a mazauninta ba, Said ma ya shigo suka hada ido, ta dauke kai. Yau fuskarsa a sake ba kamar jiya ba. Ya zo har gaban kujerarta ya ajiye mata tulin wasu takardu. Gabadaya notes din da ya shige ta ne ya je ya yo mata photocopying dinsu. Ba tare da ya ce komai ba ya koma mazauninsa. A kwanakin biyu gaba daya ba sa magana da juna, ya kasa cire abin da idanunsa suka gane masa daga kwakwalwarsa, ita kuma ta kasa yi masa bayanin da ya kamata ta yi masa. Kunya ta ke ji a ce ita yanzu matar aure ce. Kwarai ta ji dadin photocopies din da ya yi mata, amma wata zuciyar na cewa ta dauka ta bishi har mazaunin sa ta watsa masa tsiyar sa, zuciya mafi adalci na cewa ta yafe masa muggan maganganun sa ya fada ne a bisa rashin sani. A kwanaki biyun in ta koma gida ba ta komai cikin kwanaki biyun sai bitar karatun da ya wuce ta. Abin da ba ta gane ba ta kira Dr. Sageer ta gaya masa ta waya ya yi mata bayani yadda za ta gane. Yana yi yana kashe ta da kalaman soyayyarsa masu ratsa zuciya da ruhinta. Yau kwanansa uku da tafiya kuma ya sauka a Abuja, amma bai kira ta ba. Ta wuce makaranta har yamma tana fama da assignments din da ta kasa solving gabadaya. Ta daga agogon hannunta ta ga karfe shidda, ko me ya hana direbanta zuwa har yanzu? Ta dauki wayarta don ta kira shi sai ta samu cajin wayar ya mutu gabadaya, don jiya kusan kwana suka yi a kan waya ita da Yareema, kuma da asubah ta manta ba ta sanya cajin ba. Gabadaya Dr. Sageer ya gama kwance kan Saade da soyayyah ba abin da ta ke jira sai dawowarsa a kashe wutar da ake rurawa a waya. Da ta tuna yau zai dawo, sai ta ga ba za ta iya zaman jiran direbanta ba, sabida tana son yi masa girki na musamman, gara ta gangara da kafarta zuwa cikin quarters dai ba nisa, ban da Yarima da ba ya so tana tahowa ita kadai da yamma da da kanta za ta dinga komawa gida ko don ta motsa jikinta. Ba ta jima tana tafiya a gefen hanya ba, motar Said ta yi parking a gabanta. Shigo in karasa da ke. Aah na gode, ka je kawai. Ki yi hakuri ki shiga, ba zan barki ki bi jejin nan ke kadai ba daf da magriba. Sai ta ji tausayinsa ya kamata, ya kasa cireta a ran sa, ta fi kowa sanin yadda yake sonta. Ko ya zai ji in ya ji ta yi aure? Sai ta ga gara ta shiga motar yau ta gaya masa gaskiya ko don ya daina kishi a kan abin da ba nasa ba, kuma ba zai taba zama nasan ba. Sannan babu yaudara a tsakaninsu har abada sai mutunta juna. Ba za ta taba mantawa da dimbin kirkinsa gare ta ba. Don haka ta bude gaban motar ta shige, ya soma tafiya a hankali, Saade ta ce, Da dai ka yi sauri maigidana yana hanyar dawowa. Ka yi hakuri ban samu damar gaya maka ba kana ta fushi, an yi min AURE! Said ya taka wani wawan birki sai da suka jirkito dukkansu, Saade ta yi maza ta rike hannun kofar motar, ta ce, Yaa Salam! Said ya dube ta a sanyaye, ya rasa abun cewa. Sai ya ja motar suka karasa kofar gidanta. Har cikin get ya shiga da ita, tana kokarin fitowa motar su Yarima na shigowa shi da Dr. Ziyad ne da ya yi wa waya ya je ya dauko shi a filin jirgi. Bakuwar motar samfurin henessyta dauki hankalinsa, kuma ba jimawa ya gane yaron, ya taba sauke Saade, kuma ya yi warning dinta tun a wancan lokacin amma shi ne shi ne bakin ciki, kishi da bacin rai sun hana Sageer tunanin abin da ya dace. Dr. Ziyad bai gama tsayar da motar ba ya bude ya fito. Cikin takunsa na Yariman Askira ya taka ya isa gaban Said, sannan ya nuna shi da dan yatsa. Wannan ya zama lokaci na karshe da za ka kara daukar min mata a mota, ko da da niyyar taimako ne. bana so, nagode. Ko kallonta ka sake yi ba taimako ba, kotu ce za ta raba ni da kai, na gaya maka, na kara gaya maka wannan. Da sauri Dr. Ziyad ya karaso ya kama shi yana fadin, Haba Dr. he is your student, ba girmanka ba ne. Saade tuni ta shige gida jikinta na rawa. Dr. Ziyad ya bi ta da kallo yana hadiyar miyau. Said tuni ya tsugunna yana bada hakuri, ya gaya musu direbanta ne bai zo ba, ya ganta tana dawowa da kafa, kuma sawu ya dauke shi ya sa ya ce ta shigo ya karaso da ita. Dr. Ziyad ya ce, Is o.k, kana iya tafiya, mun gode. Bayan wucewar Said ya kwace hannunsa daga na Ziyad ya ce, Da ka bar ni na dan sassaba masa kamanni, gobe ko da kudi aka hada shi bai kara daukar matar mutane a akwalar motarsa. Cikin mamaki Dr. Ziyad ya ce, Daga zuwa na Istanbul da dawowata kana nufin ka kara aure? Is she this girl da ta wuce ciki yanzun nan? Dr. Sageer ya harare shi sosai da ya tuna waye Ziyad a kan mata, ya ce. Babana ya aura min yarinyar da na ke riko ce tun da jimawa. And now ina Sultana? Mun rabu. Na mayar da ita kasarsu. “This is serious, ashe za ka iya rabuwa da Rose? What a lucky girl, amma ta ciri tuta, ya ya sunanta? Sageer ya zabga masa harara ya ce, Don Allah malam kama gabanka, ina ruwanka da sunan mata ta? Dariya Ziyad ya yi, ya ce, Ina nan ina jiran ka, in ka gama kwasar amarci za ka zo neman new catch. Da sauri Dr. Sageer ya ce, Waiyazu billah, sai dai wani Sageer din ba ni ba, kai ma ina maka fatan shiriya, kuma ina mai ba ka shawarar ka dauko iyalinka daga Istanbul ka dawo da su kusa da kai ya fiye maka wannan kazamtacciyar rayuwar. Ziyad sai dariya yake yana mamaki, in wani ya ce masa Sageer zai bar mata saboda mace daya ba zai taba yarda ba, amma a sanin da ya yi masa shi kaifi daya ne, sannan ba ya taba fadin abin da ba haka yake a zuciyarsa ba. Ko sallama Dr. Sageer bai bari sun yi ba ya shige falon gidansa ya kullo kofa ta ciki. Ya bar Dr. Ziyad a tsaye ya kasa tafiya. Ba abin da idanunsa ke hango masa sai kyakkyawar surar BAGGARA-SAADATU diyar Fulani Bilkisu, a lokacin data juya baya tana shigewa cikin gida. ****** A yadda ta hango bacin ran da ke kunshe fuskar Yareema ta san ba za su kwashe ta dadi ba. Tana shiga dakinta ta aje jakarta ta sunce ta daura tawul ta shiga wanka, tana tsakiyar wanka a shower sai ganin Yareema ta yi ya bude kofar toilet din ya shigo. Idanunsa sun kada, amma ganinta cikin wannan yanayin tuni ya birkita shi. Ko a Yankari bai taba samun damar ganinta yadda ya ganta a zahirin yau ba cikin hasken farin lantarki. Da kayan jikinsa da komai ya tafi zuwa gare ta. Da sauri Saade ta ja da baya ta ce cikin karkarwar murya, na tuba Prince Duka jikinsu rawa ya hau yi cikin wani yanayi, ita nata rawar jikin na tsoron abin da zai yi mata don huce bacin ransa ne akan Said, yayin da shi kuma nashi na tasowar wata irin soyayya ne da bai taba ji ba a rayuwar sa a kan kowacce diya mace. Ka yi hakuri don Allah ba zan sake ba. Saade ta fadi cikin karkarwar murya, amma daga irin rikon da Yareema Sageer ya yi mata, ruwan yana sauka a kansu su biyu, tun daga sumar kansu har zuwa yatsun kafarsu, da yadda ya soma sumbatarta fiercely ya tabbatar mata ta hanyar da zai huce fushin nasa kenan. All of a suddenga Saade,komai ya faru cikin shower.. gently, romantically yet abruptly(in an abrupt manner). Abin nufi, bata zaci abinda ya kawo shi shower din kenan ba, ta zaci ya zone don ya gaggaura mata mari a yadda ta gaidanun sa lokacin da ya gan ta a motar Saidu. Sai ta ga alamarin ya juye zuwa zazzafar soyayya mara misaltuwa. Dukkansu sai da suka yiwani irin kuka(for emotion and satisfaction), wanda soyayyar juna, kewar juna da tsananin kauna suka kawo shi. Wata sabuwar rayuwa ce mai gardi da Saadatu da bata taba tsintar kanta a ciki ba. Wani sabon yanayi ne a gangar jiki da ruhin Yareema Sageer, ya ji nan duniya bai iya kara sake hada jiki da kowacce diya mace bayan Saadatu diyar Mallam Hashimu da Fulani Bilkisu. Kalaman mahaifinsa suka sake dawo masa a ranar da ya mallaka masa SAADE. Za ta dauke dukkan kwadayinka daga kan sauran mata, in dai Bilkisu ce ta haife ta. Allah ya saka da alkhairi Alanguburo. Allah ya kara yawan rai, Allah ya ba ni ikon rike amanar da ka damka min da gaskiya da amana, har zuwa ranar da muka daina numfashi. Kalaman da Yareema ke yi a fili kenan, yana kankame da matar sa Saade, ruwa na sauka a jikkunansu daga saman shower. Ba ta san adduar me yake yi ba har da sunan ASKIRAMA a ciki, daga baya ta fahimci gode masa yake da ya mallaka masa ita ta zama cikon farin cikin sa. Ko ita a yau tana gode masa da ya mallaka mata gwarzon dansa mafi soyuwa a gare shi, wato Dr. SAGEER YUSUF ASKIRA,Basaraken Askira daya cikin dubu, sadauki kuma jarumi a fanninnunawa matar sa kauna da soyayya. A baya gani ta ke Mai Askira ya katse mata rayuwa, yayi mata aure ba a lokacin da ta shirya ba. Yanzu kuwa ta gane Askirama ya cika rayuwar ta ne, ya ingantata.Ya suturtata cikin alfarmar aure. Aure suttura ne, cikar mutunci ne, garkuwa ne kuma rufin asiri ga diya mace, sannan gata ne da ba kowacce mace Allah yake yi wa Rahmar sa ba. Don haka godiyar ta ga Allah madaukakin sarki da kuma godiyar ta ga Mai Askirainfinite ce. Kaunar ta mijinta ta gama ratsa koina na sassan jiki da zuciyarta. Ta fara tantamar ya ya rayuwa za ta ci gaba da kasancewa ranar da babu wannanmuhimmiyar soyayyar ta Yareema Sageer a cikinta??? ***** DR. ZIYAD SAHEEB Ya kasa zaune ya kasa tsaye a dakin barcinsa, ya rasa inda zai sa kansa. Shaidaniyar zuciyarsa na ci gaba da kawata masa surar sullubebiyar matar abokinsa, yarinya danya sharaf! Irin Africans din da kalar fatar jikin su ke da wuyar samu a cikin matan Nigeria. Ka kasa gane half-caste ne ko kuwa shuwa-arab ne? Dr. Ziyad ya kudire a ransa, ko ta tsiya ko ta arziki sai ya samu rabonsa a tare da matar Dr. Sageer, da ma ai sun saba sharing yammata, ya san Sageer bai taba neman matar aure ba, amma shi kam zai gwada saarsa a kan tasa, zina ai duk sunanta zina, kuma su ma wadanda yake neman a baya ai wani za su aura watarana. Don haka don an yi masa abin da shi ma yake yi ba laifi ba ne.Dole ya juyawa harkar su baya yana da wannan precious gem din a cikin dakin sa. Ya san ba zai sha wahalar samun kan yarinyar ba, yadda yake farin balaraben Turkish. Ya fi Sageer kyau nesa ba kusa ba, ya kuma san yadda matan Nigeria ke son fararen fata. Karfe takwas na dare ya kira Sageer a waya. Dr. Sageer na makale da Saade a lokacin suna karatun Organic Chemistry ana yi ana soyayya tamkar sun cinye juna wayar Dr. Ziyad ta shigo masa. Kamar ba zai dauka ba, sai kuma ya dauka. Akwai abinci ne a gidanka in shigo in ci? Cook dina ya yi tafiya. Sageer ya ce, Za mu bai wa Uche ya kawo maka yanzu, ka daina zuwar min gida, ba gidan Sultana ba ne yanzu, gidan Saadatu ne. Saadatu! Dr. Ziyad ya fada a hankali, wane irin suna ne mai tafiyar da ruhi haka? Duk wayonka sai na dandana abin da ka ke dandanawa. O.K no problem, a kawo. Da haka suka ajiye wayar. Yareema ya yi tsaki, sannan ya dubi Saade da ke kalmashe cikin jikinsa. Da ya sani bai daga wayar bama balle ya bata masa mood din sa. Kin yi ragowar abinci ne? Ta ce, Eh. Ba ta son abin da zai tada ita daga jikin Yarima sam a daidai wannan lokacin, tana cikin amarcinta, suna yi suna karatun su. Karatun ma ya fi shiga a haka (inji Saade). Ta ji wayarsu da abokinsa, kuma ta tabbatar dole sai ta tashin. Daure ki hada masa abinci a basket ki ajiye a kitchen, zan kira Uche ya kai wa Dr. Ziyad. Tana cuno baki ta mike tana fadin, Ba shi da mata shi? Ya yi dariya, ya ce, Yana da ita. Me ya sa ba ta ba shi abincin ba? Ba ta nan ne, tana Istanbul har yayan sa, ki taimaka. Ta sake turo baki gaba, sannan ta mike zuwa kitchen din, wandon three quarter ne a jikin ta da yar farar shimi (armless) ta je ta yi yadda Yareema ya bata umarni ta dawo. Shi kuma ya kira Uche a waya ya gaya masa abin da zai yi. Da safe Dr. Ziyad ya sake kiransa, Karfe nawa za ka shiga ofis yau kuma karfe nawa za ka dawo? Wannan wata tambaya ce da Ziyad bai taba yi masa ba. Nan da nan ya sha jinin jikinsa.Hausawa suka ce wai Shege shi ya san makwantar shege. “Why are you asking? Zan zo mu yi lunch ne tare. Yareema ya daure fuska sosai, ya ce, Look Dr. Ziyad, gidana gidan aure ne, ko da can ni nake zuwa gidanka ba kai ka ke zuwa gidana ba. Sabida ba matar aure a gidan ka. Ni ba zan hana a ba ka abincin gidana ba, amma na gaya maka gara ka dawo da Guneet Nigeria ya fiye maka wannan rayuwar. Maganar gaskiya matar da nake so nake kishi nake aure yanzu, don haka ba zan kai abokai gidana ba. In waccan rayuwar ce ni na bari, na gaya maka na kara gaya maka na bari. Don haka muamalarmu yanzu za ta koma ne strictly official, (ta tsaya a ta ofis kadai). Wani maketacin murmushi Dr. Ziyad ya yi, ko dama shi ya sake dulmiyar da Yareema a harkar neman mata bayan aurensa da Aisha-Sultana kuma ba karamin shaidani ba ne. Ya riga ya rantse sai ya kwanta da matar abokinsa ko da hakan zai kawo karshen abotarsu. Ya gani kuma ya yaba. Ko ana ha-maza-ha-mata kuma sai ya yagi rabon sa. Tun daga ranar yake studying shige da ficen Dr. Sageer da Saadatu zuwa cikin makaranta da lokutan dawowarsu ta tagar dakin barcin sa. Tsayin sati biyu yana hankalce da duk wani motsinsu, ya fahimci duk ranar alhamis yana dawo da Saade da wuri wajen karfe biyu na rana, shi kuma ya koma ofis ba ya sake dawowa sai shidda na yamma. Ranar wata alhamis wadda Saadatu ta kira fateful day, watanninsu ukku kenan da aure, a duka wadannan watannin ba su je Askira ba amma kusan kullum suna waya da kowa nasu. Yareema ya dawo da ita gida, ya ci abinci sannan ya dau keys dinsa ya fice yana ce da ita zai rufe gidan ta waje, ko an buga kada ta bude, shi in ya dawo zai bude da kansa. Uche zai kawo mata cefane ta kofar baya zai shigo, in ya gama shigar da su zai rufe ya koma baskwata. Bayan fitarsa Saade ta shiga wanka, wankan ma a gurguje ta yi shi don hankalinta na kan karatun paper din da za ta zana gobe, wadda ta kasance last paper ta kammala aji biyu (level 2). Ta fito wanka kenan daure da towel iya gwiwarta, ta shiga dakin barcinsu ta zauna a kan stool din mudubi ta janyo lotion dinta na Makari ta soma shafawa, kanta cikin shower cap. Tana yi tana bin wakar balarabiya Nancy Agram cikin wayarta da ke gefe, ta ji an murda kofar dakinta an shigo. Tana juyawa da sauri don a zatonta Yarima ne ya yi mantuwa ya dawo, sai ta ga wani balaraben mutum. Ya ma fi larabawa kyau. Ba ta taba ganinsa ba, yana sanye da jallabiyya, kawai sai ta sa a ranta aljani ne. Wata kara da Saade ta tsandara sai da Uche ya jiyo ta daga baskwata, ihu ta ke tana neman a kawo mata dauki da dukkan karfin muryarta. Dr. Ziyad ya karasa da sauri ya toshe mata baki, ya buga kanta da bango, sannan ya sa kafa ya tadiye ta ta fadi kasa. Duk da ta ji azaba ba yar kadan ba har cikin kwakwalwarta hakan bai sa ta kasa hobbasar ceton kanta ba. Bedside lamp da ke kusa da hannunta ta dauka ta kantara masa a ka. Fitilar ta fashe a kan Dr. Ziyad jini ya wanke masa fuska, shi kuwa Uche tuni ya kira Ogansa a waya tun karar farko da ya ji Saade ta kwallara. Rapist, at your home Oga!. Abinda kawai ya gaya wa Sageer ke nan. Ya na so ya shiga ya taimaki Saade yana tsoron ko Ziyad na dauke da makami. Shi kam Uche matsoraci ne na karshe. Duk da raunin da ta ji masa da fitila bai dame shi ba, ya dafe wajen da fitilar ta huda masa wanda tulin gashin kansa ya rufe shi. Sai jini da ke bulbulowa ta wajen, ya mike da mugun zafin nama ya dauke ta da mari haggu da dama. Saade ta nemi jinta da ganinta na wucin gadi ta rasa. Dr. Ziyad ya yi amfani da wannan damar ya fincike tawul din da ke jikinta Saade ta sake yunkurawa tana ihu, ya sake sanya kafa ya tadiye ta, Uche yana daga bayan tagar dakin yana ta jera wa Yarima kira, ga shi ba shi da lambar police ko security din makarantar cikin wayar sa, wata zuciyar ta ce ya dauki dutse ya shiga ya kwada wa Dr. Ziyad, wata zuciyar ta hana shi, in ya zo da tsautsayi ya mutu shi ma kashe shi za a yi, a kan matar da ba tasa ba ai ya san shima maigidan nasa yana danawa a gidan Ziyad din, abinda suke yi ne tare yau aka yi masa har cikin dakin auren sa.. Yana wannan sake-saken jikin sa yana bari sai ganin hancin motar Yarima ferrariya yi ya shigo gidan da wani irin mugun gudu, kasa tsayar da motar ya yi sai da ta daki daya dalleliyar motar da ke fake a gefe, sannan ta tsaya cikin kudurar Ubangiji, bayan ya take birkin tsayar da mota. Da gudu ya fito, jikinsa ba inda ba ya tsuma, hatta jijiyoyin kansa da makwallatonsa sun mimmike. Tsabar rudewa ya rasa ina ya jefa mukullin gidan, ga shi ya kulle ta ta waje. SaiUche yayi masa nuni da kofar kitchen ta baya. A lokacin Uche ya zargi ta kofar kitchen Dr. Ziyad ya shigo. A guje Yareema Sageer ya danna kai gidansa, don tun daga Kitchen za ka fara jiyo ihun da Saade ke ta kurmawatana ambaton sunan Sageer da neman taimakon Allah. A falo ya tsaya cikin gigita mara misaltuwa, yana son tantance daga inda ihun Saade ke fitowa. Daga karshe ya gane dakin barcin su ne. Tuni Ziyad ya kai ta kasa, yana ta kicin-kicin cire jallabiyyar jikinsa zai haike mata.. domin ya gama galabaitata da duka karfin kokawar ta ya kare, sai ambaton sunan Allah take hawaye masu zafi na kwaranya, ya yi nasarar cirewar kenan ya ji an ba shi (one blow one die) daga keyarsa. Da ma ga shi jiki ba jiki ba, siriri ne sai tsayi kamar falwaya, sai da ya tuntsira daga kutufo dayada Dr. Sageer ya yi masa, Yareema ya bi shi ya dinga buga kansa da bango yana naushin hancinsa da bakinsa. Saade ta yi amfani da wannan damar ta ja jiki da rarrafe ta shige toilet dinta ta rufe. Ta kifa kai jikin jacuzzi tana girza wani irin kuka jikinta yana ta rawa da kakkarwa, wanda sautin sa yake fitowa tun daga karkashin zuciyarta. Me wannan mutumin ko aljanin zata ce ya zo ya yi mata? Kisa ko me?? O.k tunda ta ganshi ya tube wando ya kuma tsiraitata to raping dinta ya zo yi. Rape, rape, rape dai da ta ke jin labari!!! Wani mugun tsoro ya shige ta, ta ji ba abin da ta ke so a halin yanzu ban da ta bude ido ta ganta a gaban uwarta. Ba ta san ya suka kare ba. Ta kasa fitowa daga toilet. Banda tsuma ba abinda jikin ta ke yi ta dunkule a wuri guda a gefen kwamin wanka. Sanyi yana kada ta. Ta dai ji karar shigowar motar security din Nigerian Turkish Nile University. Gabadaya kuma suka shiga motoci suka tafi har Yareema domin su yi report karkashin hukuma. Har Uche aka tafi, don shi ne zai bada shaidar komai. Uche ya fada wa kwamishinan yan sanda duk abin da ya sani, cewa yana shigar da cefane ya kai wasu ya koma don ya debo wasu, sai ya tuna wayar sa ya barota a baskwata tana caji ya je don ya dauko, da wannan damar Dr. Ziyad ya yi amfani ya shigo gidan ta kofar kitchen. Ihun Saade da ya jiyo da lekawa da ya yi ta taga ya gansu suna dauki ba dadi. Kiran Yarima da ya yi da daya makwabcinsu Dr. Wole da ya kira universitysecurity bayan shigowar Yarima. Lokacin da hukuma ta matsawa Dr. Ziyad kan ya amsa laifinsa kada ya wahalar da hukuma, budar bakin sa sai ya ce shi ma Yarima yana neman mata, komai suke yi ai tare suke yi, don haka bai kamata ya kawo zancen nan ga hukuma ba tunda abin da yake yi wa matan wasu ne shi ma aka yi wa tasa..kuma sharing matan suke yi. Yarima bai taba jin nadamar aikata zina a tsayin rayuwar sa irin ta yau ba. Lallai Ubangiji ya yi gaskiya, ita zina bashi ce, kuma bibiyar mai ita take yi, in dai ka yi ta a rayuwarka ko ba a yi da dan ka ba zaa yi da matarka ko kanwarka. Kuka riris Yareema Sageer ke yi akan bencin kwamishinan yan sanda, ya kuma yarda gaskiya Ziyad ya fada. Amma shi tunda yake bai taba neman matar kowa ba sai watsattsun bisa titi, to why matar sa? Amma da gaske ya taba raping yar wani duk da baiwa ce tun a shekarun tashen balagarsa. Amma ai an yi masa hukuncin addini, me ya sa tun bayan nan bai daina ba? Sai ma hakan ya bude shafin rayuwar kaico a gare shi? Sai ya ji koma me Ziyad ya yi masa kamun Allah ne. Ubangiji Subhana yayi gaskiya da yace (in kayi zina da yar wani to hakika zaa yi da yar ka ko kanwar ka ko matar ka.). Ubangiji Yana kyale mu mu yi ta saba masa, ranar da zai yi mana talala sai ya yi mana ita a kan abin da muka fi so fiye da komai a rayuwarmu. Yana son Saade, yana kishinta yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Dr. Ziyad ya keta mata haddi, amma abin nan da Ziyad ya fada sai ya ji ba shi da sauran guts na neman hakki a kansa. In har ya yarda da fadar Ubangiji a kan zina. To ya yarda kawai kamun Allah ne tun a gidan duniya. Wani kamun sai an je lahira. Ya yi kukansa mai isar sa a gaban Ziyad da kwamishinan yan sanda, sannan ya share hawayen sa ya mike yace a sake shi, ya janye karar sa, amma yana so hukuma tayi masa iyaka da Dr. Ziyad ba shi ba shi har abada! Kuma daga yau ya ajiye aiki a jamiarsu ta Turkawa (Nigerian Turkish Nile University). Yana tuki a kan hanyarsa ta komawa gida yana hawaye. Hawayen nadamar duk abin da ya aikata a baya. Shi kansa ya san talala ce Allah ya yi masa da soyayyar Saade, soyayyar da ko a labarun hikaya bai taba jin wadda ta yi daidai da wadda yake yi wa Saadatu yar Bilkisu ba. Yau aibunsa ya janyo an shiga gonarsa an keta haddin sa. Ya shigar da motar maadanarta, sannan cikin sanyin jiki ya kashe ta ya fito, kayan jikinsa duk sun baci da jinin hancin Dr. Ziyad, da sanyin jikin dai ya bude kofar falon don bai san a halin da zai riski Saadatu ba. Falon yana nan yadda yake tun safe, kofar dakin barcinsu inda abun ya faru har yanzu a bude, ya leka can bai ganta ba sai ya fito zuwa nata dakin. Tana kwance a kan gadonta tana kallon ceiling hawaye na bi ta gefen idonta. Fuskarta duk ta kumbura ta yi jazur. Ba ta taba shiga tashin hankali a rayuwarta irin yau ba. Ba ta taba ganin abin da ya tsorata ya firgitata tsananin firgitawa irin yau ba da aka yi attempting raping dinta da tsakar rana har dakin aurenta. Dr. Sageer Yusuf, ya nufi Saadatu da sassarfa, ya dago ta daga kwanciyar da ta yi ya rungume a kirjinsa. Ga mamakin Saade shi ma kukan yake yi. Cikin wata kassararriyar murya tamkar ba tasa ba yake magana. Saadatu did hedid he succeed??? Ya kasa karasawa sabida tsoron abin da zai fada din. Ta runtse idonta ta kankame Sageer jikinta yana rawa. No he didnt. Wata irin kakkarfar ajiyar zuciya Yareema Sageer ya saki, wadda bai taba yin irinta a tsayin rayuwarsa ba. Ko an yi ko ba a yi ba, ya ji abin da miji ko uba yake ji in an yi zina da yarsa ko matarsa. A fili ya ke furta, ASTAGFIRULLAH WAATUBU ILAIHI. Saadatu ta fashe da kuka tana rokon Yareema ya maida ta Askira, ita ta hakura da karatun. Yareema ya ja lallausan duvet ya lullube su, ya kwantar da Saade saman kirjinsa. Ki kwantar da hankalinki don Allah Saadatu. Aikin ma gabadaya na aje. Alfarma daya nake nema kada ki fadawa Fulani ko Maimartaba wannan kaddarar da ta faru, ni kuma duk abin da ki ke so zan yi miki, I promised. Saade ta ce, In ban fada ba za ka maida ni Askira gobe? Ya ce, Insha Allahu za mu koma gabadayan mu, amma sai na mika resignation letter, ki ba ni kwanaki uku. Da wannan ya samu ya lallashe ta. Amma shi kansa Yareeman tsoronsa ta ke ji, ta daku a hannun Ziyad koina na jikinta ciwo yake yi, ba ta gaya wa Yareema ba ne don kada ta kara daga masa hankali, ganin mawuyacin halin da yake ciki, amma kanta ciwo yake sosai sabida yadda Ziyad ya buga shi da bango. Duk yadda ya so ya samu yadda yake so a daren yau, Saadatu ta ki, shi kuma yana so ne ya yi amfani da soyayya ya gusar da tsananin tsoron da ya dankare mata a zuciya, amma ta ki bada damar hakan. Ya gaji da kokawa da ita, ya mike ya kunna fitilar dakin. Sai kuka ta ke mai ban tausayi. Ya ce, For Gods sake Saadatu, ni ma rapist din ne? Kukanta ya karu, ta ce, Yau daya dai ai sai ka kyale ni in ji da abin da ya dame ni, I cantdo it, gida nake son tafiya. Yareema ya dawo ya zauna daidai kafafun ta, ya debi kafafun ya aza bisa cinyoyinsa, ai kuwa ta saki wata kara don azaba, wannan ya tabbatar masa akwai targade a yatsar kafarta. Sosai ya ci gaba da jan yatsun kafarta a hankali har ya gane mai targaden. Ba tun yau ba ya iya gyaran targade, tana kuka tana komai haka ya gyara mata. Sai lokacin ya lura cewa, goshinta ma ya kumbura sosai. Hawaye suka ciko idonsa, ya ce, Im sorry Saadatu, ni na jawo miki, one is responsible for the consequences of what he have done. Amma ke kam ba ki da laifi, tsarkakakkiya ce aka wanke aka bani cikin girma da daraja. Dole gobe mu je asibiti a binciki lafiyarki, in ma yayi kika boye min ayi miki wankin ciki. Ni ba inda za ni, kuma na gaya maka bai yi ba. Ta fada cikin kuka, ciwo har cikin kokon kanta. Kawai ka sa ni a jirgi in tafi Maiduguri, daga can sai a dauke ni a filin jirgi, bazan iya kara kwanaki uku a gidan nan ba. Ya kara sassauta murya mai nuna ya fi ta damuwa da abin da ya same ta. Na rage kwanakin ki ba ni kwana biyu mu tafi tare, in ma kin ce kada mu sake zuwa garin Abuja ba za mu sake ba!. Da wannan ya samu ya lallashe ta ta hakura ta yi barci. Washegari da asubah a firgice ta tashi tana tambayarsa aljanin nan ya sake dawowa? Ya kankame ta yana gaya mata, Relax Saadatu ba fa aljani ba ne, abokina ne Dr. Ziyad wanda yake karbar abinci a wajenmu. Mamaki da tsoro ya kashe Saade a kwance, ta kasa cewa komai, har duniya ta yi lalacewar haka? Aboki kuma makwabci mafi kusanci ya nemi raping matar amininsa? Wannan wace irin rayuwa ce? Tsoronta ya nunku fiye da tunanin ta na cewa Ziyad aljani ne. Abuja ta kara fice mata a ka, ba abin da ta ke so irin ta bude ido ta ganta a dakin ta na unguwar Fulani Bilkisu. Da gari ya waye ya yi wanka ya shirya, sannan ya rubuta resignationletterdaga NTNU. Da ya zo fita ne Saade ta ce, bai barinta ita kadai sai dai su tafi tare, tana da paper din karfe takwas. Duk da ba ta karanta komai ba, a matsayinta na matar Dr. Sageer wadda ko a kwance suke ba ya rabo da tisa mata karatun fannin su na Pure and Applied Chemistry, ta san ba za ta kasa rubuta wannan takardar ta Inorganic Chemistry ba. Shi ma ya fi so su tafi taren, don haka ya taimaka mata ta yi wanka. Tana fitowa daga paper ta same shi a mota yana jiranta, dukkansu ba mai walwala, suka nufo gida. A daren ba ta bari sai gobe ba ta hade kayanta tsaf ta daure. Lamarinta har da na shagwaba kuma, ya yi - ya yi su je asibiti a duba ta ta ki. Washegari ya shiga don ya gama cike sauran takardun ajiye aiki, ya ce mata insha Allahu ba zai wuce awanni biyu ba. Da kyar ya lallabata ta yarda bayan ya ba ta mukullan kofar kitchen da na kofar shigowa duka a hannunta. ****** Yareema Sageer bai dade da fita ba Ya Gumsu da kanwarta Aunty Daja wadda ke aure a nan Abuja tana auren wani ministan yada labarai, suka zo gidan cikin wata zabgegiyar mota. Ya Gumsu ta zo auren babbar yar Aunty Daja ne Abuja tun shekaranjiya. Tun da ta iso ta ke ce da Daja a kai ta gidan Yareema, Daja na ba ta hakuri kan ta bari a kai amarya ko me za su yi sai su yi, ita ma ba ta bayan hada zuria da yar annamimiya Fulanin Askirama. Suna sauka daga mota suka karaso kofar shiga falo, suka soma yi mata wani irin mahaukacin bugu, wanda ya karasa razana razananniya Saade, wadda da ma ta ke zaune a darare tana jiran dawowar Yareema da trollies dinta uku a gabanta. Ta gama sa wa a ranta yau komai dadin bakinsa a Askira za ta kwana. Sai kuma ga wannan mahaukacin bugun, ba abin da ta kawo a ranta sai Ziyad ne ya dawo. Idanunta suka raina fata, hawaye ya soma malalowa. Ba ta so ta yi ihu ma kada ya san tana cikin gidan, sai mazari jikinta yake daga tsayen da ta ke, wani fitsari ya kwace mata. Amma me? Sai ta jiyo murya kamar ta mata suna kiran sunanta. Ba ta yi wa Ya Gumsu farin sanin da za ta dau muryarta ba, amma sai ta ji tana fadin, Ni da gidan Dana aka bar ni ina buga kofa da mutuncina na Gumsun gari da komai? Da sauri Saade ta karasa ta bude kofar da mukullan da dama suke rike a hannunta. Ta gane Ya Gumsu, dayar ce ba ta sani ba. Tana kokarin yi musu barka da zuwa ta ji wani lafiyayyen mari ya sauka a kan kuncinta, Aunty Daja ma ta kai mata nata. Shegiya karuwa yar karuwa, tsintattun bisa titi. Idan ba Bilkisun ce ta haifa min Yareema ba, ba kuma ita ta ajiye ki a gidan nan ba, to sawunki a likkafa ki kama hanyar gidan ubanki, tunda an ce kina da shi. Idan na ganki a masarautar Askira sai na sa an nakasta ki yadda ba Yareema ba babu wani namiji da zai kwashe ki. Fice mana a gida ki san inda dare ya yi miki kafin in sassaba miki kamanni. Ta hankado ta waje, Daja kuma ta dauki hijab dinta ta jefo mata suka dinga hankada ta har kofar fita gidan, bayan Daja ta kara zazzabga mata mari. Farar fuskar nan ta yi jawur tayi kitumur kamar gauta. Marukan da ta sha sun kai goma. Yatsunsu ya kwanta lambam a kan farar fatar fuskar Saade. Kuka ma wani lokacin rahma ne ga dan Adam, a lokacin da zuciyarsa ta rasa abin yi. To Saade ta kasa ko da fidda hawaye, tana nadamar yarda da aure da soyayyar Yareema Sageer alhalin tana da masaniya kan cewa, mahaifiyarsa ba ta kaunar tata kamar ajalinta. Ya yi amfani da dukkan dabarunsa na wayayyen Da namiji ya sanya soyayyarsa a zuciyarta, ya ribace ta ya kassara zuciyarta. Yau mahaifiyarsa ta yi mata wulakancin da ko ita mayya ce dole ta hakura da Yareema Sageer sai a wannan lokacin ne ta ji hawaye masu dumi sun zubo mata. Ya ya za ta yi ta je Askira? Duk da Ya Gumsu ta ce kada ta je din, amma ba ta da inda ya fi can, tunda uwarta tana can, za ta bar masarautar Askira ne only ranar da babu Fulani a can ko ranar da ita ma Askirama ya kore ta. Ko kudin mota babu a tare da ita, daga ita sai hijabin sallarta. Amma ta tabbata za ta iya kai kanta Askira, idan ta ganta a Maiduguri. Ko da da rarrafe da jan ciki ne. Tana wannan tunanin tana kuka, ba ta san cewa ta hau bisa titi ba ta bar tafiya a gefen hanya. Daidai lokacin da shi kuma ya fito daga NTNU yana sharara gudu don tafiya gida, ya hango wata mace na tafiya tsakiyar titi kamar bata ji ba ta gani, motoci na ta kauce mata, wasu su bi ta da zagi, wasu su kunna mata fitilar zagi, amma ba ta ko san suna yi ba. Ya sakar mata kakkarfan horn don ta sha gabansa, ta juya a firgice sai ya ga Saade. A hankali ya sauka a gefen titi, ya fito da sauri ya bi bayanta yana kiran sunanta. Saadatu Hashim, Saadatu Askira ina za ki je haka? Muryar Said abokinta, Saidu-Saidunta. Yau da shi ta aura wa zai yi mata wannan wulakancin da cin zarafin? Wani hawayen ya sake zubo mata, ta sa fuska cikin hijabinta tana kuka. Said ya hau waiwaye cikin tsoro. Har zai ce ta shiga motarsa ya kai ta inda za ta je ya tuna gargadin Yareema Sageer. Kada ka kara daukar matata a motarka ko da da niyyar taimako ne. Said ya naushi hannun damansa da hannun hagu, ga shi kuma ba zai iya tafiya ya barta a kan titi ba, ko da kuwa supreme court Dr. Sageer Askira zai kai shi a dalilin hakan. Da ganin halin da ta ke ciki tana tsananin bukatar taimako, ba zai barta ta ragaita a babban birni irin Abuja ba. Wane irin taimako zan iya ba ki? Said ya fada cikin tsoro, yana tsaye nesa-nesa da Saade yana kuma waiwayawa dama da hauni kada Dr. Sageer ya zo ya same shi. Kudin mota. Ba ta san lokacin da ta furta ba. Ina za ki je? Ya tambaya da sauri. A hankali ta ce, Garinmu Askira. In aka sauke ki a Maiduguri za ki iya zuwa har can Askiran? Da sauri ta gyada kai. Said ya ce, Zan sa ki a tasi zuwa airport, sai in bi bayanku, sai mu je in yankar miki ticket din Maiduguri. Saade ta hau godiya, tana yi masa addua. Ji ta ke kamar ma ga ta ga Fulani a gabanta. Hakan kuwa aka yi, Said bai bar airport din ba sai da ya tabbata jirgin Maiduguri ya daga da Saade. Ya kuma damka mata naira dubu goma, ya bar filin jirgin cike da tausayinta. A ganinsa iyayensu sun cutar da ita da suka aura mata babban mutum kamar Dr. Sageer, ba zai ba ta kulawar da in shi ya aure ta zai ba ta ba, ban da kishin balaI bai san komai ba (a ganinsa). Tunda jirgin Azman ya lulluka sararin samaniya ya doshi arewacin Nigeria, Saade ta kankame jikinta wuri guda tana kuka, ba ta san ya ya za ta iya rayuwa babu Sageer ba. Amma ta tabbata Ya Gumsu ta raba su kenan, ba za ta kara bari su rayu inuwa guda ba. Ya taba cewa yana fuskantar barazana akan auren su, wanda ya sanya shi tabbatar da auren su a lokacin da bai shiryawa hakan ba, yanzu ta tabbatar ba komai bace barazanar, Ya Gumsu ce. Har gobe bata yi naam da zaman su tare ba. Wannan tunanin kadai na matukar tayar da hankalin Saade, ta rasa inda za ta tsoma zuciyarta ta ji dadi. Wani irin sanyi ta ji yana shiga har cikin bargonta. Ba jimawa hakoranta suka soma karo da juna, kafin a yi haka zazzabi mai zafi da ciwon kan da ta kwana a ciki sun hadu sun rufe ta ruf. Ta sauka a filin jirgin saman Maiduguri cikin mawuyacin hali. Ba ta gaya wa kowa tana tafe ba balle a san da zuwanta a zo a dauke ta, sannan ba wayarta a hannunta ta baro ta a kan gadonta. Duk da cewa ta haddace lambar Fulani, amma ta ga gara ta bi motar kasuwa ta karasa Askira, tunda akwai kudi isassu a hannunta. A nan airport ta samu wani mai taxi yana faman binta da nacin tambayar ina zaa kai ta? Ta ga cewa, zuwa tasha da neman motar Askira karin wahala ne a gare ta, ga shi da ma ta yi matukar jigata, sai ta juya ta ce da shi, Nawa zan ba ka ka kai ni har Askira? Mai taxi ya yanko kudin da a tunaninsa ko rabinsu ba za ta biya ba. Amma sai ya ga babu musu ta amince. Ya bude mata kofa ta shiga ya rufe, ya ja mota suka naushi hanya. ****** ASKIRA EMIRATE Lokacin da suka shiga garin Askira magriba ta kawo kai. Ita ta dinga nuna masa hanya har kofar fada. Ya ajiye ta ta mika masa duka dubu goman, sannan ba tare da ta kara cewa uffan ba bayan godiya, ta durfafi cikin gida. Amma me? Tana saka kafa a soro na farko hajijiya ta soma dibarta, ga yunwa ga wahalar zaman mota. Ga wani irin masifaffen ciwon kai da ke sakadarta, taku biyu ta yi a soron farko Fadawa na zazzaune sai gani suka yi mace ta fadi a wajen, sakamakon kafafunta da suka kasa daukarta, duhun yunwa da na hajijiya kuma suka mamayi ganinta. Taimakon Allah ne kadai ya kawo ta Askira lafiya. Fadawa biyu sun shaida ko wace ce, kasancewar cikinsu akwai direban fada da ya ke kai su El-Kanemi. Cikin kidima suka kira bayi mata, su uku suka dauke ta ranga-ranga sai Unguwar Fulani Bilkisu. Ba aladar Askirama ba ce bin dakunan matansa, amma Fulani Hibbani wadda ita ce mai girki, sarkin gulma da daukar zance ta shigo yanzun nan ta same shi yana cin abinci, kamar ta manta shi din ne ta ke magana da shi, tsabar gulma da ke cinta. Mai Askira ashe abin da Yareema ya yi ke nan? Ya sako yar Bilkisu bayan ya yi mata shegen duka? Ta dawo rai a hannun Allah Anya shi ma ba giyar yake sha ba kamar matar. Sauran maganar makalewa ta yi a bakinta ganin wata irin zabura da Askirama ya yi. Kafin ta ankara kuma ta tsinto shi a bakin kofa bayan ya saka takalminsa na gashin dawisu. Fanna tare da dukkan kuyangin Fulani suna kan Saade, sai firfita suke mata bayan an samu ta farfado, tana kwance shame-shame bisa cinyar Fulani, tambayar duniyar nan Fulani ta yi mata, amma ta ki cewa komai. Fulani ta soma fusata, amma ta yi kokarin hadiye fushinta. Ba za ki gaya min ina Yareeman ba? Ya san kin taho? Ke da wa ki ka zo? In sakinki ya yi ki yi mana bayani. Kallo daya Fanna ta yi wa sauran kuyangin suka hau darewa suna barin falon, ta yi hakan ne ganin irin rikicewar da Fulani ta yi har ta manta cewa suna tsaye. Ko sakin Saade aka yi ba za su so a ji ba, a wannan gidan na gulma da jiran kiris a kan duk wani abu da ya shafi uwargijyarta. Gyara kimtsi kimtsi gyara Zakin Askira. Suka jiyo kuyangi na fadi daga waje, tabbacin Alanguburo ya durfafo unguwar da kansa. Kamar kiftawar ido kuma sai ga shi a kansu, sabida saurin da ya shigo da shi ba irin tafiyar sarauta da yake yi ba. Lafiya Bilkisu? Me ya faru? Ya tambaya cikin matukar kidima yana kallon kumburarriyar fuskar Saade da ta hade ta cakude ta yi jajir. Wa ya kawo ta? Ina Yareeman? Dukanta ya yi? Muryarsa ta karye gabadaya cikin debe tsammanin abin da Hibbani ta gaya masa. Fulani Bilkisu ta yarfar da hannu, ta ce, Wallahi Allah ban san komai ba. Yadda ka ganta ni ma haka na ganta. Na kuma yi tambayar duniya ta ki ce min komai. Jikinsa har rawa yake ya ce, Bari in kira shi a waya, amma in ya tabbata abin da aka gaya min ne zan sa kafar wando daya da Yareema. Yana kokarin kiransa ne sai ga kiran Yareeman ya shigo. Ya amsa wayar ba tare da ya ce uffan ba. Daga can bangaren Yareema ya ce cikin wata irin murya da Askirama ya kasa gaskatawa ta Sagirunsa ce. Alanguburo, Allah Kawun jo (Allah ya kara maka yawan rai) a taimake ni a gaya min ko Saadatu ta zo Askira??? Kamar ba zai yi magana ba, amma tabbas yana son amsa guda daya kwakkwara daga bakin Yareema. Ka fara gaya min abin da nake son sani, sakinta ka yi? Yareema ya wani irin girgiza kai, tamkar Askirama na ganinsa, gumi ya wanke masa fuska, muryarsa na hardewa ya ce, Babu saki tsakani na da Saadatu har abada! Babu wulakanci tsakanina da amanarka har abada. Sai kauna da soyayya mara yankewa domin na samu fiye da abin da ka kwadaita min samu cikin aurena da Saadatu Na je in kai resignation letter ga V.C in cike takardu in dawo mu taho tare sabida wata yar matsala da na samu wajen aikin nawa, kafin in dawo sai sai sai. Ya kasa karasawa. Ambatar sunan mahaifiyarsa a wannan gabar ya san daidai yake da raurawar igiyar aurenta kamar yadda ya tabbata nasa auren yana rawa a halin yanzu, in har komawar Saade gida ya tabbata kuma ya je kunnen Askirama. Wata tsawa da Maimartaba ya daka masa sai da ta hautsina gabadaya kayan cikinsa, Ba za ka gaya min abin da nake son sani ba? Sakinta ka yi ko aah? Yareema ya kifa kai jikin kujera ya saka kuka kamar Mai Askira na gabansa. Ban sake ta ba wallahi ban sake ta ba Ya Gumsu ce ta kore ta, kuma Uche ya gaya min har dukanta sun yi. Im on my way nowto Askiratunda alhamdulillahi ta iso gida. Waye ya gaya maka ta iso gidan? Ka fada wa Babarka ta share dakin Saadatu ta zauna, don nata dakin na rufe shi daga yau. Kai kuma bana bukatar ganinka gabana ka je ta aura maka duk yar uban da ta ke so. Yareema kadan ya rage ya zauce, bai iya sauraron bakaken maganganun Askirama ba ya ji sallamar Ya Gumsu da Aunty Daja. Ya Gumsu ta dube shi ta kyabe baki, ta ce, Yanzu sabida na raba ka da wannan jarabar shi ne ka ke yanka wannan uban gumin? Sannu tattabara sarkin soyayya. Ai da ma waadin watanni uku muka yi da kai za ka mayar wa uwarta yarta yadda ka karbe ta. To na ji shiru, shi ne na zo ni da kaina na sake ta, ka gaya min hadisin da ya ce ba ta saku ba. Aunty Daja ta karbe, Ban da abinka Yareema, uwarka gata ta ke maka, yanzu aure na neman ci gaba ake yi ba na komawa baya ba. Kamar ka Yareeman Askira mai jiran gado ka rasa matar aure sai agolar gidanku? Ban da uwarka tsayayya ce ai da yanzu labari ya sha bambam. Bai san sanda ya kai mata kutufo ba, ta yi maza ta kauce ya naushi iska. Ya daga ragaitattun idanunsa ya dube ta. Aunty Daja ki ke ko wa? In uwata za ta shiga hurumina in kyale ta ban da ke wallahi. Na auri agolar tunda ke kin auri Minista ina ruwanki? Agolar na ga ta fi dacewa da rayuwata, sai ki zuba ruwa a kasa ki sha kun kore ta kamar yadda Askirama ya kori uwata. Bai ankara ba ya ji hawaye na son zubo masa, don haka ya tashi ya bar wajen. Ko a jikin Ya Gumsu, ta ce, Ya dade bai kore ni ba, tunda ya auri uwarta na kara gane kansa? Sau dubu gara min tubabbiyar nan a kan diyar Bilkisu. Dadin abun ina da inda zan zauna ko ba gidanka ba. Kuma ba zan bar gidan nan ba sai ka rubuta takardarta ka ba ni Yareema bai tsaya ba ya nufi motarsa. Yana ji Aunty Daja na lallashin Ya Gumsu, ta yi hakuri tunda dai sun kore ta ba sai ya yi saki ba, ko ba komai sun kunsawa Bilkisu bakin ciki, kuma in tana son yarta ba za ta barta ta dawo ba a yadda suka ci zarafinta. Yanzu abin da ya kamata ki maida hankali a kai shi ne, nema masa auren Hajjaju. Ya Gumsu ta balla mata harara tana zama cikin royal chairs din Saade, ta ce, Ke ma kina wasa ne, wa zai karba masa auren a halin yanzu na taba yar mowa? Da na sani ma ban kore ta ba, dagewa na fara yi aka auri Hajjajun, bayan ta shigo sannan mu san yadda zamu yi da ta gidan, amma yanzu na tabbata na bata goma ne daya ba ta gyaru ba. Tunda ki ka ji ya ce ubansa ya kore ni. Ya Gumsu ta fada cikin damuwa, wadda ba ta karasa har kasan ranta ba. Aunty Daja ta yi tsaki, ta ce, Haba Gumsun Askira, ke ce fa uwar Yareema, uwar Ya Maira, masarautar Askira taki ce ke da yayanki, kin taba jin an saki Gumsun gari uwar iyali? Ai sai dai ya yi fushinsa ya gama ya sauka, amma ba sa saki, shi ya sa na tabbatar miki yaron nan ba zai saki yar Bilkisu ba, mu dai yi kokari ya yi aure na shiga tsara ki manta da wata yar Bilkisu. Kishiya kadai ta ishe ta. Hum! In ji Ya Gumsu. Ba ta san irin bayanin da za ta yi wa yar uwarta ba, ta gane cewa, kishi da BAGGARA ba abu ne mai sauki ba, sai dai ita kishiyar ta yi ta jin jiki tana kunsar bakin ciki har karshen rayuwar ta. Ta yadda Mai Askira zai yarda ya karba wa Yarima auren yar sarkin Bauchi yanzu shi ne ba ta sani ba. Babu ubansa Sarkin Askira kuma wa zai bashi auren? Ko ita za ta je ta nemo masa waliccin auren yar sarkin Bauchin da kan ta? Ta fahimci ta lalata chance dinta ne kawai na kara auren Yarima da korar Saade da dukan ta. Da ta sani ma kafewa ta yi the other way kan cewa, tunda ta bada dama ya auri zabin ransa da zabin ran mahaifinsa, to ita ma ya auri zabinta. Amma yanzu ta tabbata kwabarta ta gama yin ruwa. Don haka ta kasa zama gidan Yarima kamar yadda ta yi niyya, ta bi Aunty Daja gidanta tunda shi ma ya fice ya bar musu gidan, ta kuma tabbata Askira ya nufa. Uche dake shigowa a lokacin yana ganin fitar su ya je ya kulle koina na gidan. Tana kallon kiran Maimartaba yana ta shigowa wayar ta, amma ta yi funfurus ta ki dagawa sabida tsoro. Ta san ba zai taba sakinta ba, amma in ka tabo shi hukuncinsa ba shi da dadi. Suna tafe a hanyarsu ta komawa gidan Daja, ta gaya mata Maimartaba yana ta kiranta, Daja ta ce, Ki dauka a yi ta ta kare. Ta kuwa daga ta hanyar cewa, Allah Kawun jo (Allah ya kara maka yawan rai). Ina kan layi. Muryar Askirama mai zurfi da kauri (husky) ta bakunci kunnuwanta. Bana zaton Yareema ya gaya miki sakona. Cewa na yi ki share dakin Saadatu ki zauna, don ba ki da daki yanzu a gidana. Cikin gatsali ta ce, Allah ya kara yawan rai wani abu aka ce na yi? Ziyara fa kawai na kawo musu. Ta fashe da kuka, kukan da daga ji za ka san bana gaskiya ba ne. Don takaici Mai Askira sai ya kashe wayarsa, kada ya yi abin da zai zo daga baya yana nadama. Ya Gumsu ta shiga bandaki a washegarin ranar za ta yi wanka. Ta sa kafa a cikin bahon wanka ba ta lura da jikakken sabulun da ke ciki ba, kafarta ta sauka a kan sabulun ta zame ta tafi gabadaya ta yi wata irin mummunar faduwa. Faduwar da sai daukanta aka yi ranga-ranga zuwa asibiti baki ya karkace yana ta fidda kumfa. Idan Ubangiji ya nufi alamari, bawa ya nuna ja da hukuncin Ubangiji, sai Ubangiji ya barshi da dabararsa, amma idan Ya ga dama talalar da zai maka ta dare daya ce. Wani rabon sai ya kawar da kai dagadoron duniya gabadaya. A ci gaba da rayuwar babu kai, babu mai tuna ka da kyakkyawar zuciya balle ya yi maka addua. Don haka Gumsun Askirais lucky that shes alive a daidai lokacin da Saade ke jikin mahaifiyarta tana ta kelaya amai kamar da bakin kwarya. Tunda ta iso ta ke zazzabi da ciwon kai, kafin wayewar gari kuma sai haraswa, ta kasa cin komai, gabadaya ta fige ta yi zuru-zuru. Fulani da Fanna suna tsaye a kanta tun jiya. Shi ma Maimartaba ba ya rufa awa guda bai kira Fulani ya ji me Saade ta ke ciki ba. A karshe ya turo likitar matan gidan don ta zo ta duba ta a san takamaimai me ke damunta. Ita dai Fulani tuni ta sha jinin jikinta. Tun daga sanda Saade ta ce ba ta son warin turarenta. Amma kuwa Yarima bai kyauta ba, ya saba alkawarin da ya yi mata. Saade is too young da haihuwa wani matsanancin tausayi ya kama ta. Amma da ta tuna ba haramci suka aikata ba sai ta rage wa kanta damuwa. Wannan rabo na kurkusa da kofar daki ina Ya Gumsu za ta kai shi? Ko kusa abin da Ya Gumsu ta yi wa Saade bai sa ta ji tana so a raba auren ba, ko don ganin halin bacin ran da Askirama ke ciki, wanda ko ita da ta haifi Saaden abin bai tabata har haka ba. Ta sa a ranta Ya Gumsu za ta yi fiye da wannan in dai a kanta ne. Kuma a washegarin ranar bayan fitar Dr. Zainab da ta duba Saade ta tabbatar wa Fulani akwai ciki na sati Shidda, ta shiga don ta yi wa Askirama wannan albishir ta ji yana amsa waya. Sai kuma ta ji ya ce, Stroke? Cikin tsananin mamaki. Gumsun da ko jiya na yi magana da ita a waya lafiya lau? Aka yi magana daga daya bangaren wanda ita ba ta ji ba, sai ta ji ya ce, Ai shi ke nan, Allah ya ba ta lafiya. Yayanta sai su je Abujar su yi jinyarta, amma Allah ya gani ni ba zan zo ba Daja, yar uwarki ta girma ba ta san ta girma ba. Na dade ina hakuri da halayenta ta kasa gane gata na yi wa rayuwar Yareema da shi bakidaya da na aura masa Saadatu. Babu yadda ban yi da ita ba ta karbi hukuncin Ubangiji, ta nuna min ta hakura har za ta kai musu ziyara, shi ne ta yi tattaki har dakin yarinya, ta ci zarafin marainiyar Allah ta koro ta tun daga Abuja har Maiduguri da Askira ita kadai a wannan marrar ta satar dan mutum kamar satar takalmi. Don haka ina nan a kan bakana, Gumsu ta ci gaba da maye gurbin Saadatu wajen Yareema Sageer. Babu Saadatu babu danta, sai ranar da ta yo tattaki har dakin Bilkisu ta ba ta hakuri a kan cin zarafin da ta yi wa yarta. Ta kuma furta da bakinta cewa ta amince su ci gaba da zaman aure da bakinta. In ba haka ba shi ma Yariman kada ya sake ya tako min gida. Yana gama fadin haka ya kashe wayarsa yana maida numfashi cikin bacin rai. Fulani Bilkisu ta karasa ta gurfana a gabansa, tafukan hannunta bisa tafin kafarsa. Cikin muryar lallashi da son kwantar masa da hankali ta yi masa albishir din da ke bakinta. Da gaske? In ji Askirama. Cikin excitement din da ba zai misaltu ba. Ta kashe shi da lallausar murmushi, ta ce, Da gaske Dr. Zainab ta tabbatar da ciki na sati shidda a jikin Saade. Sabida haka Askirama ka yi hakuri da duk wani bacin rai, tunda Ubangiji ya nuna mana ayarsa. Idan ta warware kwana biyu a manta da komai a mayar wa da Yarima matarsa. Mai Askira ya girgiza kai ya ce, Ayoyi kam ai muna ta ganinsu. Yanzu kanwarta ta kira ni ta shaida min cewa, suna asibiti da Gumsun Gari, ta fadi a bayan gida ta samu stroke. Innalillahi wainna ilaihi rajiun. In ji Fulani. An gaya wa Yarima da su Yaa Maira? Cikin damuwa ya ce, Yarima ya taho tun jiya ta mota, babu jirgi, amma Awaisu ya gayaminya samu minor accidentahanya, bai ji ciwo ba amma ya bugu, kuma motar sa ta jikkata, ya iso Askira tun jiya, ni na ce da Awaisu ya gaya masa kada ya sake in ganshi gabana ko bangarenki. Ya Maira kuma sun kama hanyar Abujan. Cikin dimbin alhini Fulani ta ce, innalillahi wainna ilaihi rajioun. Zama bai ganmu ba, ya kamata a shirya mana tafiya mu uku, ni da Yakirjinoma da Hibbani. Yareema na tabbata Awaisu zai bashi duk kulawar data dace, amma don Allah Askirama ka bar shi ya dawo gidan nan. Ya yi ajiyar zuciya, wannan karon cikin muryar sa akwai sassauci, ya ce, Su za su je, amma ban da ke. In kin tafi wa zai kula min da Saadatu da Chiroman Gari? Ta yi murmushi kadan, jin har ya bai wa dan cikin Saade Sarauta tun kan ya iso duniya. Ta ce, Fanna za ta kula da su sosai. Bai kamata a ce su sun tafi ni na zauna ba, sai ta dauka sabida abin da ta yi wa Saade ne wanda ni sam bai shafe ni ba. Ta kare zancen ta da cewa. Ai Saade yarta ce! Koda bata auren Yarima. Askirama ya kura wa matarsa Bilkisu ido, yana mamakin kyawawan halayenta. Matansa sun kasa fahimtarta ne, amma duk ta fi su kyan hali, ba ta taba dauko zancen wata cikinsu ta kawo masa. Su kuwa basu da aiki sai fadin aibunta. Sun dauki kishin duniya su duka sun dora a kanta. Sun kasa gane ba kyawun halitta kadai ke rudarsa a kan Fulani Bilkisu ba, har da kyawawan halayenta. Amma duk yadda ta so Askirama ya barta zuwa Abuja duba Ya Gumsu ya ki amincewa da hakan. Yaa Maira ce ta zo ta hada kan sauran kannenta mata da maza aka ba su motoci da dogarai suka kama hanyar Abuja. Cikin tashin hankali. Hibbani da Yakirjinoma jirgi daya suka bi tare da Ahmad da Suhail wadanda za su kula da su. Fulani ta kira Yareema a waya bayan ta koma dakinta. Muryar Yareema har ba ta fita sosai, kamar ta wanda ke fama da mura, shi kadai ya san halin da yake ciki. Ciwon da jikin sa ke masa sakamakon buguwar mota bai dame shi ba kamar hukuncin da Askirama ya yanke akan sa na nesanta shi da Saade. Yana gidansa tun isowarsa ko falo bai leko ba tunda Askirama ya aiko Awaisu ya gaya masa sakon kada ya sake ya ganshi a fada ko shigifar sa, kuma kada ya sake ya je inda Saade ta ke. Har sai mahaifiyarsa ta bada hakurin cin zarafin da ta yi mata har dakin auren ta. Ta kuma yi alkawarin karbar Saadatu matsayin suruka sannan ne shima zai janye nasa takunkumin. Shi ya san wannan decision ba mai sauki ba ne ga Ya Gumsu, a yadda ya san kafaffiyar zuciya irin tata in tana kin abu. Kuma bai fita daga wannan zullumi da tashin hankalin ba a daren jiya Aunty Daja ta kira shi tana kuka, wai Ya Gumsun ta fadi a toilet ta samu stroke. Ya kwana cikin wani hali na kaka-ni-ka-yi, and he is speachless.Wordless. Moodless. Ko magana ba ya iya yi. Awaisu ya so ya taya shi hira a daren ranar bayan ya bashi magani ya kira likita ya duba shi ya tabbatar babu mummunan rauni a jikin sa, ya ce ya tafi kawai ba ya bukata, sai kuma yanzu da wayewar garin yau ya samu wayar Fulani Bilkisu. Yareemah, kana lafiya? Ta fada cikin tausayawa. Ji ya yi idanunsa sun cicciko da kwalla, bai zaci wannan rahmar daga gare ta ba. Abin da bai sani ba shi ne, ita halinta ya bambanta da na sauran mata. Mace ce mai hangen nesa da tsananin kawaici da maida dan kowa nata. Im sorry Fulani, Im sorry. Ya furta in a subdued voice. Ta yi murmushi, ta ce, Ba zancen Saade ya sa na kira ka ba. Na kira ka ne in jajanta abin da ya faru da Ya Gumsu. Da accident da aka samu, Allah ya tsayar haka, Ya sa kaffara, Allah ya ba ta lafiya. Na so in bi su Yaa Kirjinoma Abujan, Askirama ya hana ni, sabida ita ma Saade kwance ta ke babu lafiya tun isowarta. Tamkar zuciyarsa za ta fito ta bakinsa sabida zullumi, ya ce cikin wata marainiyar murya, Me ke damunta? Fulani ta yi dan jimm! Kafin ta ce, Na dauka ka sani ai. Gabansa ya yi mugun faduwa, kada dai Saade ta gaya musu maganar Dr. Ziyad ne? Yau da ya shiga uku in Askirama ya ji zancen nan ya san aurensa da Saade ya kare. Hawaye suka fito daga idanun Yareema Sageer ba tare da ya shirya ba. Amma sai Fulani ta fadi abin da ya gigita shi, ya wanke zuciyarsa daga duk wani rudani da dimauta da ta ke ciki. Ciki ne tare da ita na kusan watanni biyu. Yareema sai da ya cire wayar daga kunnensa, don ya tabbatar da wanda yake magana, My inlaw ba gizo kunnuwansa ke masa ba. Ya wani irin lumshe idanunsa yana karbar wani irin excitement a cikin kirjinsa. Don haka ka kwantar da hankalinka ka koma Abuja ka kula da lafiyar mahaifiyarka. Saade tana karkashin kulawarmu insha Allah. Kafin sannan zuciyar Askirama ta huce sai a ba shi hakuri. Abin da nake so yanzu shi ne ka koma Abuja ka yi jinyar mahaifiyarka. Insha Allah, I will. Ya fada cikin girmamawa. Har sun yi sallama ya kasa jurewa. Cikin jin nauyi ya ce, Fulanin Sarki zan iya magana da Saadatu? Fulani ta ce, Ta samu barci, in ka koma Abuja ka samu nutsuwa ka kira ni, zan ba ta wayar insha Allahu. Da wannan suka yi sallama. A washegarin ranar ya tattara ya koma Abuja. ***** Yau asibitin national hospital Abuja ya ga iyalin masarautar Askira, ko ina ka wulga motoci ne cike da dogarai masu rubutun Askira Emirate. Tabbacin mara lafiyar na da alaka da hamshakiyar masarautar Askira. Lokacin da Yareema ya iso an kai Ya Gumsu daki na musamman (V.I.P room) an ba ta kwanciya. Sanda suka shiga shi da Awaisu Ya Gumsu barci ta ke yi. Amma jin muryar Yareema na magana da likita sai ta hau kokarin bude idonta. Duk da barcin da ya ci karfinta kokarin magana ta ke yi da bakinta da ya karkace, amma ta kasa. Yareema ya matsa daidai kanta yana hawaye yana fadin, Ki yafe ni ya Gumsu, na kasa cika alkawarin da na yi miki, amma na alakanta hakan da rabon gaggawar da ya rantse a tsakaninmu. Ya Gumsu Saadatu ciki gare ta, na kasa cika alkawarin ki Ya Gumsu na kasa. Ya saka kuka tare da kifa kansa a kan cikinta. Da hannunta mai lafiyar ta mika tana shafa sumar kansa, tana ci gaba da kokarin furta magana abu ya gagara, sai hawaye ke bi ta gefen idonta. Amma daga yadda ta kama shi da hannu daya ta kankame tana hawaye ya san alheri ta ke son fada. “Is ok Ya Gumsu, ki yi barci. Ni dai fatana ki fahimci cewa Saadatu alkhairi ce a gare mu kamar yadda Alanguburo ya hango. Ya Gumsu ki kwantar da hankalinki a kan Fulani Bilkisu da ahalinta, wallahi ba ta nufinki da sharri. Idan Askirama ya fi sonta ba ya nufin ke uwar yayansa ba ya sonki. Yana son ta ne saboda kyautatawar ta gareshi tafi taku. Amma kowa da gurbinta, kuma kowa da matsayinta. Sai ki duba ki tace ki ga shin me take yi wanda Askirama ke so? Kema sai ki kwaikwaya. Shaidan ne ya ke kambama miki soyayyar Askirama ga Fulani Bilkisu, amma ita in ya sa ta tana yi, in ya hana ta tana hanuwa. Ke kuwa fa Ya Gumsu? Abin da ki ka ga dama shi ki ke masa, yana hakuri saboda mu, Ya Gumsu lokaci bai yi ba da girma zai bayyana a halayenki? Hawayenta ya dadu, sai gyada masa kai ta ke akai-akai kamar kadangaruwa. Yarima ya ci gaba da cewa. Ya Gumsu ki yafe mini ban cika alkawarin da na yi miki ba, musamman da na ji kin ce bayan watanni uku za ki raba mu. Na kasa Ya Gumsu, na kasa Saadatu ciki ne da ita, zan yi azumin kaffara ki yafe mini. Tana so ta ce masa babu kaffara a kanka, tunda ba fadar Ubangiji ba ce, sannan baka sabi Allah ba, amma ta kasa. Yarima ya rungume ta yana ci gaba da rokonta rangwame da afuwa a kan aurensa da Saadatu wanda ya kara karya zuciyar Ya Gumsu, ta amince soyayyar danta ga yar Fulanin Askirama wani hadi ne daga Allah, domin ya dinke barakar da ke tsakaninsu. Ya kawo maslaha da fahimtar juna ga iyalan Maimartaba Sarkin Askira. Kwanan Ya Gumsu da iyalanta uku a National Hospital, sauki na samuwa a hankali. Ya Maira ta kira Yareema gefe ta ce tunda jikin da sauki, kuma an ce gashi ya rage za a dinga yi mata, ko zai nema musu sallama su koma gida? Sai a yi hiring professional din da za ta dinga yi mata gashin a gida? Sun yi yawa a asibiti, kuma ba wanda zai yarda a ce ya koma gida. Don wani hotel suka kama a nan kusa da asibitin mazansu da matansu. Yareema ya amince da shawarar Yaa Maira, ya nema musu sallama a washegari. Daga asibitin koyarwa na Maiduguri aka dauko physiotherapist din da za ta dinga kula da Ya Gumsu a gida ana biyanta. Yareema bai samu nutsuwa ba tun saukarsa Abuja, don haka bai kira Fulani Bilkisu ba. Amma ko me yake yi Saadatu na manne cikin ransa. Minti bayan minti, sakan bayan sakan son Saadatu karuwa yake a zuciyarsa. Tamkar nisa da suka yi da juna wani medium ne na linking zuciyoyinsu wuri guda. Haka kuma yake ga Saade, wadda ke can tana fama da kanta, amma kullum hankalinta yana kan mijinta Yareema Sageer. Ko yana cin abinci? Ko yana cikin irin damuwar da ta ke ciki? Ko shi ma Ya Gumsu ta mare shi a kan ta? Tambayoyin da ta ke yawan yi wa kanta ke nan ba ta da mai amsa mata. Domin Fulani ta lafiyarta ta ke ba ta mata zancen Yarima sam-sam. Sun dukufa ita da Fanna wajen kula da ita da dafa mata duk abin da suka san za ta iya ci ko da loma daya za ta yi masa. Dr. Zainab ma na kokari a kanta matuka, ta taimaka aman ya tsaya, amma kullum cikin tashin zuciya ta ke, don haka Fanna ta samo mata goro tana taunawa. Ta rame ta yi duhu, da ganinta za ka san a satin nan ta yi jinya ta sosai. Tana kwance a dakinta suna labari da Zarah Fulani ta shigo ta same su. Ta ce, Saade su Yareema sun dawo fa, an sallamo Ya Gumsu, don haka ki daure, ki kwarara jikinki yanzun nan ki je ki duba ta, ko da kuwa ba za ta amsa ba. Saadatu ta fiddo ido cikin razana, Fulani ta lumshe mata ido tare da girgiza mata kai, ta ce, Do as I said, sai Fanna ta raka ki. A sanyaye ta mike ta soma daura laffaya a jikinta. Fanna ce ta yi mata jagora suka tafi unguwar Ya Gumsu. Wata kuyangarta ta shiga ta yi musu iso, sannan ta fito ta shiga da su har tankareren falon da Ya Gumsu ta ke kwance. Gabadaya yayanta maza da mata suna zaune a falon tun daga kan Yaa Maira har zuwa auta Ahmad. Yareema Sageer na zaune a gefen Ya Maira daga kan tattausan kilishi, ya mike santala-santalan kafafunsa da waya a hannunsa yana latsawa. Sanye yake da alkyabba ruwan zuma wadda ta sha aiki da zare ruwan gwal. Duk hirarrakin da suke yi ba ya sanya musu baki domin gabadaya hankalinsa yana ga son ganin Saadatu, da sabon matsayin da zai kalle ta da shi na mother of his children. Lokacin da wata baiwa ta shigo ta isar da sakon cewa ga matar Yarima nan za ta shigo duba Ya Gumsu ko kadan bai ji su ba. Text messages yake rubutawa yana aikawa wayar Saade mai dauke da alkawurruka na soyayya da kauna masu wuyar samuwa daga bakin mazan aure a wannan zamanin. Duk da ya san cewa ba ta tare da wayar tata ta baro ta Abuja. Kamar cikin mafarki, kamar daga sama ya tsinkayi sassanyar muryar Saaden na sallama a falon. Ya riga kowa dagowa a rikice, a mamakance, sannan excitedly yake dubanta. Da shi ta fara hada ido, ta yi saurin sunkuyar da kanta. Idanuwan yayye da kannen Yareema suka yi mata caaa wanda hakan ya sa kafafunta hardewa kamar za ta fadi. Kafin Fanna ta riko ta Yareema ya riga ta. Babu wanda ya ga sanda ya mike cikin zafin nama ya taro Saade, ya ruko ta har gaban Ya Gumsu, ya zaunar da ita daidai kafafunta yana fadin, Ya Gumsu ga Saadatu ta zo duba ki!. Kunya a wurin Saade kamar ta ce kasar ta tsage ta shige. Amma da yake dukkaninsu wayayyu ne ko a jikinsu, murmushin kauna suke mata dukkansu. Yaa Maira ta ce, Barta ta zo nan kusa da ni ta zauna Yarima, dawo nan gefe na Saadatu. Cikin jin nauyi ta zame daga hannun Yarima ta tsugunna har kasa ta ce, Ya Gumsu sannu da jiki, Allah ya kara afuwa. Ya Gumsu ta daga mata kai alamar ta amsa, sannan ta rike hannunta cikin nata. Tana ta motsin maganarta wanda da alama so ta ke ta bai wa Saade hakuri. Saade ta girgiza mata kai tana hawaye, Allah ya ba ki lafiya Ya Gumsu, da yardar Allah za ki fadi duk abin da ki ke son fada. Mun yi laifi a yafe mana. Sai kuka, Yaa Maira ta zo ta kamata ta tayar da ita daga gaban Ya Gumsu, ta ja ta suka zauna tare, ta ce, Ba ki mata laifin komai ba Saadatu kin ji, kuma ta yafe muku duniya da lahira, Allah ya yi muku albarka. Kowannensu da kalar kulawar da yake nuna mata a falon, duk suka yi mata sannu da jiki. Awaisu ya yi sallama ya shigo, ya duba Ya Gumsu da jiki sannan ya dubi Yareema da ke gefe kusa da Yaa Maira yana hagunta Saade na damanta (babbar Ya, UWA). Tana ta tsokanar su; Princess Saa Allah ya sa ki haifo min mai kama da ni ba mai irin hancin Yareema ba (pointed noise), kin san in hanci ya cika tsayi muni yake komawa. Ahmad ya ce, Kai Yaa Maira! A dinga yi ana tsoron Allah, ko makaho ya shafa ya san Yaya Yareema ya fi ki kyau nesa ba kusa ba. Awaisu ya katse hirar tasu da cewa, Yareema bakinka na Neitherland sun iso airport din Maiduguri, zan je in taho da su. Gidanka zan sauke su ko guest house din Maimartaba? Yareema ya harare shi, ya ce, Awaisu! Kana shiga lokacina fa, this is family time, ka je ka ji da customers dinka kai kadai. Duk inda ka ga ya dace, ka kai su. Family ba za su ji dadi ba sai da kudi. A nemi kudi a bai wa family Malam, ina zan sauke su? Gabadaya aka yi dariya ban da Yareema da Saade wadda ke satar kallon Yareema ta kasan idonta, tana mai alhinin muguwar ramar da ya yi cikin sati guda kacal. Duk da haka kyawunsa da kwarjininsa suna nan, sai ma abin da ya karu. Sai lokacin Awaisu ya lura da Saade a falon tana daga gefen Yaa Maira, ya ce, Aah! Madame, are you here? Dole idanun Yareema su rufe, ga masoyiya a kusa me zaa yi da kudi? Don Allah ki yi masa magana ya gaya min inda zan kai bakin turawanshi. Saade ta yi dan murmushi ba ta ce komai ba, sai ma kara kasa da ta yi da kanta, gabadaya ta takura domin duk motsin da ta yi sai ta ji kaifafan idanun Yareema a kanta. Maganar Turawa da Awaisu ya yi ita ta sa Yaa Maira tunawa da Aisha-Sultana. Da sauri ta ce, Yareema, ina Sultana? Ban ganta ta zo duba Ya Gumsu a Abuja ba? Ai kuwa duk suka tattaro hankalinsu a kanshi, sai yanzu duk suka tuna ba su ganta din ba, including Saade ta dau ido ta dora masa, ita dai ta san sun yi tafiya tare, kuma ya dawo shi kadai bai kara yin zancenta ba. Yareema ya dubi Yayar sa Yaa Maira sannan sauran kannensa maza da mata, sannan matar sa Saadatu da aminin sa Awaisu, ya ce, Dukkanku ba bare a nan. Ba wanda zan boye wa sirrin gidana, muddin wanda ya dace ku ji ne. Aisha-Sultana (Rose) mun rabu. Na maida ita kasarsu. Gabadaya suka sa salati domin babban zunubi ne saki a masarautar, tun daga iyaye da kakanni. A kan wane dalili? Askirama ya sani? In ji Yaa Maira. Yareema ya yi ajiyar zuciya, calmly ya shiga ba su labarin halin da yake ciki da Sultana tun komawarsu Abuja da ta sarki shan giya ta kuma cire mahaifa ba da izininsa ba. Ya ce, Na yi ta hakuri ne da shan giyarta saboda nobody is perfect. Dukkanmu masu sabo ne in one way or the other. Sabida ni ma kaina din Im not perfect either. Amma sallah fa? Ba zan iya jure rayuwar aure da wadda ba ta sallah ba, sabida yayana da lahira ta. Ya ci gaba da gaya musu yadda Askirama da kansa ya zo har gidansu ya same ta drunkard, ya ce, bai ce in sake ta ba, amma bacin ran da na gani cikin idanunsa da gaisuwata da ya daina amsawa ya sa na ga duk son da nake mata gara in hakura da ita. (Ya boye musu abu guda daya, cewa ba zai iya adalci tsakanin kowacce mace da Saadatu ba, don ya sirranta soyayyar da yake wa matarsa ga yan uwansa, wanda hakan shi ya kamata ga duk namijin da ya san ciwon kansa). Yaa Maira ta fahimce shi, amma sai ta ce, Wani hanzari ba gudu ba, Sultana ba ta ce ta yi RIDDA ba, sakin da ka yi mata saboda shan giyarta zai sa ta kullaci musulmi, ta ga cewa, tukuicin soyayyarta gare ka kenan, ta baro kowa nata da addininta ta biyo ka a karshe ga abin da ka saka mata da shi. Ban sake ta saboda giya kadai ba. Na gaya miki ta karbi musulunci, amma ba ta sallah, mene ne marabarta da addininta na baya? Addinin ma da babu shi sam domin kuwa ba kirista ba ce, bayahudiyya ce (Jew). To cut it short, na yi nadamar aurenta tun farko, ban taba zaton Alanguburo zai amince ba, amma tashi guda ina fada bai turza ba, sai ya amince. Had I know akwai Saade, kamar yadda ya ce tun farko ita ya so na aura ba zan taba yin wani aure ba. Saade ba ta san lokacin da ta mike ta yi kofar fita ba, inda ta baro Fanna, kunya kamar ta yi ya ya. Tana ji Yaa Maira na fadin, Ka kore ta ka ji dadi. Saadatu dawo kin ji, yanzu zan sa Awaisu ya tattara shi su tai su ba mu wuri. Ina! Saade ta kai kofa. Cewa ta ke, Yaa Maira zan dawo ne, idan na kara jin sauki. Yareema ya daga murya yadda za ta jiyo shi ya ce, In zo zance anjima bayan isha? Ai saade kadan ya rage ta zura da gudu, suka dinga yi mata dariya. Tana komawa unguwar su ta tadda Fulani ta dafa mata lafiyayyen faten acca da ya ji ganyen alayyahu da kabewa, ta zuba a faranti tana firfitawa da kanta tana jiran shigowarsu. Tana shigowa ta nufe ta da sauri. Allah Sarki UWA! Saade ta fada a ranta, ta karbi cokali tana shan faten Fulani na tambayarta jikin Ya Gumsu, ta ce, ita ma tana jira Askirama ya shigo gida ne su shiga tare su dubo ta. Saade ta tambayi Fulani, Ya ya aka kare ne da zancen auren Hanne? Ta ce, An kai zancen kotun musulunci an yi mata gaiba, mun rabu a kan cikin watannin in ta gama iddah za ta dawo nan gabana, yaron a kai wa iyayen mijin. Plan dina akan ta shi ne a kai ta El-Kanemi, ta samu kwalin kammala sakandire sai a sama mata UNIMAID. Ta zauna hostel in sun yi hutu ta zo nan wajena ta yi hutun, har Allah ya ba ta mijin aure. Saade ta gode wa Fulani, godiya maras adadi, tsarin da ta yi a kan rayuwar Hanne ya yi mata. Ta ce, Su Raheema ko waya? Ta ce, Kusan kullum muna magana da Maman, Raheema ta koma makaranta (university of Heartfordshire) wannan watan za ta kammala daga nan ku sha biki. Zan tambayi Maman lambarta na UK tunda yanzu akwai waya a hannunki. Ta kyabe baki ta ce, Ni da na ji zafin maruka ina na tuna da wata waya? (Tana nufin marin da su Ya Gumsu suka yi mata). Fulani ta ce, Mari? Nan ta gaya mata duk yadda aka yi, amma ba ta manta rokon da Yareema ya yi mata ba na ta boye zancen Dr. Ziyad ga iyayen su, it will create a serious problem idan suka ji, tunda dai mun bar NTNU din gabadaya shi ke nan. In ji yareema Sageer. Sai dai tana tantama idan hukuncin da Yareema ya yanke musu is geniune, da gaske Abuja ta fice mata a ka, shi ma kuma Yareema haka, Dr. Ziyad yayi shattering zuciyar sa into pieces ya karya masa zuciya, ita kuma ya jefa tsoron rayuwar Abuja mai tsanani a tata zuciyar. To amma makomar karatunta ta ke hangowa, shekaru ukun da ta kwashe cikin wahala da fadi-tashi sun tashi a banza ke nan? Above all aka ce sabo turken wawa. Ta saba da NTNU. Babu wata jamia da za ta bi bayan Nigerian Turkish Nile University a wurinta. Fulani da ta ji duk abin da ya faru tsakanin Saade da su Ya Gumsu, sai ta jinjina kudirar Ubangiji. Ya Gumsu mai ja da ikon Allah dare daya yau gata ta zama sai dai a kwantar a tayar. Shin wannan bai ishi dan Adam ishara ba ya yarda cewa shi ba a bakin komai yake ba? Duk mulkinsa da izzarsa bai wuce talalar Ubangiji ba a duk lokacin da ya so? Bai isa ya sa, bai sa ya hana abinda Ubangiji ya hukunta ba? Matar nan ta jima tana cutar da ita, da harshenta, da bakin ta, da hannunta, da komai nata. Don ma dai kowa ya tabbatar cewa ba ta yin asiri ta tabbata da in akwai abin da ya fi shi sai ya Gumsu ta yi mata. Wannan sai Hibbani, shi ya sa ita din ba ta wasa da addua da tsayuwa gaban Sarki Allah a tsakiyar kowanne talatainin dare. Ta nisa ta dubi yarta Saade, ta ce, Saadatu marriage is not a bed of roses. Babu wani aure da ba shi da kalubale, ki sa a ranki Gumsu ita ce kalubalen aurenki, kuma ga yadda abubuwa ke tafiya na fahimci tsoron Allah ya kama ta. Ki cire ta a ran ki ki yi wa mijinki mai sonki biyayyah, komai za ta yi miki ta yi kadan ta raba wannan auren tunda har ga zuria a tsakani. So ni da Ya Gumsu yanzu mun zama JINI DAYA. Kun riga kun yi tiding wannan barakar da ke a tsakani. Ni kuma ko me ta yi mun a baya na yafe mata. Allah ni ma ya yafe mini, ina kuma rokonsa ya ba ta lafiya ta koma taka kafafunta a doron kasa. Kuma tunda kin warware ki soma shirin komawa dakinki tun kafin Yareema ya zubar da kawaici da kunyar da ke tsakanina da shi. Dazu ya roke ni Fanna ta raka ki dakinsa na gidan nan yana son gaisawa da babynsa tunda Askirama ya hana shi shigowa nan. Ni kuma bazan yi abunda in Askirama ya ji zai yi fushi da ni ba. Tunda har ya cire kunya ya fadi gaisawa da baby kin ga daga hakan wata rana abin da zai gaya min sai ya fi haka. Saade ta soma tirjiya, har da buga kafa na shagwababbun yaya, Ni wallahi ba yanzu zan koma ba, abin da jinyar Ya Gumsu suke yi? Ko na koma ba shi da lokacina. Fulani ta ce, Duk inda yake in dare ya yi ai zai dawo gidansa ne Saadatu. Dare mahutar bawa, don haka na gaya miki ki soma shiri, ba za ki kara kwana uku a sassan nan ba. Yau din nan zan bai ma Askirama baki, har ga Allah Yareema tausayi yake bani don ba shi da laifi. Saade har da hawayenta ita ba za ta koma yanzu ba sai Ya Gumsu ta warke. Warkewar da babu wanda ya san ranarta sai Allah? In ji Fulani cikin lallashi. Kamar yadda ta alkawarta da yake yau ita ke da Mai Askira, tare suka je suka duba Ya Gumsu. Da lokacin kwanciyarsu ya yi ta yi ta ba shi hakuri kan ya sassauta wa Yareema, cikin alamarin nan ba ta ga laifinsa ba, tunda shi bai ma san Ya Gumsu za ta je Abuja ba, kuma sanda ta je din Saadatu ta tabbatar mata shi ba ya gidan, sannan abin da ya faru da Ya Gumsu kadai ishara ce babba, Allah ya nuna musu su dukkansu a daina jayayya, a bar wa Allah ikonsa. Zuciyar Maimartaba ta tausasa, shi ya sa yake son Bilkisu amma matansa sai su ce wai kyawunta ne. Me ake da kyau in ba hali? Ai ga Hibbani nan kyau har kyau, amma ban da gulma, tsugudidi da daukar zance ba ta iya komai ba. Ya ce ya yarda a je a gyara musu gidansu kafin su koma. Ya kuma kira Yareema don ya ji yaushe za su koma Abuja. Yareema bai boye ba, ya ce da Askirama ya ajiye aikinsa da NTNU, wani zai nema. Cikin mamaki Mai Askira ya ce, A kan me? Yareema ya runtse ido, tuno cewa Ziyad ya ga tsiraicin Saade kadai yana kona zuciyarsa yana tafasa ta ba dan kadan ba. Ya ce, Allah ya kara maka yawan rai a taya mu addua Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare mu bakidaya. Zan yi mata transfer zuwa babban reshen jamiar tasu da ke Ankara (capital of Turkey) ta karasa shekara biyunta. Ni ma zan yi wasuprojects (applied research) da jamiar na tsawon shekara daya. In mun gama sai mu dawo Askira da zama gabadaya, bazan kumazama a garin da ba Askira ba, ina so in bude jamia tawa ta kaina (private university) tunda ni da ita duka fanni daya muke karanta sai mu hadu mu tafiyar da jamiar. Kafin in samu lasisin budewar (licence) shi ne abu mai wahala,domin a nan Askira nake so in bude jamiar ba a maraya ba. Askirama mutum ne mai ilmi kuma wayayye, sosai ya fahimce shi, yana alfahari da haihuwarsa a kullum. Da daya ne tamkar da goma wanda yake barranta kansa da sarauta when it comes to neman ilmi, duk ya fi yan uwansa maza talent da jajircewa a kan harkar ilmi. Ya yi addua ya sa musu albarka, ya ce, gobe insha Allah za su je Abuja su mika neman visa da neman tranfer din shi da Saade, in sun gama komai zuwa sati daya za su tashi zuwa Turkiya daga Abuja ba za su dawo Askira ba sai bayan shekara daya. Askirama ya ce bai yarda ba, idan watan haihuwa ya kama wa zai kula da ita? Yareema ya yi alkawarin zai kula da Saadatu kamar yadda zai kula da kansa. In watan haihuwar ya kama zai daukar mata Fanna, in kuma ta kammala karatun kafin nan tunda semester biyu ne kawai zai dawo da ita ta haihu a gabansu. All he need is to be isolated shi da Saadatunsa. Shi kadai ya san irin ragaitar da ya shiga a wadannan kwanakin da suka yi nesa da juna. Ba ya son hayaniyar gidan Sarauta ko kadan. Da kyar Maimartaba ya amince da wannan tsarin na Yareema, amma yana adduar ta gama karatun kafin watan haihuwar ta ya tsaya ta zo ta haihu a gaban su. Yana da jikoki kusan guda 20 amma na Yarima isspecial domin babu kamar sa cikin duka jikokin da zai haifa ko ya haifa a baya. Yana masa adduarsamun nasara akan duk abinda ya sa gaba kuma ya gama rubuce-rubucen da zai je ya yi na tsawon shekara guda a ANKARA UNIVERSITY wanda zai bashi damar hawa Professorial Chair. ***** Kin faya nawa, kin faya yanga Saade, don kin ga Askirama na biye miki, shin sau nawa zan aiko Fanna ta gaya miki Yareema na cikin mota tun dazu yana jiran ki zaku wuce ne? Duk wani shiri da za ki yi meyasa tun jiya baki yi shi ba? Saade ta cuno baki hadi da marairaice murya Fulani gashi na fa nake gyarawa kawai, ya ce baya son ganin sa a cukurkude, nikuma bana so kowa ya taba min kai, shine nake tajewa da kaina. Fulani ta karbi katon matajin dake hannun ta tace bari ni in taje miki, in ba haka ba zaki yi awa guda kina abu daya. Ta taje mata, ta tufke mata shi da murtukekiyar kalbaa tsakiyar ka. Ta kawo katon hair-bound kalar kayan jikin ta wato sky-blue ta zagaye mata shi. Fuskar Saade ta fito tsam, tayi cute da ita. Fulani ta taimaka mata ta nannada laffayar. Sannan suka fito. Ko kusa bata gaya mata kasar zasu bari ba don ta san halin shagwabar Saade da rigimar ta, cewa zata yi bazata iya shekara babu Fulani ba. Sun bata lokaci suna sallama, kamar kada su rabu,finally suka rabun. Saade na kwallah Zarah na kukan sai ta bi ta, da kyar Fulani ta rarrasheta da cewa asibiti zata je ta dawo, kafin Fanna ta raka ta wajen Ya Gumsu. An jinginar ta jikin pillow bakin da ya karkace ya sha gashi ya koma daidai. Amma har yanzu bata motsa daya hannun yadda ya kamata amma kana iya gane abinda take cewa. Sauki dai yana ta samuwa cikin yardar Ubangiji da kulawar yayan ta. Idan Allah ya baka yaya masu jin kan ka ya baka komai na duniya. Kishiyoyin ta ma baa bar su a baya ba wajen nuna kulawar su akan iftilain da ya same ta. Ya Gumsu na ganin shigowar su ita da Fanna ta mika mata hannun ta mai lafiya, da sauri Saade ta karasa ta zube gaban Ya Gumsu. Hannu ya Gumsu ta dora a kanta tana shi mata albarka tare da cewa cikin harshen barbarci. Wa gafurne kla awodune nyiro dikkuna samma so ro, Nadimtikna.(Ki yafe min na yi nadama a akan duka abinda na aikata, na yi nadama). Saade tace baki yimin komai ba sai alkhairi Ya Gumsu, Allah ya baki lafiya. Ta mika hannun ta mai lafiya kasan filon ta ta dauko warwaron zinare guda uku ta zura a hannun Saadatu. Saade ta rike hannun Ya Gumsu tana godiya. Daga nan Fanna ta rakata unguwar Yaa Kirjiloma da unguwar Yaa Hibbani duk tayi musu sallama, kowacce da dan abin arzikin ta na sallama don tun faduwar Ya Gumsu jikin kowacce yayi lakwas, musamman Hibbani ta rage daukan zancen kowa ta kaiwa Askirama. Impatientlykuma admiringlyYareema Sageer ya dubi Saadeda hanzari, lokacin da aka bude mata motar da yake ciki mai duhun glassai ta yadda baka iya hango wanda ke ciki. Zaquwar son ganin ta na tsayin wannan lokacin da ya dauka ba tare da ita ba yasa ya hadiye fushin sa na jiran data bar shi yana yi a mota. Data shigo ma aka rufe kofar motar jikin kofa ta koma ta makure ta juya masa keya. Da ta san yadda zuciyar sa ke racing a cikin kirjin sa sabida excitement din ganin ta finally by his side da bata juya masa keyarnan ba. Yarima ya girgiza kai yace ki yi lokacin ki ne Maman Chiroma, ko ba haka Askirama yace sunan Baby ba? Ba ta san ya san da wannan maganar ba don haka ba shiri ta sunne kanta cikin cinyoyintadireba na barin kofar masarautar sai taji sanyin hannun Yarima a gadon bayanta a janyo ta sosai barin jikin sa sannan hannun sa ya kurda kasan marar ta yana shafawa cikin a hankali, ya sunkuyo daidai saitin cikin nata yace. Stay blessed Chiroma. A ranta tace shin in kuma ya mace ta haifa fa? Yarima da Baban sa zasu yi farin ciki? Yadda Mai askira da Yarima suke ta ambaton haihuwar da namiji? Zata so ta yi wa Yarima wannan tambayar, amma jin nauyi bazai bar ta ba. Kamar ta yi azarbabi in tayi maganar nan tun yanzu amma curiousity na cewa ta daure ta tambayi Yarima tun yanzu. A dan zamanta gidan sarautar ta fahimci burin kowacce mace a gidan shine ta haifi da namiji har murna suke da Fulani Bilkisu ta haifi Zarah. Kuma a karan kanta gani take Askirama bai damu da Zarah ba kamar sauran yayan sa. Bata ji yana fadin a kawo ta fada ba. A ganin taHaihuwar dai ta janyewa Fulani Bilkisu gorin rashin haihuwa ne kawai a gidan amma da ita da babu sammakal. Direba ya ja mota suka dauki hanyar Abuja. Inda zasu yi visa su tashi zuwa Ankara. Basu tsaya ba sai lokacin sallahr Azahar a gidan mai. A motar ma Yarima bai bar ta sakat ba da nauikan soyayyar sa mai tsayawa a zuci wato (sumba). Ta amince shi din expert ne a wannan fannin, ta yarda yayi missing din ta fiye da yadda zai iya bayyanawa, ta ga hakan cikin emotions dinsa da rawar da jikin sa ke yi a kan ta, tun da shi mai karancin magana ne sai dai actions da shaukin dake cikin zuciyar sa su fadi halin da yake ciki. Sai dare suka shiga Abuja, kuma ba gidan su suka nufa ba kai tsaye hotel din (Fraser Suites)Yarima ya baiwa direban umarnin shiga. Tuni ya sa an kwashe komai na su daga gidan malamai na NTNU dama gidan mallakar jamiar ne. Suna shiga dakin da suka kama Yarima ya maida kofar ya yi azamar rungume Saadeverytightly, this seems like eternity! Ya Allah! Na roke ka, kada ka hora laifuka na ta hanyar nesanta ni da abinda na fi son kasancewa da shi a rayuwata. I missed you Saadatu!. Ta kara narkewa a jikin Yarima sai yanzu ta san itama tayi kewar wannan kulawar ta Yareema Sageer, zaman ta tare da jamaa ne yasa bata gane hakan ba, ajiyar zuciya take saukewa a jejjere, tace Prince, ina cikin damuwa, an ce ina da ciki, kuma na ji kuna ta kiran sa Chiroma tun ban haifa an ga me na haifa ba.. Ina cikin damuwar idan mace kuma na haifa fa? Wata zaka auro ta haifa maka namiji? Ko kuwa ita din bazaka so ta ba tunda bazata yi sarauta ba? Yadda ta karasa maganar cikin karaya sai da ta sanya Yarima Sageer dariya. Ya dago fuskarta bisa tafukan sa. Ya ce Saadatu in kin so ki jero min dozen na yaya mata, ki gani in zan so su ko ba zan so su ba, ki gani in zan kara auren wata matar don ta haifo min namiji. Namiji baya alkawari akan aure musamman Basarake wanda ya gaji aure-aure amma ni Sageer! A yau ina mai tabbatar miki da cewa idan harba kaddara ce ta bi raayin kan ta ta aura min wata ba, na gama aure a rayuwa ta. Abin da baki sa ni ba niSageer shaanin sarauta ba ya gaba na, Maimartaba na so in haifi namiji ne don ya tabbatar ba zan yarda in karbi sarauta ba. Amma ba don in kin haifi mace ba zamu so ta ba, ko hakan ne zai sa a kara yi min aure. Mun dade da gane illar hakan cikin gidan mu wato fifita haihuwar maza akan ta mata don haka in kina tunanin hakan, to ki dai na. Ajiyar zuciya Saade ta yi, a kalla yanzu ta samu peace of mind don ta san Yarima ba ya fadin abinda ba haka yake a zuciyar shi ba. Daga nanwanka su kayi kasancewar sun yi duka sallolin su a hanya. Suna idarwa ya yi musu odar abinci mai rai da motsi, amma kallo daya Saade ta yi wa abincin tace bazata ci ba, dan wake take so mai manja da yaji. Dan wake Saadatu? Yarima ya fada cikin damuwa. To yanzu ina zamu nemo shi a daren nan? Ta yarfarda kai ta ce mu je mu zazzzaga na san bazaa rasa mai dan wake ba. A take Yarima ya mike ya dau mukullin mota, Bukari ya kwanta yanzu (direban da ya kawo su) mu je mu nema. Ko dama so take ta fita din ta shaki freshair, ta gan ta Yariman Askira na tuka ta a mota da kan sa, wannan priviliged yana sanyata nishadi, shiyasa ta kakalo dan wake, in tace haka kawai su fita cewa zai yi ya gaji kuma dare yayi, yanzu kuwa ko don dan sa ya samu abinda yake son ci ta san ba shi da zabi banda su fita din. Shiga wannan titi fita wancan suna tafe suna hira har ya samo mata danwaken a wani karamin eatry. Basu dawo ba sai 11 na dare, tun daga bakin kofa Saade ta soma tausayin kanta, domin Yarima bai yi duka wannan wahalar neman danwaken ba sai da ya fanshe ta. A hakan ma yana tausayin ta sabida cikin jikin ta amma ta biya duka basussukan sa da ta ci tun kafin barin ta Abuja zuwa yau da kyakkyawan reward. Washegari suka nufi Turkish Embassy suka shigar da neman visa. A kwanaki bakwai da suka yi suna jiran fitowar visar su ta tafiya Ankara sai suka zama kamar renakun honeymoon cikin hotel din Fraser Suites. Abin ki da mace mai yaron ciki, komai na jikin ta ya canza, don haka mannewar da Yarima yake mata har tsoro yake bata tamkar bai taba aure ko kusantar mata a rayuwar sa ba. Auren sunnah daban yake, kuma macen alfarma daban Allah ke halittawa mijin ta ita. Shikansa ji yake kuruciyar sa na karuwa, lafiya da kuzari na kara shigar shi. Auren kananan yara ga maiyawan shekaru yana da wannan advantage din. Yayi amfani da zaman hotel din ya nema mata transfer ta yanar gizo daga NTNU zuwa ANKARA UNIVERSITY. A ranar da visar su ta fito transferdin Saade ma ya samu. Washegari suka bi Turkish Airlines zuwa kasar Turkiya. Duk wasu memories na zaman ta a kauyen Tsanyawa tare da Baban ta, zuwan ta Askira wajen mahaifiyar ta, zuwa Abuja zaman gidan Dr. Sageer da yayi sanadin auren ta da Yarima Sageer din,ta kasa manta ko daya. Ta yi musu kundi (littafi na musamman). Wato shi bawa tun haihuwar sa an rubuta masa dukkan kaddarorin sa. A hankali zaici karo da kowanne.Ta debo duka memories dinta taho dasu Ankara cikin kundin adana tarihin ta. Kuma bata san shirin Yarima ba sai bayan saukar su a babbanfilin jirgin saman birnin Istanbul wato HavalimanıİşletmesiA.Ş. Istanbul Airport.Cewa ita da gida sai ta gama karatun digirin ta, ko ta haihu ko kafin ta haihu. Zai aika a dauko mata Fanna. A lokacin da Yarima ya gaya mata hakan a filin jirgin ne suna tafiya zuwa terminal, hannayen su sarke cikin na juna. To ko taji damuwa ba kamar yadda ya zata ba, sabida a halin yanzu shakuwar da suka kara yi a dan tsukin ta zarce ta baya, a dan takaitaccenzaman su na kwanaki bakwai a Hotel dinFraser Suites, a halin yanzu tafi son kasancewa da shi har fiye da kowa a rayuwar ta. Daga Istanbul suka bi jirgin kasa (Turkish Railways) daga Halkali wanda zai kai su zuwa Ankara (capital of Turkey). ****** ANKARA Basu bar Ankara ba sai da Saade ta shiga watan haihuwar ta bayan bikin yaye su (convocation) na kammala digiri akan (Pure&Applied Chemistry) inda Saadatu Hashim Askira ta fiddo kwalin ta mai daraja ta farko. In aka duba kuma da idon basira duka nasarar karatun Saade sai ace hobbasar Yarima Sageer ne, miji mai cin tudu ukku a rayuwar Saade; malami kuma masoyi, ta wani fannin Yayan da bata da shi, kuma wanda babu kamar sa a rayuwar ta. Alkawarin da ya daukar wa Mai Askira ya cika shi, ya rike Saade da dukkan amana, ya rike ta da dukkan kauna da soyayya haka ya zama mijin marainiya. Ya gama appliedresearches din da ya je yi, yayi nasarar rubuta littafai muhimmai akan fannin sa. Wadanda suka bashi damar zama Farfesa, domin bayan dawowar su Askira da dan lokaci kalilan ya kama aiki da jamiar Maiduguri (UNIMAID) wannan ne dalilin komawar rayuwar su garin su Askira bakidaya, ko ya je Maiduguri baya wuce kwanaki biyu ko uku zai shigo Askira. Har gobe yana nan akan burin sa na kafa privateuniversity a garin Askira kuma yana cigaba da fafatukar hakan. Saade da ta tashi haihuwa sai ga kyautar Allah ta yaya mata har guda biyu. Wadanda suka ci sunan Ya Gumsu da Fulani Bilkisu. Soyayya ta karshe yan biyu (amaren Askirama) yadda ake kiran su cikin gidan sun gan ta wajen Mai Askira. Dr. Sagir kuwamaida Sahlah da Suhailah ciki ne kawai ba ya yi sabida soyayya. Ya Gumsu ta dade da samun lafiya kuma tuni ta kama girman ta ta kuma daina adawa da Fulani Bilkisu. Ta yarda da duk abinda Askirama ke fada a kan ta. Sun hada kai sun samarwa Mai Askira madauwamin kwanciyar hankali a shekarun tsufan sa. Yayin da Sahlah da Suhailah suka zamo masu debe masa kewa don kullum sai ya fita da su fada ya ajiye a hagu da daman sasuna kiriniyar su yana gudanar da alamuran mulkin sa. Ko kusa babu wanda ya yi mummunan furuci akan haihuwar yaya mata da Saade tayi a masarautar bakidaya, sabida yara ne masu shiga rai, da ko baka yi niyyar daukar su ba sai sun ja hankalin ka ka dauke su. Jinin BAGGARA ne dana BABARBARE ya hadu ya bada wadannan twins masu tsananin kyau da shiga zuci. In har ba UNIMAID zai tafi ba zaka same shi tare da yan biyun sa a cinyar sa ko a gefen sa ko a hannun sa. Prof. Sageer Yusuf Askira. ****** MURFI Nakuda take tamkar bazata tashi ba, nakuda ce da ko haihuwar yan biyu bata yi mai zafin ta ba. Ta riga ta fidda rai da rayuwa, tana kwance ne a cinyoyin Yarima Sageer ta hada gumi kashirban, gashin kanta ya watsu bisa jikin sa. Idan na taba cutar da kai a tsayin zaman mu ka yafe min Baban Suhailah, ta fanni na baka yi min komai ba sai alheri da soyayya Yaya Yareema. Idan na mutu,kada ka kara aure zan yi ta jiran ka aljannah har ka iso, ka ji? Ka cewa Fulani ta yafe min its not easy being a mother! Na kara daraja ta fiye da baya, na kara son ta fiye da wanda nake mata, na kara ganin kimar ta da martabar ta.. na so in yi tsawon rai in biya mata Hajji Allah bai yi ba.. Sai ga wani uban nishi ya biyo baya, Sageer ya dauka tafiyar kenan! Sabida haka numfashin sa ya soma kokarin barin kirjin saamma sai me? Kafin ya bude ido sai ya ji nurse Aisha na cewa cikin farin ciki. HERE COMES OUR PRINCE! Sai kuma baby data taro ya callara kuka wanda ba kwanyar Yarima kadai ya shiga ba har da ta unconscious Saade, kuma kukan ne ya maido ta a hayyacin ta. Nurse Aisha ta nade jaririn a tawul bayan ta goge masa jiki daman zaitun (olive oil) ta zo ta dora shi a ruwan cikin Saade wadda ke kwance kane-kane a jikin Yarima tana mai kallon komai kamar cikin mafarki. Yau itace da haihuwar namijin finally. Bayan ta fidda rai, domin kuwa bayan Twins sai da ta kara wasu setin twins din again duka mata, wadanda suka ci suna Rahimah da Hannatu. Sai yau haihuwa ta uku taji ana kiran Prince. A hankali ta lumshe idon ta da wahala tasa duk suka zurma ciki suka kankance, ta bude su akan kaykkyawan Babyn ta wanda bata ga fuskar kowa a kan fuskar sa ba sai Ahmad autan su Yarima, wato dai daYa Gumsu yake kama. Hakika La taqnadou min rahmatullah. Allah yana jinkirta maka abunda kake so zuwa lokacin da ya ga yafidacewa ya baka, abin so shine ka kasance cikin yin tagociya a adduaarka, wato idan kaza alkhairi ne a gare ni Allah ka bani, idan ba alkhairi bane Allah ka musanya min da mafi alkhairin sa. Not Allah ka bani kaza anyhow. Yarimah ya dauki babyn yana kallowith affection sannan ya lakuce masa hanci. kai Chiroma shine ka wahalar min da mata ko? Kasa har ta fara bada wasiyyar hana ni aure idan ta zarce? Daidai lokacin da Askirama da Fulani da Ya Gumsu suka shigo fuskar su fal fara don tuni albishir din isowar Chiroma ya je musu. Nan nurse Aisha take basu labarin wasiyyar Saade ga Fulani da Yareema. Suka ce me zasu yi ba dariya ba. Fulani ta ce yanzu ma bata baci ba a bani kujerar makkah na in je in yi azumi acan ni da takwarata, ban daukar takwarar Ya Gumsu tunda bata zuwa kwana waje na. Askirama yace to kai an ce kada ka kara aure ka jira sai an hade a aljannah, nikuwa da har na shirya maka kwarkwarori uku tunda Saadatu jego zata fara. Yaa Gumsu tace lala-lala Askirama in wasa nea bari, kaima ka haramtawa kan ka naka, a na me shi zaa takura shi a kai Alanguburo? Cewa yayi bai iya jiran matar sa ta gama biki? Kunya ta lullube Saade amma ta ji dadin yadda Ya Gumsu ta dage ta hana a baiwa Yarima concubones, ta san da watakila shikenan ta bar shakar numfashi daidai a duniyar subhanah.yammata hudu rus! Ga Yarima Sageer? Ai karshen ta a barrow zaa kwasheta zuwa asibitin masu dan karamin tabin hankali. Shima Askirama jin baki ne irin nasa, don ya san ba abinda Yarima ya ki jini irin ace ya kara aure. Da an fadi hakan zai jawo ayar Allah ya ce sai zaku iya adalci, shikuma bai iya adalcin tsakanin Saadatu da wata diya mace, da muguwar rawa gwamma kin tashi. Shiyasa Askirama yake so ya dauki kwarkwarori duk adadin da yake so, amma wani zubin har zuciyar sa yana ganin Yarima ya hada da concubines zai kara fiddo da kimar sarautar sa. A yanzu dai Yareema Sageer ya ce baya da bukata bai sani ba dai ko can gaba in ya fara tsufa. Baby ya ci sunan Askirama YUSUF. Ana kiran sa Chiroma. Tsakanin Mai Askira daYa Gumsu ban san wa ya fi son jikokin nan ba. Ya Gumsu kullum ta dubi yaran sai ta kara nadama ta yi dana sanin ja da hukuncin Ubangiji, lalle ne ko rabon wadannan yaya biyar ya isa ya kayar da ita kwanan ta bai kare ba. A halin yanzu ta fi kowa alfahari da auren Yarima da Saade ta kuma yardada abinda Askirama ke fadi cewa Saadatu diyar Bilkisu,rufin asiri ce, suttura ce ga dan su Yareema Sageer Yusuf Askira. Masha Allahu laquwwata illa billah. Nan na kawo karshen littafin MASARAUTARMU 3&4. Kurakuran dake ciki ku tayani rokon Allah ya yafe mini. Abin alfanun da ke ciki Allah ya hada mu a ladan nida ku bakidaya. Sumayyah Abdulkadir 18/11|2021. Ina mukualbishirda sabonlittafinamaisuna NA HUCE!Wanda zaizo a matsayingoronsabuwarshekarainsha Allah. TUNA SUNAN SA; NAHUCHE (DagaFushina) NA HUCE.. LITTAFIN SUMAYYAH ABDULKADIR Hawayen da yake ta rikewa ne suka kwace masa, ya juya kadan ya dubi Rahinah wadda ke kallon bayansa a lokacin, suka kuma hada ido, ji ta yi zuciyar ta na son karyewa (rauni irin na diya mace na son mamayar ta) amma ta amince wannan shine decision mai kyau ga rayuwar ta. Sai ta maida idanunta ta lumshe su a hankali. Tana sauke ajiyar zuciya. Shi kuma ya sa kai ya fita daga dakin, babu ko waiwaye. Kamar yadda yake ji a ransa ba zai kara waiwayar RAHINAH OMAR a rayuwarsa ba. Ko da bayan cikar burin ta, na zama cikakkar otorhinolaryngologist. **** Ta dauki hoton karamin kyakkyawan yaron mai kama da ubansa a komai tana kallo with so much adoration, hawaye na sauka a kan fararen kundukukin ta. Ta san yanzu ya girma, watakila aji hudu na firamare? Cikin kowanne hali dai ta san zai kula da shi. Damuwar ta ba a kan kulawar da yaron zai samu ba ne domin hakika tana da tabbacin HABIBUNAHUCHEzai kula da dansa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa. Damuwar ta akan yadda har gobe ta kasa kallon kowanne namiji da idanun sigaraure, kowa ya zo sai ta ga bai kai shi ba, ko farcen kafarsa bai kama ba, ko da kuwaya fi shi komai na rayuwa. Duk da cewa ta san shi ne kawai a matsayin dalibin jami'ar Cologne ba'a matsayinsa na yanzun ba (mamallakin NAHUCHE HOTELS) amma tana bibiye da duk wani fadi-tashinsa na rayuwa tun daga ranar da ya raba ta da Dan su. Dalilin bibiyar ne ba ta sani ba har yau, tunda ita ta ce bata son sa. Farin jini kam har bata san irin nata ba, manema ba irin wadanda Allah bai ba ta ba, kuma burin Dada shine ta yi aure tun kafin Allah ya dau ranta, amma har gobe ta kasa kallon kan sauran maza daga shi sai dan mutanen NAHUCHE. The one that took away her pride na diya mace. Wanda ta tabbatar zuwa yanzu ya manta da ita, a irin shuhurar da Allah ya yi masa cikin shekaru goma kacal da rabuwarsu. Bata san hawaye take ba. Sai da ta ji dandanon gishiri a bakin ta. Hawayen da ta tabbatar ba za ta daina zubar da su ba har zuwa karshen rayuwarta. Idan har rayuwa ba ta koma yadda take a baya ba; with him aside. "Auren Wucin Gadi". "Auren kwanaki bakwai kacal". Wadanda abubuwan da suka wakana cikinsu sun fi tsayin na shekaru bakwai. Wanda ya samar da kaddarar Dan da ke a tsakani, Dan da silar zuwansa duniya ne ya yi connecting komai, ya hada zukata ya kuma raba su cikin kwanaki bakwai. Jami'ar Cologne din Jamus ita ce tushe, mafari, ginshiki na dukkan walagigin rayuwar da ta samu kanta. -Takori Downloaded From https://tknovels.com.ng