Downloaded From https://tknovels.com.ng  MASARAUTAR MU!. 3 SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com babbangoro2015@yahoo.com SADAUKARWA Ga 'yar uwar da muka rasa a TAKORITES. Allah ya jikan ki da rahma HASNA'U yasa aljannah ce makomar ki. Ya bamu guzurin tadda ke. Takorites bazamu taba mantawa da ke ba. Da zaman amincin da muka yi tare.Muna son ki Hasna. JINJINA Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. GARGADI Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, youtube, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali. MASARAUTAR MU 3 Cikin raunin murya marar amo da rashin karsashi kamar ta wanda ya sha duka sabida yadda tayi kasa sosai, Yarima Sageer ya duka gaban mahaifin sa Askirama tamkar zai shige cikin sa, ya soma magana cikin sanyin murya da hardewar harshe. Allah Kawun jo (Allah ya baka yawan rai) amma me ya sa tun lokacin da na dawo daga Amsterdam din, na kuma zo da bukatar auren Sultana baa tambayi raayi na a kan Saadatun ba? Allah ya ja da ran ku da a ce kun bayyana min kudirin ku akan mu tun farko, tun a wancan lokacin, a kan zabin da ku ka yi min, zan hakura ne da nawa zabin duk son da nake masa in karbi zabin ku. Saboda na san duk wani hukunci da za ku yi a kaina alkhairi ne wanda ni duk yawan shekaru na ba zan taba iya hangowa kaina ba!!!. Sai hawaye suka fito sharr! Daga idanun Yareema Sageer, wadanda a yanzu Askirama ya tabbatar na farin-ciki ne ba na komai ba; hawayen wani irin contentment da Dr. Sageer bai taba ji a rayuwarsa ba. Sai ya ji rayuwarsa a yau ta cika, ta zama cikakkiya, duk wani gibi dake cikin ta ya cika, amma a baya incomplete yake jin ta somehow shattered. duk da tarin dimbin achievements din da ke cikin ta. kamar akwai wani wawakeken gurbi a can kasan zuciyar sa da a da can, yake jira a cike, gurbin da bai san ko na menene, ko kuma na wanene ba, ya samu aka cike masashi yau unexpectedly. A yanzu ya gane cewa ya jima yana jiran shigowar Sa’adatu cikin rayuwar sa, he'spatiently waiting for her to come to his life ba tare da ya sani ba, sai a yau ya gane hakan. A can baya kafin zuwan wannan ranar jin sa yake tamkar bashi da komai tamkar bai taba mallakar komai a rayuwar sa ba, duk da ba abinda bai mallaka din ba a rayuwar tasa including ASIAN WIFE. Amma a yanzu da yake durkushe gaban Mai Askira yana yi masa wannan bushara sai yaji tamkar Askirama ya mallaka masa dukkan mulkin matan duniya, da mulkin dake cikin duniyar, mulkin da ya fi na garin Askira girma da ilahirin El-Kanem Borno Empire, da duk wani nau'in farin cikin dake cikin duniya da dan adam ke burin samu da ya mallaka masa Saadatu diyar Bilkisu da Mallam Hashimu. Na gode da wannan gatan Mai Askira, Nagode ZAKIN Askira, ina mai rokon Ubangiji da ya fi ni godewa, na kuma karba da hannu bibbiyu. Ina rokon Allah Ya sa daga yau ba za ku sake jin wani abu a kaina wanda ya jibinci laifuffukana na baya ba. Hakika na sani Askirama ni Sageer mai yawan laifi ne, mai saba muku ne, mai ketare tarbiyyar da kuka yi masa, amma hakan bai sa kun yi fushi da ni ba, kullum burin ku da fatan ku shine in dawo hanya madaidaiciya, wanda hakan yasa a kullum nake cikin tuba da neman gafarar Ubangiji. Ina rokon Allah ya fidda ni kunyar ku, Ya ba ni ikon rike muku yar ku da amana. A yi min godiya wurin Fulanin Sarki (yana nufin Fulani Bilkisu), kodayake bari in je in same ta da kaina. Askirama sai gani ya yi Yarima Sageer ya mike cikin wata irin azama, jikin sa har bari yake, gabadaya ya zama ba cikin nutsuwar sa ba, ya rude saboda excitement din da ya samu kan sa a ciki. Wanda Mai Askira zai iya rantsewa bai taba ganin sa cikin kwatankwacin irin wannan farin-cikin ba. Sai Askirama ya mika hannu ya kamo hannun sa, kada ya je ya yi abun kunya a gaban bayi da kuyangin Fulani Bilkisu, kuma dai Fulanin ta gaya masa Saade ta dau fushi tun jiya ta kulle kanta a daki. Wanda ke nuna ita bata murna da auren ko kadan. Kamar yadda nasa dan ke neman shidewa sabida farin-cikin hakan. Zo zauna in kirawo Fulanin ka yi mata godiyar nan a gabana, kada ka je sassan ta yanzu har sai bayan biki. Baa zuwa. Zuwa lokacin Saadatu ta huce daga laifin da muka taru muka yi mata. Yareema ya yi murmushi yana sosa kai, laifi? Auren sa ne ya zamo laifi ga Saade? Kodayake bai kamata hakan ya zamo abin mamaki ba a gare shi duba da cewa daga shi har ita respect ne a tsakanin su, babu wata magana bayan wannan, koda ace akwai din ita a gareta babu komai tunda bai taba furta mata ba, ko nuna wata alama da zata gane cewa he sincerely admires her tun farkon rayuwar ta a gidan sa. A lokacin suka hada ido da mahaifin sa wanda ya kura masa ido kawai yana murmushi, yana karanto duk abinda yake son karanta. Yareema Sageer yayi hanzarin dawowa daga duniyar tunanin da ya fada cikin jin nauyin kaifafan idanun Askirama. Kada dai ya zamanto cewa Mai Askira ya gane a rude yake gabadayan sa? Kuma already a rijiya yake? A rayuwar shi babu farin cikin da ya taba ruda shi irin na yau, kai mawuyaci ne wani abu yasa ya kasa mallakar kan sa amma yau? Saadatu a matsayin matar sa! Wani al'amari ne da bai zata ba. It comes abruptly. And it touches him more than he can imagine. Wani abu ne da bai taba kawowa zai samu da sauki haka ba, duk da zuciyar sa ta dade tana buri, kwakwalwar sa na kiyasta masa, ruhin sa na kwadayi da mafarkin kasancewar hakan. Ba don bashi da gatan samun ta ba, sai don yana ganin hes not worth enough ga mallakar ta matsayin mata, in yayi laakari da tarin aibubbukan sa. Maimartaba ya kira Fulani ta wayar hannun sa, suka yi magana ya aje, ya dubi Yarima wanda jikin sa ke ta (tsuma) ya kasa nutsuwa a waje daya, ya zama very upset, bai taba ganin dan sa Sageer cikin kwatankwacin irin wannan halin ba.. daga haihuwar sa har girman sa. Wanda ke nufin....(already Sageer na son Sa'adatu)!!! Ba abin da ya furta a zuciyar sa sai godiya ga Ubangijin talikai, ya ce da Sageer a hankali cikin muryar sa ta girma da sanyawa dan adam nutsuwa, yana murmushin kasaita irin nasa ta kyakkyawan gashin bakin sa da farin gemu ya zagaye; Be a Prince!". (Wato ya koma Yariman sa). Yareema ya dafe goshin sa yana yar dariya da jerarrun hakoran sa bakidaya a waje, wannan ma wani abu ne da Mai Askira bai taba gani ba, iyakacin sa murmushi ga duk abinda yayi impressing din sa, sannan ya kuma koma cikakken Yariman sa ta hanyar kokarin sarrafa kan sa da komawa cikin nutsuwar sa. Sai ga sallamar Sarauniya Fulani Bilkisun Askirama cikin kwalliyar ta ta kasaita, ta shigo ta kofar da suka saba shigowa bangaren Askirama ita da sauran matan sa, kowacce akwai kofar da ta bulla unguwar ta, zuwa turakan Mai Askira. Takun ta kadai abin kallo ne ga mijin ta. Yarima na ganin shigowar ta ya dukar da kai kamar tsohon da ya yi wa sarki karya. Surukuta sosai yake nunawa yau ga Bilkisu. Bai taba jin kunyar ta matsananciya ba irin yau. Kafin zuwan wannan ranar, jin ta yake kamar Yayar sa Yaa Maira, ba matar mahaifin sa ba. Alal hakika yana son matar nan ba tun yau ba, sau-tari, mantawa yake kishiyar Ya Gumsu ce sabida kirkin ta, mantawa yake da duk wani sabani da ke tsakanin ta da mahaifiyar sa sabida son da yake mata da kulawar da itama take bashi. Ashe Allah ya rubuta Kakar yayan sa ce masu zuwa nan gaba cikin kudurar Ubangiji. Jinin su ne zai zo ya cakude wuri guda ya kara binding din su together. A can gaba. Ya kara dunkule su matsayin iyalin Sarki Yusufu Mai Askira. Ya kara nutsuwa a wurin da yake tankwashe zaman Rakuma akan kafafun sa, sannan ya gaishe ta da sassanyar murya, bayan ta zauna kusa da Mai Askira tana zolayar sa. Ango! Ango ka sha kamshi. In ji Fulani cikin murmushi. Maimartaba ya juya gare ta yana tambayar ta, “Fulanin Askira Me ku ke shiryawa ne game da biki? Fulani Bilkisu ta gyara zama,sannan ta kaskanta murya cikin yanayin ladabin da Askirama kadai take yiwa magana da shi ta ce. Alanguburo, ai ni rabon da in ga Saade tun jiya da na gaya mata. Ta shige daka ta kulle kofarta, watakila idan ta ji mutanen Tsanyawa sun zo ta bude, kuma dai dama bukukuwan gidan nan Ya Gumsu ce ta ke tsara su ga shi kuma tana fushi da ni a kan laifin da babu ruwa na. Maimartaba ya ce, Zan turo Yaa Maira (babbar yarsa) ku tsara komai, Murjanatu ma tana kan hanya za su zo su same ki. Wannan kiran kuma na Yarima ne ba nawa ba, shi yake son ganinki, zai bi ki unguwarki na ce ya bari in kirawo ki nan, na ga yana ta bare-baren jiki kada ya je ya yi abin kunya a gaban bayi. Dariya Fulani ta yi, shi kuma Yarima ya kara dukar da kai, murya a raunane ya ce. Fulanin Maimartaba, Allah ya baki yawan rai, na gode. Allah ya jikan magabata, insha Allahu ba zan ba ku kunya ba. Na karbi auren Saadatu da hannu bibbiyu. Allah ya ba ni ikon yin adalci a tsakaninsu. Sosai Fulani ta ji dadin kalaman Yarima Sageer, suka wanke damuwarta kaso hamsin cikin dari na tunanin Yarimazai wulakanta mata Saade tunda yar talaka ce kuma yana da mata Baturiya, damuwar hakanta ragu daga ranta, don ba ta zaci haka zai karbi maganar ba with due respect, tunda uwar shi ma ba ta so. Ta ce, Da kai da Saade duk daya ne a wurina Yarima, kamar yadda Askirama bai taba bambantata da ku yayan da ya haifa ba. Rokona daya gare ka Yarima ina so ka raba musu gida, sabida Saade ba za ta iya zama waje daya da Aisha - Sultana ba, shekarun su, tunanin su, akidunsu da halayyar su ba zai taba zuwa daya ba. Ka ga kuwa zama da juna zai musu wahala. Ya saci kallon Askirama ta kasan idanun sa,sabida tsoron ko ya ji abin da Baggarar matar san nan ta ke fadi? Sai ya ga hankalin shi ba ya kan su sam, waya yake yi ma da yar sa Yaa Maira lokacin, wadda ke aure a masarautar Biu. Tana gaya masa cewa sun taso suna hanya har sun wuce Maiduguri. Wani sigh of relief Yarima ya sauke da ya fahimci Askirama bai ji ta ba. A ran sa fadi ya ke na tabbata sanda aka yi miki aure da Baban Saade baki yi girman ta ba kuma kin haifeta lafiya. A fili kuma ya ce, Insha Allah zan nema mata nata muhallin, daya bukatar kuma zan duba insha Allahu ran ki ya dade. Ai ba abinda zai gagara. Da wannan ya yi musu sallama ya mike zai fita. Sai Askirama ya sake yafito shi. Be a man also, after being a Prince (ka zama namiji bayan zama Yarima) wanda ba mai iya juya raayin sa, wanda ya san cewa mata da karkataccen haqarqari aka halicce su tunanin su ba kamar na maza bane, ka san yadda za ka lallaba mahaifiyarka har ta sauko daga dokin fushinta, ta karbi Saadatu matsayin diyar ta, ta sanyawa auren ku albarka. Tashi ka je ku tsara komai kai da Awaisu. Allah ya yi wa rayuwarku ku duka albarka. ***** Yaa Maira ta iso daga masarautar Biu kamar yadda mahaifinta ya kira ta don ta zo su yi shirye-shiryen bikin dan uwansu. Haka Murjanatu ta taso dagaIstanbul tun jiya ta sauka Abuja. Zata biyo connecting flight zuwa Maiduguri yau. Kamar yadda Maimartaba ya yi mata umarni cewa, idan ta iso kafin ta shiga koina ta fara ganinsa tukunna. Yaa Maira, ta bi wannan umarnin na mahaifin ta, ta yi saa babu kowa tare da Mai Askira lokacin da ta shiga falon ganawarsa da iyalinsa. Ta same shi yana cin abinci. Ita dai ta ji an daura wa kanin ta Yareema aure, amma ba ta san da wa Askirama ya daura ba. Yanzu da ta ke durkushe a gabansa suna magana ta Da da mahaifi, bayan ya kare cin abincin sa sun gaisa, ta fahimci ko wace ce Maimartaba ya zaba wa kanin ta Yareema Sageer. Ba kowa bace face Saadatun Fulani Bilkisu!!! Yaa Maira, wadda sunan ta na sarauta kenan, tana da wata baiwa ta daban kamar yadda na fada a baya ta sunsunar kaddara. Tun ganinta da Saadatu na farko jikinta ya ba ta wannan yarinyar will some day become part of them, za kuma ta zamo wani jigo a rayuwarsu. Zubin halitta da komai nata na Fulani Bilkisu ne, Bilkisun da ke juya zuciyar Maimartaba a halin yanzu. Bilkisun da babu tauraruwa mai hasken ta a idanun Mai Askira. Sai ba ta yi mamaki ba ko kadan da wannan zabin na mahaifin su domin BAGGARA matan manya ne. Abu daya ta ke so ta tantance yanzu shi ne hakikanin alakar dake tsakanin Bilkisu da Saadatu. Mai Askira sai bai boye mata ba, ya gaya mata hakikanin alakar da ta hada Bilkisu da Saadatu. Yar ta ce ta cikin ta! Mamaki, alajabi da tuajjibi kamar ya zauta Yaa Maira, kodayake dama ta dade tana kiyasta hakan, kawai sai ta ji ta karbi Saade da dukkan zuciyar ta matsayin suruka. Duk da aibanta ta da Humaira ke yi duk sanda suka taru bata taba fadin wani mugun hali a tare da ita ba, in ka fahimci duka kushen Humaira akan Saade to kishi ne na son da Askirama ke mata da daidaita musu matsayi da yake yi lokacin suna makaranta. Sai ko taya uwar ta Yaa Hibbani kishi da Fulani Bilkisu. Sai kuma kyawun Saaden da take cewa irin na shegu ne. Ita ta sani uwar Saade mai nagarta ce, cikin matan gidan kaf babu mai kirkin ta, saidai kishi ya hana aga hakan a kare da fadin aibun ta. Maimartaba ya sa mata albarka domin ta ce ta karbi amanar Saadatu a dakin su, ita ce uwardakinta daga yau, za kuma ta yi duk irin kokarin da za ta iya wajen ganin cewa mahaifiyarsu (Ya Gumsu) ta sauko ta sanya wa alamarin albarka. Da wannan ta bar falon Askirama zuwa unguwar Ya Gumsu. Tana tafe tana saka irin lallashin da zata yi mata. ***** Yaa Gumsu ta yi mamakin ganin Yaa Maira a daidai wannan lokacin, don dai ita da kanta ba ta gaya ko dayan su zancen auren Yarima da Saade ba saboda tsananin kiyayyarta ga auren. Yaa Maira ta kwaso gabadaya yayanta maza da mata sun taho, kallo daya ta yi wa Ya Gumsu, ta tabbatar da abin da Askirama ya gaya mata na cewa tana matukar adawa da auren, ba kuma don komai ba sai don kishinta da Fulani Bilkisu. Ya Gumsu hakimce cikin royal chair ta babban falon ta, kuyangi na yi mata firfita da maficin gashin dawisu. Wasu na tausa mata kafafu, wasu na zubo kirari amma duka basu ishe ta kallo ba sai kumburi take kamar zata fashe. Ta daga ido tana kallon Yaa Maira da ke warware lafiyayyar laffayar jikinta don ta ji dadin hutawa, sun sha zaman mota daga Biu zuwa Askira. Take gayawa Yaa Gumsu. Ya Gumsu ta harare ta sosai, sannan a hassale ta ce. To da ki ka kwaso bataliyar yayanki ku ka zo kuka cika min gida me ku ka zo yi? Wa ya gayyato ku? Na ayya gayyar sodi?” Dariya Yaa Maira ta yi, ta ce, Allah ya taimaki Gumsun Gari, mu ai ba sai an gayyace mu ba. Su Murjanatu ma duk suna hanya. Ya Gumsu ta kara shaka sosai, amma ta ja bakinta ta yi shiru sabida kuyangin da ke zazzaune wasu a tsaitsaye, zuciyar ta na tafasa. Ta kara ganewa Mai Askira bai dauki auren nan da ya daura da sauki ba tunda har da kan sa yake gayyatar yayan sa abinda bai taba yi ba. Allah kadai yasan iya gayyatar da yayi da irin hamshaqan sarakunan da ya gayyato akan auren nan. Bata kara magana ba sabida kunar zuci. Kallo daya Yaa Maira ta yi wa kuyangin da ke wurin duk suka mike suka bar falon, suna masu yi mata kirari irin wanda suke yi wa diyan Ya Gumsu. A tashi lafiya Yaa Mairar gida, A gana lafiya uwar marayun Askira, A fito lafiya cikin alheri Yaa Maira uwar diyan Yaa Gumsun Askira bakidaya.. Daidai kafafun ta Yaa Maira ta zauna suke kara gaisawa a nitse, gaisuwa irin ta Da da mahaifi, Yaa Gumsu na kokarin hadiye fushin ta, yaran duk sun bazama cikin gida, kowa ya tafi wurin saanninsa yadda suka saba in sun zo gidan. Yaa Maira ta ce da mahaifiyar ta cikin sanyin murya. Sai muka ji abin alheri Yaa Gumsu, da ma zaman Yarima da mace daya ai ba yi ba ne, Yarima fa, Yariman Askira Mai jiran gado! Balle wadda ba ta fito daga jinsinmu ba balle addinin mu. Na yi farin ciki kwarai da gaske don dama ni auren nan na farko na Yarima bai kwanta min ba ko kadan, babu wani biki na alaadunmu da muka yi sabida abin kunya ne ma mu fito mu fadi ga wadda ya aura a cikin masarautun da ke zagaye da mu. Sai kuma ku yo gayya a auren shegiya mara asali? Tukunna ma kin san da wa ya daura masa auren da kike wannan giringidishin? Subhanallah, Yaa Gumsu tofar da miyan bakinki tun kafin malaiku su rubuta. Saadatu ba shegiya ba ce, diyar Bilkisu ce ta cikinta Tayi aure ta haife ta da mijin ta na fari kafin ta auri Askirama..!. A razane Yaa Gumsu ta dago ta dubi diyar ta Yaa Maira. Sai Yaa Maira ta yi amfani da wannan damar data samu wajen luguiguita zuciyar ta. Tiryan-tiryan ta soma bai wa Ya Gumsu labarin Bilkisu da yadda ta haifi Saade, sak yadda mahaifin su ya bata labari, ta kare da labarta mata Bilkisu ta boye musu Saade yarta ce sabida ba ta son gori musamman daga ita Yaa Gumsu in ta ji cewa ba a budurwa Mai Askira ya aure ta ba ta kade har ganyen ta da gori. Karshen maganar da Ya Maira ta fada shi ya kara sanyayar da jikin Ya Gumsu. Dangin mahaifinta na hanya, wan mahaifinta uwa daya uba daya Alhaji Kyari Babagana, na tabbata kin san wannan sunan, don kuwa shi ne yake bai wa Bulama fatun da yake kai wa kasar Italiya. (Bulama kani ne ga ya Gumsu, wanda suke sanaa daya da Alhaji Kyari). Ita ma Ya Maira Askirama ne ya gaya mata hakan. A binciken da yasa aka yi masa akan asalin mahaifin Saade. Ya Gumsu da ke ba ta son nuna karayarta, sai ta hau mitar rashin dalili. Ban da munafurci me ye na boye mana cewa yarta ce? Ina ruwanmu don ta taba aure? Gori yana tsiro a goshi ne? Duk wata harka ta kishiya sai kin samu dunkulallen munafurci a ciki. Ashe ma a bazawara ta zo shi ne ta bi ta juye kan tsoho, kinibabbiya, haba! Ni fa in ce wannan so da Askirama ke wa yarinyar nan da walakin, ashe agola diyar mowa ce, to muna jira mu ga wan baban yarinyar da idanunmu don mu tabbatar ba shegiyar bace. Kuma shi Yareema shi ke nan ba zai auri yar sarauta ba, auren misali sai dai ya gani a wurin tsararrakin sa? Alhalin ba gata aka fi shi ba? Daga jinsin yahudawa da masu kanan ido sai jinin talakka agola a matsayinsa na Yarima mai jiran gadon Askira? Ya Maira ta yi kasa da murya ta ce. Yaa Gumsu, gara talaka, agola tushen musulunci tashin musulunci a kan tubabben da aka ce daga kwalba ta ke yi a bar, sallar ma ta daina. Ki gode wa rahmar Allah Ya Gumsu alheri Askirama ke nufinmu da shi. Yariman ai ba wankakke ba ne kin fi kowa sani. 'Yar Bilkisu aka cutada auren Yarima ba Yarima ba. Ni tun ganina da yarinyar na farko na san za ta zame mana wani jigo cikin zuriar mu. Tana da charisma mai yawa. Tana da wisdom bayyananne. Allah ne bai taba kai hankali na kan Yarima ba, musamman da ya zo ya yi auren sa daga baya. Amma na yi zaton Ashgar zaa bai wa, sai dai lalurar sa ba za ta bari ya yi aure ba, Jiki na ya dade da bani hakan cewa bazata wuce mazan gidan nan ba koda ba daga dakin nan ba. Yaa Gumsu Ta kyabe baki tace Mairam ki fita ido na in rufe, na bi wisdom da gudu na tattake babu takalmi a kafata me yasa baa baiwa dakin Yaa Kirjiloma ba? Uban wa yace miki Ashgar bazai iya aure ba? Sai Yarima na dana dora dukkan buri akan sa da yayan da zai haifa? Kawai sai kuka ya kwace mata. Yaa Maira ta rasa yadda zata yi da Yaa Gumsu, duk dabarar ta ta kare. Haka ta yi ta tausar Ya Gumsu tana nuna mata muhimmancin wannan aure ga mutuncin Yarima da rayuwarsa, da alkhairin da ta ke hangowa a cikinsa na kimtsuwar Yarima. Yaa Gumsu baki da masaniyar cewa har yanzu Yarima Sageer bai bar bin mata a garin Abuja ba? In baki sani ba ki sani, in kuma kin sani ki tuna. Ko jikin ta ya yi sanyi dai ba ta nuna ba, Ya Gumsu akwai Ki-Fadi, ko ma me ye ba za ta so hada jini da Bilkisu ba gara dan kowa a kan nata. Da ta rasa hujjar kamawa sai ta ce da Yaa Maira. Shi ke nan kuma shi ba zai yi aure irin na gidansu ba? Ba zai yi auren martaba (auren sarauta) ba sabida ubansa na auren uwarta? Yaa Maira ta sake kwantar da murya, Allah ya taimaki Gumsun Askira, ai akwai sauran damarmaki. Yarima na da gurbin wasu matan biyu bayan Saadatu, ki ka sani ko duka ya auri yayan masarautu a sauran guraben yadda kike masa shaawa? A nan ne Ya Gumsu ta yi ajiyar zuciya, don shaf bacin rai ya sa ta manta da hakan, yayi zabin sa ya yi zabin mahaifin sa dole nan gaba kadan ya yi nata zabin. Ta ce, Yanzu ki ka yi magana Mairam, daga yau zan fara binciken yayan babban gida wa Yarima. Ba zai yiwu a ce duka aurarrakinsa babu zabina a ciki ba. Yaa Maira ta ce, Oh ni ya su. Amma Ya Gumsu ki bari ki ga kamun ludayin zaman nasu tukunna, kafin ki nema masa sabon aure. Yarima kodayake basarake to bature ne na gani kashe ni. Ba zai so da kuruciyarsa a cika masa gida da mata ba. Ki yi hakuri ki daga masa kafa zuwa wani lokacin. Haka ta yi ta lallashin Ya Gumsu cikin kwantar da kai da lalama, kodayake da ma cikin yayanta kakaf Yaa Maira ce kadai ta iya tafiyar da ita cikin hikima duk taurin kanta. Ko dai ba ta sauko duka ba, to Yaa Maira ta yi nasarar dakushe kiyayyarta da auren kashi talatin cikin dari. Tunda ta ji Saade ba shegiya ba ce sannan yar Fulani ce ta cikinta ba yar riko ba kamar yadda suke tsammani. Kuma ta ji cewa dangin ubanta za su bayyana kansu. Wannan ne kadai ya sassauta zuciyar Ya Gumsu har ta yarda ta amince musu su je su shirya biki nasu na aladar masarautar Askira. Amma ita tana nan sassan ta ko waje bazata leka ba. Don farin ciki Ya Maira a take ta hau buga wa kannenta mata da maza waya ta ce duk su hadu yau a Unguwar Fulani Bilkisu kan shirin bikin Yareema bayan sallar isha’. Kafin lokacin Mairam-Murjanatu ta iso. Ko hutawa ba ta yi ba suka dinga firfitowa daga sassan iyayensu mata zuwa na Fulani Bilkisu. Da ma kuma tun da yamma Yaa Maira ta aika wa da Fanna sakon zuwan nasu. Fanna kuma ta gaya wa uwargijiyarta. Don haka ba su zauna ba tun lokacin suke dafe-dafen abinci na alfarma domin saukar su Yaa Maira da sauran yayan Askirama maza. Humaira ce kadai ta ki zuwa don ta shiga matukar damuwa da wannan auren da aka daura. Fulani Hibbani kuma ta ce ta raba kanta da wahala, fadan da ya fi karfin ka ka maida shi wasa, ta fita batun Fulani Bilkisu da yarta, don sun gama da ubanta saidai wani sarkin ba shi ba, in kuma ta ki ji ita ce a wahale. Saade da ma ba ta yarda ta bar dakinta a bude tun daga lokacin da suka yi magana da Fulani a kan aurenta da Yareema, ita kanta Fulanin haushi take bata yanzu don ta lura ta gama mika wuya ga auren sabida son da take wa mijin ta Askirama, kuma bata dauki shirin sa da wasa ba, ko don bata san waye Dr. Sageer ba? Ko kuma bata dauki hakan da muhimmanci ba? Aisha Sultana bazata yi masa karya ba da ta ce hes committing adultery kuma SAI YA BARI ITAMA ZATA BAR GIYA, wannan ne gidan da Fulani ta amince a kai ta kuma cikin mutanen da take mata fatan rayuwa ta har abada? Ita kuma Fulanin kamar ta san tunanin da take yi sai ta fita sabgarta, shirye-shiryenta ta ke kain da nain, ta ce cikin ran ta, Allah shine mai shirya bawa bani da tsumi banida dabara sai abinda Allah ya shiryawa rayuwar ki Sa'ade. In kun tafi Abujar ku karata can, ni biki ne a gaba na. dama ai tare kuka zo, don kun koma tare matsayin miji da mata yanzu babu laifi. To yau ma tana jin su suna maganar kabakin abincin da za a shirya wa su Yaa Maira ita da kuyangin ta wadanda a nan za su ci abincin dare, bata dai ji hakikanin me zai kawo su ba amma taji ana maganar abinci na gani na fada zaayi yayan Askirama gabadayan su, da gudu ta kara murza key din kofar ta duk da dama a kulle ta ke. Kada ma wani ya shigo in da take. A bar ta ta ji da damuwar ta ita kadai tunda babu mai taya ta bakin cikin kaddarar da ta same ta. Karewa ma kowa harkar gaban sa yake yi, dan tausayin ta da Fulani ke ji a farko ta zubar. Abinci wannan Saade ta daina cinsa sai fruits kawai ta ke sha a firjinta, sai ko fresh milk din oldenburger gora-gora idan yunwa ta matsa mata. Yau kwanaki biyu kenan rabon da ta sa Fulani a idonta. Wayarta ta kashe ta don ta san dole Saidu zai kira ta, ba ta san da wanne baki za ta fara masa bayanin ita matar aure ba ce yanzu, ta san babu kyau mace ta dinga muamala da wani kuma. Ta ce ita matar Uncle Yarima ce ma ai yanzu ai abun kunya ne bayan ta gama yi masa homar Yayan ta ne. Saidu-Saidun ta hakika zata yi kewar sa. Babban tsoron nata shi ne kada Yarima ya kira ta a waya. Tuna sunansa kadai fadar mata da gaba yake yi. Duk wata kyakkyawar alaka da ke tsakaninsu a baya daga yanzu ta yanke ta. Karatun ma in dai ba hostel zaa maida ita ba ta hakura ta yafe shi har abada. Tana nan kusa da uwarta da kanwarta, a rayuwa wannan shi ne babban kwanciyar hankalinta wato ta gan ta tsakanin Fulani da Zarah. Bayan ita ma Zaran ko za ta wuni tana buga mata kofa ba za ta bude ba sai Fulani ta zo ta kore ta a wurin. Wajejen karfe takwas suka fara shigowa mazansu da matansu iyalin Mai Askira. Yaa Maira ce karshen shigowa har da bawan Allah Ashgar wanda bai san me ake yi ba shi dai an kira shi kuma ya zo. Babban falon saukar bakin Fulani na musamman aka bude musu, kuyangin Fulani sai shige da fice suke suna shirya abinci na alfarma. Sai hirarrakinsu ke tashi cikin kasaita da taushin murya kamar ba magana ke tashi a falon ba sabida yadda suke yin ta cikin nutsuwa da salama. Sassan Fulani Bilkisu ya game da kamshin turaruka na alfarma, wannan na wane wannan. Ya kuma cakude da na wuta irin nasu na barebarin usli, ga sanyi da rabar iya kwandishan na ratsa su. Ba jimawa Fulanin Askirama ta shigo cikin falon, as usual cikin kwalliya ta alfarma, ta fi kowacce iya tsara kwalliya cikin matan Mai Askira kamar yadda duk ta fi su kuruciya da daukar ido. Da faraa sosai wadda ta fiddo hakoran Makkanta na danyen gold guda biyu ta ke musu barka da zuwa. Ta dubi Mairam-Murjanatu cikin jin dadi ta ce, Har da mutanen Istanbul? Lallai kuna ji da wannan yar kanwa taku, ga shi ta shige daki ta rufe balle ku gaisa. Ya Maira ta ce, Kyale Saadatu kin ji? Kunya ce irin ta Baggara, me ake da amaryar da babu kunya? We really appreciate, muna nan tare har abada ai. Mairam Murjanatu ta muskuta cikin lallausar royal chair three seater da take zaune a kai, ta ce, Shin wane shiri ki ka yi Fulani game da biki ki gaya mana mu ji? Fulani ta yi dan murmushi ta ce, Ban shirya komai ba. Na bar muku wuka da nama, ku ne Yayyenta kuma surukanta. Ni ina gefe yar kallo ce. Yaa Maira ta ce, To madallah da wannan girma da anka ba mu, mu kuma za mu shirya mashahurin biki na alada, wanda za a dade baa manta a masarautar nan ba. Za mu huce na auren farko da ba mu samu yi ba. Daga nan Fulani ta yi umarni a zo a yi serving dinsu abinci. Sun dade suna tsare-tsare da shirye-shiryen yadda abubuwa za su gudana a junansu, bayan sun gama cin abinci. Fulani ba ta saka musu baki sai dai ta raka da eh ko aah. Yaa Maira ta dubi kannenta su Murjanatu ta ce. “Kamar yadda kuka riga kuka sani a aladar bikin gidan nan za mu fara da sakun lalle ranar laraba, alhamis za mu yi nakiya, jumaa wushe-wushe, ranar asabar ake daurin aure, to tunda an riga an daura ba shiri, to a ranar ne za mu yi kelatul (wanke kai da kitso na amarya), sannan mu yi Biji Ginata (ana shimfida tabarmi ne a ranar a ajiye amarya ana kida ana wakoki bayan an yi mata kwalliyar masarauta. Ranar lahadi za mu yi kaulu na amarya da ango da safe (kaulu shi ne, zaa ajiye miyar yauki a gaban amarya bayan an mata kitso da kwalliya, Baaba za su goyo amarya (sisters din Maimartaba su ne Baaba) su kai ta wajen Kaulu, yan uwa da iyaye su dinga dibar wannan miyar yaukin suna shafa mata. Da daya da daya kowa zai zo yana shafa mata yana ajiye wa amarya kyauta, wasu har gold suke badawa, wasu iphone ko mota ya danganta da mukamin mutum a masarautar, wasu kuma kyautar kudade suke yi, kaulu kenan. Da yammacin lahadi kuma za mu yi ‘dubdo’, wato wunin biki a gidan amarya bayan an kai ta ranar asabar da daddare (a wannan ranar yan uwa da iyaye za a wuni ana shige da fice a gidan amarya. Ke kuma Fulanin Maimartaba ke ce da alhakin yin Miskero (abincin da ake kai wa gidan amarya ranar wunin) wanda jamaa da ke shiga da fita a gidan za su ci. Sannan a satin bikin gabadaya har ila yau ke za ki dinga ciyar da amarya da ango abinci mai kyau. Har zuwa ranar da za a kai amarya, wato asabar. Idan asabar ta zagayo kuma ana ‘tulur’, wato sati daya da kai amarya, ranar ne ke da kawayenki (Fulani Bilkisu) da yan uwan amarya za ku je gidan amarya, mu kuma za mu yi mata kwalliya, sai a saka mata muciya a hannu, a ranar za ta fara girki kenan, ana wakoki da raye-raye, a ci a sha, to daga nan biki ya kare. Ranar asabar kuma za mu kawo lefe. Fulani ta ce, Turkashi, wani aiki sai Amale, bikin Kanuri sai Askira! Allah ya sa muna da rabon gani. Aka yi adduoi aka shafa, bayan mazan ma sun yi nasu tsare tsaren, sannan duk suka fara watsewa. Amma sai da daya daga cikin kannen Yarima da ake kira Houdda yar dakin Yakirjinoma ta je har kofar dakin Saade ta yi magana ta hudar kofar dakin tamkar mai yin waka cikin harshen Kanuri. Ki gama boyon amarya, kin riga kin zo hannu, da sannu za mu yi miki kaulu, kelatul, biji ginata da tulur, sannan mu damka wa Yarima ke. Murjanatu ta zuba mata duka a baya [dundu], ta ce, Houdda kar da ki tsoratata ta kara kunshewa a daki duk zafin nan da ake yi, in kika firgita masa amarya ke da shi ne, kin fi kowa sanin halin sa. Saade da ke cikin daki duk tana jinsu ba ta san sanda ta fashe da kuka ba.. Da gaske dai ya tabbata an yi mata auren kenan, this is the reality da take ta kokawa da zuciyar ta wajen yarda da shi. Take yaudarar kanta da kanta da cewa mafarki ne. Iyalin Askirama bazasu bata lokacin su su zo har da na wata kasa ba idan ba gaskiya bane. [They are very serious people] a sanin data yi musu. Auren kuma ba da kowa ba sai UNCLE YAREEMA! Yariman da ta yi wa farin sani, uban dakinta mijin Aisha-Sultana. Yanzu ya tashi daga mijin Sultana ita kadai, ya koma mijinsu su biyu. Da wane karfin zuciya za ta iya karbar wannan sauyin rayuwar na bagatatan da ya zo mata rana daya? Ta tura kanta karkashin filo tana ta kuka, wani irin kuka wanda tun lokacin da Fulani ta sanar da ita zancen auren ba ta yi shi ba sai yanzu. Yanzu data ji ana shirye-shiryen biki kain da nain daga kowanne bangare. Daga bakin kofa ta ji ana sallama da wata irin murya cike da doki da zakuwa ga son ta bude. Muryar da ba za ta taba mantawa ba. Ko mutuwa ta yi ta dawo bazata kasa shaida muryar Hanne ba, Hannenta, Hannen Tsanyawa! Diyar Innar Hanne da Baba Saleh. Ai ba ta san lokacin da ta isa ga kofa ta bude ta da sauri ba. Hanne da Saade aka tsaya ana kallon-kallo, kafin su runtuma da gudu su rungume juna tsam tsam. Cikin yan kallon sakanni da suka yi wa juna, kowacce ta karanto irin sauyin rayuwar da ke tare da yar uwarta. Bi maana, Hanne ta gano tarin sauyi na ci gaba da nasarar rayuwa a tare da Saadenta, domin inda a hanya ta ganta ba za ta gane ta ba, to dadin abun mahaifiyarta Fulani ce da kanta ta tabbatar mata Saade na cikin dakin nan a kwance, in ta yi magana ta ji ita ce za ta bude mata. A yayin da Saade ta hango tarin nakasu da koma baya a rayuwar Hannenta, ta zama kamar mai shekaru arbain bayan ko ashirin ba su rufa ba. Ta yi baki; ta rame; ga goyon wani katon yaro a bayanta wanda da gani ka san ya wuce goyo domin har rinjayarta yake. Saade ta soma kokarin kwanto dan daga bayanta don Hanne ta ji dadin zama, suka karasa bakin gado suka zauna suna hawaye. Ina Baba Saleh? Abin da Saade ta fara tambayar Hanne kenan. Hanne ta idasa rushewa da kuka, ta ce, Baba ya jima da rasuwa Saade. Baba ya dade a kushewar sa. Mu kuma ba mu san garin da ki ke ba da tuni mun zo, shekara da shekaru muna kewarki. An yi min aure shekaru hudu baya da saurayinki Naziru, tunda na samu ciki ya gudu birni ya bar ni yau shekaru hudu ba mu kara jin labarinsa ba, kin ga dan da na haifa masa nan, Inna ta sa masa sunansa Naziru. Jiya kawai muna alwala a gindin rijiya sai ga sako daga gidan Maigari wai mu zo an zo daukarmu za a kawo mu inda ki ke. Inna Laure ta ce ba zaa zo da mu ba, ita kadai zaa dauko, sai da direban ya ce an ce masa iyalin Baba Saleh da Inna Laure, sannan ta yarda aka taho da mu. Saade ta rungume dan Hanne a jikinta tana tuno Naziru don kamar su daya, ta ce, Yanzu ina Innarmu da Inna Lauren? Aka bude kofar dakin aka shigo, Fulani ce, sai tsofaffin guda biyu biye da ita. Duk sun tsufa sun yamutse a idon Saade. Tana kuka ta ke rungumarsu daya bayan daya, ta ce, Inna, ku yafe min. Na dade ban neme ku ba, ajizanci ya tabbata gare ni, wallahi karatu ne ya sha kaina sam bana samun hutu. Inna Laure da Innar Hanne suka rike ta suka zaunar a tsakiyarsu suna fadin, Babu komai Saade kin ji? Allah ne ya nufa sai yanzu za mu sake haduwa, komai kana da niyya sai Allah ya nufa. Innar Hanne ta ce, Shi ma Babanku yana ta wakar zai dawo ya sake duba lafiyarki, sai cuta ta sarke shi, bai jima yana jinya ba mutuwa ta raba mu. Mu kuma ba mu san garin ba, mun dai san masarauta ce a Borno. Sai yau da ki ka sa aka tura har Tsanyawa aka dauko mu cikin mutunci a mota. Ashe Saade aure ya zo? To Allah ya sa an yi ke nan, Ya ba ku zaman lafiya. Saade kamar jira take sai ta rushe da kuka, ta ce, Innar Hanne ku roki Fulani, don Allah ta bai wa Maimartaba hakuri, bana son auren. Inna Laure ta ce, Kul Saade! Aure sunnar Annabi ne, wanda ba ya son sunnar Manzon sallallahu alaihi wasallam hakika Manzon rahma ya ce ba ya tare da shi. Ni dai rokonki zan yi ki yafe mini, na ga babbar ishara a kanki, duk abin da na yi miki kin manta ki ka ce a je a dauko miki ni har Tsanyawa. Ta saka kuka sosai. Saade ta ce, Inna Laure, ni ba ki yi mini komai ba sai alheri, rike ni da ki ka yi tun ina karama shi ne babban alherinki gare ni, don haka ni komai ya wuce a wurina. Daga nan hirar ta koma kan yadda auren Hanne da Naziru ya kasance, Innar Hanne ta ba ta labarin Naziru ya sha kuka bayan tafiyarta Askira, A karshe da ya tabbatar ba za ki dawo ba ya like wa Hanne, Baba Saleh ya cire ta daga makaranta ya ba shi aurenta cikin mutunci. Amma tunda Hanne ta samu ciki aka neme shi aka rasa a Tsanyawa sanadin kamuwar Babanku da hawan jini ke nan. Hanne ta haihu a gida, ba ta jima da haihuwa ba Babanku ya cika, ni na yi ta dawainiya da su da sanaoin hannu iri-iri har kawo yau. Fulani ta ce, tunda ya shekara hudu bai dawo ba kuna da damar kai kara kotun muslunchi a ba ta yancinta, ko ta samu ta yi wani auren. Shi kuma in da gangan ya gudu ya barta Allah zai saka mata, in kuma wani uzurin ne ya rike shi, Allah ya sada su da alkhairi. Zan yi magana da Maimartaba ya shige muku gaba Hanne ta samu yancinta. Hanne ta ce, Burina kenan, ban san ina da wannan damar ba da tuni na yi amfani da ita. Ina matukar son in koma makaranta in raini Naziru shi ma in sa shi makaranta. Fulani ta ce, Kada ki damu Hannatu, insha Allahu komai zai yi daidai bari mu kare bikin Saade. Sai da suka raba dare suna hirar yaushe gamo, a dakin Saade duk suka sauka don saboda zuwansu ta manta da damuwar ta, ta cire wa ranta kunci, ta ware suna ta hira da Hannenta. Washegari Fulani ta raka su suka yi gaisuwa wajen Askirama, ya ji mutuwar Baba Saleh sosai, Fulani kuma ta gaya masa maganar Hanne, Askirama ya ce zai shiga maganar bayan biki insha Allahu. Tun zuwansu Hanne, Saade ta samu walwala, amma ta ki kunna wayarta. Tabbas da ta ga sakonnin Yarima Sageer har guda uku. Sako na farko ga abinda Yarima Sageer yace. “Thank you for being the PRINCESS Im waiting for.Thank you for coming to my life when my heart is desperate to have you..(Madallah da zamowar ki GIMBIYAR dana ke jira tuntuni, madallah da zuwan ki cikin rayuwa ta a lokacin da zuciyata ta dimauce ga son mallakar ki). - Sageer. Na biyu kuma yace. “Saadatu save a soul by picking my call(Saadatu ki cece ni ki daga kira na). - Sageer. Sakon Yarima na karshe ga Saade cikin harshen hausa ne, ga abinda Yareema ya rubuta ma Saade. Kin ki bude waya saboda ni ko Saadahtouh? Bonono kenan rufe kofa da barawo. Bari in tuna miki wani abu guda daya da baki sani ba ko kika manta; daga rana irin ta yau mun zama abu guda,tare zamu kare rayuwar bakidayan ta,daga nan har gaban abada, ko makwanci bazamu kara rabawa ba sai bisa unvoidable reason.. Duka wannan bidirin da Yarima ke yi shikadai yake yin abinsa Saade bata san yana yi ba don kememe ta ki kunna wayar ta kamar ta san tashin hankalin dake jiran ta cikin ta daga zafafan kalaman sa [ba raba makwanci har karshen rayuwa]. Da ga karshe Yarima ya kasa hakuri, Saade ta kure dukkan hakurin sa, idan ba ganin ta yayi ba ba zai samu nutsuwar fuskantar bikin nan dake gaban su ba, ba zai koma nitatstsen Sagirun sa ba, matukar son ganin Saade yake anyhow ko jin muryar ta, don ya ga da fuskar da ta karbe shi matsayin miji ne ko akasin sa? Ko har yanzu kallon Uncle take masa? Ya aiko a gaya wa Fulani ta yi ma Saadatu magana ta kunna wayar hannunta su yi magana, mai muhimmanci. Da Fulani ta sa Fanna ta gayawa Saade, sai Saade ta ce ma Fanna ta ce da Fulani ta kunna har sun yi maganar, bayan kuma ko taba wayar daga inda ta yi mata kyakkawar maboya ba ta yi ba. To me Uncle Yarima zai ce mata? Na ji auren da aka yi mana bagatatan ni ma bana so ko me? Ko ki kama kanki ni ina da mata ta da nake matukar so? Ba ta bukatar wata sabuwar muamala a tsakanin su bayan official one irin wadda ke tsakanin su a baya, cuta ce an gama yi mata tunda an hada ta da shi, don haka ta yi kememe ta yi kemadagas ta ki kunna waya. Kulawa ma yabawa ce inji 'yan magana. Ya gaji da trying wayar Saade a daren yau, ana cewa a kashe, sosai yake son ya gan ta don ya ga da fuskar da ta karbi wannan babban alkhairin da ya same su. Yes shi a wajen sa alkhairi ne, GIANT (katoton) alkhairi ma kuwa, da bashi da yadda zai iya bayyana farin cikin sa da muhimmancin sa gare shi! An bashi abinda ya dade yana so yana kwadayi batare da ya cancanta ba, ba kuma tare da ya furta ba kuma ba tare da ya sha wahala ba sannan cikin girma da daukaka. A ganin sa hes not worth enough (bashi da darajar da zai mallaki Sa'ade) innocent soul kaman Saade, in yayi laakari ga tarin nakasun sa da laifuffukan sa na baya. Ya dade yana sunsunar takalmin, bai san ta yadda zai yi ya dauka ba. Sabida ganin cewa Sa'ade tafi karfin sa. Sai Askirama-Mai Askira cikin dimbin alfarmominsa da karamcinsa da ba su taba karewa a gare shi ya sunkuya ya hutar da shi, ya dauko takalmin nan ya miko masa har inda yake. Me zai ce da Mai Askira? Me zai ce da Fulani Bilkisu banda Allah ya ja kwanan su? Sun yi masa gatan da ya kasa yiwa kansa. Ba zai gushe yana rokon Allah Ya kara soyayya a tsakaninsu, ya ba shi soyayyar Saadatu kwatankwacin ta mahaifiyar ta Fulani ga Askirama! Da ya gaji da trying wayar Saadatu ta ki kunnawa sai ya kira Yaa Maira. Ya san Yaa Maira ce kadai zata yi masa wannan taimakon, sabida yadda take son sa da tausayin sa, in ba haka ba shi da ganin Saadatu sai an gama biki. Yaa Maira na dagawa ta ce, Angon Saadatu ka sha kamshi. Murmushi Yarima ya yi, cikin jin wani irin karin nutsuwa a zuciyar sa da ruhin sa wanda bai taba ji a baya ba, da wannan daddadan suna da inkiya da Yaa Maira ta kira shi da shi, ya ce, ni bana kamshi Yaa Maira tunda amaryar ba ta son ganina ko kadan balle ta san min kamshin, ko murya ta bata son ji Yaa Maira. Ko kai na ya fara furfura ne ban sani ba? Kin san yammata basa son mai furfura, rabo na da ita tun ranar da muka zo, ko waya ta ki kunnawa don kar in kira ta in ji muryar ta in samu nutsuwa. Dariya Yaa Maira ta yi, in wani ne yace Yarima ne wannan zata musa, Yariman da magana a gare shi sai dole, fitar kalma wannan tsada gareta daga bakin sa, amma yau shine yake joking, lallai Saadatu ta ciri tuta kaman uwarta, wane irin sirri gare su haka? Da suke juya zukatan sarakuna? Bata tantama in nan gaba kadan Saade bata juye kan Yarima ba kamar yadda mahaifiyarta ta juye na Askirama. Ita dai in auren Saa zai raba Yarima da bin mata ba ta da damuwa a kan hakan, ta tabbata dama ranar da ya auri matar da yakewa hakikanin so zai bari, musamman idan halittar su ta zo daya, tunda Mai Askira ya hakura da kwarkwarori tun zuwan Baggara Bilkisu,ta ce, Amma Saadatu ba ta kyauta ba, an gaya mata miji wasa ne? Bari in je in samu Fulani zuwa anjima a shirya muku ganawa ta musamman, don in anka shiga hidimar bikin nan ba za ku samu ko ganin juna ba. Tana kashe wayar ta nufi unguwar Fulani Bilkisu. A falon ta tadda ta tare da mutane, nan ta nemi kebewa da Fulani, suka dan yi magana kuskus, Fulani ta kama baki cikin mamaki. Ashe Saade ba ta kunna wayar ba? Na rasa me ke damun yarinyar nan??? Yaa Maira ta ce, Ki bi ta a hankali dai, Saadatu na bukatar lallashi har zuciyarta ta samu nutsuwa da auren, kada ki manta baku nemi shawarar ta ko amincewar ta ba, don haka lallashi ne naku ba tursasawa ba, shi ma Yarima gajen hakuri ne irin nasa, ina ce tare za su koma Abujan? Fulani ba ta saurari Yaa Maira ba ta nufi dakin Saade cikin fushi. Ita da Hanne ta same su tana ware sitturunta masu kyau kala-kala daga wardrove tana bai wa Hanne. Suna yi suna hira. Gabadaya ta manta da damuwar da take ciki sabida zuwan Hanne. Ashe ba ki kunna wayarki ba Saa? Fulani ta fada daga bakin kofa. Tana kokarin hadiyefushin ta. Saade ta turo baki gaba irin na shagwababbun yaya, Babu caji ne, amma yanzu zan saka daman. Ya yi kyau!. In ji Fulani, sannan ta juya ta bar dakin cikin fushi. Dakinta ta koma ta dauko wani dandatsetsen leshi cotton mara nauyi kalar maroon da ratsin golden, an yi masa dinkin riga da zani fitted, ta saka Fanna ta saka shi a kabbasa ya turaru tukun ta feshe su da turarukanta na musamman, ta kuma zabo mayafin da ya dace da su kalar golden sannan ta dawo dakin Saade, Hanne ta mika wa kayan, Taimaka mata ta shirya Hanne, tana da baki daga Abuja. Tana gama fadin haka ta juya. Mamaki ya kama Saade, ita yaushe ta yi kawa a Abuja? Kawarta daya Saidu ne, kuma Fulani ba za ta ce ta yi kwalliya saboda shi ba, watakila ya gaji da nemanta a waya ne ya taho har Askira, amma ta ya ya Fulani za ta ce ta yi masa kwalliya irin wannan? Sai ta mikawa Hanne kayan. Bar kayan nan Hanne, Fulani ba ta san wanene ne ya zo ba. Hanne ta ce, Tunda dai ta ce ki saka, to ki saka kawai, baki ganin kin bata mata rai ne?. Ta mika mata zanin, daya bayan daya ta sanya, sai ga Fanna ta shigo tare da wata mata, wadda Saade ta san ta mai kwalliyar Fulani ce during occassions, ta ce, Fulani ce ta turo ta ta yi mata kwalliya. Haka matar nan ta zaunar da ita kan stool ta yi mata wani irin light serene make up, karo na farko da cute fuskar Saade ta ga sassanyan fentin bature, tana kunci tana komai matar bata biye mata ba tunda bisa umarnin Fulani take, a ganin ta ma fushin da Saade ke yi ya kara ma fuskar ta annuri, classique and gentle amaryar Yareema, [inji mai kwalliya cikin ran ta], bada jimawa ba tuni Saade ta fito a beautiful Princess dinta. Matar wadda babarbariya ce ta feshe ta da tsadaddun turarukan humra, sannan Fanna ta kamo hannunta suka fito, Saade ta kasa magana bin Fanna kawai ta ke, Fanna ba ta tsaya da ita a koina ba sai falon saukar bakin Fulani na musamman. Falon shimfide yake da kilisai na alfarma da tumtum a koina, da hoton Mai Askira cikin nadi da amawali windowsize a gabas maso kudu na dakin, sannan zagaye da golden din kujeru na zamani. Har bisa royal chairs na falon ta kaita ta zaunar da ita, ta gyara mata lullubi, sannan ta juya tana fadin, A fito lafiya uwargijiya ta, takawar ki lafiya Gimbiya Saadatu. Fanna ta fita da kamar minti biyu, angon na Saadatu ya bayyana gabadayan sa cikin falon. Yana takun sa na kasaita tamkar mai tafiya akan gajimare. Shalelen Askirama da Ya Gumsu. Kanin Ya Maira da Mairam Murjanatu. Mijin Aisha Sultana. A yanzu kuma angon Saadatu saar mata. Wato [Dr]Yareema Sageer Yusuf Askira. Kamar dama yana falon dake bin wannan tun dazu yana jira. A yau sanye yake cikin royal attire dinsa, shudiyar alkyabba da jamfa na wani rantsattsen yadin filtex, hular kan sa Dara ce baka gashin jikinta na reto daga gefen damana fuskar sa ba karamin kyau tayi masa ba. Tunda Saadatu ta ke a tsayin rayuwar ta ba ta taba ganin mutum maabocin cikar zati, ilhama da kwarjinin Yareema Sageer da ke tsaye nan a gabanta a yau ba. Gabadaya ya canza mata, daga wayayyen dan bokon nan da ta sani mai tsukewa cikin suit da necktayil zuwa hakikanin BASARAKE na gasken-gaske, sarautar ma ta Askira wadda duk yankin Borno babu kamarta. Ji ta yi kamar ta narke a wurin lokacin da Yareema ya tako ya tsaya a gabanta, kamshinsa na Invictus (Paco Rabbanne) da ke hargitsa ta ya mamayi hancinta. Ta sunkuyar da kai ta kasa ko kwakkwaran motsi.Dr. Sageer ya yi taku daya, biyu, ya tsaya a gaban Saadatu, kwalliyar da aka yi mata bai taba ganin ta da ita ba haka kalar kayan jikin ta ya matukar karbar lafiyayyar fatar jikin ta, ya kara fiddo zahirin kyawun ta da kwarjinin ta na Shuwa Arab, duk wani fushi da ya zo da shi da niyyar sauke mata a kan rashin kunna waya tunda aka daura aure, sai ya ji yana melting yana bin rariya, yayin da wata matsiyaciyar soyayya ke maye gurbin sa. Ya zuba hannuwansa duka a cikin aljihun sa, lumsassun idanun sa a kan ta, murya a sanyaye kamar ba Uncle Yareeman da ta sani ba, ya ce, Saadatu laifin me na yi miki ki ka ki kunna wayarki? Atleast mu gaisa ko? Rabo na da ke tun zuwan mu garin nan. Kin san yadda na azabtu a kan hakan? This is sheer punishment! Ba don Yaa Maira ba kenan har mu koma Abuja ba zan ganki ko na ji muryarki ba Saadatu, me yasa? Do you know how difficult and tortured is this to me? Maimakon ta ba shi amsa sai hawaye suka zubo. Ganewa da ta yi cewa Yarima Sageer bai cikin irin bacin ran da damuwar da ita take ciki akan auren bazatan da aka yi musu. Karewa ma ya karbi alamarin da hannu bibbiyu. Har yana fadin rashin ganin ta tun zuwan su gidan ya azabtar da shi. To dama can yana jiran hakan ne ko yaya ne? Ko dama akwai wani abu makamancin so a ran sa da bai taba nuna mata ba sabida girman kan sa? Aka dauke ta a bagas aka bashi don shi dan gatan Askira ne? Hawayen da suka sa Yarima saurin durkusawa a gaban Saadatu ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba. Ya dora tafin hannun sa akan kafar ta. Zuciyar sa cike da fargabar kada dai Saadatu bata farin-ciki da kasancewa cikin iyalin sa? Kada dai hawayen ta na nufin..bata yi naam da zamantowa matar sa wani bangare na rayuwar sa ba? Idan hakan ne a ran ta shi yaya zai yi da rayuwar sa yanzu? Ya riga ya afka a rijiyar da zurfin ta ya fi na gaba dubu. Babu mai iya fito da shi sai Saadatu. Already Saadatu ta dade da mamaye shi, ta mamaye kowanne gurbi da kowanne sako na zuciyar sa ba tareda ya san lokacin da hakan ya fara ba… Ya wayi gari ne ya gan shi dumu dumu a soyayyar Saade. A wannan lokacin hes helpless idan Saade ta ce bata auren sa yaya zai yi? Bai iya sakin ta! Baa saki a gidan su, ko ana yi bai taba sakin Saadatu. Ba kuma ya so ya nuna mata weakness din sa. Ya daga hannu zai rike natafor the first time a tarihin rayuwar su don ya korewa kan sa shakkun kasancewar ta mallakin sa a yanzu, ta yi saurin ja da baya cikin matukar razana! As if lantarki ya jona mata. Tare da maida hannayen ta duka baya ta sarke su a bayan ta. Yareema Sageer Ya daga lumsassun idanunshi yana kallon Saade, a galabaice, a susuce cikin wani yanayi na damuwa da rashin sanin abin cewa. A lokacin ne Saade ta soma shesshekar kuka a hankali, kukan da ya ratsa har cikin kwanya, ruhi da zuciyar Yareema ya hargitsa shi, ya sake kai hannu zai rike ta, ta yi maza ta sake ja da baya. Kada ka kuskura ka taba ni, ni ba zan auri mai yin ZINA ba, Allah ya tsare ni, kuma ba zan kuma bin ka Abuja ba!. Cikin wata irin razana Yarima Sageer ya wara manyan idon sa ya dubi Saadatu, da iyakacin girman su, a ina ta ji wannan maganar? Ya bude baki zai yi magana, ga dukkan mamakin sa maganar ta makale ta kasa fita, kafin ya ankara Saadatu ta mike ta nufi kofa da zummar ficewa. Da wani irin zafin nama Yarima ya sha gabanta, ya kama duka kafadunta biyu ya girgiza ta da karfi. Sai da kashin kafadar ta ya amsa. Bata san sanda tace, zaka balla ni!. A kausashe Dr. Sageer yace. “Kin san da wa ki ke magana Saadatu? Are you scolding me? Hawayen da ke tare cikin idanunta suka idasa gangarowa akan kuncin ta, ta ce cikin karyayyar murya marar amo da rashin karsashi. Im not scolding you. Kawai ina gaya maka abinda na dade da sani ne a kan ka. Na san da wa na ke magana mana; Yarima ne, Yariman Askira, Yarima Sageer mai jiran gadon Askira, amma ba mai halin real Askirama ba Shi Askirama ba ya zina, matan sa ba sa shan giya, ba sa zuwa Bar, sannan suna yin sallah”. Ta bude dukkan idanun ta dake jike da hawaye ta cigaba da cewa A gidan Yarima duk ana yin wadannan abubuwan dana lissafa, don haka babu ni a wannan gidan. Matattarar shaidanu da sabon Allah. In kuma aka takura min sai na bi ka, wallahi zan gudu! Ba za ku kara ganina ba, da ma ba ku san daga ina na zo barana daya kawai kuka ganni a gidan ku, don bani da gata ubana talakane kuma ya mutu, ni sai a yi min aure ba izini na. Saadatu ba ta yi aune ba idanun ta bakidaya a rufe, tana ta zubda rashin kunyar ta ta hanyar fadin duk abinda ya zo bakinta wa Yarima, ta hakan ne kawai zata amayar da kuncin dake zuciyar ta, tunda in ba shi din ba wa zata iya gayawa wannan? Burin ta ya ji haushi ya bar musu sassan su, in yaso kada ya kara dawowa. Ba zaton ta ba tsammani ta ji Sageer ya janyota jikin sa gabagadi da wata irin azama da zafin nama, jikin sa na shaking [tsuma] kamar kamar bai taba rike mace ba a tsayin rayuwar sa sai wannan karon. Har kuma ran sa da zuciyar sa abinda yake ji kenan a zahiri. Kafin ta yi kokarin zamewa ko kwacewa sai jin taushin bakin Yarima Sageer ta yi ya sauka a kan nata ya sima sumbatar ta in an abrupt manner, wanda hakan ya rufe sauran bakar maganar da ta ke so ta furta. Cewa ita a rasa wanda zaa aura mata sai mai yin zina? Ba gara Saidu ba? Kafin ta tantance what is going to happen next? Dr. Sageer ya soma hawaye, bai taba nadama ba akan rayuwar sa irin yau, gabadaya jikin sa yayi sanyi da kalaman Sa'adatu, ba tare da yayi shawara da zuciyar sa ba ya fara sumbatar ta gently, expertedly, and then by dragging her closer, sai ya cigaba da kissing dinta softly, then a urunce wato [da sauri da sauri]. Tun daga karkashin zuciyar sa sautin sumbar take fitowa tana bada sauti. Duk kokarinta na kwatar kanta hannun Yareema ta kasa sai da ya yi sumbar mai isar sa tukunna, ya sanyata cikin jikin sa a hankali ya rungumeta tsam-tsam ta hanyar hada bugun zuciyoyin dake cikin kirjin su wuri guda, inama zata iya jin tari nadamar dake cin ran sa daga bugun kirjin sa? Yana yi yana sauke kakkarfar ajiyar zuciya. Sai kuma ya bi hawayen fuskarta yana dauke su tsaf da lips din sa. Ya dago fuskar ta da hawaye kadai ke zuba tana kakabin abinda ke faruwa a mafarki ne ko ido biyu? Dr. Sageer ya sanya fuskar ta cikin tafukan sa, sannan ya sake ta ya ja da baya kadan yana jifanta da wani irin sassanyar kallo, wanda Saadatu ba ta taba gani a tare da shi ba. Gabadaya ya rikide mata ya koma tamkar ba shi ba. Ga dai nadama ce fal da tsoron rasa Sa'ade a ran sa tunda ta san ko wanene shi, amma abinda ya furta ba lallashi bane ba kuma nadamar dake baibaye da shi bane. Yarima Sageer is always bold, baya yarda ya nuna weakness din sa a komai. Kin fara da kissing mai yin zina Saadatu, kafin ku sha giyar tare ke da matar sa. Daga nan ku zarce BAR din ke da ita ku sha ku yi mankas ku dawo gida ina jiran ku. Na bar ki lafiya sai mun hadu a kauyen naku na Tsanyawa in kin gudu, amma ina rokonki don Allah in kin tashi gudun, ki fi ruwa gudu. Ya zuba hannuwa cikin aljihu yana kara jifarta da killing smile dinsa wanda shi kadai ya iya abunsa, ya kuma san maanarsa. Bai tsaya sauraron amsarta ba ya juya cikin sassarfa da takunsa na haiba da mulki ya bar falon. Ya bar Saadatu a tsaye kamar an kafe ta a wurin. Ta kai hannu ta shafo kasan lips dinta a hankali. Damshin yana nan. Haka kamshin mouth freshner din bakin sa yana nan. Shin abin da ya faru yanzun da gaske ne ko a mafarki ne? Ta yi kissing da mijin auren tafor the first time a rayuwar ta? Kuma ba kowa bane Uncle Yareema ne, guardian din ta na NTNU Dr. Sageer Yusuf Askira? Ta fi karfin minti goma a tsaye, ta kasa maida nutsuwarta, ta kasa yardar wa kanta abin da ya faru ba mafarki bane, ta dauki everything as an illusion. Kafin ta ja matattun kafafunta ta zauna. Me wannan ke nufi tsakaninta da Yareema Sageer? Ba dai wannan shi ne rayuwar kusancin da ake nufi yanzu zasu yi tare har abada ba, maimakon tasu ta Guardian da step sister irin ta baya? Koda take yarinya karama ta san me aure yake nufi a darasin biology. Kawai sai ta ji kuka ya kwace mata. Shikenan ita tata ta kare. Ta zauna a dandaryar kafet ta yi kukanta mai isarta. Kanta cikin cinyoyinta, kan ta har sarawa ya shiga yi. Fanna da ke jiran fitowarta daga daya falon, ta ga fitar Yarima da sassarfa da jimawa, da ta ji shiru-shiru Saadatu ba ta fito ba, sai ta biyo bayanta ta same ta a zaune tsakiyar kilishin falon tana ta kuka. A zuciyarta ta ce, Dole ki koka Saadatu, wannan mutumin ya fi karfinki ta koina. Da dai sun barshi da bayahudiyar matarshi ita kadai zata iya dashi, amma ina innocent yarinya irin Saade ina fitinannen Yariman Askira? Tun suna yara suke da labarin sa cikin gidan nan, wa ya san irin rayuwar da yake yi a Abujar? Fanna ta tsugunna da gwiwa bibbiyu a gaban Saade, cikin lallashi da ladabi ta ce, Ranki ya dade ki yi hakuri ki tashi mu koma daga ciki. Tana so ta gaya wa Fanna damuwar ta. Don ta san ita kadai ce a yanzu zata saurareta har ta fahimce ta. Ko ta fada mata abin da Yarima ya yi a gare ta yanzun nan, da abin da ya ce da ita, amma sai ta ji ta kasa. Maganar ta yi mata nauyin da ba za ta iya furtata ga kowa ba koda kuwa Fulani ce. Ta mike cikin mutuwar jiki, Fanna ta kama hannunta suka koma ciki. Ta gaban Fulani da su Inna Laure da ke zaune suna raba kayan daFulani ta diddinka musu suka wuce zuwa dakin Saaden. Fulani ta daga kai ta dube su. Idanun Saade jawur da alama ta ci kuka ta koshi. Ko me aka yi mata kuma? Fulani ta fada a ran ta. Suka wuce zuwa dakin Saade inda suka tadda Hanne tana gyara dinkunan Saaden da aka kawo daga wajen dinki. Fanna ta koma bayan shigar Saade daki. Bisa gadonta ta haye ta ja duvet ta rufa har saman kanta. Ba ta son magana da kowa, don ko Hanne ba ta jin za ta iya gayawa abin da Yarima ya yi mata wanda ya kara tsoratata da auren. Ita ma Hanne har ta gama abin da ta ke ta yi wa danta shirin kwanciya ba ta tambaye ta komai ba. Fulani ta so ta kira ta don ta ji dalilin kukan da ta fahimci ta yi, wata zuciyar ta hane ta. Gara ta bar Saade ta koyi rike sirrin auren ta yanzu girma ya hau kanta. In dai ba matsala ce wadda ta zama dole su sani ba. Washegari duka gidan ya rikice da hayaniya ana shirye-shirye. Kowa da ke cikin masarautar nan ya ci wa bikin nan na Yarima buri da alwashi don huce haushin wanda ba a yi ba a aurensa na farko. Maimartaba ya aika da goron gayyata zuwa dukkan masarautun Borno guda bakwai, (Bama, Borno, Dikwa, Gwoza, Shani, Uba sai kuma Askira wadanda su suka hadu suka bada Borno Empire. Hakan nan ya aika da sakon gayyata har fadar Shehun Borno don haka Mai Askira ba karamin shiri yake wa wannan auren ba. Duk wani gyara da ake wa amare na kayan mata Fulani ba ta yi wa Saade, banda Su dilke su halawa da dukhan kafin a mata lalle, (mai gyaran jikin Fulani daga maiduguri ta zo ta mata gyaran jiki), a cewarta Saade yarinya ce sai nan gaba in ta kara shekaru koda zata bata kayan mata, duk da tana tantama idan Yarima zai daga kafar yadda ya alkawarta. Kodayake fa bai bata cikakkiyar amsa ba akan hakan in zata iya tunawa cewa yayi zai duba. Ta yi ajiyar zuciya cike da tausayin Saade, ta san duk ranar data shiga hannun Yareema sai Allah. Tunda dan Askirama ne. Ranar talata, wato ana i-gobe sakun lalle Saade ta fito wanka tana busar da lallausar gashin kanta da dryer don ta cire wa kanta damuwar Yareema ko aurensa yanzu, ta hada su su duka ta zuba a kwandon shara, ta sa a ranta ba inda za ta yarda a kai ta, ko dai a barta nan a gaban uwarta ya koma gidan sa shi kadai yayi ta auren, ko ta bi su Innar Hanne su koma Tsanyawa ta yi zamanta a gidan su Hanne. Karatun ta hakura ta yafe in dai sai ta amsa sunan matar Yareema Sageer. Ina ita ina zama da yar giya matsayin kishiya? Ta je bar din ta ta dawo ta rotsa mata kai? A hakan ma kowa yana zaman kan shi ya suka kare balle suna zaman auren sa su duka? Wannan shine tunanin Saade. Wata siririyar muryar budurwa ta yi sallama daga bakin kofa, da yakeSaade ta bada baya ne tana fuskantar mudubi, amma jin wannan murya ba ta san lokacin da ta yi azamar juyowa ba, muryar sounds so familiar a kunnenta. Murya ce da ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta manta mai ita ba. Tana tsaye jikin kofa, harde da hannayenta a kirji, yar gaye da ita kyakkyawa sai murmushi ta ke. Ta kara tsayi da haske, ta murje sumul fiye da sanin da Saade ta yi mata. Idanun Saade suka bubbude gabadaya, ta saki dryer din hannunta kasa, kafin ta tafi da mugun gudu ta rungume RAHEEMAH. Fulani ta shigo, a bayanta wata mata ce da akalla za ta girme ta. Kyakkyawa da ita, da ganinsu ka ga mazauna kasar sanyi, sai kannen Rahima su biyu Sarina da Jamila. Kallo daya Saade ta yi wa matar ta gane mahaifiyar Rahima ce sabida tsabar kamannin su, wadda Rahima kullum ke kira da “Mama”. Ta saki Raheema ta tafi ga Mama za ta tsugunna, Mama ta yi saurin riko ta a jikinta, sannan ta rungume ta. Cewa ta ke, Masha Allahu, yau ga ni ga Saar Raheema, Saadatu Saar Mata! Ta kama su ita da Raheema ta rike a jikinta, Sarina da Jamila sai murmushi suke mata. Ta tafi gare su suka rungume juna don dai ita duk wani ahalin Raheema tana sonsa a kan dalilin da zuciyarta har yau ba ta sani ba. Raheema shi ne ki ka gudu daga El-Kanemi babu ko sallama, babu notice? Na shiga damuwa Raheema, zaman makarantar ya fice min a ka saboda rashinki. Na dade kafin na saba da rashinki Raheema, nayi kewar ki yadda harshe na ba zai iya bayyanawa ba, don Allah kada ki sake tafiya ki barni Raheemah. Sai kuka. Raheema tana share mata hawaye da tafukanta, ta ce, har yanzu kina nan da kukan wofin kin nan ko? Is o.k Saadatu. Im here now, da ni za a sha shagalin biki, ba zan tafi ba sai na raka ki dakinki. Ni ma ba da son raina muka koma Italy ba, kuma ban samu damar dawowa El-Kanemi don in miki sallama ba. Ki yi hakuri. Sannan ne suka zazzauna a kasa, iyayen na daga gefen gado suna kallon su withaffection. Nan Fulani ta gaya wa Saade labarin da ya girgiza zuciyarta, cewa ita da Raheema yan uwa ne na jini, da mahaifinta da mahaifin Raheema uwarsu daya ubansu daya. na dade da gane hakan ban dai gaya miki bane tuntuni, don in Baban Rahimah ya san ke ce ba zai bar ki hannu na ba. Saade sai ta ji duk wata damuwar duniya ta yaye mata. Feeling din da mutum ke ji idan ya san cewa yana da dangi na jini kuma na halali. Lallai da ake cewa wani farin cikin ya fi gaban kuka, sai dariya. Ta zama kamar wata karamar zararriya don murna. Ta rungume Raheema, ta saki ta rungume Sarina, ta saki ta kamo Jamila ta rasa inda za ta sa su don kauna, su kuma sai dariya suke mata, don sun riga ta jin labarin tun suna Italy. Maimartaba ya kira Fulani a waya ya gaya mata ta sa a rako Saade da Rahima falon saukar bakinsa ta gaisa da Babanta, wato Alhaji Kyari Babagana. Tare da Fulani suka tafi har falon ganawa ta musamman da bakin Maimartaba Sarkin Askira. Kallo daya ta yi mishi ta hango kamanninshi da mahaifin ta Malam Hashimu, saboda jini ba ya buya. Har kasan kafafunshi ta je ta zauna ta gaishe shi a ladabce. Shi kuma ban da kallonta da tasbihi ba abin da yake a fili, tamkar Bilkisu ta yi kaki ta tofar, ko kadan ba ta debo dan uwansa Hashimu ba ko da da kalar fata ne. Sai yanzu ya tuna kallon sanin da yayi mata a ganin sa na farko da ita a El-kanemi. Ashe fuskar Bilkisu ya hango cikin idanun ta. Alhaji Kyari ya ce, Madallah da yata mai albarka, Allah ya sanya alkhairi da albarka cikin aurenki. Allah ya hada hankulanku, Ya bada zaman lafiya. Ba ta iya ta amsa wannan adduar ba, saboda nauyin da ta yi mata a zuciya da kwakwalwa. Idan ta ce, ameen, Allah ya amsa adduar fa? Aurenta da Yarima ya zama tabbatacce ba mafarki ba kamar yadda ta ke kallonsa? Duk da Yareema Sageer ya tabbatar mata cewa, reality ne, ta hanyar da bata taba zato ba, kuma ba shi da alamun ja da baya daga hukuncin iyayensu? Don haka ya rage nata ta cigaba da yaudarar kanta da kanta, da cewa mafarki ne. Sun dade yana mata tambayoyi tana ba shi amsa a kan marigayi da rayuwarsu a Tsanyawa, karatun da ta ke yi a yanzu a NTNU da kuma burin ta na yanzu wato barin karatun ta zauna a gida. Daga shi har Askirama suka hada baki wajen tambayarta, Saboda mene za ki bar karatunki Saadatu? Ko shi Yareeman ne ya ce ba ya so? In ji Maimartaba, sounding worried da hukuncin Saaden, duk da ya san hakan mawuyaci ne a matsayin Yareema Sageer na malamin jamia cikakke ya ce ya hana matar sa karatu. Saade ta bude baki a hankali kamar mai ciwon makogaro, ta ce, Saboda na fi son in ci gaba da zama a Askira, bana son komawa Abuja Alanguburo. Fulani ta ce, Babbar magana, mijinki yana wani gari ke kina wani gari, a dalilin me? Maimartaba ya yi saurin cewa, Ya isa Fulani, Saadatu za ki zauna a gidan Yarima na Askira har ki kare hutunki? Inyaso daga baya sai mu raka ki Abuja da kanmu ni da Fulani ki koma makaranta, kin amince? Askirama ya yi maganar cikin lallashina uba mai tsananin kulawa. Kaunar da Mai Askira ke nuna mata da yawan alkhairinsa gare ta ya fi gaban ya yi hukunci ta ce, aah. Sauran zai kasance ne tsakaninta da Yarima, tunda shine bai ce shima baya son auren ba, yayi uwa ya yi makarbiya ya amshe auren, ita ta fada a ce ta yi rashin biyayya, da kyar in Fulani bata bubbuge mata baki in ta fada hakan a gaban Askirama ba, amma tsakaninta da Askirama babu jayayya. A hankali ta gyada kai alamar ta amince, idonta kuma ya cicciko da kwalla. Amma ta yi kokarin maida su sabida Askirama. Ko yayan da ya haifa ba ta taba jin ya raka gidan miji ba ko ya je gidajen auren su. Amma ita ya ce shi da kansa zai kaita. What an honour! Wannan ba karamin girma ne da kulawa ya ba ta ba. A wannan daren daga Raheema har Saade sai goshin asubahi suka kwanta. Labarin juna suke bai wa juna. Inda Raheema ita ma ta sanar da ita ta samu miji a Damaturu suna karatu tare a jamiar Heartfordshire, U.K. sunansa Usman Bello Jajere. (Jajere garin fulanin Damaturu ne suna da kyau farare ne kuma suna karatu sosai yan garuruwan Jajere da Kollere. Yan Jajere kan yiwa kan su kirari da Jajere garin jajaye in ka ga baki to bako ne), amma aure sai ta gama karatu, shi kuma ya dawo gida ya yi service. Ba abin da Saade ta tuna a lokacin sai Saidu, da yanzu ita ma yaro dan makaranta kamarta za ta aura, ina ma ta bawa Saidu damar da yake nema tuntuni tana gwasale shi? Yanzu gashi girman kanta ya sa an dauki mijin wata an ba ta wanda a haihuwar kauyensu Tsanyawa ya haife ta. Allah kadai ya san irin farin cikin da Usman zai sa Raheema, ita kam yanzu sai dai ta je ta yi ta fama da yar giya Wannan tunanin ya fiddo hawaye daga idon Saade, wanda Raheema ta nace sai ta ji dalilin saukarsu. Don bata ga dalili ba. Saade ta tuna cewa, wannan Raheema ce, mai kaunarta da zuciya daya tun tana bakauyiyar ta, kuma yar uwar da ba ta da kamarta a yanzu. Babu wanda ya dace da sanin halin da zuciyar ta ke ciki a halin yanzu ya kuma fahimceta ya bata shawarar data dace kamar Rahimah. Don haka Saade ta gyara zama, ta warwarewa Rahimah komai a kan rayuwarta gidan Yareema Sageer, da halin da matarsa ke ciki, irin kyautatawar da yake mata, girmansa da ta ke gani, har da labarin Said sai da ta bata. Amma ta rasa dalilin da ya sa ta kasa ce da Raheemah Aunty Sultana na yawan cewa Sageer yana neman mata. Maganar ta yi nauyi sosai a bakinta tunda ba ta taba gani da idonta ba, shaidar zina kuwa sai ka kwana a ciki in ba ka yi taka-tsan-tsan ba. Ta gaya wa Raheema damuwarta shi ne ba ta taba jin wani abu a zuciyar ta a kan Yareema ba, bayan na kasancewarsa guardian dinta a Abuja. Ita a wurin ta Uncle Yarima Yayanta ne mai kula da alamuran karatun ta. Rana daya ta ji labarin aurensu daga bakin Fulani bagatatan kamar saukar aradu, ita ta fi son in auren ne ma a aura mata Saidu ba za ta damu ba, shine tsaran auren ta daidai da rayuwar ta ta yar talaka. Amma ina zata kai YARIMAN ASKIRA??? Raheemah Kyari, ta yi wani irin lallausar murmushi. Ta kama hannayen Saade ta rike cikin nata. “inda kowacce mace take kai mijin ta Saadatu! Ina ma ni ce ke Saade! Ki yarda ba tun yau ba cewa you are among the luckiest. Auren matured men shi ne aure, wadanda suka san ciwon kansu, ki rabu da samarin nan yan rawar kai ki kama mijinki da iyayen ki suka zaba miki kin ji? What is your own business da rayuwar matar sa? Kuma tunda Fulani ta ce ya raba muku gida, kuma ya amince, ina ruwanki da matarsa? Wannan rayuwar su ce shi da ita bai shafe ki ba.” Saade ta zumburo baki, Raheemah ba za ki gane ba. I have no feelings a kan Yareema Sageer, na dauka zaman auren sai da feelings din soyayya yake yiwuwa??? Raheema ta girgiza kai, ta ce, inji wa? Saadatu, ki gode wa Allah kawai, ki kuma hada da addua, ki roki Allah ya sanya miki soyayyar mijinki, kuma zabin iyayenki. Soyayya da kike ambato shirme ce, cike take da unbearable challenges, aure daban soyayya daban, sai kin yi auren soyayyar in gishiri ya sauka daga kan kaza za ki gane shayi ruwa ne. Above all kin ce kina ganin girman Yareema, to magana ta kare. Along the way soyayyar za ta zo, irinki in ku ka tashi soyayyar ma mahaukaciya ku ke yi, kuma makauniya, tunda kin ce ba ki ga alamun shi yana kin auren ba. Muryar Saade abin tausayi ta ce, Sai ma kin ji bakar maganar da ya gaya min da na ce ba zan koma Abuja ba zan gudu kauyenmu he was like (in yi ta gudu, in fi ruwa gudu, giya in shirya sha tare da matarsa) meaning bai dauki maganganun nawa da wani muhimmanci ba. Raheema ta yi dariya sosai, ta ce. I would like to see Yarima Sageer. Sister you are blessed for having him as a husband, ina son brave men, wadanda suka yarda da kansu, cika baki ko rikicin mace ba ya razana su su ja da baya a kan soyayyar su. Ni ma sai in ce, Sai kin dawo, a gaida mutanen Tsanyawa. Saade ta kai mata bugu ta goce tana mata dariya. Muryar ta abin tausayi tace. Wato dai Raheema kema kina bayan in auri mai mata ko? Ta je bar ta dawo ta yi min dan karen duka? Dariya sosai Raheema ta sake yi, ta ce, Tunda ki ka ce ga inda ya auro ta kuma ga asalinta me ye abun mamaki don ta sha giya? Su fa yadda muke shan soft drinks, haka suke shanta don baki taba fita ketare bane, canjin addininta ba zai sa ta iya dainawa farat daya ba, tunda dai ba shi yake sha ba shi kenan falillahil hamdu, ki yi mata addua Allah ya sa tana da rabon dainawa. Sai kiran sallar asuba suka ji a kunnuwan su, dole suka mike don bada farali. Daga nan kuma suka kwanta, Hanne sai barcinta ta ke hankali kwance bisa katuwar katifa ita da danta Naziru. ***** Washegari aka tashi da event na farko, wato sakun lalle. Masarautar ta cika ta batse da yan uwa da abokan arziki da baki da aka gayyato daga masarautu daban-daban, ga kuma alummar garin Askira wadanda ma ba a gayyata ba. Da ma in dai biki na gidan sarki ne ba sai an gayyace su ba, kwansu da kwarkwatarsu suke tahowa daga gidajensu zuwa gidan Sarki. To balle auren Yareema Sageer kuma wanda Maimartaba da kanshi ya shelanta gayyatar ga kowa da ke Askira, bayan saukowa sallar jumaa a babban masallacin jumaa. Don haka ba a taba ganin taron bikin da ya hada jamaa irin na yau ba a masarautar gabadaya. Tun daga kan auren su Yaa Maira har zuwa kan na yar sarki ta karshe da aka aurar Najaatu. An saka amarya a lalle lafiya, Raheema da Hanne da kanwar Raheema Sarina sune kawayen amarya. Washegari alhamis aka yi NIYA wato ranar yin royal snacks su nakiya, alkali, dubulan, bakilawa da sauransu daro-daro don raba wa mutane. Ranar jumaa aka yi WUSHE-WUSHE. A babban filin dake cikin fada aka kira decorators suka tsara shi yayi kyau sosai. Wushe-wushe shine wuri daya da Yareema da Sa'ade Zasu hadu a duk tsawon bikin su, makada ne aka gaiyyato daban daban daga garuruwa daban-daban ciki har da HajjaGumsu da yaran ta da suka zo daga Maiduguri. Sai da aka taru ana kade-kade ango ya zo cikin manyan kaya da abokan shi karkashin rakiyar Awaisu Ibrahim Waziri da kuma sisters din shi mata su Mairam Murjanatu, Yaa Maira and co.zagaye da shi cikin laffaya mai hasken sararin samaniya suna rike da kaskon turaren wuta suna turara shi, makadan fada na biye da su,suna kide-kide da bushe-bushe suna wake Yarima da amarya Saadatu har su ka kai shi mazaunin da aka tanadar musu shi da Saadatun. Abokanen shi kuma aka yi musu shimfidun kilishi na alfarma daga gefen sa, sannan su yan uwan shi mata su kuma suna zaune inda aka tanadar musu. Sai aka cigaba da wasa da kide-kiden cikin zakuwar fitowar amarya, wanda yawanci sai an dan ja lokaci sosai kawai dan a ja wa ango rai, haka aladar bikin masarautar Askira ke gudana a kowanne bikin dan sarki. Saade an shirya ta cikin laffaya an rufe ta ruf har kai. Sannan kawayen ta su Rahimah da Hanne sun saka ankon dongasho da su murjani sun rike kaskon turarukan wuta suka sako ta a tsakiya kamar yadda aka koyar dasu.Maman Rahimah da Innar Hanne na rike da ita cikin rakiyar kide-kide har aka kai ta aka zaunar a gefen Yarima Sageer, wanda a lokacin da Saade ta zauna a gefen sa sai da ya dauke numfashin sa na wucin-gadi. Kawayen ta kuma by her side akan shimfidundake kallon na abokan ango. Daga nan sai aka cigaba da kide-kide da wasanni.Saade bata yarda sun hada ido da Yarima ba duk kokarin sa ga son faruwar hakan, bata ma bude fuskarta daga cikin laffaya ba, duk kokarin Yarima Sageer na son gano halin da kwayar idon ta ke ciki a wannan lokacin hakan bai yiwu ba. Tana jin sanda Uncle Sageer da yan uwan sa mata da maza da abokai suka yi ta yi mataruwan liki. Har tsakar dare ana wannan shagalin kafin taron wushe-wushe ya tashi. Kuma Yarima bai samu damar ganin Saadeprivately ba har su Maman Rahimah suka kama ta suka koma cikin gida. Ranar asabar kuma aka yi KELATUL wato aka wanke wa amarya gashi aka yarfa mata kitson bare-bari kanana-kanana sun kai guda dari uku. Da yammacin ranar kuma aka yi biji-ginata inda aka shimfida manyan tabarmi aka ajiye amarya a tsakiya ana kida ana wakoki irin na barebarin Askira. Bayan an yi mata kwalliyar masarauta. Ranar lahadi aka yi kaulu na amarya da na ango da safe. Kaulu shi ne za a ajiye miyar yauki a gaban amarya bayan an mata kitso da kwalliya. Baaba suka goya amarya suka kai ta filin da ake yin kaulu. Yan uwan Yareema na ciki daya da na sauran dakunan suka dinga dibar wannan miyar yaukin suna shafa mata, sannan daya bayan daya suka zo suna ajiye mata kyaututtuka na bajinta haka sauran matan Maimartaba. Da yammacin ranar aka yi dubdo, wato wunin biki a harshen Hausa. Biki ya yi biki ba ka jin komai a masarautar Askira sai kade-kade da bushe-bushen algaita. Duk wadannan events din da ake yi ango bai ga fuskar amarya ba, kuma Fulani Bilkisu ita ke da alhakin yin miskero, wato abincin da ake kai wa gidan amarya. Kuma ita ke ciyar da ango da amarya dadadan girke-girke masu kara lafiya da kuzari. In ta girka sai kuyanginta su kai sassan Yareema su ci shi da Awaisu. Korafi kam Awaisu ya sha shi gurin Yareema, kan cewa shi fa bikin nan ya ishe shi hayaniya ta yi masa yawa. A ba shi amaryarshi kawai su kama hanya. Shi ba auren fari ba to wadannan aladun duk na menene? Awaisu sai dai ya yi murmushi don ya gama gane Yareema Sageer ya karbi auren nan da hannu bibbiyu. Har fiye da auren sa da baturiyar sa mai kananan ido. Auren da yake kira na soyayya kuma babu ya shi. Abin da bai sani ba, kuma yake matukar son sani shi ne, da ma can Yareema yana son Saade ne ko sai da aka ce an aura masa ita ya fara son ta?? Sai da Baaba (kannen Maimartaba mata) da kannen Ya Gumsu suka shigo tafiya da amarya ne idonta ya karasa raina fata. Domin a baya kallon komai take matsayin almara ko mafarki. Saadatu ta kankame Fulani tana ihu sosai ita ba inda za ta je ta bar Fulani. Sai yanzu ne ta tabbatar da gaske an yi mata aure, kuma ba da kowa ba da Yariman Askira, Uncle Yareeman da ta ke girmamawa fiye da kowa in ka dauke iyayenta, Dr. Sageer a NTNU, kuma mijin Aisha-Sultana. A karshe Baaba sai goya amarya suka yi tana kuka tana komai, kannen Yareema mata su Houdda sai tsiya suke mata, ko irin nasihar nan ta uwa Fulani ba ta samu damar yi mata ba sabida kukan da ta ke tun safe ya daga mata hankali. Su Mama (Babar Raheema) da su Raheeman suna gidan amarya tun safe inda ake aikin jere da kafi. Duk wasu furnitures da aka zuba a sassan Saade dake gidan Yarima Alhaji Kyari ne ya taho da su tafiyayyu daga kasar Italiya, wadanda Maimartaba ya yi mata an wuce mata da su Abuja. ****** SAADE A GIDAN YAREEMAN ASKIRA Daga ita sai Hanne da Raheema a bedroom din da aka zaba aka shigar da ita, wanda shi yafi kowanne kayatuwa, sai kuyangi da bayin Fulani da ke ta kintsa duk inda aka bata. Fadin dukiyar da Askirama ya dankara a gidan Yareema Sageer bata baki ne, ki sa a ranki gidan Yariman Askira mai jiran gado, shi ke nan zance ya kare. Gida ne ginin sarauta (royal mansion) wanda aka yiwa zubi na zamani,turawa suka zana shi suka kuma zo suka gina daga Amsterdam, da aka yi wa sassan matan aure har hudu, komai da ke cikin wannan sashe shi ne a wancan sai bambancin kalar fenti. A sashen kowacce mace manyan faluka ne bi-da-bi har guda Uku da dakunan barci Uku. Babun ce kawai babu a gidan Yarima Sageer Yusuf Askira. Sassan Aisha Sultana shi ne na farko, sai na Saade sannan wasu guda biyu a rufe. An ware bangaren bayi da hadimai daga can karshen gidan. Sassan Yarima kuma yana upstairs wanda girmansa ya yi a hada sassan matan nasa guda biyu. Komai da ke cikin sassan Yarima ya zo da shi ne daga Amsterdam kuma duk bayan shekaru biyu ake fidda komai na gidan a sake, a yo odar wasu. A raba wa talakawan gari, ko bayi da hadimai. A can gidan Wazirin gari Ibrahim a dakin Awaisu Yarima Sageer ne tsaye jikin mudubin dogon yaro yana sanya links din hannun farar shadda kal da ya saka, sai tashin kamshin invictus dakin Awaisu ke yi. Awaisu ya kasa danne dariyarsa ganin irin kwalliyar da Yareema ke yi wadda ko ranar da zai raka shi dakin Aisha-Sultana bai yi irinta ba, ya karkata hula ya sake karkatawa yafi sau biyar, ya ga bata yi kyau ba ya cire ya sake canza wata, [to wancan aure ne da aka riga aka kwashe albarkarsa tun a waje]. A ransa Awaisu godiya yake wa Allah yana kuma adduar Allah ya sa auren nan ya zamo karshen duk wasu matsaloli na dan uwansa Sageer. Amma dai sai gobe za mu je sayen baki ko? Ka ga yanzu dare ya yi sosai, na san duk sun yi barci bai kamata mu tada amarya ba tana barcin gajiyar biki irin wannan. Inji Awaisu cikin seriousness. Wata harara da Yarima ya juyo ya zuba masa sai da ta sa Awaisu durkushewa a inda yake yana dariya. Kafin ya dago daga dariyarsa Yarima ya gama saka takalmansa ya fice yana fadin. In ka ga dama kada ka je, da ma ba ni na gayyace ka ba, aure dai ka sani ba yau na fara ba balle ka ce rawar kafa na ke yi. Awaisu bai bar dariya ba da ma gwanin ta ne, ya saka takalmansa ya bi bayan Yareema Sageer yana cewa, Ko don in bata maka lokaci kafin ka shiga dakin Sa'adatu dole in bi ka. Yarima ya girgiza kai jin abinda Awaisu ya ce, ya ce, Awaisu! Mind your language. Saadatu is my step-sister rainon ta na yi wa uwarta alkawarin zan yi, kuma shi zan yi din. Zan ba ka mamaki, jibi-jibin nan zan koma wurin mata ta. Awaisu don dariya har da hawaye, ya ce, Aah Yarima, kada wata tara ta cika kuma mu zo bikin radin suna, wannan rainon in dai kai za ka yi shi Saadatu ba za ta taba girma ba. Suna ta barkwancinsu na aminai har suka karaso gidan sarki, don Yareema ya ce sai ya je ya yi wa Ya Gumsu sai da safe, ya kuma nemi albarka kafin ya karasa wajen Saadatu. [Da ya san abinda zai tarar, da ya yi wucewar sa kai tsaye dakin amaryar sa, in ya so da safe ya zo tasani]. Dazu da yamma Yaa Maira ta kira shi cikin sirri sun yi magana, inda ta ce ya bi Ya Gumsu a hankali da duk abin da ta ke so, don ba karamin yaki ta yi da ita kafin ta amince a yi bikinnan cikin dadin rai ba. Yarima ya yi sallama a hamshakiyar turakar mahaifiyarsa Ya Gumsu, Awaisu bai biyo shi ba ya zauna a mota don ya ba shi dama ya gana da Ya Gumsu. Tana hakimce bisa kujerar mulkinta sai karkada kafa take yi cikin izza lokacin da Yarima ya yi sallama. Ta hadiye wani malolon abu da ya tokare ta a makoshi ganin irin kwalliyar da ya caba da bata taba ganin sa cikin irin ta ba, wanda ke nuna yana farin ciki da auren diyar Fulani Bilkisu. Har kasan kafafunta ya isa ya gurfana yadda suke gaida iyayensu, ya yi gaisuwa ta amsa cikin dacin rai. Daga nan duk suka yi shiru. Yarima ya kasa ce mata ya zo neman albarkarta ne zai shiga dakin amaryarsa, aka ce wargi ma wuri shika samu. Ita kuma tana ta kitsa abubuwan da ta shirya fada masa ba tare da tunanin me zai je ya zo ba. Ya Gumsu ta dubi dan ta Dr. Sageer wanda kansa ke sunkuye a gabanta. Ji yake kamar ya yi fiffike ya fice ya tadda Saadatu. Shi kansa ya rasa ko wane irin excitement yake ciki mai neman karar da numfashinsa. Zuciyarsa har wani irin bugawa ta ke yi in ya tuna Saadatu zai je ya tadda a matsayin matarsa yau, ba yar amanar da yake riko a gidansa ba kullum yana fama da zuciyarsa a kanta. Sai jin muryar Ya Gumsu ya yi a tsakiyar kansa. An yi aure na gani, kuma na sa albarka kamar yadda Yaa Maira ke so. Maimartaba ma yake so, amma Yareema ban yarda ka taba yar Bilkisu ba. Ina nufin ban yarda ka hada shimfida da ita ba, don kuwa jinina ba zai gogi jinin Bilkisun Askirama ba. Balle in hada zuria da ita. Na ba ka watanni uku ka zo ka kara aure, aure na mutunci na gidan mutunci, duk wadannan matan naka tarkace ne, tunda babu jinin sarauta ko daya a cikinsu. Na samo maka mata yar Sarkin Bauchi, sunanta Hajjaju, mun gama magana da mahaifiyarta ta ce kana iya zuwa ku fara fahimtar juna, in dai da gaske ni na haife ka Yarima wannan shi ne umarnina. Ta mike ta shige turakar barcinta ta rufo kofa ta bar Yarima sai tsiyayar zufa yake daga tsugunne, ya rasa inda zai sa kansa. Don kwata-kwata bai fahimci inda zancen Ya Gumsu ya dosa ba, ko kuma ya ce ya fahimta, kwakwalwarsa ce ta kasa fassarawa. Ya Gumsu na da masaniyar cewa weakness dinsa shi ne Mace. Macen ma ta aurensa wadda zuciya da ruhinsa ya dade yana so da kwadaituwa akan ta, to in ta ce ba zai tabbatar da aurensa da Saade ba, neman matan ta ke so ya koma wanda ya yi wa Maimartaba alkawarin ya daina? Ya yi wa Ubangijinsa alkawarin daga ranar da ya mallaki Saadatu ya daina? Wane irin aure sai ka ce namamajo, aure wata uku ya zo ya kara aure wai Hajjaju? Yo shi ko sunanta Makkah ina zai kai ta duk son matansa? Guda biyun sun ishe shi sabida shi ba wai mata yake so ya tara ba, in ya samu abunda yake bukata a guda daya zai iya kama kan sa. Abin da ya rasa daga matarsa Aisha-Sultana (sai jar fata da yalolon gashi) wanda ya kai shi ga bin son zuciyarsa da zugar aboki Ziyad maimakon ya nemi karin aure. Rana daya Mai Askira ya hutar da shi da yake shi uba ne mai tsinkaye, mai son gyara rayuwar yayansa ba ya dagula ta ba irin Ya Gumsu. Shi bai dauki wannan auren da ta ke son yi masa gata ba, sai hanyar huce haushinta a kan auren diyar kishiyarta Fulani Bilkisun Askirama. Amma ya sani a yadda Ya Gumsu ta ke kan dokin zuciya irin wannan, ba wasu kalaman lallashi da zai yi amfani da su da za su sa ta saurare shi. Mafi aala ya nisance ta har sai ta huce, tunda dama ga alfarmar da ita ma Fulani Bilkisun ta nema daga gare shi, na cewa zai bar Saadatu ta gama makaranta kafin ya dora mata nauyin aure. Jiki a salube Yareema Sageer ya baro turakar Ya Gumsu, ya tadda Awaisu a mota, bayan dogarai sun bude masa ya shiga, Awaisu ya ja motar ta kofar shiga gidan Yareema ta baya suka bi, duk da cewa ba wata tafiya ce mai nisa ba, trackable distance ne daga masarautar. Hanne, Raheema da Saadatu ne kadai a dakin, Hanne da Raheema hirar tsaruwar gidan Saadatu suke yi da komai da ke cikinsa. Yayin da Saadatu ke ta kuka har zuwa lokacin, tun suna lallashinta har sun gaji sun kama hira sun koma yi mata dariya. Hanne ta ce, Sai ki yi ai, dadi ne ya yi miki yawa. Ni mijin nake so ya gudu ya bar ni, ke Allah ya kashe Ya ba ki kina so ki yi butulci, kukan dadi ki ke yi, ki ci gaba Saade. Raheema ta ce, Ni in ni ce na samu wannan gidan na Saa ai bude ido zan yi in sha kallon abuna mu more niimar da Allah ya ba mu. Sai jin gyaran muryar Awaisu suka yi daga bakin kofa. Ya yi sallama suka amsa, sannan ya dan shigo ya dube su ya ce, Me kuke jira ba ku kama gabanku ba?. Hanne ta ce, Kudin sayen baki mana!. Ya yi dariya don daga jin maganarta ya san yar kauye ce futuk, ya ce, Ai ke ce sayen bakin amma fadi me ki ke so a ba ki ki fito ki bar Yarima da Sa'adatun sa? Sai ga Yariman ya iso kofar dakin ya ce cikin kasaitarsa da muryar da ke gigita Saade har cikin kwanyarta. Ba jimawa kuwa jikin ta ya hau tsuma. Awaisu please drop them at home, na gaji da yawa. Awaisu ya ce, Sun ce kudin sayen baki suke jira. Ya ce, ka ba su ko me suke so, amma ku kama gabanku dukkanku, har kai. Ai kuwa Saade ta sake rushewa da kuka ta kama hannun Raheema ta kankame. Yanzu tafiya za ku yi da gaske ku bar ni ni kadai Raheemah? Yareema ya jiyo abinda Saade ta ce, da kukan da ta ke yi mai ratsa zuciya, zuciyar sa ta motsu, ba zai iya jure jin sautin kukanta ba, daga Awaisu har su Raheema ba su ankara da sanda ya shigo dakin ba, sai sunkuyawarsa da daukar Saadatu kacokam a hannayensa biyu kamar ya dauki karamin yaro, ya juya ya fice yana ce da su. please....Mun sallame ku, mu kwana lafiya. Saade wadda kanta ke rufe ruf cikin laffaya tana aikin kuka, bata gane me ke faruwa ba, har sai da Yareema ya soma hawa matattakala da ita a hannun sa,wadda zata sada su da turakar sa, sannan ne ta gane a hannun Uncle Yareema ta ke dungurugum, ta hanyar jin kamshin invictus paco rabbanne da taushin hannayen sa da ya mamaye ta. Ta kuma ji an raba ta da kasa kacokam. Kukan ya makale don kansa ta koma salati tana wutsil-wutsil da kafafunta. Su Raheema me za su yi ba dariya ba? Yarima bai sake bi ta kansu ba ya bi matattakala da Saade a hannunsa zuwa upstairs dinsa. Bai dire ta a koina ba sai a kan sofa. Yana ajiye ta tana zabura tana mikewa suka tsaya a tsaye kamar zakaru suna kallon-kallo, idanunta jazur wadanda suka sha kuka suka koshi. Idanunsa a lumshe, wadan suka jiku da soyayya. Ba ta ankara ba ta ga Dr. Sageer ya juya cikin tafiyar sa ta kasaita, ta dauka daya dakin zai shiga don rage manyan kayan dake jikin sa, don a sanin data yi masa bai iya zama da kaya masu nauyi na tsayin lokaci, ta samu damar da ita kuma zata fice ta koma kasa. Maimakon hakan data yi hasashe, sai gani ta yi ya isa ga kofa ya murzawa dakin keydin dake jikin kofar, ya kuma zare mukullin ya jefa a aljihun gaban rigarsa. Ya koma can jikin gado yana rage nauyin kayan alfarmar dake jikinsa, ya cire babbar rigar ya ajiye a gefe, sannan ya zauna a bakin gado ya dauki wayarsa yana daddannawa ya baiwa banza ajiyar ta. Har zuwa lokacin Saade na tsaye inda ya barta kamar mutum-mutuma. Ta kasa motsawa ko nan da can. A yadda Yarima ya ganta ya san ba karamar rigima ta ke ji ba, sai motsi take da baki amma ta kasa magana. A yadda yake ji shikuma ya shirya wa kowacce irin rigima da za ta zo da ita, koda zasu babbaka kan su a dakin, tunda finally ya mallake ta shi ke da nasara cikin kudura da iradar Ubangiji, ba don ya isa ba, babu tsumi ba dabararsa. So duk wani protest da zai zo daga gareta zai iya shanye shi. Tunda iya wuya ita aka kwara. Matsalar sa daya sarautar sa bazata barshi ya iya lallashin mace ba, ko ya nuna weakness. Ta ya ya zai yi wasa da wannan kyautar bazata mai daraja da mahaifinsa ya yi masa? Bai kara bi ta kan Saade ba yana ta latsa wayarsa. Da Awaisu yake magana kasa-kasa, inda Awaisu ya tabbatar masa ya maida su Raheema wajen Fulani, ya kare da cewa, Ka tausaya wa yarinyar mutane please Yareema. Ka rike ta amana. Ka san dai a cancanta baka cancanci auren ta ba Allah ne ya dube ka da rahmar sa. Dubi yadda ta ke ta kuka kamar ranta zai fita, wallahi ta matukar bani tausayi. Very young da aure. Ya san Awaisu gaskiya ya fada. Amma a ki-fadi irin nasa. A kufule ya amsa. Ina ruwanka da matar mutane da har ka kalle ta ka san kuka ta ke yi? Awaisu ka fita idona in rufe, ka fiya shiga sabgata da yawa, ko kukan jini ta ke bai shafe ka ba, tunda dai ba Asiya ba ce. Wannan maganar da kake yi ba hurumin ka bace. Awaisu sai dariya yake har Yarima ya kashe wayarsa. Malama, in kin gama kukan ki yi mana light-off, zan kwanta. Saadatu ta sake bare baki tana kuka da sauti kamar karamar yarinya, wane irin light-off ita da namiji a daki daya? Kukan nata sai ya koma bai wa Yarima dariya, amma da yake ba gwanin yinta ba ne, sai bai yi ba. Ga tension din da Ya Gumsu ta saka shi a ciki. Ga maganar Awaisu ta taba shi. Ya mike zuwa closet din jikin bango yana canzawa zuwa pajamas. Ta gefen ido Saadatu ta sato kallonshi, ai kuwa riga yake kokarin sa wa ta hango ingarmanphysique chest din Yareema Sageer Yusuf Askira da manyan damatsansa wanda ke lullube cikin muscles da ba shiri ya sanya ta kauda idonta. Jikin ta ya hau tsuma. Ta kuma durkushe a kan kafafunta ta bude shafin sabon kuka wanda ya ratsa har cikin kwakwalwar Yareema Sageer. Zuciyarsa ta karaya, ko kusa bai yi niyyar rarrashinta ba a yau, so yayi su yi duk irin rigimar da zasu yi ya nuna mata ba gudu ba ja da baya a auren su duk rashin son ta da auren. Auren su mutu-ka-raba ne. Amma kukan nata ya karya lagonsa, ya ji ba abin da yake so irin ya san hakikanin damuwarta a kan aurensa. In dai har za ta yi hakuri ta zauna da shi cikin kowane hali, shikuma zai yi duk abinda take so komai tsaurin sa. Gefen gadon ya koma ya zauna, ya dunkule hannayensa cikin junansuya dora habar sa akan su, ya rasa abinda yake masa dadi. A yanzu ko bata furta ba ya gama gane Saade bata farin-ciki ko kadan da zamowar shi barin rayuwar ta. Wannan kukan data ke yi ya wuce na amarci, kuka ne mai nuna an zalince ta, an katse mata rayuwa. A hankali ya kira sunanta da wata irin lallausar murya da shi kansa yake tababar kasancewar tasa ce. Saadatu! Ba ta amsa ba, haka nan ba ta fasa kukanta ba, kukan da ke cin ran sa, sannan ba ta dago ta dube shi ba. Tana nan durkushe a inda ta ke kamar an kafe ta a wurin, nannade cikin jar sassalkar laffaya ta bare-barin usli. Yarima ya mike daga zaunen da yake a gefen gado, a hankali ya soma takawa zuwa gaban Saade, kafarsa na nitsewa cikin tattausar kilishin tsakiyar dakin.Pajamas ce ruwan toka kawai a jikin sa iya gwiwar sa samfurin Marks and Spencer, ya daure tsakiyar da igiyar ta. Yana zuwa hanayenta da ta rufe fuska da su ya kama, ya tsuke su tsakiyar tafukan tausasan hannayen sa, ya bude fuskarta wadda ta yi kaca-kaca da hawaye ta yi jazur, da ka ganta a wannan lokacin za ka san BAGGARA ce. Kamar uwa da uba duka shuwa-arab suka haife ta. Hannayenta da ya kama ya ja ta a hankali zuwa jikinsa daga tsayen da suke. Bata kai shi tsayi ba iyakacinta kirjin sa.Slowly yake rungume ta tightly, ta yadda kowacce gaba ta jikinsu sai da ta hadu da yar uwar ta. Haduwar fatar jikin su wuri guda tamkar jan wutar lantarki ya haifar ga kowannen su. Da wata irin azama Saade ta soma kokarin janye jikinta daga na Yarima Sageer, saboda wani alamari ne da bai taba faruwa da ita ba (physical contact) da kowanne Da namiji, balle wanda ta ke wa ganin matsayin babban Yayanta. Tsatstsauran rikon da Yarima ya yi mata ya sa ta kasa kwacewa, tun tana kokawar da mutsu-mutsun kwatar kanta har ta gaji tubus! Ta bari, hawayen fuskarta Yareema ya soma wiping da lips dinsa, wanda hakan ya jefa Saade cikin wani hali da ta kasa ganewa. Wani ignition ne tamkar electrical shocking ke yawo a cikin gangar jikinta a duk lokacin da lips din Yarima ya sauka a kan fatar fuskarta. Duk da haka kokari ta ke ta kwace jikinta amma bai bata damar hakan ba. Kina so in cika ki Saadahtouh? Muryar Yareema Sageer tamkar ba tashi ba. Ta zama very pale idan aka kwatanta ta da ta dazu da yake magana cikin izza da sarauta. Kai ta daga, domin kwarai ta ke so ya cika tan ko ta shaki numfashi yadda ya kamata, sabida ba ta saba da hakan ba. The feeling is awesome, and their closeness is so intoxicating. (Kusancin ta da shi mai bugarwa ne). Kai za ta iya rantsewa babu namijin da ya taba rike mata hannu in this manner ta ji irin abinda ta ji yanzun tun tasowarta, don haka komai da Yarima yake yi a yau is so strange to her, zuciya da gangar jikin ta sun kasa karbar sa. Maimakon ya cika ta kamar yadda take fata, sai ya kwantar da kai gabadaya a kafadun ta ya kanainaye cikin jikin ta. Har tsayuwa ta soma gagarar ta domin ya saki duka nauyin sa a jikin ta, amma yasa hannu daga bayan ta ya tare ta. Yareema ya soma magana da murya mai kassara zuciyar diya mace, mai nuna karbar laifi da shirya repenting, zaka rantse ba shine Dr. Sageer din da ka sani a NTNU ba. Kuma Yariman Askira mai jiran gado. Mafi soyuwa a zuciyar Mai Askira. “Na ji kuma na yarda da korafin ki na cewa an miki laifi an aura miki mai yin zina. Ba tare da an nemi yardar ki ba. Ba zan iya cewa kin yi karya ba. Sai dai kada ki manta su din iyayen mu ne bamu da kamar su, nima baa nemi yarda ta ba, da an nema da na gaya musu ban cancanci mallakar pure soul irin ki ba Saadah!. Tunda bakin alkalami ya riga ya bushe ni da ke duka bamu da abin yi banda fuskantar reality na rayuwar da ke jiran mu a gaba, mu manta da ta baya. Ko me ki ke so zan miki Saadah, in har za ki amince ki zauna da ni. Duk sharuddan da za ki kafa min a zamanmu zan bi su, in dai za ki ci gaba da amsa sunan matar Sageer Askira. Saadatu this is not the right time to discuss anything sensitive like this, dukkan mu hutu muke bukata, don haka so nake ki kwanta ki huta na gaji Saadahtouh, bikin Askira mai wahala ne, hutu kawai nake bukata yanzu, ke ma kin gaji da hidimar bukukuwan mu na aladah, ki yi hakuri da kukan nan haka mu kwanta mu yi barci. Mu bar wa gobe tattaunawar, komai dacinta zan saurare ki! Na yi alkawarin canza komai na rayuwata zuwa mai kyau daga ranar dana mallake ki Sa'adah na yi alkawarin nan. Ka bude min kofa in fita to. Karo na farko da ta yi magana tun shigowarsu dakin. Domin kalamansa sun sanyaya mata zuciya. Saadahtouh, ke matar aure ce yanzu, kuma macen arziki ba ta raba makwanci da mijinta sai bisa lalura. Muryar Saade bata fita sosai sabida kukan da ta sha. Ta ce. Don Allah Uncle Yarima ka bar ni in koma wancan dakin, ni ba zan iya kwana daki daya da kai ba. Ta fadi da iyakar gaskiyarta. Me ki ke tsoro? In kin kwana gado daya da mijin ki Malaiku ne za su yi ta sa miki albarka har garin Allah ya idasa wayewa, musamman if you act as my messeuse (idan kika zama mai min tausa) duk jikina ciwo yake mun saboda zirga-zirga da hayaniya. Please Saadah help me... Ya fada yana kara makalkale ta ta yadda suka dunkule wuri guda kamar curin alkaki, ba tare da Saade ta san yaushe hakan ta faru ba Saboda gabadaya muryar Dr. Sageer ta gama kashe duk wani kuzarinta. Ta saukar mata da wata irin kasala. Ita ma ba ta san me ta ke tsoro a kwanansu daki guda bisa gado guda babut shes really-really afraid, wani abu ne STRANGE a gare ta, don bata taba ganin inda akai hakan ba. Duk da ta san a yanzu an daura musu aure amma zuciyar ta ta kasa karbar wannan sabon dingimemen sauyin da sauki. Tana wannan tunanin mai matukar dagula zuciya, ba ta yi aune ba sannan bata tantance komai ba ta ji Uncle Sageer ya soma warware laffayar jikin ta tun daga sama cikin nutsuwa har ya sauketa kasa tsaf, ya saura daga ita sai underwear din dake jikin ta, kallo daya Dr. Sageer ya yiwa Saadatu cikin fararen under wear ya ji komai na duniya ya tsaya masa; including numfashin sa. Daga hakan ya sunkuce ta ba tareda ya tsaya sake kallon ta ba, bai dire ta a koina ba sai a royal bed din su, ya ja wani lallausar duvet ya lullube su, tare da latsa makunnin lantarki daga nan inda ya ke kwance. Fitilu shudaye suka maye gurbin masu haske (dim light). A dirowar jikin gadonsa ya bude ya fiddo turarensa Invictus (Paco Rabbanne) ya soma feshe su dukkan su, ya ce. Bana son wadannan turarukan matan barebarin da aka gumbuda miki, daga yau kada ki sake shafa su, we will be using the same scent, wadannan sun cika karfi da yawa hawa min kai suke yi. Daga yau za mu dinga using nawa tare (Paco Rabbanne), you can use it too ba shi da karfi. Saade ta zumburo baki kamar yana ganinta, ai kuwa ya gani ta cikin dan hasken dim din wanda hakan ya sa shi yin abin da bai shirya ba. A hankali ya soma sumbatar Saade tun daga yatsar kafarta At first hes doing it gentle kafin gabadaya ya koma hungrily, da gani za ka san abu ne da ya dade yana fatan kasancewar sa. Ya dauki Saadatu diyar Fulani Bilkisu ya kai ta wata kololuwar duniyar soyayya da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba. A yadda Saade ta yi amanna ta mika wuya ko me Yarima ya nema a lokacin tabbas zai samu, domin ba ta san inda Yarima Sageer ya dauke ta ya kai ta ba. Amma sai me? Kalaman Ya Gumsu ne suka fado cikin kwakwalwarsa suka katse duk wani hanzari nasa. Ban yarda ka taba yar Bilkisu ba, ban yarda ka hada shimfida da ita ba. Sai kuma na Fulani Bilkisun Ina neman alfarmar ka daga mata kafa har ta kare makaranta. Yarima ya rasa inda zai sa kansa a wannan lokacin. Ji ya ke tamkar ransa zai bar gangar jikin sa. A hankali ya mirgina ya koma can karshen gado ya runtse idanunsa yana ambaton sunan Allah. Saade na jin shi, amma ba ta san dalilin sa na janyewar ba. Da nutsuwa ta soma dawo mata sai ta ji wata matsananciyar kunya ta kama ta. What happened like this? Wannan wane irin abu ne mai tsauri da nauyi yake faruwa tsakaninta da Uncle Yarima haka? Kanta ta tusa cikin pillow kamar ta roki gadon ya tsage ta shige. Tana jin saukar numfashin Yareema a hankali har daga baya ta gane ya yi barci. Ta yunkura da zummar ta nemi mukulli ta fice, amma sai ta ji caraf! Hannuwan Yarima sun maida ta kwanciyar, ya kuma sake mirginowa ya rungume ta sosai a jikinsa. Bai kuma kara attempting komai ba, tun tana fargabar faruwar wani abu makamancin na dazu har ta gane barcin sa ya yi nisa sosai. Akai-akai Saade ke sauke ajiyar zuciya tana tambayar kanta, wannan shi ake nufi da auren ke nan? Su dunkule su zama abu guda in every aspect kuma marufar sirrin juna? Sirrin da yafi karfin kwatance ko fadar sa ga wani. As a university student ba za ta ce kwata-kwata ba ta san manufar aure ba duk da babu wanda ya taba zaunar da ita ya gaya mata, duk sakewar da ke tsakaninta da Fulani magana irin wannan ba ta taba hada su ba. Baggara akwai kunya tamkar Fulani suke, sai dai kuma sun fi Fulani ilmin addini. Sai goshin asubahi ta samu barci, kuma ko na minti daya Yarima bai yarda ya raba ta da jikinsa ba. In ma ta yi kokarin zamewa tsaf cikin barcin zai kara kanainaye ta. Tun tana jin kunya har ta gaji ta yi barcin ta a jikin sa. Ko don wannan turaren nasa mai dadin kamshi da sanyaya zuciya za ta so su wayi gari a haka. Daren yau bakidayansa wani yanayi ne da ba za ta taba mantawa ba a tarihin rayuwarta. Ba ta maraba da auren Yareema Sageer, ba ta kuma taba mafarkin faruwarsa ba, amma daga daren jiya zuwa yau sai ta ji dama su dauwama a haka! Ba tareda wani dan adam ya kara ratsa tsakanin su ba. The moment is awesome because its strange but pleasant ga Saade, don haka image din ya tsaya a kwakwalwarta. Hoton ta makalkale cikin jikin Yarima Sagir, ya kasa bacewa dagascreen na zuciyarta. A haka aka yi kiran assalatu. Da yake ba ta dade da samun barcin ba, ko motsi ba ta yi ba. Har Yarima ya mike ya je toilet din da ke makale da dakin ya kammala abin da zai yi ya fito Saade ba ta da alamar farkawa. Duk da bahagon halin Ya Gumsu, a baya na gaya muku cewa yayanta akwai sallah. Sai ya tsaya a daidai fuskar Saade yana taje jikakkiyar sumar kanshi. Yarfin ruwan a fuskarta ya sa ta bude ido kadan, sai idonta cikin na Yarima. Da fari ta dauka a dakinta ta ke na Abuja, amma ta san Uncle Yarima bai taba shigar mata daki a irin wannan lokacin ba. Ta sha ganinshi da pajamas ko a gidanshi, amma ya kan daure tsakiyarta da igiyar jikinta, amma yau bai daure ba, physique chest dinsa dauke yake da suma a kwance luf, wanda hakan ya sa ta saurin kauda kanta. Sai kuma ta tuna wai fa ashe su din yanzu miji da mata ne. Ajiyar zuciya ta kwace wa Saade daga kwancen da ta ke. Har sai yaushe kwakwalwarta da zuciyarta zasu karbi reality na kasancewar ta matar Yarima Sagir ne? Yareema ya mika mata hannu da nufin ta kama ya taimaka mata ta tashi, amma sai ta juya daya barin ta rabu da shi. Ya ce, Tashi Saadahtou mu yi jamin sallah kina makarar da ni. Saadatu ta yi shiru, ta ya ya za ta iya gaya masa cewa, period ta ke yi? Ba za ki tashi ba? Ya fada for the second time yana mamakin abin da zai hana ta yin sallah, sai kuma ya tuna mace ce, don haka ya juya ya tada sallarsa. Har gari ya soma haske Yarima na sallah, ita kuma ta kasa komawa barci. Tunanin rayuwar da za ta riske ta a gaba ta ke yi. Tunda yanzu rayuwarta ta zama dependent upon Yareema. Sai yadda yayi da ita. A baya shi din guardian ne, amma a yanzu matsayinsa ya zarta na kowa kenan including iyayenta. Wannan ba karamin nauyi ba ne aka dora mata, wanda ba ta san ya ya za ta yi da shi ba. Ta duba ta laluba cikin tsokar zuciyarta ko za ta ga SO ko akasin sa a kan Yareema Sageer? Amma sai ba ta samu ko guda dayan su ba, babu soyayya haka babu kiyayya tsakanin ta da Yarima, sannan daga daren jiya zuwa yau alamuran Yareema Sageer masu ban mamaki ne da suka soma rikita hankali da nutsuwarta. Tana nan kwance har Yareema ya gama sallolinsa, ya sunce ya shiga wanka. Da ya fito ya tambayi Saade, Manyan kaya zan sa ko kanana? Ta yi masa shiru. Ya ce, Alright. Bari kawai in sa kanana, ban sani ba ko saboda tsufana ne ba kya so na. Ta juya masa baya bata ba shi amsa ba. Ya gama sanya kayansa riga da wandon BALANCIAGA ruwan goro masu ratsin black. Sai ya fito a Georgeous Prince dinsa. Kai bazaka ce ya taba aure ba. Ya hawo bisa gadon daidai inda ta juya fuskarta yau zaki sha tea irin wanda baki taba shan irin sa ba. Sai ta rufe idanun ta gabadaya daga barin kallon sa, don ji ta yi zuciyar ta na racing. A cikin dakinsa akwai karamar butar dafa shayi, ya jona kettle din bayan ya yi hade-haden shayinsa na naa-naa da girfa, yadda Saadatu ta juya masa baya ta ki juyowa yana taba ransa, sabida shi dai ba haka matarshi ta sabar mishi ba. Da sun wayi gari da ta soma haba-haba da shi har sai ya ce ta dame shi. Ya zuba kakkamsan shayinsa a dan karamin farin kofin shayi na karau, ya zauna a gefen gadon daga daidai kafafunta yana sipping a hankali. Kamshin shayin da yake sha duk ya cika ta, ya kuma tayar mata da appetite na abinci, sai lokacin ta tuna rabonta da abinci. Tun na safiyar jiya da Hanne ta matsa mata ta ci lomar sinasir guda biyu. Akuyar cikinta har wani irin kugi ta ke yi cikinta na murdawa da yake tana da ulcer kadan tun a El-Kanemi. Dole ta mike ta nufi toilet ta yi brush, ta yi wanka ta kuma nemi pad din da za ta canza ta rasa. Kayan jikinta ta maida, wato doguwar riga mai bin jiki ta roba wadda ake sa wa a kasan laffaya (underwear), ba ta nada laffayar ba ta fito gashin kanta da ya sha kitson nan jelunan sun kwanta lambam a wuyanta. Kai tsaye ta nufi kofa don ta tuna Raheema ta gaya mata ta sa mata pad din a lokar jikin gadon dakinta da suka kai ta jiya. Amma me? Kofar a kulle gam, kuma ya zare mukullin jiki. Ta juya a sanyaye ta dube shi suka hada ido yana kurbar shayi, ya ga damuwa karara a tare da ita. Ya ajiye kofin hannunsa a kan lokar gadon ya taso a hankali ya iso gabanta. Hannayensa duka biyu ya zuba a cikin aljihun wandonsa, ya dube ta keenly, murya raunane ya ce, Me ya sa ki ke guduna ne Saadatu? Ta sadda kanta kasa. Ya ce, Ki kwantar da hankalinki kin ji, za mu zauna mu yi magana ta fahimta kafin mu tafi Abuja, yanzu nan da awa guda za ki ga gidan nan ya cika, don haka ki yi hakuri ki ba ni one hour in yi ta tare da ke, kada ki bar ni ni kadai. Murya can kasa kamar an shake ta ta ce, Zan dawo, abu zan dauko. Gaya min ko mene ne in dauko miki, amma ba za ki bar dakin nan ba sai na miki umarni. Kamar ta fashe da kuka, ta ce, Ba ka san inda yake ba, besides abin na mata ne. Yarima ya ce, Okey. I can relate. To mu je tare, kada ki yi min wayo ki shige daki ki rufe. Ta turo baki, ta ce, Na yarda. Sannan ya bude kofar suka sauka zuwa downstairs. Bayin da aka ba su suna ta hidimar tsaftace gidan suka wuce su bayan sun gurfana sun yi gaisuwa, yana kallo ta bude lokar ta dauko ledar sanitary pad ya sa ta a gaba suka koma upstairs dinsa. Suna shiga dakin ta wuce toilet, kafin ta fito Yarima ya zuba mata shayin da ya sha yana firfita mata between two cups. Ta fito tana taku a hankali kamar mara gaskiya ta zauna a kan sofa bed can nesa da shi ta zuba uban tagumi da hannaye bibbiyu. Yareema ya taso zuwa inda ta ke, ya rusuna ya mika mata shayin, sannan ya zauna daidai kafafunta, kai ka ce ita ce Yariman ba shi ba. Ta sa hannu ta karbi shayin don ba ta yi wa yunwa fulako. Ganin yadda ta ke shan shayin da sauri duk da zafinsa ya sa shi tambayarta. Tun yaushe rabonki da abinci? Saade ba ta ce komai ba, sai shan shayinta ta ke yi, kan ka ce me ye wannan ta zuke shi. Da gaskiyar sa bata taba shan shayi mai dadin nasa ba da wartsake makoshi. Ya mike zuwa ga bed side fridge dinsa, ya dauko danyar madarar oldenburger mara sanyi, ya zo ya bude ya tsiyaya mata a tambulan ya zauna dab da ita ya kai kofin bakinta. Da farko kunya ta ji, amma kuma an ce mata suna son kulawa irin wannan daga mazajensu, kulawar da ba duk maza ke iyawa ba sabida girman kan su. Sai ta ji ta kasa tankwabe wannan kulawartasa, ta bude baki tana shan madarar sosai daga hannun Yareema, sai da ta shanye madarar tas, zai kara mata ta ce a hankali, Ya isa. Sai ya ajiye kofin ya juya ya kwantar da kai a cinyoyinta. Hannayensa zagaye da kugun ta. Now, tell me Saadatu, why dont you love Sageer? Ta rasa inda za ta sa kanta, sabida Uncle Sageer ya yi kwanciyarsa akan cinyoyinta, ya mike kafafunsa bisa sofa din. Uncle Ta fada a hankali very upset and unease. So take ta ce ya daga ta kada wani ya shigo, amma kunya ta hana ta. Kada ki kara ce min Uncle, ban san ta ina na zama Uncle dinki ba. Ni ba kanin Fulani ba, ni ba kanin Baban ki ba... Ni, (ya nuna kan sa) ni ne SAGEER kawai, Sageer Askira, ba ni da wani lakabi bayan wannan. Ya sa tafukan hannunsa a fuskarta. Very smooth and supple. In ji dai ba shafe-shafen zamani ki ke ba? I love natural skin shi ya sa nake son Sultana. Ai ba ta san lokacin da ta ture kansa daga cinyarta ba ta mike. Allah ya so ta bai cire mukullin daga jiki ba, ta bude kofar ta yi ficewarta. An ce ko babu SOYAYYA kishin cikin AURE daban yake. Haka ta wuni ranta a bacea kan yar maganar da Dr. Sageer ya fada akan Sultana, yayin da Dr. Sageer ya wuni cikin matsanancin nishadi da bai taba tsintar kansa a ciki ba. A yadda ya fahimta insha Allahu ba zai sha wahalar samun soyayyar Saadatu ba, tunda har ta fara kishin matarsa. Dama ya fada ne don ya ga reaction din ta. Ya canza kayan jikinsa zuwa Jabba da hular data dace da kalar kayan wato deep-brown, ya fesa turarensa ya fito. Tuni bayi sun cika tebir da abinci naui-naui. wanda aka kawo daga unguwar Fulani Bilkisu. A cikin bayin da Maimartaba ya ba su akwai wata kuyanga Sadiya, burinta kawai Yarima ya yi kwarkwara da ita ba tun yau ba, don haka ba karamin dadi ta ji ba da aka hado da ita cikin hadiman gidansa. Yanzun ma yana fitowa ta fadi gabansa, Gyara kimtsi da kyau, lafiya dan zakin Duniya lafiya dan malafar duniya, lafiya dan mai fada da cikawa lafiya dan mashasha lafiyarka dama da hauni mai nasara zauna daidai dan bawan Allah zauna daidai dan masu alheri. Yana zama bisa dining table ba tare da ya dago ido ya dube ta ba, ta hau yi masa firfita da maficin gashin Dawisu tana ci gaba da zubo kirarin. Daidai lokacin da Saade ta bude kofar dakin ta fito cikin wata irin sassaukar kwalliya ta riga da zane dark blue na yadin karen miski wanda ba a samunshi koina sai gidan sarauta. Wani kallo da ta sakar wa Sadiya ya sa ba shiri ta juya tana mata nata kirarin. An fito lafiya uwar masu gida, zauna daidai uwar alheri taka lafiya matar Zakin duniya. Saade ta kira sunanta a hankali kafin ta wuce ta ce, Sadiya! Kada ku kara zuwa nan in ba ni na kira ku ba. Lokacin aikinku daga karfe shidda ne zuwa bakwai na safe, da kun gama jera abincin karin kumallo shi ke nan na sallame ku. Sadiya ta amsa a matukar ladabce, sannan ta fice. A ranta tana fadin, Ta Allah ba taki ba. Insha Allahu ni ce Sa-dakarsa ta farko duk boyon da za ki yi masa, me ya kai ki auren Basarake in kin san kishi gare ki? Yarima yana jinsu kansa a duke yana danna wayarsa, sai ya ji murmushi ya kwace masa. Ya dauka zuba masa abincin ta fito ta yi, amma tunda ta kori Sadiya sai ta juya ta koma daki abinta ta barshi a nan zaune. Sai ya ji ya kasa ci. Ya zuba abincin daidai misali a kan plate, ya dauka ya bi bayanta. Ta zauna kenan a bakin gado ta yi tagumi, wadannan yammata da aka cika mata gida da su kullum suna sintiri a gaban Yareema yaya zata yi da su? Ta isa ta ce zata zauna babu kuyanga? Ko cewa zata yi a kwashe su a kawo mata tsoffi? Kowa ya ji hakan a take zai fassara ta da kishi. Ita kuma ta san ba kishi take ba tsoro ta ke ji, tunda ta san wa aka aura mata. Tana wannan sake-saken sai gani ta yi tattausan hannun Yarima mai daure da agogon ‘Swatch Blustery’ ya miko mata plate cike da soyayyen dankali da sauce din koda da hanta. Saade ta dago ido a hankali ta dube shi. Ya daga mata gira, ya ce, Karbi. Sai ta kasa tankwabe wannan kulawar a karo na biyu. Ta sa hannu ta karba cike da jin nauyi, ita ba ta ba shi ba shi ya dauko da kansa ya kawo mata, ta tuna wane ne Yareema Sageer a masarautar Askira gabadaya da yadda kannensa da yayyensa duka ke sonshi da girmama shi. In ta ce ba ta ji wani iri a ranta ba kan rashin kyautawar ta ta yi karya, sai ta ji somehowkamar abin da ta ke yi ba daidai ba ne. Don haka ta motsa dan bakinta a hankali yana shirin ficewa daga dakin tace. Uncle kai ba za ka ci ba? Ya juyo gabadaya ya fuskance ta sabida ya tsani wannan Uncle din da ta ke ce masa. Ya ce, This will be the last time da za ki sake kirana Uncle tunda dai ni ba kanin Fulani ba ne, idan ba za ki fadi sunana ba ki sa ma min wani. Amma ki ka sake ce min Uncle Allah zan cire hijabin da ke tsakaninmu Saadatu, wanda ke sa ki yi min kallon kanin Babanki. Maganar ta bata dariya amma bata yi ba. Ya juya ya fice yana cewa, Mun tafi Ta-Sani ni da Awaisu. Murmushi ya subuce wa Saade, kowanne irin hijabi ne tsakanin nasu? Oho! Ta maida hankali ga cin abincinta, kunnenta har motsi yake sabida yunwa da dadin abincin wanda daga jin kamshin sa ta san daga unguwar Fulani Bilkisu yake. Yareema da Awaisu sun je sun gaida Alhaji Kyari, bayan sun gaida Maimartaba, sannan suka wuce cikin gida, unguwar Ya Gumsu suka fara zuwa suka kwashi gaisuwa, ta amsa musu kadaran-kadahan sai kallon Yareema ta ke da wutsiyar idanu kamar mai son gane cewa ya bi umarnin ta ne ko aah? Ya maida Saadatu cikakkiyar matar sa? Tsoronta Allah tsoronta ranar da Sageer zai hada shimfida da Saadatu, don ta san daga ranar ba za ta sake gane kansa ba,kamar yadda ba ta kara gane na ubansa ba tunda ya auri uwarta, kai ba ita kadai mahaifiyarsa ba, har waccan baturiyar tata ta kare. Ita ta san sirrin matan BAGGARA, ta san ta inda Fulani Bilkisu ta bi ta birkice musu kan miji kenan. Allah kadai ya san iya abubuwan da ta koya wa yarta, da sirrin mallakar da ta dankara wa Saaden(Allah Sarki ZATO. Mu kasance masu kyautata zato ga yan uwanmu musulmi, in ba haka ba za mu kare ne da daukar nauyin zunubansu. TAKORI). Daga wajen Ya Gumsu suka nufi unguwar Yaakirjiloma, Mairam Murjanatu na shirin tafiya tare da yayanta, tana ganin Yarima faraarta ta fadada, ta ce, Ka ga ango sha kamshi. Angon Saa da Aisha-Sultana. In ce ko an rago min kazar amarci? Dariya Yareema Sageer ya yi, don yana son Yayarsa Murjanatu sosai, tana da son zumunci da hadin kansu, shi sai yanzu ma ya tuna wai ana kai wa amarya kaza, shi haka ya tafi hannun sa na dukan cinya, dan banzan Awaisun nan kuma bai tuna masa ba, amma babu komai bari lokacin ya zo su koma Abuja, zai yi komai don Saadatu. Ko dawisu ne zai sa a gasa mata ba kaza ba. Ya ce, Mairam Murja, ba dai shirin tafiya ake ba? Na dauka za ku zauna har ku raka amarya Abuja? Murjanatu ta ce, Na so hakan, amma Ambassador ya yi waya maza-maza in koma sabida yara sun koma makaranta, kada ka damu za mu zo suna next year in Allah ya yarda. Yarima ya ji kamar ya nutse kasa don kunya, amma a zuciyarsa ya ji dadin wannan fatan nata, fata na gari lamiri in ji masu iya magana, kuma babu wanda zai so ta haifa masa Da a duniya irin Saadatu. Wani disappointment din is a blessing (Aisha Sultana da ta cire mahaifa) don an ce yaya suna tsotso dabiu da halaye na mahaifan su. Ya ce, Wa zai kai ku Maiduguri (airport)? Ta ce, Maimartaba ya bada mota da dogarai su kai mu, Humaira da Najaatu za su raka mu har su ga tashinmu sai su dawo. Ya fiddo wayarsa daga aljihun gabansa yana fadin, Bari in kira Suhail da Ahmad duk su raka ku, tafiya da maza za ta fi dadi. Ya yi magana da Ahmad da Suhail, sannan suka yi sallama da Murjanatu, suka karasa falon Yakirjinoma suka yi gaisuwa ta sa musu albarka. Ta kawo turaruka ta ce a kai wa Saadatu. Daga nan sai Unguwar Fulani Hibbani. Najaatu da Humaira suka gaida yayyun nasu, Sageer da Awaisu. Humaira sai faman dauke kai ta ke don tsananin haushinsa da ta ke ji, ya rasa wadda zai aura sai yar Fulani Bilkisu don kawai a wulakanta iyayensu? Ita tun filazal ta tsani Saadatu sabida son da Askirama ke mata, balle yanzu da ta zama surukarsa kuma matar Yarima dungurugum. Shi bai kula Humaira na ciccin magani da shi ba, ya dube ta da kulawa, ya ce, Auta, sai yaushe za a shigo mana? Ta yi wani dan murmushi na dole, ta ce, Matarka Yaya Yareema Junior ta ce fa, ya za a yi ni in je gaishe ta? Ai sai dai in ta zo nan mu gaisa. Cikin mamaki ya ce, Junior? Don sam bai gane me ta ke nufi ba. Ta ce, Kwarai, tare aka kai mu makaranta a El-Kanemi, ina aji uku tana aji daya, she has been washing my pants and undies, kai har gugar kaushi ta ke min, everything. Yareema ya kufula iya kufula saura kadan ya kai mata mari Awaisu ya rike shi. Ya ce, Saadatun? Wa ya ce miki baiwar gidanku ce? To yadda ki ke ya a gidan nan haka ita ma ta ke, idan watarana na ga kafarki a gidana sai na kakkarya ki, sakarai kawai. Ya Hibbani ta fito daga dakinta tana daura dankwali, ta ce, Yareema mene ne? Ina barci na ke jin tashin fadanka. Nan ya gaya mata a gajarce. Hibbani ta kyabe baki, ta ce, Kada ka ga laifin kanwarka Yareema, saboda da farko mu ba mu san yarta ba ce, boye mana ta yi. Cewa ta yi yar riko ce ta karbo, so don Humaira ta sa ta aikatau a makaranta ba ta yi laifi ba. Kada ka manta Humaira yar sarki ce, jikar Sarki. Wannan kuwa ko asalin ubanta ba mu sani ba. Idanun Yarima suka kada kamar gauta, ya bude dukkan idanunsa yana duban kishiyar mahaifiyarsa Fulani Hibbani, zai yi magana ya ce ita ma sun san nata asalin ba yar kowan ba ce, sadakarta aka kawo wa Askirama, Awaisu ya toshe masa baki, ya ja shi suka bar sassan gabadaya. Humaira ta ce, Humm! Aka ce auren hadi ne na Askirama, ashe da ma can yana sonta, dubi yadda yake neman dukana. Hibbani ta ce, Tabdijan! Ya Gumsu ta ga ta kanta, ai zama bai gan ni ba, bari in je in gaya mata Yareema ya gama afkawa har fiye da ubansa sai ta yi da gaske, kin ga yadda jijiyar kansa da ta wuyansa ke tashi? Humaira ta ce, Ni tunda nake ban taba ganin makiran mutane irin wadannan Baggaran ba, kyawunsu ke rudarSarakuna, amma wallahi kyawun da babu asali aikin banza ne. Hibbani ba ta saurare ta ba ta figi mayafi ta nufi Unguwar Ya Gumsu. Karya da gaskiya duk ta gaya mata, Ya Gumsu mai neman kuka an jefe ta da kashin awaki ba ta san sanda ta fashe da kuka ba tana fadin, Tawa ta same ni, ni Gumsu. To ba inda za ta bi shi a nan za ta zauna a Askira, ya je can wajen baturiyar ya zauna, ko ba komai su ba sa mugun abu, zuciyarsu ba muguwa ba ce. Bangaren Fulani suka nufa, Awaisu na ta cooling dinsa yana cewa ya yi hakuri, mata ne haka suke, sun gaji kananan maganganu wadanda bai kamata a biye musu ba. Sabida yadda ransa ke bace, duk tsokanar da Fulani Bilkisu ke masa ya kasa tankawa sai murmushi kawai yake. A karshe ta yi musu addua da fatan alkhairi. Ya sunkuyar da kai da ganinshi ka ga wanda ke gaban surukar da yake matukar girmamawa, ya ce, Allah ya taimaki Fulani, ina ganin fa gobe za mu wuce Abuja, nan hayaniya ta yi yawa ba ta barin mutum ya huta. Fulani ta ce, Haba Yareema, ka yi hakuri ku cika sati daya a gama miskero sai ku tafin. Ba da son ransa ba ya amince, don ba zai iya yi mata musu ba, amma kwarai maganganun Hibbani da yarta sun sa so yake ya dauke Saade su bar Askira. Ba zai lamunci kowa nasa ya taba mutuncinta ko na mahaifiyarta ba. Daga nan sai gidan su Awaisu wato gidan Wazirin gari Ibrahim, nan ma suka kai gaisuwa, sai gidan Galadima, Zanna, Shettima, Wali da dukkan king makers daya bayan daya sai da suka bi su suka kai gaisuwa, suka kuma yi musu godiya da ban gajiya. Sai goshin magriba ya dawo gida, Awaisu da ya sauke shi bai tsaya ba ya wuce gidansa. Awaisu na da matarsa Asiya har da albarkar yara biyu. Sanda Yarima Sageer ya shigo gidansa koina tsaf-tsaf sai tashin kamshin turaren wuta yake kuma koina shiru. Kuyangi da hadimai sun kulle koina sun wuce bangarensu. Saadatu ta gaya musu daga karfe shidda na yamma ta sallami kowa. Ita da za a raba ta da wannan tarin yammatan masu jini a jika daga gidanta da sai ta fi jin dadi, to ta san ba ta isa ta zauna babu kuyangi ba a matsayinta na matar Yariman Askira mai jiran gado, ba ta isa ta karya aladar masarauta ba. Zai wuce ke nan zuwa upstairsdin sa da zummar yayi wanka sannan ya zo ya duba Saade, sai ya ji motsin mutum, da sauri ya juya, wata siririyar kuyanga ce ta sha hoda da jambaki ta zube a gabansa. Allah ya taimake ka dan zakin duniya, sunana Sadiya ko da ana bukatar kwarkwara (sa-daka). Kamar daga sama sai ga Saadatu ta bullo daga kitchen din falon za ta wuce, ta yi wannan kyakkyawan gani ta kuma ji abin da Sadiya ta ce. Kofin tangaran na (mug) da ta hado zazzafan shayi mai kauri ta saki ya fadi kasa ba da saninta ba, ji-ka ke tush! Kofin ya tarwatse, gilashin da ruwan zafin duka a kan kafarta. Da sauri ta durkushe ta kama kafar wadda har ta soma fidda jini. Sadiya da Yarima suka yi kanta a tare. Wata irin tsawa da ta daka wa Sadiya sai da hantar cikinta ta kada, Dont touch me, get out! Ki hada kayanki duka ki koma cikin gida, kada in kara ganinki a sassana. Da gudu Sadiya ta fice ta san yau kashinta ya bushe, ta yi shuka a idon makwarwa. Babu bayani ga sauran bayi yan uwanta ta hada kayanta ta koma gidan Sarki a daren. Yarima ya sunkuya ya kama kafar, ta ture hannun sa tana kokarin janye kafarta. Azaba ba yar kadan ta ke ji a cikin tsokarta ba amma ta fi jin zafin tayin da Sadiya ta yiwa Yareema fiye da ciwon, kawai sai ya sunkuce ta ya yi saman benen da ita, duk inda suka wuce sai jini ya disa. Shi ba likita ba, amma ba ya rabo da first aid box a gidansa, toilet ya kai ta cikin jacuzzi ya wanke jinin ya cire kwalbar da ta makale tana kuka tana kankame shi, sannan ya sa mata iodine don azaba ba ta san sanda ta rungume shi ba. Ya dauko ta suka dawo daki bisa sofa ya shimfidar da ita yana ta faman jera mata sannu. He looked worried and disturbed kamar a jikinsa ciwon yake. Ya dauko pain reliever da gorar ruwan Faro ya ba ta ta sha. Ya kwantar da kanta bisa cinyoyinsa yana shafa kanta hankali. Saade sai ajiyar zuciya ta ke, amma bacin ran Sadiya bai gushe daga zuciyarta ba. Kamar Yareema ya fahimci hakan sai ya ce, Me ya sa ki ka kori yarinyar can? Da jajayen idanunta ta harare shi. Ba ka ji me ta ce ba ne? She wantto be your concubine bayan na ce kada in kara ganinsu daga karfe shidda, amma shi ne don ta raina ni ta dawo da ta ji dawowarka. Wani murmushi ya subuce wa Yareema, mace ba ta kishi sai a kan mijin da ta ke so, ko ta fara so. Ya ce, To me ye abun damuwa anan? Za ta taimaka miki ne ta dauke dukkan lalurorina har zuwa lokacin da za ki karbe ni a matsayin miji, tunda ba ki sona Saadatu ba laifi ba ne don sauran mata sun so ni, beside ba haramci ta fada ba. A hankali Saade ta janye kanta daga jikin Yareema Sageer, ta kwanta daya barin akan pillow, sabida yadda zuciyarta ke tafarfasa. A wannan lokacin ta tabbata da za ta ga Sadiya sai ta yi mata mummunan lahani. Yareema Sageer ya je ya kwanta a barin da ta maida fuskarta, ya yi mamaki da ya ga cewa kuka ta ke yi. Im sorry idan maganata ta bata ranki Saadatu. Gaskiyar magana ita ce, ba kya sona, ban san dai wa ki ke so din ba. Amma jikina yana ba ni wannan siririn yaron fari da na ke yawan ganinku tare nemai wuya uwa marikin lema. Ni na gaya maka? Ta tambaya cikin rishin kuka. Ban taba ce maka bana sonka ba Yaya Sageer, kuma ni ban taba son kowa ba. Karatu kawai nake so in yi. Auren ya yi min wuri, ka ga fa duka shekaruna sha tara, level 2 nake. Akwai sauran shekaru biyu a gaba kafin in yi nutsuwar da zan iya daukan marriage responsiblities, sannan baa nemi amincewa ta ba aka daura mana aure, ba mu fahimci juna ba in this aspect ta ya ya ka ke tunanin hankalina zai karbi wannan auren? Sosai Yareema ya fahimce ta, ya sanya hannu cikin jelunan kitsonta yana murzawa a hankali, ya ce, Na fahimce ki Saadatu. Ni kuma na ba ki dama ki ci gaba da yin rayuwarki yadda ki ka saba gudanar da ita a Abuja banda kula wannan yaron. Ni bazan takura miki ba. Insha Allahu ba abin da zai canza har sai lokacin da ki ka ji cewa you are ready to accept me as a husband, kafin nan ina so ki ba ni dama in zama malamin ki kuma aminin ki, mai koya miki karatu kuma abokin shawarar ki mai kula da dukkan alamuranki. Alfarma daya za ki yi mun, duk lokacin da zan sumbace ki kada ki ce min aa, ina matukar son in sumbace ki, na yi miki alkawarin ba zan wuce hakan ba. Da sauri Saade ta wara ido cikin jin kunya ta dube shi. A hankali ta ce, Yaya Sageer ina jin kunya!. Ya janyo ta gabadaya zuwa jikinsa, ya ce, I will take care of that daga yau, a hankali zan cire kunyar dukkanta har watarana da kanki za ki zo ki ce, Yareema Sageer.. Saade ta yi maza ta rufe idon ta. Ta cusa kai kasan filo. Shikuma ya yi amfani da wannan damar ya dauke filon ya kuma hade bakinsu wuri guda yana kissing din nata gently, softly, affectionately. Tun Saade na kokarin janyewa har ta soma lumshe yan idanunta. A zuciyarta tambayar kanta ta ke, wato bayan kissing din akwai abin da ya fi shi kenan anan gaba,tunda gashi Yareema yana cewa, ba zai wuce sumbar ba? To ko mene ne? Ko wace rana ce Yarima zai nemi hakan? Wannan din kadai sai ta rufe ido ta kuma kai zuciya nesa sabida nauyin sa..Idan akwai abin da ya fi shi a nan gaba ba ta san ya ya za ta yi da ranta ba. Sauran kwanakin su a Askira sai suka zamo na jinyar kafa da sassanyar soyayya, wadda Yareema Sageer yake matukar kokari wajen ganin bai wuce gona da iri ba. He is not going far beyond what he begged for. He is only kissing her, sumba mai sunan sumba in dai ga Saadatu ne ba ya taba gajiya, baya taba koshi. Rannan ya ce mata, “theres charisma in kissing You. Kwanansu shidda a gidan su na Askira kafarta ta kame, ya ce ta hada duk abin da ta ke bukata gobe za su bi jirgi tare da Maimartaba da Fulani zuwa Abuja. Alkawarin da Askirama ya yi na kaita Abuja gidan mijinta da kan sa ya ce zai cika shi da yardar Ubangiji. Washegari tunda asubahi an shirya motocin da za su kai su Maiduguri (filin jirgi) sannan an zabi wadanda za su yi wa Maimartaba da Fulani rakiya, cikin masu rakiyar Fulani har da Fanna wanda hakan ya faranta ran Saadatu sosai, fargabarta ta komawa Abuja ta ragu kashi sabain cikin dari ganin irin wannan rakiyar gata da zaa yi mata. ****** Jirgin Azman ya sauke su a Abuja da yamma lis. Direban Dr. Sageer da na abokinsa Dr. Ziyad su suka zo suka kwashe su a manyan motoci zuwa gidajen malamai na NTNU. Tunda suka sauko daga jirgi yake ta gwada kiran lambar Sultana tana ta ringing amma ba ta dauka ba. Ya san duk inda ta ke zuwa yanzu ta dawo gida. So yake ya gaya mata tahowarsu tare da su Maimartaba don ta sa Uche ya tanadi abinci na musamman, amma ga wayar tana ta ringing ba ta daga ba. Ya yi tsaki, sannan ya kira Uche, wanda ke Baskwata a lokacin yana wanka, ita ya kamata ta bai wa Uche umarni ba shi ba, amma da bai same ta ba dole ya kira shi. Uche, Im already on the way with his Royal Highness, cook to your best, deliciously. Madam ta dawo? Uche ya yi shiru da waya a kunne, ta ya ya zai ce masa ta dawo, amma tun shigowarta tana main falo tana drinking kada ya zo da iyayensa yanzu? Kafin ya hada amsar da zai bai wa ogan nasa Sageer ya kashe wayarsa. Da sauri Uche ya hau sake kiran shi a waya amma rashin kyawunnetworkyasa yakasa samun shi. Kuma kafin ya sanya suttura a jikin shi ya wanke kumfar jikin shi ya baro baskwata (boys quarters) zuwa cikin gidan ya ji saukar dirin motocinsu suna shigowa get din gidan. Duk da yake arne ya san drinking alcohol is very bad to Muslims more especially women in marital homes, its against their religion, tradition and culture. Sai ya ji tausayin ubangidansa ya kama shi, don yana son Sultana. Allah ya sa kada father din ya ce ya sake ta. Yana daga kitchen wanda ya bi ya shigo ta kofar baya cikin mutuwar jiki yana lekensu ta window suna ta shigowa cikin nadi da amawali da kaya na sarauta a jikin kowannensu. Ga wata mace kuma an lullube a cikin alkyabba wata baiwa ta riko ta. Yarima ya bude kofar falon wadda sakayota kawai aka yi. Maimartaba shi ne farkon shiga don Yareema ya dan ja baya ya bashi hanya cikin girmamawa sannan Fulani ta mara masa baya. Suka kuwa yi kyakkyawan gani, wanda ba su jin za su taba mantawa a rayuwar su. Aisha-Sultana ce daga ita sai half vest da wando three quarter baki, tana kwance magashiyyan cikin manya-manyan kwalaben whiskey. Ba barci ta ke ba, kuma tana jin shigowarsu amma ko yatsarta ba ta iya motsawa, idanunta a lumshe. Ba su taba ganin GIYA a fili ba, amma kallo daya suka yi wa kwalaben da kuma yanayin da ta ke ciki suka gane komai. Ko da ma can suna da labari. Kunya! A wurin Yareema kamar ya ce da kasar ta tsage ya shige. Allah ya so shi yan rakiyar sun tsaya daga waje, yau da ya gama tozarta a rayuwarshi. Maimartaba sai kawai ya juya ya ce da Fulani, Bana zama a inda ake saba wa Allah, sannan yata ma ba za ta zauna ba. Ku juya mu tafi. Yareema ya sha gabansa yana roko. Alaguburo, Allah Kawun jo na tuba, na bi Allah na bi ku. Zan dauki mataki a ba ni dama ta karshe. Nan shi ne gidan Saadatu sabida cikin makarantar su ne. Ita na riga na kama mata wani gidan a Maitama, kusa da wajen aikinta. Maimartaba ya yi tsaki ya fice, amma Fulani ba ta fita ba. Ya ce da dogarawan da ke bakin kofa a nema masa hotel din da zai sauka gobe da asubah zai juya inda ya fito. Fulani ta ce da Yarima wanda ya zauna ya dafe kansa da dukkan hannayensa.Bai taba wulakanta irin yau ba. (Don ma ba shi aka kama a gidan Dr. Ziyad ba ke nan!) Kunyar duniya kenan da tozarcinta kafin a je lahira. Me ye riba a kin bin umarnin Allah kowanne iri ne? Bai san ya zai yi da Sultana ba, ya yi fadan ya yi nasihar, ya yi barazanar duka a banza. Har duka ya yi duk da ba girman sa ba ne. Nadamar nashi laifuffukan suka kara lullube shi. Mai yiwuwa ta nan Allah yake kama shi kan nasa laifin. Don kuwa duk da halin ta yana son kayar sa. A fili yake fadin, Astagfirullah! Astagfirullah!!. Ya kuma alkawarta ma ransa daga wannan ranar duk wani sabon Allah ya bar shi. Sultana kuma zai dauki mataki na karshe a kanta. Fulani ta dafa kafadarsa, Ka kwantar da hankalinka Yareema, zan ba shi magana. Amma tunda ya ce ba zai zauna ba, to da gaske ba zai zauna din ba. Ka yi hakuri ka tashi mu je ka nema mana masauki, ita Saa zata zauna tare dasu Fanna zan bashi hakuri. Tuni Fanna ta janye Saadatu zuwa dakinta wadda ke rufe cikin alkyabba ba ta san a kan me ake cece-kuce ba. Yareema ya mike yana hararar Aisha-Sultana wadda ke sakar masa murmushi cikin maye. “Darling you.you are back? Bai ce mata komai ba ya bi bayan Fulani suka fita. Hotel din TRANSCORP HILTON ya kai su, ya kama musu daki na musamman kwana daya. Saadatu ba ta san su Fulani sun juya ba, ita da Fanna kawai aka bari a dakin, ta dauka tare da su za su kwana cikin gidan suna wani dakin ne. Fanna kuma sai dauke mata hankali ta ke da hira don kar ta gane abin da ake ciki. Haka ki ka tsara dakinki ranki ya dade gwanin shaawa? In mun tafi gobe sai ki kara tsara komai na gidan yadda ki ke so tunda ke kadai za ki zauna a cikin sa. Na ji maigirmaYarima ya ce Uche ya hada kayan uwargida ya sa a mota. Ki kula da cikin mijinki ta fannin girki bana jinki, na san Yareema ya gama morewa. Haka ta yi ta hilatarta da daddadar hira har Yareema ya je ya dawo daga kai su Askirama Hilton. Ya leko kadan ya ce da Fanna, In kin gama direba yana jiranku a waje zai kai ku inda za ku kwana. Fanna ta gurfana tana godiya hadi da kirarin da suke yi masa, sannan ta dau jakarta tare da cewa da Saadatu. Sai mun zo suna. Idon Saade ya yi rau-rau kiris ta ke jira ta fashe da kuka. Ta ce, Fanna Fulani fa? Au, ta ce a yi miki sallama sun tafi masauki ita da Askirama, gobe kafin mu wuce za ta leko ku yi sallama. Saade sarkin kuka nan da nan ta fara. Ya tabbata kenan ta shigo kwaryar sauran mata. Aure yau ya raba ta da Fulani, rabuwa ta har abada sai dai a je ziyara. Ta yi kuka, ta yi kuka bayan fitar Fanna da ta gaji ta shiga bayinta ta daura alwala, tana jin Yareema yana ta yi wa Uche fada da harshen turanci kamar Charles Dickens ya diro Nigeria, kan don me sanda ya bugo masa waya bai gaya msa Sultana tana falo drunkard ba? Uche ya rasa kalaman kare kansa sai cewa ya ke, “Im very-sorry Sir.. Yana so ya yi masa bayanin cewa wanka yake yi a baskwata lokacin, kuma kafin ya harhada bayanin da zai masa akan harshen sa ya kashe waya, ya bi bayan kiran network ya hana shi samun sa, ko kumfar jikin sa bai tsaya wankewa ba yasa wando ya fito kawai sai ganin motocin su yayi har sun shigo harabar gidan amma Yarima bai bashi damar yin wannan dogon bayanin ba sabida yadda ransa ya yi mugun baci. Wata muguwar tsawa ya buga masa ya ce ya bace masa da gani. Saade ta kyabe baki ta tada sallah. Ai gara da Askiraman ya gani da idonsa, watakila shi in ya hana ta ta daina, tunda mijin nata ba shi da fuss a kanta, har nema yake a rufa mata asiri. Ba ta san ya ya suka kare ba shi da matarsa. Ta fito ta shiga kitchen don ta sama wa cikinta abin da za ta ci ba ta gansu a falo ba, ba ta ga kwalaben giya ba. Ta dan tsaya tana nazarin falon ta ji tashin motar Yareema, ta daga labule ta leka ta waje sai ta hango shi ya yi ribas ya nufi get zai fita, Sultana tana gefensa kanta a kwance jikin kujera. Tsaki ta yi cikin jin kishi, ta ce a ranta, Da kyar in ba shi ya dauke ta ya sa ta a motar ba, don in ta sha ta yi tatil din nan ko yatsanta ba ta iya motsawa, da ma ta gama gane shi gwani ne wajen daukar matarsa a hannu. Ta zubo abinci iya wanda za ta iya cinyewa da Uche ya girka yanzun nan, ta zauna a dining tana ci. Shiru-shiru har ta gama ta koma daki babu Yareema. Tun tana duba agogo har barci ya ci karfinta, ta kishingide a kan gadonta, gadon yammatancinta a NTNU. A yau ya rikide ya koma na gidan aure! Kudurar Ubangiji ta fi ga haka. Duk da bacci ta ke, amma zuciyar ta cike ta ke da damuwa, Yarima ya manta da ita cikin gidan ne ko kuwa? Ya dau matarsa sun fice. Ba ita ta bude idanunta ba sai da masallacin gidajen Malamai na NTNU suka tada sallar asubahi. Ko da ta tashin ma da Yareema a ranta ta tashi. Ta yi zaton ganinsa a gefenta yana barci ko sallah, don ta gane shi maabocin sallah ne a zaman su na Askira kwanaki bakwai tare, kuma ya gaya mata muddin suna tare ba su ba raba makwanci, tun tana jin nauyi da kunya har ta saba da hakan cikin kwanaki bakwai da suka yi tare matsayin maaurata. Itama in ba sa manne cikin duvet bata jin dadin barcin. Amma ga mamakinta har zuwa lokacin Yareema bai dawo ba. Tana alwallah tana hawaye, hawayen da ba ta san dalilinsu ba. ***** Har karfe sha biyun dare yana tare da Aisha-Sultana a sabon flat din da ya kama mata a Maitama, jira yake giya ta sake ta, ta wartsake sannan su yi magana. Tunda suka zo ta ke barci, maigadin da ya daukar mata shi ya fiddo duk kayan sanyawarta jaka-jaka daga bayan motar Yareema ya shiga da su ciki, wadanda ya sa Uche ya kwaso mata. Da ya kashe motarshi ya dauke ta a kafadunsa zuwa cikin apartment din, ya kwantar da ita bisa gado kasancewar ya yi order already an zuba komai na bukata a gidan. Haka ya zauna zaman jiranta ta wartsake, ya tashi ya yi alwala ya yi sallar isha, sannan ya zauna kiraye-kirayen waya, ya gabatar da dukkan uzurorinsa ta waya. Amma duk abin nan da yake Saadatu na makale cikin ransa. Allah-Allah yake Sultana ta farka su yi maganar da yake so su yi, ya tafi wajen Saadatu. Sulatana ba ita ta farka ba sai karfe sha biyu na dare. Ta yi mika sannan ta hau bude idonta a hankali, sai ta ganta a bakon wuri. Ganin Sageer a gefe yana sallah, sai tsoronta ya ragu. Ta sani ko ma ina ne shi ya kawo ta kenan a lokacin da ta ke cikin maye. Darling ina ne nan? Ta tambaya tana hamma. When did you get back? I missed you!. Hararar ta ya yi, sannan ya dauke kansa. Can kuma ya dago ya dube ta cikin ido. “My father saw you drunk!. Sultana ta zaro ido, Oh dear! Me ya sa ba ka gaya min kun taho ba? Ya galla mata harara, ya ce, sau nawa zan ce miki in kina son zamanmu ya dore sai kin bar shan giya? Ta zumburo baki, sannan ta mike ta yi kan Sageer ya soma ja da baya ya kuma kira sunanta da karfi, Sultana! Ba ta fasa abin da ta ke ba, ta ce, Ai ni ma na gama magana, ranar da ka daina branching da yammatan bisa titi ni ma zan daina shan giya tell your Dad Im sorry. Ya ce, Sultana na dade da bari, har na kara aure. Don Allah ki daina in ba haka ba rabuwarmu ita ce mafi alkhairi. Sauran maganar makalewa ta yi a makoshinsa sakamakon cewa, Aisha Sultana ba ta ba shi damar karasawa ba. And then she seduce him. Da ma ya dade cikin kishirwa, sai ya kasa tankwabe tayinta da kaunar da ta ke kokarin nuna masa. Ga dukkan alamu ba ta ji cewa da ya yi ya kara aure ba, idan kuma ta jin, to ba ta fahimta ba. Yareema Sageer bai tashi dawowa Sageer dinsa ba sai karfe hudu na sulusin dare. Lokacin da kuma ba zai iya tafiya gida ba. Ya tuno Saadensa, da kadaicin da ya barta ciki ranarta ta farko a gidan mijinta. Amma a addinance bai aikata haramun ba sabida girkin Sultana ne, ya yi mata kwana bakwai dinta da addini ya bata babu kwange. Ya duba agogo ya kuma dubi Sultana da ke ta sharar barci. Ta inganta masa daren jiya kamar ba gobe, iyaka iyawarta. Don dai ta mantar da shi laifinta amma duk da haka ya kasa mantawa, abu in ya hada da Maimartaba ba ya daukansa da sauki. Ya yi wanka ya tsarkake kansa ya dauro alwalla. Bai jima yana nafilfili ba ladani ya kira sallar asubah a masallacin da ke kusa da su sai ya ga bara kawai ya shiga masallacin tunda ba su da nisa daga can ya wuce gidan Saadatu, sai ya hukunta Sultana. Ya hau dukan bayan Sultana ya ce ta tashi ta yi sallah shi zai wuce masallaci daga can ya wuce gida. Ta ce, Wane gidan kuma? Na dauka mun yi parking zuwa nan ne? Ya ce, Kin yi parking dai, amma mu muna can, ke da gani na sai ranar da ki ka bar GIYA Sultana. Da haka ya fice tana ba shi hakuri, amma ko juyowa bai yi ba. Ita ma ta yi shirin ofis ranta a bace. Ba abin da ta ke so a duniya irin Yareema Sageer. Shi kadai ne daidai da rayuwarta haka babu mai wahalar da ita a duniya irinsa. Amma me ya sa ya kasa gane cewa alcoholism is an addiction? Tana tuki cikin hawaye har ta isa wajen aikinta da ke kan titin Aguiyi Ironsi. Ya karya kan motar ya shiga gidan sa. Yayi horn maigadi ya taso da azama ya bude masa kofa, misalin karfe shidda na safe, yana shigar da hancin motar maadanin ta yana harhada kalaman da zai yi amfani da su wajen lallashin Saade bisa wannan babban laifi da yayi mata da bai san yadda zai yi ya wanke kansa ba. ****** MU KARASA A LITTAFI NA 4. KADA KU DAMU TARE SUKE. TAKU HAR ABADA; SUMAYYAH ABDULQADIR (TAKORI). 26|11|2021 NA HUCE.. LITTAFIN SUMAYYAH ABDULKADIR Hawayen da yake ta rikewa ne suka kwace masa, ya juya kadan ya dubi Rahinah wadda ke kallon bayansa a lokacin, suka kuma hada ido, ji ta yi zuciyar ta na son karyewa (rauni irin na diya mace na son mamayar ta) amma ta amince wannan shine decision mai kyau ga rayuwar ta. Sai ta maida idanunta ta lumshe su a hankali. Tana sauke ajiyar zuciya. Shi kuma ya sa kai ya fita daga dakin, babu ko waiwaye. Kamar yadda yake ji a ransa ba zai kara waiwayar RAHINAH OMAR a rayuwarsa ba. Ko da bayan cikar burin ta, na zama cikakkar otorhinolaryngologist. **** Ta dauki hoton karamin kyakkyawan yaron mai kama da ubansa a komai tana kallo with so much adoration, hawaye na sauka a kan fararen kundukukin ta. Ta san yanzu ya girma, watakila aji hudu na firamare? Cikin kowanne hali dai ta san zai kula da shi. Damuwar ta ba a kan kulawar da yaron zai samu ba ne domin hakika tana da tabbacin HABIBUNAHUCHEzai kula da dansa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa. Damuwar ta akan yadda har gobe ta kasa kallon kowanne namiji da idanun sigaraure, kowa ya zo sai ta ga bai kai shi ba, ko farcen kafarsa bai kama ba, ko da kuwaya fi shi komai na rayuwa. Duk da cewa ta san shi ne kawai a matsayin dalibin jami'ar Cologne ba'a matsayinsa na yanzun ba (mamallakin NAHUCHE HOTELS) amma tana bibiye da duk wani fadi-tashinsa na rayuwa tun daga ranar da ya raba ta da Dan su. Dalilin bibiyar ne ba ta sani ba har yau, tunda ita ta ce bata son sa. Farin jini kam har bata san irin nata ba, manema ba irin wadanda Allah bai ba ta ba, kuma burin Dada shine ta yi aure tun kafin Allah ya dau ranta, amma har gobe ta kasa kallon kan sauran maza daga shi sai dan mutanen NAHUCHE. The one that took away her pride na diya mace. Wanda ta tabbatar zuwa yanzu ya manta da ita, a irin shuhurar da Allah ya yi masa cikin shekaru goma kacal da rabuwarsu. Bata san hawaye take ba. Sai da ta ji dandanon gishiri a bakin ta. Hawayen da ta tabbatar ba za ta daina zubar da su ba har zuwa karshen rayuwarta. Idan har rayuwa ba ta koma yadda take a baya ba; with him aside. "Auren Wucin Gadi". "Auren kwanaki bakwai kacal". Wadanda abubuwan da suka wakana cikinsu sun fi tsayin na shekaru bakwai. Wanda ya samar da kaddarar Dan da ke a tsakani, Dan da silar zuwansa duniya ne ya yi connecting komai, ya hada zukata ya kuma raba su cikin kwanaki bakwai. Jami'ar Cologne din Jamus ita ce tushe, mafari, ginshiki na dukkan walagigin rayuwar da ta samu kanta. -Takori Downloaded From https://tknovels.com.ng