An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (The light of the soul) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* The writer of MATAR DAMISA MY ENEMY And now HASKEN RUHI *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ First EP 1 to 2 ★ *DELHI*★ *★SHAPRIS SHATTIMA* wani hamshaƙin mutum ne wanda a ƙalla bazai wuce shekara 35 a duniya ba, yana da bala'in kuɗaɗe wanda shima kansa bai san adadin su ba, bayan mahaifinsa ya rasu ya bar masa maƙudan kuɗaɗe wanda shi kaɗai ya ci gadonsa sakamakon shi ɗaya tilo iyayensa suka haifa, iyayensa sun rasu ne sakamakon hatsarin mota da suka yi, Shaprees yana da uwar ɗaki wato shugabar sa Madam Nablah wacce ta haramta masa dukiyarsa ta hanyar sirka masa su da kuɗaɗen jini, ta rinjaye shi zuwa fadar ta wato Devil's World. Da matarsa Sophia ƴar ƙasar Nigeria dake garin Maiduguri ƴar shuwa, ita ɗin ba kowa bace fa ce ƴar talakawa, Mahaifinta gadin maƙabarta yake, sannan ita ta kasance tallah take a bakin titi, anan Shapris ya yi ido huɗu da ita ya nace akan Auren ta ba tare da iyayenta sun so ba, domin sun san mahaifinsa ba ƙaramin mutum bane suna tsoron kar ɗiyarsu ta wulaƙanta, daƙer suka amince da Auren Shaprees da Sophiatu, daga baya ya tafi da matarsa can ƙasar Delhi dake shima ɗan Maiduguri ne, a can ya cigaba da gudanar da harƙoƙinsa na halal da kuma na haram domin ya kasance shi ɗin ɗan secret society ne.... Yau shekara goma da Auren Shaprees bai waiwaito Nigeria ba, Sophia tayi kewar iyayenta matuƙa kullum kukan ta shine Shaprees ya dawo da ita gida amma sam ya ƙi duk da yana matuƙar ƙaunar matarsa Sophia, yau suke gudanar da walimar cikar shekara goma da Auran su a ƙasar Delhi, kowa ya hallaru a wani wantalelen gidan party, abokan harƙalla duk sun hallaru. Wata zankaɗediyar mata ne take zaune a wani tsararren kujera, kana ganinta kasan ƴar hutu ce domin ba ƙaramar Hajiya ba ce, tana sanye da kayan ƙyale-ƙyale a jikinta wanda duk ya kasance komai na gwal ne da zinare, wannan ita ake ƙira da Madam Nablah or Hajiya Nablah ita kaɗai tana zaune sai pressing phone ɗin ta take, can taji an furta *Devil Mom* kamar daga sama Madam Nablah taji maganar nan tana tunanin wani mai ƙarfin izzah ne yazo kanta yana ƙiranta da sunan nan a halin yanzu, alhalin wannan sunan ba'a furta ta sai a cikin fadar ta mai suna Devil's World.... Madam Nablah sai da ta ɗan jinkirta kafin ta ɗago da kanta a slow tana bin wanda ya ƙira ta, dara daran idanuwanta ne suka sauƙa akan wata dirarriyar mata fara tas wacce tasha makeup tana sanye da Net cloth doguwar riga har ƙasi, Madam Nablah kallon matar tayi up and down sannan tasau murmushi tare da faɗin "Happy Anniversary..." Sophia hararar ta tayi daga bisani ta zauna a ɗaya daga cikin jerukan kujerun wurin tana faɗin "10 years married without Babies..." Madam Nablah glass cup ta ɗauka tare da kai lemon dake cikin cup ɗin kan lips ɗin ta, sai da ta kurɓa ta ajiye kafin ta ce "Oh so sorry my daughter..." Sophia a fusace ta ce "i am not your daughter my friend because baki cancanci ki zama uwa ba..." Madam Nablah murmushi ta sau sannan ta ce "kamar yanda har yanzu kike zaune ba Babies..." Sophia ta ce "Shaiɗaniya kawai ai ke kika mun sanadi, kina tunani duk abinda kika umarci mijina baya sanar mun ne? tin shekarun baya nasan da cewa ke kika haramta mun samun ƴaƴa ta hanyar yin barazana da rayuwar mijina, kin bashi zaɓi biyu rayuwarsa ko mahaifana, inason mijina shiyasa ban goyi bayan rasa rayuwarsa ba na amince akan salwartar da mahaifana, wallahi kin cuce ni, kuma bazan taɓa yafe miki ba, biyayyan da mijina yake miki bai hana ki cutar da shi ba, ke kin mallaki ƴaƴanki a hannu amma shi kina masa baƙin cikin samu nasa farin cikin..." Zaro ido Madam Nablah tayi tare da faɗin "Keee! wa ya sanar miki cewa bazai haihu ba? shima zai samu nasa ƴaƴan amma bata tsatsonki ba..." Girgiza kai Sophia tayi sannan ta ce "ki sa a ranki cewa babu sirrin da zaki sanar masa wanda zai ɓoye mun, duk abubuwan da kike shiryawa na makircin ki na sani..." Madam Nablah ta ce "haka kuwa wata rana zai sanar miki cewa ina buƙatar rayuwar ki..." A zabure Sophia ta ɗauki kwalba zata kwaɗa mata taji an riƙe hannun ta wanda take ɗauke da kwalbar, a hanzarce ta ɗaga kanta sama tana ganin wanda ya riƙe mata hannun, miƙewa tayi tana kuka ta ce "Shapris kana jin abinda take fa ɗa koh?..." Rungumar ta yayi tare da faɗin "ki kwantar da hankali, ki daina saka abu a ranki..." Sophia tayi saurin katse shi da cewa "taya zan kwantar da hankali na kana tare da wannan shaiɗaniyar mata marar imani..." Shapris ya ce "Please Sophia! ki koma gida zan iso ki..." Tana kuka ta ce "Oh kana so na tafi ta ƙara shirya maka wani makirci ko?..." Wani irin tsawa ya daka mata tare da faɗin "Please Sophia..." Haka tana kuka ta bar wurin da gudu, juyawa ya yi ya bi bayanta da kallo cike da damuwa, jin an ambaci sunansa ne yasa ya juya yana kallon Madam Nablah wacce ta miƙe tana shirin tafiya ta ce "around 2am mu haɗu a Devil's World muna da meeting..." Daga nan tayi tafiyar ta, shi kuwa ya bi bayan matar sa... Akan gado ya tarar da ita sai sharar kuka take, shima zama ya yi cikin sassanyar murya ya ƙira sunan ta tare da faɗin "meyasa kike damun kanki akan abinda ba canzuwa zai yi ba.." Ɗagowa tayi tana kuka ta ce "meyasa bazan damu ba, bayan rabani da tayi da mahaifana yanzu kuma rayuwata take nema fa?..." Girgiza kai yayi tare da faɗin "hakan bazai taɓa faruwa ba, ke ɗin rayuwata ce rasaki dai dai yake da rasa rayuwata Sophia, ina sonki wallahi..." Tana sharar hawaye ta ce "amma meyasa kafi ɗaukar Madam Nablah da mahimmanci akan ni?.." Shafrees kamar zai yi kuka ya ce "to ya zanyi Sophia? Rayuwar mu gaba ɗaya a tafin hannunta yake, a yanzu zata iya salwartar mana da rayuwa, shiyasa nake so kiyi taka tsantsan da ita, kina binta a hankali, saboda haka nake yin duk abinda ta ce nayi..." A zabure Sophia ta miƙe tana faɗin "cab ɗin to wallahi babu wanda ya isa ya saka ni na yiwa wannan shaiɗaniyar mata biyayya, bazan bita a hankali ba sai dai ta kashe ni, ai yanzu ma ta gama da rayuwata tinda ta dishar mun da farin ciki na, wai ma Shapris meyasa bazaka fita daga shirginta ba?..." Shapris idonsa akan Sophia ya ce "barin ta dai dai yake da barin duniyar nan, duk wanda ya shiga ƙungiyar Madam Nablah baya taɓa fita sai dai gawarsa ta fita, wani kuwa ɓatar da gawarsa take, tanada ƙarfin iko na bala'i, tsafin da Madam Nablah take da shi Allah ne kawai masani, ina cikin ƙungiyar ta ne amma zuciyata sam bata tare da ita, yanzu ta ina zan fara tinkarar barin ƙungiyar Devil's World? Sophia bazan iya ba, in har kuwa zanyi to sai dai ki nema mun gafarar Ubangiji domin zaki rasani ne, ki tayani da addu'a..." Sophia tana kuka ta durƙusa a gaban Shapris tare da riƙo hannayensa tana faɗin "Insha Allahu babu abinda zai same ka mijina, zan cigaba da addu'a zaka bar ƙarƙashin zalunci, nidai nasan halin mijina ba azzalumi bane sannan baya cutarwa, suna ne kawai ka rataya a wuyanka amma nasan baka jan jinin kowa..." Ya ce "ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru da ke nayi miki alƙawari bazan taɓa barin a zalunce ki ba a karo na biyu, sannan idan Allah ya kaimu gobe zaki tafi Nigeria ki je ki dubo iyayenki tsawon shekara goma rabonki da su..." Farin ciki ta shiga yi ta rungume shi tana godiya, da haka suka sha soyayyar su har tayi bacci, shi kuwa ko rintsawa bai yi ba domin ƙarfe 2 na dare sunada meeting ɗin da zasu gudanar... Misalin ƙarfe 2:30 na dare cikin fadar Devil's World dake can ƙasin ruwa wasu mutane ne suke tsatstsaye duk suna sanye da dogwayen riguna jajaye masu huluna wanda ya rufe musu fuskoki, da wani dogon tebur a tsakiyar su kowa da kujerar zaman sa, sun kasu part biyu ko wani layi mutum takwas ne suna facing juna a yayin da tebur yake tsakiyar su, a can ƙarshen tsakiyar tebur kuwa Shugabarsu ce wato Devil Mom ita kuma tana sanye da baƙar doguwar riga mai hula wanda ya rufe fuskar ta sai iya red lips ɗinta ne a waje wanda yasha jan baki, ita kaɗai ce a zaune akan wani tsararren kujerar ta na gwal wanda ya fita daban a cikin su, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya duk sauran fuskokin su a rufe suke amma tasan kowa a wurin, ita kaɗai ce mace kuma shugabar su mai ɗauke da ƙarfin izzah da tsafi na ban al'ajabi, lips ɗin ta ne ya fara motsi sai fararen hakwaranta kawai kake gani yanda take juyar da jan harshenta tana faɗin "ku zauna..." Sai a yanzu ta basu umarnin zama wanda tin tinin suke tsaye, kowa yana ajiye da cup na ruwan jini a gaban sa, haka kowa yake ɗaukan glass cup mai ɗauke da jini yana sha tamkar lemo, Madam Nablah ba tare da ta buɗe fuskar ta ba ta ce "Shaprees meyasa har zuwa yanzu idan an baka jini baka sha? tsawon shekaru da dama kana cikin ƙungiyar nan why?..." Shaprees wanda yake zaune daga Nesa-nesa shima fuska a rufe ya ce "I don't know why..." Madam Nablah ta ce "yanzu ka ɗauka kasha jinin nan, umarni nake baka..." Shaprees ba tare da ya motsa ba ya ce "Devil Mom I can't ..." A fusace Madam Nablah ta dunƙule hannunta tare da bugawa akan tebur haɗe da furta "Shaprees Shattimaa babu mai ƙarfin ikon bijirewa magana ta sai kai, ba wai bazan iya ɗaukan hukunci akan ka bane, yanzu inaso kayi abinda nace now now..." Shaprees ta cikin hula ya kanne idanuwansa cike da takaici ya ɗora hannunsa akan cup, haka hannunsa yake kakkarwa gaba ɗaya ya kasa ɗaukan cup ɗin, haka yasa hannu biyu yana ƙoƙarin ɗago da cup ɗin haka hannayensa duk suka ɗau kakkarwa, gaba ɗaya ya kasa control kansa daga ƙarshe cup ɗin ne ya kuɓuce daga hannunsa ya faɗo ƙasi duk jinin ya wantsalu, wani irin haɗiyar yawu ya yi cike da tsoro da fargaba, ya rasa gane meye matsalar a duk lokacin da aka tilasta masa shan jini sai hakan ta faru. Madam Nablah jinjina kai tayi tare da faɗin "many times hakan yana yawan faruwa but don't worry I'll do something..." A fusace ta miƙe daga kan kujerar tayi sama kamar mai furawa, bata taɓa taka ƙasi in har ta shigo fadar ta ba, komai a sama take yinsa ko tafiya take a sama take yin sa, Shaprees bai ankara ba ya ji an ajiye masa wani cup mai ɗauke da jini a gaban sa tana daga bayan sa take faɗin "dama ta ƙarshe Shaprees! zan baka zaɓi biyu kuma a ciki dole kayi ɗaya a yanzu yanzun nan saboda haka na buƙaci a taru yau domin yau ba ranar meeting bane, a cikin zaɓin da zan baka dole kayi ɗaya Shaprees, zaɓi na farko ka sha jinin nan ko ta halin ya ya ne, zaɓi na biyu ko kaban rayuwar matarka a yanzu..." Shaprees wani irin bugun zuciya ya ji daman tsoron wannan ranar yake, ba shi da kowa sai matarsa shiyasa idon Madam Nablah yake kanta sannan jinin Sophia da Madam Nablah bai zo ɗaya ba shiyasa basa shiri, Sophia ta kasance mahaddaciyar Alkur'ani mai girma ne sannan tanada yawan ibada a koda yaushe, ta tsaya akan mijinta da addu'a shiyasa har yau Madam Nablah ta kasa cin galaba akan Shaprees, shiyasa take neman rayuwarta domin ta mallaki ruhin Shaprees wanda bazai taɓa bin umarnin kowa ba in ba nata ba.... ___________________________________ Sophia tin lokacin fitar mijinta ta tashi zaune daman ba wani dogon bacci tayi ba, haka ta tashi ta ɗauro alwala ta fara jero salloli tana addu'a da nemawa mijinta tsari daga wurin Ubangiji, haka nan tana kan sallaya ba abinda take sai adduoi hakan yasa Shaprees ya kasa shan jinin da aka bashi, kullum a cikin haka ake..... Ita kuwa Madam Nablah tasa Shaprees a gaba akan zaɓin da ta bashi, yana matuƙar ƙaunar Matarsa shiyasa ya zaɓi shan jini amma kuma hakan ya gagara yu wa, da zaran ya ɗauki kofin jinin sai ya ɓarar da shi ƙasi shiyasa Madam ta zaɓa masa rasa matarsa domin a cewar ta hakan shine maslaha a tsakanin su, already tasan Sophia ce take taimaka masa shiyasa ta kasa cin galaba akan sa, Shaprees haka yake kukan zuci yana tunanin matarsa Sophia, Ita kuwa tana can sai karatun Alkur'ani mai girma take bayan ta kammala salloli da addu'o'i, Shaprees bashi da ƙarfin ikon da zai dakatar da faruwar haka domin Madam Nablah tana kwance akan gadonta zata iya kashe mutum daga can nisan duniya. Wani irin murmushi tayi na mugunta sai yawo take ta mu su a saman kan su, tana yawo a sama tare da aiwatar da tsafinta tana maganganu... Shaprees gaba ɗaya idanuwansa ne suka yi jawur tsabar tafasa da zuciyarsa ya ke yi, haka yake daure wa domin faɗan da yafi ƙarfinka sai ka mayar shi wasa... Madam Nablah duk wani ƙoƙarin ta yana shirin fin ƙarfinta akan Sophia domin duk wani tsafin da ta tura wurin ta sai ya dawo mata, abun ba ƙaramin mamaki ya bata ba, hannu tasa ta ɗage hular kanta wanda ya rufe mata fuska tare da wurga ƙwayar idanuwanta kan Shaprees, tasau murmushi sannan ta ambaci sunansa "Shaprees..." A taƙaice ya ce "Madam Nablah..." Ta ce "Da hannunka nake so ka kawo mun Sophia nan wurin..." Cikin takaici ya ce "impossible..." Zaro manya manyan idanuwanta tayi waje a fusace ta ware tafin hannunta sai ga wani baƙin hayaƙi yana fito wa nan ta saita goshin Shaprees wannan hayaƙin ya shige shi nan danan tunaninsa ya juye sai abinda ta ce masa na lokaci ƙanƙani kafin ya dawo hayyacinsa, A fusace ta ce "ina buƙatar ganin tsayinka..." ba tare da ɓata lokaci ba ya miƙe tsaye fuska a rufe sannan ta ce "yanzu-yanzu kaje ka taho mun da Sophia now now..." Ba tare da ya bata amsa ba ya yi gaggawar ɓace wa ɓatt, bai sauƙa a ko ina ba sai a bedroom ɗin matar sa Sophia, Sophia ganin mutum a tsaye tsangamgam ko motsi babu yasa tayi saurin ɗagowa domin tasan sauƙar sa, hannu tasa ta rufe Kur'anin da take karanta wa daga bisani ta buɗe wardrobe ta ajiye tayo kan sa tana furta "Shaprees kaine a wannan yanayin? meyasa fuskarka a rufe nan fa ba wurin meeting ɗin ku bane, ka shigo gida ne..." Hannu tasa ta buɗe fuskarsa lokaci guda tayi baya a tsorace tana binsa da kallo ganin yanda ƙwayar idanuwansa yake chanza colour yana fitar da farfatsin wuta, Cikin sassanyar murya ta furta "Shaprees..." Kafin ta ankara har ya damƙo hannunta suka ɓace a tare, basu sauƙa a ko ina ba sai a gaban Madam Nablah wacce take zaune a kan katafaren kujerar ta na sarauta wanda sai ka taka matakala kafin ka iso kan kujerar dake sama, Madam Nablah ganinsu yasa ta tintsire da wata irin mahaukaciyar dariya.. Sophia idonta akan Madam Nablah ta ce "daman nasan aikin ki ne, shin lokacin rabani da rayuwata ce ya yi?..." Madam Nablah girgiza kai tayi sannan ta ce "bazan barki kiyi mutuwar sauƙi ba, sai naga yanda Ruhinki zai wulaƙanta a cikin fada ta, sai na nuna miki yanda ƙarfin ikona yake, sai na shafe labarinki a doron ƙasar nan, zan ɓatar da gangan jikin ki yanda babu wanda ya isa ya san yanda kike, Ruhinki kuma haka zata rinƙa zagaye cikin hayaƙin uƙuba ta..." Sophia cike da jarumta ta ce "haka kuma Ruhina saita hanaki sukuni, sai ta hanaki bacci, Ruhina da hannunta zata sheƙe ki, a shirye nake da ganin duk wani ƙalubalen ki Shaiɗaniyar Uwa..." A fusace Madam Nablah ta fitar da wani haske daga cikin tafin hannunta tare da wurga mata shi, da wannan hasken Madam Nablah ta ɗago ta sama tana juyar da ita, sai da ta gama wahalar da ita kafin ta fara raba Ruhinta da gangan jikinta, daga sama gangan jikin Sophia ta faɗo ƙasi yaraf sai Ruhinta da Madam Nablah ta sauƙar da ita ƙasi da wannan hasken hannunta, Ruhi tana tsaye Madam Nablah ta ce "yau zan nuna miki cewa Devil Mom ba sa'ar kowa bace, ki biyo ni..." Madam Nablah ce tayi gaba sai Ruhi da take binta a baya, sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa a cikin fadar ta kafin ta buɗe wani ƙofa mai bala'in girma tana buɗewa sai ga wani irin iska mai ƙarfin gaske ya ɗauke Ruhin Sophia zuwa ciki, ciki kuwa wani irin haske ne ga hayaƙi kamar gajimare baka iya ganin abinda yake ciki tsabar tsafin da Madam Nablah tayi a wurin, ana shiga da Ruhin Sophia ƙofar ta rufu da kanta, murmushi kawai Madam Nablah tayi sannan ta juya... Shaprees yana dawowa hayyacinsa ba abinda ya fara tarar wa sai gangan jikin Sophia dake yashe a ƙasi, a ruɗe ya yo kanta yana ƙiran sunan ta, "Sophia! Sophia!! Sophia!!! ki tashi dan Allah kar ki mutu ki barni dan Allah..." Madam Nablah ce ta bayyano lokaci guda tana faɗin "ka kwantar da hankalinka na kilacce maka matar ka, wannan gangar jikin ne babu amfanin da zata yi maka..." tana kaiwa nan ta ɗauki jikin Sophia ta hanyar iska ba tare da tasa hannunta ba ta buɗe wani akwati ta jefata a ciki tare da rufe ta sannan ta tura ta cikin ƙasin ƙasin ruwa... Shaprees haka yake kuka yana faɗin "Matata! Matata shin mezan ce wa iyayenta da suka bani amanar ta? na sanar musu cewa gobe Sophia zata koma Nigeria why?..." Madam Nablah zama tayi akan kujerar ta tana faɗin "kai kana cikin Secret society Amma sam babu jarumta a tattare da kai, duk abinda na buƙata sai na same shi, saboda haka yasa hatta mijina ban bar shi ba, sai da jininsa ƙarfin ikona ya ƙara wanzuwa sannan tsafina ya ƙaru haka yasa na yi sadaukarwa da jinin mijina kuma na jure hakan, why you bazakayi hakan ba, daman matar ka ce matsalar ka yanzu babu ita zaka iya gudanar da aikin ka, yanzu inaso ka shanye mun jinin dake ajiye a gefenka Shaprees..." Kamar yanda ta ce haka ya ɗauki cup zai kai bakinsa yaji kansa yayi wani irin sarawa lokaci guda ya yanki jiki ya faɗi, bai ƙara sanin halin da yake ciki ba... NEXT NEXT NEXT.... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 3 to 4 Shaprees bai tsinci kansa a ko ina ba sai akan katafaren gadonsa, farfaɗowarsa ke da wuya maimakon ya tarar da matar sa Sophia sai yayi ido huɗu da Madam Nablah zaune akan kujerar ɗakin tana jiran farfaɗowarsa, a zabure ya tashi zaune yana ambatar sunan Sophia, haka ya tashi a gurguje ya je gaban Madam Nablah yana faɗin "Please where is my wife? kar ki ce ta mutu dan Allah..." Dogon numfashi Madam Nablah ta sauƙar tare da faɗin "So sorry Shaprees a wannan lokacin ka rasa matar ka domin ni ba'a ja dani kasan da haka, amma kar ka damu zan baka kyautar wacce zata maye maka gurbin Sophia, domin ina matuƙar ji da kai hakan yasa bana iya cutar da kai duk da tarin laifukan da kake mu, kyautar da zan baka shine abu mafi soyuwa a rayuwa ta, duk duniya babu abinda nake so sama da abinda zanyi maka kyautar sa..." Shapris leɓɓensa na kakkarwa ya furta "wani abu ne?..." Madam Nablah tasan murmushi sannan ta ce "Ɗaya daga cikin triplets daughter na, Ƴan mata uku sune ɓangarorin jikina, to na mallaka maka ɗaya daga cikin su duniya da lahira kuma zata haifa maka kyawawan ƴaƴan da kake so..." Girgiza kai Shaprees ya yi sannan ya ce "a duniyan nan babu macen da zata kai Sophia a wuri na, kinyi kuskuren cutar mun da ita Devil Mom, domin ita ɗin rayuwata ce..." Madam Nablah ta ce "ga shi lokaci guda na sauya rayuwarka Shaprees, yanzu sabuwar rayuwa zaka cigaba da gudanar wa..." Tana kammalawa ta miƙe tare da faɗin "daga nan airport zan wuce domin a yau zan koma Nigeria..." Bata jira wata amsa ba tayi ficewar ta, Shaprees ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba ganin yanda ake juyar da kwakwalwarsa, haka ya cije lips ɗinsa na ƙasi acikin ransa yake furta "Madam Nablah a yanzu wasan zai fara, idan kin san wani baki san wani ba, kin taɓo mun tabon da bazan taɓa warkewa ba, kin rusa mun farin cikina, kin rabani da rayuwata, bazan barki ba sai na ɗau fansa akan ɗiyarki da kika mallaka mun, zan nuna miki waye Shaprees Shattima...." Haka ya gama maganganu a cikin zuciyarsa idanuwa duk sun yi jawurrr, A lokacin ya ƙira waya ya sanar cewa yana buƙatar yin transfer zuwa Nigeria. Domin yasan duk abinda Madam Nablah tasa a gaba sai ta kai ƙarshen shi, tinda har ya kasa ceto rayuwar Sophia to yasan ya rasa ta har abada kenam, shiyasa zai yanke hukuncin komawa Nigeria sai dai abu ɗaya yake shakka shine sanar wa iyayen Sophia cewa ya rasa ɗiyarsu... Haka yake ta wannan tunanin... *NIGERIA...* Wasu maka-makan motoci ne guda biyar suka yi parking a harabar wani makeken gida mai upstairs hawa huɗu, bodyguards ne a tsatstsaye sun fi goma kowa yana riƙe da bindigar sa wanda ya kasance sune masu gadin gidan, wani daga ciki ne ya buɗe murfin mota wanda a ciki wata miskilalliyar mata ne mai ɗagun kai haɗe da girman kai, ƙafarta ɗaya ta soma sauƙo da shi wanda yake ɗauke da wani irin takalmi mai tsinin gaske, a hankali ta sauƙo gaba ɗaya a daidai lokacin da wasu ƴan mata su uku masu kamanni ɗaya suka nufo wurin parking, haka suka jeru tsayinsu ɗaya, kamanni kuwa kamar mutum ɗaya, kyau kamar su suka halicci kansu ga farin fata kamar ƴaƴan turawa, amma sai dai kowacce da kalar zuciyar ta. Madam Nablah ce ta fito tana kallon su ɗaya bayan ɗaya daga bisani ta farkon tazo dab da Madam Nablah sannan ta rungume ta tana faɗin "your welcome Mom..." Madam Nablah murmushi tasau tare da shafa gefen fuskarta ta ce "my big daughter Tasleem, god bless you...." Jinjina kai Tasleem tayi sannan ta koma yanda take ta tsaya sai kuma ta biyu wato Nasreen itama rungumar mahaifiyarsu tayi sannan ta ce "your welcome Mom..." Madam Nablah sumbatar ta tayi akan goshi sannan ta ce " I Appreciate you my lovely second daughter...." Sai ga ta ukun itama ta zo ta rungumi mamanta tana faɗin "Mom I really missed you..." Madam Nablah itama rungumar ta tayi sosai a jikinta tana faɗin "Ohhhh so sorry my heart partner Asmeen ..." Sannan ta kallesu gaba ɗaya daga sama har ƙasa ko wacce dressing ɗin ta ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba, kowa da kalar dressing ɗin ta... Cikin nuna farin cikin ganin ƴan matan ƴaƴanta ta ce "my triplets daughter I missed you..." Su ma duk murmushi suka sake cikin jin daɗi da haka duk suka wuce ciki, a babban falo Madam Nablah ta tarar da wani matashin saurayi kyakkyawa mai ji da kansa yana zaune yana fuskantar television, yana ganin Madam Nablah ya yi saurin kawar da kansa gefe domin ko kallonta ma baya son yi, haka ya yi kamar bai ganta ba. Madam Nablah tsaya kallon sa tayi ga triplets a ta bayanta su ma suna tsatstsaye, murmushi tayi sannan ta ɗauki remove ta kashe tv idonta akan matashin ta ce "Abeesh shin baka ga shigowa ta bane?..." Miƙewa yayi tare da wurga mata wani irin kallo sannan ya ja dogon tsaki yabar falon, kai tsaye upstairs ya haura yanda room ɗinsa yake. Cikin ɓacin rai Madam Nablah ta kawar da idanuwanta daga kallon hanyar da yabi itama haura wani upstairs tayi ta nufi room ɗin ta ba tare da ta furta komai ba... Triplets duk kallon juna suka shiga yi ko wacce da saƙe-saƙen da take a ranta daga bisani su ma suka wuce room ɗin su dake can saman upstairs na ƙarshe hawa na huɗu, babban room ɗin su ne wanda manyan gado uku ne a ciki, ko wacce da gadonta, sai other room wanda ya kasance nan ne wurin kayayyakin sakawar su wardrobe da mirror sai wasu ƙofofi guda biyu bathroom and toilet room... Nasreen zama tayi a bakin gadonta hankali a tashe kamar zata yi kuka ta zabga tagumi bisa alamu kamar ta tafi dogon tunani, Asmeen ce ta zauna kusa da ita tare da dafa kafaɗarta ta ce "Nasreen!.." shiru bata amsa mata ba still ta sake ƙiran sunan "Nasreen!!..." Tasleem wacce ta gaba cire kayan jikinta ta zauna daga ita sai short jeans da singlet ko kallon yanda suke bata yi ba ta nemi gadonta ta kwanta tare da lalumar wani littafin English... Asmeen da ƙarfi ta sake ambatar sunan Nasreen a saitin kunnenta, a firgice Nasreen ta juyo tana furta "Na'am ABEESH...." Asmeen zaro manya-manyan idanuwanta tayi tare da faɗin "Abeesh kumaaaa?...." Tasleem wacce ta fara karanta littafi a ruɗe itama ta juyo tana kallon Nasreen, Aasmeen wacce take kusa da Nasreen dafa kafaɗarta tayi cike da tausayawa ta ce "Nasreen wai me yake damunki haka? Abeesh fa naji kin furta, mutumin da yake zaman ƙiyayya da mahaifiyar mu, kinaga ko zama baya yi a wurin da take amma kin ɗauki damuwa kin ɗora masa, meye matsalar ki ko dai son sa kike?..." Nasreen da sauri ta juyo tana kallon Aasmeen haɗe da girgiza mata kai tana faɗin "ko kaɗan wallahi, indai so na soyayya ne bana jinsa a raina amma ina son sa a matsayin ɗan uwantaka domin shi ɗin jinin mu ne, kin san da cewa mahaifinsa da mahaifin mu marigayi uwa ɗaya uba ɗaya suke, bashi da kowa bayan mu idan bamu ja shi a jiki ba ina zai shiga? ƙiyayyarshi da mahaifiyar mu kuma Allah ne kaɗai yabar wa kansa sani, bamu san me ya haɗa su ba haka muka tashi tin yarinta muka gan su a haka, na farko bamu isa mu tuntuɓi Mom akan abinda ya faru ita da Abeesh ba kuma shima Abeesh da zaran an kawo masa maganar Mom barin wurin yake baya tsayawa ya saurare mu, abun yana damu na wallahi...." Tasleem dogon tsaki ta ja sannan ta ce "meye to abin damuwa bayan haka kika tashi ki ka gansu, idan baki cire wannan damuwar ba wata rana sai dai a samu gawar ki, ni ban yadda dake ba son sa kike..." Nasreen murmushi tayi sannan ta ce "kin dai san inada wanda nake matuƙar ƙaun..." bata ƙarisa fitar da maganar ba Aasmeen tayi saurin toshe mata baki da hannu tana girgiza mata kai... Nasreen cikin fushi ta zamar da hannun Aasmeen daga kan bakinta ta miƙe tsaye tana faɗin "wai har yaushe za'a daina hukunta mu haka ne? nifa na gaji so ake mu mutu babu Aure ne? mun kai minzalin fara soyayya amma kullum a cikin daƙushe mana farin ciki ake, babu abinda muka nema muka rasa a duniyan nan sai abu ɗaya wato farin cikin soyayya, har yanzu bamu san daɗin soyayya ba, kullum a cikin ɓoye soyayya muke saboda kar a cutar da wanda muke so haba dan Allah...." lokaci guda Nasreen ta fashe da matsananci kuka mai azabtar da zuciya... Aasmeen itama hawayen take ta miƙe tsaye tare da dafa kafaɗarta tana faɗin "Nasreen idan bamu ɓoye soyayyar mu ba shin ya zamuyi? kina ga fa duk wanda muka fara soyayya da shi a cikin kwana ɗaya sai an samu gawarsa a jikin gawarsa kuma sai an samu takarda mai ɗauke da rubutun sunayen mu gaba ɗaya, Tasleem, Nasreen, Aasmeen duk a rubuce kuma hukuma babu abinda zata iya yi akan mu duk da bamu muke yin kisan ba, nasan a ɓangaren ki Nasreen an samu gawar samari kusan 50 waɗanda suka baki saƙon soyayya, haka nima a ɓangarena an samu gawar samari waɗanda suka ce suna sona da yawa, Tasleem ce kawai take yiwa samari kwarjini haɗe da yi musu wulaƙanci amma duk da hakan har da sunanta a rubuce a jikin takardar da aka samu a jikin ko wani gawa indai ya furta mana kalmar soyayya, Nasreen ba wai soyayyar ce matsalar mu ba, babban matsalar mu shine kashe waɗanda zamu yi soyayya dasu, kashe waɗanda basu ji ba basu gani ba duk a saboda mu...." Nasreen share hawayen fuskar ta tayi tana fuskantar Aasmeen ta ce "anya kuwa bamu da baƙaƙen aljanu?..." Aasmeen ta ce "i think so but bakya tunanin Ayub student ɗin school ɗin mu da ku ka fara soyayya dashi akan abinda zai faru da shi?..." Nasreen ta ce "Insha Allahu babu abinda zai faru dashi domin na tsayar da addu'a ta sosai akan sa, kinga sauran duk basa wuce kwana ɗaya ake kashe su shi kuma Ayub yau satin mu guda dashi, shiyasa nake da hope akan sa...." Aasmeen jinjina kai tayi sannan ta ce "amma naga ƙoƙarin Ayub da har yake da ƙwarin gwiwar zuwa wurin ki alhalin yanzu kam school kowa gudun mu yake, ba wanda yake son tsayawa a kusa damu balle har soyayya, har sun sa mana suna Mayu, nidai a yanzu bazan ƙara karɓan soyayyan kowa ba domin bazanyi sanadin mutuwar Ɗan mutane ba..." Nasreen sauƙe numfashi tayi sannan ta kalli wurin da Tasleem take sai faman karatun ta take, Ta ce "Tasleem ke babu abinda zaki ce a wannan al'amarin ne?..." Tasleem ɗagowa tayi fuska ba annuri ta ce "kin taɓa jin na tsoma baki na a cikin zancen soyayyar ku? ko kun fiso nima a rinƙa rubuta mun alhakin ɗaukan rai? kun san abinda yake faruwa damu amma kun kasa fahimtar komai, ta sanadiyarku ake hallaka bayin Allah amma ku bakuda imanin da zaku dakatar...." Nasreen ta katseta da cewa "inda munada halin dakatarwa da tin yaushe mun dakatar..." Aasmeen ta ce "taya zamu dakatar alhalin bamu san lokacin da abun yake faruwa sai dai mu ji labari..." Cikin fushi Tasleem ta ce "ehen zaku iya dakatarwa ta hanyar daina soyayya da kowa, hakan ne zai ceci waɗanda ake hallakarwa, soyayyar banza da wofi dole sai anyi ta ne? kuma kunsan in kunyi ta ma ba samun soyayyar ku ke ba sai jawa kan ku zargi ko kuma jawa kan mu gaba ɗaya tinda nima ba'a barni ba, Ni da bana kula kowa babu ruwana da kowa amma sai an samu sunana a rubuce a takardar gawar samari ku, ni yanzu akwai mai zarrah da ikon da ya isa ya tuntuɓeni da maganar soyayya ne? duk da ba kowa yake gane kamannin mu ba amma ni na fita daban saboda mata ma basu ishe ni kallo ba bare maza...." Nasreen ta ce "Uhmmm Tasleem kenam kin manta ne, amma lokacin da muke primary duk cikin mu kece kawai mai shiga shauƙin soyayya, ke da Amaar Junaid bakwa rabuwa kullum kuna tare duk da a lokacin abokai za'a ƙira ku domin baku kai minzalin Aure ba duk da a lokacin shi yana Jss 3, nasan in badan kin rasa shi ba da yanzu kam sai dai a ƙira ku da Julleit and Romeo tsabar soyayya...." Nasreen da Aasmeen tafa hannayensu suka yi suna kwashewa da dariya, sannan suka juyo da ganinsu kan Tasleem, abinda suka gani ne ya tayar musu da hankali lokaci guda, ganin Tasleem a wani irin hali ta riƙe kanta sosai da hannu biyu tana faman shiɗewa, ƙwaƙwalwarta ne yake wani irin juyawa yana hargitse wa gaba ɗaya ta fita hayyacinta lips ɗinta ne yake kakkarwa a hankali take furta "Mom! Mom!! Mom!!! Mom!!!!..." hannunta riƙe da kanta sai juyi take tayi akan gado kafin su Nasreen su yo kanta har ta faɗo daga kan gado tana hargutsa sumar kanta, idanuwa sunyi lufu-lufu ga wani irin zazzafan hawayen da yake zubo mata, a yanzu dai bata cikin hankalin ta, gaba ɗaya hankalin ya gushe, still bata daina furta "Mom! Mom!! Mom!!! Ba.... A ruɗe Nasreen ta kalli Aasmeen sannan ta ce "gudu ki ƙira Mom kice ciwon Tasleem ya tashi, sauri dan Allah..." Ganin bazata iya mata wani magani ba yasa ta rungume ta sosai a jikinta tana tottofa mata addu'o'i.. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga Aasmeen tare da Mom sun shigo tare da, tsayawa Mom tayi tana ƙare Tasleem da kallo daga bisani ta ce "duk ku fita can falo ku jira ni..." Hakan kuwa suka yi Nasreen da Aasmeen fita suka yi daga ɗakin, Cikin ƙarfin tsafi Mom ta ɗago Tasleem da hannunta ba tare da ta taɓa gangar jikinta ba sannan ta ɗora ta akan gado, itama Mom haurawa saman gadon tayi tare da ɗago kan Tasleem ta ɗora akan cinyar ta, sannan ta ɗora hannunta akan goshinta domin tabbatar da abinda ke damunta, rufe idanuwanta tayi sosai hannunta akan goshin Tasleem, abubuwan da suke yawo a cikin kwakwalwar Tasleem ta fara gani, haka take ganin video abinda yake cikin ƙwaƙwalwar Tasleem ta cikin ƙwayar idanuwanta ga murya Tasleem tin tana ƙarama yanda yake dukan dodon kunnen Mom, muryar da yake fitowa shine "Mom! Mom!! kar ki kashe shi Aboki na ne, dan Allah, ina son sa Mom Aboki na ne Amaar Junaid, Mommm kar ki jefa shi cikin ruwan nan mutuwa zai yi, zan rabu da shi Mom ki ƙyale shi Moommmm...." Da sauri Mom ta buɗe idanuwanta waɗanda suka koma kamar na aljana babu ɗigon baƙi a cikin idanun duk sun koma fari soll, haka take sauƙe numfashi ganin wannan al'amarin ya kasa barin cikin kwakwalwar Tasleem, duk da tin daga lokacin faruwar hakan Devil Mom ta tsafe mata tunanin ta yanda zata manta duk abinda idanuwanta suka gani, zata manta abinda ya faru amma da zaran an ambaci sunan Amaar Junaid Shikenam za'a nemi hankalin ta a rasa, abun zai dawo mata ƙwaƙwalwa wanda in ba'ayi saurin gusar mata da tunani a lokacin ba, ƙwaƙwalwar ta na baya zai iya dawo mata gaba ɗaya wanda komai da komai zata tuna shi shiyasa Mom take tsoron wannan ranar hakan yasa duk kallonta akan Tasleem yafi tsayawa saboda kar a kawo mata maganar Amaar ciwon ya dawo, a duk faɗin duniyar da take idonta yana kan Triplets ɗin ta, ta cikin madubi take kallon duk abinda suke ko a makaranta, sannan duk mutumin da ya tare mata yara da sunan soyayya sai taga bayan sa, ita take yin kisan da duk ake yi akan triplets sannan ta rubuta sunayensu su uku ta ɗora akan gawa, Devil Mom takan iya ɓacewa ta ƙoma duk yanda ta ga dama, takan iya ratsa jikin gini tayi wucewar ta, takan iya ɓace wa taje ta samu mutum a duk faɗin duniyan da yake, tana daga zaune zata tura spirit ɗinta yake yayi kisa ya dawo ya shige gangan jikinta, rubuta sunayen ƴaƴanta da take a jikin takarda sannan ta ajiye akan gawa tana yin haka ne saboda kowa yayi nesa da yaranta.... Idonta akan Tasleem wani irin haske ne ya fito daga cikin idanuwanta ya shige kan goshin Tasleem wanda kota farfaɗo bazata taɓa sanin abinda ya faru da ita ba, daga nan Mom ta sake lumshe idanuwanta lokaci guda ta buɗe su sai eyes ɗin ta suka koma normal yanda suke, tashi tayi tabar ɗakin a yayinda ita kuma Tasleem wani irin nannauyar bacci ya ɗauke ta.... A falo Madam Nablah ta tarar da su Nasreen da Aasmeen suna ta zarya sun gagara samun nutsuwa duk da ba karo na farko da Tasleem take shiga wannan halin ba amma suna matuƙar damuwa da hakan, Nasreen ganin Mom ɗin su yasa duk suka je wurin ta suna faɗin "Mom ta tashi ne?..." Cikin zafin rai Mom ta riƙo sumar gashin su duk su biyun rai a ɓace take faɗin "idan na sake jin kun ambaci sunan Amaar Junaid a cikin gidan nan to duk sai na hallaka ku..." Daga nan ta sake su tare da nufan upstairs zata nufi room ɗin ta, har zata haura ta ɗaga kanta sama ta order site upstairs taga Abeesh ne tsaye ya goya hannayensa biya akan ƙirjinsa shima idonsa akan ta rai a ɓace... Kawar da kanta tayi ta shige room ɗin ta... Nasreen da Aasmeen kallon juna suke cike da mamaki kowa da abinda yake rayawa a cikin ransa, sun kasa fahimtar komai, Aasmeen ce ta furta "shin me yake faruwa ne?..." Nasreen ta ce "Nima ban sani ba, amma al'amarin Mom ya fara bani tsoro duk da bamu san komai akanta ba..." Fuska ɗauke da damuwa idonta ya sauƙa akan Abeesh wanda ya maida kallonsa kansu yana tsaye a saman upstairs ɗin ɗakinsa, bayan sun haɗa ido girgiza mata kai kawai ya yi sannan ya koma room ɗin sa. Nasreen idonta itama a sai tin yanda room ɗin sa yake ta furta "ina zuwa..." itama ta haura upstairs zata nufi room ɗin Abeesh... Ita kuma Aasmeen ɗakinsu itama ta haura zata je ta dubo jikin Tasleem.... NEXT NEXT NEXT UPDATE ZAI RINƘA ZUWA MUKU DA MISALIN ƘARFE 8 NA DARE .... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 5 to 6 Nasreen ce zaune a kusa da Abeesh a bakin gado cikin tausayawa take kallonsa hannunta akan nashi dake dafe kan cinyarsa, haka take kallonsa yayin da kansa ke kallon ƙasi fuska ba annuri, hannunta ta kai kan haɓar sa tare da ɗago da kansa ta juyo da shi, shima haka ya sauƙar da idanuwansa kan kyakkyawar fuskar ta ba tare da ya furta komai ba, Nasreen cikin sassanyar murya ta ce "Ya Abeesh nasan kana cikin matsala amma ka kasa sanar mun, dan Allah ka sanar mun abin da yake damun ka..." Kawar da kansa ya yi tare da sauƙe nannauyar numfashi ya ce "Nasreen! kin damu akan sanin matsala ta hakan kuma bashi da wani amfani..." Nasreen ta ce "ko da addu'a zan taya ka ai..." Ya ce "ki taya ni da addu'a kawai amma kar ki nemi ki san tashin hankalin da ke tattare da ni, just ki bar ni a yanda kika ganni..." Nasreen ta ce "Ya Abeesh...." Ya yi saurin taren bakin ta da cewa "Please Nasreen, na roƙe ki..." Girgiza kai kawai tayi ta ce "Shikenam ba komai..." Daga nan ta fi ce daga ɗakin tare da rufe masa, shi kuwa bayan fitar ta wasu zafafan hawaye ne suka fara zubo masa yana cizan leɓɓen sa.... Nasreen bayan ta koma ɗakin su tarar da Aasmeen tayi zaune a gefen Tasleem wacce ta wuce da bacci. "Bacci tayi ne?..." A cewar Nasreen! Aasmeen amsa mata tayi tana shafan sumar kan Tasleem wacce take bacci. Gaba ɗaya sleeping dress ne a jikin su bayan sun gama hira ko wacce kwanciya tayi akan gadon ta bayan sun kashe hasken ɗakin. Misalin ƙarfe 2 na dare Madam Nablah ce take tsaye a jikin wani ƙaton photon mijinta uban triplets ɗin ta, wanda tsayin photon ya wuce tsayin ta sosai, tana sanye da wata baƙar doguwar riga wanda har ƙasi yake ja ta baya, sai da ta gama shafa photon, kan ta a sama tana kallon fuskar mijinta wanda ya juma da mutuwa daga bisani ta rufe idanuwanta ruf, lips ɗin ta na motsi kamar mai karanta abu a cikin ranta nan da nan photon ya rabe gida biyu sai ga wani ƙofa ya bayyano, ƙofar sirrin da ba wanda yasan da wurin, murmushi tayi sannan ta buɗe ƙofar ta shige ciki, ɗakin da ta shiga duhu ne ƙirin baka iya ganin komai hakan ma sai da tayi tafiya mai nisan gaske kafin ta durƙusa ƙasi tasa hannu ta buɗe wani murfi kamar murfin rijiya nan ta shige cikin ramin tana taka matakala a hankali har ta sauƙa ƙasi, wannan wurin gidan ƙasa kenam domin wurin sai ka ce kogo, hannu tasa ta kunna hasken kogon sai a lokacin haske ya bayyana, Madam Nablah cikin iko da ƙasaita ta jawo wani kujerar gefenta ta zauna a gaban wani dattijon bawan Allah wanda ta ɗaɗɗaure shi da igiyar kaca akan kujera ga ta rufe masa fuska da baƙar hula, ƙafa ɗaya ta ɗora akan ɗaya tana wani irin shu'umin murmushi, lokaci guda tasa hannu ta fizge hular fuskar tare da watsa masa ruwa akan fuska, a ruɗe bawan Allah yake fitar da numfashi kansa ya kasa tsayuwa wuri ɗaya tsabar azabar yau da kullum tsawon shekaru 25 yana cikin wannan kogon a haka, ga fuska cike da farin gemu da duk jikinsa daga shi sai gajeren wando a jikinsa. Madam Nablah cike da izzah ta furta "Abu Abeesh..." Dattijo murya na kakkarwa yake faɗin "Nablah na roƙe ki da wannan azabar da kike mun tsawon shekaru ki kashe ni haka na huta, duk da nasan wannan matsalar da kika shiga ba yin kan ki bane, a koda yaushe ina sanar miki cewa ƙwaƙwalwarki baya tattare da ke, akwai wanda yake juyar miki da tunani a koda yaushe, amma nasan duk abinda zan ce miki bazaki saurare ni ba saboda ke ɗin ba asalin Nablah mu bace, ke baƙar Aljana ce kike jikin Nablah mu har ku ka yi amfani da ruhinta ta kashe mijinta wanda take tsananin masifar so da ƙauna, Insha Allahu asalin Nablah zata dawo da ƙarfin addu'o'in da muke mata a koda yaushe...." Madam Nablah cikin tsawa ta furta "dakata haka Abu Abeesh wa ya sanar maka cewa ni ba Nablah ba ce? tabbas kamar yanda kake fa ɗa kullum cewa an sauya ƙwaƙwalwar Nablah haƙiƙa hakane, amma inaso na sanar maka cewa yanzu wannan ƙwaƙwalwar shaiɗanu ta zama na Nablah, wancan ƙwaƙwalwar kumaaaa...." Nan ta tintsire da wani irin shu'umemmen dariya har idanuwanta suna farfatsin wuta. Abu Abeesh girgiza kai ya yi yana faɗin "Insha Allahu bazaki gama da duniya lafiya ba shaiɗaniyar baƙar Aljana, ki sani zaki mutu ne kuma mutuwar wuta..." A fizge ta miƙe tsaye tana faɗin "babu yanda za'a yi nayi mutuwar wuta Babban Malami domin ni kaina wutar ce mai ƙona duk wanda naso..." Ta ƙarasa maganar tana wurga masa wutar tsafi daga cikin tafin hannunta, kamar kullum dai tsafin ta baya aiki akan Abu Abeesh, duk tsafin da zata mishi baya kama shi. Murmushi ya yi sannan ya ce Nablah kenam kar fa ki manta ni ne mai kama Aljanu na ɗaure su sannan babu tsafin aljanin da zai yi mun aiki a jiki, hakan yasa na gagare ki baki da wani zaɓi sai ɗaure ni da kika yi anan kogon..." Cikin izzah ta ce "in da ka gagare ni shin meya hana ka gudu tsawon shekaru a cikin tarko na, Babban Malami babu abinda zaka iya mun sai dai ka ƙare rayuwar ka a cikin ƙunci da damuwa..." Abu Abeesh murmushi ya yi tare da faɗin "ban damu da halin da nake ciki ba ni dai roƙo na a gare ki shine kada ki cutar mun da yaro na Abeesh..." Ta ce "Yaron ka Abeesh yana nan cikin ƙoshin lafiya, sai dai kuma yasa a ransa cewa baka raye a duniya na gama da shafin ka..." Daga nan tayi wani tsafi madubi ya bayyana sai ga Abeesh akan sallaya yana ta jero addu'o'i. Murmushi Abu Abeesh ya yi sannan ya ce "ina alfahari da kai yaro na Abeesh, ka cigaba da ibadar ka wata rana zaka ci nasarar rayuwa, zaka ci nasara akan maƙiyan ka..." Ya ƙarisa maganar idonsa akan Madam Nablah, itama katsar da video tayi ta juya zata tafi taji ya furta "Ɗan uwana Ƙanina kuma Mijinki yana kwance a cikin kabarin sa yana Allah wadar da Shaiɗanun da suke jikin ki..." Murmushi Madam Nablah ta yi sannan ta ce "babu Shaiɗanun dake jikina domin ni shaiɗaniyar kaina ne, sai dai ƙwaƙwalwar baya ba irin ta yanzu bane..." Ɗaukar hular tayi ta rufe masa fuska sannan ta haura sama ta rufe kogon tayi tafiyar ta.... Washegari da safe kowa ya hallaru a dinning za'a yi breakfast Madam Nablah da iyalan ta daga baya sai ga Abeesh shima ya fito ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun wurin, Madam Nablah ita da kanta ta zuzzuba musu a plate kamar yanda ta sa ba kullum idan tana nan, bayan ta kammala itama zama tayi idonta akan Abeesh ta ce "miyasa bazaka gaishe ni ba?..." Abeesh kan sa a gefe ko kallon yanda take bai yi ba, ganin ta ishe shi da ƙorafi yasa shi tura plate ɗin baya ya miƙe zai bar wurin Nasreen dake gefensa tayi saurin riƙo hannunsa idonta akan sa sai faman girgiza masa kai take tare da zaunar da shi, zama ya yi idonsa akan Madam Nablah ya ce "idan kika ƙara mun magana bazan ci girkin ki ba, kowa ya zauna a matsayinsa..." Madam Nablah idonta akan plate ɗin abincin ta sai faman caccakan plate take da spoon fuska ɗauke da murmushi, bata ƙara furta komai ba har suka kammala. Tasleem da Nasreen da Aasmeen sun gama shirin su zasu wuce school har sun nufi bakin ƙofa suka ji Madam Nablah ta furta "Waye Ayub?..." Gaba ɗayan su daskare wa suka yi a wurin jin tambayar da Momminsu tayi, kallon juna suka shiga yi Nasreen da Aasmeen tinda suka kalli juna babu wacce ta ƙibta ido, ita kuwa Tasleem kanta a ƙasi domin tasan wannan tambayar a iya su biyu ake yi bai shafe ta ba. Madam Nablah ƙiran sunan Nasreen tayi ta ƙara maimaita wa tana faɗin "Waye Ayub?..." Nasreen cikin tsoro da fargaba ta ce "am am Mom wani ɗan school ɗin mu ne..." "Meye alaƙar dake tsakanin ku?.." A cewar Madam Nablah. Nasreen ta ce "Mom friend ɗina ne, shi yake mun assignment idan na kasa..." Jinjina kai kawai tayi sannan ta ce "ku je, sai kun dawo..." gaba ɗaya fice wa suka yi kai tsaye wurin parking suka nufa sai da suka zaɓi wata tsararriyar mota ƙirar jeep suka fita, Tasleem ita ce mai yin driving... Shima Abeesh fito wa ya yi cikin shirin sa zai wuce wurin aiki can hospital, haka yazo ya wuce ta gaban Madam Nablah zai fita, murmushi ta sau tana ƙare shi da kallo daga bisani ta ce "sai ka dawo my Son..." Ko kula ta bai yi ba ya yi ficewar sa.... *SCHOOL* Tana zaune a cikin class ita kaɗai bayan gama lecture tana rubuta assignment, bata ankara ba taji an furta "Amincin Allah ya tabbata a gareki ya sarauniyar kyawawa..." Daga nan shima ya zauna akan kujerar gefenta tare da ɗora hannunsa akan nata wanda take rubutu da shi, Zuciyar ta ne kawai yake haurowa ta ma rasa wani irin hukunci zata aiwatar, fuskar nan ba annuri ko kaɗan, ga dara-daran idanuwa waɗanda suka kaɗa suka yi ja kamar wata iska haka ta juyo a slow ta sauƙar da zararrun idanuwan ta akan fuskar Ayub tare da zabga masa wasu irin rikitattun mari akan fuskar sa har sau biyu, babu shiri haka ya miƙe a tsorace yana riƙe da fuska yanda ta mare shi, yana sauƙar da numfashi cikin tsoro yake girgiza kai tinin gumi har ya wanke masa fuska yana faɗin "No no no wannan ba Nasreen ba ce Tasleem ce, tabbas wannan Tasleem ce, a hargitse ya kalli yanda abokansa suke a gefe guda su uku ya ce "ku ka ce Nasreen ce a zaune anan?..." Ɗaya daga ciki ya ce "to ina zamu gane alhalin duk kamannin su ɗaya kuma yau kaya iri ɗaya suka sanya..." Ayub ya ce "ta ya zaku haɗa fuskar Nasreen da wannan mai fuska kamar jahannama..." juyowar da zai yi ya ga sun haɗa ido, ganin irin kallon da take jifansa da shi ne yasa shi faɗin "Kun ga mu tafi, muje mu lalumo Nasreen..." Su na fita suka fara sakin dogon numfashi ɗaya daga ciki ya ce "anya wannan bata da Aljanu?..." Ayub ya ce "Tasleem ai bata shiri da kowa, ko ƙawaye bata da su saboda inaga bazata rasa abokan Aljanu ba..." Su na cikin tattaunawa sai ga wani ya zo wuce wa ya ce "Ayub ya kake tsaye anan ga can Nasreen tana zaman jiran ka..." Ya ce "Aina?..." Acan kan lilo tana karatu. Daga nan suka nufi wurin, su na zuwa suka tarar da ita tana ta lilo da littafi a hannun ta, tsayawa ya yi ta bayan ta yana taya ta lilawa, da sauri ta juyo tana son ganin wa ye a bayan ta ganin Ayub ne ya sa ta sakin dariya tana faɗin "Ayub kai ne?..." Shima murmushi ya yi sannan ya ce "Ni ce rabin raina fatan kin wuni cikin so da ƙaunata..." Zaro ido tayi tare da buɗe baki tana mamakin abinda ya furta.. Ayub ganin ƙaramin wushiryar haƙorin ta yasa shi toshe bakin sa da hannayensa biyu cike da jin kunya ya yi saurin sunkuyar da kan sa, Aasmeen cikin dariya ta ce "Ayub ni fa ba...." Yayi saurin taran maganar ta da cewa "eh eh na sa ni ke ba Nasreen ba ce domin naga wushiryar ki ita kuma bata da shi, amma tana ina ita ɗin?..." Ta ce "i think tana library..." Ya ce "okay Nagode sosai, ayi karatu lafiya..." Jinjina kai tayi haɗe da sakin murmushi tana mamakin yanda Ayub yake mistake akan su har yanzu ya kasa banbance su..... Ta gefe guda kuwa spirit ɗin Madam Nablah ce take tsaye da baƙaƙen kaya a jikin ta tana bin su Ayub da kallo, cikin fushi ta wurga kacar hannunta zuwa gare shi dake basu yi nisa sosai ba cikin ƙanƙanin lokaci kacar ta zari sawayensa sai da ya yi sama sosai kafin ya doku a ƙasi, kan sa ne ya yi wani irin mummunan buguwa akan wani ƙaton dutsen dake wurin, lokaci guda sai ga mutane sun nufo wurin wanda abokansa su ma basu san dalilin faɗuwar sa ba, kafin a ankara Madam Nablah ta zama guguwa ta yo kan Ayub dake kwance, nan ta rufe shi wanda ba'a iya ganinsa sai baƙin guguwa, a hankali Ayub yake ƙoƙarin buɗe idanuwansa ganin yana cikin ɓakin guguwa ga kan wata baƙar Aljana a sai tin fuskar sa tana furta "Tasleem! Nasreen!! Aasmeen!!!, Tasleem, Nasreen, Aasmeen...." Haka take ta maimaita wa, Ayub idanuwansa kamar zasu faɗo ƙasi tsabar tsoro da firgici ga hannayensa yanda ya toshe kunnuwansa da su saboda tsananin gigicewar muryar, Muryar har kasu wa bibbiyu suke ana ƙiran sunayen triplets, da haka har ya sume a wurin daga nan guguwar ta ɓace ɓatt... Mutane kuwa har an taru kowa yana mamakin ganin abun al'ajabin nan duk da basu ji mai ake faɗi ba, su dai abinda suke iya gani shine ƙurar guguwar da ta ke wa ye shi, Aasmeen itama tana wurin zuciyar ta ne yake wani irin bugawa kamar zai fasa ƙirjin ta, tsoron ta shine kar shima Ayub ya shiga halin da sauran suka shiga akan su, tana cikin wannan tunanin sai ga motar Ambulance ta tafo cikin gaggawa, nan da nan aka ɗauki Ayub rai a hannun Allah aka wuce da shi hospital, ana tafiya da shi sai ga Nasreen ta tafo da gudun gaske jin labarin halin da Ayub ya shiga, tana zuwa ta nufi wurin Aasmeen tana faɗin "Meya faru da Ayub? yana ina?..." Aasmeen tana kuka ta ce " nima ban sa ni ba yana shirin zuwa wurin ki daga nan ban sa ni ba..." Suna cikin wannan tattaunawar sai suka ji an furta "wannan takardar fa?...." Duk kowa ya maida hankalin sa kan mutumin da ya ɗauki wata takarda a wurin da aka ɗauki Ayub, mutumin buɗe wa ya yi cikin ɗaga murya ya fara karanta wa "Tasleem! Nasreen!! Aasmeen!!! Whoever falls in love with them will die (duk wanda ya fara soyayya da su zai mutu) zai mutu! zai mutu!! zai mutu!!!..." Cikin tsoro da fargaba kowa ya mai da kallon sa kan su, Nasreen da Aasmeen su na ƙarƙame da juna jikin su har rawa yake tsabar tsoro da firgici ga hawaye ya ƙi tsayuwa a idanuwan su, Mutanen wurin kuwa tinin har wurin ya har gutse da hayaniya kowa da abinda yake faɗi ana ƙiran su da Mayu, zagi ta uwa uba haka ake musu wasu har sun tsigo bulalu zasu dake su, maza sun kai goma kowa da itacuwa a hannayen su wasu katako suka nufo yanda Nasreen da Aasmeen suke cikin zafin nama, Nasreen da Aasmeen rungumar junan su suka yi tare da sau wani irin gigitaccen ihu dai dai lokacin da matasan nan suka ɗago makaman su zasu kwaɗa musu sai ji suka yi an hankaɗa su gefe duk su biyun suka hautsina ƙasi, kafin Nasreen da Aasmeen su ɗago su ga wanda ya hankaɗa su har an rausa sanduna akan Tasleem wacce ta maye gurbin ƴan uwan natan, ihun Tasleem ne ya karaɗe ɗuk makarantar, Nasreen da Aasmeen ganin a Tasleem duk aka kwaɗa wa itacuwa yasa su ma suka fara ihu su na ƙiran sunan ta, Tasleem lokaci guda ta faɗi sumammiya da gudu suka ƙarisa wurinta su na kuka, matasan nan har sun ƙara ɗago da makamansu zasu rausa wa sauran nan suka fara jin kukan Kura daga nesa nesa, hankalin kowa ne ya kar kata wurin da suke jin tafowar Kura, ganin wurin su ya nufo yasa kowa ya fara guduwa maza da mata kowa ta kan sa yake, masu sanduna duk jefarwa suka yi kowa ya kama gaban sa, sai Tasleem wacce take sheme a wurin da Nasreen da Aasmeen kuma su na zazzaune a wurinta su na ta jijjiga ta akan ta tashi amma ko motsi babu, iya su kaɗai aka bari a filin makarantar duk kowa ya shiga ajijjiwa sun rurrufe ko ina, wasu har murna suke Kura zai hallaka su domin su annoba ne a cikin makarantar a cewar sauran ɗaliban, Kuran nan kuwa ganin baya ganin kowa sai ƴan mata ukun nan yasa ya nufi wurin su yana huci kamar wanda ya yi shekara bai ga nama ba, Aasmeen ganin Tasleem baza ta tashi ba kuma ga Kura ta kusan isko su yasa ta fara ƙiran sunan Nasreen tana faɗin "Nasreen ki tashi mu gudu kinga Kuran nan ta kusan iso mu, Nasreen kar muyi two zero ki tashi please..." Asmeen gani tayi Nasreen ta kifa kanta akan ƙirjin Tasleem haɗi da rungumar ta yasa itama bazata iya tafiya ta barsu ba itama durƙusawa tayi ta rungumi Nasreen da Tasleem tare da kifar da kanta akan su tana kuka, Ga Kura yanda yake yo wa kan su ta bayan Kuran kuma wani zabgegen mutumi ne mai kyakkyawan ƙirar jiki yana sanye da wandon kakin Soldier da farar t-shirt mai gajeran hannu, fuskar sa daga nesa sai walwali yake kamar shi ya halicci kan sa, yana bin bayan Kuran ganin ya kusan isko wasu ƴan mata a wurin yasa shi ƙara ƙarfin gudun sa kafin Kuran ya yi sufa kan ƴan matan har wannan matashin shima ya yo sufa wurin su ya kwanta a gefen su tare da ɗaga hannunsa ya cabko wuyan Kuran dai dai lokacin da shima ya yi tsalle zai fa ɗa kan su, wani irin juyi matashin nan ya yi da Kuran ya doka shi a ƙasi tare da danne masa kan sa yanda bazai iya ɗago wa ba, haka Kuran yake shure-shure ya kasa ɗago wa. Asmeen ce cikin ƙarfin hali ta ɗago a hankali jin yanda Kuran yake gurnani cikin tsoro da fargaba take kallon Kuran idanuwa kamar zasu faɗo daga nan ta sauƙar da ƙwayar idanuwanta kan matashin Sojan nan, a hankali ta fara bubbugan bayan Nasreen itama ta ɗago jin wurin ya yi tsit sai gurnanin Kuran, ganin wanda ya danne Kuran ne yasa ta zaro ido cike da mamaki, kallon juna suka yi ita da Asmeen babu wanda ya furta komai a cikin su... Sauran ƴan makarantar kuwa su na kallon abinda yake faruwa ta window har da masu video su suka fi yawa. Daga baya sai ga motar sojoji su biyar duk suka parker a tsakiyar filin makarantar wasu daga cikin sojoji suka fito da kaca suka ɗaɗɗaure Kuran daman su suke tafe da shi ya ƙwace musu shine dalilin da yasa Kurar ta shigo musu makaranta, bayan an shigar da Kuran cikin mota wannan matashin ne ya kalli wurin da su Nasreen suke sai da ya ƙare su da kallo sannan ya ce "A ya yin da mutane suke guduwa ku meya hana ku gudu? ko bakwa son rayuwar ku ne?..." Nasreen tana kuka idonta akan Tasleem wacce har zuwa yanzu bata samu farfaɗowa ba. Sojan ganin duk mutum ɗaya yake gani kuma su uku yasa ya kanne idanuwansa sannan ya buɗe su a hankali tare da maida idonsa kan su yana mamakin wannan al'amarin, Asmeen ce ta yi ƙarfin halin cewa "Ƴar uwar mu ce take a sume kuma baza mu iya barin ta a wurin ba, gwara ko mai zai faru ya faru damu gaba ɗaya..." Sojan ya ce "kuna nufin ku ce ku ɗin ƴan Uku ne?..." Asmeen ta ce "eh we are triplets..." Jinjina kai ya yi sannan ya ce "mai ya faru da ita?..." Har Asmeen zata yi magana Nasreen tayi saurin katse ta da cewa "hatsari ne ya faru da ita, jini yana zuba sosai a kan ta..." nan ta fashe da kuka... Lokaci guda zuciyar sa ta karye domin a rayuwarsa ya tsani ganin hawayen mace, idan kana son ganin raunin sa to ka haɗa shi da hawayen mace, jin kukan ta kuwa tamkar ana juyar masa da ƙwaƙwalwa ne tinin kansa yake hau matsanancin ciwo, jin kan sa yake tamkar mahaukaci domin akwai abubuwan da yake yawan tunawa a rayuwar sa da zaran ya ji sautin kukan mace, A yanzun ma jin sautin kukan Nasreen yasa kan sa ya fara juyawa, cikin lokaci ƙanƙani ya dafe kan sa da hannu bibbiyu tare da rufe idanuwansa sosai shi kaɗai yake jin abinda yake ji, a gigice ya furta "please ki daina kukan nan bana so..." Nasreen jin maganar da ya yi kamar ba'a cikin hayyacin sa yake ba yasa tayi saurin ɗagowa tana kallon sa, Asmeen ma shi ɗin take kallo bayan ya dawo dai dai ya kalle su sannan ya ce "it's okay! ku yi haƙuri ku taso zata tashi yanzu..." Cikin kulawa ya miƙa wa Asmeen hannu itama ta ɗora nata ya miƙar da ita tsaye, itama Nasreen ɗago ta yayi yana bata haƙuri akan kar ta sake yin kuka, ya durƙusa a gaban Tasleem ya yi alama a wani daga cikin sojojin su akan ya miƙo masa akwatin maganinnuwa zai yi treat ɗin ta, har an miƙo masa komai da komai yakai hannu zai ɗago ta, yanda ya riƙo kafaɗunta guda biyu wani irin shocking ya ji ya bi jikinsa wanda tsabar ƙarfin shocking sai da ya ɗagu sama ya yi baya a gigice ya doku a ƙasi, itama Tasleem tsabar shocking ya bi jikin ta ba shiri ta farfaɗo daga doguwar suma haka jikin ta yake ta kakkarwa, lips ɗin ta ne yake motsi alamar tana so ta furta wani abu ta kasa. Nasreen da Aasmeen ganin a halin da Tasleem ta farfaɗo yasa duk suka nufi kanta su na ambatar sunan ta.... Sojojin dake wurin ne duk su ma suka nufi wurin Matashin Sojan nan ganin abinda ya faru da shi, ɗago shi suka yi su na faɗin "Sorry Ogah! fatan babu abinda ya faru da kai..." Shi kuwa idonsa akan Tasleem yana mamakin taya wannan al'amarin zai faru da shi haka ta silar ta, sannan yana tambayar zuciyar sa shin wacece wannan yarinyar???.... *TO MASU KARATU ANAN ZAN KAWO ƘARSHEN KASHI NA 5 DA 6 SAI MUN SAKE HAƊU WA A KASHI NA GABA*... *NI CE ASMEETAH TAKU HAR KULLUM*... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 7 to 8 Tasleem tana ƙoƙarin tashi wani soja yazo ya durƙusa a gabanta da boxes na magani yana faɗin "Ogah ya turo ni akan nayi treat ɗin ki..." Daga nan ya ciro bandej da sauran maganinnuwa, ga Nasreen da Aasmeen su ma suna gefe guda. Sojan nan tinda ya shige motar su ya kama kansa wasu abubuwa suke ta dawo masa ƙwaƙwalwa, ga wasu sojojin a gefensa, "Amaar! Amaar!! Dan Allah kar ka tafi ka barni, dan Allah Mom ki ƙyale shi kar ki rabani da Amaar, Amaar...." Gaba ɗaya ya fita hayyacin sa sai fama cakurkuɗa sumar kan sa yake, ya kasa manta abubuwan da suka faru da shi yana yaro. "Ta Ta Tasleem! Tasleem ki taimake ni kar Momminki ta kashe ni, ki taimake ni Tasleem, ki ce wa Mommin ki kar ta kashe ni dan Allah, Tasleem zata jefa ni a cikin ruwan nan ki taimake ni, mutuwa zanyi idan ta jefa ni a wannan ruwan wayyo Allah Mamanaa, Abbanaaa...." A firgice ya dawo hayyacinsa yana sakin nannauyar numfashi sakamakon ruwan da ake yayyafa masa, a hankali yake furta "Tasleem! Ina zan same ta?.." Idonsa ne ya sauƙa akan tafin hannayensa da har yanzu yake ta zogin shocking ɗin jikin Tasleem, nan da nan hannayen har sun yi jawur, wani tunani ne ya ƙara dawo masa, wannan matsalar da yake ciki yasa an nema masa wani babban malamin duba wanda ya sanar masa cewa wannan matsalar ƙwaƙwalwar bazai warke ba har sai ya haɗa ƙwayar ido huɗu da Tasleem, ma'ana su kalli juna na tsawon minti biyar babu wanda ya ƙibta a ciki, sannan alama ta farko da zai nuna masa Tasleem shine da zaran ya taɓa jikinta zasu ji shocking gaba ɗayan su, abinda zai kawo ƙarshen shocking gaba ɗaya su daina ji shine da zaran sun rungumi juna shocking ɗin ya ratsa jikinsu na tsawon minti talatin ba tare da sun rabe da juna ba Shikenam daga nan bazasu ƙara jin wani shocking ɗin ba.... Bayan ya gama wannan tunanin da aka sanar masa a ruɗe ya miƙe tare da ficewa daga cikin motar zai nufi wurin Tasleem, ganin basa nan sai sojojin su da suke ƙoƙarin ta da mota tambayi wanda yayi treat ɗin Tasleem cewa ina suke? Sojan ne ya bashi amsa da cewa "Ogah ai tin tinin na kammala, sun tafi..." Da sauri ya tambaya cewa "ina suka yi?..." Mutumin ya sanar masa cewa "Ɗaya daga cikin su ne taje ta kawo musu mota suka shiga, yanzu kam ko bayan motar su baza'a iya hangowa ba..." Cikin takaici Amaar ya cusa yatsun sa cikin sumar kansa yana faɗin "Oh god! saboda su nasa aka dawo dani Nigeria, meyasa zaka bar su su tafi?..." Sojan ya ce "sorry Ogah ai ban san kana neman su ba..." Amaar cikin nuna damuwa ya ce "Please a duk yanda ka gan su ka sanar mun, ina buƙatar ɗaya daga cikin su, marar lafiyan nake so..." Sojan cikin yaƙe yake faɗin "Oga ai sai dai kawai duk wacce na gani a ciki nayi maka magana amma ina zan iya gane mai lafiyar da marar lafiyar a cikinsu, kana ganin komai nasu iri ɗaya ne asalin ƴan uwa masu kama ɗaya..." Amaar bai bi maganar sa ba haka ya shige mota suka tafi su ma...... Bayan isar su Tasleem gida a falo suka tarar da Momminsu da wani cikakken jarumin mutumi wanda kana ido huɗu da shi zai maka kwarjini, yanayin sa kamar irin mutanen da basa son rainin nan ne, fari kyakkyawa da shi. Da sallama a bakin su suka ƙarasa cikin falon, Nasreen tana riƙe da hannun Tasleem wacce gaba ɗaya jikin ta ba ƙwari, Madam Nablah tana ganin Tasleem ɗaure da bandeji a kan goshin ta yasa ta saurin miƙe wa tsaye tana faɗin "Meya same ki Tasleem?..." Aasmeen ce ta buɗi baki ta ce "Mom Ɗaliban school....." Nasreen tayi saurin katse ta da cewa "ta ɗan samu hatsari ne..." Madam Nablah miƙewa tayi tana taku cikin ƙasaita tazo gaban Tasleem tana kallon cikin ƙwayar idanuwanta, duk abinda ya faru sai da ta kalla a cikin ƙwayar idon Tasleem ta hanyar ai watar da tsafin ta, murmushi kawai tayi sannan ta koma yanda take zaune before ba tare da ta furta komai ba domin tasan yaranta su na fuskantar wannan ƙalubale... Shapris wanda idonsa yake kan su ya kasa ƙibta wa mamaki yake yanda Madam Nablah take da waɗannan zuga-zugan ƴan Uku masu kamanni ɗaya. Su Nasreen har zasu haura upstairs suka ji Madam Nablah ta ƙira su, dakatawa suka yi tare da dawowa cikin falo su na amsa ƙiran Momminsu, cikin izzah Madam Nablah ta ce "tarbiyyar da na baku kenam?..." Tasleem Nasreen Aasmeen duk kallon juna suka shiga yi ba tare da sun fahimci abinda take nufi ba, Nasreen ce ta buɗi baki ta ce "Mom! me muka yi?..." Madam Nablah ta ce "ku makafi ne? ko baku ga baƙo na ba? ko bai cancanci ku gaishe shi?..." Nasreen ta ce "Sorry Mom a hargitse muke shiyasa..." Nasreen ce ta fara durƙusawa a gaban Shapris tare da faɗin "Barka da zuwa, fatan mun same ka cikin ƙoshin lafiya..." Shapris murmushi ya yi sannan ya amsa mata cikin kulawa. Itama Asmeen durƙusawa tayi ta gaishe shi cikin nutsuwa, ya amsa mata itama cikin kulawa da kuma yabon su. Tasleem dake tsaye wani irin juyar da ƙwayar idanuwanta tayi tare da furta "hajijiya nake ji ina buƙatar hutawa..." Daga nan ta nufi upstairs, kafin ta haura Madam Nablah cikin fushi ta ƙira sunan ta "Tasleem ki zo nan ban sallame ki ba..." Cikin nuna damuwa Tasleem ta ce "please Mom...." Shapris idonsa akan Tasleem domin taurin kanta ya yi matuƙar burge shi, daman fatan sa shine a cikin ƴaƴan Madam Nablah ya samu mai taurin kai wacce zai sauƙe fushin sa akan ta... Madam Nablah idon ta akan Tasleem ta ce "ki zo ki durƙusa a gaban baƙo na ki gaishe shi kamar yanda sauran ƴan uwan ki suka yi..." Tasleem Sarkin zuciya lokaci guda zuciyar ta ya hauro ga manya-manyan idanuwanta yanda take zaro su ta ce "impossible Mom! bazan taɓa durƙusa gwigwowina a gaban halittar da muke matsayi ɗaya a wurin Ubangiji ba..." Madam Nablah ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba cikin fushi ta miƙe tsaye tana faɗin "Tasleem idan bazaki bi umarni na ba zaki shiga uƙuba ta..." Tasleem haka ta tanƙwashe ta ce "Mom no one like me haka zuciyata take bata tanƙwasuwa sai dai kawai kiyi haƙuri ki barni a yanda kika ganni, zuciyata ta dabance...." A tsawa ce Madam Nablah ta furta sunan ta cikin fushi, har yanayin ta ya fara canzawa, ƙwayar idanuwanta sun canza launin green, kafin yaran sun ankara Shapris ya yi saurin miƙe wa tsaye ya nufi Madam Nablah yana bata haƙuri akan ta sauƙo, ya tare ta yanda yaran baza su ganta ba domin ya fahimci basu san halin da mahaifiyarsu take ciki ba, Cikin ɓacin rai Madam Nablah ta rufe idanuwanta sosai sai da ta koma normal kafin ta ratsa ta gefen Shapris ta je har yanda Tasleem take tsaye gira a haɗe, hannunta ta cabko tare da wurga ta saman kujera tana faɗin "ki nutsu ki saurare ni..." Nasreen sarkin shiga damuwa tin tinin har hawaye sun fara zubo mata, ganin yanda mommy da Tasleem suke musayar yawu, ta rasa gane wannan matsalar har sun fara zargin cewa Tasleem ba lafiyar ta ƙalau ba... Asmeen kuwa asalin matsoraciya kenan, yanda ta ji Momminsu tana darara tsawa kamar wata dodonniya yasa jikinta ɗaukar rawa, ga yanda ta rurrungumi Nasreen tsabar tsoro.. Madam Nablah juyo wa tayi tana kallon su Nasreen sannan su ma ta basu izinin zama, ba mu su haka suka zauna dab da Tasleem kowacce jikin ta kamar wacce aka watsawa ruwa ba ƙwari sai Tasleem da take ta huci idonta akan Shaprees tana jin haushin sa domin saboda shi ake tsawatar mata... Shapris haƙuri yake ba wa Madam Nablah tare da faɗin "Sorry Madam control your self, ki daina biye wa yaran nan domin yarinta ke damun su..." Madam Nablah sauƙe numfashi tayi sannan ta ce "okay Shikenam yanzu inaso nayi abinda ya tara mu anan..." Su na cikin wannan halin sai ga Abeesh ya shigo da sallama a bakin sa, cikin nuna farin ciki Nasreen tayi saurin amsa masa tare da faɗin "your welcome my lovely bros..." Murmushi ya sau mata tare da shafa sumar kanta yana faɗin "Allah ya miki albarka my gimbiya..." Itama Asmeen masa sannu da dawowa tayi, ya amsa mata cikin kulawa tare da sanya mata albarka itama, Idonsa ne ya sauƙa akan Tasleem wacce ko ɗagowa bata yi ba balle yasa ran zata gaishe shi, murmushi yayi domin tin tinin yasan halin ta haka take a ko ina ma, bai biye mata ba haka ya sa hannu ya shafa gefen fuskar ta yana faɗin "my juju..." Itama hannu ta ɗora akan nasa tana jinjina masa kai amsuwar ta kenam, shirin barin falon yake ba tare da ya kalli yanda Madam Nablah take ba balle baƙon ta, Madam Nablah ce tayi saurin ƙiran sunan sa "Abeesh ba kaga baƙona bane?..." A slow Abeesh ya juyo yana kallon Shapris daga bisani ya ce "your welcome..." Shapris ɗaga masa kai kawai ya yi ba tare da ya furta komai ba, Abeesh juyawa ya yi zai wuce Madam Nablah ta ƙara dakatar da shi tana faɗin "Abeesh ka zo ka zauna ina son yin magana da ku gaba ɗaya..." Ko kallon ta bai yi ba ya ce "ba ki ga yanzu na dawo daga wurin aiki bane? ina buƙatar hutawa..." Madam Nablah ganin zai iya tizgata a gaban Shapris wanda yake matuƙar jin maganar ta ne yasa ta sauƙar da muryar ta tana faɗin "Abeesh just two minutes please..." Cije lips ɗinsa ya yi ta ƙasi sannan ya juyo cikin falon, samun kujera ɗaya yayi ya zauna shima.... Shapris abun mamaki ya bashi ganin Madam Nablah ta kasa control mutanen gidan ta hatta ƴar cikin ta amma sai tana bayyana tsoron ta da kwarjinin ta a mutanen waje, ya rasa gane dalilin haka, ta wani ɓangaren kuma yana tunanin har yanzu a cikin yaran gidan ta babu wanda yasan asalin wacece Madam Nablah ba, tana ɓoye musu kan ta shiyasa ta kasa hukunta su, Haka yake ta wannan tunanin har Madam Nablah ta katse shi da wata iriyar tambaya da ya daki dodon kunnen sa, Wannan tambaya ba shi kaɗai ba hatta sauran mutanen wurin tambayar ya girgiza su... Nasreen da Aasmeen zaro ido waje suka yi suka kallon Momminsu, tunani suke ayya kuwa wannan tambayar daga bakin mahaifiyar su ta fito?... Tasleem wacce take sunkuye da kanta ƙasi jin tambayar da mommy tayi ne yasa ta watso da gwala-gwalan idanuwanta kan Madam Nablah, idanu kamar zasu faɗo ƙasi domin duk ta fi sauran ƴan uwan nata manyan idanu sosai, sai take ƙara gwalalo su kamar wata aljana... Madam Nablah ƙara maimaita tambayar tayi idonta akan Shaprees tana faɗin "Shapris kai nake tambaya, shin a cikin waɗannan ƴan mata uku wacece ta fi burge ka? ina nufin ka zaɓi wacce tayi maka kamar yanda nayi maka alƙawarin zan baka ɗaya daga cikin triplets ɗina, to yanzu zaɓi nake baka domin ka cancanci haka...." Shapris haka yake bin ko wacce da kallo gaba ɗaya ya kasa gane wa zai zaɓa a cikin su domin duk kamannin su ɗaya, ya so ya nuna Tasleem amma sai dai duk sun hargitse kayuwan su bazai iya gane ta ba domin fuskar ko waccen su ba annuri jin wannan batun sai fuskokin su ta zama kamar na mutum ɗaya, Ganin bazai iya ware guda ɗaya a cikin su ba yasa shi kallon yanda Madam Nablah take yana girgiza kai ya ce "Madam kawai ki zaɓa mun da kan ki..." Madam Nablah ta ce "okay tinda kai ka buƙaci haka zan zaɓa maka..." Shapris ya ce "amma sai dai kiyi musu alamar shaida ta yanda zan rinƙa banbance su ..." Girgiza kai Madam Nablah tayi sannan ta ce "babu wata alamar shaida da zan musu, kai da kan ka zaka rinƙa banbance su..." Madam Nablah idonta ta sauƙar kan wacce take ƙarshen kujera ta furta "Aasmeen..." Aasmeen wacce take last sopa sai dai ƙirjinta ya buga jin ta ambaci sunan ta tana tsoron kar ita ce zata yiwa kyauta... Madam Nablah ta ce "inaso kiyi mun dariya yanzu..." Asmeen kallon Nasreen tayi wacce take gefen ta daidai lokacin da itama Nasreen ta kalle ta suka haɗa ido su na kallon juna, Lokaci guda Aasmeen ta fashe da kuka. Madam Nablah ta ce "dariya nake so ki yi mun ba kuka ba, kar ki ɓata mun lokaci..." Asmeen tsabar kuka ya ci ranta sosai kasa buɗe bakin tayi sai da Madam Nablah ta darara mata wata uwar tsawa tukun ta shiga taitayin ta ba shiri ta washe bakin ta tana dariyar dole... Madam Nablah kallon Shapris tayi sannan ta ce kaga wancan ita gushiryar haƙorin sama gare ta, ita ce Aasmeen kuma rabin raina, ina matuƙar ji da ita..." Shapris jinjina kai ya yi alamun ya gamsu. Madam Nablah kallon Nasreen tayi sannan ta ce "ke kuma ki mun murmushi..." Nasreen kallon mommy tayi sannan ta ce "Mom murmushi kuma?..." Madam Nablah ta ce "ko baza kiyi bane?..." Ta girgiza kai tare da faɗin "a'a Mom ban isa nayi jayayya dake ba..." Saida Nasreen ta rufe idanuwanta sosai kafin ta sau wata iriyar murmushin dole mai kama da kuka... Madam Nablah ta kalli Shapris sannan ta ce "ka ga wannan kuma dimple gare ta, ko magana take zaka ga kyawawan dimple su na lotse wa..." Madam Nablah ɗagowar da zata yi ta kalli Tasleem sai karaf suka haɗa ido, har sai da gaban Madam Nablah ya yanke tsabar ta tsorata da irin kallon da Tasleem take mata ga fuska a murtuƙe ba annuri, da sauri Madam Nablah ta kawar da idonta tana faɗin "Shapris ita kuma wannan ta hanyar idanuwanta masu firgitarwa zaka gane cewa Tasleem ce da kuma yawan fushi domin rabon da Tasleem tayi murmushi tin tana yarinya ƴar shekara 10 a duniya...." Madam Nablah tuna lokacin da Tasleem ta daina murmushi a rayuwar ta tayi, tin lokacin da ta jefa Abokinta Amaar Junaid cikin ƙaton rafi wanda yake cike da ruwa daga lokacin aka daina ganin farin cikin Tasleem, da zaka kwana kana nuna mata abun farin ciki bazata taɓa nuna wa ba, domin ba'a san farin cikin ta ba kullum sai baƙin ciki... Madam Nablah ta cigaba da cewa "ita ɗin sam bata nuna farin cikin ta a kowa kullum a cikin wannan yanayin za kana ganin ta, Tasleem Kenam...." Shapris jinjina kai yayi idonsa akan Tasleem sai yanzu ya gano ta.... Madam Nablah ta ce "Shapris na zaɓa maka ɗaya a ciki wato ita ce Aasmeen my lovely daughter...." Cikin tsoro da fargaba Aasmeen ta ce "why Mommy?...." Madam Nablah ta ce "Yes Aasmeen, bazan taɓa zaɓa miki abinda zai cutar da ke ba, saboda haka na ri ga da na yanke hukunci na, na mallaka wa Shaprees ke a matsayin matar sa ta Aure...." Sannan ta maida idonta kan Shaprees ta ce "Shapris ga Aasmeen na mallaka maka ita, inaso ka riƙe mun ita amana, na baka amanar ɗiyata Aasmeen..." Shapris ya ce "insha Allahu Madam zan riƙe ta kamar yanda kika umarta..." Shapris har cikin zuciyarsa bazai taɓa haƙura da ɗaukar fansar matarsa Sophia ba, dole sai ya ɗau mummunan hukunci akan jinin Madam Nablah ko wacece kuma yayi alƙawarin bazai taɓa ƙyale wannan ahalin ba..." Madam Nablah idonta akan Aasmeen ta ce "shi ɗin mutumin kirki ne, bazai taɓa cutar da ke ba..." Aasmeen tana kuka ta ce "Mom wani abu yana faruwa da mu, kin kasa sauraron mu a duk lokacin da muka kawo miki kukan mu, duk wanda ya fara Soyayya da mu mutuwa yake, dan Allah kar ki jefa rayuwar sa cikin hatsari..." Madam Nablah da Shaprees kallon juna suka yi domin Shapris yasan dole da hannun Madam Nablah akan abinda yake faruwa da ƴaƴanta, itama tasan ita take ai watar da hakan sai kawai ta wayance akan maganar tana faɗin "duk wanda kika ga ya mutu to lokacin mutuwar sa ne yayi, don haka ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru da Shapris..." Nasreen riƙo hannun Aasmeen tayi tana ƙoƙarin rarrashin ta... Madam Nablah ce ta kalli yanda Abeesh yake sannan ta ce "sai kuma Nasreen da Abeesh..." Nasreen da Abeesh duk ɗago kansu suka yi suna kallon juna daga bisani suka mayar da kallon su kan Madam Nablah, ta cigaba da cewa "na daɗe da tsara hakan a raina cewa Abeesh da Nasreen zasu zamo ma'aurata, don haka ya kamata ku ƙara fahimtar juna, na riga da na yanke hukunci na, hukunci na kuma shine dai dai, Nasreen da Abeesh ku fara tsara rayuwar ku kafin lokacin bikin ku..." Daga nan Madam Nablah ta miƙe tsaye tana faɗin, "Ke kuma Tasleem zan ji dake daga baya..." "Aasmeen idan kun kammala fahimtar juna ke da Shaprees ki kaishi order part na musamman yanda zai zauna sannan daga yau ke zaki na masa gyaran room ki kai masa abinci part ɗinsa, gyaran gado da wanke toilet room duk ke ce, kar ki kuskura naga kin yi masa ba dai dai ba, sannan bana son ganin house worker a part ɗin Shaprees domin shi ɗin naki ne, babu macen da ta fi cancanta taje part ɗinsa in ba ke ba, Wannan shi ake ƙira da training kafin Aure..." Kema Nasreen daga yau ke za ki na gyara part ɗin Abeesh ba ƴar aiki ba, idan naga ba kiyi abinda nace ba haƙiƙa zaki ga ɓacin raina, kina ji ba..." Nasreen gaba ɗaya ta ɗauke wuta domin bata taɓa tunanin zata Auri Abeesh ba, bata taɓa jin soyayyar sa ta Aure a cikin zuciyar sa ba, sai kuma tunanin Ayub ya faɗo mata a rai... A tsawace Madam Nablah ta ce "kina jin abinda nake cewa ko Nasreen?..." A firgice Nasreen ta amsa mata.. Madam Nablah bata tsaya ta ji daga bakin Abeesh ba kawai tayi tafiyar ta, kai tsaye upstairs yanda room ɗin ta yake ta nufa... Abeesh kallon ta kawai yake gaba ɗaya ya rasa abin cewa, yanda kasan an sa masa kwaɗo ya gagara yin magana,. Shima a fizge ya miƙe gudu-gudu sauri'sauri ya bar falon, domin haɗa shi da Nasreen da akayi ba ƙaramin nauyin ta yake ji ba, har kunyar haɗa ido yake da ita samm bai so wannan haɗin ba..... Tasleem ganin irin rainawa ƴan uwanta wayo da akayi ne yasa ta tashi cikin takaici ta haura saman upstairs zata shige room ɗin su, Nasreen tana kuka itama haka ta tashi ta haura upstairs room ɗin su... Aasmeen itama kuka take da sauri ta miƙe tare da shirin barin falon Shapris ya dakatar da ita yana faɗin "Amaryata shin baza ki kaini wurin mazaunina bane?..." Asmeen tsayawa tayi idonta akansa yanda suka yi jawur domin haɗin yazo mata a bazata, tsoro da fargaba duk ya ratsa ta bugu da ƙari bata san shi ba, bata taɓa ganinsa ba lokaci guda ace an bayar ta a shi, abun yana ƙona mata rai...... NEXT NEXT NEXT New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 9 to 10 Shapris miƙe wa ya yi tare da tako wa har yanda Asmeen take a tsaye, a gaban ta ya tsaya yana ƙare fuskar ta da kallo a yayin da ita kuma take kallon ƙasi ta kasa haɗa ido da shi, hannu yasa ya ɗago da haɓarta a hankali ta sauƙe kyakkyawan idanuwanta akan fuskar sa tana bin sa da kallo daga bisani ta kawar da kanta gefe tare da faɗin "mu je na kai ka part ɗin ka...." Sauƙe numfashi ya yi tare da bin bayan ta suka bar falon, sai dai suka fita can compound na gidan kafin suka hau wani beni mai hawa uku acan aka tanadar masa da tsararren part site ɗin sa, Su na shiga falon suka tarar an tsara komai, komai da komai na rayuwar duniya an zuba a falon, ba abinda zai nema ya rasa, falon kaɗai ma abun kallo ne, Murya ciki-ciki Asmeen ta furta "inaso zan koma part ɗin mu..." Murmushi Shaprees ya sau tare da faɗin "baza ki rakani ciki ba ne?..." A ruɗe ta furta "ciki kuma?..." Ya ce "eh! ko baza ki iya ba? sai na ƙira Mommyn ku a waya tazo ta shigar dani ciki..." Aasmeen kamar zata yi kuka ta ce "Shikenam! four bedrooms ne a site ɗin nan, ka zaɓi a wannan kake son zama?..." Sai da ya baza eyes sannan ya ce "aina bedrooms ɗin suke?..." Idonta na kallon gefe ta furta "duk su na upstairs, 2 su na hawa na biyu, 2 a hawa na uku..." Goya hannayensa ya yi akan ƙirji yana hura iskar bakin sa da alamun akwai abinda yake tsarawa a cikin ransa, Ya ce "Ok mu je hawa na ukun, domin bana son zama a farko-farko, kinsan mijin ki matsoraci ne..." Su na cikin wannan halin sai ga wasu security su biyu sun shigo da kayayyakin sa, daga nan ya sallame su, gyaran murya ya yi sannan ya ce "my Bride zaki iya taya ni ɗaukan jakakkunan nan?..." Ba tare da ta furta komai ba tasa hannu ta ɗauki kaya biyu tabar masa sauran biyun ta haura saman upstairs, Shima murmushi ya yi ya ɗauki sauran ya bi bayan ta.... Sai da suka hau saman upstairs ta uku sannan suka buɗe room ta ƙarshe suka shige, ga wantalelen gado da kujeru ata gefe guda har da plasman da ƙaramin frig, ta wani site guda dake cikin bedroom wardrobe ne da mirror and drowers, da kuma bathroom, su na shiga ta ajiye masa kayayyakin sa tayi saurin juyawa zata fice yayi saurin dakatar da ita, ba tare da ta juyo ba ta ce "na gama maka komai ai yanzu..." Goya hannayen sa ya yi akan ƙirji tare da murtuƙe fuska kamar bai taɓa yin murmushi ba, zuciyar sa kawai take haurowa da zaran ya tuno da matar sa Sophia, Cikin ɗaga murya ya furta "Keee!..." Cike da mamaki Asmeen taji wannan kalma ya daki dodon kunnen ta, a firgice ta juyo tana kallon sa ganin ko shine domin taga yanayin sa kamar bazai iya cutar da mace ba... Ya cigaba da cewa "Ke mallaki nane a yanzu, inada ikon da zan sa kiyi mun duk abinda nake so, saboda haka ki cire wannan jiji da kai naki ki fuskance ni da idon girmama wa...." Asmeen lumshe idanuwanta tayi sai ga zafafan hawaye sun gangaro mata, murya a sanyaye take furta "ban kasance mai jiji da kai ba ya meri pati, ka mun afuwa domin fushin ka a gare ni tamkar wuta ne mai cin duk ilahirin jikina..." Shapris cikin izzah ya furta "idan kuwa kina gudun ɓacin raina to kiyi duk abinda na umarce ki..." Jinjina kai tayi tare da faɗin "Insha Allahu Indai bai tsaba wa Ubangiji na ba..." Ba tare da ya furta komai ba yasa hannu ya fara cire kayan jikin sa, Asmeen ganin haka yasa tayi saurin juya bayan ta jikinta har wani kakkarwa yake, ba ƙaramin tsorata tayi ba ganin ƙiran jikin sa, Sai da ya kammala cire komai ya bar iya short pant a jikinsa sannan ya tako dab da Asmeen yasa hannu ya rungumeta ta baya yana faɗin "Meri Bi-wi shin kina son kasance tare da ni?..." Asmeen tsabar ta gama tsorata hatta muryar ta ma ƙakkafe wa yake, hawaye sun gagara tsayuwa, numfashin ta ne yake haurowa da ƙarfi-ƙarfi lokaci guda sai ji yayi ta faɗa jikin sa ba alamun motsi, ganin kamar a sume take yasa hankalin sa yayi matuƙar tashi, a ruɗe ya ɗago ta tare da kwantar da ita akan gado yana jijjiganta, ganin babu alamar zata farfaɗo yanzu yasa ya yi saurin zuwa wurin frig ya buɗe ya ɗauko ruwan sanyi sannan ya fara yayyafa mata, cikin ƙanƙanin lokaci ta farfaɗo a ruɗe tana furta sunan "Mom! Mom!! Mom!!!..." Cikin fusata ya wani darara mata wani irin mahaukacin tsawa yana zazzaro idanu waje, bata san lokacin da ta haɗiye kukan ba ga yanda idanuwanta suka yi jawur tsabar firgici da tashin hankalin da ta shiga, Jawo ƙafafuwan ta yayi ya zaunar da ita a bakin gado sannan ya ɗora ƙafarsa akan gadon dab da ita ya matso da fuskar sa kusa da nata yana mata kallon ƙurilla sannan ya ce "zan cigaba da dasa miki tsorona a cikin zukatan ki, sannan zan toshe duk wata kafar da zai sa ki raina ni Meri Bi-wi..." Asmeen gaba ɗaya ta gagara gane manufarsa, zuciyar ta cike yake da tambayoyi, girgiza kai ta yi idonta akan sa ta ce "nasan akwai dalilin da yasa ka shiga jikin mahaifiyar mu, shin meye manufar ka akan mu har aka mallaka maka ni, shin cutar da ni zakayi ko kuma so kake kayi rayuwar aure dani tsakani da Allah?..." Kafin ta lumshe ido bata ankara ba taji wasu zafafan mari har sau biyu akan kyakkyawar fuskar ta, a ruɗe ta kama fuskar ta cikin tsoro da firgici tana sakin ihu domin ba ƙaramin mari ya yi mata ba, har sai da ta fara ganin farfatsin wuta... Cikin tsawatar wa ya ce "zan zubar miki haƙwara idan baki mun shiru ba, har ke zaki mun maganar cutar wa? cutar wa ya wuce wanda uwar ku ta mun..." Tana kuka ta ce "tin kafin Aure?..." "ko zaki janye ne?..." Tana hawaye ta ce "idan ka cigaba da cutar dani zan janye..." Murmushi yasau tare da faɗin "okay fine! ki janye sai na Auri mahaifiyarki ita ai zata iya zaman Aure dani tinda ba haramun bane, yanzu zan je na sanar mata cewa kin janye...." Cikin kuka ta furta "Nooo! Dan Allah kayi haƙuri Meri pati, zan cigaba da zama da kai a duk halin da na tsinci kaina, wannan kalmar da ka furta ya mun muni, gwara ka ɗauki wuƙa kaita yankan naman jikina hakan zai fi..." Sauƙe ƙafarsa yayi daga kan gadon ya nufi hanyar toilet yana faɗin "zan shiga wanka, ki shiga kitchen ki girka mun abinda zan ci..." Cikin girmamawa ta ce "godiya nake Meri pati..." Ta miƙe tare da ficewa daga room ɗin tana ƙoƙarin goge hawayen fuskar ta.... Nasreen da Tasleem ne suke zaune a bakin gado sun jeru kamar masu karɓan gaisuwa, a hankali Nasreen take motsa lips ɗin ta tana yiwa Tasleem nasiha akan ƙin bin umarnin mahaifiyarsu, "Tasleem kin san uwa uwace koda ita ɗin mahaukaciya ce balle mun samu uwa jajirtacciya kuma mai kula akan ƴaƴanta, tana matuƙar ƙaunar mu meyasa baza mu bi umarnin ta ba? meyasa baza mu mata biyayya a matsayinta na uwa ba? mu kaɗai ta haifa ƴan uku babu namiji a saman mu da ƙasan mu, mai yasa baza mu zamo mata jajirtattun jaruman triplets ba...." Tasleem lumshe ido tayi tare da faɗin "please it's okay! shin a yanzu bama mata biyayya ne ko bama bin umarnin ta?..." Nasreen ta ce "bakya tsoron ta sannan bakya bin umarnin ta..." Tasleem murmushi ta sau idonta na kallon gefe guda ta ce "meyasa kika yi wannan tunani akaina ?..." Nasreen ta ce "abinda ya faru yau ke da Mommy, a gaban baƙon ta kika rufe ido kamar ba mahaifiyar ki ba, kina sa'in sa da ita akan abinda bai kai ya kawo ba, just ki durƙusa ki gaishe da baƙon ta shine problem haba Tasleem, ana sara ana duba bakin Gatari mana, mata mai mutunci mai daraja mai kima a idon kowa amma ta kasa samun wannan darajar da mutunci a idonki, I think ko wani kika ga yana cin mutuncin mahaifiyar ki sai yanda ƙarfin ki ya ƙare balle ke da kan ki..." Wani irin tsawa Tasleem ta dararawa Nasreen har sai da Nasreen ta toshe kunnuwanta, haka Tasleem ta miƙe tsaye tana faɗin "ke kin kasa fahimtata shin waye zai fahimci halin da nake ciki? waye zan gaya wa damuwata? duk babu domin kuma bakin ku ɗaya da mahaifiyata wacce ta kasa bamu lokacin ta, muhawara, shawara, damuwa duk mun kasa sanar mata saboda tsoron da ta dasa wa zuciyoyin mu, gani take idan ta zauna da mu tasan matsalolin mu zata cutu ne, har yau mommy bata taɓa yi mun abinda nake so ba taya itama zata samu abinda take so a wurina? Nasreen babu wacce zata fahimci halin da nake ciki, akwai wani sirri a jikina wanda idan mungu ya raɓe ni ƙiyayyarsa ta zaunu kenan a cikin zuciya ta, ina jin ƙamshin mungu a ko ina yake, duk wanda yake cikin ƙungiyar mugunta zan sa ni idan na kalli cikin ƙwayar idanuwansa, Allah ya bani baiwar gano haka wanda babu tsafin da zai kawar mun da wannan baiwar da Allah ya bani, mommy tana daga cikin mungwayen faɗin duniya domin naji hakan a jikina..." A ruɗe Nasreen ta miƙe tsaye tana faɗin "Tasleem ki dakata haka, shin kin taɓa ganin ta aikata wani abinda ba dai dai ba?..." Tasleem ta ce "ko ban gani ba amma naji hakan a jikina..." A tsawa ce Nasreen ta ce "Zancen banza kawai..." tana kuka tana girgiza kai ganin bata da ta cewa ne yasa ta fice daga ɗakin, Tasleem bin bakin ƙofar tayi da kallo tana mamakin kanta yanda take jin wasu abubuwa a jikin ta, ta kasa yadda da abinda take ji akan mahaifiyar ta amma wasu lokuta takan yadda da haka, haka take ta wannan tunanin har ta nemi wuri ta zauna... Nasreen bayan fitar ta a falo ta tsaya sai kai kawo take ta kasa samun nutsuwa, maganganun Tasleem ne suke yawo mata a kai, bata taɓa tunanin Tasleem tana da ƙwarin gwiwar da zata furta waɗannan maganganu, tana cikin wannan halin taji an da fa kafaɗarta, a zabure Nasreen ta juyo tana kallon wacce take bayan ta, idonta akan Madam Nablah ta ce "Mom daman ke ce?..." Madam Nablah murmushi ta sau tare da faɗin "maganar zucin mai kike?..." Nasreen ta ce "Mom ba komai..." "Kin tabbata?..." A cewar Madam Nablah.. Jinjina kai Nasreen tayi alamar eh. Madam Nablah ta ce "zuwa nan da anjuma kaɗan ku je supermarket ku zazzaɓi kayan da zaku yi hidimar shagalin bikin ku, kayan ɗaurin Aure kuma nasa ayi mun ordersu daga can London da kayan furnitures..." Nasreen cikin rashin fahimta ta ce "Mom wani irin kaya zamu zaɓo bayan kayan sakawa da furnitures, kuma naji kina maganar biki tin yanzu shin yaushe ne?..." "Sai na nema wa Tasleem abokin haɗi kafin na yanke rana...." a cewar Madam Nablah, sannan ta nufi waje tana faɗin "zan fita saina dawo..." Nasreen a hankali take lumshe idanuwanta domin jin maganar take kamar a cikin mafarki... Juyawar da zata yi kwatsam ta tarar da Abeesh yana sauƙo wa daga saman upstairs kan sa a ƙasi, itama ganin sa yasa tayi saurin juya bayanta tana ƙarƙame da idonta, domin yanzu ba ƙaramin kunyar sa take ba, tsaya wa ya yi ata bayanta yana so yayi magana amma yana tunanin shin wacece a cikin su, A hankali ya furta "My Juju?..." (Tasleem) A hankali ta girgiza kai alamar ba ita bace still bata juyo ba, ya kuma cewa "my Sis?..." (Asmeen) Ta sake girgiza kai alamar a'a. Murmushi ya sau domin shima tin tinin ya gane Nasreen ce tin sauƙowar sa, domin ko wacce ya karanci halayen ta, ɗaukar takarda da biro ya yi bayan ya gama rubutun sa ya ajiye akan table ɗin falo sannan ya wuce ta gefenta idonsa akan kyakkyawar fuskar ta ga idonta a lumshe bata son haɗa ido da shi, shima kuma hakane yana jin nauyin ta haka ya fice daga falon daman wurin aiki zai tafi, Nasreen tana jin ya ta da mota sai a lokacin ta buɗe eyes ɗin ta tana sakin nannauyar numfashi, ta juya kenam idonta ya sauƙa akan takardar da yayi rubutu a ciki, sai da ta ɗau tsawon mintuna kafin tasa hannu ta ɗauki letter tare da buɗe wa, abinda ta fara karantawa shine rubutun saman takardar "Amincin Allah ya ƙara tabbata ga wannan baiwar Allah mai ɗauke da kyakkyawar murmushi akan fuskar ta, ina fatan kin tashi cikin wadataccen lafiya, Dokar hana kaimun abinci sai ke ya fara aiki yau, amma baki kai mun ba kin bar ni da yunwa Allah yasa kar murmushin fuskar ki ta ɗauke wuta akaina saboda wannan dalilin, bazan taɓa ƙin ki ba sarauniya amma ban san taki zuciyar ba, idan har kin amince da ni ina mai baki haƙuri akan cewa ban iya soyayya ba, sannan tsoron soyayya nake, Bissalam...." Bayan Nasreen ta kammala karantawa tsabar farin ciki bata san lokacin da ta hau saman kujera ta faɗo ƙasin carpet ba, ta rungumi letter akan ƙirjinta sosai tana hamdala, haka ta rufe idanuwanta sosai tana jero addu'o'in farin ciki da warkewar zuciya, cikin farin ciki ta fara buɗe eyes ɗin ta ganin Asmeen a tsaye ta zuba mata ido ne yasa Nasreen miƙe wa ta nufi wurin ta tana faɗin "Asmeen sai yanzu kika dawo? kodai ansha ruwan soyayya ne..." Asmeen itama murmushi tasau tare da faɗin "ina taya ki murnar samun abinda kike so ƴar uwa..." tasa hannu ta rungume ta, Asmeen hawaye ne kawai suke zubo mata na baƙin cikin halin da ta tsinci kanta na rashin dace da masoyin gaskiya wanda yake sonta tsakani da Allah..." Nasreen jin kukan Asmeen ne yasa ta ɗago da ita tana faɗin "lafiya kuwa Asmeen? meya faru dake? dan Allah ki sanar mun Please..." Nasreen itama hawaye ne suka cicciko mata ganin a halin da ƴar uwar ta take ciki ga kuma idanuwanta sun yi jawur tsabar kukan da tasha kafin ta bar part ɗin Shaprees.... Asmeen ganin yanda Nasreen ta ruɗe lokaci guda yasa ta wayince tana murmushin ya ƙe ta ce "No no no please my Sister..." Nasreen ta ce "to meyasa kike kuka?..." Asmeen tana murmushi ta juyar da harshe yaren su tana faɗin "Meri pati mere liye bohot pyaar karta Hai, aur main bhi use apne dil ki dhadkan se pyaar karti hoon...." Nasreen cikin kuka ta ce "idan har hakane meyasa kike kuka? ni ban yarda da ke ba..." Asmeen riƙe hannunta tayi ta ce "Nahe! Nahe!! Nahe!!! Kukan farin ciki nake..." Itama Nasreen murmushi ta sau tare da ƙara rungumar juna cikin kulawa... The Soldier Amaar Junaid: yana zaune a ƙerarren gidan wanda ya mallaka bayan dawowar sa daga ƙasar Bangladesh country in south Asia, Sojan ƙasar Bangladesh bayan ɓatar da shi da akayi a cikin ruwa tsawon shekaru Ashirin, ba tare da sanin yanda iyayensa suke ba. Takaitaccen tarihin Amaar Junaid. Shi ɗin ɗan nan ƙasar Nigeria ne ɗan haifaffen garin Maiduguri, su biyu iyayen su suka haifa shine babban ɗa a wurin iyayen sa sai ƙaninsa mai suna Abeesh wanda mahaifiyar su ta rasu a haihuwar Abeesh, tin daga lokacin mahaifinsu ya cigaba da kula da su, duk wata tarbiyya da ilimin boko da Islam sun samu a wurin mahaifinsu, Akwai wani ƙanin mahaifinsu Amaar wato Alhaji Ahmed Tajiddeen ya buƙaci a bashi ƙaramin yaron Yayansa wato Abeesh kasancewa shine ƙarami, zai fi samun kulawa a hannun mace wacce zata zamo masa tamkar Uwa, daga lokacin Alhaji Ahmed ya damƙawa matar sa Madam Nablah Abeesh a hannunta domin a lokacin bata samu haihuwa ba, kuma Madam Nablah a lokacin mutumiyar kirki ce ga sanin darajar mutane, ita ta cigaba da kula da Abeesh ta mayar shi tamkar ita ta haife shi, shi kuma Amaar baya buƙatar zama a wurin kowa sai a gun mahaifinsa amma yakan je gidan da ƙaninsa yake kullum domin dubo shi, mahaifinsu kuma bai ƙara Aure ba haka yake zaune.... Bayan wasu ƴan shekaru itama Madam Nablah Allah ya azurtata da samun yara mata ƴan uku tin daga lokacin aka rasa tunanin Madam Nablah, ƙwaƙwalwarta ta sauya zuwa munguwar ƙwaƙwalwar da bata tunanin komai sai na cutarwa, ta faɗa cikin wani ƙungiyar da bata san da zaman sa ba, ganinta kawai tayi a ciki anan aka bata umarnin ta kawo jinin mijinta idan har tana son ta zama sarauniyar gagara duniya, hakan kuwa akayi sai jin labarin mutuwar mijinta akayi lokaci guda, Mahaifinsu Amaar kuwa bayan ya fahimci halin da ake ciki ya buƙaci ɗan sa Abeesh amma Madam Nablah fur ta ƙi amince wa daga ƙarshe ma ɓoye Abeesh tayi yanda ba wanda zai ƙara ganinsa... Amaar Junaid ya kasance mai matuƙar ƙaunar ƙaramin ƙaninsa Abeesh, daga lokacin shima ya daina ganin Abeesh, ya damu sosai amma sai dai akwai wacce take ɗebe masa kewa, Ɗiyar ƙanin mahaifinsu wato ɗaya daga cikin triplets, sun yi matuƙar shaƙuwa sosai, triplets tin suna yara ba'a iya banbance su amma Amaar Junaid yana iya gane gwanar sa wato Tasleem, a makaranta basa rabuwa haka a gida, a baya yana yawan zuwa gidan Madam Nablah saboda ƙaninsa Abeesh yanzu kuma da ya daina ganinsa sai yake zuwa saboda Tasleem, duk wannan shaƙuwar da suka yi akan idon Madam Nablah suke, kwata kwata bata jin Amaar a ranta tin daga lokacin da wannan matsalar ya faru da ita taji an dasa mata ƙiyayyar Amaar, ta tsane shi sosai ji take kamar ta kashe shi, idan Madam Nablah taji tana son aiwatar da abu a ranta takan aiwatar da shi ne cikin sauƙi ba tare da ta takura kanta ba... Wata rana Amaar yana gidan Madam Nablah yana wasa a filin ball dake other site shi da Tasleem, A lokacin Amaar yana shekara 10 ita kuma Tasleem ko wacce tanada shekara biyar biyar a duniya, Su na cikin wasan su sai ga Madam Nablah a filin wasan, dai dai lokacin da Amaar ya wurgo wa Tasleem ball a lokacin Madam Nablah ta cabke tana masa wani irin kallo na ƙiyayya, Tasleem ce ta tsaya a gaban ta tana faɗin "Mom ki bamu kwallon mana..." Amaar yana dariya ya ce "A'a Tasleem itama Mommy tana so zata yi wasa damu..." Idon Tasleem akan fuskar Madam Nablah ta ce "Mom meyasa kike fushi to kuma idonki akan Amaar ɗina..." Madam Nablah sakin murmushin yaƙe tayi sannan ta durƙusa ƙasi tana shafa fuskar Tasleem tare da faɗin "My beauty Tasleem inaso ki ara mun Amaar ɗinki zai rakani wani wuri yanzu zamu dawo..." Tasleem hannu tasa tana toshe hancin ta tare da faɗin "Mom meyasa duk turaren da kika saka kike warin jini ne?..." Madam Nablah a ruɗe ta zaro manya-manyan idanuwanta cike da tashin hankali ta ce "jini kuma Tasleem aina?..." Tasleem ta ce "eh kina warin jini shiyasa bana son zama a kusa da ke, kuma ina mafarkin ki kina cin ɗanyen naman mutum, kuma kina zama namomin daji...." Madam Nablah rufe idanuwanta tayi sosai tana girgiza kai ta ce "ki daina faɗin haka kin san mafarki ba gaskiya bane, kina addu'a..." Tasleem murmushi tasau a lokacin ta ce "TOH Mommy, amma ina zaki je da Amaar? nima zan bi ku..." Madam Nablah ta ce "a'a jira mu yanzu zamu dawo..." Ta miƙe tsaye idonta akan Amaar ta ce "ka je ka shiga mota bari na ɗauko key..." Daga nan ta wuce, Tasleem kamar zata yi kuka ta ce "Amaar baza ku tafi dani ba koh?..." A ruɗe ya zo gunta yana faɗin "a'a kar kiyi kuka Tasleem, zamu yi wa Mommy wayo kema ki biyo mu, kawo kunnen ki na gaya miki wata magana..." Kama kunnen ta yayi ya mata raɗa a kunne, tana dariya ta ce "yeee haka zan yi wa mommy wayo..." Tana faɗin haka ta tafi da gudu ta je ta buɗe bayan both ɗin mota ta shige, shi kuma ya buɗe back seat ya zauna, ba jumawa ta dawo itama ta shiga taja motar suka tafi, tafiya taƙi ƙarewa saida sukayi tafiya mai nisan gaske har sai da bacci ya ɗauke Tasleem a bayan both, Basu tsaya a ko ina ba sai a cikin daji kusa da bakin wani rami mai ɗauke da ruwan gaske wanda ba'a iya ganin ƙarshen ruwan, tana huci ta ce "Amaar sauƙa..." Cike da tsoro da fargaban wurin yana kallace-kallace ya fito daga motar, babu kowa sai kukan tsuntsaye da kuma ƙarar tafiyar ruwa... A ruɗe ya kalli Madam Nablah wacce itama fitowar ta kenan ya ce "Mommy ina ne nam?..." Tasleem itama tashin ta kenam daga bacci taji Amaar yana tambayar ina ne nam, cike da zumuɗi ta haura saman kujerun motar ta fito ta ƙofa, kallace-kallace ta fara yi itama, tana tsaye a jikin mota ta bayan Madam Nablah, Amaar yaga fitowar Tasleem amma sai ya nuna bai ganta ba saboda a ɓoye tazo ta, sai ji suka yi Madam Nablah ta furta "Amaar nan ɗin wurin mutuwar ka ne, anan zaka mutu..." Amaar yana zazzaro ido waje cike da tsoro ya ce "waye zai kashe ni?..." Dariya Madam Nablah ta yi sannan ta ce " Ni mana, waye zai kashe ka in ba ni ba, Ni ce ajalinka..." Kuka Amaar ya fara yi yana faɗin "me na miki zaki kashe ni?..." Madam Nablah ta ce "baka kai nayi maka bayanin abinda nayi niyyar yi ba..." Lokaci guda idanuwanta suka chanza colour sai ga fiƙoƙi sun fito waje nan ta zama Kura, Amaar ja da baya yake har ya faɗi ganin Kurar tana yo wa kansa yasa ya miƙe da gudun gaske, itama Kurar bin bayansa tayi, Tasleem ganin abu yana shirin fin ƙarfin idanuwa sun ƙafe baki ya gagara rufuwa, kamar wacce aka zabure ta tayi wani irin ihu tare da furta "Amaaaaarrrrrr...." Itama ta bi bayan su da gudu, gudu kaɗan tayi ta rinke su Amaar yana kwance a ƙasi yanda ya faɗi sai Kurar da take ta huci a gaban sa, Tasleem tana kuka ta ce "Mom daman ke ce a cikin mafarki na, shine kika ce mafarki ba gaskiya bane ashe ke ce mai ƙarya..." Jin maganar Tasleem ata baya ne yasa Kurar juyowa dai dai lokacin da ta dawo asalin mutum ɗin ta tana sanye da baƙaƙen kaya ga idanuwa yanda suka canza launin kore, Madam Nablah mamaki take ta yanda Tasleem ta biyo su, Tasleem da gudu ta je wurin Amaar ta faɗa jikin sa tare da rungumar sa sosai tana kuka tana faɗin "Mom bazan bari ki kashe mun Amaar ɗina ba, ke ke ke ɗin ba mutum ba ce..." Amaar shima kuka yake ya rungumi Tasleem sosai yana faɗin "Tasleem dan Allah kar ki bari Mommyn ki ta kashe ni, ita ɗin ba mutum ba ce, zata kashe ni..." Murmushi Madam Nablah ta yi taje yanda suke zata raba su, haka suka ƙanƙame juna suna ihu, duk da yara ne amma ta kasa ɓanɓare su ga ihun da suke yi gaba ɗaya sun takura ƙwaƙwalwar ta sam bata ƙaunar ƙara ko ihu ko kiɗa mai sautin gaske.... Wani dabara ne ya faɗo mata a rai, ta lumshe ido tare da tsafe musu jiki da tsafin hannunta, nan suka fara jin shocking yana ratsa jikin su kamar electric, ba shiri suka rabe da juna duk suka watse gefe guda, Madam Nablah riƙo hannun Amaar tayi ta ɗago shi tsaye tare da jan sa suka fara tafiya, ganin haka yasa itama Tasleem ta jajirce ta miƙe ta bi bayan su da gudu tana faɗin "Mom kar ki kashe mun Amaar dan Allah, Amaar! Amaar!! Amaar!!! wayyo Allah, Mom kiyi haƙuri...." Shima haka yake waiwayo wa yana miƙa wa Tasleem hannu tare da faɗin "Tasleem dan Allah ki taimake ni, kar ki bar mominki ta kashe ni, Tasleem ki taimake niiiii...." Madam Nablah sai da tazo bakin ramin ruwa tukun ta ɗaga Amaar sama zata jefa shi ciki, Tasleem tana ihu ta ce "Mommmmm! kar ki jefa mun shi cikin ramin nan, ruwa ne a ciki zai mutu mommy...." Ai kafin Tasleem ta rufe baki har Madam Nablah ta sau shi ciki, Tasleem a ruɗe tasau wani irin ihu ta taho da gudu itama zata faɗa Madam Nablah tayi saurin riƙo ta suka koma baya, haka Tasleem take dukan mommynta aka ta sake ta zata bi Amaar, ganin bazata sake ta ba yasa ta kafa hakwaranta ta garzaya mata cizo anan ta kuɓuce tayi bakin rami da gudu itama tayi tsalle ta faɗa cikin rami, A gigice Madam Nablah cikin tsoro da fargaba tayi wani tsafin ta sai ga hasken green yana fita daga cikin tafin hannayenta guda biyu da wannan tsafin ta ɗago da Tasleem sama kafin ta ƙarasa cikin ramin, haka ta miƙar da hannayenta sai ga Tasleem ta tafo gare ta cikin iska, a ruɗe ta kamo ta tare da rungumar ta sosai tana faɗin "ki dakata da wannan shirme nakin..." Tasleem gaba ɗaya ta fita hayyacinta ko motsi bata iya yi sai bakin ta dake furta "Amaar! Amaar!! Amaar!!!...." Da wannan sunan ta sume akan cinyar mahaifiyar ta, a lokacin Madam Nablah ta wallafa wani tsafin ta tana shafar sumar kan Tasleem tare da faɗin "ki manta da wannan al'amarin da ya faru akan idonki, ina so bakin ki ya rufe akan ƙiran sunan Amaar, bakin ki ya toshe, tunanin ki ya gushe yanda bazaki iya tuna duk abinda ya faru dake ba, Tasleem! ko a mafarki bana son wannan al'amarin ya dawo miki...." Haka take ta wannan surutan tana shafa kanta, duk sai da ta mantar da ita komai har Amaar a cikin ƙwaƙwalwar ta, daga nan ta ɗauke ta tare da nufan mota ta kwantar da ita a back seat, sannan itama ta shiga ta ja mota suka tafi....... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 11 to 12 Cigaban labarin...... Wata zurariyar mota ce GLK 350 4matic ta parker a wurin parking beside Supermarket. Wacce take back seat ce ta fara fito wa kana ganin ta kasan ƴar hutu ce, tana sanye da Swiss Lace mai bala'in tsada da ɗaukar ido, komai nata two match ne sai black glass mai designer da ta toshe eye ɗinta da shi, Tana rufe murfin motar sai ga wata ta ƙara fito wa ta front seat the same irin kayan wanca ne a jikin ta, sai ga ta uku wacce take driving itama ta fito still irin shigar sauran biyu, Ƴan uku masu kamanni ɗaya sun jeru komai nasu iri ɗaya sai taku suke irin na sarakuna, mutanen wurin kowa idonsa akan su, wasu har da video domin kowa ya sha'awance su amma kowa fargaban tinkarar su yake domin babu wanda bai san ƴaƴan Madam Nablah ba ce, Yaran da duk wanda ya kulasu ƙarshen rayuwar sa kenam sai dai a gani da ido a ƙyale.. Tasleem tana tafiya tana juyar da key ɗin mota dake hannun ta, kai tsaye cikin supermarket suka shige, su na shiga ko wacce ta bi layin kayan da take son ɗauka, Nasreen layin kayayyakin drinks ta bi domin idan ta shigo abinda take fara ɗauka kenan kayan fruits, tana taku a hankali tare da duba abubuwan da take so ba tare da ta duba gaban ta ba ta yi tuntuɓe da wani Basket da yake ajiye akan hanyar da zata wuce sauran kaɗan ta kife a ciki, mutumin da ya ajiye kuwa shima yana tsaye ya juya bayansa yana ta waya, jin motsin mutum ne yasa shi juyo wa yana faɗin "oh my god sorry my sister, fatan baki ji ciwo ba..." Cikin murmushi Nasreen ta ɗago tana faɗin "No kar ka damu, ban ji komai ba..." Ɗagowar da zata yi suka haɗa ido, zaro ido tayi cike da mamaki tana faɗin "kamar na taɓa ganin wannan fuskar koh..." Cikin rashin fahimta ya ce "aina kenam?..." Nasreen ta ce "nasan daman bazaka iya tuna da mu ba amma mu kam a duk inda muka ganka zamu gane ka, domin zuciyoyin mu basa manta wanda ya kyautata musu..." Mutumin murmushi ya yi sannan ya ce "naji kamar jam'i kike, wata ƙil ba ke kaɗai kika gane ni a yanda muka haɗu ba ko?..." Nasreen jinjina kai tayi sannan ta ce "Ni da ƴan uwana, amma nayi mamakin rashin gane mu daka yi, amma ba abun mamaki bane domin duk wanda yake soyayya baya taɓa ganin fuskar mace in ba ta masoyiyar sa ba...." Bai san lokacin da ya saki dariya ba Ya ce "ke da kanki kinyi tambaya sannan kin bawa kan ki amsa, oh daman haka duk wanda ya faɗa soyayya yake? to wata ƙila nima hakan ne shiyasa na kasa gane ki..." Jinjina kai Nasreen tayi sannan Ta ce "Okay! akwai wasu ƴan mata uku da ka cecesu daga hannun Kura a filin school of UNIMAID..." Amaar Junaid cike da mamaki ya ce "Okayyy! Na tuna, kune ƴan ukun nan?..." Da sauri Nasreen ta amsa masa cikin fara'a... Su na cikin wannan halin sai ga Asmeen ta nufo wurin su tare da faɗin "Nasreen da wa kike tsaye ne shin kin kammala ɗaukan abinda zaki ɗauka ne?..." Nasreen ta ce "Asmeen shin kin gane wannan bawan Allah?..." Buɗe baki Asmeen ta yi cike da mamaki ta ce "laaa! wannan ba wancan sojan da ya taimaka mana a school ba ne?..." Nasreen ta ce "shine mana..." Amaar da murmushi akan fuskar sa ya ce "a cikin ku wacece marar lafiya?.." Asmeen ta ce "kana magana akan ɗayar ƴar uwar tamun ne? babu ita a cikin mu, ni sunana Asmeen wannan kuma Nasreen, munyi farin cikin haɗuwa da kai, shin ko zamu iya sanin sunan ka?..." Nasreen kallon ta tayi ta ce "Ke fa kin cika surutu, kin san irin waɗan nan basa son surutu da yawa..." Asmeen ta ce "An gaya miki shi ɗin kamar Sister mu ta gida ne..." Amaar ya ce "kar ku damu I'm a simple Man, ni ɗin ba kamar yanda ku ke tunani bane, na kan iya rayuwa da kowa cikin mutunci da daraja, ni surutu na ma har ya zarce na Sis Asmeen..." Asmeen tayi wani irin tsalle ta ce "wow to kin ji fa, zamu zo ɗaya da shi, please zaka iya bamu number wayan ka, ai zamu na gaisawa...." Nasreen ta ce "Da farko dai mu fara jin sunan sa..." Sauƙe numfashi ya yi sannan ya ce "Sunana Major A.J..." Nasreen ta ce "Ma sha Allah..." Asmeen ta ce "wow kin ji fa suna mai daɗi wai Major A.J, am to number waya..." Ya ce "okay bari na baki..." Asmeen ta ce "tsaya tsaya kafin nan zamu iya yin selfie?..." Amaar ya ce "why not..." Nasreen ta ce "Asmeen abin nakin ya fara yin yawa, ki bar shi haka kar daga yanzu mu gundure shi..." Asmeen ta ce "haba one selfie kam wani gundura..." Kafin su ankara suka yi wani mutumi ya yi magana yana faɗin "Ɗan uwa kayi nesa da waɗannan yara domin zasu zamo Ajalin ka, su ɗin Mayu ne duk namijin da ya tsaya da su sai ya mutu...." Nasreen zaro ido waje tayi har eyes ɗin ta sun cicciko da hawaye cikin tsoro da fargaba ta riƙo hannun Aasmeen... Itama Asmeen jikin ta ba ƙaramin sanyi ya yi ba, lokaci guda farin ciki ya ɗauke akan fuskar ta, ƙararar damuwa ne akan fuskar.. Amaar cikin rashin fahimta haka yake kallon mutumin daga bisani ya ce "ban fahimci abinda kake nufi ba..." Mutumin ya ce "inaso ne na ceceka daga munguwar hallaka, waɗannan ƴan mata su ɗin Annoba ne, basu da aikin yi sai kisa da shan jinin matasa duk wanda yace yana son su ko ya yi gigin tsayawa da su..." Amaar maida idonsa yayi kan su yana mamakin irin furucin da ake akan su, cikin sassanyar murya ya furta "wai da gaske ne?..." Asmeen girgiza kai ta fara yi tana kuka, a razane Nasreen ta riƙo hannun Aasmeen tare da faɗin "kin ga zo mu tafi..." Ba shiri suka bar wurin... Amaar kallon mutumin ya yi sannan yasau murmushi yana faɗin "shin akwai wata hallakar da zanyi a gaba wanda ya wuce na baya??..." Mutumin ya ce "Ni dai na gaya maka gaskiya yauwa sai anjuma..." daga nan yayi tafiyar sa... Amaar tsayawa yayi wuri ɗaya tare da lumshe idanuwansa, ƙwaƙwalwar sa ce ta fara tariyo masa abubuwan da suka faru da shi kamar a mafarki, Fuskar Madam Nablah da bazai taɓa manta kamannin ta ba ya fara gani lokacin da ta zama Kurar daji, da idanuwanta da suka canza zuwa wani launi da ban, da lokacin da Madam Nablah ta ɗaga shi sama ta sake shi a cikin ramin ruwan hallaka dai-dai lokacin da Nasreen da Asmeen suka ƙwalla ƙiran sunan Tasleem, A ruɗe ya buɗe idanuwansa jin wannan sunan da bazai taɓa manta shi a cikin ƙwaƙwalwar sa ba, jin suna ta ƙiran sunan Tasleem yasa ya nufi wurin su da gudun gaske, domin a duk yanda yaji mace mai suna Tasleem sai ya neme ta sannan ya yi ƙoƙarin taɓa koda hannun ta ne domin tabbatar da asalin Tasleem ta hanyar jin shocking, A yanzu ya samo asalin Tasleem ɗinsa wato ƴar uwar su Nasreen da Asmeen... A bakin titi ya iske su suna tsaye su biyu Nasreen da Asmeen ko wacce da damuwa akan fuskar ta, Muryar Amaar suka ji yana faɗin "lafiya kuwa??..." Nasreen da Asmeen a tsorace suka juya suna kallon sa tare da kawar da idonsu suna kallon mutanen wurin, kowa idonsa akan su ana nuna su alamar maganar su ake. Amaar ne ya sake furta "me yake faruwa ne?..." Nasreen ce tayi ƙarfin halin cewa "Ƴar uwar mu ce ta fito cikin damuwa ta shige mota ta tafi, bamu san ina ta tafi da motar ba..." Asmeen ta ce "naga an ƙira ta a waya kamar wani magana aka sanar mata, daga nan ta tafi da sauri cikin fushi..." Nasreen ta ce "ke ma dai kinsan koda yaushe a cikin fushi take, yanzu aina zamu same ta?..." Amaar ya ce "ga can mota ta shin zan iya kai ku yanda take?..." Nasreen ta ce "a'a bama son wani abu ya faru da kai, mun gode zamu jira ta..." Amaar ya ce "ku na nufin kuce na gamsu da abinda wancan mutumin ya faɗa akan ku?..." Asmeen ta ce "ka yadda da shi tabbas abinda ya faɗa maka gaskiya ne, shiyasa muke rayuwarmu mu kaɗai, babu wanda yake shiga shirgin mu..." Amaar ya ce "kar ku damu akan abinda mutane zasu ce akan ku, Indai kuna da kyakkyawar zuciya babu wanda zai ci galaba akan ku, ni ina tare da ku babu abinda zai cutar da ni..." Nasreen da Asmeen har zuwa wannan lokacin basu dawo normal ba, ko wacce da hawaye akan fuskar ta... Amaar ya ce "a matsayina na ɗan uwanku Musulmi inaso ku mun wata alfarma dan Allah..." Nasreen ta kalle shi cike da mamaki ta ce "wani irin alfarma?..." Da murmushi akan fuskar sa ya ce "inaso ku bani dama na zama abokin ku na amana, wanda zai rinƙa saka ku cikin farin ciki sannan mai tare muku faɗa a koda yaushe..." Nasreen da Asmeen kallon juna suka yi sannan suka mayar da eyes ɗin su kan sa, Nasreen ta ce "har ka tuna mun da wani ɗan uwan mu wanda muka rasa shi tsawon shekarun baya, ya kasance shine mai tare mana faɗa kuma mai kishin mu, mun rasa shi har abada..." Asmeen tana hawaye ta ce "YA AMAAR..." Nasreen itama tana hawaye ta jinjina kai... Amaar yana tsaye shima sauran kaɗan hawaye ya yanko masa yayi saurin kawar da kan sa gefe tare da faɗin "Allah sarki! Ina so ku bani damar maye gurbin sa..." Asmeen da sauri ta furta "mun baka..." Nasreen kallon Asmeen tayi tana sakin murmushi, duk basu san lokacin da suka tsinci kan su cikin farin ciki ba, Shima yana murmushi ya basu damar shiga motar sa zasu bi bayan Tasleem ta hanyar connecting location da phone number ta.... Cikin lokaci ƙanƙani suka isa wurin da motar ta take a tsaye cakk, Asmeen ta ce "wannan ne motar mu, i think tana ciki..." A ruɗe Nasreen ta ce "Polo Grand Hotel?..." Sai a lokacin Asmeen ta lura da yanda suka zo, a zabure ta furta "Hotel kuma, me tazo yi?..." Amaar idon sa akan motar ya ce "tana cikin motar bata fita ba, ina tunanin tana jiran fitowar wani ko wata..." Su ma suna cikin mota basu fita ba, sai gani suka yi wani saurayi ya fito daga cikin Hotel ya nufo motar ta, yana zuwa ya fara knocking, saurayin irin masu jiji da kai ɗin nan ne, tantiran ƴan daba domin har da sigari a hannun sa yana zuƙa... Bayan wasu mintina sai ga Tasleem ta buɗe murfin motar ta sai da ta fara sauƙar da ƙafar ta ɗaya kafin wasu seconni ta fito da ɗayar cikin ƙasaita da izzah ta fito a cikin motar tana taku a hankali sai ƙarar sautin takalmin ta ake ji har ta zagayo yanda saurayin yake a tsaye yana busar taba, Tsayawa tayi a gaban sa tare da goya hannayen ta akan ƙirji, ga wani tsararren black glass akan dara-daran idanuwan ta suna facing juna... Cikin izzah ta furta "Sarkin ƴan daban yanki Arewa, gagara hukuma...." Wani irin mahaukacin dariya ya yi tare da hura mata hayaƙin tabar bakin sa, yana faɗin "ba iya hukuma ba gagara kowa ne..." Murmushi ta sau ko motsi bata yi ba balle hayaƙin tabar sa ya dame ta, ta ce "ban da kowa domin baka kai ka gagari kowa ba har yanzu da sauran ka..." Wani irin kallo ya yi mata yana faɗin "me ke tafe da ke murɗaɗɗiyar yarinya mai murɗaɗɗen tunani, ai da kin mun magana har wurin da kike zan je na same ki, amma yanzu ina cikin jin daɗi na da Babies ɗina akan gado kin zo kin takura mun akan na fito waje, shin meya hanaki shiga cikin Hotel ɗin?..." Tasleem tana tsaye fuska ba alamar annuri ta ce "kar ka yi kuskure dangantani da shiga cikin Hotel sannan ba wai jin daɗin kaina ne yasa na biyo ka har yanda kake ba, ba muhawara nazo muyi ba..." Nasreen suna cikin mota ta ce "me Tasleem take a wurin wannan mutumi marar ɗa'a?..." Asmeen ta ce "kamar tattaunawa suke akan wata magana, amma meye alaƙar dake tsakanin su, a sanin mu Tasleem bata tsayawa da kowa tayi zance saboda bata da lokacin kowa..." Amaar idonsa akan ta ya kasa furta komai... Tasleem cikin fushi ta furta "Meyasa kayi mata fyaɗe?..." Mutumin jin tambayar da tayi masa ne ya sa shi tintsirewa da dariya ya ce "Amma kin raina mun wayo yarinyar nan, yanzu don nayi fyaɗe har sai an tambaye ni Meyasa nayi? ka ji banza! jin daɗin rayuwata mana, wai ma tsaya kina magana ne akan waye? kinsan sunada yawa akwai yara sannan akwai ƴan mata akwai tsofi shin wa ye daga ciki?...." Haka zuciyar Tasleem yake hauro wa kamar ta murɗe masa wuya amma da haka ta daure cikin ɗaga murya ta furta "Yarinya ƙarama ƴar shekara uku marainiyar Allah wacce ake rainon ta a gidan marayu, fara zuwan ta makaranta kenam ka shiga cikin makarantar kayi mata fyaɗe saboda kaga babu wanda zai ɗauki hukunci akan ka, to wannan yarinyar tana cikin ƙarƙashin kulawa ta, duk ƙananun yaran da suke cikin gidan marayu tamkar jinin jikina nake jin su, da hannuna na yi rubutu na ɗauki yara 15 ƴan shekara 3 zuwa 4 na sanya su a makaranta, a cikin motata na ɗauke su na kai su makaranta na biya musu kuɗin makaranta, yau kwana uku da fara zuwan su, yau kuma aka ƙira ni ake sanar mun ta'addancin da kayi musu, kayi wa ƙananun ɗalibai biyar fyaɗe a lokaci guda kuma kana tunanin baza'a yi maka komai ba saboda kana yaron Minister, tirrrrrrr...." Tinda Tasleem ta girma bata taɓa yin kuka ba sai yau, ta cikin glass ɗin kan idonta hawaye yake tsiyaya kamar da bakin gora.... Duk waɗannan maganganu da tayi babu wanda bata ɗaga murya kowa ya ji ba, Su Nasreen dake cikin mota duk suna jin abinda take faɗi, haka hawaye yake tsiyaya a cikin idon Nasreen itama, Asmeen kuwa ba abinda take faɗi sai Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Shima Amaar ya jinjina wa rashin imani irin na wannan mutumin... Mutumin da ake ƙira da Firoj ɗan gidan Ministan garin ba abinda yake sai dariya, haka yake ɗaga murya shima yana faɗin "wannan ba sabon abu bane a wurin Firoj, ƙananun yara ya irin shekarun ta sun fi dubu waɗanda nayi wa fyaɗe, wasu sun mutu wasu sun warke wasu suna kwance ba lafiya duk na sa ni........" Kafin Firoj ya rufe baki har Tasleem ta zuciyo ta zabga masa mari akan fuskar sa, kafin ya ankara ta riƙe kafaɗunsa biyu tare da ɗago da ƙafarta tayi amfani da gwiwarta da iya ƙarfin ta ta buge masa tsuriya, ba shiri ya durƙusa ƙasi yana ihu tare da riƙe wurin, Tasleem ƙafa tasa ta canki ƙirjinsa ya faɗi ta baya yana kallon sama, kafin ya ɗago ta ɗora ƙafar ta da take sanye da takalmi mai bala'in tudu da tsini ta taka tsuriyar tare da miƙe wa tsaye akan sa, haka take ta tattaka tsuriyar da takalminta ta wurin tsinin. Firoj ba abinda yake sai ihu gaba ɗaya ƙarfin jikin sa ya ƙare sai buga hannayensa yake a ƙasi, Kafin ka ce mai mutane har sun taru masu video kowa yi yake, ana gulmar ɗan gidan Minister, Sai da ta gama lugwigwita masa masarrafai duk babu wanda ya dakatar da ita kafin ta sauƙa akan sa, tana murmushi ta nufi bayan both ɗin motarta ta buɗe ta ɗauki wani sanda na ƙarfe ta koma yanda yake kwance yana birgima, haka ta fara doka masa wannan ƙarfe a duk wurin da tasan zai raunana, da ta samu kan gwiwarsa ta fara kwaɗa masa sai da ta karya masa ƙafa ɗaya sannan ta gurɗa ƙafa ɗaya, ta koma kan hannayensa nan ma sai da ta karya masa hannaye biyu... Nasreen da Asmeen kuka suke suna so su fito su dakatar da Tasleem kar tayi kisan kai amma Amaar ya riƙe su, yaƙi barin su fita, sai roƙon sa suke amma yaƙi bari sai ma key da ya sa a motar gaba ɗaya yanda baza su iya buɗe wa ba, Har cikin zuciyar Amaar so yake sai yaron ya suma domin a faɗar sa bashi da amfani a cikin al'umma, in ma kashe shi tayi a cewar sa babu abinda za'a mata.... Nasreen a tsawace take faɗin "wai kai bakada imani ne? so kake ta kashe shi itama a rataye ta? shin kasan shi ɗin ɗan gidan waye ne? ɗan gidan Minister ne fa, kuma nasan dole sai an kamata...." Amaar cikin ɗaga murya ya furta "Tasleem bazata taɓa kamuwa ba koda kashe shi tayi, ko shugaban ƙasa bai isa kamata ba, a yanzu zan buɗe ku ne kuje ku dakatar da ita saboda kar ta shiga bakin duniya cewa tayi kisan kai, bazan so hakan ba...." Yana kaiwa nan ya buɗe motar sa, da gudu Nasreen da Asmeen suka fice, nufan yanda Tasleem take ta dukan Firoj suka yi domin a halin yanzu ko motsi ya daina yi, baya cikin hayyacin sa amma duk da hakan Tasleem bata daina kwaɗa masa ƙarfen nan ba, duk ta faffasa masa kai.... Nasreen da Asmeen ne suka rirriƙe ta tare da ƙoƙarin jawo ta gefe da ƙyar domin kokuwa suke, Tasleem ba abinda take furtawa illa "ku sake ni na ƙarasa ɗan banza, yau ni zanyi ajalinsa, ku sake ni nace shin kun san abinda ya aikata mun ne?..." Nasreen itama cikin ɗaga murya ta ce "baza mu sake ki ba Tasleem, bakida hankali ne zaki yi kisan kai..." A tsawace Tasleem ta furta "banida hankali Indai akan marayun yara ne..." tare da yin wurgi da Nasreen har sai da tayi dungure sau uku sai gata a gaban Amaar wanda fitowar sa kenan a cikin motar sa, A fusace ta juyar da ƙwayar idanuwanta kan Asmeen wacce ta gama tsorata da irin fusatar da Tasleem tayi har tayi wurgi da Nasreen, ba shiri kuwa ta yi baya da gudu... Amaar hannu yasa ya ɗago da Nasreen har goshin ta ya fashe sai jinin dake zuba, Tasleem kallace-kallace take tana neman abun da zata ƙara sa Firoj domin ƙarfen hannun ta duk ya lanƙwashe, idonuwanta ne suka sauƙa akan AMAAR, ta ɗau tsawon seconni tana kallon wurin da Amaar yake, sai dai abun mamaki ba Amaar ɗin take kallo ba, bindigar dake sokare a aljihun wandon sa take kallo, tana tunanin yanda zata je ta ciro shi, Kafin a ankara har ta tafi da gudu ta ciro bindigar, kafin Amaar ya ankara har ta kunna kunamar bindigar ta sai ta Firoj, Nasreen da Asmeen ihu suka fara yi suna bata haƙuri akan ta dakata, Amaar wani irin sufa ya yi tare da riƙo hannun ta ya ɗaga sama dai-dai lokacin ta danna kunamar bindigar sai ga bullet ya fita yayi sama, ga shocking ɗin da yabi jikin su wani irin ihu Tasleem tayi sai da suka ɗagu sama suka doku a ƙasi, bindigar hannun ta ya cillu gefe guda... Tasleem cikin ƙarfin hali ta ɗago da kanta tana ƙoƙarin juya bayanta tana son ganin wanda ya riƙe ta har wannan shocking ya same ta, kafin ta juya kuwa Amaar yayi saurin tashi jiki na ɓari ya ɓuya a bayan mota, Dafe goshin sa yayi domin ba ƙaramin juyawa ƙwaƙwalwar sa ke yi ba, Asmeen da gudu ta nufi yanda yake tana faɗin "Ya Amaar kana lafiya, zan iya taimaka maka?..." Itama Tasleem tunanin ta ne ya fara gushe wa, ƙwaƙwalwar ta na juyawa, wani irin sauti ta fara ji ana faɗin "Tasleem ki taimake ni, kar momynki ta kashe ni, Tasleem dan Allah, Tasleem ki taimake ni...." a cikin kwakwalwar take jin waɗannan sautin, itama dafe kanta tayi tana birgima.. Nasreen ganin ciwon Tasleem yana shirin tashi yasa ta tafi wurin da take kwance da gudu tana ƙiran sunanta, Dai-dai lokacin da motar Minister ta iso da wasu motoci na sojoji da polisawa sai jiniya ne yake ta tashi. Ta ɓangare guda itama Madam Nablah ta zo da motocin security ta......... NEXT....... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 13 to 14 Minister yana sauƙa da gudun gaske ya nufi yanda yaron sa yake a kwance shame-shame, kafin ka ce mai sai ga Ambulance an zo ɗaukan sa, Madam Nablah wacce fitowar ta kenan daga cikin mota idanuwanta suka sauƙa akan Tasleem wacce take ta birgima tana riƙe da kanta sai sambatu take wanda ba'a jin abinda take faɗi, Madam Nablah ganin ƙwaƙwalwar Tasleem ne yake shirin motsawa ne yasa gaba ɗaya hankalin ta tashi, yanzu ba'a gida suke ba balle tayi mata abinda ta saba idan ciwon ya motsa, a yanzu nuna tsafin ta zai bada matsala, babu wanda yasan ita matsafiya ce still ga yaran ta a wurin, tana cikin tunanin yanda zata yi ba zato ba tsammani taji dirarren murya ya sauƙa akan dodon kunnen ta, Minister ne yake zazzaro idanu cikin fushi yake faɗin "Nablah kun wuce gona da ƙiri, shin ɗiyar ki tasan wa ta taɓa kuwa? to ki sanar mata cewa ta taɓo masifa da bala'i akan ta sai tayi nadamar tozarta Firoj da tayi...." Madam Nablah idonta akan Minister tana sakin murmushi cikin izzah ta ce "Hmmm! Minister kenan tabbas nasan yaron wa Tasleem ta taɓa amma ina so ka sani cewa ita ma Tasleem ƴa ce ga babban mutum wanda duniya ta san shi, idan ka manta zan tuna maka, iya ɗin ɗiya ce ga Governor wannan ƙayataccen garin da muke ciki, sannan mahaifiyar ta Madam Nablah wato ni ba ƙaramar mata ba ce da za'a taɓa mun ƴaƴa nayi shuru na ƙyale...." Minister ya ce "maganar banza! kina maganar ƴar governor shi da ya juma da barin muƙamin? shekara nawa da shafe shafinsa, a bayan sa govenoni nawa aka yi? to bari kiji wallahi tallahi sai na ɗau hukunci akan wannan al'amarin, zan sa a ɗaure ɗiyar ki a gidan yari har sai yarona ya samu isasshen lafiya..." Madam Nablah ta ce "Idan kuma ya mutu fa?..." A fusace Minister ya ce "itama dole zata mutum, sai ta girbi abinda ta shuka..." Madam Nablah ta ce "okay fatan nasara..." Daga nan Minister da mutanen sa suka tafi kai tsaye hospital suka nufa yanda aka kai Firoj... Madam Nablah kallon Nasreen ta yi sannan ta ce "ku kai mun ita cikin mota..." Nasreen da Asmeen ne suka yi ƙoƙarin ɗago ta suka nufi cikin mota da Tasleem, Shi kuwa Amaar tinda idanuwansa suka sauƙa akan Madam Nablah ya nemi wuri ya ɓuya amma idonsa yana kanta, ya gagara manta wannan kamannin tin shekarun baya... Madam Nablah shiga motar ta tayi ga Tasleem a back seat a kwance, da gudu Madam Nablah ta ja mota ta bar wurin sai security ta da suka bi ta a baya, Nasreen da Asmeen su ma motar su suka shiga zasu bi bayan su, cike da damuwa suka ja motar suka bar wurin, Amaar dake tsaye gaba ɗaya fuskar sa ta jagalgale ba alamun annuri a fuskar sa, tsananin damuwa ne a kwance a fuskar sa, yana kukan zucin abubuwa da yawa na farko ya rasa mahaifinsa wanda bai san meya faru da shi ba, a cewar mutane da yayi tambaya sun sanar masa cewa mahaifinsa ya daɗe da rasuwa, amma ba'a san mai ya kashe shi ba, Sannan ga damuwar rashin Ɗan uwansa Abeesh duk da ya ji labarin yana gidan Madam Nablah amma shi ko kaɗan baya ƙaunar zuwa gidan, saboda baya son kowa ya gane shi a yanzu sai ya gama binciken sa akan Madam Nablah... Shima motar sa ya shige tare da nufan yanda ya miƙa, abinda ya ra ya a ransa shine zai je can tsohon gidan su, wato gidan mahaifinsa wanda tin lokacin da aka rasa shi gidan yake kulle babu mai shigar sa... Madam Nablah su na isa gida tasa security ɗaya ya ɗauki Tasleem tare da bashi Umarnin ya kaita can part ɗin ta, itama ta bi bayan su, Nasreen da Asmeen bayan sun iso a falo suka zauna kowa da damuwa akan fuskar ta, su na cikin wannan halin su ka fara jin ringing ɗin telephone dake ajiye akan table ɗin falo, hakan na nufin ana ƙiran mutanen gidan ne, kowa zai iya ɗaukan ƙira ko a cikin ƴan aikin gidan ma, Nasreen idonta akan Telephone amma ta kasa motsawa tsabar jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Asmeen ce tayi ƙarfin ɗaukan wayar tare da karawa a kunne, tana faɗin "hello wa kake nema a cikin mutanen gidan?..." Ta cikin wayar ta ji an furta "Asmeen, Asmeen nake nema..." Cike da mamaki Asmeen ta ce "waye kai ɗin?..." Shima ya ce "ke ɗin wacece?..." Asmeen ta ce "naji ka ƙira sunana shin meke tafe da kai?..." Daga cikin wayar ta ji an furta "kin tafi kin barni da yunwa, uban wa zai yi feeding ɗina?..." Gaban Asmeen ce ya yi matuƙar bugawa da ƙarfin gaske jin Shaprees ne, A ruɗe ta ce "kayi hakuri gani nan zuwa, Allah ya huci zuciyar ka..." Tana kaiwa nan ta ajiye wayar cikin damuwa ta miƙe tana goge hawaye ta fice daga falon, kai tsaye part ɗin Shaprees ta nufa... Ita kuwa Nasreen kanta ta kwantar akan sopar kujera, da haka har bacci ɓarawo ya ɗauke ta a wurin, Bayan wasu mintina sai ga Abeesh ya dawo daga wurin aiki, har zai wuce idonsa ya sauƙa akan Nasreen dake ta shan bacci, murmushi ya sau domin ya gane cewa Nasreen ce, zuwa yayi gabanta ya durƙusa yana ƙare ta da kallo daga bisani ya ajiye jakar hannun sa akan kujera sannan yasa hannu ya ɗauke ta, kai tsaye upstairs ya haura ya nufi part ɗin su da ita, yana zuwa ya kwantar da ita akan gado sannan ya tofa mata addu'o'i ya fice a ɗakin yana sakin murmushi shi kaɗai.... Tasleem ce kwance akan gadon Madam Nablah an gama tsafe ta, an juyar mata da tunanin da yake shirin dawo mata, daga nan bacci ya ɗauke ta... Amaar gidan da ya shiga ainahin gidan su kenan, gidan ya yi kaca-kaca kamar gidan bola tsawon shekaru Ashirin babu mutum ɗan Adam da ya ƙara zama a cikin gidan, yana shiga falo ya tarar da ƙaton photon su tin suna yara shi da Abeesh da Mahaifinsu a tsakiyar su yana rungume da su, photon duk yayi ƙura sai da yasa hannu ya share ƙurar tukun photon ya ɗan haske, ga photon mahaifiyar su, komai na falon yana nan ba'a taɓa komai ba sai dattin da suka yi, ga kujeru da plasman da frig da su dinning table, yana kallace-kallace har ya wuce can bedroom ɗinsa lokacin da yake yaro, wasu abubuwan sa na wasa ne gasu nan da kayayyakin sa, ɗauko jakarsa yayi ya buɗe wasu photunan sa ne a lokacin baya, har da photonsa da Tasleem su biyu da kuma wanda sukayi shi da triplets gaba ɗaya su ukun, da photon sa da Abeesh, ɗaukan photunan yayi zai tafi da su, bayan ya gaba da room ɗin sa ne ya koma falo daga nan ya wuce ɗakin Mahaifinsu, yana shiga hawaye suka fara yanko masa domin ba ƙaramin kewar mahaifinsa yake ba, nan ma ya ɗauki abubuwa masu mahimmanci daga baya ya fice, ya bar gidan gaba ɗaya.... Bayan kwana biyu Da misalin ƙarfe goma na dare Madam Nablah tana zaune a kujerar falo tana kurɓar coffee idonta akan plasman tana kallon labarai, Nasreen ce ta sauƙo falo daga upstairs da sallama a bakin ta, ganin Madam Nablah bata amsa sallamar ba yasa ta ƙara maimaita wa still bata amsa mata ba, Nasreen ƙara maimaita sallamar zata Madam Nablah ta katse ta da cewa "Oh my god! wannan wani irin naci ne haka, idan kika yi sallama sau ɗaya ai sai ki haƙura tinda ni ba kurmiya bace..." Nasreen ta ce "sorry Mom na ɗauka baki ji bane..." Zama tayi itama idonta akan Madam Nablah ta kuma cewa "Mom yau kwana biyu ban ga Tasleem ta fito daga ɗakin ki ba, shin bata farfaɗo bane har yanzu?..." Madam Nablah ta ce "Nima jiran farfaɗowarta nake, har yanzu bata farfaɗo ba..." Nasreen ta ce "subhanallahi amma bata ɗauka irin wannan long time bata farfaɗo ba ai..." Madam Nablah ta ce "Nima ban san dalili ba..." Nasreen ta ce "but meyasa Tasleem take shiga wannan halin, nasan akwai silar faruwar haka..." Madam Nablah ta ce "Nasreen ki je ki kwanta dare yayi, bana son irin wadannan tambayoyi...." Nasreen ba yanda ta iya haka ta tashi ta bar falon... Itama Madam Nablah haurawa upstairs tayi zata koma room ɗin ta. Tasleem tana kwance idanuwanta a buɗe tana kallon saman ceiling, ta daɗe da farfaɗowa amma sai dai bata nuna wa uwar cewa ta dawo hayyacinta ba, saboda wasu abubuwa da taga uwar tana yi cikin dare, sannan takan yi wasu tsafinta akan Tasleem ba tare da tasan ta farfaɗo ba, abun ya yi matuƙar ɗaure wa Tasleem kai, tana tunanin duk waɗannan abubuwan na meye su, sannan tana tunanin kar mafarkin ta ya zamo gaskiya, tana so ta tabbatar da gaskiyar mafarkin ta ne yasa bata nuna ta farfaɗo ba saboda tasan mommy bazata bar ta a ɗakin ta ba, Tana cikin wannan tunanin ta fara jin motsin mutum da sauri ta rufe idanuwanta, ta ɗage motsin ta kamar gawa, Madam Nablah tana shigowa ta nufi yanda Tasleem take a kwance, zama tayi a bakin gado idonta akan ta shafa sumar kanta tayi sannan ta ɗora hannunta akan saitin wuyanta tana son tabbatar da ko ta farfaɗo, Tasleem ɗage numfashin ta tayi har na tsawon seconni daga baya Madam Nablah ta ɗage hannunta akan wuyan ta, dalilin da yasa ta ajiye Tasleem a room ɗinta tana gudun kar a cikin sumar ta bayyanar da duk wani sirrin da yake ranta, domin taji tana wasu sambatu, Madam Nablah tsaya wa tayi a tsakiyar room ɗin ta tayi wani irin juyi a hankali ta sauya kayan jikin ta suka koma launin baƙaƙe na zuwa Devil would domin akwai meeting ɗin da zasu gudanar, gashin kanta ya warwatse zuwa gadon bayan ta, miƙar da tafin hannunta tayi sai ga hular tsafi na sarauta ya bayyano akan tafin hannunta, ta ɗora akan ta sai sheƙi yaƙe dake da zinare aka yi shi..... Waɗannan abubuwa duk akan idon Tasleem suka faru, ba ƙaramin tsorita tayi ba amma bata nuna hakan ba ko motsi bata yi ba, akan idonta Madam Nablah ta je ta tsaya a gaban ƙaton photon mahaifinsu tare da furta wasu kalmomi sai ga photon ya rabe gida biyu tasa hannu ta buɗe ɓoyayyen ƙofar ta shige, tana shiga ƙofar ta rufu sannan photon ya haɗe... Tasleem a zabure ta miƙe tare da nufan wurin da sauri, itama tsayawa tayi ta gwada furta kalmar da Madam Nablah ta furta sai ga photon ya ƙara rabewa biyu sannan ƙofar ta buɗu itama ta shige ciki... wani irin duhu ne a ciki bata iya ganin gabanta sai hasken hular kan Madam Nablah da yake ta haska mata hanyar wuce wa, har ta ɗan nisa, itama Tasleem da sauri take bin wannan haske take bin bayan ta har sai da suka yi tafiya mai nisan gasken Tasleem taga Madam Nablah ta tsaya cakk, cikin tsoro da fargaba ta durƙusa ƙasi tare da laɓewa kar ta juyo ta kalle ta, Tasleem gani tayi Madam Nablah ta tsuguna itama tare da sa hannu ta buɗe wani murfi dake ƙasi kamar ramin rijiya, tana buɗe wa ta miƙe tare da shige wa ciki tana taka matakalar benin da zai kaita ƙasin gida. Tana shige wa sai ga Tasleem ta taso itama ta nufi wurin tana zuwa itama ta shige ramin, haka take taka wa a hankali domin idan baka yi a hankali ba zaka iya gangarawa ciki, ganin a tsaye zata iya faɗuwa ne yasa ta zauna akan matakalan take ja da mazaunanta a hankali da haka ta isa ciki, bata ƙarasa shige wa ba taga Madam Nablah a tsaye a gaban wani mutumi yana ɗaɗɗaure da kaca akan kujera, fuska a rufe da baƙar hula, dake Madam Nablah tana shiga ta kunna hasken wurin hakan yasa Tasleem take iya ganin komai, Madam Nablah ce tasa hannu ta buɗe masa fuska, Ta ce "sannun ka da hutawa Abul Abeesh..." Tasleem zaro ido tayi waje jin an furta Abul Abeesh, idonta akan mutumin sai dai bazata iya gane shi ba domin tin suna yara ƙanana aka ɗauke shi, yanzu kuwa fuskar sa duk ya cika da gashin gemu, ga furfurar azaba da ya cika masa kan sa, a hankali Tasleem ta maimaita "Abul Abeesh" a cikin ranta. Abul Abeesh murya na kakkarwa ya ce "ina roƙon Allah da kada ya ɗauki rayuwata har sai na ga ƙarshen zalunci ki Nablah, ko kaɗa bakida imani, yanzu da me kika zo mun..." Madam Nablah ta ce "duk abinda zanyi sai na zo na sanar maka, kuma babu wanda ya isa ya dakatar da ni akan haka, yanzu nazo ne na sanar maka cewa zanyi sadaukarwa..." Murmushi Abul Abeesh ya yi sannan ya ce "a shekarun baya kin sadaukar da jinin abu mafi muhimmanci a rayuwar ki wato jinin mijinki uban ƴaƴan ki..." Ƙirjin Tasleem ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske, a razane ta ɗauke numfashin ta jin abinda kunnuwanta suka jiyo mata, haka ta ƙara jajirce wurin control kan ta, ta cigaba da saurorin mutumin da ake ƙira da Abul Abeesh... "A shekarun baya babban yarona yayan Abeesh nasan ke kika salwartar masa da rayuwa ta hanyar sadaukar wa...." Madam Nablah ta ce "kar ka sako wannan yaron a lissafi na domin jinin sa bai mun amfanin komai ba..." Abul Abeesh ya ce "Ma sha Allah! Jinin sa bazai taɓa miki amfanin komai ba kuwa har abada..." Madam Nablah ta ce "hakan na nufin yana raye?..." Abul Abeesh ya ce "hakan na nufin jininsa ya fi ƙarfin ki kamar yanda jinin Abeesh ya fi ƙarfin ki..." Madam Nablah cikin izzah ta tintsire da wata iriyar dariya. Abul Abeesh ya ce "yanzu shin wa ye zaki sadaukar a cikin ahalin ki?..." Ta ce "abu mafi muhimmanci a gare ni..." Abul Abeesh ya ce "ɗaya daga cikin ƴan ukun ki..." Ta ce "tabbas wacce ta gagare ni, ita zan sadaukar, biyun kuma zan Aurar da su..." Abul Abeesh ya ce "kina nufin kice Tasleema?..." Ta ce "tabbas..." Murmushi ya yi sannan ya ce "kiji tsoron Allah Nablah, ƴar cikin ki ma bazaki bar ta ba? to ina miki albishir da cewa Tasleema gagarau ce, tanada baiwar da babu yanda zakiyi da ita, jininta guba ce a gare ki..." Madam Nablah ta ce "banida lokacin sauraronka, inada meeting da zan gudanar a Devil's World, idan na kammala zan dawo ta nan..." Hular da ɗauka tare da rufe masa fuska, sannan ta kashe hasken wurin ba tare da ta haura ba ta ɓace ɓatt... Tasleema har ta saddaƙar da cewa Mommynta ta kama ta domin a halin yanzu bata da ƙarfin jikin da zata haura zama ta fita daga cikin wannan kogon, ganin duhu ya biyo baya kuma babu motsin kowa yasa ta ƙara sa sauƙowa, jiki ba ƙwari ta lalumi yanda hasken yake ta kunna, idonta akan Abul Abeesh dake rufe da hula, a hankali ta taka wurin da yake a zaune tasa hannu ta buɗe masa fuska, A hankali ya ɗago da kansa idonsa ya sauƙar kan Tasleema wacce take tsaye itama idonta akan sa, a hankali ta durƙusa a gabansa hawaye ne yake ta gangaro mata cikin kakkarwar murya ta furta "waye kai?..." Abul Abeesh cikin mamaki ya furta "tsawon shekara da shekaru babu wanda ya taɓa shigo wa nan sai iya mai mallakin wurin, yau an wayi gari wata ta shigo ba tare da sanin shugabar wurin ba, shin bakya tsoron abinda zai faru dake idan aka gano ki?...." Tasleem tana kuka ta ce "kana nufin kace kai ne mahaifin Abeesh? daman kana raye baka mutu ba?..." Abul Abeesh ya ce "na mutu a idon mutane amma a zahiri ina nan tsawon shekara ashirin..." Tasleem ta ce "mahaifiya ta ba ƙaramar munguwar azzaluma ba ce, naji na tsane ta sosai, idan ina ganin wasu abubuwa a cikin mafarki na ban ɗauka da gaske ba sai yanzu dana tabbatar, banaso na zauna a wurinta saboda na kan ji tana ƙarnin jini, nakan ji zuciyata tana bugawa da zaran na zauna kusa da mungu..." Abul Abeesh ya ce "hakan yasa take so ta sadaukar da ke, amma ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru dake..." Tasleem ta ce "Allah ne ya kawo ƙarshen kuɓutar ka shiyasa ya kawo ni har yanda kake..." Abul Abeesh ya ce "a'a ki bar ni a yanda kika ganni, tinda har Allah ya nuna miki a yanda nake kuma kinsan ina raye wannan ma abun a gode masa ne..." Tasleem jinjina kai tayi sannan ta ce "zan sanar cewa kana raye, Abeesh zai yi farin ciki sosai..." Abul Abeesh ya ce "kar kiyi kuskuren tafka wannan babban kuskure, idan kika yi haka zakiyi sanadiyar mutuwar ki ne da kuma na ɗana Abeesh, alfarmar da zakiyi mun sannan ki ci moruwar ƙwaƙwalwar ki shine ki nuna baki san komai game da mahaifiyar ki ba, kar ki nuna mata cewa kinsan komai akan ta, kinsan ita matsafiya ce, kar kiyi garajen sanar wa wani cewa ina raye, ki zauna a yanda kike, kar ki nuna wa mahaifiyar ki sauyi domin tanada matuƙar wayo, lokaci guda zata iya gano ki...." Tasleem ta ce "shikenam nima banason wasan ya fara daga yanzu..." Abul Abeesh ya ce "ki tafi Tasleem, mahaifiyar ki zata iya ankara yanzu..." Tasleem a ruɗe take faɗin "shikenam! shikenam!! zan tafi..." Juyawa tayi ta fara haurawa sama da gudu, tana fita daga ramin ta miƙi yanda da ta zo da gudu duk da duhu ne wurin amma tasan ina ta dosa, tana zuwa bakin ƙofa ta samu a ƙarƙame, ta yi ƙoƙarin buɗewa amma ta kasa, tayi tayi amma ƙofa ko motsi, haka take ta bubbuga ƙofa ko ƙara baya yi ga duhu, tana wannan yanayin har lokaci ya ja, domin yanzu ƙarfe 2 zata yi, Tasleem tana zaune a bakin ƙofa har ta gaji da bugawa, can wani tunani ne ya faɗo mata, lokaci guda ta tuno ta kalmar da mommynta ta furta kafin ƙofar ta buɗu, a zabure ta tashi tare da rufe idanuwanta ta furta wannan kalmar sai ga ƙofa ta buɗe, da gudu ta fice, tana fita ƙofar ta rufe kanta, sauƙe numfashi ta ke sosai na gajiyar da ta sha, sai da ta nutsu tukun hankalinta ya daidaita sannan ta nufi wani wardrobe wanda Madam Nablah take yawan zuwa wurin domin gudanar da wasu tsafin ta, hannu tasa zata buɗe taga a rufe, haka take jan murfin wardrobe amma ta kasa buɗe wa, ƙananun drowowi ta fara buɗe wa tana neman key ɗin wardrobe wanda ya fita daban a cikin sauran wardrobe ɗin ɗakin, wannan kana ganin kasan abubuwa masu mahimmancin gaske ne a ciki domin na darma ne wanda key ɗin sa daban yake, ta gwaggwada key ɗin da ta samu da dama amma yaƙi buɗuwa, jefar da sauran key ɗin tayi ta kama hannayen wardrobe da ƙarfin gaske ta fara ja domin a jikin bango yake a manne bazai iya faɗowa ba, tana cikin ja hannunta ta caku da ƙarfen jikin wardrobe nan danan sai ga jini, a zabure ta sau hannun wardrobe tana yarfe hannun domin ba ƙaramin zogi yake mata ba, jinin da ya zuba daga hannunta ne ya ratsa jikin wardrobe wanda sirrin buɗe ta sai da jini, bazai taɓa buɗuwa ba sai an yanke hannu da jini a jikin wardrobe ɗin, hakan ma sai da jinin mai wardrobe ɗin kuma jinin Madam Nablah yazo daidai dana Tasleem hakan yasa wardrobe ɗin ya karɓi jinin, lokaci guda ya fara ƙoƙarin buɗuwa da kansa.... Madam Nablah tana can Devil's World tare da mutanen ta a ciki har da Shaprees suna gudanar da meeting, lokaci guda Madam Nablah taji kanta ya sara mata, idanuwanta suka juye zuwa ja, babu komai a cikin idanun illa zallar jini, da sauri ta buɗe tafin hannunta tare da ɗago da hannun sai ga video ya bayyana akan tafin hannunta gani tayi an buɗe mata secret wardrobe ɗin ta, a zabure ta buɗe manya-manyan idanuwanta waje waɗanda suke cike da jini, idanuwan sun koma zallar jan jini babu ɗigon baƙi ko fari amma bata ga wanda ya buɗe ba, iya cikin wardrobe aka nuno mata wanda ba ita ta buɗe ba.... Kallon mutanen ta tayi sannan ta ce "mun tashi wannan taron domin akwai matsala a yanda nake.... Tasleem ganin abubuwan da suke cikin wardrobe ɗin ne ya ƙara firgitar da ita, abubuwan tsafi ne har da ƴar tsana kusan guda uku, da namijin ɗan tsana an caka masa wuƙa, sai wannan kuma an ɗaure masa kai da igiya, abubuwa na ban tsoro gasu nan kaca kaca, sai wasu kwalabai da suke ɗauke da ruhinan mutane a ciki, Tasleem gani tayi wasu ƙananun halitta sai motsi suke tayi a cikin kwalba kuma kamar mutane amma ƙananu ne sosai domin a cikin kwalba suke, Tasleem ba ƙaramin razana tayi ba ganin abubuwan nan, bata ankara ba taji kukan kuliya ata bayanta, a ruɗe ta juyo baya ganin kuliyar baƙa ƙirin sai jajayen idanuwa ga ta ƙatuwa sai jowa kanta take, a zabure Tasleem tabi ta gefenta da gudun gaske tana ihu, kuliyar nan haka take sufa tana yowa kanta, duk yanda Tasleem tayi sai kuliyar ta bita, haka suka yi kaca-kaca da ɗakin har tayi nasarar buɗe ɗaki ta fice, nan ma haka kuliyar ta bita, Tasleem ta nufi kitchen itama kuliyar ta bi bayan ta, a ruɗe Tasleem ta ɗauki muciya ta buga wa kuliyar a goshin ta, haka ta fara kwaɗa mata, da taga muciyar bazai mata ba ta lalumo wuƙa ta saita kuliyar ta wurga mata daidai lokacin da kuliyar ta ɓace ɓatt, Tasleem cikin tsoro da firgici haka take sakin numfashi daƙer, da gudu ta fice daga kitchen ta nufi part ɗin su da gudu, tana zuwa ta buɗe ɗaki ta shige tare da rufe wa tasa key tana sakin numfashi na azaba ga yanda gumi ya wanke mata duk ilahirin jikinta, tsayawa tayi tana bin ƴan uwanta da kallo sai shan baccin su suke kowa da gadon sa, toilet ta shige ta watsa ruwa a jikinta sannan ta ɗauro alwala tazo ta tsayar da Sallar lafula, daga wannan lokacin har sallar asuba bata rumtsa ba...... Next Next Next New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 15 to 16 Bayan an ƙira sallar asuba Nasreen ce ta fara buɗe idonta, ganin haske dadau-dadau ne yasa ta buɗe idon gaba ɗaya tare da tashi zaune tana jero addu'o'i, kallon yanda Asmeen take a kwance tayi taga sai sharar baccin ta take, mamaki ne ya mamaye fuskar ta ganin an kunna hasken ɗaki kuma kafin su kwanta sun kashe, za mo wa tayi daga kan gadon zata sauƙa idon ta ya sauƙa akan Tasleem dake zaune akan sallaya, a zabure ta furta "Tasleem..." Tasleem tana zaune ta haɗe kai da gwiwa sai sharar kuka take tayi, a tsorace Nasreen ta rarrafa kan sallayar tare da rungumar ta tana faɗin "lafiya kuwa Tasleem, meya same ki kike kuka haka? yaushe kika shigo ɗakin?..." Tasleem gaba ɗaya jikin ta ba ƙwari haka ta kwantar da kanta akan Nasreen tana kuka ba bakin magana... Gaba ɗaya hankalin Nasreen ba ƙaramin tashi ya yi ba, suna cikin wannan halin itama Asmeen ta farka, duk taruwa suka yi akan Tasleem su na share mata hawaye tare da rarrashin ta, Asmeen ta ce "ina tunanin ita da Mommy ne kinsan basa shiri..." Tasleem ta ɗora kanta akan cinyar Nasreen ta ce "Mommy bata mun komai ba.. " Nasreen ta ce "to meyasa kike kuka domin nasan haka kawai babu abinda zai sanya ki kuka..." Asmeen ta ce "tabbas domin sai abu ya kai abu kike kuka, bakya kuka akan ƙaramin matsala, shin me ya sa kika baro ɗakin mommy cikin dare?..." Nasreen ta ce "kema dai Asmeen kin san Indai ta farfaɗo kam baza ta barta ta zauna mata a ɗaki ba, tin muna yara ƙanana mommy bata barin mu mu shiga mata ɗaki, yanzu haka ni ban san ya kalar ɗakin Mommy yake ba, ban taɓa shiga ba..." Asmeen ta ce "nima ban taɓa shiga ba kuma itama Tasleem wannan ne karo na farko da ta shiga ɗakin mommy, ni nayi mamakin yanda mommy zata bar mutum har tsawon kwana uku a ɗakin ta, ni da na sani ai dana baki wayata kin yi mun video ɗakin Mom..." Nasreen murmushi tayi tare da faɗin "ke fa kinada matsala..." Tasleem abubuwa da yawa ne suke yawo mata a ƙwaƙwalwar ta, tana tunanin Abu Abeesh a yanayin yanda ta gan shi, sannan kayan tsafe-tsafen da ta gani a wardrobe ɗin momy wanda sai da jini yake buɗuwa, na uku shine baƙar kuliyar da ta gani amma wannan ba abun tashin hankali bane a wurin ta domin tasan mommynta ne tinda zaman ta a ɗakinta ta ga ta koma har macijiya sannan ta koma tsuntsuwa, duk da hakan bai sa tayi razanar da za'a gane ta farfaɗo ba, amma abinda ya fi ɗaga ma ta hankali shine jin itace tayi silar mutuwar Mahaifinsu, lokaci guda kuka ya ƙara yanko mata... Cikin nuna damuwa Nasreen take faɗin "Haba Tasleem meyasa bakya jin rarrashi ne? ban saba ganin kina yawan kuka haka ba sai yau....". Tasleem cikin kuka ta furta "Daddy..." Asmeen ta ce "Daddy kuma?..." Nasreen cike da mamaki ta ce "yau ɗin kewar Daddy ne ya motsa ?..." Daƙer suka samu nasarar rarrashin ta kafin su ma suka yi sallah... Misalin ƙarfe 7 na safe Tasleem da Nasreen tare da Asmeen duk hallaruwa suka yi a falo sunyi shirin makaranta, su na jiran fitowar mommynsu, can sai ga ta tana ɗaure da farin towel akan ƙirjinta, towel ya tsaya mata a iya gwiwa ta fito tana tajar gashin ta da mataji da haka ta fara sauƙo wa down stairs, Asmeen baki ta sake tana kallon mommy ta kasa furta komai, itama Nasreen cike da mamaki take kallon ta a cikin ranta ta furta "yau kuma Mommy, fitowa falo da ɗaurin ƙirji da ƙaramin towel?..." Tasleem tana zaune haka take bin Mommy da kallo tin daga ƙasin ƙafarta wanda ko takalmi babu har saman ta, a tsakiyar falo Madam Nablah ta tsaya Tare da cigaba da tajar sumar gashin ta wanda yake har gadon baya ga shi baƙi ƙirin, jikin ta kuwa kamar na budurwar robot fari tass, ƙafar ta ko takalmi babu, bayan ta kammala tajar gashin kanta tsayawa tayi tana bin yaran da kallo ɗaya bayan ɗaya fuska ba annuri, ga goshinta wuri guda yayi jawur alamun ciwo taji a wurin, Asmeen idonta akan Madam Nablah ta ce "good morning Mom, meya sameki akan goshi ?..." Nasreen ta ce "yau kuma ya kika fito haka? kuma alama daga wanka kika fito..." Murmushi Madam Nablah ta sau idonta akan Tasleem ko sauraron su bata yi ba balle su sa ran zata basu amsa, Tasleem gaba ɗaya ta tsargu da kallon da mommynta take mata, cikin wayince wa ta miƙe tsaye tare da nufan wurin Madam Nablah da murmushi akan fuskar ta ta ce "Mom good morning..." ta furta haka tare da rungumar ta, sannan ta sumbace ta a gefen fuskar ta... Nasreen da Asmeen kallon juna suka yi domin ba ƙaramin mamaki wannan al'amari ya basu ba, ganin Tasleem ta rungumi mommy tare da sumbatar ta. Madam Nablah kallon Tasleem take tana wani irin tunani, maganar zuci take tana faɗin "me hakan yake nufi? kenam Tasleem bata san ko ni wacece ba har yanzu? duk da abinda ta gani a daren jiya?...." tana cikin wannan tunanin Tasleem ta katse ta da cewa "Mom! Mom!! jiya naga kuliya a ɗakin ki, shine dalilin da yasa na gudo room ɗin mu, kuma ban ganki ba, bayan tashi na nayi ta duba ki bakya nan, to nayi tunanin kina toilet ne shiyasa na buɗe wardrobe akan zan ɗauki riga nasa kuma sai na tarar da kayayyakin wasan yara a cikin wardrobe, daga baya sai ga kuliya, na tsorata sosai, Mom inadai kuliyar bata Miki komai ba?..." Tasleem ta ƙarasa basajar ta idonta a cikin na Mom, kuma tasan wannan kuliyar itace domin ga tabon muciyar da ta kwaɗawa kuliyar ya bayyana akan goshin Mom. Madam Nablah cike da mamaki take kallon Tasleem sai yanzu ta tabbatar cewa Tasleem bata san komai ba, itama wayince wa tayi tare da faɗin "kuliya kuma a cikin gidan nan? amma ban ga kuliyar ba shin tana ina?..." Tasleem ta ce "Mom kamar fa ɓace wa tayi..." Nasreen zaro ido waje tayi tare da faɗin "kuliya kuma ta ɓace?..." Madam Nablah ta ce "what? anya kuwa ba mafarki kika yi ba Tasleem?..." Tasleem ta ce "a'a ba mafarki bane..." Asmeen ta ce "gaskiya azo a fitar mana da kuliyar nan, domin bazan iya bacci ba yau ..." Madam Nablah ta ce "shikenam ku tafi makarantar ku, daga baya sai ku nemo wanda zai fitar muku da kuliyar..." Daga nan Madam Nablah ta nemi wuri ta zauna akan kujera tare da ɗaukan kofin shayi tana kurɓa... Nasreen ta ce "Mom yau zamu fara jarabawar gama makaranta a taya mu da addu'a..." Jinjina kai kawai Madam Nablah tayi tana kurɓar shayi..... Gaba ɗaya fita suka yi a tare, Tasleem da tunani ta fita daga gidan, tana tunanin ta yanda zata ɓullo wa wannan al'amarin, tana mai baƙin ciki a halin da ta tsinci mahaifiyar ta kuma tayi alƙawarin kawo karshen wannan al'amarin, har yanzu ta kasa yarda da zuciyar ta cewa mommyn su ce ta kashe Daddyn su... Kamar yanda suka saba kullum ita take driving ɗin su a mota, har sun shiga zata ja motar sai ga Shaprees ya tsaya musu a gaban mota wanda basu san yana wurin ba, zuwa yayi wurin ya tsaya a wurin glass ta ɓangaren Tasleem yanda take jan motar, Nasreen ce ta fara yin magana tare da faɗin "Barka da safiya Ya Shaprees..." Ya ce "yawwa sannun ki mai hankali..." Asmeen gaba ɗaya ba fara'a akan fuskar ta kamar zata yi kuka ta ce "ina kwana meri pati..." Tasleem ta gefen ido ta kalle ta ba tare da ta furta komai ba... Amsa mata ya yi idonsa akan Tasleem, ganin ita bazata iya gaishe shi ba yasa shi faɗin "ke baki iya gaisuwa bane?..." Tasleem ta ce "ban iya ba" a takaice.. Kama kuncin ta ya yi yana murzawa tare da faɗin "ke sakaliya ce ko?..." Tasleem da sauri ta kawar da fuskar ta tana faɗin "You are bastard, jahilin bawa marar tunani, har kai waye da zaka taɓa fuska ta..." Cikin ɓacin rai Shaprees ya buɗe murfin motar tare da ja wo hannun ta ya fito da ita sannan ya rungume ta yana faɗin "Ba ma iya taɓa fuskar ki zanyi ba har rungumar ki nayi, meye zaki yi..." Tasleem da iya ƙarfinta ta fisge kanta daga gare shi a fusace ta zabga masa mari, yana ɗago da kansa ta ƙara zabga masa wani marin tana huci... Nasreen da Asmeen su ma fito wa suka yi suna kallon ikon Allah, gaba ɗaya sun kasa gane meye dalilin faruwar haka.. Tasleem tana huci ta ce "kai baka kai namijin da zaka taɓa jikina ba, ba ka daga cikin tsarin namijin da nake so da alfahari da shi, kuma duk duniyan nan babu shi sai mutum ɗaya...." Madam Nablah wacce take saman upstairs tana kallon duk halin da ake ciki, jin abinda Tasleem ta furta ne yasa ta ƙara saurara ta ji waye mutumin da yake cikin zuciyar ta. Tasleem ta cigaba da cewa "ban san shi ba amma ina jinsa a raina, ban taɓa ganin sa ba amma makauniyar zuciyata tana tare dashi a koda yaushe, banza da kai maciyi Amana, duk wasu saƙonninka da kake turo mun ta wayata kafin na karanta sai na bawa ƴar uwata Asmeen sannan a gaban Nasreen ta karanta mun saƙon da ka turo mun, duk mun san kai ɗin munafiki ne, to ni nafi ƙarfin ka kuma duk wulaƙanci da kake wa Asmeen na sa ni, muna sane da kai amma zanyi maganin ka..." Shapris idonsa ya sauƙar kan Asmeen wacce tin ɗazu sai kuka take ta sha, tana rungume a ƙirjin Nasreen.... Sannan ya kalli Tasleem ya ce "kin mare ni sannan kin zage ni kin wulaƙanta Ni amma ki sa ni taki lafula ne akan nawa, domin ni ɗin wuta ne, zan koya miki hankali, kina maganar ina turo miki saƙonni to ki tambayi mahaifiyar ku na sanar mata cewa zanyi chanji, don haka ke nake so ki zama baiwata..." Murmushi Tasleem ta yi sannan ta ce "lallai za'a bawa kura ajiyar nama kenam, to ka sa ni cewa ni ɗin kura ce wacce zata yi yaga-yaga da naman jikin ka, kuma ni ruwa ce wacce zata yo ambaliya ta kashe wutar dake tsakiyar kan ta, wawa kawai..." Shapris ya buɗe baki zai yi magana kenam Madam Nablah tayi saurin dakatar da shi ta hanyar ƙiran sunansa, duk ɗaga kayuwan su suka yi suna kallon sama, idonta akan Shapris ta ce "mun gama magana ai, meye abun faɗa kuma, na maka alƙawarin duk abinda ka tambaya a wurina zaka same shi don haka na sauya maka kamar yanda ka buƙaci haka, yanzu Tasleem ta zamo mallakin ka...." Tasleem a ruɗe ta furta "what?..." Madam Nablah ta ce "bana son yawan magana ku kama hanya ku tafi makaranta sai kun dawo..." Tasleem buɗan baki tayi zata yi magana Asmeen ta tafo da gudu tare da kama hannun ta tana faɗin "dan Allah Tasleem ki amince, ki taimaka mun inaso daga yau kar na ƙara zuwa ɗakin sa, cutar dani yake Please, kin manta alƙawarin da kika mun?..." Jinjina kai Tasleem tayi sannan tasa hannu tana goge hawayen Asmeen ta ce "mu tafi..." motar su suka shiga a ɗari suka bar gidan... Exam Hall kowa ya hallaru ana rubuta examination, ko wani seat mutum ɗaya ne, Nasreen tana gaban seat ita kaɗai, Tasleem kuma a tsakiyar seat a yayin da Asmeen take can ƙarshen seat, sai sauran mutanen class babu mai motsi a cikin su, kowa abinda yake gaban sa yake, sai security masu zagaye su, wani mutumi ne ya shigo exam hall da sallamar sa tare da gabatar da kansa, shima ya buƙaci bawa student tsaro wurin gudanar da Exam, Nasreen ɗagowa tayi idonta suka sauƙa akan Amaar Junaid a cikin ranta ta furta "Major A.J..." haɗa ido suka yi ya kanne mata ido ɗaya tare da sakin murmushi... Itama murmushi tayi sannan ta cigaba da rubutun ta, Itama Asmeen daga can seat back ganin sa yasa ta washe baki tana ƙoƙarin ɗaga masa hannu, ɗaya daga cikin security ne ya hango ta ya ce "ki maida hankali kafin na kore ki yanzu..." Dasauri Asmeen ta sunkuyar da kanta ƙasi ta cigaba da rubutun ta, Ita kuwa Tasleem ko ɗago wa bata yi ba daman bata san shi ba, tana cikin rubutun ta taji daga gefen ta an furta "ƴan mata zan iya taimaka miki?..." Ɗago wa tayi tana masa wani irin kallo na rashin fahimta, sai gani tayi ya ajiye mata wata takarda akan booklet ɗin ta ya yi gaba, da sauri ta juya tana kallon sa, ganin ta juya bayanta ne yasa wasu security su biyu suka zo wurin da take, suna faɗin "ke a ɗakin exam kike juyawa?..." Ɗaukan takardar gabanta suka yi suna faɗin "whattt! Cheating on an exam..." A tsorace Tasleem ta zazzaro da manyan idanuwanta waje tana faɗin "ni mai zan yi da satar amsa, ku duba note ɗina ba iri ɗaya ba ne..." Kowa juyowa ya yi yana kallon ta, Nasreen itama ba ƙaramin tsorita tayi ba ganin an kama Tasleem. Ɗago ta suka yi tare da ƙoƙarin fitar da ita suna faɗin "kiyi waje bama son ƙara ganin ki a ɗakin jaraba again, kuma sunan ki zai tafi sama, za'ayi reporting ɗin ki as a cheater..." Tasleem haka take kuka tana roƙon su amma sun ƙi haƙura sai ma yaga takardar exam ɗin ta da suka yi, dole tana kuka ta fita, kuma wannan exam shine final na gama school degree, daga baya shima Amaar aka gano babu wanda ya turo shi makarantar nan, kawai aikin kansa yayi har ya shigo class, security sun ɗauka turo shi aka yi, shima waje akayi da shi.... Tasleem zama tayi akan wani dakali tayi tagumi sai hawayen dake zubo mata, gani tayi an miƙo mata white handkerchief, ɗago wa tayi tana kallon wanda ya miƙo mata handkerchief ganin wanda yayi mata sanadiyar exam ɗin ta ne yasa ta miƙe tsaye a zabure tsabar tashin hankalin da ta shiga gaba ɗaya ta ruɗe ta rasa mai zata masa haka ta ɗago da yatsar ta tana nuna shi tare da faɗin "waye kai? daga ina kake? wa ya turo ka wuri na? kazo ka ruguza mun gobe na, shin kana da matsala dani ne? bazan yafe maka ba, ka fita a harƙata...." Amaar gaba ɗaya bai ji daɗin halin da Tasleem ta shiga ba, ji yake zuciyarsa tana masa raɗaɗi, ganin zubar hawayen ta tamkar ana sauya masa tunani ne, jin sautin kukan ta tamkar ana hura masa wuta ne a cikin zuciyar sa, A hankali ya furta "Please...." A tsawace ta daka masa tsawa tana faɗin "ka riƙe Please ɗin ka, babu abinda zaka ce mun, kaima kana ɗaya daga cikin maƙiya na kenan?..." Girgiza kai tayi tare da barin wurin da gudu, Shima bin bayan ta yayi, tana gudu yana binta har ta fice a cikin makarantar ba tare da ta ɗauki mota ba, tana tafiya har ta hau kan titi, bata sani ba har ta je tsakiyar titi sauran kaɗan mota ya buge ta Amaar ya yi saurin riƙo hannun ta ya jawo ta, jin shocking yasa Tasleem rausa ihu ta fizgi hannunta daga nashi tayi saman ƙwalta a ruɗe zata faɗi Amaar ya rungumo ta duk da shocking da yake ratsa shi amma bai bar ta ba saboda tseratar da rayuwar ta, basu san lokacin da suka gangara ƙasin ƙwalta ba yana rungume da ita haka jikin su yake kakkarwa kamar ana jona musu electric, a ruɗe suka rabe da juna kowa ya kama gefen sa, ihun Tasleem ne ya jawo hankalin kowa zuwa kan su, kafin kace mai mutane har an taru, Tasleem kamar mahaukaciya ta miƙe tana sossosa jikinta ji take kamar ana hura mata wuta a jikin ta, ba shiri ta jefar da takalmin ta da gyalen da ta yafa sai gashin kanta da ya baje akan gadon bayan ta haka ta cigaba da gudu akan titi tana ihu, gaba ɗaya babu hankali a tattare da ita, haka kanta yake juyawa ko gabanta bata iya gani... Amaar tinda ya kwanta bai motsa ba yana jin yanda jikinsa yake ta zogin wuta kamar wanda ake hura masa wutar, yana cikin wannan halin sai ga wani mota ya parker a bakin titi, wani soja ne ya nufo yanda yake da gudu... Tasleem tana cikin gudu sai ga motar su Nasreen ta tsaya a gaban ta, da sauri su ma suka yo kanta su ka riƙo ta tare da jan ta cikin mota, nan da nan suka nufi gida.... Bayan sun koma gida Nasreen da Asmeen ne suke riƙe da Tasleem sun saka ta a tsakiya, a falo suka tarar da Madam Nablah da Shaprees, Madam Nablah tana ganin su a wannan halin ta miƙe tsaye a zabure tana faɗin "what's wrong with her?..." Nasreen ta ce "Mom mu dai abinda muka sani shine an kore ta a exam hall sakamakon samun ta da cheating exam amma mun san sharri aka mata, daga nan bamu san komai ba sai ƙiran mu da akayi a waya aka sanar mana cewa tana kan titi tana ihu..." Tasleem yanda kasan mahaukaciya gashin kanta duk ya tawarwatse sai kuka take tayi tana dudduba jikinta tare da faɗin "ji nake wuta yana cin jikina, wuta ne yake ta cin jikina..." Madam Nablah idonta akan Tasleem ita kaɗai tasan mai take kallo, abun mamaki ya bata ganin sihirin wuta a tattare da Tasleem, kuma wutar na tsafin ta, dogon tunani ta shiga yanda akayi tayi wa Tasleem asirin wuta, lokaci guda ta furta "AMAAR..." a cikin ranta domin ta tuna lokacin da tayi musu asirin raba gangar jikin su ta hanyar amfani da shocking na wuta, cikin fargaba take furta "ya akayi yanzu kuma sihirin wutar ya dawo gare ta? wanda sai sun haɗa jiki kafin wutar yayi amfani kuma yanzu bata tunanin Amaar yana raye balle su haɗa.... Madam Nablah dawo hayyacinta tayi daga dogon tunani idonta akan Tasleem ta sanar wa Nasreen cewa "ku wuce da ita can ɗakin ku...." Haka suka wuce tare da haura upstairs..... Tasleem zama tayi a akan gadonta tana faɗin "zogi nake ji, wuta ne fa yake ta cin jikina, waye shi ɗin? daga ina yake?..." Nasreen addu'o'i take ta tofa mata ko zogin zai ragu mata, suna cikin wannan halin sai ga Madam Nablah ta shigo tana riƙe da wani glass cup, zama tayi a kusa da Tasleem tare da miƙa mata cup ɗin ta ce "kar ɓi ki sha, zaki daina jin ƙunar wutan..." Tasleem karɓa tayi takai bakin ta zata sha, ta tuno da kalar tsafin da Mommyn ta take yi, tana tsoron kar ta mata tsafi a cikin ruwan, a ruɗe ta ɗago kanta ba tare da tasha ruwan ba, ta miƙa wa Madam Nablah cup ɗin ta tashi da gudu ta shige toilet, tana shiga ta kunna shower a kanta, haka ruwa yake ta zuba, ta ɗau tsawon minti 15 a cikin ruwan, fuskar Amaar ne yake ta mata gizo, ta kasa daina tambayar zuciyar ta waye shi ɗin? daga ina yake?...." *NEXT NEXT NEXT.....* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 17 to 18 Tasleem sai da ta watsa ruwa a jikin ta kafin taji sanyi a ranta... Bayan sati guda da kammala Exam itama Tasleem Mommyn su taje har makarantar tayi magana an dawo da Tasleem ta ƙarasa exam ɗin ta cikin sauƙi... Yau ranar hutu ne duk sun hallaru a falo hatta Abeesh shima a zaune yake a falo yana danna computer sa, Nasreen da Asmeen kuma suna zaune su na kallon plasman, Tasleem kuma tana kan dinning table da cup ɗin Lipton a gaban ta sai pressing phone ɗin ta take, su na cikin wannan yanayin sai suka ji an fara knocking, Asmeen ta bada umarnin shigo wa, turo ƙofa akayi security ya sanar cewa "mai feshin maganin sauro da ƙwari ne ya zo..." Nasreen ta kalli Asmeen ta ce "wa ya turo mai feshi kuma?..." Asmeen kafaɗa ta ɗaga alamar bata saniba itama, suka kalli Tasleem tare da faɗin "Oganniya ke kika turo shi?..." Tasleem sai da ta kurɓi ruwan tea kafin ta basu amsa da cewa "Oganniya tana can room ɗin ta, sai ku je ku tambaye ta..." Security ya ce "Indai babu wanda ya turo shi bari na je na kore shi..." Nasreen ta ce "Ya Abeesh ko kai ka turo shi?..." Abeesh yana zauna ya ce "kin dai san bana shiga shirgin gidan nan..." Nasreen kallon Security tayi sannan ta ce "ka ce ya shigo wata ƙil Mommy ce ta ƙira shi..." Security ya ce "Ok..." sannan ya fice... Bayan wasu mintina sai ga wani matashin mutum ya shigo falon da sallama a bakin sa, duk amsa masa suka yi tare da kallon yanda yake yana sanye da facemark a fuskar sa, kayan jikin sa irin na ƴar feshi yana ɗauke da abun feshi akan kafaɗar sa, Sai ga Madam Nablah itama ta sauƙo daga saman room ɗin ta tana riƙe da key ɗin mota tana son fita unguwa, ganin mutum a tsaye yasa ta tsayawa tana ƙare shi da kallo ta ce "from where?..." Nasreen da Asmeen sun yi mamakin tambayar da mommy tayi masa domin a tunanin su ita ta ƙira shi, Mutumin kuwa yana tsaye zuciyarsa ce take ta faman bugawa domin Madam Nablah ba ƙaramin tsoro ta sanyawa zuciyar sa ba tin yana yaro ƙarami, ƙarfin tsafin da take amfani dashi ya so yafi ƙarfin ƙwaƙwalwar sa, murya ciki-ciki ya ce "am nima turo ni akayi akan nazo nayiwa gidan nan feshin ƙwari..." Madam Nablah ta ce "iya aikin da kake yi kenam?..." Girgiza kai ya yi sannan ya ce "eh a'a ehhh ina gyaran nepa da sauran abubuwa..." Ta ce "okay dalilin da yasa na tambaye ka kenam, daman inaso naji ko kana gyaran wutar nepa inaso zaka gyara mun wutan ɗakunan gidan nan..." Mutumin da yayi covering fuskar sa da face mark ya ce "okay ba damuwa..." Madam Nablah ta kalli yanda Nasreen take zaune ta ce "a ɗakunan gidan nan ina ne wutar ta ɓaci?..." Nasreen ta ce "Mom nepar ɗakin wardrobe ɗin mu ya lalace, sannan na ɗakin Yaya Abeesh nan ma ya lalace sai kitchen, ina tunanin iya su ne...." Madam Nablah kallon mutumin tayi sannan ta ce "yau kayi na feshin gobe kuma sai ka dawo kayi gyaran nepa...." Jinjina kai yayi tare da faɗin "okay Maadam..." Sannan ta miƙi hanyar fita tana faɗin "ku kai shi yanda zai yi aikin feshin, duk wani lungu ya feffeshe wurin..." daga nan tayi ficewar ta. Asmeen ce ta miƙe tana faɗin "muje na nuna maka..." Idonsa kuwa akan Abeesh yanda yake ta daddanna computer, Asmeen tsaya wa tayi a gaban sa tana faɗin "lafiya kuwa? Malam mai feshi ina ta maka magana..." Amaar hannu yasa tare da janye face mark ɗinsa, Asmeen cike da mamaki ta buɗe baki ta ce "Ɗan uwaaaa..." Nasreen jin haka yasa ta ɗago itama ganinsa yasa tayi saurin miƙe wa tana faɗin "laaa kai ne a gidan mu Ɗan uwaa, meya haɗa ka da feshi kuma?..." Da sauri Amaar yayi mata alamar tayi shiru saboda Abeesh yana wurin... Nasreen murmushi tayi tare da faɗin "kar ka damu Ɗan uwa, Ya Abeesh bashi da matsalar komai, kuma baya shiga abinda bai shafe shi ba..." Asmeen tayi saurin cewa "Ɗan uwa wannan shine Yayan mu kuma shine wanda Nasreen zata Aura, ba ruwan sa, shi ɗin salihi ne..." Amaar ya kasa daina sakin ƙayataccen murmushi, idonsa akan Abeesh, Abeesh yana jinsu amma ya kasa ɗagowa, sai gani ya yi an miƙo masa hannu, Abeesh kallon hannun ya yi tare da kai idonsa kan fuskar Amaar sai murmushi yake ta sau masa, shima murmushin yayi tare da miƙa masa hannu suka gaisa. Juyawar da zai yi ya hango Tasleem tana zaune akan kujerar dinning ko kallon yanda suke bata yi ba, nufan yanda take yayi yana zuwa ya ce "hello akwai sauro a yanda kike ne?..." Shiru Tasleem bata bashi amsa ba, tana magana a cikin ranta "lallai wannan ba ƙaramin rainani ya yi ba, haka kawai ina zaune zai wani mun yi bahagon tambaya..." Ba tare da ta bashi amsa ba ta miƙe tana mai jan dogon tsaki zata bar wurin, miƙewar da tayi kwatsam idanuwanta suka sauƙa akan fuskar Amaar, wani irin kallo take masa sama da ƙasa daga bisani tasau murmushi itama tana faɗin "kafin ka kora mun sauron wurin, ka fara wanke dattin jikin ka...." ta ƙarasa maganar tana mai ɗaukan cup ɗin ruwan tea ta ɗaga sama tana tsiyaya masa a tsakiyar kansa, haka ruwan tea yake zubo masa ta fuska har cikin rigar sa, ba abinda ya ji a ransa sai ma ƙara tu sa ta da yayi a cikin zuciyar sa, haka yake ta sakin murmushi a hankali ya furta "ke ɗin ta musamman ce, duk abinda kika yi dai dai ne, kuma fushin ki na ƙara miki kyau sosai da sosai...." Nasreen a cikin ranta take faɗin "tabbas akwai alamar tambaya a tsakanin su..." Asmeen ta ce "Ɗan uwaa daman ƙaunar ƴar uwar mu kake shiyasa a supermarket kake tambayar ta?..." Tasleem fuska a murɗe ta wurga wa Asmeen harara, cikin fushi ta bar wurin, har zata haura saman upstairs taji Amaar ya furta "I love you Tasleem, ina matuƙar ƙaunar ki..." Tasleem tsaya wa tayi tana sauraron sa zuciyar ta ce take ta hargutsuwa, ji tayi bazata iya haƙura ba haka ta juya da gudu ta nufi yanda yake zata shaƙo shi, shi kuwa ganinta yasa ya ware hannayensa biyu tare da faɗin "come and hug me..." Sai da ta zo dab da shi ta ja burki domin ta tuna shi da zaran ta taɓa shi wuta ne yake cin jikin ta, tsaya kallon sa tayi daga bisani ta furta "waye kai?..." Yana murmushi ya ce "I'm your lover..." A tsawace ta ce "shirmen banza, idan baka sanar ko kai waye ba sai na shaƙe ka..." ta kai hannun ta kusan wuyansa kamar zata shaƙe shi ta fasa, girgiza kai tayi tare da juyawa ta nufi upstairs, haurawa tayi ta shige room ɗin su... Amaar kamar zai yi kuka haka yake bin ta da kallo, tsananin tausayinta yake sakamakon abinda ya faru dasu tin basu mallaki hankalin kansu ba. Nasreen ce tayi magana ta ce "Ɗan uwa me yake faruwa ne?..." Murmushi ya yi tare da faɗin "zan miki baya ni da zaran mun nutsu..." Asmeen ta ce "wani bayani zaka yi bayan mun fahimci komai, amma kayi kuskure da ka fara sanar mata kana sonta, da ma ta hannun mu kazo zamu fi jawo maka hankalin ta amma kaga yanzu zata saka ka a jerin maƙiyan ta...." Ya ce "ba komai zan sa ta dawo dani masoyinta na musamman kamar yanda take a cikin zuciya ta..." Asmeen ta ce "ai kuwa idan kayi haka ka cika jarumi na musamman..." Nasreen ta ce "kar ka damu Ɗan uwa ina tare da kai kuma zan taya ka jawo maka hankalin ta..." Amaar murmushi ya yi sannan ya kalli yanda Abeesh yake a zaune ya zuba musu ido yana tunani a ransa cewa "daman saboda masoyiyar sa wannan mutumin ya shigo gidan nan? lallai ya cika jarumi kenam ba mai feshin magani ba ne ?..." Yana cikin wannan tunanin sai gani yayi Amaar ya nufo wurin da yake yana faɗin "Please Boom boy ka taimaka mun kaima wurin shawo mun kanta, ita ɗin rayuwata ce..." Abeesh yamutsa fuskar sa yayi tare da faɗin "who is Boom boy?..." Nasreen hannu tasa ta toshe bakin ta tana ƙoƙarin haɗiye dariyar ta, Asmeen kuwa kwashe wa tayi da dariya tana faɗin "Boom boyyyyy...." Suna cikin rahar su sai ga Tasleem ta sauƙo daga saman upstairs da gudu tana riƙe da ƙaramin bindiga a hannunta, tsayawa tayi ta saita shi tana faɗin "wato ka raina ni koh? har kana da ƙwarin gwiwar shigowa gidan mu ka furta mun soyayya? to yau sai dai a fita da gawar ka domin bazan ƙyale ka ba..." Tana kaiwa nan ta harba bindigar daman already ta kunna kunamar bindigar da sauri Amaar ya sunkuya ƙasi bullet ta wuce ta saman sa sai akan plasman, plasman ne ya dagargaje haka Asmeen ta shige ƙarƙashin dinning tana zunduma ihu, Nasreen kuwa bata san lokacin da tayi tsalle ta faɗa kan Abeesh ba, Abeesh shima rungumar ta ya yi sosai yana tunanin ta yanda bullet zai fara shigan sa domin ba ƙaramin tsorita ya yi ba, itama Nasreen tana rungume dashi sai zabga ihu take tana faɗin "dan Allah azo a taimaka mana, Tasleem ki daina kar tsautsayi yasa ki harbe mu wayyo Allah..." duk toshe kunnuwa suka yi tsabar ƙarar bindiga sai farfasa abubuwan falo ake irin su glass da su flowowi, ta ko ina Tasleem harbi take tana bin Amaar da gudu, duk yanda yayi da gudu haka take binsa tana harbi, har yanzu bata yi nasarar samun sa ba, nufan wurin dinning ya yi Asmeen ta kwarara ihu tana faɗin "dan girman Allah ɗan uwa kar ka yo ta nan ka taimaki rayuwata..." Abeesh riƙo hannun Nasreen yayi tare da ɗagota suka nufi upstairs da gudu, cikin sa'a suka shige bedroom tare da rufe ƙofa... Iya Amaar ne da Tasleem suke ta zarya a falo gaba ɗaya sun yi kaca-kaca da falon, sun farfasa komai na falon, hatta kujeru duk sun fuffuje da harbin bullet, daƙer Amaar ya ɗauki pillow kujeru guda biyu ya yo kan Tasleem da gudu kafin ta ankara ya yi tsalle ya faɗa kanta, gaba ɗaya faɗuwa suka yi akan carpet tana ƙasi shi kuwa yana saman ta ya danne hannayenta da filellikan kujerun da ya ɗauko yanda bazasu ji shocking ba, ya sakata a tsakiyar sa ba tare da ya danne ta ba sai iya hannayenta da ƙarfin sa yanda bazata samu ƙarfin ture shi ba, tana ƙoƙarin tashi amma ta kasa har ƙarfin ta ya ƙare haka tana ji tana gani ta kwanta tana kallon sa fuska a murtuƙe sai sauƙe numfashi take, shima kallon cikin ƙwayar idanuwanta yake tare da sakin murmushi ya furta "saboda tsananin ƙaunata da kike ne yasa zaki kashe ni?..." A fusace ta furta "na tsane ka wallahi ni ka ɗaga ni..." Kan sa yake matso dashi saitin fuskar ta zai sumbace ta, ganin abinda yake shirin yi ne yasa ta fara jujjuyar da kanta tana faɗin "bana so, kar ka sumbace ni, bana so, na gaya maka zan tsine maka albarka, ja'iri kawai..." Numfashin su ne yake haɗe wa yana shirin haɗe musu baki, ta ce "wallahi kana kawo bakin ka zan cije ka..." Sauran kaɗan ya haɗe musu baki ya yi saurin kawar da lips ɗinsa zuwa kan sumar gashin ta, cikin so da ƙauna ya sumbace ta akan gashin ta a hankali gudun kar su ji shocking...." A hankali yake hura mata iskar bakin sa ta ko ina, haka yake bin fuskarta da iskar bakin sa, ita kuwa ganin ba yanda ta iya ne yasa ta lumshe idanuwanta, ji tayi yana mata magana a sai tin kunnen ta a hankali cikin sexy voice "calm down! calm down!! calm down!!!...." Sai da ya fahimci ta samu nutsuwa tukun yayi saurin miƙe wa tare da ɗaukan abubuwan da yazo da su ya fice kafin ta ankara ta tashi.... Asmeen tana ƙarƙashin dinning idonta a kansu baki ya gagara rufuwa tsabar yanayin da suka shiga ne ya sanya ta nishaɗi.... Abeesh tinda suka shiga room ɗin sa suka tsaya a bakin ƙofa Nasreen kuma ta kwantar da kanta akan ƙirjinsa tayi lumuuu, shima kansa ya ɗora akan tsakiyar kanta ya lumshe ido gaba ɗaya basa cikin hayyacin su, Abeesh ƙamshin sumar kan Nasreen ba ƙaramin hargutsa masa ƙwaƙwalwa ya yi ba... Tasleem har zuwa yanzu bata buɗe eyes ɗin ta ba, bata ma san Amaar ya tafi ba sai dariyar Asmeen ce ta dawo da ita cikin hayyacin ta, a zabure Tasleem ta tashi daga kwancen da take a ƙasin carpet ta lalumo bindigar ta tana jujjuyawa tare da faɗin "yana ina? yana ina? yau sai nayi maganin sa..." saita Asmeen tayi da bindigar tana faɗin "ina wannan ja'irin mutumin yake?..." A tsorace Asmeen ta ce "kin ga dan Allah ki ajiye bindigar nan kar tsautsayi yasa ki harbe ni, shi kam ya daɗe da tafiya..." Tasleem ta ce "kashhhh! naso na ragargaza masa ƙwaƙwalwa..." Suna cikin wannan yanayin sai jin sautin motar Mommyn su suka yi ta dawo, A ruɗe Asmeen ta ce "innalillahi Mommy ta dawo..." Tasleem haura saman upstairs tayi tana riƙe da bindigar ta, Da gudu Asmeen ta haura saman upstairs room ɗin Abeesh taje tana bubbuga ƙofar, sai a lokacin Abeesh da Nasreen suka dawo hayyacin su, sai ji suka yi Asmeen tana faɗin "Nasreen mommy ta dawo..." Nasreen zaro ido tayi tana faɗin "mommy ta dawo?..." Cikin jin kunya Abeesh ya nufi cikin room ɗinsa ita kuma ta buɗe ƙofa ta fice, a tare suka sauƙa falo ita da Asmeen daidai lokacin da Madam Nablah ta shigo falo tana taku kamar bazata taka ƙasi ba, ganin yanda falon ya koma ne yasa ta tsaya cakk tana bin falon da kallo, cike da mamaki ta ce "whattt! me nake gani haka?..." Nasreen da Asmeen bakin su a haɗe wurin faɗin "your welcome Mom..." Madam Nablah ta ce "ba wannan ba taya falo na ya koma haka? wasan dambe ku ka yi ne? ko an mayar mun da falo kasuwa ne ban saniba..." Duk girgiza kai suka yi alamar a'a, Ta kuma cewa "shin yaƙi akayi ne? ko farmaki aka kawo muku?..." Ganin basu da amsar da zasu bata ne yasa suka ce "Mom ɓera ne..." Asmeen ta ce "ɓera ne ya fito falo saboda jin warin feshin magani da akayi, shine muke ta gudu..." Madam Nablah ta ce "Amma harbin bindiga nake gani ata ko ina, har a jikin bango, da kujeru ga plasman bullet ya fasa mun shi, flowowin ɗakin duk sun ragargaje, jikin frig alamar bullet, wai shin wani irin asara ku ka tamka mun ne haka? kayayyakin ɗakina masu bala'in tsada kun mun asarar su duk a saboda ɓera..." Asmeen ta kuma cewa "bindigar mu muka ɗauko zamu harbe ɓeran shine yake ta guduwa ko ina shiga yake, tsautsayi ne a yafe mana..." Madam Nablah fuska ba annuri tana kallon gefe ta ce da su "ku tafi ku bani wuri..." Haka suka ja jiki a sanyaye suka koma can room ɗin su... Madam Nablah ganin ba kowa a falon ne yasa ta lumshe idanuwanta, ta ɗago da hannayen ta sama sai ga wani irin haske mai launin green sai ga falon ya fara juyawa, a hankali a hankali har ya fara juyawa da gudun gaske, itama Madam Nablah haka take juyawa a cikin falon har sai da falon ya koma duhu ƙirin baka iya ganin abinda yake ciki, har ya koma normal, sai da falon ya ɗau tsawon mintina sha biyar daga bisani sai ga haske ya bayyana, Innalillahi wani irin tsaruwa falon yayi kamar ba'a Nigeria ba, komai da komai an canza kayan furnitures, kujeru na musamman masu bala'in tsada wanda babu mai irin su a doron ƙasa, plasman kuwa daga ƙarshen bango har ƙarshen bango tsabar girman sa, tsaruwar falon bazai misaltu ba... Tana kammalawa ta haura saman upstairs can room ɗin ta, falon kamar babu abinda ya faru a cikin sa, Bayan awanni Asmeen ce ta sauƙo falo ganin yanda falon ta koma ne kamar wacce tayi ɓatan kai, haka take ta kallace-kallace ta kasa gane wa shin a gidan su take ne ko kuma ƙasar waje aka fita da ita, tsabar ta gama tsora ta da gudun gaske ta koma room ɗin su, tana zuwa ta jawo hannun Nasreen suka fito falon a tare, itama Nasreen abinda ta gani ne ya tada mata da hankali, a ruɗe ta ce "a yaushe aka sauya komai na gidan? hatta fentin an sauya launin sa. Tasleem itama fitowa tayi, tsaya wa tayi tana bin falon da kallo daga bisani ta ce "Aljanun nan sun iya gyara kam..." Nasreen da Asmeen kallon ta suka yi tare da faɗin "Aljanu kuma?..." Tasleem ta ce "eh in ba su ba wani bil adam ne zai iya wannan aikin a wuni guda?..." Nasreen gaba ɗaya itama abun ya ɗaure mata kai... Madam Nablah tana kallon su ta cikin ɗakinta ta mirror, yanke hukuncin kawar musu da tunanin taya akayi aka maida falon na musamman tayi, tana cikin room ɗinta ta ƙirƙiri skeleton robot kamar mutane sannan ta sanya musu Aljanun da zasu zauna a jikin robot suna aiki kamar mutane, duk abinda aka sanya su suyi zasu yi, bayan ta gama ƙirƙiran su ta kuma basu umarnin su koma falo, haka robot suka fara motsi su biyar suka fita daga cikin room ɗin Madam Nablah suka nufi falo, A jere su biyar suka fara sauƙo wa falo, Asmeen ce ta fara ganin su a tsorace ta nuna su da yatsa ba tare da tayi magana ba, su ma sauran kallon wurin da take nuna wa suka yi, Nasreen ganin su yasa ta zaro ido waje tana faɗin "ƙalu innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, meye waɗannan skeleton?..." Tasleem kuwa tana ganin su kanta yayi wani irin sarawa kamar wanda aka kwaɗa mata guduma, Madam Nablah ce ta biyo bayan su tare da faɗin "ku kwantar da hankalin ku waɗannan robot ne kamar yanda ku ke gani ana showing ɗin su a TV, duk siyan su nayi daga yau zasu rinƙa rage ayyukan gida, har girki su zasu na yi, gyaran gida su ne, komai da komai sannan duk abinda ku ke buƙata ku sanar musu zasu yi muku..." Asmeen cike da mamaki ta ce "Mom irin robot ɗin da muke gani a Film yau su ne a gidan mu? ...." Madam Nablah ta ce "eh su ne, musamman nasa aka kawo mun su daga China..." Nasreen ta ce "Mom kina nufin kice su suka tsara falon nan? amma kuma naga komai na falon an chanza..." Madam Nablah ta ce "daman ina ajiye da kayan furnitures, yau kuma nasa aka kawo mun waɗannan robot suka tsara mun falon kamar yanda na umarce su..." Asmeen ta ce "wow so beautiful, abinda nake gani like dreams yanzu kuma gasu nan a realty...." Tasleem gaba ɗaya hankalin ta bai kwanta da waɗannan robot ba, ji take ƙirjinta yana bugawa sannan kanta kamar ana buga mata guduma, Tasleem nufan wurin robot tayi yanda suke a jere ta tsaya a gaban su tana ƙare su da kallo, idonta tasa a cikin ɗaya daga cikin robot tana kallon can cikin idonsa, gani tayi a cikin eyes ɗin sa wuta ne yake ta ci, haka tabi duk sauran da kallo su ma haka suke, lokaci guda taji wani irin hajijiya yana shirin ɗaukar ta... Madam Nablah idonta akan Tasleem tana tunanin ita ce kawai zata kwabsa mata, tana da saurin gane sihiri shiyasa Madam Nablah bata yinta sosai duk da jininta ce, Tasleem ce ta fara faɗin "ni gaba ɗaya hankalina bai kwanta da su ba, bana son su gaba ɗaya, dan Allah a fitar da su daga cikin gidan nan, bana son ganin su..." Madam Nablah ce tazo ta tsaya a gaban Tasleem tare da faɗin "Kinga Tasleem sai dai daga yau kar ki ƙara fito wa falo ki rinƙa zama acan cikin room ɗin ku domin babu yanda zan kai su, kamar yanda na tsara haka zasu cigaba da gudanar da aikin su a cikin gidan nan, sannan zasu rinƙa mun recording duk abinda yake faruwa, don haka ki koma can bedroom ɗinki, abinci da komai duk za'a rinƙa kai miki can...." Tasleem cikin fushi da tashin hankali ta bar falon ba tare da ta furta komai ba, saman room ɗin su ta haura tana kuka domin zaman gidan nan ya fara isar ta.... Shima Abeesh yana tsaye a saman upstairs ɗin sa yana jin duk jawaban Madam Nablah akan robot ɗin ta, shima tsabar ɓacin rai koma wa yayi cikin room ɗin sa...... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 19 to 20 Yau kwana uku da ƙirƙiran robot, yanzu su suke komai a gidan, Madam Nablah duk ta kori ƴan aikin gidan ta, hatta girki yanzu robot ne suke yi sannan su shirya akan dinning, Asmeen kuwa an samu abokan wasa, sai dai ta sa su a gaba taita kallon su tana dariya, robot ɗin burge ta suke shiyasa take taya su aiki, Nasreen kuwa da zaran sun kammala girki zata ɗauki kulolin Abeesh ta kai masa can room ɗin sa, Tasleem kuwa kamar ta hallaka idan tayi ido huɗu da robot domin bata ƙaunar su sam, tana room ɗin su ta gama shirin ta zata fita, ta feffesa ko ina na jikinta da turaruka kamar yanda ta saba, sannan ta ɗauki handbag ɗin ta da waya tare da key ɗin motarta ta fice, A falo ta tarar da Madam Nablah akan dinning da Nasreen da Asmeen, fuska a ɗaure tana kallon gefe ta ce "zan fita..." Nasreen ta ce "an kammala girki fa, yanzu nake shirin ta shi naje na ƙira ki..." Tasleem kallon ta tayi sannan ta ce "yau kwana nawa rabon da kiga na ci abincin gidan nan?..." Nasreen kallon Mommyn su tayi wacce take ta cin abincin ta ko kallon su bata yi ba. Tasleem ta cigaba da faɗin "har duniya ta naɗe Indai waɗannan Aljanun ne zasu cigaba da yin girki a gidan nan wallahi bazan ci ba, idan inaso zan iya shiga kitchen na girka abinda raina yake so, idan kuma naso zan fita naje restaurant ne.." Hanyar fita ta nufa taji Madam Nablah ta furta "ina zaki je?..." Tasleem tana yamutsa fuska ta ce "restaurant..." Madam Nablah ta ce "ki zo ki kaiwa Shaprees abincin sa kafin ki tafi..." Tasleem cike da mamaki ta furta "whattt? Mom ni kuma? why shi bazai rinƙa zuwa yana yin lunch ɗin sa anan ba?..." Madam Nablah ta ce "kiyi abinda na saka ki bawai umarnin ki zan bi ba, haka na tsara ..." Tasleem sai da ta ɗan tsaya na mintuna kafin ta nufi kitchen tana turo baki ta ɗauko jerin kuloli a paranti tayi waje, kai tsaye part ɗin Shaprees ta nufa, tana zuwa ta tura ƙofa ta shige, cikin sa'a ta tarar da shi a falo yana zaune akan sopa idonsa akan plasman da remote a hannunsa, ba tare da ta furta komai ba ta wuce shi ta kai masa dinning, Shi kuwa tin shigowar ta ya gane cewa Tasleem ce domin ba haka ɗabi'ar Asmeen yake ba, duk san da zata shigo da sallama a bakin ta cikin tsoro da fargaba sannan zata durƙusa har ƙasi ta gaishe shi.. Tasleem har zata fita ya dakatar da ita ta hanyar furta "Ke!..." Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba ta ce "Keke na kasuwa, kawo maka za'a yi ne?..." Ganin tana shirin raina masa wayo ne yasa ya miƙe shima ya nufo yanda take tsaye, bata ankara ba taga ya zagayo da hannayensa biyu ta sai tin cikin ta tare da mannota jikin sa yana faɗin "ki sauƙe wannan girman kan naki domin ni ne shugaban ki..." Tasleem cikin ɓacin rai da salon mugunta da iya ƙarfinta ta gwara masa kanta akan lips ɗinsa, ba shiri ya sake ta tare da toshe bakinsa da hannayensa biyu har sai da ya durƙusa, kafin kace mai har lips ɗinsa ya fashe sai jini, Tasleem juyo wa tayi tana kallon sa gira ɗaya a ɗage ta ce "Tasleem ce ba Aasmeen ba, kayi kuskure da baka gama tantance mu ba, wannan ɗin da kake gaban ta tafi guguwa iskanci...." Tasleem zaro black glass ɗin ta tayi tare da toshe wa tana masa wani irin kallon up and down ta cikin glass ta ce "daga yau Tasleem ce zata cigaba da kawo maka girki ba Asmeen ba sai ka kiyaye, ka rinƙa kwantar da tsuriyar ka domin tana harin abinda yafi ƙarfin ta ne...." Daga nan tayi ficewar ta.... Shi kuwa Shaprees har zuwa yanzu yana durƙushe gaba ɗaya jini ya gama wanke masa hannu domin ba ƙaramin bugu tayi masa akan lips ɗinsa ba, ga lips ɗin laushi kamar auduga shiyasa bashi da ƙarfi abu kaɗan ne zai fasa shi, wani irin ɓacin rai ne ya ziyarto cikin zuciyar sa, wani irin mugunta yake shirya ma ta.... Tasleem kuwa a gaban sa ta jefar da duk wani tunanin sa da ɓacin ransa domin ba shine a gabanta ba, yanzu abinda ta tinkara shine Amaar, da shi take kwana take kuma tashi a ranta, tsananin haushin sa take kamar ranta zai fita, babu wanda zai mata laifi bata ɗauki fansa ba hakan yasa tasa aka nemo mata address yanda yake, yanzu haka akan hanyar ta na zuwa gidan sa take.... Ita kaɗai tana driving tana tunanin abinda yayi mata a gidan su, duk duniya babu wanda ya taɓa sumbatar ta a ko ina sai shi mai ƙarfin hali da zuciya, hakan ma a cikin gidan su bayan ya furta kalmar soyayya da ta haramta wa kowa, ga laifin yasa an kore ta a ɗakin jarabawa... Tana cikin driving bata san ma ta iso gidan sa ba sai ganin ta tayi a ƙofar bakin gate, wasu sojoji ta gani a tsaye kusan su biyar ko wanne da bindigar sa, tunani ta fara yi shin wannan mutumin babban soja ne ko kuwa? a labarin sa da ta binciko an sanar mata shi ɗin sojan Bangladesh ne, yazo gudanar da wasu ayyuka kafin ya koma. Ƙarfin hali tayi ta sauƙa daga cikin mota ta ƙarasa wurin da sojojin suke a tsaye da ƙafa, tana isa wurin su ta tsaya Tare da furta "excuse me..." Wani soja ne ya ce "Ke cire glass ɗin fuskar ki..." Murmushi ta yi sannan ta ce "ba abin ta da hankali idan har glass ne matsalar ka ga shi nan zaka iya kaiwa Madam ɗinka domin nasan baka da arziƙin siyan wannan glass..." Tana kammalawa ta wurga masa shi, Wani sojan ne ya buɗe baki zai darara mata tsawa tayi saurin ɗaga masa hannu tana faɗin "Uhm uhm tsaya mana, ba'a ɗaga mun murya domin ni ba ƙaramar mace ba ce, ga can motata na parker ta acan, ba wurin ku nazo ba, nazo wurin ogan ku ne..." Ya ce "Ogah bai san kowa a wannan ƙasar ba don haka ki juya, idan kuma neman taimako kika zo nema sai ki bari idan ya fita ki tare shi a hanyar sa ta wuce wa, nake ga zai fi miki..." Tasleem kallon sa tayi up and down sannan ta ce "ka ga nayi maka kama da masu neman taimako? sannan babu ruwana da ko yasan wani a ƙasar ko bai sani ba nidai burina ka ƙira shi a waya yanzu ka sanar masa cewa ya yi baƙuwa..." Sojan ganin ita ɗin bata wasa bace yasa ya yi dialing call number Amaar, Shi kuwa har yana shirin shiga bathroom zai yi wanka towel a ɗaure a kunkumin yaji ringing, ɗaga wa yayi aka sanar masa cewa ya yi baƙuwa bai tsaya jin ko wacece ba ya sanar cewa a barta ta shigo, daga nan ya shige toilet domin a tunanin sa ko wacece tazo zata iya jiransa ya fito daga wanka sannan ya gama shirin sa.... Tasleem bayan an sanar mata cewa ta shiga dogon tsaki taja tana taku kamar wata sarauniya sai ƙarar takalmin ta kake ji ƙwas ƙwas ƙwass ta shige, a mashigar babban falo ta ƙara tarar da wasu sojoji munana marasa fara'a da jajayen idanuwa, har zata ratsa su ta shige suka dakatar da ita tare da faɗin "Ke tsaya mana ..." Tasleem cikin ɓacin rai ta ce "meye kuma du? sai kace wanda na shigo gidan shugaban ƙasa...." Wani soja ne yazo gaban ta yana shirin jona mata na'ura a jikinta wanda zai bayyanar da abinda ta shigo gidan da shi, Tasleem ta ce "wai meye haka zargina ake ne?..." Sojan ya ce "kowa ma ba abin yarda bane, haka ake yi duk wanda zai shiga ciki sai an auna shi anga da mai zai shiga..." Sauƙe numfashi Tasleem tayi cike da takaici, wani ƙara suka ji a cikin jakar ta nan suka fara faɗin "ciro abinda yake cikin jakar ki..." Tasleem hamdala tayi a cikin ranta domin har tayi tunanin ta tafo da bindigarta ta fasa, haka ta sa hannu a jaka ta ciro waya tana faɗin "wayata ce dai ba komai ba sai key ɗin motata..." Sai da suka bincika sosai kafin suka barta ta shige ciki, tana shiga falo ta fara jin wani irin sanyi mai ratsa jiki, sai da ta gama ƙarewa falon kallo da kuma ƙaton photonsa dake manne a jikin bango da kakin sojan sa, ganin abinda take kallo bashi ya kawo ta ba yasa ta ja tsaki tare da kallon saman upstairs wanda take tunanin nan ne bedroom ɗinsa, har zata hau taji muryar wata mata ta fito daga kitchen tana faɗin "Malama ina zaki je ne, ki jira shi anan falon mana..." Tasleem kallon matar tayi taga tana sanye da kayan aikatau a jikinta sannan ta ce "shin zan iya tambayar ki?..." Matar ta ce "ina jinki..." Tasleem ta ce "meye matsayin ki a cikin gidan nan?..." Matar ta ce "ni mai aikin gidan ce, bani kaɗai ba mu huɗu ne a gidan masu aiki..." Tasleem jinjina kai tayi sannan ta ce "dakyau wato ya ajiye zuƙa-zuƙan mata a gida har ku huɗu kamar wasu matan sa...." Sauran ƴan aiki guda uku ne suka fito falo su ma tare da faɗin "wannan fa daga ina?..." Tasleem ta ce "lallai kun dace da matan gidan..." Duk murmushi suka fara saki tare da dudduba kan su tare da faɗin "Allah yasa mu zama matan sa, wayyo farin ciki, in haka ta faru ni ce farkon matar sa..." A cewar wata daga ciki, haka duk suka fara mita kowa a cikin su so take Amaar ya ce yana sonta shiyasa koda yaushe basa zama cikin ƙazanta kuma kullum da kwalliya a fuskokin su... Tasleem ganin batada lokacin su yasa ta barsu a wurin ita kuma ta haura saman ɗakin sa, tana zuwa ta shige bedroom, gani tayi babu kowa sai ƙarar ruwa da take taji a toilet alamun wanka yake, kana shigo wa room ɗin kasan ɗakin sa ne saboda tsananin ƙamshi da room ɗin yake koda yaushe baya rabuwa da turaruka, ga photunan sa a mammanne a jikin bango, Cike da mugunta tana sakin murmushi ta zaro wayarta a cikin jaka tana maganar zuci "tinda har ka nuna mun cewa kai ɗan iska ne to ni yau zan nuna maka cewa ni oganniyar ka ce...." Ajiye jakarta tayi akan gadon sa sannan ta nufi toilet tsayawa tayi a bakin toilet sai da ta kunna Camera wayanta kafin ta tura ƙofar toilet da ƙafarta cikin ƙarfi sai ga ƙofa ta buɗu anan ta saita Camera wayanta akan sa yana wanka, Da sauri ya ɗago da kansa yana kallon bakin ƙofar, ga yanda ruwa yake ta zubowa a kansa dake shower ya kunna, Tasleem murmushi take tana masa video tare da faɗin "ina kai ɗan iska ne ko? to yau zanga ƙarshen iskancin ka..." Amaar cike da mamaki yake kallon ta daga bisani ya ce "daman ke ce baƙuwar tawan?..." Tasleem ta ce "eh..." Amaar murmushi ya yi ko girgiza bai yi ba yana tsaye tsirara haihuwar uwarsa ya ce "to yanzun mai kike yi haka?..." Ta ce "video nake maka..." Ya ce "mai zakiyi da video?..." Murmushi tayi sannan ta ce "posting zanyi a social media, saboda iskanci irin taka kaje har gidan mu ka sumbace ni to yau zan nuna maka ranar ka kaima, zan kawo ƙarshen iskancin ka, facebook, TikTok, Instagram, Twitter duk zan tura videon tsirarar ka kowa ya gani, daga nan za'a fara raina wayon Soja..." Amaar bai san lokacin da ya tintsire da dariya ba yana faɗin "ai da sai ki mun bayani kice a social media zaki tura ni sai na miki style na video kala-kala yanda zanyi trending, oyaaa muje zuwa...." A lokacin Amaar ya fara ɗirkar rawa yana girgizawa tare da juyawa yana murguɗa ɗuwawun sa, sannan ya juyo yana tura tsuriyarsa gaba da baya tare da yo wa kanta yana faɗin "yi mun video dakyau ƴan mata yanda zanyi trending sosai na samu followers...." Tasleem video take amma hankalinta da idanuwanta duk suna kan sa, haka take bin sa da kallo daga ƙasin ƙafarsa har zuwa saman sa, gaba ɗaya jikin sa duk gargasa sun kwanta luf ga tsayi jikinsa fari tass, haka take bin saman faffaɗan ƙirjinsa da kallo, gaba ɗaya hankalinta baya jikinta, ga waya a hannunta har ta manta mai take da wayan. Amaar ganin yanda eyes ɗin ta suke a kansa ko ƙibtawa babu duk sun lullumshe kamar mai jin bacci, daga ganin ta yasan bata cikin hayyacin ta, murmushi ya sau tare da girgiza kai ya ciro towel ya ɗaura a kunkumin sa, a gabanta ya tsaya Tare da murza yatsun sa a saitin idanuwanta yana faɗin "yadai ƴan mata kin gama yin video ne?..." A ruɗe ta dawo hayyacin ta tana dafe goshin ta tare da faɗin "kai baka da kunya samm, haka tarbiyyar ka yake?..." Amaar ya ce "Uhmm to ki poster mana Kinga sai a tantance a tsakanina da ke waye marar kunya..." Karɓan wayarta ya yi yana duba video ya ce "yawwa ga shi nayi saving video, aina zaki fara yin posting TikTok ko Facebook ko Instagram?...." Da sauri Tasleem ta karɓi wayar daga hannunsa tana faɗin "bani wayata kar kayi posting don na fahimci baka da kunya ko kaɗan..." Tana karɓa tayi saurin goge wa, tare da sakin dogon numfashi tana lumshe ido kamar mai jin bacci... Amaar murmushi yasau tare da nufan wurin mirror yana ɗaure da towel.... Next Next Next New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 21 to 22 Amaar a tsaye yake a jikin mirror yana shafa cream sai satar kallon Tasleem yake a ta cikin mirror, ita kuwa baki ya gagara rufuwa sai masifa take ta zabgawa ganin ya ƙyale ta bai ce mata komai ba yasa ta ƙara fusata tana faɗin "wai ma mahaukaciya ka mayar dani ne? ina maka magana ko gyaran murya ka kasa yi..." Sai yanzu Amaar yayi magana tare da faɗin "so kike nayi gyaran muryan ne?..." Ta ce "Oho dai ban damu ba indai har kana ji na to ka fita daga cikin rayuwata tin kafin nasa ƴan iskan gari su koya maka hankali bar ganin kai soja ne..." Amaar shi dai murmushi kawai yake yana tunanin lokacin da take ƙaramar ta, yana girgiza kai tare da furta "Tasleem ɗina bata da masifa sai surutu amma yanzu masifar ma ta koya...." Cikin rashin fahimta ta ce "me? wato rainin nakan har ya kai haka? har wani Tasleem ɗin ka? wato baka ji abubuwan da na faɗa maka ba ko?..." Idon ta ne ya sauƙa akan ƙaramin bindigar sa dake ajiye akan gadon sa, cije lips ɗinta tayi tare da nufar wurin da sauri taje ta ɗauko, bai ankara da ita ba sai ji yayi tana faɗin "kai lusarin Soja idan baka ji tsoro na ba ai dole zaka ji tsoron mutuwa ko?..." Amaar ta cikin madubi ya kalle ta yaga ta saita shi da bindiga, juyowa ya yi yana kallon ta daga bisani ya girgiza kai ya ce "kin manta baki kunna kunamar bindigar ba..." A fusace ta kunna tare da saita kan goshin sa, Amaar ya ce "shin zaki iya harbana?..." Ta ce "to sai me idan na harbeka? ina ruwana da rayuwar ka..." Ya ce "kina ganin idan kin harbe ni zaki fita daga gidan lafiya kalau?..." Tasleem tana yamutsa fuska ta ce "to na gwada yin harbin ne?..." Ya ce "eh gwada mana..." ya furta hakan tare da yo wa kanta daga shi sai ɗaurin towel. Ta ce "kar ka matso kusa dani na gaya maka, stay away from me, zan harba fa..." Ganin yazo dab da ita ne yasa ta rufe idanuwanta sosai tare da harba bindigar cikin rashin sa'a babu bullet ko ɗaya a ciki, da sauri ta buɗe ido tana kallon bindigar cikin takaici tayi wurgi da shi. Amaar kuwa murmushi ya yi tare da faɗin "ashe zaki iya kashe ni?..." Tana ja da baya ta ce "mai zai hana, me zan yi da rayuwar takan..." Yana matsa wa kusa da ita, ita kuwa tana ja da baya, bata san lokacin da taje bakin gado ba sai ji tayi ta faɗa saman gado, kafin ta ɗago shima ya rufu kanta ba tare da ya danne ta ba, kamar dai yanda ya mata da ya je gidan su, Tasleem hannu tasa zata ture shi ya yi saurin furta "shocking, kin manta ne? kina taɓa ni zaki ji wuta, amma idan kina son hakan ya faru bari na danne ki..." Tasleem a fusace ta fara faɗin "Are you mad? are you stupid? are you crazy? danne ni fa kace zaka yi shin kai ɗin daman ɗan iska ne? ...." Ya ce "aww daman ke baki sani ba, to bari na nuna miki kalar nawa iskancin..." Ƙara rufuwa ya yi a kanta yana shirin sumbatar ta tayi saurin katse shi da cewa "dakata! wai meye hakane kasan kai ba mutum bane amma kake son ka cutar da rayuwata, jikin ka wuta baka san da zaran ka taɓa ni tamkar na faɗa cikin wuta bane....." Murmushi ya yi sannan ya ce "bakya son na taɓa ki ne?..." Tasleem kamar zata yi kuka ta ce "eh bana so, dan Allah ka ɗaga ni bana son jikinka ya gogi tawa akwai matsala, ni nasan kalar raɗaɗin da nake ji a jikina..." Tana ƙara shige wa cikin katifar hatta hannun ta bata so tayi motsi da shi saboda kar ta taɓa shi, Amaar ya ce "okay idan bakya son na haɗa jiki da ke sai kin furta cewa kina sona..." Tasleem ganin ba yanda ta iya ne yasa ta buɗe ƙaramin bakinta tare da fashe wa da kuka tana faɗin "ina sonkaaaaa...." Ya ce "wani irin abu ne haka? kin furta kalmar so ba armashi, ki dakatar da kukan ki furta mun kalmar love cikin zazzaƙar muryar ki da baki taɓa furta wa kowa ba...." Shiru tayi tana kallon sa wani irin takaici take shaƙa babu yanda ta iya haka ta furta "i love you..." Amaar juyar da kunnen sa yayi sai tin ƙaramin bakin ta yana faɗin "ban ji ba sake furta wa..." Fuska a ɗaure ta ce "i love you..." Ya ce "tirrr da wannan murɗaɗɗiyar fuskar taki zaki furta mun wannan kalmar? ki sau fuskar sannan ki yi murmushi sai ki furta mun...." Tasleem fuska a ɗaure ta ce "bazan yi ba..." Amaar idonsa ya wurga kan hannunta da ke gefe guda yanda ta miƙar da su, a hankali ya ɗago da yatsar sa ɗaya ya ɗora akan hannun ta, ai kuwa haka jikinsu ya yi shocking sauran kaɗan ya fa ɗa kanta ya yi ƙarfin halin da fa gadon, Lokaci guda Tasleem ta fara hawaye tana faɗin "shin me ya kawo wannan al'amarin cikin rayuwata, kai ɗin waye ne? Mutum ko Aljan?..." Amaar yana sakin murmushi daƙer, ƙwaƙwalwarsa ce take ta juyawa, ga bala'in ciwon da yake masa, haka duk san da ya taɓa jikinta ko kaɗan ne sai wannan ƙwaƙwalwar tasa ta motsa, domin ya fita jikkata, a hankali yake furta "Tasleem! Tasleem ki ki kice wa Mommyn ki...." Yana so ya kawar da wannan tunanin amma ƙwaƙwalwarsa ta ƙi barin sa, abubuwan da suka faru dashi ne yake ta dawo masa sabo kamar yanzu ake aikata abun, idan yana magana akan lamarin baya sanin mai yake faɗa, a yanzu lips ɗinsa ne suke ta kakkarwa yana so ya furta abu amma yana tunanin meye zai zo bakinsa, yana fargaban furta abu a wannan yanayin da yake ciki domin baya son ya tayar da ciwon ƙwaƙwalwar Tasleem.... Tasleem haka take bin fuskar sa da kallo tare da faɗin "kar fa ka danne ni, meye haka kake yi? wai kai ɗin waye ne? ni ka ɗaga ni..." Ita ɗin ma zogi take ji a jikinta na shocking da ya taɓa ta, daƙer Amaar ya yi control kan sa idanuwansa sun yi jawur shima kallon ta yake lokaci guda walwala da fara'a duk suka ɗauke daga kan fuskar sa, a hankali ya furta "ki furta kina sona, ina so na zama mutum na farko da kika fara furta kalmar soyayya a gare shi...." Tasleem ta ce "idan na furta maka hakan shi zai sa ka bar ni?..." Jinjina kai ya yi alamar "eh..." Murmushi ta sau har sai da ƙayataccen dimple ɗin ta ya lotsa sannan ta furta "i love you..." Wani irin bugu zuciyarsa tayi lokaci guda yaji kamar an wanke masa duk wata damuwa, bai san lokacin da shima ya sau murmushi ba tare da furta "i love you too baby...." Tasleem ɗaga gira ɗaya tayi tare da faɗin "to ɗaga ni hankalinka ya kwanta yanzu ko? kasa na furta kalmar da tinda nake a rayuwata ban taɓa furta ta ba hasali ma na tsani kalmar, hankalinka ya kwanta, ɗaga ni to..." Amaar tunani ya yi cewa yanzu ne yake da damar da zai cire motsawar ƙwaƙwalwar sa ta hanyar haɗa ido da ita na tsawon mintina biyar, idan har ya yi haka ƙwaƙwalwarsa zata huta, zata daina shiga hargutsin da take shiga... Girgiza kai ya yi sannan ya ce "baki gama ba ...." Tasleem kamar ta fashe da kuka ta ce "me zan maka again? yarjejeniyar da muka yi kenam cewa idan na furta maka kalmar so zaka ɗaga ni..." Ya ce "the second one shine za ki tsaya ne mu kalli juna na tsawon minti biyar..." Tasleem cikin rashin fahimta ta ce "wani irin sihiri kake so kayi da ni?..." Ya ce "kin ga kayan tsafi ne a cikin ɗakin nan?..." Ta ce "to meye dalilin yin haka?..." Ya ce "idan har kina so ki tafi to sai kinyi abinda na sa ki..." Tasleem ba yanda ta iya haka ta zuba idanuwanta a cikin nasa wanda shima haka yake kallon cikin eyes ɗin ta, kallon juna suke ba tare da sun ƙibta ba, har minti biyar ta cika, tana cika eyes ɗin Amaar suka rufe kan su sakamakon canjin yanayin da ya samu a cikin kwakwalwar sa, gaba ɗaya ya fita daga cikin hayyacin sa haka ya tafi luu ya kwanta akan Tasleem, ga ba riga a jikin sa daga shi sai towel, shocking ɗin da suke ji ya wuce misali Tasleem ihu take tana so ta ɗaga shi daga kanta amma ta kasa, ga tsananin shocking dake gudana a jikin ta, shi kuwa a wannan lokacin baya jin shocking sakamakon suman da ya yi baya cikin hayyacin sa, Ihu take tana neman ɗauki amma duk wannan ihun babu mai jiyo ta domin Indai ka shigo ɗakin duk motsin da zaka yi babu mai jin ka saboda ta ko ina glass ne a rufe, irin glass ɗin da duk ihun da zaka yi baza'a ji ka ba... Sai da suka ɗau tsawon minti goma bata samu nasarar ture shi ba daƙer ta tattaro ƙarfin ta duk da shocking ya gama cin duk ƙarfin jikinta ta wantsilar da shi gefen ta, a minti sha biyar minti biyu ne babu da yanzu sun warke da jin wannan shocking amma lamari ya koma baya, in da ace minti 15 ta cika Shikenam zasu daina jin shocking ɗin gaba ɗaya, amma kash minti biyu ya rage, Tasleem a ruɗe ta sauƙa daga kan gadon tana tangaɗi kamar wacce tasha maye, ita ma kafin ta ƙara sa bakin ƙofar ɗakin har ta faɗi sumammiya a ƙasin carpet shi kuma yana kan gado.... Misalin ƙarfe 12 na dare Nasreen da Asmeen ce suke zaune a falo ko wacce tayi tagumi su na jiran dawowar Tasleem, duk ba bu wacce ta rintsa a cikin su ga mommynsu ta ƙarƙame room ɗin ta sun buga mata yafi sau a ƙirga amma taƙi buɗewa, ita kuwa tana can wurin meeting ɗin su da suka saba, shigowar Abeesh ne yasa duk suka miƙe tsaye su na faɗin "ka same ta?..." Abeesh girgiza kai ya yi tare da faɗin "duk wurin da ya kamata ace naje dubo ta saida naje amma ko inuwar ta ban gani ba, abun zai ban mamaki ganin bata taɓa fita takai dare ba..." Nasreen cike da damuwa ta ce "yanzu ya zamu yi? number ta yana tafiya amma ba'a picking ..." Asmeen ta ce "duk saurin jin bacci na yau kamar wanda aka ɗauke mun bacci, bana jin sa ko kaɗan saboda rashin ƴar uwar mu, daga zuwa restaurant shikenam ta ɓata babu labarin ta?..." Nasreen ta ce "Asmeen ba muyi tunanin dubo part ɗin Ya Shaprees ba, ko zaki je ki duba mana ita..." Asmeen ta ce "kin dai san Tasleem ba zama zata yi a part ɗin sa ba..." Nasreen ta ce "by in case mana, ko ina ma ai zamu duba tinda nema muke..." Asmeen ta ce "Allah na gani bazan iya zuwa part ɗin Yaya Shaprees a wannan daren ba, ki rufa mun asiri mutumin da yanda kasan kwarton sama haka yake..." Nasreen tsaki ta ja tare da faɗin "ke fa kinada matsala, to ni bari naje..." Har tayi gaba Abeesh ya riƙo ta tare da girgiza mata kai yana faɗin "ita tasan dalilin da yasa bazata je ba, meyasa zan bari ke kije?..." Nasreen ta ce "Ya Abeesh dole zan je na duba ta acan, hankali na bazai taɓa kwanciya ba, Allah ya bamu uwa bamai kula da ƴaƴanta ba, why baza mu kula da junan mu ba...." Ta ƙarasa maganar tana kuka, Asmeen ce tazo ta rungume ta tana rarrashin ta, Abeesh ya ce "idan kun ƙira wayar ta tana shiga?..." Asmeen ce ta bada amsar "eh..." Ya ce "zamu yi amfani da phone number ta wurin yin tracking domin mu gano a yanda take ..." Nasreen a ruɗe ta ce "eh! ehh hakan ma zamu yi, da tinda mun yi tunanin haka da bamu sha wahala ba..." Hakan kuwa suka yi gaba ɗayan su fita suka yi, su na zuwa suka shiga mota tare da nufan bakin gate, Security ne suka dakatar da su tare da faɗin "ina zaku je a wannan daren?..." Nasreen ta ce "please gaggawa muke, yanzu zamu dawo..." Security ya ce "Madam ta bamu umarnin idan dare yayi kada mu bar kowa ya fita daga gidan nan haka kuma na waje bazai shigo ba..." Abeesh ya ce "okay bari na sallame ku yanzu idan Madam ta dawo sai ta dawo da ku, tinda inada right ɗin koran ku a gidan nan..." Security kallon sauran ya yi sannan ya ce "ba komai zaku iya wuce wa tinda su matan suna tare da kai, amma bakwa neman escort ne?..." Abeesh ya ce "No...." sannan aka buɗe musu get suka fita, suna bin hanyar da suka yi tracking number Tasleem har suka isa unguwar da take, abun mamaki ya basu ganin su a headquarters, ta ko ina sojoji ne, kafin su shiga ciki sai da wasu sojoji suka dakatar da su, Abeesh ya kalli su Nasreen sannan ya ce "ku sassauta damuwar ku, bama son su fahimci akwai matsala..." Bayan Soja ya yi musu knocking a glass car ɗin su, ya ce "daga ina sannan ina ku ka nufa?..." Ga haske ta ko ina kamar rana Abeesh ya ce "mu baƙi ne zamu je........" Sojan ya ce "baƙi daga ina?..." Abeesh ya ce "daga Kaduna...." Sojan ya ce "zuwa ina?..." Abeesh ya ce "yallaɓai ga shi kuwa mun iso, akwai gidan ɗan uwan mu a cikin nan unguwar zamu sauƙa a gidan sa ne..." Sojan ya ce "gidan wa?..." Nasreen ce ta kalli wayarta ta duba sunan gidan da Tasleem take sannan ta kalli sojan ta ce "gidan Major A.J Banglash...." Nasreen ta faɗa ne ba tare da tayi tunanin mai irin sunan da ta taɓa ji ba, sai Asmeen ce tayi saurin kallon ta tana mamaki taya tracking ɗin da suka yi zai nuno musu gidan Major A.J wanda suke ƙira da Ɗan uwa..." Daga baya itama Nasreen sunan dawo mata cikin kwakwalwa ya yi tana tunanin taya zai kasance gidan Major AJ?..." Sojan jin sunan da suka ambata ne yasa shi mamaki sam bai yadda dasu ba jin daga Kaduna suke, alhalin yasan cewa Major AJ ba ɗan nan ƙasar bane kuma yana daga cikin manyan sojojin cikin quarters... Alama da hannu yayi wa sauran sojojin duk suka zo wurin, Nasreen da Asmeen zazzaro idanu suka fara yi cikin tsoro da fargaba suka ce "mun shiga uku..." Sojojin su na zuwa suka ce duk ku fito daga cikin motan nan, haka aka tsare su da tambayoyi, daga masu musu tsawa sai masu zaro musu jajayen idanuwa gaba ɗaya sun shiga cikin firgici, idon Asmeen ne ya sauƙa akan wata maroon jeep car, leƙa number motar tayi taga na gidan su ne, taɓa Nasreen tayi tana nuna mata motar Tasleem, Nasreen zaro ido tayi ga hawaye duk ya wanke mata fuska ta ce "Ya Abeesh motar Tasleem..." Shima gani ya yi tare da girgiza kai yana faɗin "da mun sani tin farko mun sanar musu gaskiyar abinda yake faruwa, gashi nan ƙarya ta jawo mana damuwa..." Asmeen ta ce "abu ɗaya ne kawai ya jawo mana wannan rikicin shine sanar musu da muka yi daga Kaduna muke, yanzu kuwa ba damar canza magana domin bazasu taɓa yadda damu ba...." Nasreen ta ce "ai kuwa dole zamu sanar musu gaskiya..." Abeesh ya ce "yanzu meye abun yi?..." Duk wannan tattaunawar da suke yi suna durƙushe ne da gwiwowinsu sun ɗaga hannu sama, ga sojoji a kewaye da su, a haka suka kwana har asuba hannu a sama, duk wacce ta rintsa to a tsawace za'a tayar da ita, Asmeen tasha kuka kamar ranta zai fita ga ta gaji sosai, hannu duk ya yi tsami, ƙafafuwa duk sun tutturje, kan gwigwarta ba ƙaramin ciwo yake mata ba, tana sauƙe hannu soja zai darara mata tsawa haka itama Nasreen gaba ɗaya ƙafafuwan ta kamar wanda aka sa ƙaton dutsi aka danne mata su ko rintsawa bata yi ba gaba ɗaya idanuwansu sunyi jajawur tsabar azaba da kukan da suka sha, Shi kuwa Abeesh kwana ya yi yana tsallen kwaɗo wani sojan yana binsa a baya da dorina, yana tsayawa za'a zabga masa dorinar, gaba ɗaya ya fita hayyacin sa.... Da Asuba misalin ƙarfe 6 da rabi gari ya washe sosai, sai a lokacin Tasleem ta samu damar farfaɗowa tana kame da goshin ta, ganin ta a kwance akan carpet ne yasa ta miƙe tana dudduba jikinta, taga ko ina yayi jawur kamar ƙonuwar wuta, tana cikin wannan halin ne sai ga Amaar ya fito daga toilet yana goggoge sumar kansa da towel da farar jallabiya a jikinsa wanda ya tsaya masa a iya gwiwa, dake shi ya juma da farfaɗowa har ya yi sallar asuba. Ganin ta farfaɗo ne yasa ya nufi yanda take tare da faɗin "kina lafiya, fatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya naga jikin ki duk ya yi ja, ya kamata na duba lafiyar jikin ki..." Gaba ɗaya a ruɗe yake wannan maganar idonsa akan ta, domin ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, shima kamar wanda ya tashi daga jinya eyes ɗin sa a shashshanye. Tasleem tsabar takaici da haushi tama rasa bakin magana, ido kawai ta zuba masa hawaye kuwa ya gagara tsayuwa sai girgiza kai take, tana tunanin wani irin hukunci zata ɗau akan sa, suna cikin wannan halin suka ji yo knocking, Amaar idonsa akan Tasleem ya bada izinin shigowa, ɗaya daga cikin masu aikin gidan ne ta shigo tare da faɗin "Sir an kammala breakfast, za'a kawo muku nan ne ko a bar muku a dinning?..." Amaar hararar ƴar aikin yayi sannan ya ce "kin gaishe da Madam ɗina?..." Ƴar aiki haɗiyar yawu tayi kanta a ƙasi ta ce "ina kwana Madam ?..." Tasleem a fusace ta kalle ta tana faɗin "da ban kwana ba zaki ganni a gaban ki a tsaye?..." Ƴar aiki kai a ƙasi ta ce "Allah ya baki haƙuri..." Tasleem tsabar masifa har jijiyoyin wuyan ta sun tattashi, fuska tayi jawur ta ce "lokacin da akayi rabon haƙuri ba'a halicce ni ba..." Amaar murmushi ya yi sannan ya kalli ƴar aiki ya ce "je ki kawo mana nan ...." yana furta wa tayi waje domin Allah take ta bar room ɗin nan domin zata iya yiwa Tasleem rashin kunya idan ta musguna mata... Tasleem gaban Amaar ta je ta tsaya tana nuna shi da yatsa tare da faɗin "kai kuma Insha Allahu ni ce ajalinka, kana ji ba nace ni zan zamo ajalinka, a hannuna zaka mutu, wallahi ji nake kamar na shaƙe wuyan ka a yanzu..." Amaar ba abinda yake sai murmushi idonsa akanta, Mai aiki ce ta dawo da paranti kuloli a hannun ta, tsayawa tayi sannan ta ce "Sir aina za'a ajiye?..." Tasleem ce ta je har gaban ta sannan tasa hannu ta karɓi parantin sannan ta dawo gaban Amaar fuska a ɗaure ta ɗaga parantin sama ta sau a ƙasi, kulolin abincin duk suka tawarwatse, ƴar aiki toshe bakin ta tayi da hannayenta biyu tana zaro ido ta ce "ke kina da hankali kuwa? Abinci mai daraja zaki wulaƙanta?..." Wani irin juyi Tasleem tayi ta shaƙo wuyan Ƴar aiki tare da manne ta a jikin bango tana faɗin "meye to? saboda ba abinci a gidan ubanki shine zaki rikice kina so ki mun rashin kunya? daman haka ƴaƴan talakawa kuke da zaran kun samu wurin hutawa sai ku nemi ku falle..." Amaar cikin sassanyar murya ya furta "Tasleem...." Juyowa tayi tare da hankaɗa ƴar aiki saida ta faɗi ƙasi tayo kan Amaar tana faɗin "ehen ko zaka rama mata ne?..." Amaar kallon ƴar aikin yayi sannan ya ce "ke bar ɗakin nan..." Haka ta tashi ta karkaɗe jikinta tabar ɗakin... Amaar ya maida idonsa kan Tasleem sannan ya ce "me kike son ci? zan shiga kitchen da kaina na girka miki abunda kike so..." Dogon tsaki taja tare da furta "bani da lokacin ka ..." Nufan toilet tayi taje ta ɗauro alwala sannan ta tsayar da sallar asuba tare da lafula, Daga nan ta ɗauki handbag ɗin ta da wayar ta, tana duba wayar taga 100 missed call ƙiran Nasreen ne sai ƙiran Asmeen da na Abeesh zaro manya-manyan idanuwanta tayi tare da faɗin "innalillahi, ban taɓa kwana a wani wuri ba sai wannan lokacin ta dalilin ka, gashi yanzu na tayar da hankalin ƴan uwana, wallahi nayi danasanin saninka a rayuwata, ka shiga rayuwata da yawa...." Tana kuka tabar ɗakin, tana sauƙa falo ta tarar da ƴan aiki su huɗu a wuri ɗaya suna gulma, Tasleem tsarguwa tayi ta kasa yin haƙuri sai da ta same su, tana zuwa ta ce "duk kuyi mun kneel down..." Kallon juna suka shiga yi kafin suka ce "me muka miki da zaki ce muyi kneel down?..." Tasleem ta ce "ko baza kuyi ba?..." Suka ce "gaskiya ba zaman ki muke ba don haka baza muyi ba..." Tasleem jinjina kai tayi sannan ta ce "gaskiya ne..." Shima Amaar fito wa ya yi ya ce "meya faru?...". Ƴan aikin ne suka sanar masa abinda yake faruwa... Kallon Tasleem ya yi Sannan ya ce "meyasa zaki hukunta su? ni nayi miki laifi ni ya kamata ki hukunta ba su ba...." Tasleem ta ce "okay kai zo ka mun kneel down..." Duk ƴan aiki zaro ido suka yi tare da faɗin "a'a ki bari mu zamu yi, domin bai cancanci wannan wulaƙanci ba..." Ta ce "meyasa da farko dana saka ku bakuyi ba? saboda haka yanzu reshe ya juye da mujiya..." Tasleem kallon Amaar tayi sannan ta ce "kai zo nan, kayi abinda na saka ka...." Amaar bai ji komai ba haka yaje gaban ta ya yi kneel down. Ta ce "ka ɗaga hannun ka sama..." Hakan kuwa yayi kamar yanda ta umarce shi... Wata daga cikin ƴar aikin ce tayi murya ƙasa-ƙasa ta cewa sauran "Asiri fa tayi masa..." Wannan furcin ne ya sauƙa akan kunnen Amaar, murmushi ya yi sannan ya ce "ba Asiri bane, tsananin so da ƙauna ne..." Duk shiru suka yi da sauri suka bar falon, ita kuwa Tasleem zama tayi akan kujerar falon ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana karkaɗa ƙafa, sai faman danna wayar ta take, shi kuma idonsa akan ta ji yake kamar ana ƙara masa ƙaunar ta ne, yana kuma farin ciki ko ba komai ta yaye masa damuwa ɗaya, wato na matsalar ƙwaƙwalwa, yanzu yabar wannan matsalar... Suna cikin wannan halin sai ga wani soja ya turo ƙafa ya shigo, har ya buɗe baki zai yi magana idonsa ya sauƙa akan Ogansu, da sauri ya ƙarisa shigowa ciki tare da faɗin "Ogah ya haka kuma?..." Tasleem ko ɗagowa bata yi ba balle ta kalli yanda suke. Amaar ya ce "No kar ka damu faɗan cikin gida ne, wannan ɗin sarauniyata ce nayi mata laifi shine take hukunta ni..." Sojan ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba sai dai babu yanda ya iya, ya sanar da abinda ya kawo shi yana faɗin "Ogah wasu ne suka zo wurinka tin jiya cikin dare misalin ƙarfe 12 zuwa 1 amma bamu bar su sun zo nan ba..." Amaar ya ce "meyasa baku sanar mun ba a tin jiya?..." Shi har ya manta kwana yayi a sume. Sojan ya ce "sun ce daga Kaduna suke kuma mun san bakada kowa a Kaduna shiyasa muka riƙe su a can cikin quarters...." Amaar ya ce "su nawa ne?..." Sojan ya ce "mata biyu namiji ɗaya..." Amaar abun mamaki ya bashi jin har da mata, yana cikin tunani yaji Sojan ya ce "amma matan ƴan biyu ne domin kamar su ɗaya sak..." Tasleem tana jin haka tayi saurin ɗagowa tana kallon Sojan, Sojan yana ganin ta ya zabura tare da nuna ta da yatsa yana faɗin "Ogah inaga fa matan Aljanu ne domin kamar su ɗaya sak da wannan ta zaunen..." Sai a lokacin Amaar ya kawo a ransa cewa ƴan uwan Tasleem ne, itama Tasleem a zabure ta miƙe tsaye tana faɗin "Nasreen and Asmeen..." da gudu tayi waje ko tsaya ɗaukar jakar ta bata yi ba, Shima Amaar bin bayanta yayi da Sojan.... NEXT NEXT NEXT New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 23 to 24 Tasleem tana isa wurin da ƴan uwanta suke a durƙushe bata san lokacin da kuka ya yanko mata ba, itama durƙusawa tayi tare da rungumo Asmeen, daga lokacin Asmeen ta suma akan ƙirjin Tasleem, a ruɗe ta fara jijjiga ta tana ƙiran sunan ta "Asmeen! Aasmeen!! ke Asmeen dan Allah ki tashi babu abinda ya faru da ke..." Itama Nasreen hankalin ta ba ƙaramin tashi ya yi ba duk wahalar da tasha hakan bai hanata jijjiga Asmeen tana kuka itama. Tasleem ta ce "Nasreen kin sha wahala sosai dan Allah kuyi haƙuri...." Nasreen cikin fushi da takaici ta finciko Aasmeen daga kan Tasleem ta rungume ta sosai tana hararar Tasleem tare da faɗin "wannan tashin hankalin da muka shiga duk ke ce sila, hankalin mu ya tashi duk saboda ke, because of you mun kwana a haka yanda kika gan mu kamar wasu ɓarayi, ga can Abeesh yanda sojoji suka masa abin tausayi...." Tasleem tana hawaye ta ɗaga kai ta kalli Abeesh yanda yake ta tsallen kwaɗo a wahalce gaba ɗaya ya fita hayyacin sa domin mintuna kaɗan zai iya haɗiyar ransa, ɗan dakatawa ya yi yana hutawa Sojan nan ya ɗaga dorina ya zabga masa a baya, a zabure Tasleem ta miƙe da gudu ta nufi wurin sa tana ƙiran sunan sa cikin kuka, tana zuwa tasa hannu ta ɗago Abeesh wanda ya kife a ƙasi, zaunar da shi tayi tare da faɗin "Sannu Ya Abeesh, kayi hakuri dan Allah...." Sojan daka mata tsawa ya yi yana faɗin "ke wa ya baki umarnin ɗago shi? wace ce ke?..." Tasleem cikin takaici da cije leɓɓe ta ɗago tana masa wani irin kallo na raini kafin daga bisani ta ɗaga hannu ta zabga masa mari tana huci ta ce "baka da matsayin da zaka san ko ni wacece, idan kuma ka takura kanka akan sanin ko ni wacece to zaka mutu ne..." Sojan ya ce "whattt ni kika mara?..." Tasleem ta ɗago hannu zata ƙara masa marin ya yi saurin riƙe mata hannu yana zaro mata rikitattun idanuwansa yana huci kamar tsohon zaki, Tasleem tana ta yunƙurin ƙwace hannunta daga riƙon da ya yi mata amma ta kasa domin ba ƙaramin riƙo ya yi mata ba.. Ba tare da Sojan ya ankara ba ya ji shima an damƙe masa hannun da ya riƙe Tasleem da shi, ɗagowa ya yi yana kallon Amaar ya ce "Oga wannan yarinyar hannu tasa ta mare ni..." Fuska ba annuri ya ce "ka sake mata hannu..." Tasleem tana ta yunƙurin zare hannun ta daga riƙon da sojan yayi mata, sannan shima sojan Amaar ya riƙe masa hannu da gasken gaske domin ji kake hannun yana ƙaras ƙaras alamun ƙashin hannun ne yake goce wa, Sojan ya ce "Oga my hand please..." Cikin tsawa Amaar ya ce "na ce ka sake mata hannu..." Sojan yana sakin Tasleem wani irin naushi Amaar ya kai masa akan lips ɗinsa har sai da ya dungura... Tasleem itama cike da takaici ta ɗaga hannu ta zabga wa Amaar mari, ba tare da ya motsa ba ya lumshe ido kafin ya buɗe har ta ƙara masa marin ta ɗayan ɓangaren. Sojojin wurin ne suka motsa zasu zo wurin Amaar ya yi saurin ɗaga musu hannu yana girgiza musu kai alamar a'a... sauƙe idanuwansa ya yi akan kyakkyawar fuskar ta wanda ya hargitse tana huci ta ce "na tsane ka wallahi, duk da ban san ka ba, ban san asalin ka ba amma ji nake kamar na kashe ka, duk kai ka jawa ƴan uwana shiga wannan tashin hankali, meyasa ka shigo rayuwa ta? dan Allah na roƙe ka da sunayen Allah ka fita daga cikin rayuwata tin kafin ka jawo mun matsala...." Amaar ya ce "idan kuma ban fita ba fa? me zai faru?..." A gigice Tasleem ta furta "zaka mutu ne, duk wanda ya shigo mana rayuwa mutuwa yake...." Murmushi ya yi tare da jinjina kai cikin salo ya juyar da eyes ɗin sa kan Nasreen wacce take zaune Asmeen a kwance kan cinyarta itama su ɗin take kallo tana mamakin ta yanda suka haɗu har suka fara wannan cakwakiyar..." Amaar ya juyar da kansa kan Tasleem yana girgiza kai ya ce "bazan iya fita daga cikin rayuwar ki kai tsaye ba sai dai idan kece kika cire ni da ƙarfin gaske, ta hanyar kisa, na fison ke da hannunki ki rabani da rayuwata ba wai aga gawata lokaci guda ba..." Tasleem tana hawaye ta ce "inda inada halin kashe ka, to da yanzu ba wannan labarin ake ba..." Buɗe tafin hannunsa ya yi tare da faɗin "bindiga..." yana alamu a sojan sa ya miƙo masa bindiga, kafin mintina aka ajiye masa bindigar akan hannunsa ba tare da sanin abinda zai aiwatar ba, idonsa akan Tasleem ya ce "ga bindiga ki harbe ni a wurin da zan mutu Lokaci guda..." wurga mata ya yi ita kuwa ta cabke tare da kunna kunamar bindigar ta saita shi tare da faɗin "kana tunanin bazan iya bane..." Amaar ya ce "nasan zaki iya shiyasa na baki damar aiwatar wa..." Sojojin sa ne suka fara "Please Oga don't allow her..." Ɗaga musu hannu ya yi tare da faɗin "ku dakata mun..." Nasreen ta gama tsurewa tana tunanin shin Tasleem zata iya harbe shi ko kuma pretending ne, Shi kuwa Abeesh tinda ya kifar da kansa bai ƙara ɗagowa ba tsabar tsananin wahalar da ya sha.... Amaar idonsa akan Tasleem wacce ta saita shi da bindiga ya ce "ki saita kan goshi na kina harba wa a take zan mutu, ko kuma a saitin zuciyata nan ma ko minti ɗaya bazan ƙara shurawa a duniya ba..." Murmushi Tasleem ta yi sannan ta ce "da kuwa zan fi kowa farin ciki idan ka bar duniya, zan harbe ka a saitin zuciyarka ne saboda anan ka ajiye soyayyata, wannan soyayyar kuwa so nake na dagargaza ta..." Jinjina kai ya yi sannan ya ce "Go ahead my beautiful girl..." Tasleem kamar wacce aka bata umarni lokaci guda ta harba bindigar sai ga bullet ya fasa ƙirjin sa...." Amaar a zabure ya ɗora hannunsa akan wurin da ta harba wato kan ƙirjinsa ta ɓangaren dama... Nasreen a zabure ta da ka uban ihu tare da furta "Tasleemmmm...." Haka sojojin suka nufo shi, a ruɗe Amaar ya ɗaga musu yatsa yana karkaɗawa alamar kar su nufo shi, Jin ƙarar harbi ne yasa Asmeen farfaɗowa a tsorace ta rungumi Nasreen tana faɗin "wayyo sun harbe mu ko? mun shiga uku sun harbe mu..." Abeesh shima ɗagowa ya yi yana kallon Tasleem cike da mamaki ganin yanda ta harbe shi, duk a tunanin sa pretending take duk da ta farmake shi a gidan su, duk da ba shi aka harba ba amma ya ji zafin harbin har cikin zuciyar sa, yana motsi da lips ɗin sa a hankali ya furta "kin fasa masa ƙirji...." Amaar tin harbin farko da ya durƙusa da gwiwowinsa bai ɗago ba, hannayensa akan ƙirji gaba ɗaya idanuwansa sun rikice sun yi jawur tsabar azaba, sai da ya ɗau tsawon mintuna kafin yayi ƙarfin halin ɗago wa ya sauƙe idanuwansa waɗanda suka canza launin ja akan fuskar ta, ga bakinsa yanda jini yake ɓulɓulowa, murmushi ya yi sannan ya ce "kin tabbata a saitin zuciyata kika harbe ni?..." Tasleem a yanda ta riƙe bindigar bata sauƙar ba tana kuka ta ce "eh! to ka mutu mana! me kake jira ne?..." Amaar yana fitar da murya daƙer ya ce "to ai baki harbe ni a yanda zan mutu da wuri ba, ba'a saitin zuciyata kika harba ba, nan ne saitin zuciya..." ya ƙarasa maganar yana nuna ɓangaren ƙirjinsa na hagun.... Tasleem ta ce "okay nayi kuskure yanzu bari na gyara kuskurena na harbin ka a yanda bai kamata ba, cire hannunka yanzu zan tarwatsa zuciyar takan...." Amaar yana durƙushe gwiwowinsa a ƙasi ya cire hannayensa daga kan ƙirjinsa, ga yanda jini ya wanke masa gaban rigarsa kamar wanda aka masa wanka da jini, Ya ce "zuciyar ai daman taki ce not mind, I love you Tasleem...." A fusace ta ƙara saita bindigar saitin ƙirjinsa tana shirin harba ta ji kukan Nasreen tana faɗin "wai ke baki da imani ne? ke wata iriyar shashasha ne marar son mai sonki sai maƙiyinki..." Tasleem idonta akan Amaar ta ce "abun burgewa ne kaso maƙiyinka..." Asmeen wacce hankalin ta ya gama dawo jikinta ta ce "dan Allah Tasleem kar ki sake aikata kuskuren da kika aikata yanzu, na roƙe ki shi ɗin mutumin kirki ne..." Murmushi Tasleem ta yi sannan ta ce "bai dame ni ba sanin ko shi waye..." Amaar lumshe idanuwansa ya yi tare da faɗin "ki aiwatar da abinda kika yi niyya My...." Ya furta hakan tare da jiran sauƙar bullet, haka zuciyar kowa take bugawa ita kuma Tasleem hannunta take motsawa tana shirin danne kan bindigar, girgiza kai tayi tana kuka ta wurgar da bindigar tare da juya wa da gudun gaske ta bar wurin, kai tsaye motarta ta shige a ɗari ta bar quarters..... Amaar kifar da kansa yayi saboda tsananin zogin da yake ji, ba ƙaramin zubda jini ya yi ba, haka ya yi ƙarfin halin tashi daƙer yana takawa, duk yanda ya taka sai jini ya zuba, sojoji ne suka yo kansa zasu kawo masa ɗauki Amaar ya yi saurin ɗaga musu hannu alamar dakatarwa yana girgiza musu kai domin a halin yanzu ba bakin magana, dakatawa suka yi domin su na matuƙar jin maganar sa, Amaar yana tafiya yana tangaɗi wani irin hajijiya ne ya ɗauke shi yana shirin faɗuwa sai ga Nasreen da Asmeen sun nufo shi da gudu suka tare shi, haka suka saka shi a tsakiya wannan ta riƙe gefen sa wannan ma haka, da haka suke tafiya, shima Abeesh tashi ya yi ya nufi yanda suke yana zuwa shima ya riƙo shi, hannun sa ya lanƙaya ta wuyansa sannan ya riƙo bayansa, ita kuma Nasreen ganin Abeesh ya karɓe su yasa ta cire gyalen kanta ta danne masa wurin harbi yanda jini zai rage zuba. Amaar sam ya ƙi barin sojojin sa su kusance shi sannan ya hana a kaishi asibiti still baya son a ƙira masa ko wani doctor, da haka suka ƙarisa shigewa gidansa, a falo suka tarar da masu aiki ko wacce tana harƙoƙin gaban ta basu san me ke faruwa ba, ganin Amaar a wannan halin ne yasa su tsorata da sauri suka dafe ƙirji tare da faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un me ya faru da shi?..." Nasreen kallon su tayi cike da damuwa ta ce "dan Allah ina ne part ɗin sa zamu shigar da shi ne..." Ɗaya daga cikin masu aikin ce ta ce "innalillahi ke ba yanzu kika fita ba? ya naga kin koma mutum biyu?..." Itama Asmeen nufan su tayi tana faɗin "please ba lokacin wannan maganar, ina zamu kai shi?..." A tsorace suka nuna saman upstairs yanda yake, su na mamakin tambayar da suke mu su kamar basu san bedroom ɗin sa ba, still ga mamakin gani mutum biyu a matsayin ɗaya.... Nasreen kallon Abeesh tayi ta ce "Ya Abeesh mu kai shi da gaggawa please, ya raunana sosai..." Haura upstairs suka yi masu aiki kuwa kallo suka bi su da shi, ganin mutane biyu masu kammani kuma halayensu ba irin na wancan ba, anan suka yi tunanin ko ƴan uku ne domin kamannin ya ɓaci... Kwantar da Amaar suka yi akan gadon sa har ya suma sakamakon jinin da ya zubar, kuma wurin da aka harbe shi wuri ne mai hatsarin gaske duk da ba'a wurin saitin zuciyar sa aka harbe shi ba, a ruɗe Nasreen ta riƙo hannun Abeesh tana kuka ta ce "Ya Abeesh ya ƙi a kai shi hospital sannan ya ce kar a kawo masa ko wani doctor, shin haka zamu zuba masa ido ya mutu?..." Asmeen ta ce "dan Allah mu ceci rayuwar sa, kun ga idan ya mutu fa dole sai an kama Tasleem, kuma prison za'a kaita..." Nasreen ta ce "idan aka kaita prison ma ita ta jawo tinda bata da hankali, ciwon hauka ke damun ta, girman kanta da baƙar zuciyar ta zai jawo mata komai, ni yanzu damuwa ta shine naga mun taimaki Ɗan uwa, nayi matuƙar tausaya masa a halin da yake ciki, yana son bayar da rayuwar sa saboda Tasleem amma ita kuma mai banzar zuciya, ina jin haushin ta sosai akan irin waɗannan abubuwan da take aikata wa ba tinani da lissafi...." Nasreen zama tayi a bakin gado tana sharar kuka.. Asmeen zama tayi a kusa da ita tare da da fa kafaɗarta tana faɗin "Nasreen ki daina kuka dan Allah, ita ɗin ƴar uwar mu ce ba yanda zamu yi da ita sai dai mu tayata da addu'a, dole ita ɗin ta mu ce..." Abeesh dake tsaye ya rasa abun cewa sai sauƙar da numfashi ya yi tare da faɗin "yanzu ya zamu yi da shi?..." A zabure Nasreen ta miƙe tare da faɗin "yawwa Ya Abeesh kai doctor ne dan Allah please ka yi masa magani..." Abeesh girgiza kai ya yi yana faɗin "no bazai yu ba saboda doka ce a taɓa majinyaci irin wannan ba tare da sa hannu a takarda ba, dole sai ƴan uwansa sun yi signing tukun..." Nasreen sake baki tayi tana kallon sa cike da mamaki ta ce "Ya Abeesh wani irin magana kake yi haka? shin baza ka iya taimaka wa ɗan uwanka Musulmi ba idan yana cikin mawuyancin hali irin haka ba?..." Abeesh ya ce "no ki gane mana, idan ana so nayi masa aikin nan dole sai an kai shi hospital, saboda bamu san halin rayuwa ba, wata ƙil zai iya mutuwa a hannu na kinga dole za'a kama ni, wannan aikin yana da hatsari sosai...." Asmeen ce tayi saurin riƙo hannun Nasreen tana nuna mata Amaar, a tsorace duk suka zazzaro ido waje suna kallon yanda Amaar yake ta amar jini, jini ne yake ta ambaliya daga bakin sa gaba ɗaya ya fita hayyacin sa, duk nufan yanda yake suka yi da gudu, basu san lokacin da suka haura saman gadon sa ba, abinda suka ji yana furta wa shine "Tasleem! Tasleem!! Tasleem ina ina ƙaunar ki, meyasa kika manta Amaar ɗinki? ni ni nine fa, ni ne fa Amaar ɗin ki, meyasa zaki manta da ni, shin kin manta alƙawarin da muka yi na cewa baza mu taɓa rabuwa ba ne? Tasleem momynki bata ƙauna ta dan Allah kar ki zama kalar ta, mommin ki ta tsane ni kema so kike ki tsane ni?...." Nasreen da Asmeen kallon juna suka yi cike da mamaki, baki a haɗe suka furta "Amaar...." Shi kam Abeesh tinda ya ƙafe a wuri ɗaya bai ƙara motsawa ba jin sunan da yake ambata, jin sunan da yake muradin sake ji a cikin kunnuwan sa, tin yana yaro ya rubuta sunan a tafin hannunsa har yau tabon sunan bai shafe ba.... Amaar cigaba da surutan sa yake yana faɗin "Tasleem ki tuna fa mommin ki ita ce ta raba ni da kowa, ta raba ni da mahaifina sannan ta raba ni da ƙanina Abeesh, ta kuma raba ni da ke tin yarinta, meyasa baza ki tuna ba? Tasleem! Tasleem ki taimaki rayuwata, na rayu ne saboda ke Tasleem, kuma zan mutu saboda keeee...." Aman jinin ne ya ƙaru, yana shure-shure.... Nasreen cikin ɗaga murya ta furta "Ya Abeesh taimakooooo..." Abeesh shima bai san lokacin da ya hautsina ba haka ya fara dube-dube yana neman abinda zai taimaka masa wurin cire bullet, ita ma Asmeen dake ta karanci fannin likitanci haka ta fara danne masa ƙirji tare da hura masa iskar bakin ta duk da aman jinin da yake, Ita kuwa Nasreen ta gagara tsayuwa bare zama sai zarya take tayi a ɗakin, ta rasa wani gudunmawa zata bayar wurin sa ma wa Amaar lafiya dake ita ɓangaren lawyer ta karanta...... NEXTT NEXTTTT New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 25 to 26 Amaar na ta aman jini yana surutai cikin fitar hayyaci, Idanunsa sun cika da hawaye, amma ba zai iya fadin kalma daya cikakke ba sai ambaton sunan Tasleem... "Tasleem... don Allah kar ki bar ni... ki dawo..." Abeesh yana ƙoƙarin cire bullet ɗin da ke cikin ƙirjin Amaar. Hannunsa na rawa saboda jinin da ke ci gaba da fita yana ƙoƙarin dannewa da towel, amma lamarin ya fi karfinsa. Idanunsa suka ciko da hawaye, yana kallon Amaar ya rasa abinda zai yi sakamakon rashin kayan aiki. Asmeen da Nasreen suna tsaye gefe, jikin su rawa. Nasreen ta rike hannun Asmeen tana karanta ayoyi cikin sanyin murya, amma zuciyarta na kukan "kar Amaar ya mutu". Asmeen kuwa ta kasa daukar numfashi daidai, zuciyarta kamar zata fasa kirjinta saboda tsananin tsoro da damuwa. “Za mu rasa shi idan muka tsaya haka!” Abeesh ne ya furta haka yana duban Nasreen “Ina kayan taimakon gaggawa? Ina kayan dinki?” Asmeen ta zabura kamar wadda aka tsawatawa, ta juya cikin sauri da gudu zuwa cikin gida domin kawo akwatin taimako. Abeesh ya matsa kusa yana kokarin danne raunin tare da cewa, “Ya Amaar! Ji ni! Ka rike numfashinka, Ka tuna da Tasleem, Ka tuna cewa zata dawo gareka...” Cikin wahala Amaar ya daure fuskarsa, sannan cikin lafazi mai rauni ya ce, “Ina... Tasleem... nace... kar ku ce mata... na mutu... nace... na... na ƙa...” Sai kuma numfashinsa ya tsaya na dan wani lokaci. Abeesh cikin firgici ya fara jijjiga shi. “Ya Amaar! Kar ka bar mu! Na ce za ta dawo gareka...” A dai-dai lokacin ne Asmeen ta dawo da akwatin taimako, tana kuka tana cewa, “Na kawo... na kawo!” Amaar yana kwance cikin rashin hayyaci, amma zuciyarsa na yawo cikin duhu da hasken rayuwar da ya shuɗe. Cikin doguwar suma yake motsa lips, sai murya tasa ta soma fita a hankali, kalmomin da suka zo kamar mafarki.. “Wannan... duk laifin Mommyn ki ce... mahaifiyar ki Tasleem ta rabani da komai... ta ce bana da amfani... ta yi amfani da ƙarfin tsafi... ta jefani cikin ƙunci...” Abeesh ya daina motsi. Hannunsa ya tsaya saman bandejin da yake shirin manne wa. Ya kalli Nasreen da Asmeen cikin firgici ya ce “Me yake faɗa?” Asmeen ta matso kusa da Amaar, idanunta na cike da hawaye ta ce “Kamar dai yana magana ne akan rayuwarsa...” Amaar ya ci gaba da surutan sa, jikinsa na karkarwa, kalmomin na fita ba tare da saninsa ba. “Tasleem... nace ki taimake ni amma ki ka bari mahaifiyarki ta raba ni da ke, ta ce banida wani amfani sai ta jefani cikin ramin ruwa cikin duhu... shekaru ashirin... ashirin...” Abeesh ya runtse ido. Idanunsa sun cika da hawaye, zuciyarsa na harbawa kamar zai fasa ƙirjinsa. “Ashe shi ne? Ashe wannan shi ne Ya Amaar ɗinmu?” Nasreen ta dafe baki. “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un,wannan mutumin da Tasleem ta harba shine Ya Amaar?” Asmeen ta fashe da kuka. “Tasleem zata hallaka kanta idan ta gano gaskiyar nan... Allah ya taimake mu!” Sai lokacin Amaar ya soma motsi, yana buɗe idanunsa a hankali, dake yanzu an tsayar da jinin da yake zuba. Abeesh ya sunkuya da sauri, yana dafa goshin sa. “Ya Amaar... kai ne? Kai ne ɗan uwana? Ka gane ni?” Amaar ya zuba masa ido, a hankali ya gyaɗa kansa. “Na gane ka... tun ranar farko da na ganka... Abeesh... ƙanina...” Dukkan su suka durƙusa suna kuka. Nasreen ta tsaya gefe tana kallon Amaar, zuciyarta na bugawa da damuwa. “Ya zamu faɗa wa Tasleem? cewa ta harbi Amaar da hannunta. Ta ɗauke shi abokin gaba ba ta san cewa soyayyarta ce ta yarinta ba.” Asmeen ta matso kusa. “Ba zamu ce mata komai yanzu ba. Sai mun tabbatar da cewa Amaar ya samu lafiya.” Sai kuma Abeesh ya ɗaga kansa ya ce da ƙarfin zuciya, “Zan bi mahaifiyarku sai na fallasa asirinta. Wannan ƙaryar dafin shekaru ashirin, yanzu ya kamata ta kare.” Tasleem na zaune gefen gado tana kuka. Ta kasa kwantar da zuciyarta. Duk da ƙiyayyar da take nuna wa Amaar, zuciyarta na tsananin bugawa tun lokacin da ta harbe shi. “Me yasa nake jin kamar... kamar na rasa wani muhimmi abu a raina?” Ta dafa kirjinta tana kallon hoto da take ajiye tun tana yarinya — hoto nata da wani yaro da ta manta sunansa. Ba ta san cewa amaar ne ba... A cikin wani daki mai baƙin duhu kamar bakar dare, wurin da ko iska ba ta motsawa sai hayakin da ke tashi yana lanƙwashe sararin sama, can ne Madam Nablah take tsugunne, gefen wani ƙaton kwanon tsafi da ke tashi da wuta mai launin jajaye da kore-kore. Hayaki yana fito da irin ƙamshin da zai iya durƙusar da mai ƙarfin zuciya. Bangon ɗakin yana da rubuce-rubuce na asiri da zane-zane na tsafi – wasu kaman jinin mutane, wasu kaman rubuce-rubucen bakaken aljanu. A gaban ta wani mutum ya bayyana – Zulqarnain, ƙaton saƙagon tsafi, wanda ba mutum ba ne cikakke, ba kuma aljani ba ne cikakke. Gaba ɗaya siffar sa na bada tsoro, jiki mai ƙiba baƙi kamar gawayi, idanunsa jajaye da ke walƙiya kamar wutar lantarki. Wani irin zafi da ɗumama ke tashi daga jikinsa. Ya zauna cikin murhun da wuta ke ci, wutar ba ta cutar da shi ita ce ƙarfin sa. Madam Nablah ta sunkuya, tana rarrafawa zuwa gareshi, ta durƙusa ta saki murya mai ƙarfi, kamar ba daga cikin halittu ba "ZULQARNAIN, UBA NA TSAFI! UBA NA IKO! KAI NE MAI SARRAFAR RAI, KAI NE MAI JUYAR DA DAKKA! Na zo... na zo neman ƙarfin da zai murƙushe wanda ya dawo daga matattu! Na zo neman ƙarfin da zai karya zuciyar Tasleem domin ta manta da ruhi... ta manta da soyayya... ta manta da gaskiya...!” Idanunta a rufe, tafin hannayenta na ɓullo da wuta, wata wuta mai launin shudi, ba kamar kowace ba. Wutar zuciya da tsafi ne, tana ƙuna da sanyi amma tana ƙone zuciya. Zulqarnain ya saki dariya mai amo irin na halittu na ban tsoro, Muryar tasa ta cika ko’ina “Kin sha wahala Nablah, amma kika rasa ƙarfin zuciya. Amaar ya dawo – ruhi da haske sun motsa. Kin bar kofar zuciyarsa a buɗe. Don haka... zan ƙara miki iko. Amma ki sani... da wannan ƙarfin sai dai ki sadaukar da ɗaya daga cikin ƴaƴanki guda uku!**” Madam Nablah ta bude idanu da sauri tare da faɗin “A’a! Kar ka… kar ka ɗauki Nasreen! Kar ka ɗauki Asmeen! Tasleem ma... tana da amfani...” Zulqarnain ya girgiza da ƙarfi. Wata wuta ta buge bango, ƙasa ta girgiza. “Ɗaya sai an sadaukar! Ko kuwa… ki rasa komai!” Madam Nablah ta dafa kanta, jikinta na karkarwa. Wata zuciyar mugunta ta fara ratsa ta. Ta tuna da Amaar – wanda take tsoron dawowar sa. Tana jin wani abu na karfi yana yawo a cikin jijiyoyin ta. Wutar da ke hannunta ta kara ƙaruwa. "Na amince... zan sadaukar... amma ku ba ni ƙarfin da zai sa Amaar ya sake ɓacewa har abada!” A cewar Madam Nablah! A wannan lokacin, wasu bakaken aljanu suka fito daga cikin wutar, suka nutse cikin zuciyar ta. Hannunta ne suka ƙara kyarma, idonta sun koma fari. A wannan rana… Madam Nablah ta zama abin da ba za a iya ɗauka da wasa ba. ƁANGAREN TASLEEM… Tana ta hawaye, ta dafe ƙirji kamar zuciyarta na wani irin tsalle. A zuciyarta, tambayoyi na ci gaba da bubbuga kamar ƙaho, “Me yake faruwa dani? Waye wanda na harba? Waye shi da zuciyata ke motsawa idan na ganshi? Me yasa hannunsa ke yi min shocking idan ya taɓa ni? Na kashe shi ne…? Ko yana raye?” A take ta miƙe kamar an zaro ta, zuciyarta na harbawa da ƙarfin da ta kasa iya jurewa. Ta nufi ƙofar ɗakin da take, tana bin dogon hallway har ta sauko falon gidan da ƙafa. Ƙafarta na taka tiles ɗin falon — hayaki ya tirniƙe idonta “Inna lillahi...! Me ke faruwa?” Falon ya cika da hayaƙi mai ƙamshi irin na tsafi — ba turare bane, ba hayaƙin gas bane — hayaƙin mugunta ne. Ba kowa a gidan. Nasreen da Asmeen suna can wajen Amaar suna kula da shi, Ita kaɗai ce. Tana kokarin juyawa zata koma bedroom ɗinsu cikin gaggawa, sai taji wata dariya mai firgitarwa kamar daga sama. Duhu ya fara lullube hasken rana kamar dare ya sauka. Idonta ya ɗauki duhu. Kyaaaaah!!! Kamar a mafarki, robot-robot guda biyar waɗanda Madam Nablah ta ce masu aiki ne suka bayyana daga duhu. ba na’ura ba ne — aljanu ne a cikin siffar robot. Dukansu biyar ne suka fara rawa da dariya, suna motsa hannaye da ƙafafu, suna tashi sama kamar masu fikafikai. “Ina zaki je, Tasleem? Ina zakiii...? Gaya mana... Gaya mana!!” Idanunsu ne suka fara walƙiya da wuta kamar bulalai. Murya kamar daga ƙasa ta fito, mai amo da cike da mugunta. Tasleem ta saki wani irin ihu — ihu na ruɗewa da tsoro. Sai ta juya da gudu, ta nufi stairs ɗin da ke kaiwa sama. Amma kafin ta taka mataki na huɗu — ƙafarta ta dagu sama! Ta hau tashi kamar iska kafin jikin ta ya faɗo da karfi, Ta ji kamar an juyo mata da duniya, amma duk da haka ta fara gangarowa ƙasi kamar tabarma ce ƙasa ke ja da ita, aljanun na ta bin ta da dariya da murya mai firgita “Ki dawooo... ki dawo ki ganshi... ki dawo ki ga wanda kika kashe…!” Hayakin ya fara shigowa hancinta, jiki na ta rawa. A daidai lokacin, ƙarar wani abu ya daki glass, ƙofar ɗakin sama da ke a buɗe ta buge da ƙarfi. Wani irin murya mai launin jinƙai ya fara bayyana a zuciyar Tasleem, ba daga wajen aljanun ba “Tasleem… ke kika harbe ni. Amma zuciyarki ta san ni. Cikin ki ya gane ni. Duhu baya hana haske zama gaskiya.” Cikin tashin hankali tayi firgigit! Tayi gigin mikewa, tana jan jikinta — tana kallon wuta da duhu da dariya na shigowa ko’ina. Sannu a hankali, tana fara gane zuciyarta ba komai ke dukan ta da tsoro ba — ruhin Amaar ne ke kiranta. Zuciyarta na bugawa kamar za ta fasa ƙirji. Tana kukan ban tsoro da na rudani, amma kuma murya mai sanyi da zurfin jinƙai na ci gaba da tashi cikin zuciyarta “Na tsaya a cikin duhu shekaru ashirin… Amma ke kika zama Hasken Ruhi na…” Ta dafe ƙirji da hannu ɗaya, tana kukan da bata san menene ba. Ba kuka ne na jin tsoro kaɗai ba — kuka ne na wani abu mai ƙarfi a cikin jininta, wani abu da ke birkita mata tunani, yana motsa tsohuwar ƙauna da ta mantawa da shi. Wata guguwa ce ta haura saman gidan, tagogine suka fara dukan juna da ƙarfi, duhun ya ƙara ƙamari, robot-aljanun nan guda biyar sun fara shigowa cikin hallway suna ɗauke da kayan sarƙa da karfe, suna faɗi “Mu ne masu gadin zuciyarki… kuma ke ɗaya ce da za ta cika sadakin macen tsafi!” Tasleem faɗuwa tayi da ƙarfi a gaban wata kujera, tana girgiza kai da karfi tana faɗin “Ku daina… Ku daina shigowa raina! Ni ba macen tsafi bace! Ni ba zan zama rantsuwa ga muguwa ba…” A daidai lokacin da daya daga cikin robot-aljanun ya nufi kanta da wata irin sanda mai walƙiya, wani haske mai matuƙar ƙarfi ne ya leƙo daga ƙofar gidan, hayaki ya watse gaba ɗaya, kuma dukkan aljanun sun tsaya cak kamar an tsayar da su! Sai ta ji sautin murya daga bayan ƙofa ana furta “Tasleem, ki guje su. Kar ki bari su yi nasara. Karki manta da haske ko da duhu ya rufe komai.” Amaar ne. Yana kan gadonsa a bedroom amma ruhin sa yana nan kusa da Tasleem kamar yana ƙoƙarin kiran zuciyarta, yana ja da tsafin da ke kulle a rayuwarta. Kallon da Tasleem ta yi da kyau a cikin wannan haske, sai ta fara hango fuskar Amaar cikin haske, da idanunsa na tausayi da yawan magana. “Kai... Kai ne…?!” Sai wani irin shocking ya sake bugarta daga ƙirji zuwa ƙafafu. Tayi ihu da ƙarfi, ta faɗi rubda-ciki a ƙasa. Tunaninta ya tafi da gani. Hankalinta ya tashi. Idanuwanta sun ɗauke. Amma zuciyarta ta ƙwace daga ƙulle. Tana cikin suma, tana hawaye, tana cewa “Na harbi wanda nake so... wanda zuciyata ke ƙira, wanda hasken ruhina ne…” Kuma a cikin wannan halin — sannu a hankali ta fara gane cewa wancan yaron da ta taɓa ƙauna tin yarinta — Amaar ɗinta ne! ƁANGAREN AMAAR... Amaar ya buɗe idanuwansa cikin nutsuwa, murmushin ciwo a saman fuskarsa da hawaye masu ɗumi a cikin kwarmin idanuwansa. Abeesh na gefensa ya tsare shi da ido, shi da Nasreen da Asmeen gaba ɗaya zuciyarsu ta yi rauni da girman gaskiyar da suka ji. Sun gane wannan mutumin shine Amaar ɗin su, yaron da aka ce ya ɓace shekaru ashirin da suka shuɗe. Amaar ya dafe ƙirjinsa da hannunsa ɗaya, ya sauke ajiyar zuciya, sannan da raunanniyar muryar ya ce: “Na gode da kulawar da kuka bani. Ban taɓa tunanin zan sake ganinku a rayuwa ba... Na rasa komai a duniya – amma Allah ya dawo mun da rayuwata ta gaskiya.” lumshe ido yayi tare da zubda hawaye ya kuma cewa “Madam Nablah… ita ce ta jefa ni cikin ruwan duhu na tsafi. Tana son ta hallaka ni gaba ɗaya, amma Allah bai yarda ba. Na rayu…” Asmeen ta ce “Wa ya cece ka Ya Amaar? Wa ya zamo garkuwa a cikin wannan duhun?” Amaar ya ɗan jiyo kansa gefe, kamar yana jin zafin tuna wani abu mai nauyi sosai a ƙwaƙwalwarsa. Idanunsa suka ƙanƙance, sai ya ce “Zan faɗa muku wata rana… Ba yanzu ba. Amma ku sani har yanzu ba a gama wannan faɗar ba.” Daga nan sai ya kama hannun Abeesh da ƙarfi yana faɗin “Kada ku faɗa wa Tasleem. Kada ku ce mata ni ne Amaar. Kada ku bari Madam Nablah ta gane ni. Har sai lokacin da na shirya… akwai wani abu da nake buƙatar na tabbatar da shi.” Nasreen cike da damuwa ta ce “Har zuwa yaushe zamu daina ɓoye sirrin nan? Idan aka gano cewa kai ne Amaar fa? Ko kuma Tasleem ta tuna da kai da kanta?” Amaar ya kalli Nasreen da ido masu tsananin natsuwa da kwanciyar hankali ya ce “Zuciya tana da hanyar da ba a iya shan kwaya a ɓoye ta ba. Zuciyar Tasleem zata gane ni, amma lokacin da ya dace.” Daga nan suka yi masa sallama. Nasreen da Asmeen suka kalli Abeesh da idon tausayi, yana so ya zauna da Yayan shi tsawon shekaru basu ga juna ba, daƙer suka samu ya yadda zasu tafi tare yana kuka, suna kuka.. Suna cikin mota suna tafiya cikin yamma, Asmeen ta ce: >“Shiyasa Mommy bata taɓa barin mu shiga bedroom ɗinta ba… Ashe akwai wani shirin da take a ɓoye” Nasreen ta jinjina kai cikin alhini ta ce “Shiyasa Mommy da Tasleem ba sa shiri, Tasleem ta taɓa faɗa mun cewa tana mafarki Mommy tana shan jini, amma ban taɓa yarda da ita ba.” Ta share hawayenta sannan ta ƙara da cewa: “Tasleem na da baiwa… Zuciyarta na gane gaskiya kafin baki ya furta.”...... ƁANGAREN AMAAR... Shi kuma Amaar ya zauna shi kaɗai, jikin sa a manne da bandeji babu kaya a jikinsa, idanunsa sun zurfafa cikin tunani. Kallon gilashin taga yake yi, yana hango rana tana faɗuwa ga duhu yana shigowa. “Tasleem…” ya furta da ƙaramin murya. Sai ya rufe idanunsa, zuciyarsa ta ɗauko masa shekarun yarinta, lokacin da Tasleem ke masa dariya, suna gudu a ciyawa, tana ce masa “Kai ne Hasken Ruhi na…” Sai ga hawayensa sun gangaro Zuciyarsa ta gama raunana Kuma ba wani bandeji da zai warkar da raunin da ke cikin zuciyar sa..... ƁANGAREN MADAM NABLAH… A cikin duhun dakin tsafi, hasken wuta mai shuɗi yana walkiya daga wani ƙaramin madubi mai jini a cikin gilashi, wanda aka ɗaure da ruƙon zinariya mai zane-zanen gargajiya. Wurin tsafin ya cika da hayaƙin turare da gurnani na shiru – kamar ana karanta wata duniyar da ba a iya gani da idon duniya. Madam Nablah na zaune akan tabarma ta zinariya, tana sanye da tufafin bakake masu yalwa, hannayenta a buɗe, dukkan tafin hannunta cike da wuta mai yawo kamar ruwan zafi. Cikin murya mai sanyi na mugunta, take furta yaren tsafi “Zaaaa'qil... H'azmaar... Ayyukan da Maruuk!” Bana hangen zuciyar maƙiyina, Bana gani abinda ke ɓoye.” Madubin tsafin ne ya fara girgiza. Sai hayaƙi ya shiga zagaye a cikinsa – hayaƙi mai launin jini. A hankali siffar wani fuska ta bayyana… fuskar Amaar. Madam Nablah ta ɗan motsa daga inda take zaune, ido a zarr kamar ba ta yarda da abinda take gani ba. “Na tura ka cikin ruwan hallaka! Me yasa kake raye?!” Waye ya cece ka?! Waye yake baka kariya daga tsafina?!” Ta miƙe da sauri, ta taka gaba ta danna hannunta a tsakiyar madubin. Sai wani irin zafin wuta ya fesa mata – madubin ya ƙi bada cikakken bayani Ya ɓoye wani bangare. “Wannan tsafi ba cikakke bane… akwai wani karfi da ya hana ni ganewa...” A cewar Madam Nablah. Nan take siffar wasu fuska biyu suka bayyana a gefe: Nasreen da Asmeen. A ruɗe ta ce “Ƴaƴana!” Ta furta da ƙarfi. “Kuna tare da shi? Kuna kusa da mutumin da zai rushe mun mulki?!” Idanunta suka cika da wuta, kamar yadda ƙarfin jikin aljanu ke ƙara ratsa kanta. Tana jin wani mugun zafi yana tashi daga ƙasan cikinta. tana tangaɗi da haka ta zauna a wurin amma bata faɗi ba, sai dai ta farka da sabuwar murya, murya mai haɗe da na wani tsatso daga duniyar tsafi tana faɗin “Ba za ku yi nasara ba, Wannan ƙyauren nawa ne. Ruhi ba zai iya haskakawa a cikin duhu ba…” Madubin ne ya bushe da hayaƙi ya ɓace. Sai wata ƙaramar ƙwarya ta karye a gefe, Hannu biyu suka ɓullo daga ƙasa hannuwan aljanu suna miƙa mata wani baƙin zobe da wasu sabbin kayan tsafi. Madam Nablah ta ɗauki zoben ta cusa ɗaya a yatsanta, ta ce “Tasleem zata dawo gare ni… koda da jinin Amaar zan ɗaure zuciyarta!” Ta sa dariyar mungunta mai amo, ta ɗaga hannunta sama – wutar tsafi ta sake fitowa, tana zagaye dakin da wani sabo, mafi ƙazantar shiri... ƁANGAREN TASLEEM… Tana kwance a cikin bedroom ɗinta, tana numfashi da ƙyar. Gumi na keto mata, jikinta yana rawa, zuciyarta na bugawa da ƙarfi kamar zata fito daga kirjinta. Har yanzu bata manta da abin da ya faru ba, robot ɗin da suka rikide, murya mai ban tsoro, rawar duhu, da faɗuwarta daga saman beni amma abin mamaki ta farka lafiya. Sai dai akwai wani abu dabam da take ji a jikinta yanzu… wani nauyi a zuciya, kamar an cire mata wani ɓangare na rayuwa amma ta kasa sanin me ke faruwa. Ta zauna akan gado, ta riƙe kanta da hannaye biyu, tana kuka a hankali. “Wayyo Allahna… me nayi? Me yasa nake jin kamar akwai wani sirri da ya ɓuya cikin rayuwata? Kuma waye wannan mutumin da na harba? Waye shi a rayuwata?” Ta tuna fuskarshi, fuskar Amaar, fuskar da ke da wani sanyi da zafi a lokaci guda. Sai zuciyarta ta tsinke da ciwo. Idanunta suka cika da hawaye. “Na kashe mutum? Na kashe shi? Amma me yasa tun daga ranar dana gan shi nake jin wani abu dabam? Me yasa idan ya kalli idona nake jin tamkar ya san sirrina fiye da yadda ni kaina na sani?” Tana cikin wannan tunanin ne sai taga kyakkyawan locket (abun wuya) a gefen gadonta. Bata san daga ina ya fito ba. Tana ɗagowa, ta buɗe… hoton wata yarinya ce a ciki da yaro gud, Ita ce – Tasleem ce da wani yaro wanda ya haɗe da ita. Sai wani irin shocking ya daki zuciyarta. Sai zuciyarta ta fara bugawa da karfi ta ce “Wannan hoton… me yake nufi?! Wannan yaron…” Ina tunanin na san fuskar nan... amma ta ina? Me yasa yake min kama da…” Nan take ta fara jin jiri. Sai ta fadi a saman gadon, tana huci, tana fitar da gumi. Zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Kamar ƙwaƙwalwarta na ƙoƙarin faɗa mata wani abu, amma akwai wani abu da ke hana shi fitowa fili. A cikin baccin da ya ɗauke ta, ta fara mafarki. A mafarkin, ta tsinci kanta tana gudu a cikin jeji – tana gudu daga wani abu, amma daga can gaba sai taga Amaar tsaye, yana mata murmushi. A bayansa kuma akwai wata mace mai bakaken kaya, idonta jajaye kamar wuta… “Karki kuskura ki tuna!” “Kar ki gane waye shi… idan kika gane, rayuwarki zata ɓace!” – Muryar Madam Nablah ce. Ta kurma ƙara a mafarkin – sannan ta farka da ihu! Ta miƙe da sauri daga gado, huci na fita daga bakinta, hawaye na gangarowa. Ta dafe ƙirji. “Zan tafi! Zan tafi inda na bar shi. Ko da kuwa ya mutu ne – sai na tabbatar da hakan da kaina.” Da sauri ta saka hijabi, ta fice daga gidan zuciyarta cike da rudani da alhini, amma wani ɓangare na zuciyarta na kokarin farka da gaskiyar da aka daɗe ana ɓoye mata… NEXT NEXT NEXT SAI DAI KUYI HAƘURI YAU BANYI EDITING BA, KODA ZAKU SAMU TYPING ERROR KU SHARAR KAWAI😃😃.... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZauw 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 27 to 28 Tasleem na tafe da sauri kamar wadda gobara ke binta. Fuskarta cike da ruɗani da tarin tambayoyi, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Kusan ta yi kamar mai hauka, saboda abinda take ji, abinda take tunani—da kuma abinda take fargaba ta aikata. A daidai shiga falon gidan nasu kenan, sai taga su Nasreen da Asmeen na shigowa cikin gaggawa daga ƙofar baya. Da ta hango su, ta nufe su da sauri, jikinta na rawa. “Ina yake? Ina wannan mutumin? Daman yana raye? Na ji kamar yana kiran sunana… don Allah ku gaya mun gaskiya! Ku gaya mun shi ɗin waye!” Asmeen ta tsaya cak, tana kallon Tasleem kamar zata yi kuka, amma sai ta haɗiye kukan ta ce “Ke Tasleem, me kika aikata?! Shin kina da hankali kuwa?!” “Wato har ke Asmeen?” Tasleem ta furta tana kallon su da kuka, “Ni fa ban gane ba, kawai na ji wani abu dabam tun da na gan shi! Amma ban san me yasa na harbe shi ba… wallahi bazan iya rayuwa da wannan laifin ba!” Nasreen ta matso kusa da ita, ta kama hannunta cikin tausayawa domin sun gano yanzu duk abinda Tasleem ta aikata da taimakon tsafin da ya gusar mata da zuciya ne cikin basar wa ta ce “Laifi ki ka aikata! Kema kin sani. Kuma ki sani wannan mutumin ba kamar kowa bane! Amma ki daina tambaya… idan lokaci yayi, za ki gane shi.” Tasleem ta girgiza kai da ƙarfi, zuciyarta kamar zata tarwatse. “Toh gaya mun! Ku gaya mun kawai ko ya mutu ne?!” Asmeen ta juyo da sauri tare da faɗin “Ba zai mutu ba insha Allah, amma ki shirya fuskantar abinda kika aikata..." Tasleem ta sunkuyar da kai tana hawaye, tana jin nauyin abinda ta aikata ba don ta sani ba, sai don wani abu na ciki da ke hura mata wuta. Nasreen ce ta kalli Asmeen tare da girgiza mata kai alamar tayi shiru da wannan batun. ** A nan ne ƙarar buɗewar ƙofa ta katse su. Fuskar Madam Nablah ce ta bayyana, tana shigowa falon kamar guguwa Idanuwanta jajaye, fuskarta ba Annuri, kamar wadda ta dawo daga duniyar aljanu. Nasreen da Asmeen suka tsaya cak, jikinsu ya ɗan yi sanyi. Tasleem ta juyo da sauri, da mamaki a fuskarta ta ce “Mommy? Ina kika je jiya? Kuma me yasa fuskarki haka?” Madam Nablah ta wuce su kamar ba ta ji ba, idonta na ɗauke da wata ƙwayar duhu, kamar ba ta cikin hayyacinta, ta tsaya dab da fitilar falon, sai ta juyo a hankali, ta kalle su ɗaya bayan ɗaya. “Me kuke aiwatar wa a cikin gidan na? Me kuke ɓoye mun?” Nasreen ta tsaya da ƙarfi, tana fidda numfashi ta ce “Ba zaki gane ba Mommy… sai ranar da Allah ya nuna miki gaskiya.” Madam Nablah ta ƙura mata ido, ba tare da tace komai ba. Idanunta sun nuna alamar karin haɗari da bacin rai. ** Abeesh da yake jin hayaniya a ƙasa tun daga ɗaki, ya leƙo, amma ganin ya hango Madam Nablah ne yasa ya juya da sauri ya koma, Bai taɓa jin zuciyarsa ta ƙone kamar yau ba. duk kyautatawar da aka yi mata amma hakan bai hana ta hallaka mahaifinsa da ɗan uwansa ba. Tasleem ce ta katse su da kuka tana faɗin "amm inason ganin sa, ba'a son raina na harbe shi ba, Allah yasa bai mutu ba...." Madam Nablah wacce take shirin barin wurin jin kalaman Tasleem ne yasa ta dakata, a slow ta juyo tana tambayar su "wa kika harba?..." Da sauri Nasreen da Asmeen suka ce "babu komai" Madam Nablah hannu tasa ta juyar da Tasleem tana son ganin abinda ya faru ta cikin ƙwayar idanuwan ta, cikin fushi da tashin hankali Tasleem ta hankaɗe mahaifiyar su tana faɗin "kar ki taɓa ni domin ke Annoba ce, ki fita daga cikin rayuwar ta na tsane ki, ina ji a jikina cewa kin raba ni da abubuwa mafi muhimmanci a cikin zuciyata, ke kika kashe mana mahaifin mu sannan kika ɓoye Abul Abeesh a cikin ɗakin duhu, bai kamata na cigaba da ɓoye waɗannan sirrika a cikin zuciyata ba, ki sani sai na kawo ƙarshen ki...." Nasreen da Asmeen sumar tsaye suka yi jin mutuwar mahaifinsu da kuma Abul Abeesh yana raye, Madam Nablah zaro idanu tayi waje tana mamakin jin waɗannan kalamai daga bakin Tasleem.... Tasleem ta cigaba da cewa "sannan akwai abinda kika raba ni dashi wanda yana da matuƙar mahimmanci a rayuwa ta, tabbas na gan shi a cikin mafarki na kuma na ganki kema da wasu rikitattun idanuwa, meye sunan sa? meye sunan sa? sunan sa A.. A.. Am, yana zuwa mun a matsayi spirit, shi ɗin haske ne wanda na tabbata da wannan hasken zai tarwatsa baƙin tsafin ki..." Madam Nablah kanta ba ƙaramin ɗaukan zafi ya yi ba, cikin fushi ta lumshe idanuwanta lokaci guda ta buɗe su da wani irin jajayen idanuwa, idanuwanta sai farfatsin wuta yake, a tsawa ce ta yi wa su Nasreen magana da cewa "ku fita ku bani wuri yanzun nan"... cikin wata ƙatuwar murya, yanzu ta fito a asalin ta na matsafiya... Nasreen da Asmeen haka jikin su yake ɓari cikin tsoro da fargaba suka yi waje da gudun gaske... Itama kuma Tasleem riƙo hannunta tayi tana jan ta har ta kaita can room ɗin su ta wurga ta saman gado... Madam Nablah tsabar tashin hankalin da ta shiga ta ma rasa abinda zata yi haka tabar ɗakin a fusace tare da rufe ƙofar... Amaar yana kwance akan gadon sa ba abinda yake tunawa illa Tasleem, ya runtse idanu, yana furta a zuciyarsa “Tasleem… ki yafe mun. Lokaci yana zuwa. Lokaci da komai zai bayyana. Amma yanzu... Sirrinmu yana da daraja.” Madam Nablah na zaune a ɗakin tsafinta wanda ke cikin ɗayan ɓangaren gidan da ba kowa ke iya shiga ba. ɗakin duhu ƙirin amma dakin na ɗauke da hasken fitilar tsafi—wato wuta mai shuɗar haske da ke fitowa daga ƙasan wani tafki mai duhun ruwa. Ta durƙusa gaban madubin tsafi wanda yake rataye cikin iska, ba tare da ya taɓa wani bango ba. Duhu ne ya mamaye zagayen madubin, sai hayaƙin da ke fitowa daga hanci da bakinsa yana motsi kamar numfashi. Madam Nablah ta daura hannunta biyu a saman madubin, ta lumshe ido, sannan ta fara karanto wani irin yare da ba a saba jin shi ba tana furta “Naqaatu-t-Tilum... Sarwaqeen Al Jabaroot... Izran Tumma... Qadhaab!” Sai wani ƙarin hayaki mai ƙanshi irin na jikin bil’adama ya turnuƙe madubin. A take, madubin ya fara juyawa, yana haska launuka dabam-dabam. ** “Na ce ku bani haske... Ku bani abin hangowa! Ina son ganin wanda ya juya tsarina, wanda ya tsallake mutuwa! Waye wannan mutumin? Waye wannan da ke ɗauke da ikon da bai kamata ya rayu ba?” A cewar Madam Nablah. A hankali, madubin ya fara nuna hoton Amaar a kwance, yana magana a cikin zuciyar sa. Amma fuskar Amaar ta bayyana ne cikin duhu—madubin na ƙoƙarin hana Madam Nablah ganin cikakken fuskar sa. Madam Nablah ta ƙara daka ƙara da cewa “Ku buɗa min! Na mallaki ikonku! Na rage rayuka fiye da dubu, ba ku isa ku ɓoye min ba!” Sai kuma wani murya mai zurfi ya fito daga cikin madubin, murya mai girgiza ƙwaƙwalwa ya furta “Ba komai zaki gani ba… yana da kariya, wanda ba za ki iya keta ba.” Madam Nablah ta ja da baya da sauri, hannunta na rawa, idanuwanta na ƙara huda da baƙin iska. Ta ce “Kariya? Waye zai iya kare wanda na hallaka?” Madubin ya koma duhu, ya ɓoye komai. A take, idon Madam Nablah ya fara kadawa da alamar fushi. Ta juyo daga gaban madubin, ta buge wani kwano da ke gefenta. “Wannan kuwa… bai mutu ba! Wannan mutumin da Tasleem ta harba… akwai wani abu da ban gane ba!” Ta fara kaiwa da komowa a dakin, tana saƙar zare a cikin zuciyarta. “Tasleem! Yarinyar nan fa ta fara juya ni. Sannu a hankali mafarkinta na zama gaskiya. Idan ba a hanzarta ba, zata zama babban barazana gare ni!” Ta tsaya cak. Wani aljanin gefenta ya bayyana daga ƙungurmin inuwa. Ba shi da fuska mai bayyana kamar wata inuwa ce dake numfashi. “Me kike so mu yi da ita?” – in ji muryar aljanin. Madam Nablah ta kalli inuwar da ƙyam, sannan ta ce: “Na shirya. Lokaci yayi da zan sake haɗa wani tsafi—wanda zai mantar da Tasleem komai. Sai dai kafin nan, dole na fara da wanda ya juya makirci na… duk da ban gane waye bane tukuna.” Ta juyo gaban madubin tsafi, ta ce da ƙarfi: “Zan tono shi da hannuna! Ko da kuwa daga ƙasan ƙasa yake…” ** A wannan lokaci, Madam Nablah bata san cewa ƴaƴanta suna kusa da tono sirrinta ba. Amma sai dai wani abu yana yawo a zuciyarta—ana matsa mata daga wani ɓangaren da ba ta fahimta ba. Kuma ita kanta tana fara jin tsoron wani abu: ta fara jin ƙyamar zuciyar Tasleem. Madam Nablah ta fito daga dakin tsafinta da takalman ta masu tsini suna kara-kara akan tiles din gidan. Fuskar ta cike da damuwa da kulle-kullen mugunta. Duk da bata iya ganin fuskar Amaar ba a cikin madubin tsafi, amma zuciyarta na kara tabbatar mata da cewa akwai wani mai iko da ke kawo cikas ga tsarinta, kuma yana kusa da ƴaƴanta. Ta iso falon, hasken shuɗi daga hayakin tsafi yana yawo a cikin inuwa. Ta zauna akan kujera cikin izza, sannan ta kalli bango kamar tana ganin ta cikin shi. “Na tabbatar ɗaya daga cikin su ne. Ko dai ɗaya daga cikin ƴaƴana, ko kuma wani daga cikin waɗanda suke yawo kusa da su. Amma wanda ya dawo rayuwa… shi ne mai haɗari.” Ta ɗauki wani ƙaramar faranti mai madubi daga saman wata kwandon karfe. Ta zuba wani ruwa kamar jinin jaki a ciki, sannan ta ɗora farantin a saman tafin hannunta. Tana faɗin “Dole na yi wani abu kafin su gane komai. Idan har shi mutumin da suka ce an harba bai mutu ba, to Tasleem zata fara tuna da shi. Kuma idan hakan ta faru…” Ta lumshe idonta, sai ga wani jini ya fara fitowa daga hancinta. Aljani ne ya fara karɓar ikon zuciyarta. Muryarta ta canza, ta koma kamar muryar tsohuwa daga wani zango daban. “Zamuje a hankali... amma da tabbatacciyar mugunta.” Ta dafa ƙirjinta, idonta na rawa. Sai wata murya daga cikin kanta ta ce: “Nablah, lokaci yayi da zaki sake kunna Randa-t-Tasfir. Ki shafa mantau a zuciyar Tasleem. Ki goge komai da zai tuna mata da wannan mutumin!” Madam Nablah ta ɗauki wasu garwashi da ganye, ta sa su a wani kwanon zinariya. Ta kunna wuta, sannan ta zuba wani ruwa wanda ya fara baƙar da iska gaba ɗaya. Ta furta “Tasleem! Kina jin na? Daga yau, duk abinda ke da alaƙa da mutumin nan... zaki fara mantawa da shi. Kamar bai taba rayuwa a zuciyarki ba!” Ta daka ƙara, idonta ya ɗauke da haske. A wani lokaci na ɗan kankanin lokaci, wani hazo ya tashi daga gindin falon da Tasleem ke ciki. ** A gefe guda kuwa... A cikin ɗakin Amaar, yana kwance, sai yayi wani nishi mai nauyi. Idonsa ya buɗe kadan, yana jin wata ƙuna a ƙirjinsa. Kamar an taɓa sa shin. Ya fahimci cewa ana ƙoƙarin juyar da tunanin Tasleem. “Wannan warin... tsafi ne... ita ce...” – ya furta a hankali. Ya ɗan yi ƙoƙarin tashi, sai dai jikinsa bai gama karfi ba yana furta "Dole in kare ta kafin ta manta da ni gaba ɗaya!" ** Madam Nablah ta sake lumshe ido, tana jin nasara a zuciyarta. Amma abinda bata sani ba shine: makircinta yana samun cikas daga wani ƙarfin da ba a iya gani da ido—karfin da ke cikin zuciyar Tasleem da Amaar... wanda zai iya karya kowanne irin tsafi..... Lokacin yamma ya gabato Rana ta fara dusashewa, iska tana kadawa da sanyi mai ɗauke da wani warin tsami. Tasleem tana cikin ɗakinta, zaune a gefen gado, tana kallon bango da zuciya mai nauyi... Idonta a lumshe, amma hankalinta bai kwanta ba. Kamar wani abu na yawo a zuciyarta yana karairaya mata tunani. Tana ƙoƙarin tuna fuskar mutumin da ta harba—wanda ke biyo mata a mafarki da a zahiri. Amma yanzu… komai na fara dushewa. Cike da damuwa take faɗin “Shin... har gaske na taba sanin shi? Me yasa nake jin kamar... ya shuɗe ne a raina?” Ta dafe kanta. Da gaggawa, idanuwanta suka buɗe. “Sunansa ma... sunansa?” Kamar wata zararriya tana tunanin abubuwa da yawa a cikin zuciyar ta, Tana ƙoƙarin tunawa, amma zuciyarta na hana ta. Fuskar da ta saba gani duk lokacin da ta lumshe ido yanzu kamar hazo take gani Ta ce “Wayyo Allah... menene ke faruwa dani?” Ta miƙe daga inda take, ta nufi madubi tana kallon kanta. Amma da ta kalli fuskar ta sosai… sai kawai taga wata surar mace a cikin madubin tana murmushi. Amma wannan murmushin... bai da armashi, yana da shaiɗanci da ruɗani. Sai kwatsam, madubin ya fashe da wani irin ƙara, wani hazo ya fito daga ciki, ya rufe fuskar Tasleem. Ta ɗan zabura baya, tana girgiza kai tare da faɗin “Babu wanda zai iya... juya zuciyata... babu wanda zai manta mun da shi...” Amma a cikin zuciyarta, muryar wani da ba nata ba take ji ana furta “Babu Amaar. Bai taba wanzuwa ba. Wannan tunanin karya ne. Wani abu ne kawai da kike sawa a ranki... kuma lokaci ya yi da zaki manta da shi har abada.” A daidai lokacin, Nasreen da Asmeen suka dawo gida. Suna shiga cikin falo, suka ji sanyi mai ɗauke da warin wani abu kamar ƙonanniyar ganye. Suka kalli juna. Nasreen ta ce “Asmeen... kina jin wani abu?" Asmeen ta ce “Ina jin kamar tsafi. Dama kinsan gidan nan baya zaman lafiya.” Suka nufi ɗakin Tasleem, suna kiran sunanta. “Tasleem! Kina lafiya?” “Ki buɗe mana ƙofa...!” Amma Tasleem tana tsaye a gaban madubi, idonta baƙi ƙal-kal, tana kallon kanta kamar wata da bata gane kanta ba. daga nan sai hawaye suka fara gangarowa daga idonta. Ta kama kanta da hannayenta biyu tana faɗin “Ni wacece ne? Waye nake nema? Me nake tunawa ne...? Shin ina mafarki ne?” Nasreen daƙer suka buɗe ƙofar suka shige da sauri, suka ruga da gudu tare da rungumar ta. Nasreen ta ce “Tasleem! Menene ke faruwa?” Itama Asmeen tambayar ta tayi tana faɗin “Me ya sameki haka?” Tasleem ta kalle su, idonta cike da hawaye ta furta “Waye wanda na harba? Me yasa nake jin kamar na rasa wani bangare na zuciyata? Me yasa nake jin kamar an sace ni... daga ciki?” Asmeen ta kalli Nasreen, zuciyarta cike da tsoro. Nasreen cikin kuka take faɗin “Tsafi ne... wallahi tsafi ne ke kokarin karya ta. Amma bazan bari ba.” ** A gefe guda... Madam Nablah tana zaune a ɗaki mai duhu, tana jin murya cikin kanta na faɗin: “Zata fara mantawa... zata daina tunawa... lokaci yana tare da mu.” Amma kuma... wani canji ya fara tasowa daga zuciyar Tasleem. Wannan baƙin hazo da tsafi… yana samun cikas daga wani ɓangare na ruhinta da tsafi ba zai iya shafanta ba, tsatsan ƙauna da soyayyar Amaar da bata da izinin mantawa da ita. ★★★ Yamma ta ƙure. Rana ta narke cikin duhun dare. A cikin ɗakin Amaar, wutar fitila tana kunne da hasken rawaya, yana zaune kan gado, bandage har yanzu na manne a kirjinsa, idanunsa a lumshe, numfashinsa mai nauyi. Zuciyarsa na tafasa da abubuwa da dama, amma wani abu daban ya fara ƙona shi tun daga ciki… Yayi ƙoƙarin rufe idanu domin samun natsuwa, amma a zuciyarsa yana jin wani irin bugun bugun zuciyar wata – bugun zuciyar Tasleem. “Tasleem...” ya furta a hankali. “Ina jin kamar tana cikin haɗari...” Wani irin ƙamshi mai wari da tsami ya doki hancinsa duk da babu komai a ɗakin. Sai zuciyarsa ta fara bugawa da ƙarfi. “Ba daidai bane... zuciyarta na ƙara shigewa cikin duhu. Wannan ba Tasleem ɗina bace... an fara rugujeta daga ciki...” Ya miƙe a hankali, duk da jikin nasa har yanzu yana rauni. Amma zuciyarsa ta yi nauyi da damuwa. Ya isa gaban madubi yana kallon kansa, ya dafe gefen bango da hannunsa ɗaya, idanunsa sun canza launi, wani haske mai kama da ruwan sama ya fara bayyana a jikin sa. A hankali ya furta “Na sha alwashin kare ta... ko da da rai na ne...” Sai kawai ya fara jin wani murya daga cikin kansa – muryar wani wanda ya ceci rayuwarsa a lokacin da aka jefa shi cikin ruwa shekaru ashirin da suka wuce. “Lokaci ya kusa, Amaar. Ikonka yana dawowa, amma ƙiyayya da soyayya sun fara yakar juna a zuciyar Tasleem. Idan tsafi ya cinye zuciyarta bazata tuna da kai ba… sai dai ka rasa ta har abada.” Ya dafe kirjinsa. “A’a... bazan bari hakan ta faru ba. Ko da zata ƙi ni... zan kareta. Amma ban isa na bari ta mutu da bakar zuciya ba...” A cewar Amaar. Sai kawai wani haske mai ɗumi ya fara fita daga hannunsa na hagu, yana yawo a cikin ɗakin – wani ƙaramin iftila’i da ya nuna cewa ikon da aka ɗora masa a lokacin da aka ceci rayuwarsa yana dawowa a hankali. Ya furta cikin salo: “Dole in gane hanyar shiga cikin mafarkinta... domin a can za a yi yaƙin farko.” A wannan lokacin, wayarsa ta ɗauki kira – Nasreen ce ke kiran sa da gaggawa. “Amaar! Ka shirya, mun dawo gida... Tasleem na cikin wani mummunan yanayi! Mun iso yanzu amma ba zamu iya samun taimako ba… sai kai!” Cikin rawar jiki da ƙarfin zuciya, ya ce: “Ki ƙara riƙe ta, ban da kowa da zai iya fitar da ita daga wannan duhun sai ni.” Ya miƙe da ƙyar, ya ɗaura rigar sa, duk da jiki yana rauni, amma zuciyarsa ta fara sauya tsari – daga rauni zuwa azama yana faɗin “Tasleem... ba zan bar ki a hannun zuciyar tsafi ba. Komai zai faru, sai kin tuna da ni.”...... A ɗakin ta dake saman bene, Tasleem ta haye gado tana karkarwa, idanunta sun lulluɓe da hawaye, zuciyarta kamar zata tarwatse. Amma abun mamaki – tana jin wani abu a ranta, kamar ana tunkudata cikin wani wuri mai duhu, amma daga ciki akwai murya – muryar da ba ta san daga ina take fitowa ba. “Ki guje wa hasken zuciyarki, Tasleem… ki rungumi duhu… ki yarda da ƙiyayya, kin fi ƙarfi idan zuciyarki ta cika da tsana...” Tana riƙe kanta, tana girgiza kai: “A'a… ba haka nake ba. Ni ba mugunwa bace... Me yasa nake jin kamar zuciyata tana canzawa? Me yasa nake jin kamar bana ƙaunar kowa... har kaina ma?” Nasreen da Asmeen sun juma da barin ɗakin sakamakon tiririn wutar ɗakin, gaba ɗaya tsoro ne a cikin zuciyoyin su... Tasleem ita kaɗai ce a ɗakin kuma daman ita kaɗai ake buƙata. Wata ƙatuwar guguwa ta mamaye ɗakin ta – hasken wuta ya ɗauke, labule ya fara yawo akan iska, zafin daki ya hauhawa. Cikin wannan yanayi, ta fara ganin madubi a bango yana sauya launi – ya koma baƙin zurfi kamar ramin shaidanu. Sai kuma ta fara ganin hoton kanta a cikin madubin – amma ba Tasleem bace kamar yadda ta san kanta ba. Wata sigar ta ce – idanu jajaye, gashi a warwatse, tana murmushi da baki cike da jini. “Kece Tasleem na gaske... Kece zuciyar da aka daƙile. Ki zo ki karɓi ikona... Ki manta da Amaar, ki manta da kowa...” Tasleem ta ja da baya tana kuka, ta durƙusa a ƙasa, tana rokonsu su daina: “Ku barni! Ku bar zuciyata! Ni ba haka nake ba!” jikin ta ne ya fara rawa da ƙarfi, kamar wutar lantarki na shiga jikinta sai da ta saki wani irin ƙara mai ban tsoro – wani haske ya fita daga cikinta na dan lokaci, ta sake faɗuwa. Wannan tsafi na ƙoƙarin cire hasken da ya rage a ranta – ƙaramin haske wanda har yanzu bai mutu ba. A ƙasan falo kuma su Nasreen da Asmeen ne suna cikin firgici. Sai da suka yi yunƙurin hayewa sama, sai suka tsaya cak – saboda ganin Madam Nablah tana tsaye a tsakiyar falo da idanu kamar ba na mutane ba, tana kallon saman bene, tana karanto wata ruɗaniyar addu’a cikin yaren aljanu. Nasreen ta matsa kusa da Asmeen cikin muryar tsoro: “Asmeen... mece ce wannan murya haka? Kuma me ya faru da Mommy...? Kamar ba ita bace...” Asmeen ta ce: “Idan har Tasleem tana sama yanzu… to akwai buƙatar mu dakatar da wannan... Amma ba mu da iko...” A wannan lokacin ne su ka ji ƙarar motar Amaar ya tsaya a ƙofar gida. Lokaci ya ƙure ko Amaar zai iya tsallake duhun da ke hana kowa hawa sama, ko kuma Tasleem zata faɗa tarkon da Madam Nablah ta kulla tun tuni. “Tasleem... ki tsaya har zuwa isowata,” Amaar ya furta a zuciyarsa, yana kallon saman gidan da hayaki da hasken duhu ke fitowa… Amaar ya fito daga motar da sauri. Da kallo guda ya gane gidan na cikin wani yanayi da ba a saba gani ba hayaki mai duhu yana fita daga tagogi, iska tana kadawa kamar hadari na shigowa, kuma wutar rana ta ɓace daga saman gidan duk da gabar rana ce. "Tasleem..." ya ambaci sunanta da ƙasa cikin murya, idanuwansa sun cika da tsoro da damuwa. Kamar wani haske daga sama, sai Amaar ya fara jin wata irin ƙara a kunne, kamar ƙira daga wani ruhin tsarkaka – kira wanda ya saba jin sa tun lokacin da aka ceci rayuwarsa a cikin ruwa shekaru da suka wuce. A wannan lokacin ne wani murya mai zurfi ta dawo masa a rai: "Lokacinka yayi, Amaar. Ka fuskanci duhun da ya raba ku... Ka shiga da zuciya tsarkaka, domin kai kaɗai ne zai iya warware abinda aka daɗe ana gina wa." Amaar ya lumshe ido, ya dafa ƙirjinsa inda aka harbe shi. A wurin nan yake jin ƙarfinsa – ruhinsa yana ɗauke da haske wanda ke iya karya tsafin da Madam Nablah ta ƙulla. Sai da yaja numfashi, ya furta: “Bismillahir Rahmanir Rahim... Allah ka bani ikon tsallake duhun da zai hana ni ceton zuciyar da ta rasa kanta.” Da haka ya taka ƙafar sa cikin falo. Yayin da ƙafarsa ta taka ƙasa – kamar ƙasa ce ta wani duniya. Lokaci ya tsaya, iska ta tsaya, sai wata ƙara ta tashi daga cikin hayaƙi: “Wannan gida ba naka bane, ruhun wuta zai karyaka, ka janye Amaar!” Madam Nablah ce ta furta hakan da wata murya da ba kamar ta ɗan adam ba. Idanunta sun yi jajaye, tana tafiya a hankali zuwa ga Amaar, tana ɓalle masa karatu a harshen aljanu. Amma Amaar bai ja da baya ba. Ya matsa kusa da ita. Kowane taku yana fitar da haske daga ƙafarsa – kamar yana takawa a wani wuri na tsarki. Ya tsaya gaban Madam Nablah: “Na dawo ba don na yaƙe ki ba, sai don na ceci abinda kika kusan lalata... Ina neman ceto Tasleem daga duhun da kika jefa ta ciki!” Kafin Madam Nablah ta yi wani ƙari, Amaar ya furta kalmomin addu’a da aka koya masa lokacin da ya rayu bayan fadowa cikin ruwan nan, kalmomi da ke iya karya tsafi mai duhu: “Allahu Akbar kabīra, walhamdulillāhi kathīra, wa subhānallāhi bukratan wa aṣīla...” Haske ya buɗe daga jikinsa, ya haura sama, ya daki tagar da ke zuwa sama inda Tasleem ke kwance cikin suma. Wata ƙara ta tashi daga cikin bangon madubi — madubin tsafin ya tarwatse! Madam Nablah ta ja da baya tana kururuwa: “Kayi kuskure Amaar! Kai ne silar lalacewata... Amma ba zaka fitar da ita daga hannuna ba!” Sai ga Abeesh ya fito daga ɗaki, cikin fushi da ƙarfin zuciya. Ya tsaya gefen Amaar: “Zan tsaya tare da kai Yaya... Duhu bai isa ya cinye gaskiya ba.” Nasreen da Asmeen suma sun tsaya a ƙofa suna karanta Ayatul Kursiyy da Suratul Falaq a ƙasa cikin fargaba. Haske yana cigaba da bayyana... Saman ɗaki kuwa, Tasleem ta fara motsawa. Idanuwanta ya buɗe amma har yanzu tsananin hayaƙi da duhu ya rufe ta... Jirjirin iska ya fara kadawa cikin falon, ƙarar murya da karatun Ayatul Kursiyy daga bakin su Nasreen da Asmeen na karuwa, Abeesh ya tsaya gefen Amaar yana girgiza kai cikin kuka, zuciyarsa cike da jin zafin ƙaddara da yanda duniya ta juya musu, amma a tare da dukkan su guda hudu, haske yana fitowa daga ƙasan ƙafafunsu, yana tunkuɗe duhun da Madam Nablah ta shafa. Madam Nablah tana ja da baya, tana furta kalmomi cikin harshen da ba a fahimta, jikin ta yana ƙara canjawa – kamar ba ta mutum ba, ta fara ɓarin jini a bakinta da hancinta, hakan ya nuna cewa ƙarfin Amaar yana cin galaba akan tsafinta. Amaar ya kalli sama, inda ɗakin Tasleem ke sama – ya lumshe idonsa. A zuciyarsa ya ce: “Allah ka karya duk abin da ke tsakanin mu da ita. Ka warware igiyar da aka ɗaure rayuwarmu da ita ta ruɗu.” Sai da ya taka step ɗaya, ya fara hawa matakalar bene... Amma kafin ya kai ƙofar matakala – ƙarfin shocking ya saukar masa daga sama! Zuuuummmm!! Wutar da Madam Nablah ta haɗa shekaru ashirin da suka gabata don hana shi da Tasleem haduwa ta tashi daga cikin ƙasa ta buge shi da ƙarfi! Amaar ya durƙusa ƙasa da ƙyar, ƙirjinsa yana bugawa, numfashinsa yana fita kamar wani wanda aka yi masa lantarki. “Subhanallah…” ya furta a hankali. Sai Abeesh ya nufo shi, amma shi ma shocking ɗin yana so ya buge shi, sai dai Amaar ya daga masa hannu: “Kada ka kuskura ka taɓa ni yanzu… wannan shirme ne da aka haɗa shekaru da suka wuce... Sai ni kaɗai zan iya fasa shi.” Ya dafa ƙirjinsa. A can ya ke jin wani tsarki na waje da baƙin ciki na ciki – rikicin da yake cikin zuciyarsa yana neman karya masa ƙarfin ruhi. Idanunsa sun fara kadawa da hawaye, ya tuna yanda suka shaƙu da Tasleem tun suna yara... yanda suka rike hannun juna da dariya a bakin su... yanda take cewa masa: "Amaar, karka taɓa bari na..." Sai ya furta da ƙarfi ya ce “Na rantse da Allah albarkacin wannan rana... ba zan taɓa barin ki ba!” Da haka sai ya miƙe da ƙarfin zuciya, ya cigaba da hawa matakala, kowane mataki da ya taka – shocking yana bugunsa – amma haske yana ƙara fitowa daga jikinsa. Tsafi yana ƙonewa kamar ganyen busassu. Kafin ya kai sama, wani sabon salo ya bayyana a cikinsa – kalmar da ya daɗe bai furta ba ya furta a zuciyarsa: "Ya Allah, idan har ni ba zan iya ceton ta ba... ka tura wanda zai iya. Amma kar ka bar rayuwarta cikin duhu!" Da haka, Amaar ya isa ƙofar ɗakin Tasleem. Ya jawo handle ɗin ƙofar a hankali… ƙofar ta buɗe da ƙara kamar ana warware sarƙar duhu. Tasleem na kwance a kasa cikin wani zobe na hayaki, idanunta a lumshe, jikin ta yana rawa, sai wata murya daga cikin bangon dakin ke cewa: “Kar ka taɓata, Amaar... idan kuka kusanci juna – za ku ƙone tare!!” Amma Amaar bai tsaya ba. Ya tako a hankali, yana sauke ajiyar zuciya. Ya durƙusa a gabanta. Yana kallonta cike da tausayi. “Zan fi son in kone tare da ita, fiye da barin ta cikin duhu.” Da hannunsa ya mika ya dafa hannunta... Zuuummmmmmmm!!! Wani karfi na shocking ya fasa dakin gaba daya! Haske ya tashi daga hannayensu, duhu ya washe! Idanun Tasleem suka buɗe cikin wani irin girgiza... suka zuba ido cikin na juna… Shin zata gane Amaar ne? Shin ruhinta zai tuna da shi kafin tsafi ya sake mamaye ta? Shin Madam Nablah zata ƙara wani sabon farmaki? *GAREKU MASU KARATU ASHA KARATU LAFIYA ....* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 29 to 30 ★★★ Tasleem ta zuba idanu cikin na Amaar, idanu masu cike da hawaye da hasken da ke tasowa daga ƙasan ruhinta. Wani sauti mai rauni ta fito daga bakin ta, kamar tana ƙoƙarin fadar wani abu, amma muryarta ya makale. Amma cikin zuciyarta, wata ƙwaƙwalwa ta fara motsawa... wani abu da ba a manta shi da sauƙi ba. “Amaar...” Kalmar ta fito daga bakinta cikin tattausar murya, Amaar ya ji ta kamar an buga gangar farin ciki a kunnen sa. Idanunta sun cika da hawaye. Wani ɓangare na zuciyarta na kokarin faɗuwa cikin duhu, amma wani ɓangare kuma – hasken da ke fitowa daga hannun Amaar – na tunasar da ita soyayya, amana, da wani alkawari da suka ɗaura tun suna yara. Madubin bangon ya fara fashewa gaba ɗaya. Wata murya mai ƙarfi ta fito daga cikin duhun: “A'a! Wannan ba zai faru ba! Zuciyarta ta nawa ce! Na shafe komai da kuke kira ƙauna! Babu wuri gare ka a zuciyarta!” Muryar Madam Nablah ne. Madam Nablah ta haura sama cikin siffar da ba mutum ba – idanuwanta jajaye kamar wuta, fuskarta na nuna zafin tsafi da haushin haske. Amma kafin ta karasa kusa da su, wata gagarumar igiyar haske ta haska dakin gaba ɗaya! Wani murya daga sama – mai laushi kuma mai ƙarfi – ta busa kamar iska, tana cewa: “Lokaci ya ƙare, Nablah. Tsafi ba zai iya shafe abinda Allah Ya rubuta ba. Zuciyar da aka haɗa da gaskiya ba za ta taɓa zama duhu dindindin ba.” A wannan lokaci ne Amaar ya daga hannunsa na hagu – inda ikon da aka ɗora masa ya fi ƙarfi. Haske ya bayyana daga can, kamar hasken safi ya bayan yanzu dare ne, Ya ce da karfi: “Ki bar mu haka Aunty Nablah! Tsafinki ya ƙare – zuciyar Tasleem ba wurinki bace!” Madam Nablah tayi ƙara mai tsayi da zafi – jikin ta ya fara tarwatsewa cikin hayaki. Wutar dake fitowa daga cikin jikinta ta dawo masa, Cikin wani kakkarfan ƙara ta bace gaba ɗaya cikin hasken da Amaar ya bayyanar, kamar ba ta taɓa wanzuwa ba. Zuuuwwwwww! Duhu ya ɓace. Gidan ya koma kamar yadda yake. Hayaki ya washe, Tsit ya sauka – tsit ɗin da ke bayyana ƙarshen gwagwarmaya.... Amaar yana riƙe da hannun Tasleem. Ita kuma, idanunta sun cika da hawaye, tana kallon sa ba tare da rudani ba. Tana jin numfashinsa, kuma zuciyarta na amsa kira – kira na ƙwaƙwalwa, soyayya, da alkawari. “Amaar… na tuna. Na tuna komai, na tuna wallahi, kai ne Mommy na ta jefa cikin ramin ruwa sannan ta canza daga mutum zuwa dabban daji, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni mi musiba ti wa aklif li khairan min ha..." A lokacin ta fashe da kuka. Ya jawota jikinsa, duk da har yanzu yana ɗan jin karamin wutar shocking har yanzu, amma bai bar riƙonta ba. "Ki kwantar da hankalin ki, ban mutu ba, na dawo gare ki my Tasleem, kuma nace miki ba zan taɓa barin ki ba, na dawo kenan....” Tasleem tana kuka ta ce "Ya Amaar nayi kewar ka sosai, ka dawo gare ni amma nayi kuskure rashin fahimtar ka, kayi hakuri Ya Amaar na aikata kuskure..." Toshe mata baki ya yi tare da faɗin "ki dakatar da wannan shirmen nakin, ki kwantar da hankalinki babu abinda zai ƙara faruwa da ke, sai dai mu tsara yanda zamu gudanar da sabuwar rayuwa ...." Tasleem tana kuka ta rungume shi sosai... Asmeen, Nasreen, da Abeesh sun hau bene da sauri. Da suka gan su riƙe da juna cikin dakin da aka cika da duhu kafin yanzu, suka tsaya cak da hawaye a idanu, zuciyoyinsu cike da mamaki da farin ciki. A ƙasa kuwa, wani ƙaramin wuri ya buɗe – kamar ƙofofin aljanu – daga cikin falo. Amma kafin wani abu ya fito, wani sautin ƙaho na haske ya buɗe sama, yana hana duhun sake hawa. Haske ya cigaba da cika gidan, kamar ana wanke dukan ƙwayoyin cutar da suka jima a can. Tsafaffen gida ya dawo gida. Haske ya dawo. Gaskiya ta yi nasara akan tsafi. --- Kwana biyu bayan haka... Tasleem na zaune a gefen ruwan swimming da ke bayan gida, tana kallon ruwa, hannunta na cikin na Amaar. Sunyi shiru na lokaci mai tsawo, kafin ta ce cikin sanyi: “Duk lokacin da zan fara mantawa da wacece ni... kai kake tuna min.” Amaar ya ce, yana kallon ta da murmushi: “Saboda zuciyarmu daya ce. Kuma idan ina da rai – zan kasance a kusa da ke.” A wannan lokacin wuni suka yi a tare wuri ɗaya..... ★★★★★ Ɓangaren Shaprees Duk abubuwan da yake faruwa a gidan Madam Nablah ya sani amma sai dai bai ɗauki hakan a matsayin damuwar sa ba, abinda ya kawo shi cikin ahalin su shine ɗaukar fansa, har yanzu akwai wannan ƙudirin a zuciyar sa, kuma ya shirya akan mallakan tsafi shima, yana son ya karɓi ikon tsafi saboda wata manufar sa, kuma ya sa a ransa cewa sai ya dawo da Sophia rayuwa..... Madam Nablah ta ajiye makamin yaƙin ta akan Amaar a wannan lokacin domin sai ta yi shiri na gaske amma har yanzu ƙiyayyarsa ruruwa yake a cikin zuciyar ta, ta koma kan Shaprees domin amsa ƙiransa, kallo ɗaya tayi masa ta gama karantar sirrin zuciyarsa na son karɓan tsafin wuta domin dawo da Sophia matar sa, Madam Nablah maimakon taji wani abu a ranta sai ma ta ƙarfafa masa gwiwa akan karɓa masa tsafi a wurin shugabanta ZULQARNAIN. Bayan kwana biyu ta shirya kai shi wurin tsafin ta. Idan ya tuna wannan ranar, yakan ji kamar ya haukace Daren da Shaprees ya rasa Sophia, zuciyarsa ta mutu kafin jikinta ya mutu. Wani murɗaɗɗen baƙin ciki ya shaƙe zuciyarsa. Bai gane yadda aka kashe matarsa ba, amma wata mata mai idon zinariya ta bayyana a lokacin da zuciyarsa ke tsaka da faɗuwa. Ita ce Madam Nablah. A yayin da yayi shiru zuciyarsa tana tuna masa da wasu abubuwa da yawa, kwatsam ya ji Madam Nablah ta furta "Ka rasa? Ina jin wannan azabar," ta ce cikin wata murya mai zuma amma mai daɗin daci. "Amma akwai hanyar da za ka ƙwato darajarka—da ikon fansa." Shaprees bai ce komai ba. Amma ido ya cika da shakku da hasarar da yake son mayar da fansa. “Zan kaika wajen wanda ya bani iko. Idan ka dace, zai baka wuta.” --- A Ƙasar Tsafi Sun sauka a wani wuri mara rana, inda haske ke fitowa daga harshen wuta da ke yawo a ƙasa kamar kogi. Wani katafaren mutum mai jikin toka da ido kamar gawayi yana zaune akan wani tsafaffen kujera, kujerar hawa-hawa ne da igiyoyin zinariya ke zagaye da shi. Wannan shi ne ZULQARNAIN, shugaban tsafin wuta. ZULQARNAIN ya duba Shaprees kamar yana leƙen ƙwakwalwarsa. Sai ya yi magana: “Wuta bata baiwa zuciya mai sanyi iko. Amma ina jin baƙin cikinka yana ƙone maka tunani...." Madam Nablah ta ce "kai mai niyya ne... Za ka iya ɗaukar fansa da wuta, ko wuta ta ƙone ka gaba ɗaya.” Madam Nablah ta ɗora hannunta a kafadar Shaprees, kamar tana turashi gaba cikin mawuyacin zaɓi. Shaprees ya matso kusa da gurin wuta. “Zan ɗauka. Ko da kuwa zata ƙone ni gaba ɗaya.” ZULQARNAIN ya ɗaga hannunsa sama, wuta ta fita daga ƙasa, ta dunkule cikin siffar kwallo. Ya miƙa wutar ga Shaprees. "Yanzu kai ne matsafi. Ka ɗauki wutar zuciyarka, ka horar da ita. Amma ka sani—duk wanda ya ƙone da wannan wuta, ba zai sake zama ɗan adam ba.” Shaprees ya karɓi wutar, tana shiga cikin zuciyarsa ta hanyar idonsa. Sai jikin sa ya ƙone da wuta amma bai jin zafi, sai wata irin shauƙin iko da duhu. Madam Nablah ta murmusa. “Yanzu ka zama nasa. Ka zama na wuta. Amma ka tuna, ni ce nake da mafita a ƙarshen hanya.” Bayan komawar su Shaprees ya ƙera wani gidan ƙasa dake cikin daji anan yake cigaba da ƙirƙirar sabbin tsafikan sa, Shaprees yana koyon amfani da wutar – da nufin dawo da Sophia – amma wata zuciya ta fara tashi a cikinsa wacce ke tambayar: “Ina sakamakon wannan iko idan ba zan iya dawo da ke ba, Sophia?” Wurin da Shaprees ke zaman dare ya dishe da duhu, sai kwatsam wani haske mai taushi da ƙamshi irin na fulawar Firdausi ya cika ɗakin. Shaprees ya buɗe idanuwansa da sauri, zuciyarsa na bugawa, domin har yanzu yana fama da azabar tunanin Sophia. Amma a can — cikin wannan haske — ta bayyana. Sophia, kamar yadda ya santa, amma cikin ƙarin ƙyalli da kwanciyar hankali. Hawaye yana bin fuskarta mai tsabta, amma idonta yana da ƙarfi fiye da yadda ya taɓa gani. “Meyasa kayi haka, Shaprees? Kana da zuciya mai kyau amma yanzu ka gusar da ita...” ta ce cikin murya mai taɓa zuciya. “Ina tare da ayoyin Allah. Kai kuma ka karɓi tsafi. Taya kake tunanin zan kusance ka? Dawo da ni rayuwa ba zai taɓa yiwuwa ba. Na rigada na bar duniya, wacce ta kashe ni. Na bar ta da Allah.” Shaprees yana kallon ta da hawaye a ido, amma wutar zuciyarsa na ƙone masa. Hannunsa ya ruɗe, yana ƙoƙarin isa gareta. “Babu amfanin ɗaukar fansa,” Sophia ta ci gaba da kuka. “Ka auri ɗaya daga cikin ƴaƴan Madam Nablah kamar yadda ta umarta. Sunada kyakkyawar zuciya, haske ne ke fita daga jikinsu… amma kada ka cutar da su.” Shaprees ne ya yi magana cikin ɗaga murya — cikin masifa da ɓacin rai ya ce “To me yasa kika bar ni, Sophia? Na rasa komai! Na rasa ki! Kuma yanzu kina ce min in bar fansa? Ba zan bar jininki ya zube a banza ba. Wallahi sai na ɗauki fansa. Sai Madam Nablah ta san cewa mutuwar ki ba zai tafi a iska ba!” Ya runtse idonsa da ƙarfi, yana juyi kamar mahaukaci, ya cigaba da cewa “Na san ba zan iya tin karar Madam Nablah ba – ikon ta ya fi nawa. Amma zan cutar da ƴaƴanta. Tasleem da Asmeen duk zan mallake su – domin ta ji zafin da na ji!” Haske ya fara ja baya. Sophia tana kuka ta fara ɓacewa. Amma kafin ta bace, ta faɗi abu na ƙarshe: “Ka shige cikin duhu, Shaprees. Amma ka sani, ba kowanne haske ne zai daina bin ka har gobe ba. Tasleem da Asmeen — idan ka cutar da su — hasken da ke cikin su zai ƙone zuciyarka fiye da kowacce wuta.” Shaprees ganin Sophia ta ɓace ne yasa shi goge hawayen fuskar sa, yana sakin numfashi mai nauyi, zuciyarsa ta tsinke gaba ɗaya. Babu abin da ya rage illa fansa. Ya yi shiru, sannan ya ce: “Wuta ta bani ƙarfi. Amma yanzu lokaci ne da zan fara shuka ta cikin ƙauna – ƙaunar ƙarya. Zan yaudari ɗaya daga cikin su, ko duka. Zasu zo mini da zuciyar su, amma ni kuwa zan tare su da azaba.” Duhu ya gama shanye shi. Amma hasken Sophia ya bar ƙura mai kyau a cikin zuciyarsa – wacce zata sake bayyana wata rana... amma sai bayan ya gamu da ɗaya daga cikin ƴaƴan Madam Nablah, ɗaya wacce zuciyarta zata tsaya masa har ma ta motsa wutar zuciyarsa cikin sabuwar hanyar da bai zata ba...... Shaprees ya zauna cikin duhun dakin ginin tsafi, fitilar bakaken harshen wuta suna walƙiya a cikin kwayar idonsa. Ya ɗora hannunsa kan kwanon giyan madubi wanda ke nuna fasalin Sophia—matarsa da ta rasu sakamakon tsafin Madam Nablah. Wani baƙin hayaƙi mai wari ya taso daga cikin kwanonin, yana dunkulewa cikin siffar mace mai haske—kamar Sophia, amma kamar ɓoyayyen haske. Ya furta "Na karɓi iko saboda ke, Sophia," ya faɗa cikin muryar da ke cike da ƙiyayya da ɓoyayyen ƙauna. "Zan dawo da ke. Ko da hakan zai ƙone duniya baki ɗaya." Madam Nablah ta shiga cikin ɗakin ta hanyar hayaki, murya tana ɓullowa da ƙarfi amma da wani salo mai kwantar da hankali. "Shaprees... lokaci ya yi. Ɗaya daga cikin ƴaƴana zata zama naka. na sake baka zaɓi a karo na biyu shin Tasleem... ko Asmeen?.." Shaprees ya yi shiru. Idanunsa suka yi duhu, amma cikin zuciyarsa akwai wani ƙaramin ɗan haske—ba hasken tsafi ba—hasken Sophia, da nufin fansa... "Zan zaɓi Asmeen," Shaprees ya faɗa, yana kallon Madam Nablah da ido mara ƙyalli. Amma zuciyarsa tana faɗin cewa "Wanda kika ba ni, shi zan yi amfani da shi wajen rugujewa. Ko Asmeen ce, ko Tasleem. Wata rana sai kin ɗanɗani zafin da kika saka min..." Madam Nablah ta murmusa. "Ka zama namu gaba ɗaya yanzu, Shaprees." ★Bayan Sati biyu A Ƙarƙashin Ƙasa A can wani ƙarƙashin duhu wanda babu wanda ya sani sai Shaprees, yana ƙirƙiran wani sabon tsari. Wata ƙatuwar alƙalami na zinariya da jini ya zana akan ƙasa, yana karanta kalmomin da Madam Nablah ta koya masa—amma yana haɗa su da kalmomin Sophia, waɗanda suka fito daga wani tsohon littafin da Madam Nablah bata san yana da shi ba. Wannan tsari ne mai matuƙar haɗari—zai iya dawo da Sophia ko ya tarwatsa shi gaba ɗaya. a hankali ya lumshe idanuwansa sannan ya ce "Zan dawo da ke. Amma ba yadda Madam Nablah ke so ba—sai yadda nake so." Shaprees ya buɗe idonsa – idanu masu duhu, amma zuciya tana kiran sunan matarsa da har yanzu yana gani cikin mafarki. “Sophia…” ya furta a hankali. “Na rantse, zan gano yanda zan dawo da ke – ko da kuwa da ran wasu ne.” Sannan ya kuma cewa “Na rantse da jinin da na zubda don tsafin nan – idan har Sophia ba zata dawo ba, sai na ga bayan Madam Nablah.” Wani irin sautin dariya ya ji daga sama, ya ji muryar Madam Nablah kamar ta wata halitta daban tana faɗin “Kayi haƙuri, Shaprees. Ita matarka ta mutu, amma ina da ‘yan matan da ba su da tabo – Asmeen zata iya haifar maka da yara masu iko domin tana da zuciyar sarauta...” Shaprees ya ce da zuciya mai ɗaci: “ me zai hana ki mallaka mun duk biyun Asmeen da Tasleem – in mallake su?..." Madam Nablah ta ɗan ƙame, sai kuma ta ce da siririyar murya: “Idan ka nemi duka biyun ba za ka samu ko ɗaya ba. Amma in ka zama mai biyayya, za ka samu ɗaya… kuma iko zai koma hannunka.” *NEXT_NEXT_NEXT* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 31 to 32 Asmeen tana kwance akan gado tana tunanin abubuwa da dama, Cikin zuciyarta akwai yawaitar tambayoyi game da abubuwan da ke faruwa kwanan nan — sauyawar halin Mahaifiyar su, asarar mahaifi, da kuma wutar da ke yawo a cikin gida ba tare da asali ba. Sai taji an buɗe ƙofa — Madam Nablah ce ta shigo cikin natsuwa amma da idanu masu bayyana tsaurin zuciya. Tsarinta ya canza fiye da yadda Asmeen ta saba gani — akwai nau’in iska mai sirrika a jikinta, kamar wadda ta shigo da zafi da sanyi lokaci ɗaya. Madam Nablah ta zauna kusa da Asmeen, tana kallonta da murmushi mai cike da nufi. Madam Nablah ta ce "Asmeen, ya kamata ki shirya zuciyarki. Lokaci ya yi da za ki yi aure." Asmeen ta ɗago ido cikin mamaki, sannan ta ce: "Aure? Aure kuma yanzu? Amma wa zai aureni? Kuma meyasa yanzu, Mommy?" Madam Nablah ta ɗan murguɗa leɓe, tana duban wata tagar duhu da ke gefen dakin tare da faɗin "Zan haɗa ki da Shaprees. Shi matsafi ne — amma ba kamar sauran ba. Na shigar da shi cikin tafiyata, kuma yana da muradin kafa sabuwar gini da mu. Zaki zama ginshikin wannan mafarki." Zuciyar Asmeen ta buga da sauri — sunan Shaprees ya faɗo kamar ƙarar bindiga cikin kunnenta, cikin wani irin sanyi da tsoro Ta ce "Mommy… wannan Shaprees, mungu ne so yake ya cutar da mu." Madam Nablah ta ɗaga hannunta cikin izza, tana dakatar da ita Daga bisani ta ce "Kada ki saurari hayaniyar zuciya. Wannan duniya ba ta da tsarki, Asmeen! Idan muna so mu rayu — mu mamaye — sai mun haɗa haske da wuta. Shaprees zai kawo ƙarfin da muke buƙata. Kuma ke — za ki kawo tsarkin da zai ɗaure zuciyarsa." Asmeen ta ɗan ja baya daga inda mahaifiyarta ke zaune, idonta cike da shakku da rudani. Ta ce "Amma Mommy… zuciyata ba ta amince da shi ba. Ina jin wani abu marar daɗi idan naji sunansa." Madam Nablah ta matso kusa da ita, ta kama hannunta da ƙarfi da sanyi a lokaci guda. Madam Nablah a sirrance ta furta "Kin san me? Wannan shine dalilin da yasa dole ne ki aure shi. Idan hasken ku ya haɗu, wataƙila zai zama abin da muke buƙata — ko kuwa… zai ƙone." ★★★★★ Bayan kwanaki biyu, a cikin wani filin tsarkakakke da aka gina da duwatsu masu ɗauke da tambarin tsafi, Madam Nablah ta shirya wata walima ta musamman. An kawata wurin da fitilu masu haske kamar taurari, amma a tsakanin wutan, akwai ƙyaftin wuta mai kala ja da ruwan dorawa — alamar tsafin wuta. Wannan ƙayataccen wurin an shirya shi ne saboda Shaprees da Asmeen, da kuma Abeesh da Nasreen walimar ganawa da juna kafin ayi taro na musamman... Asmeen ta shiga cikin wurin, sanye da riga mai wedding gown wanda yake jan ƙasi, Idonta cike da tsoro, amma zuciyarta a daure take, domin ta yanke shawarar jurewa komai. Wani sanyi ne ke yawo a jikinta, duk da irin zafin wuta a kusa. A can gefen ƙarshen filin, Shaprees yana tsaye, sanye da tufafin matsafa, baƙi ƙirin da zinari a gefen wuya. Fuskar sa ta bayyana kwanciyar hankali, amma idanunsa sun bayyana wani nau’in azaba da tsantsar kishi. Ganin Asmeen ya motsa wani abu a cikin zuciyarsa — tunanin Sophia, da kuma wutar fansar da ke ruruwa a jikinsa. Asmeen ta matso kusa da shi, tana ƙoƙarin karanta fuskarsa. Amma kafin ta iya magana, Shaprees ya fuskance ta da wani murya mai sanyi amma mai ƙarfi: Ya ce "Ke ce Asmeen Ƴar matar da ta haifar da ƙaddarar rayuwata" Asmeen ta kalle shi, tana jin girgiza daga wannan furuci. Amma ta tsaya da tawali’u. Ta ce: "Ni ce, kuma ba ni da laifi a cikin abin da ya same ka. Amma na zo ne da niyyar zaman lafiya… ba tsoro ba, ba ƙiyayya ba." Shaprees ya ɗan murguɗa leɓensa, ya juya gefe kamar yana gujewa idonta. Sai ya ce: "Zaki auri wuta, Asmeen! Amma ki sani, wutar da nake dauke da ita ba ta da tausayi. Idan kika ƙone, kada ki ce ba a gargaɗe ki ba." Abeesh da Nasreen kuwa suna zaune a kan wasu tsararrun kujera sun sha kwalliya gwanin burgewa, kana ganin fuskar su kasan akwai farin cikin masoya akan fuskar, kamar babu wani damuwa a cikin zuciyoyin su... Gefe guda Tasleem ce take zaune akan kujera ita kaɗai sai ɗaga kai take tana zuba ido taga ta ina zata fara ganin Amaar domin baya wurin, gaba ɗaya ta shiga damuwa, a yanzu idan Amaar yayi nisa da ita gani take kamar za'a ƙara cutar da shi ne, bata son zama babu shi, especially idan ta tuno da mungun hatsarin da ya faru da shi sai tayi tunani inama ace fatar jikinsu a haɗe yake yanda duk yanda zai taka tare da ita zai yi, ga yanda take kallon Asmeen cikin tausayawa masu ɗauke da hawaye. Tana jin wani abu na fargaba yana motsawa a cikin zuciyarta — wani ɓoyayyen sirri na mahaifiyarsu yana shirin faruwa wanda ake shirin haɗa wa da Asmeen, A cikin ranta ta furta. "Idan dai Shaprees yana da wuta… to, zan zamo ruwa domin kashe wannan makircin..." A yanzu zuciyar Tasleem tayi sanyi sakamon dakatar da ita da Amaar ya yi akan wasu abubuwan da take so ta aikata akan mahaifiyar su, Ya zaunar da ita sannan ya mata nasiha akan illar bijirewa iyaye, ya ƙarfafa mata gwiwa akan ta riƙe addu'a sannan tana taya mahaifiyar ta da addu'a cewa Allah ya shirye ta ya dawo da ita kan hanyar turban musulunci, A lokacin ta zamo kamar ruwa domin a halin yanzu babu maganar da take ji sai na Amaar, a yanzu tunaninta da ƙwaƙwalwar ta da zuciyarta duk sun zamo mallakin Amaar, ta bar hannun Madam Nablah sakamakon ƙarfin Addu'ar da Amaar ya dage mata da shi, baya bacci koda rintsawa ne sai bautar Allah, da yawan addu'o'i akan ahalin gidan nan domin ya fahimci suna fuskantar barazana gaba ɗayansu, balle shi kansa ya rigada yafi ƙarfin Madam Nablah domin cikin zuciyar sa haske ne mai yawan ambaton Allah subhanahu wata'ala, zuciyarsa tafi ƙarfin wani tsafi ya mallake ta, na kusa da shi ma baya tunanin tsafi zaiyi tasiri yanzu a cikinsa.... Madam Nablah ce itama ta shigo cikin tsararren wurin cikin doguwar riga baƙa tana taku cikin ƙasaita, takalmin ta na ƙara ƙaras ƙarass, duk zuba mata ido suka yi har ta nemi wuri ta zauna a gefen Tasleem.. Asmeen da Shaprees su ma sun nemi wuri sun zauna a wuri na musamman da aka tanadar musu... Tasleem wacce tunaninta ya zurfafa bata ma san Madam Nablah ta shigo ba, tana tunanin Amaar wanda ake shirin daƙile mata shi a karo na biyu, tana tunanin bazata taɓa Auran kowa ba in ba Amaar ba... Madam Nablah, wacce ke zaune a kujera na musamman a gefen Tasleem, tana kallon fuskar ta, gaba ɗaya ta gama karantar sirrin zuciyarta ta furta cikin murya ƙasa-ƙasa ta ce "Tasleem… bazan taɓa haɗa ki da Amaar ba. sai da zaɓi guda – ya mutu, ko ki manta da shi har abada. Ba zan haƙura da haɗin ƙauna tsakanin zuri’ata da maƙiyina ba." Tasleem ta lumshe ido, tana jin kamar zuciyarta na fashewa. Amma ta farka da ƙarfin zuciya, ta matsa kusa da Mahaifiyarta ta ce: "Na san kina ɓoye wani abu, Mommy. Amma na sha wahala sosai don na fahimci wanda nake so, kuma bazan bari tsoron ki ya hana ni bin gaskiya ba. Ko da ace Amaar maƙiyinki ne – me ya sa? Me ya Miki ne da har ya kai haka?" Madam Nablah ta yi shiru, idonta na sauya launi zuwa duhu, tamkar wuta, Amma kafin ta iya amsawa, Asmeen ce, ta nufo wurin Tasleem cikin riga ta aure, amma idonta cike da hawaye. Asmeen ta zo dab da Tasleem sannan ta furta cikin raɗa "Tasleem… akwai wani abu da ya kamata ki sani. Ban taɓa amincewa da auren Shaprees ba. Na yarda ne domin Mommy ta ce dole, amma ina jin kamar ana shigar da ni cikin wani abu mai hatsari." Tasleem tana hawaye kafin ta furta wani abu suka ji wani sassanyar muryar mace, iya su kaɗai ne suke jin sautin Muryar, Sophia ce, ruhinta na yawo a cikin haske. Tana furta "Kada ku yarda. Shaprees yana cikin wahala, zuciyarsa ta rikice. Amma wani abu na kirki ya saura a cikin zuciyar sa Kuma Asmeen – ke ce za ki iya kai shi ga warkarwa, ko kuwa ki bar shi ya zama wuta mai cin komai." Cike da mamaki suke kallon juna ba tare da sun fahimci kome ba, Asmeen cikin tsoro ta ce "Muryar wacece wannan?..." Girgiza kai Tasleem tayi sannan ta ce "Ruhi ce, ina tunanin tanada alaƙa da Shaprees..." A wannan lokacin ne Amaar ya shigo filin, duk da an hana shi shiga, cikin kaya na alhurma, ya kalli Madam Nablah sannan ya taka izuwa yanda take a zaune dab da Tasleem..... Ya ce da ita "Ki ƙi ni, amma ba za ki hana gaskiya ta bayyana ba. Zai zo lokacin da kowa zai san cewa wannan haɗin aure da kike so – shine makamin da zai juyo ya hallaka ki." Tasleem na zaune bayan ta lallami Asmeen ta koma wurin Shaprees da zama, tayi farin cikin ganin Amaar a wannan lokacin, Idonta akan Mommyn su tana mata wani irin kallo na ƙiyayya.. Madam Nablah murmushi tayi tare da kawar da kanta gefe ba tare da ta furta komai ba domin a halin yanzu shakkar Amaar take, tasan yanada ƙarfin iko daga haske, sannan yanada tarin addu'o'i wanda shine ya zamo makarin sa idan ta cigaba da kai masa hari itace zata ƙone, hakan yasa ta haƙura ta barsu amma a cikin zuciyar ta tana furta cewa "akwai lokacin da yaƙi zai turnuƙe tsakanin haske da duhu, a wannan lokacin ne zata yi sadaukarwa na musamman ga halattacciyar jini, kuma a lokacin Amaar zai ɗanɗani kuɗar sa... Dalilin da yasa Madam Nablah ta haɗa Shaprees da Asmeen tsafinta ya sanar mata cewa ƙoyayen haihuwar Shaprees suna hasken ƙarfi wanda amfani dasu zai iya sa ta zama sarauniya mai mulkan bil adam da Aljanun duniya, zai zama sai da umarninta kowa zai aikata abun kansa, ma'ana idan tayi amfani da jinin yaron da Shaprees zai haifa kuma ya zamana jinin yaron ya shafi jinin Asmeen domin sirrin dake jikinta, dalilin da yasa Madam Nablah ta kashe Sophia take kuma ƙoƙarin haɗa Auren sa da Asmeen.... Abeesh kuma akwai shaƙuwar jini tsakaninsa da Madam Nablah wanda bazata iya cutar da shi ba, duk abinda yake mata bazata taɓa cutar da shi ba duba ga yanda ta raine shi, Allah ya ɗora mata ƙaunar sa a cikin zuciyar ta, tin yana yaro kuma tana son yaro namiji, bata shaƙu da ƴaƴanta kamar yanda ta shaƙu da shi ba... Amaar kuma tin lokacin da wannan ƙibtila'in tsafin da ya same aka sanar mata cewa "Amaar shine makaryin tsafinta sannan shi zai kashe wutar tsafin da ta kunna, tin yana yaro da zaran ta ganshi ko ya zauna kusa da ita sai taji ƙunar azaba a cikin zuciyar ta, sannan idan zuciyoyin mutum biyu suka haɗu to haske zai kawar da duhu, Amaar da Tasleem da zaran sun yi Aure to komai zai bar ta, zata rasa komai, baƙaƙen Aljanun da suke jikinta duk zasu ɓace su barta, ZULQARNAIN wutar dake jikinsa zai narke ya zama ruwa, hakan yasa Madam Nablah take ƙin su...... Bayan kwana 2 Bayan an daidaita lamurra, Amaar ya yanke shawarar cigaba da zama a gidan Madam Nablah don kula da Tasleem. Tasleem kuwa kullum tana kuka, tana rokon gafarar Amaar. ba wai ƙiyayyar da ta nuna masa ba sai don lokacin da Madam Nablah zata hallaka shi ta kasa ceton sa.. A koda yaushe suna tare ita take masa komai yanzu, ta sauƙar da duk wani girman kanta da jini da kai domin ta ɗauki Amaar a matsayin malama mai bata kariya, ta dogara da Allah sannan ta dogara da Amaar domin ya fita ƙarfin Addu'ar da zai kawar da sharri, A wannan lokaci Tasleem tana sauƙowa daga upstairs tunaninta yana wani wuri, har yanzu abubuwa basu gama sakin ta ba, a hankali take taka benin bata ankara ba taji ƙafar ta ya zame sai kawai tayi baya zata faɗi, daidai lokacin da Amaar zai wuce ganin ta yasa ya tafi a slow kamar wani zaki ya riko ta tare da mannota kan ƙirjinsa, a tsorace Tasleem ta ɗago nan suka kalli juna, Murmushi Amaar ya yi tare da faɗin "Kin taimake ni da kika faɗi a cikin zuciyata, ba tare da kin je ƙasa ba!" Tasleem ta sakar da wani ƙayataccen murmushin da tinda take bata taɓa yinsa ba mai kyalli, lokaci guda kuma hawaye ya cika idonta. tana magana cikin rawar murya: "Yaa Amaar... Ka yafe min. Ban san cewa kai ne ba, kuma ban san na cutar da kai ba." Sake dogon numfashi Amaar ya yi sannan ya ce "Oh my god Beb Tassl har zuwa yaushe zan gaya miki cewa ki cire wannan batun a bakin ki, abinda ya wuce ya wuce meyasa zaki na tunawa, kar ki damu ƙaddarar mu ne tazo da haka, yanzu ba gani kina kallona ba? to Allah bai sa zan mutu ba..." Amaar ya dafa kafadarta da lallami, ya kuma ce wa "Koda ban yafe ba, zuciyata ta riga ta yafe. Kuma zuciyar da take gafara, ita ce mafi lafiya." Abeesh da Nasreen suna cikin sabuwar soyayya mai dauke da barkwanci da nishadi. Su biyu suna da matukar nishaɗi, musamman Nasreen wacce kullum tana kokarin saka Abeesh dariya. A safiyar yau ne a bayan gida cikin tsararren wuri kamar stadium, a Abeesh yana kokarin koya wa Nasreen yadda ake harba kibiyar mashi, tana dariya ta saita yanda zata harba tazo yin harbi hannunta ya kuɓuce ta harbi kibiyar kan Abeesh kibiyar ta makale a turken rigarsa, dake kibiyar wasan yara ne kamar na roba, har ta tsorata kamar tana tunanin zai ji ciwo sai kawai taji yana dariya, Ta ce: "Na harbi zuciyarka fa, karka ce kibiyarta ta wasan yara ɗaya ne da ta farauta.!" Abeesh yana dariya ya ce: "Allah ya tsare! Na fi jin tsoron kibiyar ki fiye da na farauta...!" Zaro ido Nasreen tayi tare da faɗin "kibiyata ta roba ce faa..." Ya ce "eh duk da hakan..." A wannan ranar wuni suka yi suna yawo cikin lambun gidan, suna ta kwasar dariya da soyayya kamar yara. Sau da yawa Nasreen tana tsokanar Abeesh da cewa: "Idan har zaka zama gwamna na zuciya. Bazan kaɗa kuri'a ba idan baka iya girki ba!" Abeesh ya ce "dole na kuwa na iya girki domin mallakar zuciya mai tsada da haske...." Ɓangaren Asmeen... Madam Nablah ta riga da ta mallaka wa Shaprees ita, yanzu a ɓangaren Shaprees take rayuwa, ta raba ta da ƴan uwanta gudun kada wani matsala ya gibto wanda zai sa a fasa Auren da tayi niyyar haɗawa... Asmeen na zaune cikin daki da aka ware mata a part ɗin Shaprees tana kallo ta tagar ɗakin inda Shaprees ke zaune a bakin gadon ta yana kokarin nuna mata kulawa, amma zuciyarta cike take da shakku. Tana jin motsin ruhi a gabanta. Wata rana kafin wannan lokacin Asmeen ta samu mahaifiyarta Madam Nablah tana kuka, tace: "Mommy, kince za ki ba ni miji. Amma kin yanke hukunci akan ruhina ba tare da sanina ba." Madam Nablah a tsawa ce ta ce: "Shaprees shine mafi cancanta. Bai kamata kina tunanin cewa zan iya cutar dake ba ko wani daga cikin ku...." Asmeen ta juya cikin damuwa, tana jin kamar zuciyarta zata fashe. A zuciyarta tace: "Zan bar jikina gare shi, amma ruhina ba zai taba karbar sa ba." Tana tsaye abunda take tunawa kenan ta rasa gane dalilin da yasa mommynta take son haɗa ta da Shaprees wanda ya nuna cewa shi wuta ne... Shaprees yana zaune duk da duhun zuciyarsa, yana jin wani abu daban daga Asmeen. Daga lokacin da ya fara ganinta tana kuka a ranar da yazo gidan nan sai ya soma jin tsoro – tsoron cewa zai iya faduwa cikin soyayya da ita. Amma a zuciyarsa, Sophia ce kawai ke zaune. Sai ya daɗa kuduri cewa:y " idan har zaki ceci ruhin Sophia daga Madam Nablah, to tabbas zan tsinci kai na cikin soyayyarki ko da bana so......" Wata rana a cikin gida, Tasleem da Nasreen sun tsara zasu yi girkin masoya, suna kitchen suna dafa delicious abinci tare. kafin su kammala abincin ya kone ƙurmus saboda Tasleem ta tsaya tunanin neman abinda zata zuba don ƙara wa girki ɗanɗano, Nasreen kuma tana haɗa wani abu daban ganin yanda girkin su yake ta ƙone wa ne yasa tayi saurin sauƙe wa tana faɗin "Innalillahi yau mai zamu ce wa masoyan mu, ga shi mun yi musu sosai akan cewa mun fi su iya girki.. Kafin Nasreen ta rufe baki sai ga Amaar da Abeesh suka shigo suna faɗin "Subhanallahi ƙonannen Abinci masoya zasu ci?..." Nasreen ta ce "bani bace Tasleem ce... Amaar yace: "Beb Tassl baki iya girki ba daman?" Tasleem tana turo baki ta ce "Nasreen ce fa bani ba..." Abeesh ya sake baki yana kallon Nasreen ya ce "Mar'atussaliha daman kema baki iya girki ba,...? Nasreen ta ce "Ya Abeesh idan ban iya girki ba shin girkin da nake kai maka waye yake yi?..." Abeesh ya ce "Robot manaaa...." Duk suka kwashe da dariya... Amaar ya ce "Idan wannan ne abincin masoya, to mun yafe wallahi, mun bar muku kayan ku Alhamdulillah a ƙoshe muke.....!" Suna wasa da dariya da haka har suka koma falo, Nasreen tana tsokanar Tasleem akan bata iya girki ba, Cikin fusata Tasleem ta kamo Nasreen suka fara kaure wa da faɗa, Amaar da Abeesh kuwa zama suka yi suna kallon su tare da tinzira su suna faɗin "duk wacce ta kayar da ɗaya to wacce aka kayar ita ce bata iya girki ba..." Tasleem da Nasreen kowa so yake ya kayar da ɗan uwansa domin su ci gasar iya girki, Har zuwa wannan lokacin babu wacce ta yarda taje ƙasa saima ƙara kaurewa suke da faɗa, a ƙarshe dai a tare suka faɗi a ƙasin carpet suna sakin numfashi daƙer.... Amaar da Abeesh ihu suka danna suna faɗin "wayyo 0 0 duk basu iya girki baaa..." Tasleem da Nasreen ƙara miƙe wa suka yi zasu ƙara dambe a lokacin Amaar da Abeesh suka miƙe kowa ya janye nashi jikinsa suna faɗin "A'a ya isa haka, kar ku raunana mana kan ku....." Suka yi dariya gaba daya, cikin nishaɗi... A nan ne labarin ke kara rikicewa, yayin da Asmeen ke neman mafita daga auren da bata so, Shaprees na fama da rikicin zuciya, Abeesh da Nasreen suna jindadin soyayya, yayin da zuciyar Tasleem da Amaar suka sake haɗe wa.... Amma wani mummunan sirri daga Madam Nablah na dab da bayyanuwa wanda zai canza komai... Nexttttttt...... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 33 to 34 A wannan lokacin da yamma, hasken rana ya kusan faɗuwa Asmeen tana tsaye a gaban window tana kallon waje tun safe ta kasa cin abinci, ta kasa aiwatar da komai, Kullum cikin zuciyarta tana son fita daga wannan gidan. Amma babu inda zata je, babu wanda zata roƙa, sai hawaye masu dumi dake zubo daga cikin idanuwanta... A ɗayan ɓangaren gidan, Abeesh da Nasreen sun shirya tafiya zuwa bakin ruwa domin shan iska da tattaunawa na musamman da ya shafi Auren su. Nasreen tana ɗauke da kwando cike da 'ya'yan itatuwa (fruits) da kayan ciye-ciye... Sun zo fita Abeesh ya tsaya a gaban ta tare da zuba mata ido ko ƙibtawa ba ya yi, domin ba ƙaramin kyau ta sha ba,. A hankali ya furta "Idan na faɗa cikin ruwa saboda kyawunki, za ki zo ki cece ni ko sai na jira malam kogi?" Nasreen tintsirewa tayi da dariya tana faɗin "Ni kuwa sai na ɗauko kwalba, na ajiye kyawunka a ciki, kada ka lalace!" Yana dariya ya ce "kyawuna ba ma ni kaina ba?..." Itama cikin nishaɗi take dariya tare da faɗin "a'a kyan ka zan adana, daga baya sai na jan ko..." Suna dariya har suka fice daga falon, zasu shige mota Abeesh shi da kansa ya buɗe mata murfin motar ta ɓangaren da zata shiga, har zata shige tsinkar jikinta ya tashi sai wani yaarrrr ta ji, ƙirjin ta ne ya fara bugawa a hankali... Abeesh ya ce "lafiya kuwa? Meta faru ne Mar'atussaliha?..." A jikinta taji cewa akwai abinda ya shafi jinin ta a nesa da ita tana kallon ta cikin damuwa da tashin hankali.... Nasreen a hankali ta ja da baya tare da juya bayanta ta ɗaga kanta saman Benin part ɗin Shaprees, gani tayi Asmeen tana tsaye ta tagar window ɗakin da take a part ɗin Shaprees dake ba nisa a tsakanin su, itama Asmeen su ɗin take kallo tana hawaye, ganin a halin da ƴar uwar ta take ciki ne yasa Nasreen kuka, lokaci guda hawaye suka wanke mata fuska, haka suke kallon juna, ita Nasreen ba halin ta je yanda Asmeen take haka itama Asmeen ba halin ta zo yanda ƴan uwanta suke, Daƙer Abeesh ya ja Nasreen suka tafi..... Shaprees yana kallonsu daga nesa yana kallon farin ciki yana ƙona zuciyarsa. A lokacin yana tare da Madam Nablah, wadda ta zo da wani shudi-shudin littafi a hannunta, koda yaushe tana kan karanta littafi abinda ya shafi spell-spell, itama tana kallon yanda Nasreen da Asmeen suke kewar juna, suna zaune a wurin shakatawa wanda yake kewaye da bukka, sai wasu tsararrun kujeru da table ta tsakiya, da duk kan alamu tana nuna masa yanda ake gudanar da wasu tsafe-tsafe ta cikin littafin ... Madam Nablah ta ce: "Shaprees, lokaci ya yi. Za ka auri Asmeen nan da kwana uku. Idan kana da wata damuwa — riƙe ta." Shaprees yana buɗe littafi a hankali lips ɗinsa na motsi cikin sassanyar ya furta "Akwai wani abu da kike ɓoyewa, Na san ba soyayya ce tasa kike son haɗani da ɗiyar ki Aure ba... na bincika cikin nawa salon tsafi kina so ne na ɗauki wani abu daga jikinta — wani sashi na asali." Madam Nablah ta sau murmushi mai haɗarin gaske. Ta juya tare da faɗin "Asmeen bata san cewa tana ɗauke da sirrin iko da nake da burin samu ba... kuma ita kaɗai zata iya dawo da Sophia — matarka — daga mutuwa." Madam Nablah ta furta hakane domin tabbatar masa da gaskiyar lamari amma a cikin zuciyar ta bazata taɓa barin ya dawo da Sophia rayuwa ba... Shaprees ya ɗan ɗago yana kallonta a ruɗe Zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, Me zai yi? Zai auri Asmeen don samun iko? Ko zai bijire wa Madam Nablah don kare wacce ba ta san komai ba?...... A gefe guda kuwa Tasleem tana kwance akan ƙirjin Amaar akan gadonsa bayan ta gama gyara masa ko ina na ɗakin, haka take sauraron bugun zuciyarsa na harbawa a hankali cikin nutsuwa, haka kawai take ji a jikinta cewa abinda ta aikata masa ta cancanci hukunci, idan ta nuno cewa da hannunta ta harbi Ya Amaar ɗin ta sai taji ta tsani kanta, idan ta tuno da Tasleem ɗin da ta tsani wanda take muradin ƙaunar gani da bege sai taji cewa ina ma zata iya canza kanta ta koma wata ɓangare da ban, Lokaci guda hawaye suka gangaro mata a hankali ta furta "Yaa Amaar...." Yana pressing wayansa ya amsa tare da shafa fuskar ta. Ta ce: "Na san bana da ikon canza abin da ya faru... amma zaka iya bani dama in gyara. Ka koya min yanda zan daina zama irin Tasleem ɗin nan da nake tsana." Amaar ya kalle ta da ido masu nuni da jinƙai da gargaɗi. Sai ya ce: "Idan kina son gyara, ki fara da gaskiya — fada min komai game da mahaifiyarki." Tasleem ta tsaya. Hankalinta ya tashi, a ruɗe ta tashi daga kansa tana kallon sa, domin babu abinda yake firgitar da ita irin a kawo mata maganar mahaifiyar ta, sai ta rinƙa jin tana tuno da wasu abubuwa na sirri, A lokacin ne Abul Abeesh ya faɗo mata a rai, mahaifin su Amaar da Abeesh, haka take jin hawaye na ƙoƙarin zubo mata a ranta take furta "Shin lokaci ya yi da zata tona babban sirrin Mommy?...." Tana tambayar kanta... Tasleem ta tsaya kamar mutum-mutumi, zuciyarta na bugawa da karfi. Amaar ne ya sake furta “faɗa min komai game da mahaifiyarki” Ta ɗan juya kai gefe, sai kuma ta dawo da kallon ta cikin idon Amaar. Sannan ta ce "Yaa Amaar… mahaifiyata ba ta yadda da haske ba. Amma bamu san da haka ba domin dukkan mu mun girma muna ganin ta tamkar tauraruwa ce mai kare mu daga duhu. Har zuwa ranar da na fara jin wasu kalmomin tsafi daga gare ta a cikin mafarki na....." Amaar ya runtse idanu yana sauraron ta, zuciyarsa na baƙin cikin halin da mahaifiyarsu ta shiga na rashin son haske. Tasleem ta ci gaba da bayani cikin rawar murya: "Tana da wani ɗaki a cikin ɓoyayyen ɓangare na gidan nan… wanda ba kowa ke sanin hanya zuwa ba. A can take tara jini, fure, da wani zane da muke tsoro mu kalla. Kuma ina jin tana amfani da wani sashi na rayuwarmu wajen ƙarfafa kanta." Amaar ya ce "Shin kin san dalilin da yasa take so Shaprees ya auri Asmeen?" Tasleem ta girgiza kai tare da faɗin "Na ji sau ɗaya tana cewa "'idan asalin Asmeen ya yanke, sai na dawo da ikon da aka ɗauke min shekaru ɗari. Ban fahimta ba. Amma yanzu ina tunanin… akwai abu mai girma da ke tattare da Asmeen."... Cikin rashin fahimta Amaar ya ce "ikon da aka ɗauke shekaru ɗari kuma?...." A lokacin Tasleem ta nutsu tare da daidaita tunanin ta cike da mamaki ta ce "shekaru ɗari ai ba'a haifi Mommy bama...." Amaar ya ce "tabbas akwai abinda ke wakana, ina tunanin ba asalin mahaifiyar ku ba ce...." Tasleem cikin rashin fahimta ta ce "ban gane mai kake nufi ba..." Amaar ya ce "kar ki damu zamu gano komai nan bada jumawa ba..." ★★★★★ Washe gari da sanyin safiya A can ɗayan ɓangaren gidan, Asmeen na zaune a gaban madubi, tana kallon fuskarta wacce ke ƙara haskakawa a duk dare. tana tunanin meyasa a duk lokacin da Shaprees ya zo kusa da ita, sai gabanta ya fadi. Zuciyarta na cika da damuwa—ba don ta tsane shi ba, sai don saboda tana jin wani abu daga jikinsa yana ɗauke da wuta na al'ajabi..... Tana cikin wannan tunanin sai ta hango wani haske a dakin, Ruhin Sophia ya bayyana, murya kamar ƙara amma tana motsi cikin nutsuwa. Ruhin Sophia ta ce "Asmeen… ki saurara. Ki kiyayi Mahaifiyarki Ba Auren ki da Shaprees take so ba — ikon dake jikin ki take nema. Sannan Mijina Shaprees ba azzalumi bane kuma baya cutarwa, tsautsayi da ƙaddara yasa ya shiga tarkon Mahaifiyarki Madam Nablah, kuma ita ta rabani da duniyan na, sannan ta datse farin cikin mijina don cikar burin ta, hakan yasa mijina yake ƙoƙarin jefa kansa cikin haɗari na tsafin wuta Amma a zuciyarsa akwai abin da ba zai iya shawo kansa da shi ba — soyayya da azaba sun yi masa kututture, amma nayi alƙawarin bazan taɓa barin mijina ya dawwama a cikin wannan wutar tsafin tsiyar ba, wanda babu komai a cikin sa sai zalunci da ƙonewar zuciya, zan kasance a cikin zuciyar mijina Shaprees kiyi haƙuri saboda zaki zama matar sa zuwa gobe...." Asmeen ta miƙe da sauri, jikin ta yana rawa. Ta furta "Ni dai ban san komai game da rayuwar ku ba, a barni na zauna cikin kwanciyar hankali kamar yanda nake a baya, kada a sako ni a cikin tsafi domin banida alaƙa da shi, sai dai na tabbata bana jin kwanciyar hankali da wannan auren." Sophia ta juya kafin ta bace, ta furta wata kalma mai zurfi: "Ke ce mafi alaƙantuwa da tsafi amma ki dage da addu'a hasken zuciyar ki zai kore duhun da ke ƙoƙarin mamaye ki...." Daga nan Sophia ta ɓace, Cikin firgici da tashin hankali Asmeen ta zauna a bakin gado tana sakin numfashi daƙer tare da faɗin "ke nan bayan Tasleem muma ana bibiyan ikon hasken mu? innalillahi wa inna'ilaihi raju'un....." ★★★★★ Abeesh da Nasreen kuwa sun dawo daga yawon su cikin dare, amma kafin su isa ƙofar gida, suka ci karo da wani tsoho mai launin fata kamar gawayi, yana tafe da sandarsa, yana fadin: "Mai dauke da sirrin zuciya, kada ka manta… masoyi na gaskiya ba ya ɓoye sirri mai wuta, ruwan da kuke sha, yana iya zama madara ko guba." Suna kallon juna cikin mamaki. Nasreen ta ce " Ya Abeesh… kana jin akwai wani abu da muke wulakanta gani?" Abeesh yana kallon tsohon ya ce "Ka sanar mana gaskiyar abinda kake nufi, nasan maganarka bazai wuce akan Madam Nablah ba..." Tsohon ya nuna Nasreen sannan ya ce "ina magana ne akan wannan yarinya, ki kula da kan ki domin akwai sirrin tsafi...." Abeesh ya kalli Nasreen cikin damuwa ya ce "Zan tona komai daga yanzu. Idan akwai sirri tsakanin ki da tsafin Madam Nablah, wannan daren zai zama farkon haskenmu ko ƙarshenmu." Tsohon ya ce: "Akwai wani ƙugi a ƙasan gidan nan, an rufe shi da tambarin zinariya. A can ne aka binne asalin wutar Madam Nablah. Kuma, idan wani daga zuriyar gidan ya shiga ƙugin nan da zuciya mai tsabta, zai ga gaskiya gaba ɗaya...." Daga nan tsohon ya ɓace ɓatt, Nasreen cikin tsoro da fargaba ta rungumi Abeesh tana ihu, da sauri ya toshe mata baki zuciyarsa na ɗar-ɗar yana tunanin maganganun Aljanin tsoho da ya fito musu, cikin tashin hankali suka shige gidan, a lokacin misalin ƙarfe 12 na dare.... A falo suka tarar da Madam Nablah zaune akan sofa tana facing plasman alamun kallo take, ba komai ne yasa ta zauna a falo a wannan lokacin ba sai jiran dawowar su Abeesh, kallon su tayi cikin izzah da ƙasaita tana yamutsa fuska kamar bazata yi magana ba ta ce Meyasa kuke hidimar gaban ku ba tare da bin umarni na ba, you support to tell me idan zaku fita wani wuri and then bana son yawon dare...." Abeesh gyara tsayuwar sa yayi yana kallon ta tare da goya hannayensa akan ƙirji ya ce "bin umarnin ki dai-dai yake da faɗawa cikin wuta, shiyasa muke tsarkakakkiyar rayuwa cikin haske, bama buƙatar duhu ya shigo rayuwar mu...." Madam Nablah murmushi tayi sannan ta kawar da kanta daga ganinsa, tana jinjina kai ba tare da ta furta komai ba, Abeesh yana gamawa ya bar falon kai tsaye upstairs ya haura zai nufi bedroom ɗinsa. Nasreen tana tsaye kanta na kallon ƙasi duk da halin da mahaifiyarta ke ciki bata daina mata biyayya ba, sannan kuma tana matuƙar jin shakkar ta saɓanin Tasleem, ta juma a tsaye a gaban Madam Nablah ba tare da kowa ya furta komai ba, sai yanzu Madam Nablah ta samu bakin furta "ki bar gabana, like kije ki kwanta..." Nasreen godiya tayi tare da barin wurin har zata hau saman beni ta hango Amaar ya shigo falo yana ɗauke da Tasleem wacce tayi bacci, yayi mata ɗaukar luɗa alamun a ɗakinsa tayi bacci, yana sakin murmushi idonsa akan Nasreen wacce ta zuba musu ido tana sakin murmushi itama.. Madam Nablah a firgice ta miƙe tsaye tana kallon su, idanuwanta kamar zasu faɗo tsabar zazzaro su da take cikin fushi gasu manya ne daman, tana huci haka Amaar ya wuce da Tasleem ko kallon yanda take bai yi ba, duk a tare suka haura saman upstairs da Nasreen tana masa dariya.... Itama Madam Nablah a fusace ta bar falon ta nufi bedroom ɗin ta, Ba jumawa Amaar ya sauƙo bayan yaje ya kwantar da Tasleem, ya nufi room ɗin sa shima..... A gefe guda kuma, Shaprees ya ƙara fusata. Duhu yana ƙara karfi a jikinsa. Amma cikin zuciyarsa, muryar Sophia tana ƙara bayyana, tana damunsa da tunanin gaskiya. Ya fito daga ɗakinsa da dare, ya nufi gidan ƙasa da ya ƙirƙira domin gudanar da tsafin sa, A can ya zana zane a ƙasa ya kira ruhin da ke ƙunshe da sirrin rayuwa da mutuwa. Yana zaune ya furta cewa: “Na yarda da duhu don in dawo da Sophia. Amma yanzu gaskiya tana fara rikita ni. Ina so in san, shin ina kan hanya?” Wani murya ne ya bayyana, da suffar mutum kamar ruhi da idanuwa jajawur ya ce: “Ka rasa hanyar gaskiya tunda ka rungumi wuta saboda soyayya. Amma yanzu, akwai hanya ɗaya – idan Asmeen ta san gaskiya to zaka cimma burin ka, Idan kuma ka ci gaba da ɓoye gaskiya komai zai ƙone.”......... A gefe guda. Tasleem tana cikin bacci ta faɗa cikin wani mafarki mai ɗauke da haske, lokaci guda ta ganta a cikin gajimare wanda ba koda kukan tsuntsu ne, iya zallar haske ne sannan tana sanye da fararen kaya har ƙasi da mayafin kai wanda aka rufe mata sumar gashi, sai waiwaye take tayi amma bata tarar da kowa ba, bata wani tsorata ba domin tasan haske ne ke bibiyan ta ba abun cutarwa ba.. Tana tsaye taga wani mutumi fari da farin gemu yana sanye da fararen kaya shima a jikinsa, haka yake kamar ruhi domin ba mutum bane hakan yasa ya fito mata a mafarki domin ya tunatar da ita gaskiya, Tasleem murmushi ne a kwance saman fuskar ta ganin tana tare da haske, Cikin muryar nutsuwa dattijon nan ya fara magana kamar haka: “Kin taɓa sha ruwa daga ruwan da aka gauraya da wutar ruhi. Ke ba mutum ba ce kawai — ke rabin ruhi ce, rabin jini. Kuma zuciyar ki na ɗauke da makullin rugujewar Madam Nablah.”... Tasleem cikin rashin fahimta ta ce “To me ake nufi da hakan?”.. Dattijon ya ce “Dole ne ki fuskanci mahaifiyarki da gaskiya. Kuma idan Amaar yana tare da ke, ku shiga ƙugin zuma kafin Duhu ya maye gurbin Domin kuna da alaƙa da juna fiye da yadda kuke tunani.” Tasleem tana motsi da lips a hankali ta furta "menene ƙugin zuma?...." Dattijon ya ce "Hmmm... Ƙugi na zuma wannan ba kalma ce da yara ke taɓa ambatawa ba, sai wanda ya san asalin wani sirri, Idan baki manta ba a nan ne kika taɓa ganin wani dattijon mutumi a tsare babu haske a yanda yake saboda tsananin tsafi, to nan ne gefen ƙugin zuma, asalin ƙugin zuma kuwa sai kinyi da gaske kafin kin san wurin, idan kika shiga nan ne gaskiya zata bayyana kanta, nan ne komai zai ruguje na tsafi, rayuwa zata dawo sabuwa..." Tasleem a ruɗe take faɗin "a yaushe wannan al'amarin zai fara aiki?..." Dattijon yayi murmushi sannan ya ce "dalilin da yasa zamu wakilce ki akan tsarin tafiyar mu, zalunci ya yi yawa, muna son haske ya kawo ƙarshen duhu, daga yanzu ke ce sarauniyar Haske, mun riga da mun naɗaki akan wannan mulkin, na kuma isar da saƙo a gareki...." Tasleem ta ce "taya za'a ban sarauniyar Haske alhalin ban san komai game da haske da duhu ba?...." Dattijon ya ce "a sannu a hankali zaki gane komai da idon sarauta, akwai wasu baiwa da muka zuba miki bayan bayyanar gaskiyar mafarkin ki, matakin da muke so ki kai a wannan zango shine ki bayyana gaskiya, domin haske tana tafiya ne da gaskiya, idan ba haske to ba gaskiya haka kuma idan ba gaskiya to kuwa ba haske, ki bayyana wa su Amaar yanda mahaifinsu yake, kuje ku cece shi daga halin da yake ciki na tsawon shekara ashirin, kada ki wuce awa 24 baki taimakawa tsohon nan ba.... Sarauniyar Haske....Ku hadu da wanda aka ɓoye – ku ƙaraɗe duhun da haske – kafin lokaci ya kure.”.... Tasleem tana hawaye tare da faɗin "Insha Allahu zan taimake shi, a yau ...." Dattijon haske ya ɓace ba tare da ya sake cewa komai ba, daga nan Tasleem ta dawo baccin ta, a ruɗe ta tashi zaune tana jero addu'o'i...." Itama Nasreen tashi tayi jin yanda Tasleem take ta addu'a cikin fitar hayyaci, tambayar ta take tayi tana faɗin "lafiya kuwa Tasleem? wani irin mafarki kika yi haka ..." Sai a yanzu Nasreen ta lura da sumar gashinta da ya koma fari tass kamar furfura, babu alamun ɗigon baƙi, a tsorace ta ce "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Tasleem ya sumar gashin ki ta koma fari?.." Tasleem bata damu ba kawai hannu tasa ta shafa kanta, sai a lokacin gashin ya fara komawa baƙi kamar yanda yake... Tasleem cike da mamaki take maimaita wa Nasreen abinda ya faru a cikin mafarkin ta, ta sanar cewa "an bata mulkin sarauniyar Haske...." Ta cigaba da cewa "Nasreen....taya zan fara gudanar da wannan al'amarin?...." Nasreen ta matso kusa da ita tare da rungumar ta ta ce "ki bi gaskiya sai ki cigaba da kasancewa a cikin haske shine abinda wannan mafarkin yake ƙunshe dashi da kuma sarautar ki, duk wata gaskiyar da kike ɓoyewa ya zamana kin bayyana ta, kada ki ɓoye sirri sannan kar kiji tsoron duhu wannan shi ake nufi da sarauniyar Haske...." Wannan bayanan Nasreen ya ƙarfafa mata gwiwa sosai, ta jinjina kai sannan ta furta "dole gaskiya zata yi nasara akan ƙarya dole haske ta wargaza duhu, yanzu ne daidai lokacin da zan buɗe wata gaskiyar da na daɗe ina ɓoyewa...." Nasreen ta miƙe tana faɗin "meye wannan gaskiyar?..." Tasleem ta miƙe tsaye tare da faɗin "UNCLE JUN mahaifin su Amaar da Abeesh...." Nasreen itama miƙewa tayi tsaye tana faɗin "haƙiƙa wannan al'amarin babba ne, kuma ya rataya a wuyan sarauniyar Haske ta ceceshi daga cikin duhun da yake domin zuciyarsa haske gare ta...." Tasleem jinjina kai tayi sannan ta ce "naji an fara ƙiran asuba muyi sallah kafin naje na samu Ya Amaar da wannan batun...." A cikin safiyar yau mai cike da shiru, wanda iska ke kadawa a hankali, Tasleem ta sauko daga saman bene Idonta cike da hawaye, zuciyarta kuma kamar ta fashe da sirrin da ta dade da boyewa. Tana shirin shiga ɗakin Amaar. Bayan Tasleem ta je ɗakin Amaar bata same shi ba ya tafi masallaci shi da Abeesh, zaman jiran sa take har ya dawo, ganin ta a zaune cikin damuwa yasa ya ƙara sa wurinta da sauri yana faɗin "lafiya kuwa Baby Tasl?..." Tasleem miƙe wa tayi ita tana hawaye ta ce: "Ya Amaar..… idan na faɗa maka gaskiya, zaka cigaba da sona?” Amaar ya tsaya yana kallonta daga bisani ya ce “Soyayya ba ta dogara da sirri ba. Amma gaskiya tana ƙara ƙarfinta.” Tasleem ta furta cikin kuka “Ni ba cikakkiyar mutum bace. A yanzu na zama sarauniyar Haske wacce aka bata ragamar rushe tsafin Madam Nablah wacce take ƙoƙarin ruguza gaskiya akan ƙarya, Na zama haske ne domin na sanar da duk wata gaskiyar da ake ɓoyewa....” Amaar ya rungume ta da ƙarfi. Yana faɗin “Tasleem… duk da haka, ke ce kike jaddada min farin ciki, ina mai farin ciki domin kin zo da haske, ba duhu ba.”... Tasleem tana hawaye ta ce "akwai wata gaskiyar da nake ɓoye muku amma a yau kuma a yanzu zan sanar maka koda wuta zata ƙone ni... Amaar ya jinjina kai sannan ya ce "wuta bazata taɓa cin sarauniyar Haske ba...." Tasleem ta ce "idan na lumshe idanuwana ƙwaƙwalwata takan kawo mun abubuwan da ke ɓoye, a cikin idanuwa nake iya ganin komai tamkar video nake gani koda mutum yana cikin ƙasin ƙasin ƙasa ne, na samu wannan baiwar ne sakamakon ɗaurani da akayi a matsayin sarauniyar Haske...." Ta kalli Amaar sannan ta kuma cewa "aikin da zan fara yi da wannan baiwar tawa shine zan gano sirrin dake zuciyar Shaprees ne, shin yana son Auran ƴar uwata da zuciya ɗaya ne ko kuwa shima akwai shirin da yake shiryawa yanzu nayi ƙoƙarin dakatar da shi.... Tasleem ta lumshe idanuwanta lips ɗin ta ne ya fara motsi a hankali tana faɗin "bayyana mun sirrin zuciyar Shaprees...." Amaar kuwa zuba wa kyakkyawar fuskar ta yayi da kallo, ji ya yi ta fara faɗin “Wannan… wannan shine Shaprees… da Sophia a zane a cikin zuciyar sa, Amma me yasa yake zaune da Madam Nablah yana dariya, bayan ta aikata masa mummunan laifi, ta ruguza masa farin ciki ta hanyar kashe masa matarsa Sophia.?”.... Da sauri Tasleem ta buɗe idanuwanta tana zazzaro su, tare da faɗin "kenan ɗaukar fansa ya kawo shi gidan nan? har yana shirin Auran ƴar uwata da niyyar cutar wa ?..." Ta kalli Amaar wanda shima abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba... Da sauri Tasleem ta ɗauko biro da takarda ta fara rubutu kamar haka: "Shaprees zaiyi amfani da ke ne, yana son janyo ki cikin shirin da zai iya sa ya dawo da matarsa wacce ta daɗe da mutuwa, ko da kuwa hakan shi zai halaka.... Ta gama rubutun tana furta wa a fili, sannan ta furta "Chuchu...." Sai ga wani tsuntsu ya bayyana ata window ɗakin Amaar yanda yaji ƙiran kenan, tsuntsu fari tass shine ɗan amanan Tasleem, tana matuƙar ji da wannan tsuntsun nata in zata yi aike da ya shafi letter shi take aikawa, da sauri ta nufe shi tana faɗin "wannan saƙon ka kai mun zuwa ga Asmeen yanzu...." Ta lanƙaya masa a wuya lokaci guda ya fura zuwa aiken.. Amaar kallon ta kawai yake cikin tausayawa, sannan yayi matuƙar farin ciki da wannan muƙamin da aka bata domin su zata amfana, zata kare su daga faɗawa cikin hallaka.... Tasleem ta tsaya a gaban Amaar cikin tausayawa ta ce "akwai wata gaskiyar da nake son sanar maka kuma ya shafe ka sosai, amma kafin nan sai na duba halin da yake ciki da kuma hanya mafi sauƙi yanda zamu gano shi...." Amaar a ɗan ruɗe ya ce "shi wa?...." Tasleem ta ce: "Ya Amaar, don Allah ka saurare ni. Zan faɗa maka wani abu mai girma… wani abu da zai iya canza rayuwarmu gaba ɗaya." Amaar yana tsaye idonsa akan fuskarta, ya ga wani irin tsoro da damuwa akan fuskarta a hankali yace: "Na saurare ki, Tasleem. Kar ki ɓoye komai." Tasleem lumshe idanuwanta ta yi tare da furta: "Naga wani tsoho a cikin wani duhun ɗaki dake can cikin ƙasa yana ɗaure da igiyoyi na tsafi, yana neman taimakon haske, wannan gaskiyar idan na bayyana shi Madam Nablah zata iya cutar da shi ko ma ta kashe shi gaba ɗaya..." Amaar cikin rashin fahimta yake faɗin "waye shi ɗin? meyasa yake cikin tarkon Mahaifiyarki?...." Ta kuma maimaitawa tana hawaye a yayin da idanuwanta suke buɗe furta: “Na ga wani tsoho... Yana cikin ɗakin ƙasa a kulle, Na ga idonsa suna kallo kamar yana magana da ido. Amma idan na faɗa, Madam Nablah zata iya hallaka shi!” Cikin damuwa da fusata Amaar ya danna hannayensa cikin sumar gashinsa kamar zai yi hauka yana faɗin "oh my god! what is wrong with you Tasleem ki sanar mun who is him?...." Tasleem murya na rawa ta furta: " Wannan tsohon shine Mahaifinku, Tabbas na san inda mahaifinku yake a ɓoye... yana raye.".... Amaar a ruɗe yake kallon Tasleem ya ce "Wane mahaifi?" Tasleem ta ce "Mahaifin ka da Abeesh — mahaifinku yana can ƙasan gidan Mahaifiyata, an tsare shi shekaru ashirin da suka gabata. Nasha ganinsa a cikin mafarki na amma ban taɓa tunanin shi bane, sai wata rana da na bi bayan Mommy a ɓoye har zuwa yanda yake amma tsoro ya hanani faɗa. Madam Nablah bata ma san cewa na sani ba." Amaar gaba ɗaya ya rikice haka yake fitar da numfashi daƙer yana faɗin "Na... na dade ina mafarkin wannan abun nima. Kuma yanzu ke kike sanar mun cewa gaskiya ne?" Ya girgiza kai ya ce "Ya kamata na je yanzu. Wannan na nufin rayuwarmu na cikin haɗari...." Tasleem ta riƙe hannun Amaar sosai, tace: “Zamuyi wannan tafiyar tare, ni kaɗai ce nasan yanda yake kuma sai da ni ku samu hasken hanya..." Amaar yana zubda hawaye haka yasa hannu ya rungumo Tasleem jikinsa tare da sumbatarta ta ko ina tsabar tsananin farin ciki, haka yake jin ƙaunarta yana ƙara shige cikin zuciyar sa.... Abeesh yana zaune a falo shi kaɗai sai murmushi yake ta zuba wa, a wannan yayin Nasreen tazo ta same shi cike da mamaki itama ta zauna kusa da shi idonta akan fuskar sa wacce ta gagara gane ma'anar wannan murmushin... Abeesh a ruɗe ya juya yana fuskantar Nasreen tsabar farin ciki bai san lokacin da ya rungume ta sosai a jikinsa ba yana faɗin "wannan ranar nake jira daman, gaskiya ta bayyana, bazan iya faɗan a yanda mahaifin mu yake ba amma muddin wani ya sanar a yanda yake kuma ake ƙoƙarin ceto shi to tabbas zan ji hakan a jikina, Nasreen gaskiya ta bayyana, daman nasan mahaifina yana raye domin akan idona akan ɗaure shi a cikin wani duhun ɗakin ƙasa amma bazan iya bayyana hakan a zahiri ba, an kurmantar dani ta yanda bazan taɓa faɗan gaskiyan abinda na gani ba amma hakan bai sa na manta ba, saboda ƙarfin addu'a dana riƙe....." Yana bayani cikin hawaye da nuna farin cikin, itama Nasreen hawayen take tana share masa hawayen sa da tafin hannunta... Ta gefe guda kuma Amaar da Tasleem ne suke tsaye wanda tin farkon maganar Abeesh suke tsaye suna riƙe da hannun juna, daga Amaar har Tasleem duk kowa hawaye yake, Amaar ba ƙaramin tausayawa ƙaninsa yayi ba... Abeesh yana ganin su ya taso da sauri ya tsaya a gaban Tasleem yana hawaye ya ce "my Juju nagode sosai, ta sanadiyar ki yanzu bakina ya buɗe wurin faɗan gaskiya akan zaluncin da aka yiwa mahaifina.... Yana girgiza kai yasa hannu ya rungumeta yana kuka, itama tana kuka tana rarrashin sa.... Amaar ya ce "a yanzu zamu je wurin da mahaifin mu yake zamu ceto shi daga hannun hallaka... Abeesh ya ce "ina tare da kai Yaya, tare zamu wannan tafiyar..." Tasleem ta kalli Nasreen ta ce "ki zauna mana anan nasan Mommy bata nan a halin yanzu, idan har ta dawo kafin mu fito ki riƙe mana ita please..." Nasreen ta ce "yanzu ina zaku nufa?..." Tasleem ta ce "dole ta ɗakin ta zamu shiga domin nan ne kawai hanya mafi sauƙi...." Nasreen ta ce "ki mallaki key ɗin ɗakin ta ne?..." Tasleem girgiza kai tayi sannan ta ce "ban mallaka ba amma yanzu zan gado yanda key ɗin yake..." Ta lumshe idanuwanta cikin lokaci ƙanƙani ta buɗe tana faɗin "ba da key ake buɗe ɗakin ba, sai da jinin jikinta ɗakin yake buɗuwa amma kar ku damu jinin mu ɗaya da ita, zanyi amfani da jini na...." Daga nan suke nufi room ɗin Madam Nablah, suna zuwa Tasleem tasa reza a hannun ta sai ga jini ya ɗiga akan ƙofar ɗakin, sai da ƙofar ta shanye jinin kafin ta karɓi jinin a matsayin mai mallakar ta, sai ga ƙofa ta buɗu da kanta, a take suka yi saurin shiga, ɗaki kamar aljannar duniya domin ba ƙaramin tsaruwa ya yi ba sai dai ko wani ɓangare da ajiyar tsafi a jiki mai ado da kwalliya.... Tasleem kai tsaye ta nufi wani ƙaton photon mahaifinta wanda ta nan ne ƙofar take, Amaar da Abeesh kallon photon suka yi sun san cewa photon mahaifin su Tasleem ne domin da wayon su ya mutu, gani suka yi Tasleem ta rufe ido tare da wasu karatun yaren aljanu kamar yanda taga Mommynta tayi domin bata manta wannan sirrin ba, gani suka yi photon ya rabe biyu sai ga wani ƙofa nan ma ƙofar ta buɗu, cike da mamaki Amaar ya ce "kenan ana amfani da wannan photon wurin tsafi?...." Tasleem ta kalle shi cikin damuwa sannan ta ce "al'amarin Mommy ba sauƙi...." A haka suka kutsa ciki da addu'o'i a bakin su, baƙin duhu ne a wurin ko gaban su basa iya gani, Tasleem rufe ido tayi tare da furta wata kalma ta haske sai ga sumar gashin ta wanda yake a kwance har gadon baya ya bayyana da wani irin haske, haske mai sheƙi wannan ya haska ko ina na wurin, haka suke kallon wurin kamar hasken rana, Amaar murmushi kawai yayi domin kaɗan daga cikin baiwar haske, Abeesh kam gaba ɗaya ya cika da mamaki ganin yanda Tasleem ta koma, sumar gashin ta ya koma fari tass kamar furfura sannan ya bayyanar da haske, a ruɗe ya furta kema tsafi gare ki?..." Tasleem tayi murmushi sannan ta ce "ba tsafi ba, baiwa ce ta haske..." Amaar ya dafa kafaɗarsa ya ce "ita ɗin sarauniyar Haske ce kar ka damu da hakan...." Shima Abeesh murmushi ya yi suka cigaba da tafiya, sai da suka yi tafiya mai nisan gaske har sun zo dab da wurin suka tarar da wani ƙofar ƙarfe anyi katanga da wurin da Mahaifin su Amaar yake, wanda babu bil'adama da zata tsallake wannan ƙofar.... Cike da mamaki Tasleem ta ce "yanzu kuma? amma lokacin da nazo nan babu wannan ƙofar...." Amaar ya ce "ta gane cewa akwai wanda yasan da wurin shiyasa ta kafa tsaro..." Abeesh ya ce "yanzu taya zamu ratsa nan wurin?...." Amaar ya kalli Tasleem sannan ya ce "kiyi amfani da ƙarfin ikonki ki sama mana hanyar wuce wa...." Tasleem gaba ɗaya ta rikice ta soma faɗin "ban san ta yanda zan fara ba..." Amaar ya ce "Tasleem zaki iya, kiyi ƙoƙarin ganin cewa zaki iya, ke fa sarauniyar Haske ne kar ki karaya da wuri haka...." Tasleem cikin ƙwarin gwiwa ta rufe idanu ta fara motsi da lips ɗin ta alamun akwai abinda take faɗi a cikin zuciyar ta, wani haske ne ya bayyana a cikin tafin hannunta lokaci guda ta da fa jikin ƙofar da hannaye masu ɗauke da haske, nan ta fara ƙoƙarin tura wannan ƙofa da ƙarfin haske, gaba ɗaya haske ne ya mamaye ƙofar... Ta jikin ƙofar suka ji murya na tashi a rikice ana faɗin: “Kuna son sanin gaskiya? Toh ku ji: Amaar ba irin mutumin da kuke tunani bane. Kuma Tasleem... ke 'yar wanda ke jini da Madam Nablah ba wai jinin haske ba. Idan gaskiya ta fito, ƙaunar da kuke yiwa juna zata koma ƙiyayya.” Tasleem ta tsayar da abinda take ta kalli Amaar tare da faɗin “Me ake nufi? kenan har yanzu haske bai gama karɓata ba saboda ni jinin Madam Nablah ce? sannan wani irin gaskiya in ta fito soyayyar mu zata koma ƙiyasta?..." Amaar girgiza kai ya yi sannan ya ce "wannan kalmar ɗorata akai akayi domin a tsoratar da mu amma soyayya da aka ginata ta hanyar gaskiya bata taɓa komawa ƙiyayya, ke Sarauniyar Haske ne bakida wani alaƙa da duhu..." Amaar ya kalli jikin ƙofar cikin ƙwarin guiwa ya ce “Komai gaskiya ce, zamu fuskance ta....." ★★★★★ A gefe guda kuwa, Shaprees yana cikin mawuyacin hali. Ruhinsa na cike da damuwa da rikicewa. Ganin mahaifin wani dattijo (mahaifin su Amaar) cikin gilashin asiri ya jefa shi cikin rudani. Shaprees yana zaune a wurin da yake gudanar da sirrin sa yana kallon cikin wuta ya ce: “Madam Nablah ta ɓoye gaskiya. Wannan ba dai-dai bane. Wannan tsoho… yana da alaƙa da hasken da Sophia ta ke kira.” Zuciyarsa ce ta fara ɓallewa daga duhun da Madam Nablah ta jefa shi ciki. A hankali, harshen soyayya da gaskiya ya fara haskaka cikin zuciyarsa. Shaprees a hankali ya furta: “Asmeen ba zata cancanci wannan hukunci ba... kuma Sophia ba zata so haka ba.” ★★★★ Madam Nablah kuwa, tana zaune a cikin ɗakin tsafinta, ta fara jin karfi yana kubucewa daga jikinta. Ta juya cikin madubi, amma madubin ya fara hayaƙi. Madam Nablah a rikice ta furta: "Wani yana shirin tono sirri... wani yana tasowa daga ƙasa?" Sai wani baƙon haske ya fito daga madubi. Fuskar Abul Abeesh ne. ta tintsire da dariya amma cikin zuciyarta ta fara jin tsoro da faduwar gaba. Madam Nablah a ruɗe ta miƙe tsaye tana faɗin: “Bai kamata ka rayu ba! Na tsare ka da tsafin da babu wanda zai iya warwarewa! Amma a yanzu ana shirin ruguza wannan tsaron da ƙarfin haske shin waye wannan mai ƙarfin ikon shiga makomata?....." Sai wani murya daga cikin madubi ya furta: “Idan haske ya haɗu da gaskiya, komai na duhu zai fāɗi...” Madam Nablah ta firgita. Ta fahimta cewa hasken da take ƙoƙarin hana wa shi ya fara fitowa. Kuma wannan haske, ba daga waje yake ba — daga cikin waɗanda ta cuta da hannunta ne..... *NEXT PAGE.....* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 35 to 36 Tasleem da ƙarfin tsafin hasken ta take ƙoƙarin buɗe ƙofar nan, cikin ɗaga murya da azaba take faɗin "Ya Amaar ku taimaka mun..." Amaar da Abeesh hannu suka sa zasu ture ƙofar, ba shiri suka ja da baya tare da yarfe hannayen su sakamakon wutar ƙuna da suka ji, ƙofar ta ƙone musu hannu, Abeesh tsabar azaba sai da ya durƙusa, Amaar ya ce "wannan ƙofar da wuta aka ƙirƙire shi, Tasleem ta ce "na ƙirƙiri haske don ƙofar ta buɗu amma na riƙe hasken ne da ƙarfina, ƙarfina ya kusan ƙarewada zaran na sake komai zai koma baya..." Amaar ya ce "a'a Tasleem ki ƙara daure wa naga ƙofar tana motsi..." Tasleem kamar zata yi ihu ta ce "to ku taya ni manaaaa...." Amaar ya ce "taya zamu taya ki alhalin bamu da ƙarfin ikon tsafi..." Tasleem ta sake furta "Da addu'ar bakin ka zaka taimaka mun, nasan zai mana amfani..." Amaar da Abeesh riƙe hannun juna suka yi tare da jero addu'o'i, da ayatul kursiyu...... Abul Abeesh yana ɗaure akan kujera ba abinda ya canza masa, kullum a haka, da baƙar hula yanda akayi rufe masa fuska da shi, wani irin sanyi yaji yana ratsa shi saɓanin tiririn wutar da yake shaƙa akoda yaushe, a cikin ransa yake faɗin "tabbas haske na kusanta na, sanyi da iska mai daɗi na ratsa tsatson jikina, alkhairi na kusanta na, ina ji a jikina ƴaƴana suna kusa da ni...." Haka yake ta maganar zuci haɗe da murmushi..... Ya buɗe idonsa a hankali. Bayan shekaru ashirin a cikin duhu da shiru, ya fara jin haske yana ƙoƙarin shiga zuciyarsa. Numfashinsa yana zurfi, ya furta "Yarona... Armaan...da Abeesh su kusan iso gareni...." A sama kuwa, Amaar, Tasleem, Abeesh, suna ƙoƙarin buɗe ƙofar da ƙarfin Addu'ar su Amaar da kuma ƙarfin hasken Tasleem. Amaar yana duban Tasleem ya ce "Za mu buɗe ƙofar ƙasa — zan ga mahaifina da idona, idan har na same shi a cikin wani mummunan hali wallahi saina ɗau mummunan fansa nima...." Tasleem ta duƙar da kai cikin takaici da jin kunyar kasancewar ita ɗiyar Madam Nablah ce tana motsi da lips ta ce "Na tsorata. Amma yanzu zuciyata ta fi ƙarfin tsoro. Ina son a yi adalci.".. Abeesh yana kallon Amaar ya ce "Yanzu ne lokacin da zamu kawo ƙarshen tsafin da ya hana mu ganin gaskiya..." ★★★★★ A bangaren Asmeen, zuciyarta na ci gaba da jagulewa. Wani wuri a zuciyarta na ƙara yi mata kira — kiran da take ji daga can cikin zuciyar Shaprees. A daren jiya, ta gan shi yana kukan ɓoyayyen sirri. Asmeen a zuciyarta ta furta: “Shaprees yana ɓoye wani abu… amma me yasa ni nake jin zuciyarsa na kiran taimako? Shin zuciyarsa ba ta duhu gaba ɗaya ba ne...?” Ta miƙe sannan ta nufi ɗakin Shaprees. A lokacin kuwa, Shaprees yana kallon wani guntun hoto da ke ɗauke da Sophia — matar da ya rasa. Shaprees a hankali ya furta “Idan na auri Asmeen, zan iya mayar da Sophia? Ko kuwa zan jefa kaina cikin wani sabon duhu?” Ya tambayi zuciyarsa a dai-dai lokacin da Asmeen ta turo ƙofa, Jin turowar ƙofa yasa ya kalli bakin ƙofar kamar daman a tsarge yake, idonta da nashi suka haɗu. Asmeen idon ta akan sa yanzu ko tsoronsa ta daina ji, ta ce "Shaprees… ba zan iya aure ba tare da na san gaskiyar zuciyarka ba. Me kake ɓoyewa...?" Shaprees ya juya a hankali, kamar mai shirin furta wani abu mai nauyi ya ce "Zan sanar miki amma ba yanzu ba, akwai lokaci...." ★★★★★ A bangaren Madam Nablah, abubuwa sun fara fita daga hannunta. Madubin sihirinta ya ƙi nuna mata abin da ke faruwa a ƙasa. Garkuwarta na dusashewa. Madam Nablah a firgice ta ce "Na sha maganin komai... me ke faruwa yanzu?" Sai kuma wani ɗumi ya shiga ɗakin. Wata murya daga baya ta furta: “Yanzu lokaci ya yi… ki fuskanci abin da kika ɓoye.” Madam Nablah ta juyo da sauri — Shaprees ne tsaye a bakin ƙofa, idonsa yana haskakawa da ƙarfin da ba ta saba gani ba. Ya kuma cewa “Na gano gaskiya. Kuma ba zan ci gaba da aikinki ba. Wani sabon haske ya fara haskaka cikin zuciyata.” Madam Nablah cike da mamaki take bin Shaprees da kallo, a ɗan ruɗe ta ce "Kasan me kake faɗa kuwa Shaprees? ka fa karɓi tsafin wuta da kuma yarjejeniya, ZULQARNAIN ba'a jayayya da shi sannan ba'a karya masa alƙawari....." Shaprees juyawa ya yi ba tare da ya bata amsa ba.... Madam Nablah haka take huci kamar wata zakanniya har idanuwanta sun canza zuwa ja kamar garwashi... A ƙasan ƙasa ƙofar da aka ɓoye Abul Abeesh, sun yi nasarar buɗe ƙofar wuta daƙer, sannan suka buɗe murfin gidan ƙasan Amaar ne ya fara shiga kafin Abeesh sai Tasleem wacce ta biyo bayan su jiki a sanyaye... Ganin mutum a zaune kan kujera a ɗaure ga baƙar hula a rufe da fuskar sa, Amaar da sauri ya nufi wurin sa tare da durƙusawa yasa hannu ya buɗe masa fuska, Abul Abeesh wanda gashin gemun sa yake cike da furfura, tsabar azaba da ganin duhu akoda yaushe har idanuwansa sun ƙanƙance, hatta girar sa saida ya koma fari na furfura, Idanunsa suka haɗu da na Amaar da Abeesh, lokaci guda ya fashe da kuka. Duk da kamannin ƴaƴan nasan sun canza daga yanda ya san su tin yarinta, ya ji a jikinsa cewa zasu dawo gare shi domin Abul Abeesh asalin malamin kimiyya ne.... Abul Abeesh da hawaye akan fuskar sa shaɓe-shaɓe ya ce "Yara naa… kun girma." Amaar da Abeesh haka suka rungumi mahaifinsu cike da damuwa suna kuka, tare da faɗin "Abul! Abul!! Abul!!!..." Amaar yana kuka ya ce "Abul! ka yafe mun, ban san kana cikin wannan kogon hallakar ba, mun kasa maka amfanin komai Abul...." Abul shima kukan yake yana goge musu hawaye da tafin hannayensa da suke ta kakkarwa tsabar ɗaurin da yasha.... Abeesh shima fashewa yayi da kuka yana faɗin "Abul na, haƙiƙa an zalunce ka, kuma bazamu taɓa barin wannan tozarcin ta sha a banza ba, domin ka haifi ƴan halak...." Abul yana rawar murya ya ce "ku bar komai ga Allah! yana sane da komai kuma zaiyi ikonsa akai, ku kwantar da hankalin ku...." Amaar cikin ɓacin rai ya ce "Abul kayi hakuri amma dole zamu ɗau fansar abinda tayi maka, Kuma yanzu lokaci ya yi da za mu dawo da adalci ta so ta hallakar dani Allah bai bata dama ba, na samu tsiratarwa daga wurin Sarauniyar ruwa...." Abul ya kalle shi da murmushi kwance akan fuskarsa ya ce "ka samu tsiratarwa daga wurin Sarauniyar ruwa? Aljanar da babu mai kirkin ta da kuma adalcin ta da yawan fara'a da murmushi, na santa sosai domin ta kasance a cikin littafin hasken ruhi, labarinta na da yawa a cikin littafin saboda mutumtaka da kuma darajar ta, asalin sunanta Aryana ake ƙiranta da suna Miemie, sarauniyar kyawawan Aljanun mata da bil'adama duk babu wanda ya kaita kyau da kyan sura, tana taku kamar ɗawisuwa, naji daɗi sosai daka faɗa hannunta sai kuma gashi ka rayu ata sanadiyar Sarauniya Miemie...." Amaar cikin tausayawa yake kallon mahaifinsa cikin ƙwarin gwiwa ya ce "hakane Abul, takan yawan kawo mun ziyara a cikin mafarki na, a hannunta na fara girma a cikin wani kogon haske, amma sai dai a matsayin mutum take fito mun, kullum a yarintar ta take bata tsufa....." Abul ya jinjina kai sannan ya kalli Abeesh cikin murmushi ya ce "yaro na kuma Autana fatan kana lafiya..." Abessh sake rungumar Abul ya yi yana kuka... A yayin da Tasleem take gefe guda gaba ɗaya jikinta a mace yake ta kasa motsawa tsabar tsananin kunya da damuwar da ta tsinci kanta a ciki.... ★★★★★ Madam Nablah a fusace ta shigo falon tana huci sakamakon maganganun Shaprees na rashin ɗa'a kuma yana so ya bijire mata, ga wasu alamomin da take ji kamar wani abu yana shirin faruwa a ɓangaren Abul Abeesh... Nasreen wacce fitowar ta kenan daga kitchen ta tarar da Madam Nablah tana haura saman benin part ɗinta,. bata san lokacin da ta furta "Mommy! Mommy!! Mommy!!!...." Madam Nablah a slow ta juyo tana kallon ƙasin falo yanda Nasreen take ƙoƙarin hauro yanda take da gudu, sai da ta iso compound ɗin part ɗin ta sannan ta tsaya a gaban ta tana faɗin "daman so nake na shigo room ɗinki zanyi miki gyara..." Madam Nablah cike da mamaki take binta da kallo cikin rashin fahimta ta ce "shin daman kina shiga room ɗina ne?..." Girgiza kai Nasreen tayi tana faɗin "but Mom laifi ne don na shiga room ɗinki?..." A fusace Madam Nablah ta ce "amma tinda kike kin taɓa shiga? and tell me wani munafurci kuke shiryawa? ina Tasleem? Ina Amaar da Abeesh?..." Nasreen lumshe ido tayi cikin tsoro da fargaba ta ce "Mom sun fita ne..." "Zuwa inaaa?..." Madam Nablah tayi tambayar idonta a cikin na Nasreen wacce take ta faman haɗa zufa.... Nasreen ta ce "i don't no..." Madam Nablah ta ce "bana buƙatar gyaran nakin, ki tafi ki bani wuri kafin nayi wurgi dake ta taga ...." Har Nasreen ta juya taji Madam Nablah ta darara mata tsawa kamar daga sama tana faɗin "Keeee! who open my room?...." A tsorace Nasreen take kallon ta, ta ce "Mom please ki ƙyale ni haka ban sani ba wallahi..." Kafin tayi wata yunƙuri har Madam Nablah ta shaƙo wuyanta tana zazzaro ido ta ce "gaya mun ina Tasleem? and waye yazo har bakin ƙofar ɗakina ya buɗe da jinina? ...." Nasreen sai zazzaro ido take tsabar shaƙar da ta sha, har ta fara jujjuyar da ido, numfashi yana shirin ɗaukewa sai a lokacin Madam Nablah ta sakar mata wuya tana huci, a fusace ta tura ƙofar da ƙafarta daman ba'a gama rufe ƙofar ba..... Tana shiga kai tsaye hanyar da zai kaita ɓangaren Abul Abeesh ta nufa da gudun gaske.... Nasreen a ruɗe ta miƙe tare da sauƙa ƙasin falo da gudu tana tangal-tangal, akan kujerar falo ta faɗa tana sakin numfashi daƙyar.... ★★★★★★ Tasleem kanta a ƙasi tana wasa da yatsunta taji an ƙira sunanta cikin rawar murya, Abul ne yake kallon ta da hawaye kwance akan fuskarsa yana faɗin "Ƴata zo mana, ya kika zauna a gefe, ke ma zo naji ɗumin jikin jikina..." Tasleem fashewa tayi da kuka kamar daman jira take a taɓota ta yi kukan, zuwa tayi ta rungumi Abul tana kuka, shi kuwa sai faman rarrashin ta yake tare da bata hakuri akan ƙaddarar da suka tsinci kansu a ciki.... Tasleem tana rungume da Abul bata san lokacin da ta ɗago a zabure ba, a yayinda idanuwanta suka koma fari soll ba ɗigon baƙi ko ɗaya, sumar gashin ta ma ya koma fari soll like furfura... Amaar da Abeesh daman sun san tanada wannan ikon, alamun akwai abinda yake shirin faruwa, Abul yana kallon ta cike da mamaki ya ce "me yake faruwa dake ne ƴata...." Amaar yana fuskantar ta ya ce "Tasleem me ya faru, ki sanar mana yanzu ...." Cikin rawar murya ta ce "gata nan zuwa, yanzu haka ta nufo yanda muke, ta kusan isko mu..." Amaar da Abeesh kallon juna suka yi suna ƙoƙarin samawa kansu mafita suna tunanin ta yanda zasu fita da Abul... Madam Nablah tana zuwa wurin ta tarar an buɗe ƙofar wuta, girgiza kai tayi sannan ta shige still ta samu ƙofar ƙasa yanda Abul Abeesh yake a buɗe, ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske tana tunanin waye mai ƙarfin ikon da ya buɗe ƙofar wuta har ya shigo yanda Abul Abeesh ya ke, alhalin babu wanda yasan a yanda yake.... A lokacin Madam Nablah ta rufe ido tare da sauya rigar jikinta zuwa baƙar doguwar riga na baƙin tsafi, fararen idanuwanta suka ɗauke zuwa baƙaƙe, sai idon ya zamo wulik ba haske ko ɗaya, sumar gashin ta duk suka tashi sama kamar wanda iska ke hura mata, cikin murmushin mugunta ta fara taka matakalar benin da zai kai ka ƙasin kogon.... Tasleem hannu ta miƙa wa Amaar shima ya riƙe nata sannan ta miƙa wa Abeesh ɗayan hannun shima ya riƙe, Amaar da Abeesh suka miƙawa Abul duk suka riƙe hannun juna suka haɗa cycle daga bisani Tasleem ta rufe ido tare da motsa lips ɗin ta ba tare da an san abinda take faɗi ba, lokaci guda sai ga haske ya bayyana kafin Madam Nablah ta ƙaraso duk suka ɓace sai ƙurar wurin, Dai-dai lokacin da Madam Nablah ta faɗo wurin, abinda ta tarar ne ya firgita mata ƙwaƙwalwa, ba ƙaramin razana tayi ba ganin babu Abul Abeesh, tsawon shekaru Ashirin tana tsare da shi amma lokaci guda ya kuɓuce mata, tsabar tashin hankali bata san lokacin da ta faɗi ƙasi ba, haka numfashin ta yake fita daƙyar, tana zaune a ƙasin ciyawar wurin..... Lokaci guda ta kurma uban ihu tana buga hannayenta a ƙasi, wurin ne ya tirniƙe da hayaƙi tsabar ɓacin ran da Madam Nablah ta shiga, ihu take bana wasa ba.... Su kuwa su Tasleem da Amaar da Abeesh ba a yanda suka sauƙa sai a ɗakin Amaar dake cikin gidan, a kan katafaren gadon Amaar suka kwantar da Abul, duk zama sukayi suna farin cikin dawo da cikon farin cikin su da suka rasa, yanzu komai ya dawo hannun su...... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 37 to 38 Madam Nablah ganin ihun takaicin bazai kaita ko ina ba yasa ta zabura a fusace, ganin tafiya zai zame mata aiki yasa ta ɓace lokaci guda bata tsaya a ko ina ba sai a wantalelen falon gidan ta, Nasreen tana zaune akan kujera ganin Madam Nablah ta bayyana kamar wacce aka cillota akan iska a durƙushe akan carpet, idanuwanta jajawur kamar garwashi, cikin fushi ta ɗago tana kallon Nasreen wacce itama a zabure ta miƙe tsaye tare da furta "Mom..." Madam Nablah miƙe wa tayi tare da faɗin "at this moment not Mom, just call me Devil Mom...." Kafin Nasreen ta ankare har Madam Nablah ta shaƙo wuyan ta tare da ɗaga ta sama da hannu ɗaya cikin ƙwayar idanunta haka suke ci da wuta, jikinta yana fitar da farfatsin wuta, sumar gashin ta haka suke bin iska su na tashi sama.... Nasreen da ta gama tsure wa bata san lokacin da ta kwara uwar ihu ba sai da gidan ya ɗau sautin, kafin muryar ta disashe sakamakon shaƙar da ta sha, Madam Nablah a fusace ta ce "ina malamin kimiyya?...." Nasreen abinda ya ƙara firgitar da ita shine jin yanda muryar mahaifiyarta ta koma kamar baƙin Aljanin duhu, ga ƙatuwar murya mai rikitarwa, haka take tambayar ta "ina malam Junaidu? Ina Tasleem? Ina Amaar? Ina Abeesh? Ina suka kai malam Junaid?...." Magana aka yi ta baya ana faɗin "gamu nan..." Madam Nablah waiwaya wa tayi da launin eyes ɗin ta na wuta tana kallon yanda aka yi magana, Tasleem ce ta sauƙo daga upstairs room ɗin Amaar ta shigo falo, bayan ta kuwa Amaar ne sai kuma Abeesh yana riƙe da Abul suna tafe a hankali sakamakon ciwon ƙafar da Abul yake fama da shi, suna shigo wa falo Abeesh ya zaunar da Abul su kuwa suka kasance a tsatstsaye, idon Madam Nablah akan Abul sai huci take tayi, Tasleem ce ta matso kusa da ita tana faɗin "Mom ki sakar mun wuyan ƴar uwata kar ki kashe ta akan laifin da bata aikata ba, in laifi ne ni na aikata ba ita ba, don haka ki sauƙar da ita dan Allah...." A fusace Madam Nablah ta darara mata tsawa tare da faɗin "kar ki sake haɗa ni da Allah, kuma ni ba Mom ɗin ku bace ni ɗin devil Mom ce...." Tasleem ta jinjina kai cikin lallami take binta akan ta ƙyale Nasreen, sannan ta ce "mai ta miki da zaki huce takaicin ki akan ta?..." Madam Nablah ta ce "Meyasa ta munafurce ni? meyasa ta ɓoye mun abinda yake faruwa?..." Sai a wannan lokacin Amaar ya yi magana yana faɗin "ina mu kike nema? to gamu mun bayyana a gaban ki shin mai zaki mana?..." Madam Nablah idonta a cikin nashi ta ce "meye dalilin da yasa ku ka shiga gonata?...." Amaar ya ce "ki tambayi kan ki, ke meyasa kika shiga gonar mu? kin dai san mahaifin mu shine babban gonar mu kuma shi kika taka, kina nufin zamu bar ki ne?...." Nasreen har ta fita hayyacinta tana shirin daina motsi, idanuwanta sun ƙaƙƙafe, gaba ɗaya hankalin Abeesh ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin a halin da Masoyiyar sa take, da sauri ya kalli Tasleem yana faɗin "Please Tasleem kiyi wani abu kar ta kashe mun ita..." Girgiza kai Tasleem tayi tare da faɗin "duk abinda zan yi yanzu zai iya cutar da jikinta, kuma dole mahaifiyata ce ko a wani hali take...." Tasleem ce ta ƙara maida idonta kan Madam Nablah sannan ta ce "Mom! Nasreen fa kike shirin kashe wa ba Tasleem wacce kike ƙi ba, ke fa kika haife ta kuma ita ɗin makullin zuciyar ki ce shin kin manta, daga Asmeen sai Nasreen masu kyautata miki, ni kuma Tasleem ni ce mai bijire miki ni ya kamata ki kashe...." Tasleem tana kuka tana roƙon ta, har sai da ta durƙusa ƙasi tana mata magiya... Madam Nablah ganin yanda Tasleem take kuka a durƙushe a gaban ta ne yasa ta jefar da makamin yaƙin ta, a hankali ta sauƙar da Nasreen ta ajiye ta akan kujera... Da gudu Tasleem ta nufo wurin Nasreen tana ambatar sunan ta tare da rungumar ta.... Ita kuwa Madam Nablah nufan wurin da Abul yake a zaune tayi cikin fushi, kafin ta ƙara sa Amaar ya yi saurin shiga gaban ta yana faɗin "kada ki kuskura, domin kuskure na farko kin yi shi, na biyu kuwa bazan taɓa barin hakan ya faru ba ni Armaan Junaid, kulawar sa ta koma hannu na...." Madam Nablah girgiza kai tayi tare da sakin murmushin mugunta ta ce "mai zaka iya yi? kaima baka fi ƙarfin nayi da ga-da ga dakai ba, na murƙushe ka hankali a kwance..." Murmushi shima ya yi tare da faɗin "wancan Amaar ɗin ba shine yanzu a gaban ki ba, wannan Amaar ɗin babu tsoro ko fargaba a zuciyar sa, dai dai nake da na farmake ki...." A fusace ta ce "mai kake taƙama da shi?...." A takaice Amaar ya furta "ALLAH...." A take ta wurga masa wani ɗan ƙulƙulen wuta a jikinsa nan rigar jikinsa ta fara ci da wuta, a zabure Amaar ya ankara haka yake karkaɗe wutar amma wutar sai ƙara ci take, ga yanda fatar jikinsa yake ƙonewa yana jin raɗaɗin ƙunar wutar... Tintsirewa da dariya Madam Nablah tayi sannan ta ce "nuna mun ikon da kake da shi har kanada ƙwarin gwiwar tinkara ta..." Abeesh gaba ɗaya hankalin sa tashi ya yi ganin yanda wuta yake ci a jikin ɗan uwansa gaba ɗaya ta gama cin rigar jikinsa, haka yake taya shi kar kaɗe wutar shima haka hannunsa tayi jawur tsabar ƙuna... Tasleem a ruɗe tayo kansa ganin yana azabtuwa da wuta tana zuwa ta rungume shi a take wutar ta mutu, sauƙe numfashi Amaar ya yi har idanuwansa sun yi ja, jikin sa ya yi burɗi-burɗi da tabon wuta.... Tasleem cikin takaici ta juyo tana kallon Madam Nablah murya na kakkarwa take faɗin "Mom ki dakatar haka, wani irin abu ne haka, meyasa bazaki taɓa canzawa ba, ke wata iriyar annoba ce?..." Madam Nablah cike da mamaki take binta da kallo, ba mamakin maganganun da take faɗa mata ba sai yanda take da ikon kashe mata wutar da ta rura, tana tunanin a yanda ta samu wannan ƙarfin, kawar da tunanin ta tayi tare da faɗin "Tasleem ni ce Annoba?..." Abeesh ne ya tsaya a gabanta cikin fusata ya ce "abinda yafi Annoba ma kin fi, ke shugaban shaiɗanu ne wanda baza ki mutu cikin haske ba, ke da shiga Aljanna sai dai ki ga masu shiga amma ke yanda kike sarauniyar wuta haka zaki tabbata a cikin wutar jahannama da yafi wutar da kike da shi zafi da raɗaɗi..........." Kafin ya ƙarasa maganar ya ji sauƙar mari akan fuskar sa, ɗagowar da zai yi yaji an ƙara zabga masa marin ta ɗayan ɓangaren, cike da mamaki yake bin Nasreen da kallo wacce jin maganganun da yake jifan mahaifiyarta da su ne yasa ta taso, tana kuka tana faɗin "Ya Abeesh na gode sosai, sakayyar da zaka mun kenam? Mahaifiyata wacce ta yi silar kawo ni duniya har muka san juna yau ita ce kake yiwa fatan tabbata a jahannama? nake ga ko wani irin hali take ciki bai kamata waɗannan munanan kalaman sun fito daga bakin ka ba, fatan shiriya da addu'a ya kamata mu dage mata ko Allah zai dawo mana da ita dai dai, to bari ka ji har yau har gobe uwa uwata ce kuma nafi sonta fiye da wani na, kuma Alhamdulillah ita ta raine ka, a hannunta ka tashi har ka mallaki hankalin kan ka....." Abeesh jinjina kai ya yi tare da faɗin "good! wato bata cancanci haka ba koh? duk da irin tozarcin da tayi mana ta kawar mana da farin ciki, ta ruguza mana farin cikin ahali, ki kalla wannan shine mahaifin mu ki dube shi dakyau tsawon shekaru Ashirin tana riƙe da shi a wurin da babu haske, a ɗaure da wasu irin caka hakan ma fuskar sa a rufe da baƙin hula, ba abinci mai kyau ba ruwa mai kyau a haka ya cigaba da rayuwa har zuwa wannan lokacin amma ki saura da sanar mun wai a hannunta na taso na girma, Allah ya wadaran irin wannan rainon domin ni ban gode ba, gwara ta barni akan titi ina gararan ba har na girma, wannan Ɗan uwana ne jinin jikina ki dubi irin zaluncin da tayi masa tin bai mallaki hankalin kan sa ba, tayi ƙoƙarin raba shi da duniya, Nasreen kin ban mamaki da har zaki shigar wa mahaifiyar ki faɗa...." Nasreen tana kuka ta ce "ba wai ina goyon bayan ta bane, fatan azabar da kake mata ne sun yi yawa..." Ya yi saurin katse ta da cewa "Azaba ita ta zaɓarwa kanta, dole nayi mata fatan tabbata a cikin ta...." Nasreen ta ce "Yaa Abeesh ba ita bace...." A fusace ya ce "ba ita bace to ke ce? ko ma wacece tasan abinda take ba daidai bane, please Nasreen leave me alone kin fiye son kan ki da yawa...." Tana kuka zata yi magana ya darara mata tsawa tare da faɗin "nace ki ƙyale ni kowa ya yi rayuwar sa..." Nasreen tana kuka tare da girgiza kai ta bar falon da gudu kai tsaye upstairs ta haura can ɗakin su.... Amaar kuwa har yanzu bai gama dawowa dai dai ba, ga hajijiyan da yake shirin ɗaukar sa... Sauran kaɗan ya faɗi Abeesh ya yi saurin riƙo shi tare da faɗin "please bro kar ka rufe eyes ɗin ka...." Tasleem itama wacce idanuwanta suka disashe tsabar kuka kallon jikin Amaar ta yi wanda wuta ta gama cin rigar jikinsa sai iya fatar sa ake gani duk ya yi jawur, zaro ido tayi waje ganin yanda wutar tsafi ta ratsa jikinsa haka wutar yake yawo a cikin jikinsa, a hankali ta ɗago da hannunta ta ɗora hannun akan ƙirjinsa, kaf sai da ta gama janye wutar jikin sa kafin ta sauƙar da hannunta tana yarfewa, domin wutar ba ƙaramin ƙarfi gareta ba, sai a lokacin Amaar ya dawo hayyacinsa ganin yanzu an cire masa raɗaɗin da yake ji a jikinsa, jikinsa ya dawo normal kamar wuta bata taɓa ba, Abeesh ne ya zaunar da shi duk suka zauna...... Madam Nablah tana tsaye ta kafa idanunta akan wanda take hari wato Abul, Abul shima ita yake kallo ganin irin kallon da take masa ne yasan akwai abinda take son aikatawa yanzu, kafin ya gama iddasa tunaninsa har ta mulmulo wuta daga hannunta zata jefa wa Abul a fusace Tasleem ta darara mata tsawa tare da furta "Mommy...." ta kunna haske ta hanyar amfani da hannunta ta saita Madam Nablah da wannan hasken, a gigice Madam Nablah ta rufe fuskarta da hannu tana faɗin "Tasleem meye haka, kinada hankali kuwa? zaki kashe mun idanu, wayyo Allah bana son haske, bana son haske zaki tarwatsa ni....." Madam Nablah sai da ta durƙusa ƙasi gaba ɗaya haske ya zagaye ta, haka take fitar da farfatsin wuta.... Tasleem kuwa gaba ɗaya ta canza zuwa asalin sarauniya, idanuwanta sun koma fari soll ba ɗigon baƙi sannan sumar gashin ta shima ya koma fari soll ga yanda haske kamar walƙiya yana fita daga cikin tafin hannunta zuwa kan Madam Nablah, haske da wuta ne suka haɗu, cikin ƙarfin wuta ZULQARNAIN ne ya buɗe idanunsa ganin haske yana shirin cin galaba akan wuta, cikin ƙarfin ikonsa yake magana da zuciyar Madam Nablah yana faɗin "idan kika bari haske ta ci nasara akan ki zaki rasa komai, ki miƙe da ƙarfin ikon ki, Nablah ki buɗe idanunki haske ne a gaban ki...." Madam Nablah duk taji wannan maganar da ZULQARNAIN ya yi mata, a fusace ta miƙe tsaye cikin ihu da fusata lokaci guda ta tarwatsa wannan hasken dake cutar da ita ta hanyar kunna wata azababbiyar wuta marar jin rarrashi da taimakon ZULQARNAIN..... Haske da wuta ne suka zama ƙanƙara tare da tarwatse wa suka zama kamar duwatsu, Tasleem ce tayi baya zata faɗi Amaar ya yi saurin riƙo ta, ita kuwa Madam Nablah yanda ta tsaya cikin jarumta ko motsi bata yi ba, ga yanda sumar gashin ta ya tarwatse duk suka rufe mata fuska... Duwatsun haske ne suke ta sheƙi da walwali a falon ga kuma na wuta shima yana fitar da nashi ƙyallin, cikin ƙatuwar murya Madam Nablah ta ce "kina so ne kici nasara a kaina? to kin yi ƙarya Devil Mom bata faɗuwa ƙasi...." Tasleem ta ce "Mom duk ke kika jawo, ke kika fusata ni...." Madam Nablah ta ce "taya kika samu wannan ƙarfin ikon? wannan ikon daga wurin wa kika samo? ta sanadiyar wa kika samu matsayin sarauta? saurauniyar haske kina shirin yaƙa ta, Shikenam! Shikenam!! Shikenam!!! ku cigaba da zama a cikin fadata akwai ranar ƙin dillanci...." Tana kaiwa nan ta nufi upstairs da gudu, ɗakinta ta shige tare da rufe wa, tana shiga ta fara sakin numfashi daƙyar tana rungumar jikinta, wani irin raɗaɗi take ji a cikin jikinta, zazzaɓi ne yake shirin rufan ta, bata san lokacin da ta fara hawaye ba, kwanciya tayi akan gadonta tayi rubda ciki tare da kifar da kanta, tana takaicin yanda Tasleem ta zama Sarauniyar haske.... Tana cikin wannan halin ne taga ɗakin ta ya turnuƙe da duhu, tsantsar duhu ne babu haske ko ziri ɗaya, da sauri ta tashi zaune tana kallace-kallace ko hannunta bata iya gani, rufe idanuwanta tayi sosai sannan ta buɗe su sai suka juye zuwa garwashi, farfatsin wuta ne yake fito wa daga cikin eyes ɗin ta, anan ne take iya ganin komai, wutar idonta ya kawar da duhun, abinda ta gani shine baƙar kuliya, wani irin kuka kuliyar tayi sai hasken ɗakin ya dawo normal amma idanun Madam Nablah basu dawo yanda suke ba, kallon kuliyar take da idon sanayya, kuliyar ce ta tako har yanda Madam Nablah take a zaune a bakin gadonta, a lokacin ne kuliyar ta dawo mutum, wata zureriyar budurwa ce ta bayyana mai tarwatsattsen gashi irin mai ƙullin nan, tana sanye da baƙaƙen kaya fuska ɗauke da murmushi a yayinda idanuwanta suke nan baƙi ƙirin ba ɗigo haske ko ɗaya, kamar yanda idon kuliya yake haka nata yake, a hankali idanuwanta suka washe zuwa normal, ta dawo kamar asalin mutum itama zama tayi a gefen Madam Nablah..... Madam Nablah kallo ɗaya tayi mata ta sau murmushi tare da faɗin "Catrina Baby Sarauniyar Duhu mai kawar da haske...." Catrina cikin izzah ta ce "nasan kina buƙatar taimako hakan yasa nazo gareki...." Madam Nablah ta ce "Nagode miki sosai Sarauniyar Duhu...." Catrina ta ce "a duk yanda haske yake to tabbas ni duhu ina wurin, an bayyanar da sarauniyar Haske a gidan nan hakan yasa nima na bayyana...." Madam Nablah ta ce "lokaci yana gab da kawo kansa, Sarauniyar haske da kuma Sarauniyar Duhu a yayinda ni kuma Sarauniyar Wuta nake tsakiyar ku...." Murmushin ƙeta Catrina tayi sannan ta ce "idan kuma Sarauniyar ruwa ta bayyana fa?...." Madam Nablah a zabure ta kalli Catrina, haka suke kallon juna, idon Madam Nablah ne ya koma wuta yana fitar da farfatsi, a yayin da itama idon Catrina ya koma duhu ƙirin..... *NEXT NEXT NEXT* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 39 to 40 Catrina cikin muryar sarauta ta sake furta. “Devil Mom... ke ce Sarauniyar Wuta. Ni kuma Catrina ce Sarauniyar Duhu. Na jiyo ƙarar rikitacciyar zuciyarki ne yasa nazo domin taimaka miki...." Madam Nablah sauƙe numfashi tayi tare da faɗin “Ki ce min da gaske ne Tasleem ta zama Sarauniyar Haske?” Catrina ta matso kusa da ita sannan ta furta “Haske da Ruwa sun haɗa hannu. Miemie zata Bayyana, Ita ce Sarauniyar Ruwa, Kuma za su sake jan hankalin ƴar ki — don ta jagoranci hasken da zai iya halaka mu.” Madam Nablah ta miƙe tsaye da murya mai cike da wutar ƙiyayya ta ce “To me zai hana mu murƙushe su gaba ɗaya? Ni zan ƙona su, ke kuma ki ɗauke su cikin duhu — ki hana su gani!” Catrina ta ce “Bazan iya daidaita ruwan Miemie ba, domin ƙarfin ikon ta ya ninka nawa Amma zan taimaka miki da sabbin aljanu. Wannan karon ba zaki ƙara faɗuwa ba Nablah...." Madam Nablah ta murmusa da mugun nufi. Idonta ya ɗauke hasken wuta sannan ta ce “Zamu fara da zuciyar Shaprees, Kafin su karɓi zuciyar Ruhi ta karɓi zuciyar sa, domin yana so ya bijirewa wuta da duhu...." Catrina ya ce “Idan Shaprees ya ci gaba da dawowa daga duhu, zan iya ɗauke masa zuciyar sa, gwara ya rasa rayuwar tasan gaba ɗaya...." Madam Nablah ta ce "ki saurara zamu bi komai a hankali ɗaya bayan ɗaya sai mun dai-dai ta rayuwar su, yanzu abu na ƙarshe da nake so na gudanar shine ɗaura Auren Shaprees da Asmeen da kuma Abeesh da Nasreen, a yau nake so a fara shirya komai gobe kuma Aure, Abul Abeesh zan bashi dama ya cigaba da rayuwa cikin ƴanci na wasu kwanaki...." Katrina ta ce "Dakyau..." Sannan Madam Nablah ta cigaba da cewa "zaki cigaba da zama a wannan gidan a matsayin baƙuwa, kada ki bayyanar da kan ki tin yanzu sai komai ya fara girmama tukun..." Katrina ta kuma cewa "Dakyau..." Madam Nablah ta kuma cewa "gobe ranar shagalin biki zamu ɗauke Tasleem, zata kasance a wani ɓoyayyen wuri da yake da sirri, wanda gano yanda take abu ne mai hatsari...." Katrina ta ce "Dakyau amma a wani wuri kike tunanin za'a ɓoyeta wanda haske zai gagara shiga?..." Madam Nablah ta ce "tafkin tsafi na, cikin ƙasin ruwa na wani yanki na dana mallaka domin ba iya Miemie ce kawai mai gudanar da ruwa ba, akwai nawa ɓangaren ruwa amma bana haske ba...." Katrina ta ce "Dakyau! na jinjina miki...." Madam Nablah ta ce "yanzu zaki bayyana a cikin gidan a matsayin baƙuwa amma ki canza waɗannan baƙaƙen kayan nakin zuwa normal kaya kamar na mutane, sannan ki gyara fuskar ki kiyi kwalliya ki bayyana kamar tauraruwa...." Murmushi Katrina tayi sannan ta ce "haba Sarauniyar Wuta shin kin manta wacece Katrina? nifa kyau na ta musamman ce, ƙirƙirarren kyau wanda ba ruwanta da kwalliya kullum a cikin kyau take...." Madam Nablah ta ce "hakane! yanzu kin zama ta gida, ki bayyana musu tamkar ɗawisuwa...." Dariya Katrina tayi lokaci guda ta canza kayan jikinta zuwa wasu matsatsun kaya na fitar hankali, surar jikin ta ya bayyana kamar gimbiyar kyawawa, shigar jeans tayi da wata ƙaramar riga wanda ya bayyanar mata da cibiya, gashin nan ya gyaru har wani sheƙi yaƙe, tayi kyau sosai gata farar fata ce... Juyi tayi cikin salo sannan ya buɗe ƙofa ta fice, sauƙar ta falo bata tarar da kowa ba, haka take bin falon da kallo, ta ko ina haske ne, jinjina kai tayi sannan ta furta "Haske! mai ƙayatar da komai amma a cikin zuciya ta ina mai baƙin cikin ganin kowa a cikin haske...." Tana cikin maganar zuci idonta ya sauƙa akan Abeesh wanda yake sauƙo wa falo cikin sauri yana sanye da farar jallabiya, bai lura da Katrina ba sai da ya shigo falon, kallon ta yake cikin rashin sani haka ya nufi bakin ƙofa idonsa akan ta ita ɗin ma shi take kallo tana sakin ƙayataccen murmushi, bai tsaya sauraronta ba haka ya fice domin sauri yake zai tafi masallaci, Amaar kuma ya tafi can headquarters sai cikin dare yake dawowa.... Katrina neman wuri tayi ta zauna tana yamutsa fuska, Nasreen ce ta fito daga kitchen tana ɗauke da kulolin abinci zata kai can room ɗin Abul..... Ganin murɗa-murɗan gashin mace ta baya yasa ta shiga tsakiyar falon tana son ganin fuskar yarinyar, itama Katrina kallo ɗaya tayi mata sannan ta ce "sannun ki triplets daughter...." Nasreen kallon sama da ƙasa take mata daga bisani ta ce "sannu fa amma sai dai ban waye ki ba, daga ina?..." Katrina ta ce "ba buƙatar tambayata daga ina nake domin babu yanda za'ayi nazo gidan da ban sani ba..." Nasreen ta ce "Ayya baƙuwa muka yi kenan? to sannun ki..." Daga nan ta bar falon kai tsaye ɗakin upstairs ta haura yanda zai kaita room ɗin Abul, tana shiga ta tarar da Tasleem zaune a kusa da Abul tana bashi madara a baki cikin kulawa... Tasleem ɗagowa tayi tana kallon Nasreen da kuloli a hannunta ta ce "haba Nasreen kin cika sanyin jiki, Abul yana jin yunwa kin gagara gama abincin da wuri, ƙarshe madara take bashi...." Nasreen ajiye kulolin tayi tare da faɗin "Afuwa nake nema Saurauniyar haske..." Abul yana jin su sai murmushi yake ta sakar musu cikin so da ƙaunar su idan ya tuno da Mahaifinsu kuwa sai ya ji tausayinsu... Tasleem hararar Nasreen tayi sannan ta ce "bana so ki daina, ai ba'a koda yaushe nake sarauniyar ba...." Nasreen ta ce "haba sarauniyar mu, ya haka ne kam..." Tasleem tana turo baki ta maida idonta kan Abul sannan ta ce "Uncle ka ganta ko? na ce bana so ta daina...." Abul kallon Nasreen ya yi sannan ya ce "ƴata ki daina to tinda bata so..." Nasreen ta ce "shikenam Uncle na daina..." Anan suka yi wasa da dariyar su har Abul cikin kulawa Tasleem ta gama feeding ɗin sa.... Abeesh ne ya dawo a yanda ya bar Katrina anan ya dawo ya same ta, har zai wuce tayi saurin miƙe wa tare da tsayawa a gaban sa tana sakar masa raguwar murmushi... Cikin sassanyar murya ta furta "Sunana Queen Katrina, ni baƙuwace a wannan gidan, zan cigaba da zama daku har lokacin da zan tafi domin hutu nazo, ƴa nake a wurin ƙawar Madam Nablah...." Jinjina kai Abeesh ya yi sannan ya ce "ƴa ga ƙawar Madam Nablah kenan hakan na nufin ɗaya kuke gaba ɗaya?..." Katrina ta ce "eh ta hanyar zumunci ba, ina karatu a ƙasar england kafin lokacin da hutu na zai ƙare, fatan kayi farin cikin haɗuwa da ni?..." Abeesh ya ce "ke ƴar wata masarauta ce? naji kamar a sunan ki kin sakala Queen....." Katrina lumshe idanuwanta tayi bata son ya fahimci komai game da ita, hakan yasa ta buɗe idon a hankali take kallon sa cikin shauƙin soyayya ta ce "inkiya ne kawai amma ni ba ƴar masaraunta ba ce...." Abeesh shima murmushi ya yi tare da faɗin "kenam saboda tsananin kyan da kike da shi ne yasa ake ƙiran ki da Queen?..." Katrina ta ce "kusan haka amma ni nasan banida kyau ai, tsokana ne kawai..." Abeesh kamar wanda aka zabure shi ya yi saurin toshe mata baki tare da girgiza mata kai yana faɗin "kin yi kuskuren furta hakan Queen, domin ko a duniyar Aljanu sai anyi dace samun mace mai kyan ki, da farko kin ban tsoro na ɗauka Aljana ce ta fito mun a siffar mutum domin kyan ki ya wuce misali..." Katrina a hankali take lumshe ido tare da buɗe su a hankali cikin shauƙin soyayya da iya makirci, still hannun Abeesh akan kyakkyawan lips ɗin ta, sai a yanzu ya ankare ya sauƙe hannunsa tare da faɗin "sorry ban san lokacin da na toshe miki bakin ba..." Katrina matso dab da jikin sa tayi tana shafan kyakkyawan sajen fuskantar sa wanda ya kwanta luf, ga ƙamshin turaren da yake tashi a jikinta na fitar hayyaci a hankali ta furta "ba komai, ai kai ɗin na musamman ne baka laifi, koda kayi laifin sai dai a sumbace ka badai a hukunta ka ba domin kai ɗin tauraro ne, kallo ɗaya nayi maka naji ka burge ni, tsorona kar ka wulaƙanta ni...." Abeesh ya ce "koda matan aljannah suna bina da gudu ke ba abar wulakantawa bane...." Katrina ta ce "Nagode sosai da wannan matsayin, ina sonka sosai fatan zaka amshe ni hannu bibbiyu..." ta miƙa masa hannu da niyyar musabaha.... Abeesh shima miƙa mata hannu ya yi tare da jinjina kai...." Dai-dai lokacin da Nasreen ta fito daga ɗakin Abul, ganin Abeesh da Catrina hannu a haɗe yasa ta tsaya cakk, wani irin bugun zuciya taji, a lokacin Katrina ta riƙo fuskar Abeesh tana faɗin "kai ɗin na musamman ne...." Nasreen wani irin zazzafan hawaye ne ya gangaro mata na kishi.. Falon ne ya ɗauki shiru. Sai karar numfashin zuciyoyin da ke dukan duniya uku: na kishi, na haushi, da na nauyin zuciya. Sai a lokacin Katrina da Abeesh suka san da zuwan Nasreen... Catrina ta gyara tsayuwarta da natsuwa kamar sarauniya. Tsayin ta da siffar ta na burgewa, Fatar jikinta fari ne sol irin ta mayu, idanuwanta zinariya mai kama da na halittar duhu, amma tana fakewa da murmushin da ke kwaikwayon na jinƙai. Ta sauƙe hannunta daga kan fuskar Abeesh, sannan ta juyar da kai tana kallon Nasreen da ke tsaye cike da hawaye da tsananin kishi. Catrina cikin sassanyar murya ta ce “Ban son na ruguza miki komai… ban san ko ke ce matar da zai Aura ba, Ni baƙuwa ce kawai.” Nasreen ta matso kusa da ita, jiki na rawa da zuciya cike da ƙuna cikin zafi ta ce “Baƙuwa ce ke kike shashshafa mijin wani? Ke kin san me kike yi kuwa?...." Abeesh haka yake jin zuciyarsa tana ruruwar baƙin cikin abinda Nasreen tayi masa, tsaya kallon ta ma baya son yi cikin fusata ya ja dogon tsaki tare da ƙoƙarin barin wurin, Nasreen tayi saurin riƙo hannun sa tare da faɗin "Ya Abeesh ka saurare ni dan Allah...." A fusace ya juyo da niyyar marin ta sai kawai ya fasa, cikin zafin rai yake faɗin "na tsani duk wacce take ƙarƙashin Madam Nablah da kuma goya mata baya akan abinda take aikatawa, kije bana sonki yanzu, ba marin da kika mun ne yasa na tsane ki ba sai don nuna kin fi damuwa da mahaifiyar ki akan mahaifina duk da cutarwar da akayi masa, kin bani mamaki matuƙa, idan kuma kika cigaba da shiga shirgina sai na raunana miki zuciya, ki sa a ranki haka..." Daga nan ya bar wurin kai tsaye room ɗin Abul ya nufa..... Catrina ta kalle ta daga sama har ƙasa. Wani irin dariyar ƙeta da raini ta sakar, sannan ta juya gefe kaɗan, ta matsa gaban kujera ta zauna tana ta kallon yatsun kafarta kamar wata budurwar zinariya Ta ce “Yana fushi dake… ko baki lura ba? Na shiga ransa a cikin mintuna kaɗan, ke da kike da shekaru da shi baki iya riƙe zuciyarsa ba…” Wannan magana tamkar sara ne a kunnen Nasreen, Zuciyarta ta buga da ƙarfi, Hannunta har ya ɗago kamar zata daki Catrina, amma sai ta tsaya, Kuka ya hana ta magana, numfashinta ne yake hawa da sauƙa... Nasreen maganar zuci take “Me na yi wa Abeesh har ya tsane ni haka? Har ya zama haka?” Ta juya da sauri, hawaye na sauƙa daga idonta, sannan ta nufi ɗakin su, Da ƙyar ta taka ƙafarta har ta kai ɗakin, ta rufo ƙofa da ƙarfi, ta zube a ƙasa tana kuka kamar karamar yarinya. --- A falon kuwa Catrina ce ta miƙe tsaye cikin natsuwa. Wani ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskarta, na gamsuwa da cigaba da rikita soyayya tsakanin Abeesh da Nasreen. Tana jin daɗin ganin kishin ya fara cin zuciya. Catrina a cikin zuciyarta ta furta "Idan ransu ya karye, zuciyoyinsu za su samu girgiza. Idan zuciya ta rikice, ina da damar shigar da duhu..." Ta tafi da natsuwa zuwa wani ɗaki na baƙi inda Madam Nablah ta tanadar mata wuri, amma kafin ta shige, ta sai da ta kalli saman upstairs mataki na ƙarshe yanda zata ɗauka.... Tana tafe tana maganar zuci “Zan iya ɗaukar zuciyarsa gaba ɗaya… idan Nasreen ba ta farka ba.”..... Da haka ta shige ɗakin masauƙin ta. ★★★★★ Daren ya sauka da natsuwa, amma zuciyoyin gida sun cika da hayaniya. A ɗakin baƙi, Catrina ta zauna a bakin gadonta, tana shan ruwan sanyi a cikin kofin gilashi mai tsada. Hasken fitilar dakin na haskaka gashinta mai sheƙi kamar zinariya mai siffar duhu. A cikin zuciyarta kuwa, akwai fassarar dabaru. Akwai shiri. Catrina ta furta a hankali "Zuciyar Abeesh… mai ƙarfi ce, amma tana da rauni idan yana fushi, Nasreen ta manta cewa soyayya ba kyauta ba ce idan ba a kula da ita..." Ta miƙe. Tana tafiya kamar sarauniya, Ta zura rigar bacci mai launin azurfa, wacce ke kwance a jikinta kamar ruwa. Sai dai ba domin son burge Abeesh kawai ba, har da saƙo: tana son ya manta da Nasreen gaba ɗaya. --- A gefe guda kuwa... Nasreen tana kwance a kan gado, idanuwanta cike da hawaye. Tana tunanin kalaman da Abeesh ya faɗa mata. Kamar wuƙa suka ratsata. Nasreen a cikin ranta take faɗin "Shin ya manta da yadda muka fara? Da yadda na tsaya masa? Me yasa yanzu yake ƙoƙarin canza mun?" Tana tashi, ta nufi kofar ɗaki da niyyar komawa wurinsa. Amma ƙafafunta suka tsaya cak. Wani murya daga cikin zuciyarta ta ce “Ki barshi! Idan har zai iya juya miki baya da wacce bai ma sani ba, to ya dace ki ƙyalle shi!” Sai kuma wata murya mai taushi ta ce “Ki fahimce shi, ki yi haƙuri, ki nemi yafiyarsa…” Tana tsaye a tsakiyar waɗannan muryoyi, zuciyarta na sarƙe da alhini, idonta na kaɗa wa da hawaye. --- A ɗakin Abeesh kuwa, yana zaune a bakin gado, tunani fal cikin kansa. Ko da yake yana jin jiki da zuciyarsa sun gaji da Nasreen saboda wata ɓacin rai da ta haifar masa, amma a ƙasan zuciyarsa akwai soyayya mai zurfi da baya iya musawa. Amma yaƙin da ke zuciyarsa ya ruɗe, musamman da wannan sabuwar halitta mai kyau da ƙamshi kamar sararin samaniya ta fara ƙoƙarin shigar masa rai – Catrina. Yana da tsattsauran ra'ayi a kan soyayya, ya yarda da gaskiya, biyayya, da sauƙin hyiali. Amma yanzu ya fara ji kamar Nasreen ta canza. Catrina kuma tana nuna masa salo dabam. Abeesh a zuciyar sa ya furta “Ta bani kulawa, ta nuna mun soyayyar gaskiya bazan iya juran ganin Nasreen a cikin hawaye da zargi ba... Ba haka nake so ba…” Misalin ƙarfe 2 na dare.... WURIN ABEESH… Dare ya tsinke da shiru. Kamar kowane dare, an jima da kashe fitila, sai hasken farin wata daga tagar ɗakin da ke daddarewa a bango, Amma ba barci a idon Abeesh. Sai juye-juye yake yi a gado, yana tunani. Tunani ne cike da rikici da soyayya, fushi, ruɗani, da sabon abu mai kama da jaraba. Ji ya yi an buɗe ƙofar ɗakin sa a hankali, juyowa ya yi yana kallon bakin ƙofar. Catrina ce ta zo masa a hankali, tana daɗa rage tazarar dake tsakaninsu, tana sanye da rigar baccin ta... Abeesh ya tashi zaune tare da faɗin “Ke kuma? Me kike nema a nan cikin dare?” Catrina ta dafe ƙofa tana dariya ƙasa-ƙasa sannan ta ce “Na kasa yin bacci, Sai naji kamar zan fi samun kwanciyar hankali idan na ganka... King Abeesh....” Ya runtse ido. Wannan sunan da ya ji a bakin ta tamkar sabon wata ne ya ratsa cikin zuciyar sa da wani salo mai ɗauke da wani sirri, mayar da idonsa ya yi kanta tare da kama bakinsa, Ya ce “Wannan ba daidai bane. Ki koma ɗakinki.” Catrina ta matso kusa da shi sannan ta ce “Ban zo da mungun niyya ba. Kawai ina so ka san cewa ba kai kaɗai bane a cikin jin zafi…” Abeesh bai ce komai ba. Sai dai yanda take kallonsa, kamar ta fahimci komai cikin zuciyarsa. Cikin daddadan murya da dabara, ta matsa kusa da shi sosai. Hannunta ya sauka a kan hannunsa, Tana son jin irin karfi ko rauni dake cikin rayuwarsa. Zuciyarsa na yawo. Bai tura hannunta ba. Amma kuma bai kama ba. Abeesh ya ce “Kin san inada rauni Catrina... Kuma ni... ni ba mutumin da ke saurin yarda da sababbin mutane ba ne...” Catrina ta saka murmushi sannan ta ce “A lokacin da waɗanda ka yarda da su suka raunata ka, wani lokacin, sabon mutum na iya zama mafita…” Yayi shiru. Zuciyarsa tana tafasa da ruɗani. Cikin zuciyarsa, yana jin kalamanta suna ratsa shi. Sai dai a lokaci guda yana jin kamar wani ɓangare daga cikinta yana ɓoye wani abu. Shiru ya shiga tsakaninsu. Catrina ta miƙe tsaye cikin salo, ta zuba masa idanu. Sannan ta ce “Zan tafi… Amma zan dawo. Kuma in Allah ya yarda, wannan zuciyar taka zata dawo da murmushinta.” Ta juya. Sai kuma ta tsaya a ƙofa, ta ce: “Nasreen ta rasa hanya. Amma ni zan iya nuna maka sabon titi... Titi na gaskiya... ko kuwa na mafarki.” Tana kaiwa nan ta fice a ɗakin, tana fita ta ɓace cikin duhu. --- A GEFE GUDA – NASREEN… Nasreen tana zaune a gefen gado, hannunta ɗauke da littafin addu’a. Amma ba karatu take ba – kallo ɗaya kawai take wa shafin, Zuciyarta na cike da ƙuna. Wani abu yana ƙona ta fiye da zafin kalmomin Abeesh: yanda ya kalle ta kamar bai taɓa sonta ba, da kuma yanda bai damu da halin da take ciki ba... Sai dai Nasreen ba mace bace da zata zuba ido ta bari soyayyarta ta rushe. Ta miƙe, ta saka mayafi, sannan ta furta da ƙarfi: “Zan kare soyayyata. Ko da zan rasa komai. Ko da zan tafka kuka. Amma ba zan bari wata yarinya ta kwace min miji ba.”..... NEXTTTTTT........ New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 41 to 42 A DAKIN ABEESH… Tsakar dare ne. Shiru ya mamaye gidan. Daga wani ƙaramin fitilar bango ana iya hango Abeesh zaune a gefen gado, da labulen window a buɗe yana kallon duhun dare yana tunani. Tunaninsa cike yake da abubuwa biyu: Catrina, wacce ke da wani jan hankalin da ba zai iya fassara ba… da kuma Nasreen macen da ya fara soyayya da ita da zuciyarsa gaba ɗaya — amma ta raunata shi. Ya dafe kansa. “Me yasa komai ke rikicewa haka?” Yayi tambaya cikin zuciyarsa. Ƙaran ƙofa ya ji Ya juyo da sauri. A hankali ƙofar ta buɗu, Nasreen ce, cikin doguwar riga mai launin ruwan hoda da hijabi a kafada. Idonta cike da hawaye, fuskar ta sharaf da damuwa. Ta tsaya a ƙofar ba tare da ta shigo ba Abeesh cikin mamaki da ɓacin rai ya ce “Ke kuma... me kike nema a nan?” Nasreen cikin murya mai rauni ta ce “Ina son magana da kai, Abeesh... ka bani minti daya... na roƙeka.” Ya ɗan kalle ta, yaja numfashi mai nauyi, ya ɗan matsa gefe a gefen gado, bai ce komai ba yayi mata alamar ta shigo. Nasreen ta shigo a hankali kamar wacce take takawa akan ƙaya. Zuciyarta na bugawa, idonta na kallon sa har ƙasa. Sannan ta ce “Na san baka shirya ji daga gare ni ba... kuma gaskiya ne, na yi maka babban laifi. Amma zan mutu cikin nadama idan baka yafe mun ba...” Abeesh ya ɗago kai ya kalle ta sannan ya ce “Wani laifi kika aikata har ya sa kika zo da dare neman gafara?” Nasreen ta durƙusa ƙasi, idanunta cike da ƙwalla ta ce “Na mare ka, kuma na goyi bayan mahaifiyata, wacce ta raɗa maka azaba har ka rasa komai da ka sani... kuma da zuciya ɗaya nake cewa na tafka kuskure...” hawaye ne suka zubo daga idonta. ta ci gaba da cewa “Nayi kuskure na zaɓar tsoron mahaifiya akan gaskiyar da zuciyata ke gani. Kuma zuciyata ta san kai ne hasken da nake nema. Amma tsoronta da karfinta ya sa na tsorata… nayi maka rashin adalci...” Abeesh ya kalle ta. fuskar sa a washe Amma zuciyarsa bata sake ba. Ya daɗe yana kallonta ba tare da ya ce komai ba. Daga bisani yace: “Kin san mene ne ya fi komai zafi a rayuwa?” Nasreen ta girgiza kai Sannan ta ce “Mene ne?” Ya ce “Kin fi jin zafin mari da kalma, amma ni, na sha wahala cikin duhun da mahaifiyar ki ta jefa ni a ciki, na rasa tunani, na rasa imani... kuma da kika mare ni, ba wai fuskata kika mara ba — rayuwata kika ƙara jefa cikin ƙunci.” Nasreen ta fashe da kuka. Ta ce “Idan zan iya komai don in gyara kuskuren nan, zan yi. Zan tsaya a gabanka kullum in zubar da hawaye na har sai zuciyarka ta huce. Zan yi komai don in dawo da kai… Abeesh... kar ka bar ni.” Shiru ya yi ba tare da ya furta komai ba, Ya tuna kukan da yayi a lokacin da ya rasa komai. Ya tuna yanda zuciyarsa ke son Nasreen... amma yanda ya tsani abinda tayi masa ya wuce misali... Ya juyo gareta, cikin murya mai sanyi da kuma karfi yace: “Zan iya gafartawa… amma bana iya mantawa da azaba cikin sauri. Ki bar ni na zauna da zuciyata. Idan da gaske kina sona, ki bani lokaci… ki bani sarari...” Nasreen ta gyaɗa kai da hawaye, ta miƙe a hankali, ta fita da zuciyarta cike da fargaba da fatan nasara... ★★★★★★ *WASHE GARI* Ana shirye-shiryen bikin Abeesh da Nasreen, da kuma Shaprees da Asmeen. Gidan Madam Nablah ya cika da shirye-shiryen biki — kallo ɗaya zaka yi ka fahimci ana shirin wani babban abu. Falo da tsakar gida sun sha ado da launuka masu ban burgewa. an rataya fitilu da fure a jikin bangon gini, ƙamshi na turaren wuta da bakhoor yana yawo har cikin sararin gidan.... Abeesh Kwance yake a cikin ɗakinsa, yana kallon saman ceiling ... zuciyarsa taƙi nutsuwa. Catrina dai ta riga ta fara nasara wajen ɗaga masa hankali — duk da bai gane asalinta ba, Yana jin sonta a cikin zuciyar sa amma yana jin hakan laifi ne, yana jin laifi ne saboda Nasreen ta nemi afuwar sa da hawaye a fuskarta, har ya haƙura da Auren ta amma saboda umarnin Abul, da kuma shawarar Yayansa Amaar, sai ya amince da wannan auren domin su gyara rayuwa. A wunin yau kowa yana cikin shirye-shiryen gobe. Nasreen na cikin ɗaki tare da Asmeen suna shiryawa, amma zuciyarta cike take da ƙunci. Tana son zuwa ɗakin Abeesh domin ta sake magana shi — ta san ba a gama warware komai ba, har yanzu akwai dusar da bata narke ba a cikin ransa. A gefe guda, Catrina kuwa tana zaune a wani lungu na falon gidan, cikin shiga mai zaman kansa. Bata fito fili ba, amma tunanin ta yana kan Abeesh ne — gaba ɗaya ta gama karantar zuciyarsa. Tana murmushi a hankali, tana cewa a zuciyarta: “Zan bar ku kuyi Aure Nasreen, Amma zuciyar mijinki ba taki bace gaba ɗaya... ba sai na kwace shi daga gareki ba, tunda nayi nasarar shiga cikin ransa.”...... TSARIN BIKIN YAU An tsara biki da sassafe. An kira limamai da shaidu, ana sa ran za a yi aure da safe kafin rana ta bayyana sosai. Ana shirin yi a cikin babban filin gida, inda aka jejjera komai na ƙayatar da bikin.... An tsara komai, an ƙawata gidan tamkar sabuwar duniya, ƙamshi na turaren wuta da na fure sun haɗu sun ba da wata irin annushuwa ta musamman. A yau ne za a ɗaura auren Abeesh da Nasreen, da kuma Asmeen da Shapreen... A ɗakin Abeesh... Yana zaune a gefen gado yana kallon tagar da ke fuskantar rana, yana ta tunanin yadda zuciyarsa ke cike da ruɗani. Soyayyar da yake wa Nasreen ta fara dusashewa, amma zuciyarsa baza ta iya fitar da ita gaba ɗaya ba. Har yanzu yana jin raɗaɗin mari da kalaman da ta furta masa a lokacin da ya bayyana gaskiyar halin Madam Nablah. Kwatsam sai ga ƙofar ɗakin ta turo a hankali, Catrina ce, ta sha ado kamar bazawara daga wata masarauta. Ba ƙaramin kyau tayi ba. Rigar da ke jikinta na launin zinariya mai kyalli, tana fidda haske da kwalliyar da ta bayyanar da surar jikinta, gashinta yana yawo har gadon baya, idonta cike da kwaɗayi da nuni. Tsaya wa tayi a bakin ƙofa sannan ta ce “Zan iya shigowa ko?” ta faɗa cikin wata murya mai sa nutsuwa da girgiza zuciya. Abeesh ya ɗan juyar da kansa yana kallon ta, duk da a yanzu bai da ƙarfi sosai akan Nasreen, yana jin wata ɓangare na zuciyarsa yana ja da Catrina. Ya gyara zama amma bai ce komai ba. Catrina ta matso a hankali, kamar wacce take jin kunyarsa, amma da mugun nufi take tare dashi, ta zauna gefensa tana kallon sa kai tsaye. Ta furta “Na san rana mai kamar ta yau kana bukatar nutsuwa, amma na zo ne in tayaka murna.” Ta ɗan ɗora hannunta a saman kafadarsa, tana shafar sa a hankali. Abeesh ya kama hannunta da nufin cirewa, amma sai ya tsaya. Ganin yanda zuciyarsa ke sauya yanayi, sai ya ce da ita: “Catrina… me kike nema a wurina?” “Ka sani ai,” ta ce da murmushi, sannan ta kuma cewa “Ba zan tsaya ba sai na samu zuciyar da nake nema…” Abeesh kallon ta kawai yake ba tare da ya furta komai ba, har ta gama yinta ta tashi ta fice... --- A can ɗayan ɓangaren part ɗin su Tasleem... Tasleem tana tare da Nasreen da Asmeen a ɗaya daga cikin ɗakunan kwana. Ta kama hannun Nasreen tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali. Cikin kulawa ta ce “Nasreen… ki manta da baya, ki tuna da yanda kike ƙaunar Abeesh. Na san zai dawo ya darajar ki.” Nasreen tana hawaye ta ce “Amma Tasleem, zuciyarsa ta riga ta fita daga wurina… ina jin yana sonta… waccan Catrina.” Tasleem ta share mata hawayen fuskarta ta ce “Wallahi in har Catrina ba ita ce uwar ƙaunarsa ba, ba zata shige zuciyar sa ba. Ke ce ta zuciyarsa... karki bari wani ya maye miki gurbi.” A gefe guda kuwa, Asmeen ce ta saki ajiyar zuciya tana kallon madubi wacce ata sanadiyar Auren nan Mommynsu tasa aka ɗauko ta daga part ɗin Shaprees Tana hawaye ta ce “Ni kuwa Tasleem, wallahi bana jin Shaprees mijina ne. In dai auren dole ne, to zuciyata ba zata taba yarda da shi ba.” Tasleem ta matso kusa da ita tare da cewa “Kada ki karaya, Asmeen. Kullum haske yana da hanya, har cikin duhu. Ni zan ci gaba da neman mafita, domin ku samu kuɗi, ku sami lafiya, kuma ku samu soyayya.” ' Tasleem wuni take tare da ƴan uwanta tana basu kulawa ta musamman.... --- A yau ne za a kai Amare ɗakin mazajen su dake cikin gidan Madam Nablah saboda tsaro Kowa yana cikin girmamawa da farin ciki a zahiri, amma a zuciya akwai sirrin da bai da mafita. Kuma a gefen wannan soyayya da ƙaddara, Catrina tana ta ƙoƙarin cin nasara da kwaɗayin zuciya... ★★★★★ Daren da aka ɗaura aure, gidan Madam Nablah ya ɗauki kyan da ba a taɓa gani ba. Wutar fitilu tana haskakawa kamar taurari sun sauko ƙasa. Turaren ƙamshi ya cika ko’ina, yana yawo cikin iska kamar harshen soyayya. Amma duk wannan ƙyalli na waje bai iya ɓoye tsananin rikici da girgizar da zuciyoyi ke fama da su ba. A ɗakin sabuwar Amarya Nasreen tana zaune a gefen gado cikin shigar bacci mai launin shudi da zinariya. Idanunta sun cika da hawaye duk da fatar da ta yi na wannan ranar, tana ƙoƙarin kare kanta tana maganar zuci “na samu soyayyar rayuwata amma zuciyata ta san gaskiya...." Abeesh bai zo ɗakin nata ba. Yana can a ɗakinsa yana kallon madubi, yana duban fuskar kansa da ido mai zurfi kamar yana tambayar kansa: “Ni waye ne yanzu? Mijin Nasreen? Ko dai ƙaunataccen Catrina da zuciyata ke bugawa saboda ita?”... Kamar daga sama, ƙamshin turaren Catrina ya karade ɗakin. Kafin ya kammala tunani, ta turo ƙofar cikin natsuwa, cikin shigar mayafi mai launin ja da zinariya. Fuskarta cike da annuri, idanunta kuwa na walƙiya da sirrin duhu. Ta tsaya a gabansa. “Abeesh...” ta kira sunansa da murya mai sanyi kamar ruɗin murya daga wata duniya. “Ka yi aure yau, amma zuciyar ka har yanzu bata samu natsuwa ba. Ni na fahimta.” Abeesh bai iya cewa uffan ba. Kamar mai shaƙuwa da ƙamshin sihiri, ya matsa kusa da ita. Ta kai hannunta ta shafa sajen fuskarsa da tausasawa, tana murmushi ta ce “Na san baka manta da ni ba. Kuma zan kasance tare da kai — ko da ka auri Nasreen. Ba zan bar ka ba.” Yayi ƙoƙarin cewa wani abu, amma muryarsa ta makale. Zuciyarsa a rikice — ba ƙyale Nasreen gaba ɗaya ba, amma zuciyarsa na karkata ga Catrina. ** A part ɗin Asmeen kuwa.... Tasleem na cikin ɗakin Asmeen, tana rarrashin ta kamar yadda uwa ke rarrashin ɗa. Asmeen tana zaune da mayafi a bisa kafadarta, hawaye na sauƙa daga fuskar ta. Asmeen tana kuka ta ce “Tasleem, kada ki ce mun Shaprees mijina ne. Zuciyata na tsoro, kuma hankalina ba ya kwance da shi.” Tasleem ta kamo hannunta tare da faɗin “Na san... na san wannan auren ba shine burinki ba. Amma ki yi haƙuri. Kada ki manta da hasken da ke cikin ki. Ki riƙe shi, kada ki bar duhu ya ruguza miki rayuwa.” Asmeen ta kalli Tasleem sannan ta ce “Kina nufin... Shaprees ba wanda muke zato bane?” Tasleem ta ɗan yi shiru, sannan ta ce, “Ina jin akwai abubuwa da yawa da muke buƙatar sani. Amma yanzu... ki kasance da tawakkali. Zaki buƙaci ƙarfin zuciya sosai.” Tana cikin rarrashin Asmeen sai ga ƙiran wayan Nasreen, Tasleem ɗaga ƙiran tayi tare da faɗin "Nasreen lafiya kuwa?..." Nasreen tana kuka ta ce da Tasleem "Dan Allah ki zo yanda nake yanzu akwai matsala...." Tasleem kallon Asmeen tayi sannan ta ce "Ƴar uwa Asmeen ki kwantar da hankalin ki Insha Allahu babu abinda zai faru, yanzu zanje Nasreen tana ƙira na...." Daga nan ta bar part ɗin Shaprees da Asmeen, ta koma can part ɗin su yanda Nasreen take .... ***** A gefe guda kuwa, Nasreen ta kai karar zuciyarta wurin Tasleem tana faɗin “Kin ga yadda yake, ko? Bai zo ba. Babu soyayya... babu daɗin aure... Catrina ce matsalar nan, ban san ko wacece ba amma... tana son ruguza ni!” Tasleem ta rungume ta sosai tare da faɗin “Na fahimce ki. Ki kwantar da hankalinki. Zuciyar Abeesh ba a wuri guda take ba. Amma ki sani — ke ce matar aurensa. Kuma Allah zai daidaita zuciyarsa idan kika dage da addu'a.” ** A ɗakin duhu kuma, Madam Nablah na zaune tana juyawa a kujerar sarautarta, tana dariyar cikin zuciya. Tana jin daɗin yadda abubuwa ke tafiya dai-dai.... Kwatsam, wani hazo mai duhu ya bayyana a gabanta — Catrina ce. Tana siffar aljana yanzu, ba mutum ba. Ta sunkuyar da kai. “Uwar Wuta, komai na tafiya daidai. Na kusa mallake zuciyar Abeesh gaba ɗaya.” Madam Nablah ta murmusa da mugunta ta furta “Da kyau, Catrina... Idan muka mallaki zuciyar Abeesh, za mu iya karya ruhin Abul da kuma shanye hasken da Tasleem ke ƙoƙarin kawo wa.” ★★★★★★ Falon ya ɗauki salo mai zafi, wutar fitila na haskaka fuskokin da ke cike da motsin zuciya. Amaar yana zaune cikin natsuwa, hannunsa a kan na Tasleem wacce take ta sharar hawaye cikin tausayi da ƙunci. “Ya Amaar,” Tasleem ta ce da muryar da ke rawar zuciya, “meyasa mommyna bazata amince da kai ba? Ta Aurar da Nasreen da Asmeen amma ni... ita ce ta hana ni farin ciki na. Na gaji da jurewa.” Amaar ya riƙo hannunta cikin tausayawa tausayi yana kallon idanunta cikin kwantar da hankali “Tasleem,” ya ce cikin murya mai laushi, “ki kasance mai tawakkali. Allah yana jarrabar bayinsa da wanda yafi dacewa da su. Ranar aurenmu na zuwa, ko da duniya ta ƙi, sammai zasu yarda. Kin cancanci soyayya mai tsarki kuma Allah bazai bar ki ba.” Tasleem ta sauke ajiyar zuciya, tana ƙoƙarin daidaita numfashinta. Suna cikin wannan tattaunawa ne sai ga ƙofar falo ta buɗe — Catrina ta shigo. Sai ta tsaya, a jikin lulluɓe da atamfa mai launin zinariya da baƙi, tana kallon su da wani murmushi wanda ba’a gane ko da gaske bane ko yaudara a hankali ta furta “Masoya... sannunku da hutawa,” ta faɗa da murya mai saukar da sanyi amma cike da nufin karya nutsuwa. Tasleem ta ɗaga kai da sauri, kamar wata wuta ce ta kunno kai a zuciyarta. Ta miƙe tsaye cikin hanzari kamar bazata jure ganinta ba “Kece Catrina ko?” ta ce cikin tsawa. sannan ta cigaba da faɗin “Ke da kika zo mana a matsayin baƙuwa amma kina ƙoƙarin ruguza soyayyar ƴar uwata da mijinta? Wace irin halayya ce haka?” Catrina ta ɗan saki dariya — wadda ke cike da wani irin kwanciyar hankali. Ta taka zuwa tsakiya cikin falo, ta tsaya gaf da gaf tana kallon Tasleem da ido masu walƙiya. “Soyayyar Abeesh?” Catrina ta ce. Ta kuma cewa “Na rigada na mallaki zuciyarsa. Kin ce Nasreen ce matar sa, amma zuciyarsa ba ta wurinta. Shi kansa yasan hakan. Ina sonsa... ko da zuciyar ku bata so...” Amaar dai bai ce uffan ba, yana zaune yana nazari, zuciyarsa na hararar wannan sabuwar halitta da ba ya ganewa. Amma a hankali yana lura, Catrina ba kamar kowa bace. Tunaninsa na barazanar cewa akwai wani abu mai zurfi da ke ɓoye a bayanta. Tasleem ta matso kusa da ita, fuskarta cike da haushi da taya ƴar uwarta kishi ta ce “Abeesh ya auri Nasreen da yardar Allah. Kuma Nasreen ba ’yar kai ba ce da za ki ƙetare ka’ida. Idan da gaske kina da ƙauna, meyasa kike cutar da wasu? Wace ce ke Catrina? Ke kamar ba mutum bace — zuciyarki duhu ne!” Catrina ta ja tsaki, idanunta suka ɗan sauya kamar na wata halitta daga wata duniya ba tare da Tasleem ta gani ba... Ta ce “Na san ku ba za ku fahimta ba... Amma lokaci na zuwa da kowa zai gane inda zuciyar Abeesh take. Kuma ke Tasleem,” ta ƙara matsowa kusa da ita, “wannan soyayyar da kike fata da Amaar — bazata yuwu ba. Mahaifiyarki bazata taɓa barin ki ba, idan kuwa har zaki taya ƴar uwarki kishi akan abinda nake so to ba shakka zan dawo kan ki ne....." Tasleem ta ɗan ja baya, ba shakka zuciyarta na girgiza. ta kalli Amaar, sai kuma ta kalli Catrina cikin ƙarfi a fusace ta furta “To ko ki kasance aljana daga ƙasan ƙasa, bazan ƙyale ki ki tarwatsa farin cikin ’yan uwana ba. Kuma ko mahaifiyata ta ki yarda da ni da Amaar, haskenmu ya fi ƙarfinku. Zamu tsaya da juna har zuwa ƙarshen ruhi.” Catrina ta yi murmushi, ta juya kamar wacce ta gama faɗin komai ta furta “Sai mu gani,” sannan ta bar falon.... Amaar ya matso ya rungume Tasleem daga baya, yana faɗa mata cikin ƙasa da murya: “Ki tsaya da gaskiya. Duhu bazai taɓa cin nasara a kan haske ba. Na rantse da rayuwata, zaki zamo matata — ko da me zai faru.” Tasleem na tsaye a tsakiyar falo tana fidda numfashi da ƙyar, zuciyarta cike da ɓacin rai da tsananin ƙishi. Catrina ta riga ta fice ta bar tashin hankali wanda ke ɗauke da ɗumbin barazana. Amaar kamo hannun Tasleem ya yi tare da juyo da ita yana kallonta cikin kulawa ya ce “Na san ke mace ce mai gaskiya, kuma ke ɗiya ce mai tsarki, kar ki bari cutar zuciyar wasu ta karyar da ke.” Tasleem ta girgiza kai tana ƙoƙarin daidaita zuciyarta daƙyar ta iya furta “ Ya Amaar... wannan baƙuwar, tana da wani abu a jikinta wanda ban fahimta ba. Ba kamar mu take ba.” Amaar ya kalli ƙofar da Catrina ta bi, zuciyarsa na dukan wasu alamomi da ba ya iya fassara shi Amma a ransa, wata faɗakarwa tana zagaye da shi — wannan ba mace ce kamar sauran ba... --- Washe Gari: ana hidimar walima na ƙawaye bayan biki... Gida ya sha ƙawanya kamar na sarauta. Jikin bango ya sha ado da fitilu, furanni da zannuwan alfarma. Kowa cikin farin ciki da murna... A ɗaya gefen gidan, Tasleem tana cikin shirin tarbar baki da shirya abinci. Fuskar ta ɗauke da murmushi, amma zuciyarta na ƙaryar fara’a, domin ana bazarana da rayuwar ta. Ta shigo ɗakin Asmeen tana riƙe da kayan ado. “Asmeen... kin shirya?” Ta tambaya da murmushin a fuskar ta Asmeen tana zaune a gaban madubi, idonta cike da hawayen da ke faman taruwa amma bata bar su sun zubo ba. A hankali ta furta “Tasleem... zuciyata na kuka, zuciyata na kirana. Na san akwai wani abu game da Shaprees da ba daidai ba.” Tasleem ta matso, ta zauna kusa da ita sannan ta ce “Ki yarda da zuciyarki, Asmeen. Amma yanzu ki nutsu. Lokaci yana da ikon bayyana gaskiya.” ★★★★ A ɗakin Nasreen kuwa, Nasreen na zaune a gaban mirror tana ƙoƙarin gyara fuskarta da kwalliya. Ta ji ƙarar buɗan ƙofa, ta cikin madubi ta hango Catrina, tana shigo ta ce “Kin shirya?” Catrina ta tambaya tana murmushi. Nasreen ta ɗan harareta, ta ce: “Ko da ke wacece, ki daina kusantar mijina. Wallahi kema mace ce kamar ni, karki cutar da wata saboda ƙiyayya ko mungun nufi.” Catrina ta yi dariya, sannan ta matso kusa ta ce “Ni kuwa, bana faɗa da ke. Abeesh shi da kansa ya shigo raina. Ki ce masa ya fita — ni na riga na mallake shi.” Ta juya cikin jin daɗi, ta bar Nasreen da bugawar zuciya. --- A ɗakin Abeesh kuwa Abeesh na zaune a gaban madubi, cikin shigar ango, fuskar sa ɗauke da damuwa da rikitaccen tunani. Baya jin daɗi kwata-kwata, komai ya yi masa nauyi. Soyayyar Catrina na damun zuciyarsa — ba da gangan ba, amma kamar aljanar ƙauna ta shige shi. Kofarsa ta buɗe a hankali. Sai ga Catrina ta shigo, cikin shigar da ba a saba gani ba, ta lulluɓe jikinta kamar matar Aure Kafin ya buɗe baki, ta matso, ta durƙusa a gabansa tana kallon idanunsa ta ce “Abeesh... na san bana da matsayin Nasreen a gurinka. Amma na san zuciyarka na kirana. Ka ce min da gaske... baka sonta yanzu kamar yadda kake sonta a baya ....” Abeesh ya dafe kansa tare da faɗin “Catrina... ban san me ke faruwa da ni ba. Idan ina jin ki, da gaske ne... to, ya zanyi da Nasreen? An ɗaura mana aure... kuma ita ce matar da na faɗa mata zan bata rayuwata.” Catrina ta lumshe ido, tana murmushi ta ce “Zaka iya kasancewa da ita... amma ka bani zuciyarka. Shi ne kawai nake nema.” Ta kamo hannunsa tana shafawa, ta lallaba cikin salo har ta ƙara rikita masa hankali. Abeesh ya zama kamar mai bacci da ido a buɗe.... Cikin salo da ƙwarewa a wannan lokacin har ta samu kansa, suka kasance da juna, ta samu nasarar sumbatar sa har shima ya biye mata, amma babu abinda ya faru har yanzu yana riƙe da mazantakar sa 🙈🙈🙈 --- A gefe: Madam Nablah tana kallon komai daga wata gilashi ta tsafi. Ta murmusa, tana magana da kanta: “Catrina... kina sauƙe nauyi. Abeesh ya fara mantawa da Nasreen. Gaba ɗaya nufin su zai rushe.”... Sai kuma murmushinta ya koma damuwa lokaci guda, tana faɗin “Amma ke Tasleem... har yanzu kina tare da Amaar. Wannan shine kuskurenki. Zanyi maganinki.”........ New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 43 to 44 Dare Ya Sauƙa.... Wani irin shiru ne ya rufe gidan, bayan walimar biki da dukkan shagulgulan da suka yi yau. Gidan ya koma cikin natsuwa, hasken fitilu masu launin rawaya na ratsa dakuna da falo cikin salo. Kowane yanki yana ɗauke da ɗan ƙamshi na turaren bikin da aka yayyafa. A cikin wannan natsuwa, akwai abubuwan da zuciya ke ɓoye wa— abubuwan da zasu fara bayyana a daren nan... --- Abeesh & Nasreen – Daren Da ya fi ko wanne Sanyaya Zuciya Abeesh yana sanye cikin fararen kayan barci marasa nauyi, yana zaune gefen gado ya yi shiru, fuskarsa cike da tunani. Sai ga ƙofa ta buɗu, Amaar ne ya shigo da murmushi a fuskarsa. “Kai Ango, yau rana ce, kar ka bari komai ya dagula maka lissafi. Ka manta da jiya, ka kalli gaba.” Abeesh ya ɗago kai ya kalleshi da ɗan murmushi sannan ya ce “Yaya... nagode. Ban san yadda zan fara ba.” Amaar ya dafa kafaɗarsa Ya ce “Da soyayya ake farawa. Ka nutsu, ka saurareta. Zuciyarta na da taushi fiye da yadda kake tunani.” Sai ya miƙe ya fice, ya bar masa dakin. Bayan ƴan mintuna, ƙofar ɗakin ta sake buɗewa a hankali. Nasreen ne ta shigo cikin kayan bacci tana sanye da dogon hijab har ƙasi kanta a ƙasa kamar sabuwar amarya. Hawayen da tasha a cikin zuciyarta sun gama goge fuskar ta, sai siririn murmushi da yake bayyana cikin salo.. Abeesh ya miƙe yana kallonta. Ba tare da ya ce komai ba, ya matso kusa ya kamo hannunta. A hankali ya furta “Nasreen...” Ta ɗago idonta da ɗan kukan da ya rage, muryar ta na rawa take faɗin “Ya Abeesh... kayi haƙuri da duk laifin da na maka. Duk da abubuwan da suka faru, zuciyata bata daina ƙaunarka ba.” Sai ta durƙusa a gabansa tana kuka ta ce “Na yi kuskure... amma nayi nadama. Kuma zan yi iyakar ƙoƙarina don zama matarka mai daraja.” Abeesh ya riƙo hannunta, tare da ɗago ta Ya ce “Na jima ina fushi da ke, Nasreen. Amma wallahi, zuciyata ta fara sabo da ke tun kafin ki nemi gafara. Na ji yarda, na kuma ji soyayya. Amma...” Ya tsaya yana kallonta daga bisani ya ƙara sa da cewa “Catrina na damuna. Ban san me ke faruwa da ni ba. Kamar wani iko ne ke jan zuciyata gareta...” Nasreen ta dafa kirjinsa tare da faɗin “Zan tsaya tare da kai. Mu fuskanci komai tare.” Suka rungume juna cikin shiru tare da kewar juna da kuma ƙarfin soyayya.... Jin knocking ƙofa suka ji, a lokacin Nasreen ta je ta buɗe, murmushi Nasreen tayi ganin Tasleem riƙe da kulolin abinci da kayan marmari, Tasleem ta ce "Amarya bakya laifi da duk kan alamu kina cikin shauƙin soyayya, ga wannan yau na makara ban kammala girki da wuri ba.... Nasreen ta karɓa tare da yi mata sannu da aiki, daga baya ta rufe ɗakin..... Daren ya lulluɓe garin da natsuwa, hasken wata na sauƙa cikin ɗakin da Abeesh da Nasreen ke zaune, soyayya na yawo a tsakanin numfashinsu. Bayan sun cin abinci, sun yi wasa da dariya mai daɗi... Nasreen na sanye da rigar bacci mai launin shudi mai laushi ta miƙe tare da ta nufi jikin mirror tana feshe jikinta da turaren ‘lily’ wanda Abeesh ke matuƙar so. Idanunta cike da annuri, murmushi na launin so yana bayyana a fuskarta. Tana kallon mijinta da wata irin sha'awar da ke bayyana muradin zuciyarta. Abeesh ya taso ya zo yanda take tsaye a gaban mirror kusa da ita, ya kamo hannunta, yana jin yadda jikinta ke rawa da raɗaɗin soyayya. Sun kalli juna tamkar zuciyarsu na magana da harshe ɗaya. "Abeesh…" ta ce cikin ƙasa da murya, kamar mafarki. "Na'am, Nasreen?" ya amsa yana shafar gefen kumatunta. "Na ji kamar wannan rana ta fi kowacce muhimmanci... so nake mu bayyana yadda muke ƙaunar juna fiye da kowane lokaci." ta furta hakan cikin shagwaɓa... Ya lankwasar da kansa, yana kallonta cikin kulawa Ya ce "Zuciyata da taki sun jima da haɗuwa tun kafin mu sani, Kuma wannan daren, zan mayar da ke sarauniya a gado na da zuciyaa ta, Rungumar juna suka yi cike da natsuwa da kulawa, Ƙamshin jikinta ya saka shi jin wata irin salama, zuciyarsa ta sauka cikin lumana. Ya sumbace ta a goshi, a kumatu, sannan ya janyota jikinsa, yana jin yadda numfashinsu ke haɗuwa cikin ɗumi da so. Iska mai daɗi ne yake ratsa su, suka ci gaba da kusanci – da hannu, da ido, da zuciya. Kalaman soyayya na sauƙa a kunnen juna, hannaye na yawo cikin natsuwa da ƙauna. A cikin dare, suka zamo tamkar ruhu guda biyu da suka haɗu, suka bayyana jin daɗi, aminci, da soyayya ba tare da ko da ƙaramar kalma ba. Wannan dare ne na soyayya mai tsarki..... Hasken ɗakin suka kashe, daga nan hankali ya gushe, sai surutai da ba'a sanin mai suke faɗi, sun koma wata duniya da ban..... Shaprees & Asmeen – Daren Auren su.. Shaprees ya shiga daƙin Asmeen da natsuwa. Ya riga da yacire kayan bikin, ya koma cikin shigar dare (kayan bacci) yana kallonta cikin wani kallo mai taushi. Asmeen tana gefen gado, tana ƙoƙarin kau da kai saboda karayar zuciyarta — bata yarda da shi ba har yanzu. Shaprees ya zauna a gefenta ba tare da ya matsa kusa ba Ya ce “Asmeen, bana son matsa miki. Na san ba kya sona, kuma bana buƙatar ki Amince dani yanzu. Amma ina so ki sani — ni ba Shaprees ɗin da kika ji labari bane, ko kika gani Ni sabon mutum ne.” Asmeen ta kalle shi, ta ce cikin sanyin murya “Kamar yadda ka ce, bana jin zan iya yarda da kai a daren nan. Amma ba na nufin zan zama uwargida marar biyayya” Shaprees ya ɗan murmusa sannan ya ce “Kin nuna min girmamawa da fadakarwa fiye da ƙiyayya. Wannan yana nufin akwai fatan alkhairi” Daga nan ya kwanta a kujerar ɗakin dake gefe da gadon yana faɗin “Zan kwana a nan gefen. Idan kina buƙatar wani abu sai ki sanar mun, Amma sai abinda kika yanke tukun.....” Asmeen ta kalle shi da mamaki. Wani sanyi ya shiga ranta, amma sai ta boye ta furta “Na gode da karramawa, Shaprees.” Shaprees ya kwanta akan kujera, ya juya bayan sa A cikin zuciyarsa yana addu’a yana faɗin "Ya Allah ka ƙarfafa ni, ka bani damar gyara kuskure na, ka sa wannan mata ta fahimce ni." Dab da Asuba misalin ƙarfe 4 Abeesh da Nasreen na kwance domin a daren yau basu samu yin bacci ba, iskar sanyi mai ɗauke da ƙamshin furanni tana kadawa a jikin labulen taga, tana zagaya dakin da hasken fitilar bango na haskaka da launin zinariya mai salo. Abeesh da Nasreen, cikin shauƙin su, suna kwance a saman gadon da aka ƙawatar da farin zanen siliki da fure-fure masu ɗaukar ido. Nasreen na kwance a gefen shi, kanta a saman kafadarsa, yana shafa gashinta da hannunsa cikin natsuwa kamar yana karanta wani sirrin soyayya da babu wanda zai iya fassara shi sai zuciyarsu biyu. Idanunta suna lumshe ba domin tana bacci ba, sai don tana jin daɗin lumshewa cikin annashuwa. Abeesh ya ɗan ɗaga kanta ya kalli fuskar da ya saba kallo tun farko da suka fara haɗuwa, amma a yau ya sake kallonta da sabuwar fahimta. Fuskar Nasreen na cike da lumana, cike da aminci da kwanciyar hankali wanda ya shige shi gaba ɗaya. "Nasreen," ya kira da ɗan ƙaramin murya. "Na'am," ta amsa ba tare da buɗe ido ba. Sannan ya ce "Ina ji kamar duk duniya ba ta da wani ɗanɗano idan baki cikin rayuwata." Sai ta murmusa, ta buɗe idonta a hankali "To ni fa na rasa inda zan sa kaina da kalaman ka," ta ce tana juya fuskarta gare shi, tana kallon idanunsa da ke cike da gaskiya. Abeesh ya kama tafin hannunta, yana murzasu a hankali sannan ya dafa kirjinta da lallausar hannunsa Ya ce , "Wannan zuciyar shine mafakina." Cikin jin daɗi, ta sanya kanta a kirjinsa, tana jin bugun zuciyarsa daidai da nata. Daga nan suka fara tattaunawa da kalmomin da basu da sarkakiya: game da gobe, game da mafarkinsu, game da iyali da fatan cika rayuwa da farin ciki. Suna kwance cikin farin ciki har zuwa lokacin ƙiran sallar asuba.. Sun ci gaba da musayar kalmomi masu daɗi, musayar kallon da ke furta: na kamu da ƙaunar ki, musayar dariya da shiru wanda ke nuni da gamsuwa da kusanci. Kafin nan sun riga sun zana hoton da ba zai goge ba a cikin zuciyarsu—na daren farko da suka kasance ba ma’aurata kawai ba, sai ma abokan amana na gaskiya da gaskiya... Daga nan Abeesh ya tashi da niyyar ɗauro alwala, ya shige toilet sai da ya yi wanka sannan ya ɗauro alwala yana fito wa ya sanya jallabiyar sa, sai da ya sumbaci Nasreen akan goshin kafin ya fita zuwa masallaci, Itama yunƙurawa tayi ta tashi da niyyar yin wanka da Sallah..... ★★★★★ Washegari da safe, hasken safiya yana kadawa cikin ɗakin Nasreen da Abeesh. Wata irin nutsuwa ce ke zagaye tsakanin su, babu hayaniya, babu kalamai da yawa. Abeesh yana kwance yana kallon Nasreen wacce ke zaune tana gyara gashinta. Fuskar ta na sakewa da murmushi mai taushi—na farin ciki da kwanciyar hankali, kodayake akwai ɗan fargaba a cikin zuciyarta. Ita kanta bata san dalilin hakan ba—zuciyarta kamar tana hasashen wani abu. Ita har ta manta da wata Catrina.... Abeesh ya miƙe daga gado, yana ƙara kusanto ta. Ya ce “Nasreen… na gode da jiya. Soyayyarki ta sake sabunta min zuciyata.” Ta juya da murmushi mai sauƙi Ta ce “Ni ma nagode da yanda ka rungume ni da haƙuri. Ina fatan soyayyarmu zata ƙarfafa.” Sai ya rungumeta a hankali. Amma a cikin ransa — akwai sanyi da zafi. Ya kan ji Catrina tana taso masa a zuciya kamar ƙamshi mai dāɗi da cike da ruɗani. Yana jin yana ƙaunar Nasreen, amma wataƙila ƙaunar Catrina ya fara shigarsa da wata hikima ta daban. A Ɓangaren Shapreen da Asmeen.. Washe da safe rana na bayyana daga tsakiyar gajimare... A cikin gidan aurenta, Asmeen na zauna a gefen tagar dakin, tana kallon yadda rana ke dukan lemar ganyen itatuwa. Shaprees na zaune gefenta, yana duba wata tsohuwar takarda da ke ɗauke da bayani akan wasu kalmomin sihiri. Amma daga gefe, idanunsa na kallon Asmeen cikin sirri—wani kallo mai cike da ɓoyayyen buri da damuwa. "Asmeen…" ya furta. Ta juyo da ɗan murmushin dole, wanda bai kai zuciyarta ba. "Na’am?" ta furta cikin sassanyar murya Shaprees ya ɗan yi shiru kafin ya ce, "Kin kyauta da kika amince ki zama matata. Zan baki kulawa yanda ya kamata Ko da ba soyayya ce ta kawo mu nan ba… zan so ki, in har lokaci ya bani dama." Asmeen ta sauƙe ajiyar zuciya sannan ta ce "Ka san ba don raina ya so ba na shiga wannan aure. Amma zan yi ƙoƙarin zama yadda ya kamata…" Shaprees ya ɗaga mata hannu kamar yana hana ta ƙarasa maganar, ya ce "Bana son ki tilastawa kanki. Amma idan wata rana zuciyarki ta buɗe, zan san hakan..." Sai ya miƙe, ya bar dakin cikin natsuwa, amma zuciyar sa tana matuƙar masa zafi —zafin rashin samun kulawa daga wadda zuciyarsa ke so, kodayake manufarsa ta farko na boye a cikin ɗumbin sirri..... ******* Catrina kuwa a wannan ranar kwata-kwata bata fito falo ba, tana kwance a ɗakin ta tsananin soyayyar Abeesh ya hanata sake wa, daga wasa abu yana shirin zamo gaskiya, bata san ya akayi tayi wannan saken ba domin ba soyayya ne ya kawo ta ba.... Bayan Sallar Isha'i kowa ya ci ya sha... Sannan kowa ya koma room ɗin sa, Ɓangaren Abeesh part guda ne a babban falon gidan, wanda kana hawa upstairs room biyu ne suka kasu biyu, room one akwai wani falo ɗan madaidaici a ciki sannan a wuce bedroom nan ne site ɗin Abeesh, other room kuma nan ne room ɗin Nasreen, kowa da room ɗin sa sai dare ake haɗuwa a room ɗaya... Cikin Dakin Abeesh... Abeesh na zaune kusa da taga yana kallon sararin sama. Yana cikin tunani mai zurfi. Zuciyarsa ba ta huta ba tun daga daren farko da Nasreen. Duk da cewa yana ƙoƙarin mantawa da komai, akwai murya a zuciyarsa da ke kiran wani suna — Catrina... Yana cikin wannan tunanin yaji Sautin ƙwanƙwasa ƙofa, kallon bakin ƙofar ya yi sannan ya ce “Shigo...” Catrina ce ta shigo cikin natsuwa, sanye da riga ruwan toka mai launin lu’ulu’u irin shigar sarauta. Gashinta a nade yana sheƙi kamar zinariya a cikin duhu. Fuskar ta na ɗauke da murmushin da yake rikita zuciya, “Na san wannan lokacin bai dace naxo ba,” in ji Catrina tana takowa cikin ɗakin da siririyar murya, ta cigaba da faɗin “amma sai na ji bazan iya barin dare ya wuce ba tare da na ganka ba.” Abeesh ya kalleta, bai ce komai ba, Sai dai yana jin wani sanyi na ratsa jikin sa, kamar ana shafawa da furanni masu ƙamshi. Murmushi ta ƙara yi, ta zauna a gefen shi. “Kayi sanyi, ko zaka iya sanar mun yanda ka kasance da Nasreen?” ta faɗa cikin lallausan salo. Kallo ɗaya ya yi mata sannan ya ce “Kada ki kawo batun Nasreen, Catrina.” Ya faɗa a nutse, ba da ƙarfi ba, ba da rauni ba. Ta ce “Shin na kawo naka ne? ba nata ba? Ka sani Abeesh Kana cikin zuciyata fiye da yanda nake fatan, Abeesh… ka daɗe kana cikin ruɗani. Ka ƙi yarda da zuciyar ka.” Ta miƙa hannu tana shafar hannunsa. Kamar kankara ne ke narkewa cikin wuta. Abeesh ya janye hannun ba tare da ƙarfi ba. Ya kalleta a karon farko, idanunsa na ɗauke da haɗuwar soyayya da fargaba. Ya ce “Ki tafi, Catrina. Kafin na rasa gaskiya. Na haƙura da soyayyar Nasreen kafin, amma yanzu… Ina ƙoƙarin gyara wa, Kar ki sa in dawo baya.” Catrina ta ce “Gyara?” ta faɗa da ɗan dariya mai cike da sarkakiya. “Kana son gyara soyayya da macen da ta mare ka saboda mahaifiyarta? Wacce ta bar ka cikin duhu lokacin da kake buƙata? Kuma yanzu kake neman haƙura saboda tsoron zuciyarka?” Abeesh ya runtse ido. Cikin ɗumi, ta matsa kusa da shi, muryarta na shigewa cikin kunnensa a hankali ta furta “Ka riga ka zabe ni a zuciyarka, Abeesh. Ko da za ka zauna da ita, sai dai jikinta. Amma zuciyarka... tawa ce.” Sai ya buɗe idonsa ya dube ta. A can cikin zuciyar sa — yana jin gaskiyarta. Amma har yanzu yana jin laifine hakan, da kuma cin Amanar wacce yake so.. Girgiza kai ya yi tare da faɗin “Catrina... ki gaya min gaskiya. Wacece ke? Me kike so daga gare ni?” ta yi murmushi a taƙaice sannan ta ce “Ni? Ni ƙaunarka nake so. Kuma kai kanka ka sani.” Ta miƙa hannu, ta dafa ƙirjin sa — inda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi. Ta ce “Zuciyarka tana furta sunana fiye da yanda harshenka ke iya furtawa...” --- A Wurin Nasreen... A ɗakin Nasreen, tana kwance da ido a buɗe. Bata jin bacci. Bata jin kwanciyar hankali. Zuciyarta tana bugawa tamkar akwai wanda ke shirin kwance mata farin ciki. Ta miƙe tsaye, tare da sanya hijabi, zuciyarta na cewa “Ina jin wani abu ba daidai ba.”... Sai ta fice daga ɗakin a hankali — zuciyarta na kiran sunan Abeesh. Nasreen ta tsaya a gaban ƙofar ɗakin Abeesh, zuciyarta na tsalle kamar ana harbi da kibiya a cikin zuciyar ta, Hannunta na rawa, amma ba tsoro bane, kishin so ne — kishi da fargaba, da son sanin me ke faruwa. A hankali ta buɗe ƙofar ɗakin... Abeesh yana zaune a gefen gado, Catrina kuwa na zaune akan cinyar shi, hannunta a kan ƙirjin sa yayin da ɗayan hannu yake zagaye ta bayan wuyansa suna sumbatar juna cikin salo da ƙwarewa, cikin fitar hayyaci Abeesh haka yake cakurkuɗa mata sumar gashi tare da shashshafa ta ko ina, har ta saman nonuwan ta, idanuwansa a lumshe, shaƙar ƙamshin turaren ta na ƙara jefa shi cikin wata duniya da ban, haka yake shocking lips ɗin ta kamar wanda ya samu lollipop.... Idanun Nasreen ne suka cika da hawaye lokaci guda, Ta tsaya a bakin ƙofar ba tare da sun lura da ita ba. Amma Catrina, kamar ta hango wani inuwa a bayanta ta jikin bango, ta juya a hankali. Da ganin Nasreen, murmushi ya bayyana a fuskarta, ba na jin kunya ba, sai na cin nasara, A hankali ta juyar da kanta bakin ƙofa yayin da shi kuma yake ƙara danne kansa a cikin rigar ta yana sumbatar saman nonuwan ta.... “Oh... Nasreen.” Ta faɗa da muryar kwantar da hankali, amma a cikin zuciyar ta tana farin ciki da wannan lokacin... “Kiyi hakuri, bamu san kina nan ba...” Nasreen ba ƙaramin rikicewa tayi ba, nufan cikin ɗakin tayi da sauri, zuciyarta na harbawa. Abeesh kuwa da sauri ya ɗago kansa a ruɗe yana kallon Nasreen, a ruɗe ya miƙe tsaye cikin firgici, ya janye Catrina daga jikinsa yana kallon Nasreen cike da fargaba. Muryar sa ne ta fara rawa yana faɗin “Nasreen, ba yadda kike tunani bane—”.. A rikice Nasreen ta ce “Shiru! Ka riga ka gama min,” ta ce cikin kuka mai raɗaɗi sannan ta cigaba da faɗin “Na farka cikin dare don in roƙe ka gafara gaba ɗaya, ka nuna mun cewa ka yafe mun amma yanzu sai na same ka da ita — ita! Wacce ban ma san ko ita wacece ba!”... Bata ƙara sa maganar ba ta fashe da kuka.. Catrina ta matsa kusa da Nasreen, tana kallonta da wani irin murmushi da yake ƙara jefa zuciya cikin matsin lamba. Ta ce “Ya kamata ki saba da hakan, Nasreen. Idan kina da kyakkyawan dutse a hannunki, mutanen duniya za su so su karɓe shi. Kuma ni... na fi dacewa da wannan dutse.” Nasreen ta juya, ta dube Catrina da wani irin kallo mai ƙayatarwa. Sai ta matso kusa da ita ta ce da ƙarfi: “Ke baƙuwa ce a gidan nan. Kuma baƙuwar da bata san mutunci ba, komai yana da iyaka! Kinyi nasarar cusa kanki a zuciyar mijina — amma wallahi ba zaki iya karɓar sa gaba ɗaya ba. Sai na nemi mafita. Domin wannan soyayya tawa ce — kuma ni ce na cancanta da ita!” Abeesh ya matso, ya riƙo hannun Nasreen. Idanunsa cike da damuwa ya ce “Ki saurare ni, Nasreen... na rasa kaina ne na cikin ɗan lokaci. Ina ƙoƙarin mantawa da ɓacin ran da kika sanya mun Amma zuciyata ta kasa jurewa ruɗanin da ke kewaye da ni...” “Na yafe maka, Abeesh,” ta faɗa cikin hawaye. “Amma ban yafe mata ba. Kuma sai na gano ita wacece!” Catrina ta zura hannayen ta cikin sumar gashinta, ta juya kamar mai cike da ƙwarin gwiwa tana faɗin “To ku ci gaba da soyayya idan zaku iya. Amma ku sani — wanda ya fara shan ruwan ni’ima daga tabkin duhu, ba zai iya sha daga rijiyar haske ba.” Sai ta juya cikin natsuwa ta fice daga ɗakin — tana barin ƙamshi mai ɓoye ɓoye, da murya mai zurfi da ba kowa ke fahimtarta ba... --- Shaprees da Asmeen... Shaprees yana zaune kusa da Asmeen a ɗakin su. Cikin nutsuwa, ya ke kokarin kawo zaman lafiya da soyayya. Bai motsa da son rai ba. Bai nemi kusanci ba. Sai dai yana nuna kulawa ta gaskiya. Yana kallon ta cikin kulawa ya ce “Na san kina jin tsoro, amma ina rokanki, ki bar ni na zama aboki a gare ki. Komai ya girmi lokaci. Ni ba duhu bane kamar yanda kike tsammani.” Asmeen ta juya daga kallonsa. Amma zuciyarta na tafasa da tambayoyi — Shaprees ya canza? Ko kuwa wata dabara ce sabuwa?... A wannan lokacin haka Shaprees ya gama surutan sa amma ko sau ɗaya bata kula shi ba sannan bata bashi haɗin kai don su zamo cikakkun ma'aurata ba, duk da bai tilasta mata akan ta amince da shi ba.... --- A cikin ɗaki Amaar na zaune akan katafaren gadon sa yayin da Tasleem take kwance a cinyar sa tana sharar hawaye. Amaar na shafa kanta yana rarrashi a hankali yake furta “Muna raye ne don mu jarrabtu, Kin ga fa ko Abeesh da Nasreen ba su da sauƙi — amma soyayya na tsira daga ruɗani idan aka dage da addu'a da gaskiya akan ci ribar sa...” Tasleem ta ɗaga kai ta ce: “In dai kai ne a kusa da ni, ko da duniya ta ƙi yarda da mu, ni bazan taɓa fasa ka ba…” Sun juma suna tattaunawa akan batun soyayyar su, da bata da wata mafita...... Washegari da safe, hasken safiya ya leƙa cikin gidan Madam Nablah, amma zuciyoyin da ke cikinsa ba su samu nutsuwa ba. Duk da anyi bikin daɗi da annashuwa, gidan ya shiga wani hali na ruɗanin soyayya da ba a iya kwatanta shi da komai sai da guguwa. Abeesh da Nasreen... Abeesh ya fito daga ɗakinsa da kyar, idanunsa ja, fuskarsa cike da gajiya da ruɗani. A daddafe ya shiga falo, yana jin zuciyarsa kamar tana nauyi. Yana kokarin mantawa da abin da ya faru da Catrina daren jiya, amma... sautin muryarta, kamshin jikinta, da idanuwanta masu sanyi suna binsa kamar inuwa. Nasreen kuwa ta rufe kanta a ɗaki. Tana kuka, tana addu’a, tana shan wahalar ganin mijinta na soyayya da wata da ba ta san komai game da ita ba. Amma ko da ta dage da addu’a, zuciyar Abeesh tuni ta samu wani rami da Catrina ta cusa kanta a ciki. yana jin haushin hakan, sai dai ba zai iya fitar da ita ba. --- A ɗakin Catrina... Catrina tana zaune a gaban madubi, tana kwalliya. Fuskar ta ɗauke da shu'umemmen murmushi, amma zuciyarta na ɗauke da ƙaƙƙarfan nufi — zata ci gaba da shiga jikinsa har ya daina jin komai ga Nasreen. Ta shafa wani turare wanda ke janyo hankalin maza, wani sihiri ne da ta ɗora don ƙara ruɗa Abeesh. Tana murmushi, tana furta cikin ƙasan harshen ta: “Zan bar Nasreen da sunanta... Amma zuciyar mijinta, mallakina ce.” --- Asmeen da Shaprees... Asmeen tana kwance a gado, tana kallon Shaprees wanda ya tayar da sallar lafula. Da kyar take iya jure halayensa na kirki da nutsuwa — sabon Shaprees daban ne da wanda aka ce mata mungu ne. Yana idar da salla, ya juyo yana kallonta da murmushi mai sauƙi Ya ce “Kiyi hakuri da ni, Asmeen. Ina sane da cewa kinyi aure da wani da ba ki so ba. Amma zan zama amini a gareki... kafin in nemi zama masoyi.” Asmeen ta saki wani numfashi mai zafi. Zuciyarta na rikicewa — ta fuskanci gaskiya tana tsoron ta fallasa zuciyarta. --- ★★★★★★★ Tasleem tana zaune a ɗakin girki, tana gyara kayan karin kumallo. Idanunta na ɗauke da hawaye, sai dai tana ɓoye su. Zuciyarta na raɗaɗin jin kishiyar soyayya a cikin gidan da mahaifiyarta ta haifar da rikici a cikinsa. Amaar ya shigo cikin natsuwa, ya tsaya yana kallonta. Yana ganin yadda damuwa ke ɓoye a fuskarta duk da murmushin ƙarya da take ƙoƙarin sakarwa. Ya ce “Tasleem, Na san kin gaji da wannan rayuwar ƙyama. Amma ki sani... ba laifinki bane. Ki dage da addu’a, domin soyayyarmu za ta sami haske—duk da duhun da ke kewaye damu.” Tasleem ta juyo, ta faɗa jikinsa tana kuka. A karo na farko, hawaye masu zafi suka gangaro daga idon Amaar shima. Zuciyar sa na kuka da shiru. Gidan Madam Nablah ya zama filin fama. Soyayya ta koma yaƙi. Hasken aure da aka yi kwanaki bai iya kakkaɓe duhun da zuciya ke ɗauke da shi ba. Nasreen... Rana ta shigo da sabuwar damuwa. Nasreen ta fito daga ɗaki cikin yanayi na gajiya da rashin kwanciyar hankali. Duk da ta kasance matar aure, ba ta jin hakan. Zuciyarta tana ji kamar wata ce ke kwace mata mijinta a gaban idonta. A cikin dare ta kasa yin bacci tana jin yanda Abeesh yake furta sunan Catrina a cikin barcin sa, ta kasa jure hakan kwana tayi tana kuka tare da addu'a sai kuma sallar dare da take yawaita yi har sallar Asuba.... A safiyar yau Nasreen tana zaune a falo tana jiran fitowar Abeesh... A lokacin da Abeesh ya shigo falo yana shirin fita, Nasreen ta tare masa hanya. Idanunta sun yi jawur, zuciyarta na rawa da tsoro da fushi da ƙuduri, cikin fushi da ɗaga murya ta ce "Ya Abeesh, na gaji! ina so yau a cikin mu biyu ka zaɓi ɗaya, ita ko ni? Ni matar ka ce, na shiga gidanka da fatan soyayya da Amana. Amma tun ranar farko na gane cewa zuciyarka ta ƙi zama da ni.” Abeesh ya tsaya cak. Fuskar sa cike da damuwa. Ya juyo yana kallonta cikin tafarfasan zuciya. Ya ce “Nasreen... ki barni nayi zaman fahimta da zuciyata. Ba na son ki ji zafi, amma gaskiyar ita ce Ina son ku duka biyu." Nasreen ta dafe zuciyarta. Kamar an watsa mata ruwan zafi. Ta yi tsit na ɗan lokaci kafin ta ce da ɓacin rai: "Wato baza ka iya zaɓa ba? Wato... ka amince da ni saboda aurena ne kawai, amma ƙaunarka na wajen wata ‘yar iska da ba a san asalinta ba”... Abeesh ya ce da zafin rai: "Ki kiyayi harshen ki Nasreen! Catrina bata cancanci ki zage ta haka ba." Nasreen tana kuka ta ce "To taya zan zauna da kai idan ƙaunar ka tana wajen wata?" Ta fashe da kuka, ta juya ta nufi ɗakin ta da gudu, tana yarfe hannu cikin kuka da zafin zuciya. A wannan lokacin, Catrina tana tsaye a bayan labule. Ta ji komai. Idonta na walƙiya da jin daɗin nasarar da ke ƙara bayyana. Amma ba ta nuna komai a fuska, sai shiru da salo. Tana murza yatsunta cikin natsuwa, ta furta da sassanyar murya: “Zuciyar maza kamar ruwa ce... sai wanda ya iya tafiyar da jirgi ke kai labari.”.... --- Daren Ranar... Nasreen ta rufe kanta a ɗaki. Ba cin abinci, ba sha ko fita falo ta kasa Sai hawaye da addu’o'in da suka hana ta narke wa gaba ɗaya... Abeesh yana ɗaki shi kadai, yana ganin laifin kan sa, sai dai zuciyarsa tana cikin rikici. Catrina kamar wani shaƙin ruwan sihiri ce, yana jin ya rasa ikon fitar da tunaninta daga ransa... --- Washegari... Madam Nablah ta lura da fushin da ke yawo a cikin gidan. Sai dai ta ƙi magana. Ita dai burinta a gama auren ne, yanzu hakan ya faru — hakan yasa ta tsiro da tafiya zuwa wata ƙasa daban wanda zata ɗauki tsawon lokaci kafin ta dawo... Tasleem na ƙoƙarin rarrashin Nasreen a gefe ganin halin da take ciki, itama ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba jin abubuwan da suke wakana a tsakanin ƴar uwarta da mijinta akan wata banzar yarinya... Asmeen kuwa tana lura da yadda Shaprees ke ƙara saduda da hakuri, abin yana shiga ranta sannu a hankali, ko da tana ƙoƙarin musawa. --- Abeesh... A cikin dare, yana zaune a falonsa shi kadai. Idanunsa na kallon bango, amma zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa yana maganar zuci “Na aurar da zuciyata gida biyu – daya da shari’a, ɗaya da soyayya... Amma yanzu soyayya ta koma rikici, shari’ar ta koma kunci.” Sai kawai murya ta fito daga bayan sa — Catrina ce ta shigo sanye da doguwar riga mai launin ja, murmushinta ya cika dakin. Tana furta “Ina jin sirrin zuciyar ka... Abeesh. Ka bar zuciyar ka ya huta. Ka zaɓi wacce zuciyar ka ke so... ba wacce duniya ke so ba.”... Ta matso kusa da shi, ta zauna. Yana kallonta, yana jin duniya ta tsaya masa, akoda yaushe ƙara rikita shi take, especially idan yana kallon fuskar ta sai yaga a koda yaushe kyan fuskar ta na daɗa wanzuwa, ba ƙaramin shiga zuciyar sa tayi ba, haka kawai yake jin cewa bazai iya rayuwa ba tare da ita ba....... *MU HAƊU A KASHI NA GABA.....* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 45 to 46 Washegari... Nasreen da Abeesh ne suke zaune a dadduma dake harabar gida wurin shakatawa suna cin abinci ba tare da kowa ya yi magana wa ɗan uwansa ba, suna cikin wannan halin sai ga Catrina ta nufo wurin a slow cikin iya taku, ta sha kwalliya kamar amarya ta biyu. Wani kamshi mai ƙayatarwa na fita daga jikinta, fuskarta cike da annuri da ƙarfin gwiwar mace mai nasara. Sai da ta zaga idonta a kansu sannan ta zauna kusa da Abeesh – ba tare da tsoro ko kunya ba, tana furta sannun ku fa, nazo taya ku breakfast.... Abeesh bai ce komai ba, Bai janye jikinsa ba, Bai ma kalle su ba. Nasreen ta girgiza kai Zuciyarta kamar za ta fashe. Ta san abin da ke wakana, amma ta rasa yadda za ta yaƙi soyayyar sihiri, Catrina ba ta yi wa Abeesh komai ba amma ta ɗauke zuciyar sa gaba ɗaya da salon ta da kuma iya sarrafa zuciya... “Abeesh...” Nasreen ta ce cikin sanyin murya tana ƙoƙarin dafa hannunsa. Janye hannunsa ya yi yana kallon gefe domin yasan maganar ta baya wuce akan Catrina... Ta ce “Dan Allah... Ka kalle Ni, Ina cikin damuwa zuciyata cike take da ƙuna, kar fa ka manta nifa Amarya ce ko sati bamu yi ba......" “Nasreen... Ki barni,” Abeesh ya ce, yana miƙewa tsaye tare da faɗin “Zan tafi hospital na makara....” Catrina bin sa tayi da ido tare da ƙayataccen murmushi akan fuskar ta.... Itama Nasreen cikin fushi ta miƙe ta bar wurin da gudu domin bata ƙaunar jin wata kalma daga bakin Catrina domin a yanda ta fusata za'a iya samun matsala... Catrina ba tare da ta damu da komai ba, buɗe kuloli tayi tana ƙoƙarin zuwa abinci zata ci.... --------OTHER SIDE Asmeen da Shaprees... Shaprees yana ƙoƙarin ƙara samun shiga a zuciyar Asmeen. Ya koyi yi mata girki, yana kai mata tea, duk wata kulawa yana ƙoƙarin bata, duk wasu abubuwan da ya kamata tana yin su shi yake yi mata domin kada ta wahala.... Amma duk da haka bata gama yarda da shi ba, zuciyarta ta hana ta gasgata cewa mutumin duhu zai iya sauyawa zuwa haske. Duk da haka a jikinta tana jin sauyin—amma zuciyarta na tsoro. Yau, ya sameta zaune a tsakiyar gado tana karanta wani ɗan littafin addu'o'i... Shi kuwa a wannan lokacin ne ya shigo da kulolin Abinci yana faɗin "Amarya na kammala girkin domin nasan kina jin yunwa sosai... Shaprees ya matso da kulolin abincin ya ajiye su akan glass table na ɗakin, shima ya zauna akan gadon a gefen ta, yana kallon ta cikin kulawa... Ya ce “Kin ci wani abu ne?” ya tambaye ta. Idonta akan littafinta ta ce “Ban ci ba.” Ya ce “To, mu ci tare.” “Ka barni kawai,” ta ce cikin sanyin murya... “Asmeen...” ya furta sunan cikin tattaunar murya, ya zamo kalar tausayi sannan ya ce “Ni ba wanda kika sani bane a baya, Ina son in gyara, in rayu da ke cikin alkhairi.” Duban fuskarsa tayi cikin tsoro da rudani. Zuciyarta na harbawa a hankali, ta ce “Kayi hakuri… bani da ikon amincewa da zuciyarka yanzu, ka ƙara bani lokaci....." Ta cigaba da karatun ta a cikin zuciya... Shapreen lumshe idanuwansa ya yi tare da furta "Oh my god...." Ya ce "okay ga nan Abincin idan kin kammala zaki iya zuba wa ki ci, zan koma room ɗina...." Asmeen ba tare da ta kalle shi ko ta furta wani abu ba, har ya fice, Yana shiga room ɗin sa kamar zai rausa ihu haka ya faɗa saman gado a wahalce, kansa a kife akan gadon yana hawayen rashin nasara.... Wata murya ce ta ratsa cikin kunnuwan sa mai daɗin sauraro, a zabure ya ɗago yana kallon wani haske da yake kewaye da Sofia cikin doguwar riga fara sol, sai sheƙi take da murmushi kwance akan fuskar ta... A hankali ta furta "ina mai jin baƙin cikin ganin hawaye a fuskar mijina...." Da gudu Shapreen ya nufo ta tare da kai hannu zai rungume ta sai kawai ya ji ya rungumi iska domin a zahiri ita ɗin ce take tsaye a matsayin ruhi ba'a cikakkiyar mutum ba... Ta ce da shi "baza ka iya taɓa Ni ba Shaprees domin ba ni ce a matsayin matar ka ba yanzu, nasan yanzu zuciyar ka tana ƙoƙarin komawa yanda kake mai haske amma dole saika fuskanci ƙalubale a gaban ka, kafin Asmeen ta gama yadda da kai domin sai ka jure, domin ita yarinya ce ƙarama, da farko ka nuna mata ƙiyayya hakan yasa yanzu take tsoron amince da kai...." Shapreen kamar zai fashe da kuka ya ce "Sofia na gaji! bazan iya jure hakan ba, ina ƙoƙarin bata farin ciki a koda yaushe amma ita gani take kamar cutar da ita zan yi, ta kasa sakin jiki da shi why?...." Sofia matso dab da Shapreen tayi tare da ɗora tafin hannunta a saitin zuciyar sa tana faɗin "ka cigaba da haƙuri da juriya, na san yanzu ka fara sonta sosai, ina so ka cire fushi a ranka...." Jinjina kai Shapreen ya yi tare da faɗin "ina sonta sosai, lokaci guda naji ta mamaye zuciyata, Nagode miki da kika taimaka mun wurin kawar da duhu daga cikin rayuwata, kika musanya da hasken alkhairi....." Sofia wasu zafafan hawaye taji sun fara gangaro mata akan kumatu..... Shapreen hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba a ruɗe ya ce "me me meya faru Sofia...." Tana kuma ta ce "ka riga da kasan cewa Sofiyyar ka tana da kishi, har yanzu ban canza ba koda ina matsayin ruhi, zan tafi domin yanzu zuciyar ka ba tawa bace...." Shapreen a ruɗe yake faɗin "ah ah Sofia kin riga da kin san cewa ke ce duniya ta, kuma har yau ina alfahari da ke, babu macen da zan so sama da ke a rayuwa, sai dai na kwatanta amma ko rabin ki bazata kai ba...." Girgiza kai Sofia ta yi sannan ta ce "ban hana ka so ta ba amma kada ka manta da ni...." Tana kaiwa nan ta ɓace, sai ƙamshin haske da ta bari a wurin.... Shapreen zama ya yi a bakin gado tare da cusa yatsun sa a cikin sumar kan sa...... --- Catrina tana zaune a bakin gadon ta sha kwalliya tana sanye da rigar bacci marar nauyi, tana jiran shigowar Abeesh domin ta tura masa message akan tana son ganin sa a ɗakin ta, bata jin daɗin jikin ta.. Abeesh kuwa jin haka bai jira komai ba ya zura jallabiyar sa ya yi waje da sauri, a falo ya tarar da Nasreen zaune tana jan carbi idonta akan plasman tana kallon tapsirin wa'azi.. Yana tsaye ata bayanta domin bata san ya fito ba, tsaya tunanin yanda zai yi ya wuce ɗakin Catrina ya yi domin dole sai ya bi ta gaban ta idan yana son zuwa ɗakin... Ɗaga kansa ya yi yana kallon agogo, yanzu ƙarshe 12 saura na dare, fuska kawai ya yi ya shige falon, zama ya yi a kan kujerar gefen ta tare da faɗin "baki yi bacci ba?..." Kallon sa tayi tare da jinjina kai ba tare da ta furta komai ba, ya kuma cewa "meya hanaki yin bacci a wannan lokacin?..." Bata ce komai ba idonta akan plasman... Cikin fushi ya miƙe tsaye yana faɗin "wato kin mayar ni ƙaramin yaro ko? ina miki magana kina wani shan ƙamshi, ni ya dace nayi fushi da ke ba wai ke ba...." Nasreen ko kallon yanda yake bata yi ba still idonta akan plasman, ciro wasu allurai ya yi a cikin aljihun jallabiyar sa da maganinnuwa yana faɗin "kin ga wancan yarinyar bata da lafiya, tana cikin mawuyancin hali zanje nayi mata allura sannan na bata maganin da ya kamata ta sha...." Daga nan ya wuce kai tsaye upstairs da zai kai ka can ɗakunan baƙi ya haura da sauri-sauri... Nasreen har ya gama haurawa bata ɗauke idonta akan sa ba, tana mamakin yanda Abeesh ya zama haka lokaci guda, kuma ma saboda ya raina mata wayo wai wancan yarinyar bata da lafiya.... Haka take ta maganar zuci, ta cigaba da zama zata jira fitowar sa.... Kallon agogo tayi taga ƙarshe 12 yanzu na dare..... Abeesh ya zuwa ya fara buga ƙofar. Catrina ta buɗe da murmushi kwance saman fuskar ta... Catrina ta masa maraba da murmushi mai ɗaukar hankali, tana sanye da riga mai launin ja mai haske, wacce ke bayyana surar jikinta, tana ɗauke da ƙamshi mai ɗaukar hankali. Abeesh bai ce komai ba, ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita. Kallon ta kawai yake yana jin wani sanyi da dumin sha’awa yana ratsa jikinsa. Catrina ta riƙo hannunsa cikin nata, ta ce da shi da murya mai sanyi “Ban san yadda zan bayyana maka yadda nake jin ka ba, Abeesh. Amma zuciyarka tawa ce gaba ɗaya...” Ya kalli idonta, ba tare da ya iya furta komai ba. Sai dai ya ji zuciyarsa na amsawa da karfi. Wannan dare ba dare ba ne na wucewa kawai—zai zama makasudin sauyin soyayya.. haka yake kallon fuskar ta kamar wanda ya samu madubi, daga bisani ya ce "ke bakya gajiya da murmushi ne? ban taɓa ganin ki cikin fushi ba..." Catrina zama tayi a bakin gado tare da faɗin "an halicci murmushi nane saboda kai, meyasa zaka ga fushi na kuma...." “Abeesh...” ta furta da wata murya mai narkar da zuciya ta ce "cutar kewar ka ne ya kamani, zan iya samun mungun matsala idan na cigaba da zama a haka ba tare da kai ba...." Sakin numfashi ya yi tare da faɗin “Zan zauna tare da ke na ɗan wani lokaci, ki kasance da zuciyata, in har shine muradin ki...." Jan hannunsa tayi ya faɗa saman kanta tana faɗin “Ba kawai zuciyar ka ba… har ma da dukkan ruhin ka nake so.…” Kallon cikin idonta ya yi... sai kawai ya sauƙa daga kanta ya zauna a bakin gado yana girgiza kai tare da faɗin "bana son wani abu ya shiga tsakanin mu, har yanzu zuciyata bai gama yanda cewa zan iya aikata wani ɓarna na saɓon Allah ba, in har kina so na da gaske to ki guji jefa ni a cikin wani halin da zai sa na kusanci macen da ba muharrama ta ba, ina nufin zina...." Catrina jinjina kai ta yi ta ce "nayi maka alƙawarin babu abinda zai shiga tsakanin mu sai alkhairi, amma dan Allah ina so a wannan daren ka zauna dani, ko zan iya bacci...." Abeesh ya ce "yanzun ya kike jin jikin nakin? na taho da allurai..." Catrina zato ido tayi ta ce "ni kuma meya haɗani da allura bayan nace cutar kewar ka ke damuna, kaine magani na, ka kwana dani sai na fi samun nutsuwa...." Abeesh kwanciya ya yi a bakin gado, itama kwanciya tayi a gefen sa tare da rungumo shi tana kallon kyakkyawan fuskar sa.... Nasreen kuwa har misalin ƙarfe 3 ta kai na dare tana jiran fitowar Abeesh daga ɗakin Catrina amma shiru har bacci ya ɗauke ta akan kujerar falo... Daren ya gangara cikin nutsuwa da ɓoyayyun ruɗani. Abeesh ya kwana a ɗakin Catrina zuciyarsa cike da rikice-rikice, amma jikinsa yana masa jagora cikin natsuwa kamar yana bin saƙon da zuciyar sa ke masa. -------Ƙiran Asubar Farko akan kunnen Abeesh, buɗe idonsa ya yi yana bin ɗakin da kallo, a hankali ya maida idonsa kan Catrina wacce take kwance akan ƙirjinsa bata samu farkawa ba... A hankali Abeesh ya ture ta gefe sannan ya tashi jiki a sanyaye ya fice a ɗakin, yana sauƙa falo ya tarar da Nasreen a wurin da ya barta tana kwance akan kujera idonta a lumshe kamar mai yin bacci, sai dai ba baccin take ba, da sauri Abeesh ya wuce gudun kar ta buɗe ido ta gan shi, yana wuce wa Nasreen ta buɗe ido tana jinjina wannan lamarin, tasan Abeesh ne ya wuce domin tin sauƙowar sa ta gan shi, ganin sa ne yasa ta lumshe idonta.... A yau bata tanka masa ba, kuma bata nuna masa cewa tasan a ɗakin Catrina ya kwana ba, haka ta zuba masa ido, Ganin haka yasa a kwana na biyu Catrina ta ƙara neman sa, a wannan lokacin ƙiran sa tayi tana kuka, ganin haka yasa ya fita nan ma da daddare ne misalin ƙarfe 10... Fitarsa ke da wuya ya fara leƙe-leƙe gudun kar ya tarar da kowa a falo, duk wannan lelleƙawar da yake Nasreen tana tsaye a bakin ƙofar kitchen tana kallon sa, hannun ta riƙe da kofin tea zata sha domin yanzu bata iya cin komai, da haka ya wuce ɗakin Catrina, a yau ma acan zai kwana.... A wannan ranar Nasreen kwana tayi bata yi bacci ba, tana kwance a ɗakin ta tana kuka kamar ranta zai fita. Idonta ya kumbura, zuciyarta cike da raɗaɗin kishi da bakin ciki. ita kaɗai sai juyi take a gado gaba ɗaya kwanciyar hankali ya ƙaurace mata.... Da safiyar gari, kafin kowa ya farka, Nasreen ta tafi ɗakin Tasleem. Tasleem tana kan sallaya yanda ta idar da sallar asuba, ganin Nasreen a cikin wani hali ne yasa tayi saurin miƙe wa tsaye tare da faɗin "lafiya kuwa Nasreen? me yake faru wa?...." Nasreen sai da ta rungumi ‘yar uwarta Tasleem kafin ta fashe da kuka, tana sharar hawaye cikin muryar kuka take faɗin “Tasleem... na gaji! Kamar a cikin mafarki nake, yana kwana da wata a yayin da ni nake matsayin matarsa! Kuma ya kasa fitar da ita daga zuciyar sa... kina ganin zan iya ci gaba da wannan zaman?” Tasleem ta saki numfashi da ƙarfi, baƙin ciki da tausayin Nasreen ne suka shige zuciyarta. Ta dafa kafadarta tana faɗin “ Na fahimce ki, Nasreen kiyi haƙuri... amma ki barni da ita. Wallahi sai ta gane cewa gidan nan ba na raini bane. Wata iriyar ‘yar bariki ce haka? ko ita ɗin mutum ce ko ba mutum ba ce—wallahi sai na tunkare ta!”... Tasleem ta share mata hawaye tana faɗin "ki yi haƙuri ki sa salama a cikin zuciyar ki, ki daina bayyanar da damuwar ki a wanda yake son ganin bayan ki, yanzu ki je ki huta zan neme ki...." Nasreen jinjina kai kawai tayi tare da ficewa daga ɗakin.... ---. Shaprees yana ɗakin su yana kallon Asmeen wacce ta fara narkewa a hankali. A wannan ranar, ta zauna kusa da shi a cikin dakin su na ma'aurata, tana tausayin yadda yake kokarin kyautata mata ba tare da nuna tsana ko kishi ba. A hankali ta furta “Shaprees... baka san yadda nake jin ba a raina, na jima ina tunanin kai wani ne dabam, amma yanzu ina ganin... ka cancanci ka samu farin ciki.” Shaprees ya kama hannunta, yana kallon ta cikin kulawa ya ce: “Ina so ki yarda dani, Asmeen. Na cire duhu daga zuciyata domin Allah. Soyayya da alheri nake nema yanzu. Kiyi ƙoƙarin bani dama dan Allah...” Asmeen wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata tare da rungumar sa tana kuka... Shima rungumar ta ya yi yana rarrashin ta cikin so da ƙauna.. Haka kawai yake jin tausayinta, especially jin ƙudurin mahaifiyar ta akan su.... ★★★★★★★ A yau... Tasleem ta tunkari Catrina da fuska ɗauke da zafin zuciya da tsantsar fushi... Tarar da ita tayi a zaune a falo tana kallon wani Film na horror.. Tasleem tsaya mata tayi a kai cikin tsantsar matsifa take faɗin “Ke! Na gaji dake, Kina wasa da zuciyar ‘yar uwata, da mutuncin mijinta. Ko kin manta wannan gida na mutunci ne? Kin raina mana hankali?”.... Catrina ta ɗaga kai tana kallon Tasleem cikin kwanciyar hankali, murmushinta bai gushe ba. Ta ce da ita: “Wannan gidan ne na mutunci ko kuma mutanen cikin ta? Hmmmm! Idan zuciyar mutum ta mallaki wani abu, ba laifi bane. Shin idan mijin ‘yar uwarki yana nuna mun soyayya... hakan laifi ne?” Wani irin cakuma Tasleem tayi wa sumar gashin ta tare da ɗago ta tsaye, Catrina daƙer ta fizgi gashin ta tana faɗin "Ashhhh!! kina hauka ne?..." Tasleem tana zaro ido waje ta ce "Yau zan nuna miki yanda ake asalin hauka, Indai zaki cigaba da bibiyan mijin ƴan uwata to sai na gurɓata miki rayuwa, shaiɗaniyar banza, karuwar gida, idan mazajen mutane kike so ki fita can bariki suna jiran wanda bai zo duniya ba ma, amma ba'a cikin gidan nan ba, domin kaf babu la'anannu, da mutuncin mu da darajar mu haka kuma da kimar mu mun kuma san kunya..." Tintsirewa da dariya Catrina tayi tare da faɗin "da farko dai ki fara zuwa ki tuntuɓi mijin ƴar uwar takin, ki bashi zaɓi shin yana so nane ko kuwa, idan ya baki amsar eh yana sona to kuwa sai dai kuyi haƙuri domin ba bu yanda zaku yi da ni, na zamo muku ciwon ido a cikin gidan nan...." A fusace Tasleem ta shaƙo wuyan ta tana faɗin "aww haka ma kike cewa? ai kuwa zaki bar gidan nan tinda ba gidan uban ki bane...." Itama Catrina riƙo ta tayi nan suka fara kaurewa da faɗa... Tasleem da Catrina sun shiga faɗa mai zafi. Gidan ya ɗauki ƙarar fashewar glashe yanda suke ta faffasawa duk a cikin faɗan, kayan ado da fitilu na falo duk suka faffaɗo ƙasa suna tarwatsewa kamar hayaki, kowa yana ji da ƙarfin sa domin akwai sirrin ƙarfi a jikin su wanda yake ɗauke da Haske da Duhu.... Catrina ta fisgi labulen taga, ta wurga wa Tasleem ta faɗi ƙasi ita da labulen, itama haka ta zuciyo ta miƙe tare da janyo kofunan glass dake jejjere akan dinning ta wurga wa Catrina sai akan goshin ta, nan da nan goshin ya fashe, a ruɗe Catrina ta sau wata ƙara.... Tasleem nuna ta take da yatsa tana faɗin: "Kin raina mana hankali Catrina! Ke ba mutuniyar kirki bace. Kawai kin zo da niyyar ruguza soyayya ne! Kin fi karfin mu ke?!" Catrina ɗago wa tayi tare da ɗaga gira, tana goge jinin da ke zubo mata akan goshi, fuska ɗauke da murmushin da ke ɗora wuta a zuciyar Tasleem. Ta ce da ita: "Na fi karfin zuciyoyin ku gaba ɗaya, Ke ki ke taya ƴar uwarki faɗa akan mijinta, ni kuma na riga da na mallake shi. Na shiga ransa yanda bazai iya manta ni a rayuwar sa ba...." Tasleem ta furta “Ukkk!” sannan ta nufi Catrina da niyyar fin karfin ta, suka kama juna da faɗa mai zafi, tana jan gashinta, tana hura hanci cikin fushi tana faɗin "Sai kin fice daga gidan nan da kanki!" Catrina kuma ta riƙe rigar Tasleem tana janta itama, har suka faɗi saman kujerar falo nan kujerar ta dungura da su, faɗa suke na gaske, Catrina ganin Tasleem tana shirin fin ƙarfinta yasa ta kafa haƙwaranta akan breast ɗin Tasleem ta garzaya mata ciwo, ba shiri Tasleem ta sau wata iriyar ƙara mai rikitarwa, sai da falon ya ɗau sautin.... Falon ya koma kamar wurin faɗan aljanu. Amaar da Abeesh jin ƙarar ihu yasa suka shigo falon a guje. Amaar ya damƙe Tasleem yana kokarin jan ta gefe, yana rarrashi ta... Tasleem tana kuka tana faɗin "wallahi mayya ce yau saina yi maganin ta, ka barni na zubar mata da haƙora....." Amaar cikin tashin hankali yake faɗin “Tasleem! Dan Allah ki bari! Wannan ba hanya bace. Ki duba kanki fa!” Abeesh kuwa ya ja Catrina yana faɗin: “Catrina! Enough! Ki dakata! Wannan ba shine nake so ba.” Tasleem ƙwace wa tayi daga hannun Amaar ta sake nufo Catrina. Gaba ɗaya gidan ya cika da hayaniya da tashin hankali... Daƙer Amaar ya sake riƙo ta tare da rungumar ta sosai.... A cikin wannan rikici, sai ga Nasreen ta fito daga kitchen hannunta rike da wuƙa mai kaifi. Idonta jajir, zuciyarta na tafasa kamar ruwan zãfi. Ta nufi Catrina kai tsaye da nufin caka mata tana faɗin: “Kina son kashe mun aure ko? Zaki kashe rayuwata ko? Wallahi sai na nuna miki ni matarsa ce ba ke ba!” Abeesh da ya hangota da wuƙar ya yi saurin tarar ta da ƙarfi ya damƙe hannunta yana faɗin: “NASREEN! Ki sauƙe wannan wuƙar! Wannan faɗa ba mafita bace. Kar ki zama mai laifi akan soyayyar da ke rikitar da kowa.” Nasreen fashe wa tayi da kuka tana ƙoƙarin ƙwace wa tana nuna Catrina da wuƙar, tana faɗin "Wallahi yau babu abinda zai hana na kashe ta, sai na rabata da rayuwar ta...." Amaar ya nufi wurin da Abeesh yake riƙe da Nasreen yana faɗin "Kin ga Nasreen ki kwantar da hankalin ki, ke ce mai hankalin cikin ku ki saurara...." Kafin Amaar ya rufe baki Tasleem ta tafi da gudu ta damƙi wuyan Catrina tare da girban sawayen ta sai yaraf a ƙasi, Tasleem danne wuyan ta tayi sosai a ƙasin carpet tana faɗin: "Nasreen zo ki huda cikin ta da wuƙar nan, umarni nake baki yanzu...." Ai kafin a ankara itama Nasreen ta nufi yanda suke da mungun gudu tare da ɗaga wuƙar zata caka wa Catrina a ciki, Abeesh ya yi wani irin sufa ya cabki hannun Nasreen kafin ta kai ƙasi, fizgar wuƙar ya yi tare da rungumar ta sosai yana faɗin "Please! Please!! Please!!! NASREEN don't do that...." Nasreen fashe wa tayi da matsanancin kuka..... tana faɗin “Ni ce matarka, amma ka zaɓi kwana da ita! Kayi min adalci kenam?! Me na maka, Abeesh?!” Kwantar da kanta ya yi akan ƙirjin sa yana rarrashin ta... Ita kuma Tasleem Amaar ne ya yi mata ɗaukan luɗa daga saman cikin Catrina yanda take ta naushin ta... Catrina tashi tayi a ruɗe ta ɗan ja baya da murmushi mai wuyar fassara. Tasleem na gefe tana jan numfashi da ƙyar, yayin da Amaar ke rarrashinta... Abul mahaifin su Amaar da Abeesh wanda yake zaune a can ɗakin sa jin hayaniya a falo yasa ya fito falo yana faɗin "me yake faruwa anan?..." Tasleem ce zata faɗa wa Abul abinda yake faruwa sai Nasreen ta katse ta da cewa "dan Allah Tasleem kar ki sanar.." Tasleem ta ce "wallahi sai na faɗi abinda ke faruwa" Amaar ya ce "Nima ban san meke faruwa ba haka na tarar dasu suna faɗa amma Tasleem sanar mana abinda yake faruwa..." Tasleem ce ta tsaya a gaban kowa, ta ce da ƙwarin guiwa: "Catrina ce take soyayya da Abeesh, tana shiga ɗakin Abeesh dare da rana, yanzu ma suna kwana tare kamar miji da mata, kuma a gaban Nasreen duk hakan yake faruwa, Wannan ai wulakanci ne ba ƙauna ba!" Lokaci guda fuskar Amaar ta canza, Zuciyarsa ba ƙaramin ɓaci tayi, bai ce uffan ba sai kawai ya nufi gaban Abeesh cikin ɓacin rai ya zabga masa mari mai ƙarfi wanda kowa yaji ƙarar sa a dakin, yana faɗin: "Kai munafuki ne?! Ka ɓata tarbiyyar ka! Ka ɓata sunan gidanmu! Wace irin rana ce wannan da zaka bar matarka ta sunnah kana kwana da wata macen banza?!".... Abeesh ya yi shiru, yana kallon ƙasi, hannu a dafe akan kunci bai iya kallon kowa ba... Catrina taji matuƙar ciwo a ranta jin marin da aka yi wa Abeesh, jure wa kawai take... Itama Nasreen sai da ta rufe idanuwanta sosai tana jin zogi a cikin zuciyar ta, bata so wannan al'amarin ya faru ba... Abul juya wa ya yi yana kallo mai ɗauke da ɓacin rai da mamaki yana duban Catrina. Cikin murya mai nauyi ya ce: "Ke... baƙar kuliya ce! Mai bakar Aniya!" Catrina ta kafe shi da ido, ta ɗan saki murmushi, kamar wata jaruma mai raina kowa. Amma bata ce uffan ba. Sai dai cikin zuciya ta tasan cewa Abul ya gane ta! Ya gane asalin ta — Sarauniyar Duhu. Amma Abul bai faɗi wannan gaskiyar ba, domin yasan dole wata rana asirinta zai tonu, yasan ko zai faɗa musu cewa Catrina ba mutum ba ce, akwai wasu da ba zasu iya jurewa ba. Ya sake juyowa ya ƙara daka wa Abeesh tsawa tare da faɗin "Ka raina mutuncina kenam? Abeesh.... haƙiƙa na raina tarbiyyar ka, Ka ɗora ma kanka laifi da ba zaka iya ɗauka ba. Ka bar matar aure ka rungumi wata iska..." --- 🔥 Cikin Zuciyar Catrina: A lokacin da suke zagin ta da fushi da kuma faɗa, Catrina ta rufe idonta, ta furta a zuciyarta: "Kun yi faɗa da ni amma Sai dai... ku sani, ban zo da niyyar ɗaukar mijin wata ba, na dawo ne don na ɗauki haske daga gare ku."... Tana kammala maganar zuci ta bar falon tare da nufan ɗakin ta.... Abul ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, a fusace ya bar falon yana mai yin fushi da Abeesh... A wannan ranar wuni akayi cikin ɓacin rai... --- A ɗakin Abeesh... Nasreen na zaune gefen gado, kanta a ƙasa, tana kuka kamar ruwan sama. Abeesh yana tsaye kusa da taga, yana kallon sararin sama. Yayi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce da muryar dake nuna cewa shi ma zuciyarsa cike take: “Na kasa control zuciyata Nasreen... Ki yarda da ni. Ban taɓa so in cutar da ke ba. Amma bazan iya fitar da Catrina daga zuciyata ba.” Nasreen ta ɗago kai, idonta jajir ta ce: “Ka ƙi ka zaɓe ni Abeesh. Na fahimta. Amma bari na faɗa maka abu guda... Duk da cewa zuciyar ka tana tare da ita, ni ce matarka a bisa doka da addini. Ni ce kake da alhaki akai. Kuma wallahi, zan tsaya tsayin daka akan aurena.” Abeesh ya juyo yana kallonta cikin tsananin damuwa ya ce: “Na san haka. Amma Catrina... kamar akwai wani abu a tsakanin mu da bana iya bayyana wa. In na kalleta, zuciyata na bugawa...” “Zuciyar da ta buga shin tana manta ƙauna?” Nasreen ta katse shi, hawaye na gangarowa. “To ka zauna da ita. Amma ka sani, bazan bar aurena haka nan ba.” --- Washegari da safe... Falonsu ya lafa, amma ba a cire kayan da suka tarwatse ba. Tasleem ta fito daga ɗakinta cikin riga mai laushi da ɗan gashi a rataye akan wuyanta, tana fitowa ta iske Catrina zaune kan kujera tana shan shayi, cikin fara’a kamar ba ita aka kusan cakawa wuƙa jiya ba. Tasleem ta tsaya cak tana kallonta, sannan ta ce da ƙarfin zuciya: “Ke fa baƙuwar da aka ba wurin zama ce. Amma ina sane da niyyarki... Soyayya dai za ta fito da gaskiyar ta, kuma wata rana za a gane wacece ke, Catrina...” Catrina ta ɗan saki murmushi, tana ɗora kofi a leɓenta sannan ta ce “Idan zuciyar mutum ta amshi abu, ko wane hali yake ciki, sai ya rasa kwanciyar hankali. Bani ce na tilasta masa soyayya ba. Shi ne yazo gare ni...” Kafin Tasleem ta bata amsa sai ga Asmeen ta shigo, cikin farin ciki da annashuwa —kamar wata sabuwar wata... Tasleem ta kalleta da mamaki ta ce: “Asmeen... me nake gani haka? ke ce yau a part ɗin nan? yau Ango ya barki kenam tin Aure rabon ki danan, ga shi har mun shiga sati na biyu...” Asmeen tana dariya ta ce "wallahi nazo ziyara ne, nayi farin cikin ganin ki sosai...." Tasleem ta ce "Asmeen ya dai nake ganin ki cikin farin ciki kodai yanzu ba wata matsala tsakanin ki da Shaprees?..." Asmeen rungumar Tasleem ta yi tare da faɗin "yanzu mijina bashi da wata matsala, ya zamo tamkar waliyi, shiyasa kika ganni cikin farin ciki, mu da duhu har abada munyi hannun riga...." Tasleem cikin farin ciki ta ce "Alhamdulillah Ƴar uwata haka nake son ji..." Catrina tana kallo Asmeen da mamaki, amma bata ce komai ba. Amma wannan haske da ke dawowa cikin Asmeen, wani sabon babi ne da zai iya karya ƙa’idar da Madam Nablah ta kafa. --- Kiyi shiri... Madam Nablah na gab da dawowa daga tafiyarta. Kuma za ta dawo ta tarar da gidan nata yana karkarwa da rudani—soyayya da ƙiyayya, barazana da mafita suna yaki a cikin gida guda. Catrina na zaune tana maganar zuci.... Suna cikin wannan halin sai ga Nasreen ta shigo falo, ganin Asmeen yasa ta tafo da gudu suka rungumi juna, haka suke farin cikin ganin juna... Su uku sun haɗa kayuwansu guda suna farin cikin kasance da juna... Yayin da Catrina na zaune cikin izza kamar itace uwar gidan. tana gyara yatsun kafarta da reza tare da tauna cingam tana ƙararas... Su ma duk zama suka yi...a falon. Nasreen tana kallon Catrina cikin kishi da zafi kamar zuciyarta na tafasa da ruwan zãfi. Asmeen tana kallon su cikin fara'a, tana riƙe da wani ƙaramin ledar kayan zaƙi domin tasan ƴan uwanta suna matuƙar son kayan zaƙi na ƙwaɗayi... Ta ce: “Tasleem! Nasreen yau na ce bari in zagaya na gaishe ku… Amma… kamar sabuwar fuska nake gani…” ta kalli Catrina sannan ta dawo da kallon ta ga Tasleem da Nasreen ta kuma cewa “Wacece wannan baƙuwa muka yi ne? Ban taɓa ganinta ba.”... Tasleem ta lumshe idonta, zuciyarta na ƙoƙarin kwantar da kai, kafin ta ɗan jinjina kai sannan ta ce: “Ƴar baƙunci ce daga can waje. Tazo gaisuwa ne ga Momy, sai ta tsaya.”... Catrina ta saki murmushin da babu laifi amma akwai shashanci a ciki ta ce: “Ni kuwa sai dai in ce nazo sadaukar da zuciya… Gidan da na samu kulawa da kwanciyar hankali. Ina jin kamar nan ne nawa gidan.”... Asmeen ta ƙara kallonta, cikin nazari da tsananin shakku, tace: “Kwanciyar hankali da kulawa…? Hmm, an ci sa’a. Sai dai kamar kin fi dacewa da ɗakin baƙi, ko ba haka ba?” Catrina ta ɗan kwashe da dariya, tana ɗan karkada gashinta ta ce: “Wani lokacin zuciya ta fi gini zama gida, Asmeen…” Nasreen ta miƙe tsaye, tana tafa hannunta kamar wacce ta gaji tare da faɗin: “Kina nufin zuciyar mijin wasu? Tunda ai kin sami sabuwar matsuguni, ko ba haka ba?” Asmeen ta kallesu duka biyu cikin mamaki, bata fahimci inda zancen ya dosa ba. Amma kafin tayi magana, sai wayar Catrina ta yi ƙara. Ta ɗauka, ta yi wata hira da ba a ji ba, sannan ta miƙe kamar wacce zata bar falon. Ta ce da su . “Zan wuce yanzu. Sai an jima...” Ta juya cikin izzarta, tana tafiya kamar sarauniya, gashinta yana kyalli kamar zinariya. Bayan ta fita, Asmeen ta juya ga Tasleem cikin damuwa tana kallon Nasreen da Tasleem ta ce “ Ku gaya min gaskiya, wacece wannan? Kuma me take nema a gidan nan?” Nasreen ta ja numfashi, idonta na ƙoƙarin cikowa da ƙwalla ta ce: “Ta karɓe zuciyar Abeesh, Asmeen. ita ɗin kamar mayya ce… Ba a san asalinta ba, ba a san inda ta fito ba, amma ya kasa rabuwa da ita.”... Asmeen ta ɗauki salati, ta dafe goshi tare da faɗin “Innalillahi... yanzu ita ce wannan ke jefa ki Nasreen cikin damuwa? Kuma Momy bata san komai ba?”... Tasleem ta girgiza kai sannan ta ce: “Momy tayi tafiya, kuma kamar da gangan take gujewa auren mu ni da Amaar. Ba komai Asmeen, komai sai dai muyi addu’a… Amma ke fa? Shaprees yana kula dake kuwa?” Asmeen ta yi shiru na ɗan lokaci, sai kuma ta ce da sanyi: “E… Yana kokari. Kullum sai ya tambayi yadda nake ji, yana kula da Ni, Na fara jin kwanciyar hankali tare da shi, duk da zuciyata bata gama buɗewa ba.” Tasleem ta riƙo hannunta cikin nata, tace: “Ina fatan ke zaki samu farin ciki, Asmeen. mu cigaba da addu'a sauƙi na nan tafe Insha Allahu..." Suka rungume juna a hankali. Amma a bayan labulen falon, wata inuwa ce ta ke kallon su — Catrina — ta dawo, ba tare da su ankara ba. Idonta ya ƙanƙance, kamar wacce ta ji wani abu da bai mata daɗi ba. “Soyayya ba ta da sauƙi ...” ta furta da siririyar murya. “...amma bazan bar shi ba. Ko da kuwa sai nayi amfani da zuciyarsa gaba ɗaya...” Bayan Sallar Isha’i Shapreen ne yazo ya ɗauki Asmeen suka tafi can part ɗin su... Daren ya zo da natsuwa, Kowa ya shiga sashi-sashinsa, Amma zuciyar Nasreen cike da raɗaɗi kamar zuciyar mace da take numfashi a cikin wuta. Abeesh yana ɗakin Catrina. A cewar shi, “zai je ɗan gaishe da ita ne” — amma Nasreen ta san cewa wannan ƙarairayi ne, domin sau nawa yanzu da take tsintar sa a ɗakin Catrina cikin dare? Ta zauna a gefen gado tana danna wayarta amma kallo ɗaya zaka mata kasan ba duba wayar take ba — zuciyarta na ambaliya da hawaye ne kawai. Sai taji numfashinta yana ƙoƙarin ɗagewa.... Tasleem ne ta shigo ɗakin cikin gajiya, tana ɗauke da wata ruwan zafi da lemon zaki. Ganin Nasreen a ɗakin ta cikin damuwa yasa ta ajiye kofin a gefe saman frig sannan ta zauna kusa da ita tana faɗin "Nasreen, wallahi ni ba zan ci gaba da kallon wannan halin da kike shiga ba. Wannan ba aure bane, wannan azaba ce." Nasreen ta girgiza kai da hawaye shaɓe-shaɓe akan fuskar ta. Ta ce "Na haƙura Tasleem... Na ce da kaina kowa na fuskantar jarabawa a cikin aure. Amma har yau kwana na na uku, mijina yana dakin wata na gaji Tasleem......." *NEXT NEXT NEXT NEXT* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 47 to 48 Nasreen tana kuka tana riƙe da hannun Tasleem tana faɗin: "Kiyi haƙuri da abin da zance Tasleem, zaman gidan nan ya isheni haka, ina zaune ne tamkar gawa, idan na cigaba da zama a gidan nan wata rana zuciyata zata buga ne gaba ɗaya ku rasa ni har abada, bazan iya juran wannan wulaƙanci da tozarci ba, zan tafi Tasleem! zan bar gidan ko hankali na zai samu kwanciya..." Tasleem rungumar ta tayi tana rarrashin ta tare da faɗin "wait Nasreen....kina maganar zaki tafi shin ina zaki je? gidan nan fa shine dolen ki koda bakya Auren Abeesh, bakida yanda ya fi nan gidan..." Cikin kuka Nasreen ta ce "ko ina zan je, kuma zan rayu a ko ina...." Tasleem ta ce: "To yanzu dai dare ya yi kiyi haƙuri zuwa gobe da safe, ki kwanta kiyi bacci dan Allah...." Daƙer Tasleem ta rarrashe ta tukun ta kwanta, a tare suka kwana a ɗakin, gari yana waye wa Nasreen ta fara shirya kayanta, tasa a ranta ita tafiya zata yi.... Har ta gama shirya komai tana zaune, cikin shirin ta.... Tasleem ta ce: "Ki yi haƙuri Nasreen, komai ya yi farko zai yi ƙarshe, wata rana sai labari da yardar Ubangiji, bamu da kowa kin sani, bamu san wasu dangin mahaifin mu ba sai Abul dake Tare da mu, sannan tin da muka zo duniya Mommy bata kaimu gun wajen dangin ta ba, mun sha tambaya har mun gaji, ta ƙi bayyanar mana su, to ya zamu yi...." Girgiza kai Nasreen tayi tare da miƙe wa tsaye tana faɗin "Ki yi haƙuri kawai domin tafiya ba fa shi, dan Allah ki kula mun da Asmeen, sannan ki bawa Abul haƙuri domin bazan masa sallama ba, idan Mommy ta dawo itama ki bata haƙuri, zan tafi...." Ɗaukan mayafin ta tayi ta yafa daman da akwatin ta take tafe, ta gama shirya komai..... Tasleem riƙo hannun ta tayi tana faɗin: "Nasreen meyasa bakya jin magana ne kam?...." Nasreen tana kuka mai zafi, hawaye na gudu kamar ruwan sama, tana girgiza kai tana faɗin: "Na gaji! Bazan iya ba! Wallahi bazan iya zama da mijin da yake da yake kwana da wata mace a gidana ba!".... Tasleem ta ƙwantar da murya tana riƙe da hannunta ta ce "Dan Allah Nasreen ki zauna, wannan gida naki ne, kar ki bar shi haka!" Nasreen janye hannunta tayi da ƙarfi tare da faɗin: "A'a Tasleem! Ki bar ni na tafi. Ki bar ni da hukuncin da na yanke wa kaina dan Allah...!" Tana kuka ta fizge hannunta daga riƙon da Tasleem tayi mata, cikin sauri ta fito falo da akwatinta a hannu, tana fitowa ta ci karo da Abeesh da Catrina, sun fito daga ɗaki suna murmushi kamar babu wani abu da ke faruwa... Itama Tasleem da sauri ta biyo bayan ta, ganin su Abeesh yasa itama ta tsaya cike da mamaki tana kallon Abeesh domin shine abun ji, ba Catrina ba... Abeesh idonsa ne ya sauƙa akan Nasreen tana riƙe da akwati, zuciyarsa ce tayi wani irin bugu ganin a halin da take ciki, da sauri ya ƙarasa shigowa falon yazo ya tsaya a gaban Nasreen, cikin rashin fahimta yake kallon ta daga bisani ya ce: "Ina zaki je da akwati?..." Nasreen tana hawaye ta ce "zan tafi inda bazaka ƙara gani na ba, ina haka kake so ko? ka zaɓi budurwarka sama da ni matarka ta Aure...." zuciyarsa ce ta ɗauki sautin bugu jin abinda ta faɗa.... Ya riƙo hannunta cikin firgici yana faɗin: "Nasreen ki tsaya, ki saurare ni. Dan Allah, ki zauna mu warware komai." Nasreen ta ce: "Uhmmm! Lokaci ya ƙure Ya Abeesh, a yanda na ƙudurta a raina cewa a yau zan bar gidan nan kuma a yanzu to babu wanda zai dakatar da ni akan hanyata, sai dai kawai kayi haƙuri amma tafiya dole ne, bana buƙatar ƙara ganin fuskar wannan baƙar munafuka...." Ta ƙarasa maganar tana kallon Catrina.... Abeesh ya ce "ki saurare ni mana Nasreen, yaushe kika koyi taurin kai ne?..." Nasreen ta ce: "Zaman duniya koya maka ake don haka don na koyi taurin kai wannan ga donsa nayi, idan kana so na cigaba da zama da kai to sai dai a yanzu ka kori Catrina daga gidan nan, sannan ka fita hanyar ta tinda ba Auren ta zaka yi ba...." Abeesh ya ce: "Gaskiya Nasreen bazan iya koran ta ba domin ba ni na kawota gidan ba....." Jinjina kai Nasreen ta yi sannan ta furta "gaskiya ne! Amma zaka iya juran rashin ganina ko?...." Ta fizge hannunta daga riƙon da ya yi mata sannan ta nufi yanda Catrina take tsaye a gefen su tana sauraron tattaunawar da suke.... Nasreen tana iskota ta shaƙo wuyan ta da ƙarfi, tana faɗin: "Zan bar miki shi! Ki cinye shi nama ɗanye idan kina so! Shashasha! Ƙaruwar banza!"... Catrina kuwa bata ce uffan ba, sai shu’umin murmushi da take yi, kamar tana jin daɗin ruɗanin da ta jefa su a ciki. Nasreen ta juyo da ƙarfi tana jan akwatin ta tayi hanyar waje tare da faɗin: "Duk wanda ya biyo bayana, wallahi ban yafe masa ba!".... Ta fice da hanzari. Kowa ya tsaya kamar babu rai a jikin su... Catrina maganar zuci take tana faɗin: "Na fara cin nasara. Amma ba zai tsaya a nan ba... Nasreen, ba barin gidan zaki yi kawai ba — zaki bar duniyar gaba ɗaya ne ...." Cikin takaici Tasleem ta juyo tana kallon Abeesh, wanda ya zauna a kujera cikin tagumi ya rasa mai yake masa ciwo a jiki, Cikin ɗaga murya ta ce: "Shikenan. Hankalinka ya kwanta ko? Matarka ta bar maka gida saboda wata ƙazamar banzar Catrina. Wallahi ka bani kunya!"... Abeesh a firgice ya miƙe da fushi yana daka mata yatsa cikin nuna yatsa yake faɗin: "Dakata Tasleem! Kar ki kuskura ki zage ta a gabana!"... Tasleem ta ɗan zaro ido, hawaye na gangarowa ta ce: "Saboda na faɗi gaskiya? Kenam tafi Nasreen a wurin ka? tabbas abun nakan ya fara wuce gona da iri, dole akwai wani abu a ƙasa ba baka kawai aka barka ba, amma zan binciko koma menene...!" A fusace Abeesh ya nufi ɗakinsa a ruɗe, ba tare da ya furta komai ba... Catrina ma ta shige nata ɗakin ba tare da wata magana ba... Tasleem ta zauna a kan kujera, tana kuka mai zafi, tana tunanin wani irin hali ƴar uwarta zata shiga.. _____________🚗💥 Nasreen tana tuƙi cikin gudu, zuciyarta cike da takaici da ciwon zuciya tana faɗin: "Me yasa Abeesh ya zama haka? Me yasa ya canza lokaci guda kamar ba Abeesh ɗina ba? Me yasa zan zauna da mijin da bai girmama ni ba?"... Tana cikin maganar zuci Kwatsam — wani duhu ya bayyana a gaban motarta, glass ɗin gaba ya rufe da baƙin hayaki. Nasreen ta firgita tana ƙoƙarin danna birki, domin ba wani ganin hanya take ba, ga shi ba dare bane balle ace dare ne ya yi, misalin ƙarfe 8 na safe ne yanzun.... Cikin baƙin wannan duhu, Catrina ta bayyana a siffar iska, tana murmurshi cikin mugunta tare da faɗin: "Kin fice da kafafunki… amma ba zaki koma da su ba, Nasreen."... A ruɗe Nasreen ta dakatar da tuƙin ba tare da ta ga a yanda take ba, ta tsaya ne a tsakiyar road dai-dai shan kwana, kafin ta ankara Sai kwatsam — wata babbar mota (trailer) ta fito da gaggawa daga ɓangaren hagun, ta buge motar Nasreen. Motar ta dungura ƙasa cikin rami.... Haka motar take ta dungure tana hawa sama da ƙasa har ta je ta bugi wata ƙatuwar mota, kafin ƙingawar ido motar ta tashi da wuta sai da tayi sama kafin motar ta kife a ƙasi, tayoyin motar suna kallon sama a ya yin da motar take ta ci da wuta..... Daga nesa wasu suka ji ƙarar fashewar mota...... Misalin ƙarfe biyar na yamma, hasken rana yana ɗan dushewa, cikin gidan da ke cike da sirrin duhu da ruɗani, Tasleem na zaune a falo, ta dafe ƙirjinta kamar wacce zuciyarta zata fashe. Tana birgima akan carpet, tana nishi kamar wacce ke shirin mutuwa... Tana magana a cikin ranta kamar zata haɗi yi zuciyar ta cikin azaba take furta: "Wayyo zuciya ta zata fashe... wani abu ya faru... nasan wani abu ya faru da jinina... wayyo Allah naaa... Nasreen ta bar gida, amma yanzu kamar ba barin gidan kawai tayi ba, NAJI... NAJI KAMAR RANTA BAYA JIKINTA....!!" Tana cikin wannan halin sai ga Amaar ya shigo, ya dawo daga wurin aiki ne, yana sanye da uniform ɗin Sojoji, har yana shirin wuce wa idonsa ya sauƙa akan Tasleem wacce take ta birgima a ƙasin carpet.... Da gudu ya ƙara sa wurin da take yana faɗin: "Tasleem?! TASLEEM!!!" Ya durƙusa ya ɗago ta, yana riƙe da kanta da hannunsa biyu, yana kallo cikin idanunta masu cike da hawaye da tsoro Ya ce: "Lafiya kuwa?! Me ya faru?! Ki faɗa mun mana! Tasleem ki faɗa min me ke damunki!" Tasleem tana kuka cikin ƙarfin murya, tana riƙe da ƙirjinta kamar wacce zuciyarta ke konewa da wuta Ta ce: "Zuciyata... Yah Amaar zuciyata tana ƙuna... kamar da gaske... zuciyata na konewa... wani abu ya faru da Nasreen, wallahi wani abu YA FARU!!!"... Sai ga Abul ya fito daga ɗakinsa da sauri jin kukan Tasleem domin da ƙarfi take, shima cikin alhini Abeesh ya fito daga ɗakin da, sai ga Catrina da ke tsaye kamar wacce ke kallon fim. Amaar ya miƙe ya kalli kowa, sannan ya ce da Abul: "ABUL, wani abu ya faru. Tasleem ba zata faɗi haka ba idan har ba da gaske bane, Ku ƙira Nasreen a waya! Ku ƙira ta yanzu!!"... Abul ya ɗauki wayarsa da sauri, yana kiran lambar Nasreen, amma wayar bata shiga. Abeesh shima ya gwada—amma wayar a kashe. Tasleem ce ta ɗaga kai tana faɗin: "Wallahi Catrina ke da laifi! Ita tasa ta bar gidan, kuma yanzu na ji a jikina ba lafiya take ba...!" Catrina ta yi murmushi kaɗan, ba tare da ta ce uffan ba. Abul ya harzuka, yana kallon Catrina da wani irin kallo na fahimtar gaskiya. Ya san akwai ɓoye-ɓoye.... 🫀 ASMEEN...... A can cikin ɗakin alfarma, Asmeen na zaune gaban mirror tana shirya kanta cikin kyakkyawan kaya na masarrafa, tana samu farin ciki SOSAI a wurin Shaprees.... Shaprees, mai zurfin ido da juyin tunani, yana zaune a bakin gado yana kallon ta. Yana murmushi da faɗin: "Wallahi Asmeen, yau ke kika fi kowacce mace kyau. Kin fi gimbiyar aljanu kyawu. Ni ke da sa'a da aka bani ke a matsayin mata." Asmeen ta dan murmusa cikin yaƙe domin ba jin daɗin jikinta take ba, haka kawai take jin wani abu a cikin zuciyar ta na ƙoƙarin taso wa.... kafin zuciyarta ta buga da ƙarfi! Ta dafe ƙirjinta da sauri, ta jingina da mirror tana kurma ƙara tare da faɗin: "WAYYO ALLAH!!! ZUCIYATA!!!" Shaprees ya yo kanta a ruɗe, yana faɗin: "Asmeen? Lafiya kuwa?! me ke faruwa?" Asmeen cikin rawar murya take faɗin: "Shaprees, zuciyata kamar zata buga. Wani abu ya faru da jinina. Wani abu ya faru da wanda ban san meye ba...... ban san meye ba amma ina jin mutuwa... ina jin bala’i!"... Sai kuma ta fashe da kuka, tana ƙwalla da gaske. Ta durƙusa a ƙasa tana faɗin: "Dan Allah ka kaini wurin Tasleem! Ka kaini wurin Nasreen! Ina jin mutuwa! Ina jin zan rasa wani abu mafi soyuwa a cikin zuciyata...!" Shaprees ya riƙo ta shima yana jin wani abu a zuciyarsa, babu abinda ya gani da idonsa amma zuciyarsa ta motsa da fargaba. Zuciyarsa ta faɗa masa cewa: "Wani abu ya tashi daga cikin duhu. Wani abu ya motsa da yuwuwar halaka..." Shapreen kallon Asmeen ya yi tare da faɗin: "Subhanallahi ki kwantar da hankalin ki babu abinda ya faru,...." Haka yake ta faman rarrashin ta... Amma furrrr Asmeen ta kasa kwantar da hankalin ta domin yanda zuciyarta yake bugawa in bata ga ɗaya daga cikin ƴan uwanta ba za'a iya samun matsala... Shapreen ne ya ɗago ta tare da faɗin: "Kin ga tashi mu tafi part ɗin su yanzu, zaki ga babu abinda ya faru da su..." Dasauri Asmeen ta miƙe ta yi gaba da gudu zata fice..... ★★★★★★ Falon gidan ya kasance cikin shiru sai numfashin da ke fita da ƙarfi ta ɓangaren Tasleem da hawayenta dake bin saman kuncin ta. Kanta na kwance akan cinyar Amaar, wanda ke goge mata gumi da hawaye, shima ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba. Tasleem har yanzu tana dafe da ƙirjinta, numfashinta na fita da ƙyar, tana furta cikin raunin murya: “Zuciyata… wayyo Allah, zuciyata tana ƙuna… Wani abu ya faru da jinina, na rantse da Allah…” Abul da Abeesh suna zaune a kujerun falon suna kallon ta cikin ruɗani da damuwa. Kowa na kallon ɗan uwansa, amma babu wanda ke da amsa, domin har yanzu babu wanda ya san takamaiman abinda ya faru da Nasreen. Sai dai kowa na jin akwai wani abu marar daɗi yana shirin bayyana. A daidai lokacin — suka ji 🚪 ƘARAR BUƊAR ƘOFA... Asmeen ce ta shigo cikin falo da gudu, zufa na keto mata a fuska, idonta cike da hawaye, zuciyarta har yanzu na bugawa kamar wata ƙarar ƙaho. Kafin kowa ya ce wani abu, idanunta sun sauƙa kan Tasleem — kwance, kamar wacce za ta gama da duniya. A ruɗe ta furta: "TASLEEM!!" Da sauri Asmeen ta faɗi ƙasa, ta rungume Tasleem tana kuka kamar ƙaramar yarinya, tana faɗin: "Na gode Allah, na gode Allah babu abinda ya same ki!! Zuciyata bugawa take kamar zata tsage! Tasleem…ina Nasreen?! Ina 'yar uwar mu?!" Tasleem ta janyo Asmeen cikin ƙarfi, suka rungume juna suna kuka kamar 'yan uwan da bala’i ya raba, amma zuciyarsu ta haɗu. Amaar ya ƙura musu ido, yana girgiza kai cikin tausayawa da ruɗani. Abul ya sauƙe ajiyar zuciya cikin damuwa, Abeesh ya lumshe idanu yana jin wani nauyi a kirjinsa da bai iya bayyana wa ba..... Sai ga Shaprees shima ya shigo falon da sallama a bakin sa yana kallon halin da ake ciki. Ya durƙusa yana kallon Tasleem da Asmeen, ya ce a hankali: “Me ya faru? Ku gaya min... wani ya mutu ne? Wani abu ne ya faru da wani a cikin gidan nan..?” Tasleem girgiza kai tayi tana faɗin: “Wallahi bamu san me ya faru ba. Amma zuciyarmu na sanar da mu cewa wani abu mai muni ne ya faru. Muna jin hakan a jikimmu kamar jininmu muka rasa...…” Shapreen ya ce "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allah Ubangiji ya rufa asiri, Insha Allahu babu abinda ya faru...." ★★★★★★ 🕯️ A can cikin ɗakin ta Catrina na tsaye a gaban madubi tana murmushi. Ta cire doguwar rigarta ga ajiye a gefe ta zauna daga ita sai breziyya da gajeran wando tana kallon kantacikin muguwar shauƙi. Idonta ya canza launi, yana dishewa da duhu kamar wanda ya taɓa wutar ruhi A sassanyar murya ta furta: “Sai dai ba ku san wani abu ba... a koda yaushe Ni ce mai nasara... da zarar labari ya iso gare ku cewa motar Nasreen ta kama da wuta...” Ta lumshe idanu ta ɗauki kwalbar turare ta zuba a hannunta sannan ta shafa a wuyanta tana faɗin: “Abeesh ya zama nawa, da rai ko da mutuwa... Kuma babu wani daga cikinku da zai iya hanani.”.... 🫀 Asmeen ta ɗago kanta daga kan kafadar Tasleem, tana kallon su Amaar da Shaprees, murya na rawa ta ce: “Shaprees, ba wai bana sonka ba, amma gaskiyar magana shine bazan iya koma wa yankin ka ba in har Nasreen bata dawo gare mu ba, Ku tashi, mu fita neman ta! Bazan iya zama haka ba tare da sanin yanda take ba.....!” Tasleem ta dafa kafaɗarta, tana hawaye ta ce: “Nima na yarda... mu tashi mu fita nema. Idan Nasreen tana raye zamu same ta Idan kuma... idan kuma ba ta raye! toh na rantse da Allah... zan bi ta duk yanda ta je.....” Su kaɗai suke ta surutan su cikin tashin hankali... Suna cikin wannan halin sai wayar Amaar ya fara ringing.... An ƙiran wayan Amaar ne dake Soja ne ake sanar masa cewa anyi hatsarin mota, mota ta kama da wuta. A ruɗe Amaar ya miƙe tsaye yana faɗin "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..." Duk miƙewa suka yi suna tambayar sa meya faru.. Tasleem da Asmeen kuwa rungumar juna suka yi suna kuka jin Amaar ya yi wannan addu'ar, Amaar ya ce "Anyi hatsarin mota zan je na dubo yanzu domin ba'a sanar mun motar waye ba..." Abeesh da Shapreen miƙe wa suka yi zasu tafi tare,. Tasleem ta ce: zata bisu, Amaar ya ce mata ta zauna a gida suma zasu je ne su tabbatar,. Itama Asmeen cewa tayi Nima zanje, Shapreen ya ce "Insha Allahu ba Nasreen bace..." Abeesh cikin tashin hankali da damuwa ya darara musu tsawa yana faɗin: "Wai meyasa kuke ja mata bala'i ne? Babu abinda ya faru da ita, matata tana nan da ranta, sharrin zuciya ne ke damun ku.... kuma zan nemo ta a duk inda ta shiga na rantse, kada ku sake ja mata mutuwa....." Tasleem kuka take sosai tana faɗin "Wallahi saina je, hankali na bazai taɓa kwanciya ba in Banga wanda yayi hatsarin ba...." Daƙer Abul ya rarrashe su suka zauna a gida, hankalin su a tashe..... Amaar, Shapreen da Abeesh sun fito da sauri daga gidan, motar Amaar duk suka shiga gaba ɗaya... Shuru ya mamaye falon bayan sun bar gidan. Sai kukan Asmeen da Tasleem ne kawai ke karaɗe falon, suna rungume da juna, zuciyarsu na tafasa da fargaba... Abul yana zaune a kujerar gefen falo, hannu a bisa habarsa yana tunanin abinda yake faruwa. Ko shi kansa bai da tabbacin halin da Nasreen take ciki. Tasleem ta ɗaga kai tana kallon shi da hawaye, ta ce cikin karayar zuciyar: "Abul... zuciyata na wani irin bugawa kamar an yayyafa mata wuta... meyasa nake jin kamar mun rasa Nasreen?" Abul ya ce cikin wata irin murya da ta cika da damuwa: "Ki zamo mai tawakkali Tasleem... dukkan abinda zai faru yana cikin rubutun Ubangiji. Amma in Allah ya yarda, ba Nasreen bace." Asmeen cikin kuka da ruɗani ta ce: "Allah ya sa...." A can gefe kuwa, Catrina ce ta leƙo daga ɗakin ta cikin sirri, ta dube su da idanu masu cike da mugunta da ƙeta. Sai murmushi ta ke ta saki, tana furta cikin zuciyarta: “Nasreen, kin bar kofar zuciyar Abeesh a buɗe... yanzu zan cika burina, ko da kuwa da wutar lahira ce..…” Sai ta koma ɗakin nata, tana tunanin yadda zata tabbatar da cewa wannan tashin hankali zai ƙara ruɗa su gaba ɗaya — domin ta ƙudiri aniyar mallakar zuciyar Abeesh da cikakken ikon gidan. Tasleem da Asmeen addu'a kawai suke suna fatan Allah yasa ba Nasreen ɗin su za'a tarar ba... Ba su dena kuka ba. Suna jiran kiran waya ko dawowar su Amaar da labarin meye gaskiya akan wanda yayi hatsari. Sai Asmeen ta riƙe hannun Tasleem tana faɗin: “Ko me za a faɗa mana... zamu fuskanta tare. Nasreen ƴar uwar mu ce wanda muke da alaka ta jini, da rai, da ruhi.....” Tasleem ta share hawayenta sannan ta ce cikin ɗaga murya: "Idan da gaske ne wannan hatsarin... Wallahi sai na bin ciko ta yanda akayi wannan hatsarin ya wakana, in har Allah ne ya aiko bisa tsautsayi, to tabbas wacce tayi sanadiyar barin ta gidan wallahi saita gane kuran ta....." *NEXT NEXT NEXT.....* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 49 to 50 TASHIN HANKALI A WURIN HATSARI Wurin hatsarin ya cika da tarin jama’a da ‘yan sanda. Ana kulle hanya. Ana nuna babbar motar trailer ɗin da ta durkusar da wata mota rami, sai hayaki da ƙauri ke tashi. Amaar ganin motar yasa ya buga birki da ƙarfi yana faɗin: “Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, na san wannan motar! Motar Nasreen ce!” Kafin kowa ya yi wani yunkuri, Abeesh ya fice daga cikin motar da gudu, yana ƙwala kira: “Nasreeeeeen!! Dan Allah karki ce kin mutu! Nasreen!!” Idanunsa suka sauƙa akan ragowar motar da ta kife a jikin bishiya gaba ɗaya ta ƙone, sai wasu guntayen rigar Nasreen da aka hango kusa da ƙofar motar, sun ƙone rabin su. Cikin dukan zuciya, Abeesh ya yanki jiki ya faɗi a ƙasa sumamme! “Abeesh!!” Amaar ne ya faɗa da karfi tare da ruga da gudu kansa. Ya ɗago kan dan uwansa yana girgiza shi cikin hawaye, “Abeesh ka tashi! Ka tashi! Allah ya kiyaye Nasreen tana raye...!” Shapreen yana tsaye cikin firgici yana ambaton addu'o’i. Cikin damuwa ya matso kusa, yana girgiza kai, ya ce: “Wannan ba hatsari bane kawai… akwai aljani cikin wannan lamarin.” Ƴan sanda da ma’aikatan agajin gaggawa sun zo da gaggawa suka fara aikin ceto. Aka dauke Abeesh cikin mota domin ya suma sosai, yayin da wasu suka ce: “Ba mu ga jikin mutumin ciki ba… akwai yiwuwar ta ƙone kurmus.” Amaar hawa motarsa ya yi cikin ruɗani domin komawa gida, domin shima zai iya faɗuwa idan ya cigaba da tsayuwa a wurin, shi kuwa Shaprees tare suka kai Abeesh hospital, Amaar a cikin zuciyarsa yana cewa: “Yanzu taya zan sanar wa Tasleem da Asmeen?Wannan al’amarin ya fi ƙarfin mutum...” --- A BANGAREN GIDA Tasleem ta ji wani irin raɗa a zuciyarta, kwatsam ta miƙe daga ƙasa, ta fashe da kuka mai ƙarfi tare da faɗin “Wayyo Allah! Wani abu ya faru da Nasreen! Na rantse da Allah na ji a jiki na! Wani abu ya faru!” Asmeen ta riƙo hannunta tana girgiza kai cikin hawaye ta ce “Bazan yarda ba… har sai na ga jikin ta da idona…” --- A ƊAKIN CATRINA Catrina na zaune a gaban madubi tana kallon ruwan hoda mai motsi da ke nuna tasirin hatsarin. Ta saki wani shu’umin murmushi tana faɗin: “Wannan itace rana ta farko. Na raba Nasreen da Abeesh, yanzu sai na mallake shi har da zuciyar sa gaba ɗaya…” Amaar ne ya shigo gidan cikin fushi, idanuwansa sun ƙumbura da hawaye, Bayan shigar sa tsayawa ya yi a tsakiyar falo yana kallon su Tasleem da Asmeen waɗanda suke zaune suna kuka, zuciyarsu cike da firgici da damuwa. Tasleem ganin Amaar yasa ta miƙe da sauri ta nufe shi tana faɗin “Ya Amaar, me ya faru?! Ka ganta?! Nasreen tana lafiya?!” Asmeen ma ta miƙe ta zo da sauri, ta ce: “Dan Allah ka faɗa mana gaskiya, kar ka ɓoye komai…” Amaar bai ce uffan ba. Sai da ya shafe sumar kansa, ya ɗan ja numfashi sannan ya girgiza kai cikin raunanniayar murya ya ce “Motar ta ce ta fāɗa rami… motar ta ƙone…” Asmeen da Tasleem suka dafe ƙirji a tare suka kurma ihu suna faɗin > “Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un!!” Asmeen durƙusawa ƙasa tayi ta kama kai tana kururuwar kuka, Tasleem kuwa ta dafe bango tana jijjiga kai cikin tsananin firgici da hajijiyan da yake shirin kayar da ita tana faɗin “Kana so kace ta mutu?!” Tasleem ta tambaya da rawar murya. Amaar ya ce: “Ba mu ga gangar jikin ta ba... amma... motar ta ƙone sosai. Abeesh shima ya suma a wurin. An garzaya da shi asibiti.” Cikin kankanin lokaci Abul ya fito daga ɗaki, yana jin hayaniya. Ya tsaya a bakin falo yana kallon kowa cikin tsananin mamaki da damuwa ya ce: “Meye wannan ihun? Me ya faru da Nasreen?” Amaar ya je ya durƙusa gaban mahaifinsu: “Abul… wata babbar mota ce ta bugi motar Nasreen, ta kife tare da ƙone wa. Ba mu ga jikinta ba. Amma…” Abul ya ɗaga hannunsa sama yana faɗin: “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Nasreen…?” Zuciyar Abul ne ta shiga bugu da ƙarfi. Ya jingina da bango yana huci. Kowa ya ruɗe. Ana kuka. Sai kwatsam Catrina ta fito daga ɗakinta da lumsassun idanu, a fuska kamar bata san me ake ciki ba. Ta tsaya a ƙofar falo tana kallon su gaba ɗaya ta ce: “Lafiya? Me ake kuka akai?” Tasleem ta juyo cikin fushi mai cike da hawayen bakin ciki ta ce: “Lafiya?! Ke! Kin yi nasara! Kin raba mu da Nasreen ko?! Ashe burinki kenan, to burin nakin ya cika?!” Catrina ta ɗan zaro ido, ta soma wani murmushin ƙarfin hali ta ce: “Ni kuma? Me nayi?” Asmeen ta nufo ta cikin tsananin fushi, ta nuna mata yatsa tana faɗin: “Karki ɗauke mu mahaukata kamar ki. Mun san ke kika jawo wannan! Wani abu ke faruwa kuma ke kika haddasa shi, inda baki shiga tsakanin masoya ba da duk hakan bata faru ba, ta silar ki ƴar uwata ta kai kanta ga hallaka....!” Catrina ta kalle su duka, sai ta juyo ta dubi Abul da Amaar, ta ce: “Wannan wautar ya isa haka. Kuna kuka ne akan wata wacce ta yanke shawarar barin mijinta ba tare da jin shawara ba?” Amaar ya ɗan matso kusa da ita, cikin murya mai sanyi da kuma ƙarfi yana cewa: “Catrina… ya isa haka. Kin daɗe kina wasa da zuciyoyin mutane. Kinyi abubuwan da suka gaza fassara. Idan har akwai adalci a doron ƙasa, to Allah zai tona miki asiri.” Catrina shiru tayi idonta ya fara sauya launi na ɗan lokaci – launin shuɗi mai duhu – amma sai ta yi saurin lumshe da idon... Sai kwatsam Abul ya dafa bango, yana faɗin: “Zan faɗa muku gaskiya… Wacece Catrina… kuma me take shiryawa...” Kowa ya juyo ya zuba masa ido. Tasleem ta ce: “Abul ka ce gaskiya... Ka san wani abu game da ita?” Abul yayi shiru na dan lokaci, yana kallon Catrina, lokaci guda ya dafe ƙirjinsa... sai kawai ya faɗi ƙasa sumamme.....! Labarai na yamma da dare suka cika kafafen yaɗa labarai: "Muna cikin jimamin rasa wata matashiya mai suna Nasreen wadda mota ta buge ta a kusa da hanyar Sabon Gari. Motarta ta kama da wuta, an samu kuntayen kayanta da wasu takardu masu nuna sunanta. amma sai dai mun rasa gawar ta, muna tunanin ta ƙone ƙurmus cikin gobarar..." Idon duniya na kan hatsarin. Amma ba kowa ya san gaskiyar abin da ya faru ... Amaar na ƙoƙarin ɗaga mahaifinsu Abul bayan ya faɗi a kasa. Shi kaɗai ke da nutsuwa amma zuciyarsa cike take da firgici. Tasleem da Asmeen suna kuka sosai har sai da suka ji muryar labarai na dukan dodon kunnen su.. Idon Asmeen ya sauka a kan television, ta soma kallon motar da suka nuna ta ƙone amma ba gaba ɗaya ba Sai kayan cikin mota da aka nuna, rigar Nasreen da wani ɗan hijabin ta... Asmeen ta furta: "Innalillahi!!! Wayyooo ALLAAAAH!!!" Tayi wani irin ihu mai taɓa zuciyar wanda ke raye, ta faɗi ƙasa sumammiya—numfashinta ya narke, jikinta yayi sanyi. Amaar ya ruɗe gaba ɗaya. Ga kuma Tasleem ta fara riƙe kanta tana fadin: “Ina jin haske… Amma cikin duhu… zuciyata zata fashe…” Sumar kanta ne ya fara canza launi. Daga baƙi zuwa fari mai kyalli kamar zaren azurfa. Idanunta suka koma fari sol kamar ba su da jijiya. Tana surutu da wata murya mai sanyi ta cigaba da faɗin: "A gaban zuciyar rana ta tashi. Haske ya motsa. Na yarda da hasken gaskiya. Amma duhu yana kusa… Catrina ce duhun!" Amaar da ya lura da lamarin Tasleem ya tsorata. ɗagata ya yi cikin sauri, ya nufi ɗakinta ya kwantar da ita, ya kulle kofa da key. Catrina wacce tin yaɗuwar Abul ta koma cikin ɗakin ta, tana zauna a gefen madubi tana kallon kanta. Sai tayi murmushi mai cike da mugunta. “Nasreen… yanzu dai kin ɓace. Wannan dukan tsarabar ta haske ta fara raguwa. Amaar, Asmeen… Tasleem… sai dai kuyi ta kuka, amma ba zaku iya hana ni mallakar komai ba.” Sai ta ɗauko wata ƙaramar ƙwarya mai tagulla daga ƙasan gadonta. Ta buɗe. A ciki akwai ƙasan zuciyar maciji da gashin mutum—duk sune al’adun mugunta da take amfani da su. kallon hoton Abeesh tayi sannan tayi ƙasa da murya tana faɗin: “Zan shige zuciyar ka gaba ɗaya. Zaka zama nawa. Sai dai fa… Nasreen ba zata dawo ba. Kuma idan ta dawo...” Sai tayi murmushi: “...zan karɓe ranta da hannuna.”..... Amaar bayan ya kai Abul da Asmeen asibiti sai da ya dubo Abeesh shima ba'a hayyacin sa yake ba, ya juma a asibitin kafin ya tuna da Tasleem a kulle a ɗakin, A gurguje ya fito daga cikin hospital ya shige motar sa, lokacin misalin ƙarfe 8 da rabi ne.. Bayan komawar sa gida. Ya shigo gidan da takun sa mai nutsuwa, ya nufi ɗakin da ya ajiye ta cikin tsanani. A hankali ya buɗe ƙofar Tasleem tana zaune gefen gado, sumar kanta har yanzu na ɗauke da wani launin fari mai kyalli. Amma idanunta cike da hawaye. Runtse su tayi kamar tana kokarin toshe wasu wahayi masu raɗaɗi daga cikin zuciyarta. Amaar yana ganin haka – ya ƙaraso ba tare da faɗin komai ba, ya zauna kusa da ita, ya rungume ta cikin So da ƙauna... Tasleem ta fashe da kuka a kirjinsa, tana faɗi cikin rawar murya: "Na gano duk wata gaskiya Yah Amaar… Na tafka babban kuskure. Ni ce Sarauniyar Haske – amma na kasa ceton Abeesh daga hannun duhu... na kasa ceton Nasreen daga hallakar mugunta... Littafin Hasken Ruhi na ya buɗe kansa a daren nan... Gaskiya ta bayyana!" Amaar ya yi shiru, yana shafa bayanta, zuciyarsa na bugawa da dukan sirri da tsoron abin da zai ji daga gareta. Tasleem ta cigaba da cewa: “Na ga cikin wahayi… Catrina ba mutum bace, Ita ce Sarauniyar Duhu. Wacce aka haifa daga duhun dare, aka renata da ƙiyayya, aka koya mata hanya guda na hallaka haske… Ita ce Kuliya wacce Littafin Ruhi ya ambata tana ɓoye a cikin mutane, tana cikin gidan nan tana shan ƙaunar da ba nata bace…” Sai ta dafe kirji tana faɗi da murya mai tsuma zuciya: “Na kasa hango komai game da Nasreen, Kuma Catrina... ita ce ta shirya komai akan ɓatan Nasreen....!” Amaar ya ɗago fuskarta, yana kallonta da idanu masu cike da tausayin gaskiyarta. Ya ce: “Ki saurara Tasleem… Babu wani kuskure da haske ya tafka idan yana cikin gaskiya. Abinda ke faruwa yanzu shine lokacin da ya dace mu gano gaskiya ba bamu yi tunanin haka ba, zamu tinkare ta ba wai muji tsoron ta ba, Littafin Hasken Ruhi ya buɗu? To yanzu lokaci ya yi da zamu buɗe shafi na gaskiya.” Tasleem ta kalle shi da hawaye a idonta tana murmushi mai ɗauke da rauni ta ce: “Zan tashi, Yah Amaar… Zan kareku. Amma sai mun fuskanci gaskiya – Catrina dole ne ta ɓuya domin ta ci nasara. Amma yanzu… ni ce haske da ba ya ɓuya.” ƁANGAREN MADAM NABLAH .... A daidai lokacin da duniya ke kuka da mutuwar Nasreen, wasu suna kwance a asibiti suna yaƙi da rai, wasu suna juyayin kuskuren su, Madam Nablah tana zaune a cikin wani daƙin duhu wanda ba'a duniya take ba, tana can duniyar Aljanu, Wuri ne dake da tsakanin haske da inuwa, inda ruhinta ke da cikakken iko. Madubinta mai sarrafa gaskiyar abubuwa yana a gabanta – tana kallo, tana jin komai, tana ƙare wa komai kallo kamar sarauniyar da ba ta iya barin masarautarta amma ta san duk abinda ke wakana. Madam Nablah tana zaune cikin wata kujera mai baƙar fata da ƙyalli, tana kallon madubin yayin da hoton hatsarin Nasreen ya bayyana. Lokacin kafin mutanen duniya su Ankara Madam Nablah ta miƙa hannunta cikin madubi ta zaro ruhinta daga jikinta – ruhin da ke cike da iko da saurin walƙiya. A cikin sa’a ɗaya, ta bayyana a cikin hatsarin, ta tsayar da lokaci – ta tsamo Nasreen cikin wuta, ta ɗauke ta da hanunta mai cike da sirrin sihiri, ta ɗauke ta cikin hayakin da ba ya barin alama, ta ɓace da ita daga idon duniya. Nasreen yanzu tana kwance a cikin wani ɗaki mai tsarki da sirri. Furen duwatsu ne a jikin bango, kyandirori masu ƙyalli suna haskaka ko ina, iska mai daɗi tana kadawa daga sama. Bata farfaɗo ba – har yanzu cikin sumarta take – amma hankali da lafiya na jikinta na dawowa sannu a hankali. Madam Nablah tana zaune a ƙasan gadon tana shafa gashinta, tana zuba mata ruwa mai ƙyalli daga kwaryar zinariya. Duk da azancin halinta da muguntar zuciyarta ƙaunar ƴarta tana da nauyi da ƙarfi. Ta furta: "Na san zaki yi zargin wani abu akaina idan kika farka... Amma bazan bari ki mutu ba, Nasreen... Ni na haife ki, kuma ke ɗiyata ce. Duniya zata ɗauka kin mutu. Amma ni – ba zan rasa ki ba." Madam Nablah ta ajiye ƙwaryar ruwa, ta ɗauko ƙaramar ƙwalba mai ruwan zinariya ta zuba akan leɓen Nasreen. Ta lumshe idonta tana karanta wani sirrin zikirin duhu da haske. "Wannan ba ceto bane kawai... Wannan shine tabbatarwa cewa har yanzu ni ce uwa... Kuma har yanzu ke ce haske na... duk da ni duhu ce." Idonta a lumshe take furta hakan... Kowa ya saddaƙar Nasreen ta mutu duk duniya har da su Tasleem da Amaar domin akwai yanda Hasken Tasleem bazai iya hasko mata wani wuri ba, misalin wurin da Madam Nablah ta ajiye Nasreen, ba'a duniya ba, a duniyar Aljanu take... Madam Nablah tana kula da ita a ɓoye cikin so da ƙauna, Bata fatan ƴarta ta zama duhu kamar ita, kuma zata cigaba da riƙe Nasreen ba tare da kowa ya sani ba... Madam Nablah ce ta bayyana a ɗakin Catrina ba tare da mutanen gidan sun san ta dawo ba, Catrina ta miƙe daga kujera da sauri, idonta cike da firgici ta ce: "Devil Mom?!" ta furta a firgice. "Ya kika dawo ta hanyar nan?! Wannan ɓangare ne na sirri..." Madam Nablah, cikin sautin murya mai ƙarfi da iko, ta taka zuwa gareta ba tare da kallo sakin fuska ba ta ce: "Ba dawowa nayi ba, Catrina," ta furta da ƙarfi. "Na zo domin KE! Kuma bazan yarda ki ci amana ba."... Catrina ta matsa baya kafin ta iya ƙara ko kalma, Madam Nablah ta miƙar da hannunta guda ta shaƙo wuyanta, ta ɗagata da hannunta daya kamar ƙaramar ƴar tsana. Catrina tana juyi, tana fizgewa, tana ƙoƙarin kiran wata ƙarfi, amma babu wani sihiri da yake aiki a gaban uwargida Madam Nablah. Madam Nablah ta ce: "Kin manta jinin da ke jikinta shine jini na! Kin manta ita ɗiyata ce, Nasreen ce Haskena! Me yasa kike ƙoƙarin halaka ta?!" Murya na girgiza ɗakin tsabar ƙarfin muryar tsafi... Catrina tana harba ƙafarta, hawaye na zubowa na tsoro da fargaba. Domin tasan Madam Nablah tana cikin fushi... kuma idan fushin ta ya kai iyaka, babu wanda ke iya tsira mutum ko Aljan.... Madam Nablah ta cigaba da faɗin: "Na san komai. Na san wahalar da kike bawa zuciyar Abeesh, kika ƙazantar da rayuwarsa, kika saka zuciyar Nasreen cikin ruɗani. Amma ki sani... Na zuba miki ido ne, duk wanda ya taɓa Nasreen zai fuskance ni ba a matsayin uwa ba a matsayin sarauniyar wuta...!" Madam Nablah ta jefar da Catrina da ƙarfi—ta bugu da jikin bango sannan ta gangaro ƙasa tana tari. Jikinta yana karkarwa. "Wannan shine gargaɗi na," Madam Nablah ta ce yayin da fuskarta ta ɗauki duhun walƙiya. "Ki kula sosai Catrina. Wannan gidan ba naki bane. kina ƙarƙashina ne amma kada ki jarabce n da barin ƴata ta mutu, domin idan ta mutu zaki fuskanci fushi na, Idan kika ƙara yunkurin taɓa ko ɗaya daga jinin jikina ba zan ƙara gargadi ba—sai hallaka." A take, Madam Nablah ta ɓace cikin duhu, kamar ba ta zo ba.... Catrina tana tsaye a gaban madubi cikin fushi take faɗin " Ina so Nasreen ta bar duniya amma kin je kin ceceta, to kuwa yanzu wasan zai fara, bazan taɓa yin sanyi ba, Abeesh nawa ne ni kaɗai, zan iya kashe kowa akan sa, soyayyar sa tayi zurfi... Madam Nablah sanin halin Catrina batada hakuri yasa tabi iska taje har asibiti ba tare da kowa ya sani ba, taje ta ɗauki Abeesh ta ɓace dashi, ta ajiye shi a cikin wani baƙin daji, shi kuwa Abeesh baya cikin hayyacin sa, har yanzu bai farfaɗo ba... Bayan kwana ɗaya an sanar cewa Abeesh baya asibiti, an je an dudduba shi baya nan, ko ina an duba baya nan.. Washegari Kowa yana asibiti iya Catrina ce kawai a gida.... Catrina na zaune da ƙafafunta a sakale, tana latsar farcen hannunta, fuskarta na ɗauke da wata irin nishaɗi da bakin ciki wanda sai mai duhu zai iya fahimta. Jin motsi a ƙofar falo bai firgitata ba, sai murmushinta ne ya zurfafa, domin tasan wacece ke shigowa. Tasleem ce ta shigo kamar wuta. Idonta cike da haske, fuskarta ɗauke da tsananin ɓacin rai da ɗokin jin amsar da take buƙata. Bata tsaya kallo ko magana ba, ta je kai tsaye ta ɗagota daga inda take zaune tare da zabga mata mari har sau biyu waɗanda suka sa numfashin Catrina tsayawa na ɗan lokaci. A fizge ta ce: "Ke kinada hankali kuwa? Mena miki kika shigo da wannan fushin kamar wacce aka tsige mata sarauta?" Catrina ta faɗa tana kallon Tasleem da idanuwanta masu ƙyalli da duhu. Tasleem ta ce "Bayan laifukan da kika yi shine zaki tambaya me kika yi? Kar ki mayar ni yarinya mana, duk shirin ki na sani, tin farkon zuwanki gidan nan, idonki kawai na kalla na gane cewa ke ba mutum bace..." Catrina tayi dariya ta ce: "aww kin gane Ni tin da shine kike wahalar da Shari'a? Eh ni sarauniyar duhu ce wacce zata tarwatsa Miki mafarki..." Tasleem ta ce "Kin gama tarwatsa ni ai tunda kika kashe mana ƴar uwar mu Nasreen akan mijinta na halak, sannan Abul yana so ya faɗi gaskiya akan ki, shine kika buge masa zuciya da mashin idonki, sannan yanzu kin ɗauke Abeesh daga asibiti, shin ina kika kaishi?..." Catrina tayi dariya ta ce "Gaskiya amma hasken ki baya baki gaskiya Indai zakiyi tunanin ni na ɗauke Abeesh, meyasa zan ɗauke shi?..." Tasleem ta ce "Saboda ƙudurin ki mana, ki fito mun da Abeesh yanzun nan kafin na tarwatsaki..." Catrina ta ce "Bani na ɗauke Abeesh ba, ban san ina yaje ba" Tasleem ta ce "ƙarya kike kinsan yanda yake munafukar banza..." Catrina ta juyar da kanta tana dariya, murmushi mai duhu yana bayyana a fuskarta. Idonta ya fara canzawa zuwa baƙi ƙirin ba ɗigon fari. Tana furta kalma mai cike da ƙiyayya: "Hasken ki bai baki gaskiya ba, Sarauniyar Haske. Na ce miki ba ni na ɗauke shi ba... Ko kuwa kina shirin ganin fushina Ni Catrina Sarauniyar Duhu ne?" Tasleem ta runtse idonta, jikinta ya haskaka gaba ɗaya. Sai ga idonta ma ya koma fari mai kyalli, kafafunta na ɗagawa da ƙarfi kamar bata taɓa taka ƙasa ba. Hasken dake jikinta ya fara zagaya falon—yana ƙona komai da bai dace ba tana faɗin: "Ƙarya kike Catrina, zuciyata ta gane ki tun tuni! Kin ɗauke shi. Ko da ba ke ba ce, kin san inda yake. Kuma yanzu ba batun faɗa bane—zaki fuskanci fushin da baki taɓa tsammani ba!" Catrina tayi tsalle gefe tana mai dariyar hauka. Tana faɗin: "Na gaya miki amma kin ƙi yadda to bawai tsoron ki nake ba, kuma ma babu wani laifin da na aikata a gidan nan, kuma in da kin gane ko ni wacece da farko nasan da zaki ɗauki hukunci duk da nasan babu abinda zaki yi mun... Tasleem ta matso gaba, numfashinta yana fita da karfi. Har yanzu hannunta na rawa Idonta ya kaɗa da wani irin zurfin haske da ba'a saba gani ba ta ce "Laifinki ya zarce sa'a Catrina. Ke kika haifar mana da bala’i. Ke kika hallaka rayuwar ‘yar uwar mu. Akan miji da ba naki bane. Na fahimceki tun da farko, amma ban taɓa cewa komai ba." Catrina ta yi dariyar tana faɗin: "Aw... kin gane ni daga farko? ke ce zaki iya dakatar dani? Ke da haskenki da bai iya ceton Nasreen ba? Ke da haskenki da bai hana Abul fadawa ruɗu ba? Kin san meye duhu? Ni ce duhu. Kuma ni ce zan rushe ku gaba ɗaya..." Tasleem ta tsaya, ta ƙanƙame tafukan hannayenta, haske ya fara taruwa a cikinsu. Idonta ya koma fari kamar ƙarfen wuta. Sai furta da ƙarfi ta ce: "Kin gurɓatar da jinin mu, kin cin amanar gidanmu, kin ɗauke mana Abeesh, kuma yanzu zaki zarge ni da rashin iya ceto? Duhu ba zai taba wuce haske ba... kuma yau... na zo daukar hakkina!" Catrina ta zaro ido. Idonta ya sauya gaba ɗaya. Ya koma baƙi ƙirin kamar akwatin tsafi mai cike da ƙiyayya. Tana nufar Tasleem tana furta wani yare wanda ba wanda zai fahimta sai ƴan duhu ke amfani da shi.... Falon ya cika da wata iska mai nauyi, tagogi suka fara kaɗawa, fitilu suka fara tarwatse wa, ƙamshi mai ƙayatarwa na fitowa daga hasken Tasleem, yayin da wani ƙamshin ƙwari da dauɗa ke fita daga Catrina. Sai kawai wata irin walƙiya ta sauka tsakanin su, kafin su kai juna hari. Lokaci guda suka ɓace gaba ɗayan su... A wani wuri suka sauƙa a cikin wata sahara da ba kowa, ba bishiya, ba tsuntsu. Wani tsarki na musamman ya rufe wurin – saharar tsakar tsafi wanda sai masu ƙarfin iko ne suke iya bayyana a wurin, wurin dandalin matsafa... Suna sauƙa Catrina ta saki wata ƙara da sai aljanu ne ke iya fassara wa, Duk jikinta ya sauya. Idonta ya koma baƙaƙe, fuskarta ta koma kamar garwashi, cinyoyinta suka lankwashe kamar mahaukaciyar ƙuliya. Ta rufo kan Tasleem da mahaukaciyar gudu tayi sufa cikin muryar ƙuliya ta yakushi fuskar Tasleem kamar zata.... Tasleem itama tɗaga hannunta tayi sama cikin nutsuwa, walƙiya ta tashi daga cikin tafin hannunta kamar gungumen wuta, ana ƙiran abun da Thunder, cikin fushi Tasleem take faɗin: “Ina da haƙuri, amma ban zama mai shiru akan abun cutarwa ba... Ina da zuciyar da tafi yarda da gaskiya, kuma ke – duhu – kece tsautsayin da ya hana ni kwana da zaman lafiya... Yau zan fanshe rayuwar da kika ɓata!” Thunder! Sai da haske ya sauƙa akan sa! Sannan ta buga Thunder akan Catrina, sai da ta nitse cikin ƙasa sannan ta fito daga cikin ƙasa da siffar babbar kuliya – baƙa kamar gabar dare! Catrina ta ce: "Kin manta ni ce nake kare duhu?!" Catrina cikin murya mai ɗauke da ƙara ta kuma furta "Ni bana jin kunya, sannan bana kara kuma bani da tsoro....!" Tasleem ta fasa dariya – dariyar girmamawa ga ikonta. Tana matso gaba, fuskarta ta koma haske, gashinta yana shawagi kamar zinariya a cikin ruwa, tana rufe da idonta tana miƙa hannu sama... Wani abu kamar lu’ulu’un rana ya bayyana a cikinta. Daga cikin wannan hasken, sauti mai zurfi ya fito daga zuciyarta – kalmomin da suka girgiza saharar da babu kowa. "Ina barin ƙauna idan na samu dama, Ina barin gafara idan zuciyata bata cika ba, Amma yau, bazan bar zafin zuciyar da kika haifar ba. Soyayya ba sakacina bace, amma rashin adalci ke neman tara kaina. Duhu! Ba za ki ci nasara ba!" Catrina ta tashi sama da kafa huɗu, tana mirgina da zafi, tana fitar da hayaki daga cikin kunnuwanta da bakinta. Sannan ta harba wani jini mai zafi daga cikinta wanda ya zo kamar mashi ya nufi Tasleem – Tasleem ta kafa ƙafarta ƙasa sai wata garkuwa ta bayyana daga haske ta kare ta..... A duk lokacin da Catrina ta fitar da duhu, Tasleem tana fitar da adalci da ƙarfi. Suna cikin faɗan Catrina ta kifa kanta a ƙasa ta fashe da ihu sakamakon wani haske da ya bugeta wanda baza ta iya jurewa ba. Duk wata ƙarya da ta gina a zuciyarta tana narkewa..... 😳😳😳😳😳😳😳😳 MA SHA ALLAH! ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFI NA ƊAYA, SAI MUN HAƊU A LITTAFI NA BIYU WANDA YA KASANCE NA KUƊI A FARASHI MAI SAUƘI NAIRA 300 KACAL👌👌 A CIKIN LITTAFI NA BIYU ZAN BAKU PAGE 1 TO 10 KYAUTA, NA MURNAR BIKINA CIKIN SATIN NAN, INA GODIYA SOSAI MASOYANA DA ADDU'O'IN KU TARE DA FATAN ALKHAIRI 🌹🌹🙏 *💋HASKEN RUHI💋* *🫀THE LIGHT OF THE SOUL🫀* It conveys a deep and spiritual meaning referring to the inner light, truth, or purity within a person. *WhatsApp 09065443871* *🌹 ASMEETAH WRITER 🌹* *BOOK TWO__________PAID_____₦300* Page 1 to 2 Tasleem ta ɗaga hannunta sama, haske yana shawagi daga jikinta kamar rana da take haskawa, Duk da haka jikinta a gajiya yake, ba saboda ƙarancin iko ba, sai dan saboda zuciyarta da ke cike da bacin rai da takaici. Catrina kuwa ta kasa kayar da Tasleem, sau uku tana faɗu wa ta tashi, amma hasken Tasleem yana cin galaba a kanta. A karo na huɗu da Tasleem ta buge ta da haske, Catrina fasa ihu tayi kamar halittar da ta fito daga ɓoyayyen wuri. Sai kawai ta faɗi ƙasa tana numfashi kamar wacce za ta mutu. Tasleem tana tafe tana faɗin: "Karya zata ƙare yau, duhu zai durƙusa gaban haske. Ba za ki ci nasarar kwace soyayya ba. Kuma ba za ki sa ƴan’uwa na su lalace da tunanin ƙarya ba!" Yayin da Tasleem ta ƙaraso dab da Catrina, sararin saharar ne ya canza launi. Rana ta ɓace. Wani duhu mai duhun gaske ya gangaro daga sama, iska na kaɗawa... Sannan ƙasa ta rabe biyu. Daga cikin ramin asirai wata mummunar aljana ce ta fito. Tana da ƙafafu huɗu, hannaye biyu, fuska mai idanu huɗu, gashinta kuwa kamar tsintsiya a tsatstsaye. Jikinta yana tafiya da Baƙin hayaƙi.... Cikin murya mai taushi wacce ke cike da haɗari, aljanar ta ce: "Ni ce Bahrasha, uwargidan duhu uwa ga kowace mugunta. Catrina ‘yata daga jini, na jiyo kiran ki... yanzu lokaci ya yi da zamu yaga sararin haske tare." Tasleem ta ja baya da sauri, idonta yana haskawa, jikinta ne ya soma rawa saboda ƙarfinta yana raguwa. Catrina ta miƙe daga ƙasa kamar halitta wacce aka rina da jini, ta ce: "Hah! Kina tunanin ke kadai kike da gata daga haske? Ni ma ina da nawa gata daga duhu. Tasleem... yanzu faɗan ba tsakanin ki da ni kadai bane. Yanzu Bahrasha ce zata koya miki yanda ake narkar da zuciya mai yawan gafara da ƙauna!" A take Bahrasha ta miƙa hannunta zuwa cikin iska – sai wata zobe ta bayyana – zobe mai cike da jinin halittun da ba a san su ba. Ta miƙa wa Catrina, ta ce: "Sa zoben jinin hauka domin ki jujjuya ki zama mace ba mutum ba Ki zama Zarimar Duhu!" Catrina ta amsa ta saka zoben, tana yin haka sai jikinta ya canza ta girma ta zama babbar halitta wacce jikinta ke huda sararin sahara da ƙura. Tasleem kuwa ta dafe ƙirjinta, jikinta yana rawa, Haske yana ƙoƙarin ɓacewa, runtse ido tayi tana magana a cikin zuciyarta. Ta ce cikin ranta: "Haske ba iko kawai ba ne Haske shi ne zuciyar da bata yarda da zalunci ba, Shi ne idon da ke ganin mai laifi amma ya farka da addu’a... Amma yau... Na yarda in tsaya domin kare aiki na ." Haske ya sake ɓarkewa daga jikinta kamar wani tauraro da ya fashe a cikin duniya. Ta miƙa hannunta, ƙasa ta buɗe, wata garkuwar haske ta taso – tana fuskantar Bahrasha da Catrina. Bayan Catrina ta sha zoben jinin hauka daga Bahrasha, ta canza zuwa wata baƙar halitta, gashinta ya tsawaita har zuwa ƙasa, fuskarta ta haɗu da wani irin tsufa da kwalliya mai ban tsoro. Idonta huɗu ne yanzu – biyu masu jini, biyu kuma kamar hantsi a cikin duhu. A bangaren Tasleem kuwa, bayan ta taso da hasken zuciyarta, ta miƙa hannu cikin iska ta furta da wata murya tana faɗin: "Ya hasken ruhi, ku buɗe ƙofofin ceto, ku aiko ma'abotan haske." Sama ta tsage. Wata murya mai tsarki ta sauka daga sama: "Anji kiran ki Sarauniyar Hasken Ruhi. Kiyi maraba da ’Yan Agaji na Hasken Tabbas!" Nan da nan haske ya fashe a sararin Sahara. Daga cikin hasken suka sauko: Jundum – Wani babban halitta mai siffar mutum yana tafe da fuka-fuki masu walƙiya. Rayyaa – Mace mai siffar haske gaba ɗaya, idanunta masu kukan adalci. Sabeeh – Yaro ƙarami da jiki mai murɗaɗɗen haske, yana tafe da takobi wanda duk sanda ya buga shi ƙasa, ruhi mai kyau yana fita daga ƙasa. Bahrasha da Catrina ganinsu yasa duk suka tsorata. Bahrasha ta furta: "Toh, shima hasken yana da mabuƙata? Lallai yau sahara zata sha jini!" Catrina kuwa ta ɗaga hannunta, ta saki wata ƙira kamar kukan dodo tana faɗin: "Masu tarin duhu, ku fito daga ɓoyayyen duniya! Ya ku halittun da na raya da kishi da tsoro, ku tsaya gaban haske yanzu!" Wani irin ƙara ne ya sa ƙasa ta tsagei! Daga cikin ƙasa suka fito: ZAKFURA – Halitta mai jikin maciji da fuskar mutum da wuya. MAYURIN ZUCIYA – Wata halitta da ke ciyar da kanta da fushin mutane. GALMASH – Halitta mai numfashi mai kone numfashin haske, tana rayuwa cikin kishi da munafunci. FAƊA YA FARA CIKIN GASKIYA Sabeeh ne ya ruga da gudu, takobinsa na walƙiya ya ɗaga sama tare da buga shi ƙasa ya haifar da rami mai kakkarfar haske ya bugi ZAKFURA a take ta faɗi haske na ƙone ta tana ihu... Rayyaa kuwa wacce take fafatawa da Aljani Mayurin zuciya ta kifa fukafukanta ta fitar da murya mai ɗaukar ruhi mai duhu. Mayurin Zuciya ya soma rawar jiki – yana ɓari – ya faɗi sumamme. Jundum ya daka ƙara, ya bugi Bahrasha da wata garkuwa mai nisan haske, har sai da ta faɗi gefe tana tari jini. Tasleem da Catrina sun sake haɗa ido. Catrina cikin murya mai ƙasƙantar zuciya da mugunta ta ce: "Wannan ba faɗar ƙaramin iko bane. Wannan faɗar zuciyarmu ce Tasleem. Ki bani zuciyarki, mu raba haske da duhu... Ki bani zuciyarki, in bar miki Abeesh..." Tasleem ta amsa da karfi: "Zuciyata tawa ce kuma na san darajarta, bana son in rasa abin da nake tsaye akai Ina tsaye akan gaskiya, ƙauna da yanci! Kuma a yau – ba za ku ƙara shan nasara ba!" Cikin wannan lokaci ne wata ƙara ta buga daga nesa alamar cewa wani babban halitta daga haske ko duhu yana isowa... Guguwar iska ta tashi cikin Sahara da hayaniya, lokacin da rana ta mai launin zinariya ta bayyana a sararin sama, wani haske ne mai sanyi da kwantar da zuciya ya sauka daga can… Wannan ba kowa bace fa ce MIEMIE... Miemie ce! tana sauƙowa, gashinta na tafe kamar ruwa mai tsarki, fatar jikinta na haske kamar zinariyar dare. Idanuwanta sun cika da tausayi amma sukan ƙone dukkan duhun da suka kalle su da ƙyashi. Kafin kowa ya ankara, ƙasa ta sake bugawa da ƙasa! Wani ƙaho na wuta ya huda sararin sama, zafi da hayaƙi da ƙamshin turaren ja suka mamaye saharar. Madam Nablah ta bayyana. Wuta tana tashi daga dukkan sassan jikinta. Hannunta biyu suna ci da harshen wuta, idanunta masu launin wuta sun cika da ƙarfi da ikirari. Zuciyarta cike da mugunta domin tana ƙaunar 'ya'yanta, amma ba ta san tausayin duniya ba. Lokacin da suka haɗa ido da Miemie, sahara ta girgiza....! Miemie ta ce da murya mai taushi amma da nauyi kamar ruwa mai zurfi: "Na zo ba domin ki ba, Nablah. Na zo domin kare gaskiya daga hallaka, Amma yau zan tsaya gaban ki — domin ke da kanki kin zama hatsarin duniya." Madam Nablah ta kalli Miemie da murmushi amma idonta na hura wuta ta ce: "Kin zo ne domin kare gaskiya amma ki sani cewa wannan gaskiyar da kuke ƙoƙarin karewa jini na ne, Ina da abin da ba ki da shi, Miemie. Ina da ƙiyayya da yaƙi. Kuma yau zan nuna miki cewa wuta ba ruwa ba ce." Nan faɗar ta ɓarke. Miemie ta ɗaga hannu ta ƙira ruwan sama daga wani duniyar ruwa, ruwa mai daraja kamar lu'ulu'u ya sauƙo ya fara zagaye ta. Madam Nablah kuwa ta fitar da harshen wuta daga zuciyarta, yana huda sanyi yana ƙone duk sanyin da ke kusa, a lokacin ta addasa zafi mai tsanani.. a yayin da sanyin ruwan Miemie ke ƙoƙarin kawar da zafin wuta.... Harshen wuta da ruwa ne suka haɗu ya fashe da wani irin ƙara wanda ya tarwatsa tsaunuka a gefe. Tsuntsaye a sama suka fāɗi matattu. Rana ta dushe.... A gefe guda: Tasleem tana fuskantar Catrina da Bahrasha. Bahrasha ta fitar da kaho, tana ƙara tare da faɗin "Na ɗauki zafi daga ruwan jini! Wani haske bazai iya kankare ni ba!".. Tasleem kuwa ta kalli Bahrasha da dariya mai izza ta ce: "Ke ne ake tsoro a cikin duhu? To, yau ki tsorata da hasken zuciyar wacce ku ke son cin amanarta!" Ta fitar da wani garkuwa mai launin haske ta buga ta a ƙasa, wata walƙiya ta fito ta sare ƙafafun Catrina, tayi sama kafin ta faɗo ƙasi, Catrina ta zama gungume domin ƙafafun ta da hannayen ta ne duk suka watse gefe guda tana ihu domin ba ƙaramin raunana tayi ba.... Amma dake Aljana ce sai ta ƙara haɗe gaɓoɓin jikinta suka dawo normal... Bahrasha ta ruga da gudu kamar giwa tana shirin yaƙar Tasleem, amma kafin ta iso yanda Tasleem ta ke, itama Tasleem ta yi tsalle tare da buga thunder hannunta ƙasa, har sai da Brahrasha ta tashi sama kamar guguwa ta faɗi gefe tsabar ƙafin haske... ƘARFI DA ƘARFI: HASKE DA DUHU A yanzu, halittun haske (Jundum, Rayyaa, Sabeeh da wasu sabbin) suna fafatawa da Galmarsh, Zakfura, da Mayurin Zuciya waɗanda suka farfaɗo da sabbin ƙarfi. Faɗar da ba’a taɓa gani ba – faɗar da take canza nau’in duniya. Sahara ta yi shiru. Wuta da ruwa sun haɗu suka zama hayaƙi mai haske. Madam Nablah da Miemie suna tsaye a sararin sama, jini da gumi na ratsawa jikinsu... Tasleem tana ƙasa cikin kallo mai cike da mamaki — tana kallon Mahaifiyarta Madam Nablah, ba ta taɓa sanin cewa ikon mahaifiyarta ya kai wannan matakin ba. A hankali take furta "Shin wannan ita ce uwata wacce ta haifeni? Ita ce ta tsare ruhi da haske da duhu a jiki guda? Shin ita ce ta fi wuta zafi?..." Zuciyar Tasleem na bugawa, yayin da hawaye suka cika idonta. Kaff Aljanu da Jagororin hasken duk tsaya kallon faɗan manyan shuwagabannin suka yi, Madam Nablah da Miemie... Miemie cikin ƙarfin iko ta haɗa ruwa ta jefa Madam Nablah a ciki... Tasleem har zata ruga da gudu wurin Madam Nablah ganin yanda aka jefa ta a ruwa mai yawan gaske, kafin ta motsa taji an riƙo hannun ta, tana juya wa ta haɗa ido da Miemie... Miemie ta tsaya kusa da Tasleem, tana kallonta da idanuwanta masu launin ruwan sanyi. Tasleem ta runtse ido, tana jin wani irin nutsuwa daga halittar da ba ta taɓa ganinta ba, amma zuciyarta ta yarda da ita gaba ɗaya. A hankali ta furta "Ke ba irin su bane... Ke haske ne..." Miemie ta ɗora hannu a kan kafadar Tasleem, ta ce da murya mai sa hankali ya mutu: "Haske bai faɗi ba. Amma idan haske da wuta suka ƙone juna, babu abinda zai rage sai ƙura. Don haka... sai a yi ƙoƙarin dakatar wa ta hanyar sadaukar da ɗaya..... A gefe guda Madam Nablah tana gefe, wanda fitowar ta kenan daga cikin ruwa tana huci da zufa, sai kuma ta fara nazarin ƴarta Tasleem, yanda zata ɗauke ta, ta rabata da ahalin haske gaba ɗaya.... Wata murya daga cikin zuciyarta ta ce: "Zan rasa ƴaƴana gaba ɗaya idan na ci gaba da wannan yaƙi... Nasreen tana hannu na a killace..... Asmeen tana gida duk da nasan baza'a taɓa samun matsala daga ɓangaren ta ba domin yarinya ce marar wayo, so nake ta kasance da mijinta har su sama mun yaro wanda zai yi sanadiyyar ɗaukaka ta....sannan kuma Tasleem a yanzu zata faɗa tarkona....." A can ɓangaren gida... Amaar ya dawo gida cikin hanzari, tare da Asmeen da Shaprees da Abul. Gidansu na cike da alhini, saboda duk sun tabbatar da cewa Abeesh ya ɓace. Asmeen ta zauna cikin firgici, tana tunanin Tasleem da babu labarinta, itama basu san yanda ta je ba, ga samuwar rashin Nasreen... Shaprees ya yi tagumi fuska a hargutse yana bin kowa da idanu masu ɗauke da mamaki, da jinjina lamarin da ke faruwa... Abul kuwa, yana kuka a hankali, yana cewa: "Na san wannan ƙaddara ce… amma a ina Abeesh yake? Wane ne zai iya ɗaukar shi daga asibiti har a ɓoye shi kamar iska?" Amaar ya lumshe ido, yana jin wani abu ba daidai ba... --- Yayinda Miemie ta fuskanci Madam Nablah bayan ta bayyana musu kamar iska, domin sun san ba zata taɓa mutuwa ba, su na so ne su kawo ƙarshen yaƙin , ta ce: "Nablah... Ƙiyayyarki ta cutar da duniya, amma so da kika ɓoye ya ceci ƴarki... Kuma zan baki zaɓi: ko ki daina, ko kuma ki rasa ta." Madam Nablah ta ce da murya mai kaifi cike da izzah ta furta: "Ba na jin tsoro... Amma ina jin zafin rasa ƴa... Idan hakan zai ceci Nasreen, Asmeen da Tasleem, zan tsayar." Ta dakatar tare da jan yo Tasleem jikinta tana faɗin "Wannan ƴata ce ta jini, bazan taɓa sadaukar da ƴata a gareku ba..." MIEMIE ce take shirin yowa kan ta domin ƙwatar Tasleem, kafin ta motsa Madam Nablah ta kunna wutar tsafin ta mai ƙarfin gaske da tsananin zafi ya busa kowa dake wurin, tsabar tiririn wutar sai da Miemie tayi baya a gigice tare da faɗuwa ƙasi, duk babu wanda bai yi sama ya doku a ƙasi ba tsabar tiririn wuta.. A take Madam Nablah ta ɓace da Tasleem a cikin wannan wutar... Catrina da Bahrasha ne suka kama kayuwansu tare da saki ƙara domin ƙwaƙwalwar baƙaƙen Aljanun ne suke tafarfasa tsabar tsananin zafin wuta su ma a take suka bace cikin duhu.... Halittun haske kuwa su ma ɓace wa suka yi cikin haske mai ɗauke da sanyi da iska mai daɗi... Miemie ta zama ruwa itama ruwan ya ɓace.. Haske ya wanke sahara. Faɗa ya tsaya. Kowa ya kowa yanda ya fito, domin ba a yanda zasu samu Madam Nablah a halin yanzu, ga tana shirin hallaka su da wuta mai tsananin ƙuna... ★★★★★ A can bayan duniyar da mutane ke rayuwa, bayan saharar haske da duhu, akwai wani tattakeƙen lambu, da itatuwa masu baƙin ganye kuma rana bata fito wa a wurin sai wata mai launin ja. A tsakiyar wannan wurin akwai ƙaramar dafaɗɗiyar alfarwa, wadda take gefen wata tafkin ruwa... A cikin wannan alfarwa, Nasreen ce ke kwance. Ita ba matacciya ba. Ita ba kuma rayayya ba. Sai dai kamar ana tsare da ruhinta cikin wani yanayi na barci mai zurfi.... 💤 NASREEN CIKIN BARCI MAI RAI... Nasreen wacce take bacci da duk motsin zuciyarta. Idonta a rufe, amma murya tana fitowa daga cikin zuciyarta tana cewa: "Abeesh... ina jin ka... amma ba zan iya miƙa hannuna ba... Ina jin sanyi... amma na kasa tashi... Waye ya tsare ni a nan?" Ruwan tafkin yana zagayawa da ƙamshi mai sanyi da ƙara kamar kuka. A gefe guda, Madam Nablah ce ke zaune tana saka rawaya a cikin ruwa, tana ambaton wasu kalmomi cikin harshen da babu mai iya fassara wa sai halittu. Ita kaɗai tasan a yanda ta ɓoye Tasleem, sannan ta bayyana a yanda ta ajiye Nasreen.. A lokacin da Catrina ta so kashe Nasreen da duhu, Madam Nablah ce ta karɓi ruhin Nasreen ba tare da barin ta mutu ba, ta kaita wannan wuri domin tsare rayuwarta har ta ci galaba akan haske.... Madam Nablah ta ce cikin wani sanyin murya da kuma ƙarfi, tana faɗin "Ance mata zata mutu, amma ni nace a’a. Nasreen zata yi rayuwa, ba sai da kujerar mijinta ba… Sai da zuciyarta da ƙaddara. Ta ci jarabawa, amma har yanzu akwai sabo a zuciyarta. Sai na goge komai, sai na shafe komai, sai na miƙe domin magance matsaloli... sannan zata tashi daga bacci, ki cigaba da hutawa ƴata Nasreen......" 💔 A cikin barcinta, hawaye suka gangaro daga gefen idonta. Zuciyarta tana kiran sunan Abeesh, kuma tana jin laifin da ta yi masa lokacin da ta fara zargin sa da Catrina... A cikin baccin take maganar zuci "Idan na tashi daga wannan wuri, zan nuna soyayya kamar yau ce rana ta ƙarshe... Amma idan ban tashi ba, ku faɗa wa ƴan uwana cewa ina ƙaunar su.... Ku faɗa wa Abeesh cewa na yarda da shi har karshen numfashi..."... ★★★★★★ Kai tsaye Tsaunin da ta ajiye Abeesh ta nufa dake wata duniyar da bana mutane ba... A wani tsauni mai hayaƙi da turɓaya, wanda wuta ke fita daga ƙasa kamar ana hura shi daga zuciyar duniya, Madam Nablah ce tsaye — jikin ta na ƙuna da harshen wuta, idonta kamar ƙarfen da aka ƙera domin hukunci. A ƙasan wannan tsauni, a cikin wata ƙaramar rami da duhu ya lullube shi, Abeesh ne kwance yana fitar da numfashi mai rauni, jikinsa babu ƙarfi, ba motsi, amma zuciyarsa har yanzu tana bugawa da ƙauna, damuwa, da ruɗani. Madam Nablah tana tsaye tana jiran zuwan wadda ta ƙira. 🌑 CATRINA CE TA BAYYANA Cikin wata walkiya da iska mai mugun ƙamshi, Catrina ta bayyana. Jikinta a gajiye daga faɗan da suka yi da Tasleem, amma idanunta na cike da jaraba na rudani. Da ta hango Abeesh a ƙasa cikin yanayin rashin lafiya, ƙirjinta ne ya buga, Sai ta ɗan yi baya, tana fadin: "Wannan... wannan Abeesh ɗin ne...?" Madam Nablah ba tare da ta ce komai ba sai da ta juya kanta a hankali, ta ɗauko ƙaramar wuƙa mai kaifi daga bayanta, wacce take walkiya da jini, sannan ta miƙa mata tana cewa: "Kamar kin fara jin tausayin kauna ko? Kin manta cewa ke sarauniyar duhu ce, Catrina. Ya kamata ki wargaza ƙauna, ba wai ki gina ta ba..." Catrina ta ɗauki wuƙar da hannunta yana rawar jiki. Ta kalli fuskar Abeesh, ta runtse ido, hawaye na cika idonta duk da bakinta yana dariya, domin ita a koda yaushe a cikin dariya take ko da tana kuka.. Madam Nablah ta ce: "Ina buƙatar ki yanke dangantakarki da zuciyarki, domin a wannan darasi, zuciya rauni ce. Ki nuna cewa kin fi zuciyar ki ƙarfi, Kashe shi... kafin ya kashe ki da ƙaunar sa." Catrina ta ce: "Na ƙi. Na ƙi! Banza nake kiran kaina sarauniyar duhu idan bazan iya amfani da duhun ba, zan yi amfani da duhu domin tarwatsa kowa amma ba zan iya cutar da Abeesh ba, Kullum idan na gan shi zuciyata tsinke wa take... Ban san yaushe na fara jin sa a cikin raina ba... Hakan yasa ba zan iya kashe shi ba!" Madam Nablah cikin ɓacin rai ta ce: "Kin gaza, Catrina! Kin zama rauni, kin koma mace mai ciwon ƙauna... Kin manta ni na gina ki! Ni na kore ki daga mutunci zuwa iko! Kuma yanzu ke kin kasa... akan wani ɗan adam?!" Catrina ta ce: "Na ƙi zama yanda kike so. Na ƙi zama wuta Saboda hatsarin ta. Ban son zama kamar ki. Kuma idan zaki kashe shi, ki fara kashe ni tukun...." Madam Nablah karɓan wuƙar daga hannun Catrina ta yi tare da faɗin: "To... na fahimta. Amma ki sani... da zarar kin ɗauki hanyar ƙauna, shikenam kin zama ƙaramin haske... kuma ina ci gaba da ganin haske a jikinki. Wannan zai zama ƙarshen ki, Catrina, idan kin ci gaba..." Sai ta juya da wuƙar, ta buga ta ƙasa, ta ɓace cikin wuta. Itama Madam Nablah ba har cikin zuciyar ta take faɗin ta kashe Abeesh ba, akwai abinda take son shirya wa... Catrina ta zauna a gefen Abeesh tana kuka. Ta riƙo hannunsa a hankali tana cewa: "Ka tashi, ka yi magana dani... Ka ce min ka yafe min... ko aƙalla ka ce min baka yafe ba..." Sunkuyar da kanta a kan ƙirjinsa tayi, hawaye suna sauƙa. Duhu ya ƙara rufe tsaunin, da alama wani sabon abu yana gab da faruwa... Catrina na zaune gefen Abeesh, hannunta na dafe da goshinsa, hawaye na gangarowa daga fuskarta mai cike da wulakantacciyar soyayya da nadama. Duk da ta kasance cikin duhu, duk da ta rayu a ƙarƙashin horo da umarnin Madam Nablah, akwai wani abu a ranta da ke bijirewa — wanda ko ita kanta ba ta fahimce shi ba: Abeesh. Tana kallon shi, sai ta furta da murya mai sanyi : “Me yasa baka da taurin zuciya kamar mu? Me yasa soyayyarka ke da sauƙin ƙona ruhin wanda bai san me ƙauna take nufi ba? Abeesh... ka karya mun zuciya da soyayyar ka...” Iskar tsaunin ta ƙara zafi, kamar tana ƙona hawayen da ke zubowa daga idonta. Duk da haka, ta cigaba da magana, tana shafa fuskarsa da ƙaramar ƙarfinta domin ƙarfin ikon ta ƙara raguwa take a yayinda take zubar da hawaye... Ta ce: “Na ga duhu, kuma ni duhu ce, na ji daɗin sukar mutane. Na yi nesa da zuciyata... amma kai ka ja ni na fara dawo da ita. Na fara jin yadda zuciya ke bugawa idan tana cikin ƙauna.” Ta kalli hannuwanta waɗanda suka saba azabtar da zuciya, yanzu suna rawar sanyi da tsoro. Sai ta ɗaga kanta, ta kalli sararin tsaunin, tana fadin: “Idan hukuncina mutuwa ne saboda ƙaunar wanda nake zaton maƙiyi na, to na yarda. Amma kar ku ci gaba da cutar da shi... don Allah, kar ku taɓa shi...” Cikin ɗan lokaci, wani ƙarar numfashi ya fito daga cikin ƙasan tsaunin. Abeesh ya motsa. Hannunsa ya dan motsa kamar wanda aka kwantar da shi tsawon lokaci. Catrina ta zaro idonta cike da farin ciki, numfashinta ya tsaya cak. ta ce da murya mai rauni: “Abeesh... Abeesh? Ka na jina?” Abeesh bai buɗe idonsa ba, amma ƙirjinsa na tashi da sauƙa. Wannan ne karo na farko da numfashinsa ya sauya tun da aka kwantar da shi. Catrina ta matso da fuskarta kusa da kunnensa, tana fadin: “Na sani... ka ji ƙiyayyata. Na sani... Na taɓa Nasreen. Na jefar da mafarkinka, Amma na fara yin nadama... kuma ko zan mutu saboda haka, na amince..... Ka yi shiru, Abeesh! amma zuciyarka ta gaya min komai.” Kamar dai wani abu na faruwa daga nesa... Catrina ta juyo da sauri. Ba a iya ganin wanda ke zuwa ba, amma da alama wani abu ne ke matsowa kusa. Idanunta ne suka cika da ruɗani, tana girgiza kai tana cewa: “Kada ku zo ku ɗauke shi. Ku bar ni in gyara kuskurena. Ku bar ni in nuna masa cewa zuciya na iya tuba, koman zurfin duhu.” Ta sunkuyar da kanta bisa ƙirjin Abeesh, ta cigaba da fadin: “Idan har zaka tashi, ko da zaka ce bani da amfani a gareka, zan karɓa. Ko da zaka watsa ni da kalmomin ƙiyayya, zan saurara. Amma kayi min alfarma... ka tashi. Dan Allah, ka tashi…” Da wannan kalmomi, hawaye suka zubo daga idon Abeesh — a hankali, ya buɗe idonsa... Sai ya ce cikin murya ƙasa-ƙasa “Ke ce...?” Catrina ta girgiza kai cikin hawaye, tana murmushi mai raɗaɗi ta ce: “Ni ce... kuma ban cancanci amsarka ba.” Madam Nablah tana tsaye a saman wani dutse mai kaifi a cikin tsaunin da aka ɓoye Abeesh. Gashinta yana motsi kamar harshen wuta, idanunta kuwa suna lumshewa a hankali. Amma zuciyarta na girgiza ganin Catrina ta tsugunna jikin Abeesh da hawaye, tana tunanin taya Aljana zata kamu da ƙaunar bil adam na tsanani.... Ta furta da siririyar murya mai cike da iko da izzah: “Catrina… Catrina… Ba ki zama ni ba, kuma bazaki taɓa zama kamar ni ba....Amma ki sani cewa ke duhu ce, kuma kina kokarin dauƙo haske? Da Soyayya? Lallai… kina kuskure, yarinya.” Catrina ta ɗago idonta, jini na zuba daga hancinta da idanuwanta Tana kallon mahaifiyar ruhi da girmamawa da tsoro ta ce: “Na rasa meye gaskiya… amma yanzu na san me nake so. Ba ku bane. Ba cutarwa ba. Na san cewa zuciya zata iya rayuwa da ƙauna.” Madam Nablah ta tintsire da dariya mai cike da haushi, tana sauƙowa ƙasa daga kan tsauni cikin hayaƙi, ƙasa na ƙonewa da wuta a inda ƙafarta ke taka wa. Lokacin da ta tsaya gaban Catrina, ta ɗaga hannunta, wata wuƙa mai kamar an harhaɗa ta da wuta da jinin halittu ta bayyana. Ta furta da murya mai ƙarfi: “Ga zaɓi: ko ki tafi ki ɗauko Abul, mahaifin Abeesh da Amaar ko kuma... ki kashe Abeesh da kanki.” Zuciyar Catrina ta tsaya. Kamar an fesa ruwan sanyi a jikinta. Sai ta girgiza kai a hankali ta ce: “Kada ki jarraba ni da hakan. Bazan iya kashe shi ba, wallahi bazan iya ba... koda kuwa duhu zai ƙona ni, koda kuwa kin cire ni daga hallita ne bazan iya kashe shi ba.” Madam Nablah ta ɗan lumshe ido. A fili ta nuna bacin rai, amma a zuciyarta baza ta taba bari a cutar da Abeesh ba balle ta sa a kashe shi, barazana ne kawai.... Domin Madam Nablah... tana son Abeesh. Jin sa take kamar ita ta haife shi, duk da yana da ɗabi’a mai kyau, Ƙwazo. Tausayi. Gaskiya. Kuma hakan ya sa ta tsani wannan halin, amma tana ƙaunarsa.... Cikin barazana take faɗin: “Idan bazaki kashe shi ba, ki tabbatar kin kawo min Abul. Idan ba haka ba... ke da shi zaku hallaka tare.” Catrina ta juyo, tana kallon Abeesh, tana shafa goshinsa da yatsanta, wanda a halin yanzu baya cikin hankalinsa, haka yake binsu da kallo ba tare da yasan abinda suke faɗi ba..... Zuciyar sa Nasreen kawai take ƙira. Catrina ta ce: “Zan kawo miki Abul... Amma idan na dawo, kar ki kuskura ki taɓa shi. Na rantse da wutar da kika raina ni da ita, zan juyar da ita akanki idan kika ƙetare haddi.” Madam Nablah ta bace da harshen wuta ba tare da ta furta komai ba... A nan ta bar Abeesh bata ɗauke shi ba, ta bar shi, saboda wani abu a ranta . Ba zata taɓa iya kashe shi ba… Catrina Ta kalli hanyar sama, ƙarfin zuciyarta yana ƙaruwa, duk da hawaye na gangarowa ta ce: “Wannan ba faɗa ce ta duhu kawai ba... Yanzu zuciyata tana ƙoƙarin ƙin kowane mungun aiki. Amma zan kare wanda nake so, koda kuwa rayuwata ce fansa.” Sai ta ɓace cikin iska… domin taje ɗauko Abul...... *💋HASKEN RUHI💋* *🫀THE LIGHT OF THE SOUL🫀* It conveys a deep and spiritual meaning referring to the inner light, truth, or purity within a person. *WhatsApp 09065443871* *🌹 ASMEETAH WRITER 🌹* *BOOK TWO__________PAID_____₦300* Page 3 to 4 Bayan fafatawar haske da duhu, Tasleem bata koma gida ba. Madam Nablah, cikin wayo da zurfin mugunta, ta hango cewa Tasleem ce kaɗai za ta iya rushe komai da ta gina tsawon shekaru na tsafi da jini, Don haka ta ɗauke ta Ta ɓoye Tasleem a wani wurin da haske baya iya haska wa, cikin kogin tsafi mai rai, wanda ruwansa ba ruwa bane kawai, tsantsar sinadarin ruhi da sirrin duhu ne ke gudana ciki. A ƙasan kogin akwai wani ɗaki da ruwa baya shiga cikinsa amma kogi ne ke kewaye shi. Tasleem tana zaune cikin wannan ɗakin, Jikinta a sanyaye, gadon da take kwance akai ba a cikin ruwa yake ba, amma ko'ina a zagaye da ruwan kogi, wanda kifayen tsafi ke zagayawa cikin iko... Kowane kifi yana da launin ido daban wasu ja, wasu kore, wasu ruwan duhu. Suna kallon ta kamar suna tsaron sirrin wani babban sihiri. A wani lokaci, Tasleem takan sauƙe numfashi tana kallo sararin ruwan da ya rufe ɗakin daga sama, tana maganar zuci: “Mommy... kin tsorata da haske na. Amma kin manta haske baya buƙatar daƙi mai duhu. Idan zuciya ce haske, zai iya gutsura duhu duk inda aka kulle shi.” 🏚️ Amaar ya shiga firgici na rashin Tasleem, ba yanda mai shiga nemanta ba amma ko ƙyallen ta ya rasa, gaba ɗaya bashida natsuwa. Ya rasa Nasreen, ya rasa Abeesh. Kuma yanzu Tasleem ma ta ɓace. Duhu kamar ya sake lullube shi. Amma zuciyar sa ta ƙi amincewa da asarar Tasleem. Yana jin kamar zata dawo, amma yana jin tamkar an tsare ta a wani wuri... Kullum yana tare da Abul wanda har yanzu ba ya iya magana sosai, amma idanunsa suna nuna damuwa da wata babbar matsala da ke maƙale a kansa, Amaar yana riƙe da hannun Abul cikin damuwa a daren yau, yana furta a hankali: “Abul, ba zan bari su cutar da mu ba. Na san akwai sirri, akwai tsafi, akwai zalunci amma akwai gaskiya. Kuma gaskiyar zata fito, koda kuwa ta fito daga cikin kogi.” Ya lumshe ido, hawaye na zubo wa... 🌊 TSALEEM A KOGIN TSARIN RUHI Duhu da sanyi da shiru su ne abokan Tasleem a cikin ɗakin ƙasa da ruwa, inda kifayen tsafi ke shawagi a zagaye da ita. Kowane motsi na su yana da ma'ana, kamar wasu wakilan wani sarki ne da ke jarrabar zuciyarta. Tasleem na zaune akan gadon da ruwa baya taɓa jikinsa daga ɗakin baya ratsa wa, amma ƙamshin ruwa yana lullube ta, tamkar ana so a rage mata ƙarfi cikin salo, Idanunta sun canza launin baƙi da ɗigon haske a tsakiya... Ta taɓa ƙirjinta, tana jin zuciyarta na bugawa da gaggawa. Ta ce: “Wannan ba ƙarshe ba ne…” ta furta cikin sassanyar murya ta kuma cewa “Haske baya mutuwa...” ★★★★★ Amaar ba ya barin Abul shi kaɗai ba. Tunda ya fara fahimtar cewa Abul na da wata matsala ta ruhaniya, baya iya bacci ba tare da ya gan shi ba. Catrina kuwa — tana lura da hakan. Kullum tana leƙen inda suke, tana tunanin lokacin da zata shigo ta ɗauki Abul kamar yadda Madam Nablah ta umurta. Amma kullum Amaar yana tsaye kusa da shi, wani lokaci har ya zauna ƙasa yana karanta masa addu’a ko kuma yana furta wa kansa: “Abul ka riƙe zuciyar ka. Ni da kai za mu bayyana komai. Tasleem za ta dawo. Gaskiya zata fito…” Bayan duhu ya shiga, babu motsin kowa, Asmeen da Shapreen na part ɗin su, iya Abul da Amaar ne kawai a wannan part ɗin, Catrina ce ta doso wajen cikin dare — sanye da mayafin duhu, ido kamar wuta. Amma tana iso kusa, sai ta tsaya daga nesa, tana hangowa daga cikin inuwa. Amaar yana zaune ne a gaban Abul yana duba fuskar sa cikin kulawa da alama suna wata magana ne... Catrina ta dafe bango, ta kalli yatsun hannunta da suka fara rawar jiki. Zuciyarta ta ambaci sunan Abeesh har yanzu tana jin son sa yana ci mata rai. A zuciyarta ta furta: “Madam Nablah ba za ta fahimta ba… Ni ba zan iya cutar da Abul ba. Kuma bazan iya ɗauke shi a gaban Amaar ba.” Ta juya a hankali tana jin kamar idan bata cika umarnin Nablah ba, zata fuskanci fushin da bata taɓa gani ba. 🔥 Madam Nablah tana kallon Catrina daga cikin madubin ta na tsafi tana jin ranta na tafasa, tayi magana cikin masifa tana faɗin: “Wanda yaƙi aiwatar da umarni... ya zaɓi hallaka kansa da hannunsa.” Sai ta ɗaga hannu wata ƙaramar ƙwarya ta bayyana a gabanta, tana tafasa jini ta ce: “Tasleem tana nan a kulle babu yanda zata dakatar Amma duk da haka Catrina ta kasa…” Ta dakata. Idonta ya canza launi — daga ja zuwa baƙi kirin ta kuma faɗin: “…zanyi amfani da mafarki na ƙarshe: tsafi mai ɗauke da hawaye. Kuma zan iya yin abinda kowa zai bar duniya.” ★★★★★ Tasleem wacce take cikin ƙalubale kullum tana tsammanin ceto amma babu wanda yazo yanda take hatta Madam Nablah tinda ta ajiye ta bata ƙara sauraronta ba, tayi kukan har ta gaji, ga wurin da take ikon ta baya aiki, amma wurin da take babu abun cutar wa, tsararren ɗaki ne wanda komai da komai akwai shi, duk abinda ake buƙata akwai, daga ɗaki tana hango ruwan da yake zagaye da ɗakin da kifaye masu gadinta na sihiri... Ruwa ne ke kewaye da ita, ruwan da ba kowa zai iya hango ƙasarsa ba, balle ya fahimci a cikinsa akwai ɗaki mai rufin sirri. Tasleem tana zaune akan gadon alhurma mai hasken milk, cike da ƙamshi mai ɗaukar hankali, amma zuciyarta na cike da fargaba da duhu. Idanunta sun kusan rikicewa saboda tsawon lokacin da ta ɗauka bata ga hasken rana ba. Amma hasken da ke fitowa daga jikinta ba ya mutuwa. A kowace rana, kifaye masu ban mamaki suna zagaya wajen ɗakin suna gadinta. Sai dai a yau, wani nauyi na daban ya sauƙa a kirjinta. Ta furta cikin karamin murya: “Ina ku ke! Ina ku ke Amaar! Nasreen!! Abul...!!!” Zuciyarta na harbawa, ta tsare ruwan da ke zagaye da ita, tana jin wata murya a wajen ruwan ana furta: “Ba za ki tsere ba, kar ki manta a ƙarƙashin ikon duhu kike...” Amma bata ga wanda ya yi maganar ba, kamar dai akwai ɓoyayyen abinda yake tsare da ita... ★★★ Amaar yana zaune kusa da gadon Abul, yana sharar zufa, fuskarsa cike da damuwa. Dama ɗaya ya rage masa a zuciya, rayuwar su ta tsere daga hannunsa. Ya rasa Nasreen. Ya rasa Abeesh. Kuma yanzu Tasleem ta bace gaba ɗaya ya ce: “Allah Ka dawo min da su… ko ɗaya ne a cikin su, kawai ɗaya...” Sai yayi shiru. Ya kalli Abul, wanda idanunsa a rufe suke amma yana sauƙe numfashi cikin nauyi. Ya ɗauki hannunsa, ya riƙe shi yana faɗin: “Zan riƙe ka. Zan kare ka daga komai, bazan taɓa barin a ɗauke mun kai ba Abul, shiyasa bana zuwa ko ina saboda kai…” 🖤 Catrina na tsaye a bayan wata bishiya cikin damuwa, ta rana ina zata sanya rayuwarta ta huta, tana tunanin Amaar da Abul daga nesa. Jikinta Gabadayanta rawa suke, zuciyarta na harbawa...cikin kuka ta ce “Zan iya shigowa yanzu in ɗauki Abul… Amma idan Amaar ya gan ni...” Ta taɓa kirjinta, inda zuciyarta ke bugawa sosai. Son da take yi wa Abeesh yana rikita ta. Amma umarnin Madam Nablah yana fasa mata kunnuwa yanda take faɗin cewa: “Tafi ɗauko Abul ko ki kashe Abeesh da hannunki...” Girgiza kai tayi tare da faɗin “Bazan iya kashe shi ba… domin ina sonshi… amma idan na kasa ɗauko Abul fa?” Ta juya baya, tana jin hawaye ya cika mata ido. Sai murya daga cikin ganye ta fito – murya ce daga zuciyar tana maganar zuci: “Catrina… duk wanda ya zaɓi ƙauna, baya tsoro. Amma duk wanda ya zaɓi biyayya ga sharri, ya rasa komai.” 🔥 A cikin wani tsauni mai duhu da yashi mai fitar da hayaki, Madam Nablah tana zaune, tana kallon cikin wata ƙwarya mai wuta. A ciki ne ta kulli Abeesh, cikin muryar tsafi ta zuba masa ruɓaɓɓen barci tana faɗin: “Zan bar ka nan har sai ka farka ka manta da komai....” Sai ta ɗago kai — ta ji Catrina na shigowa. Bayan gaisuwar tsoro da nauyin ido, Madam Nablah ta miƙa mata wuƙar zinariya wacce ke ci da wuta ta ce:: “Ko ki ɗauko Abul... ko ki kashe Abeesh yanzu nan. Babu hanya ta uku. In ba haka ba, ke kanki na fi karfin ki.” Catrina ta kama wuƙar da hannunta, tana kallon Abeesh wanda ke fama da barcin sihiri. Sai ta furta cikin murya mai ɗauke da kuka: “Bazan iya kashe shi ba. Ina jinsa kamar rabin raina. Ki kashe ni idan kina so... Amma kar ki ce in cutar da shi.” Madam Nablah ta lumshe ido, zuciyarta na tafasa da wani abu da ba ta iya bayyanawa. A zuciyarta ta furta: “Abeesh... ɗana ne fiye da komai.” Amma a fili, ta fitar da murmushi mai tsananin barazana da tausayi a lokaci ɗaya.... Madam Nablah ce ta karɓi wuƙan tare da saita zuciyar Abeesh tana faɗin "Ok! tinda ke kin kasa saboda ƙauna, Ni zan kashe shi da hannuna..." Catrina a ruɗe take faɗin "A'a dan Allah, Devil Mom please zan ɗauko Abul amma kar ki cutar da Abeesh...." Madam Nablah ta ce "je ki to..." Catrina ɓace wa tayi a hanzari ta koma duniyar mutane... Kamar iska haka Catrina ta bayyana cikin dakin, tana tafiya da saurin takun da ke bayyanar da tsoro da ƙuduri a lokaci guda. Abul yana kwance akan gadon, yana ɗan fama da hawan jiki, amma idanunsa na bude suna hangen kowane motsi. Da ya hango Catrina, sai ya miƙe da sauri yana ƙura mata ido. Ya furta da mamaki da ƙiyayya: “Ke? Me kika dawo yi gidan nan?! Ko kin manta irin abinda kika haddasa?!” Catrina ta tsaya ba tare da ta motsa ba, tana kallonsa da ido mai taushi. Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce da murya mai rauni: “An aiko ni ne… akan mu tafi tare.” Abul ya matsa baya kadan, yana kallonta da shakku. Ya girgiza kansa yana furta: “Waye ya aiko ki? Ina kike lokacin da komai ya rushe? Ina Abeesh? Ina Tasleem? Ina Nasreen?” Catrina ta ɗauke kai gefe, ta lumshe idanu kamar mai ƙoƙarin ɓoye damuwa ta ce: “Ban sani ba… wallahi ban san inda suke ba. Ni ma ban gan su ba tun lokacin.” Abul ya fashe da dariyar takaici, yana girgiza kai tare da faɗin: “Ke da kika fi kowa sanin shirin Madam Nablah, da kika fi kowa kusanci da ita, kina cewa baki san inda suke ba? Kar ki ɗauke ni sakarai, Catrina!” Catrina ta matso gaba da sauri, idanunta cike da hawaye, tace: “Wallahi ba na tare da sharrin da ke faruwa yanzu! Na zo ne domin… domin kawai in ɗauke ka mu bar nan kafin wani abu ya faru da kai.” Abul ya ɗan ɗaga murya ya ce: “To ki gaya min gaskiya! Abeesh fa? Ya ya yake? Ki ce min da bakinki! Ina Nasreen da Tasleem?” Catrina ta durƙusa a gabansa, tana girgiza kai tana faɗin: “Ban san inda suke ba. Ka yarda da ni... Abul, ban san komai ba game da su...” Abul ya janye jikinsa, ya ce da ƙarfi: “Bazan tafi dake ba, Koda kin faɗi gaskiya. Bazan yarda dake ba har sai Amaar ya dawo.” Catrina ta ɗaure fuska hawaye na gangarowa daga fuskarta. Tayi ƙoƙarin kama hannunsa amma ya tureta da ƙarfi yana faɗin: “Ki fita. Bana son ganin ki yanzu. Ki je ki bar ni.” Catrina ta tsaya cak, zuciyarta na tafarfasa. Tayi juyi, ta juya za ta fita amma kafin ta kai ƙofa ta tsaya ta ce: “Duk da baka yarda da ni ba… ina fatan wata rana zaka gane banason a cutar da ku. Kuma ni… ni bana so a cutar da Abeesh.” Sai ta fice a hankali, ta bar ɗakin cike da damuwa, yayin da Abul ya bita da kallon shakku da tausayi a lokaci guda. Bayan wasu ƴan mintuna sai ga Amaar ya dawo daga waje ransa a cunkushe kamar dutse a ƙirji. Kusan kullum yana zaune kusa da mahaifinsa Abul, yana kulawa da shi cikin ladabi da biyayya. Duk da yawan tunani da bugawar zuciya Amaar bai taba barin mahaifinsa shi kaɗai na wani lokaci mai tsawo ba —sai yau. Ya shigo ɗakin cikin hanzari, yana kallon yanda Abul yake a zaune yana faɗin: “Abul, lafiya? Me yasa ka barni na ɗan fita? nasan tabbas Catrina ta shigo gidan nan...” Abul ya dube shi da murmushin tausayi ya ce: “Tana so ta tafi da ni… amma ban yarda na bita ba.” Amaar ya ɗaure fuska, idanunsa suka ɗauke da barazana ya ce: “Allah ya tsare, babu inda zaka je tare da ita. Catrina tana karkashin umarnin Madam Nablah. Kuma yanzu komai yana cikin hatsari.” Yayi shiru na ɗan lokaci kafin ya sauƙe ajiyar zuciya ya kuma cewa: “Mun rasa Nasreen... har yanzu babu labarinta. Abeesh ma ba’a san inda yake ba. Tasleem kuma… bata dawo daga yanda taje ba.” Hawaye ne suka cika a idanun Abul, Abul ya kama hannunsa, yana ƙoƙarin ƙarfafa masa guiwa da cewa: “Ka dage Amaar. Rayuwa fa gwagwarmaya ce. Sai jarumai ke cin nasara.” Ɓangaren Tasleem!! Idanunta sun cika da tambaya, zuciyarta na ƙuna da damuwa akoda yaushe a cikin tambayar “Ina Nasreen? Ina Abeesh? Ya aka yi faɗa ya ƙare haka? Kuma… me yasa na kasa komawa gida?” Kamar wata mai juyayyar ƙwaƙwalwa ta kasa fahimtar komai... Tana ƙoƙarin tashi daga gadon, sai wani zafi ya shige jikinta, alamar an ɗaure ikon tafiyarta da tsafin ruwa. A lokacin wani kifi ya zagayo kusa da gilashin ruwa dake kewayen ɗakin, yana jujjuya kai kamar yana kallonta. Tasleem ta matso kusa da glass din ruwa, ta furta cikin siririyar murya: “Ina nan… amma ba zan daɗe ba. Zuciyata tana tsaye ga gaskiya. Babu tsafi da zai iya hana haske dawowa...” Yayin da Amaar ke ƙoƙarin nemo Tasleem da kuma laluɓo gaskiyar halin da ake ciki, Catrina ta dawo cikin gida amma zuciyarta a ɗaure take, Akwai wani sirrin da Madam Nablah ta ɓoye — kuma Tasleem tana cikin haɗari fiye da yadda kowa yake tunani. Madam Nablah a yanzu tana shirye-shiryen ƙarshe: Ko dai a rasa komai, ko kuma ta kafa mulkin duhu har abada. Sai dai kuma... har yanzu Miemie bata ƙara bayyana ba. Kuma ikon haske yana ƙara ƙarfafa ne a cikin zukatan masu gaskiya..... ★★★★★ Nasreen tana kwance a cikin dogon baccin ta tayi wani irin mafarki mai razanar wa, a gigice ta farka daga bacci tana ambaton sunan Abeesh, tana sakin numfashi a tsorace domin tinda tayi hatsarin mota daga lokacin bata ƙara sanin yanda kanta yake ba sai yanzu, yanzun ma babu Madam Nablah ne yasa har tayi saurin farka wa amma itama Nasreen ba yanzu ake son ta farka ba..... Nasreen haka take bin ɗakin da take da kallo, a fili ta ce: "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, kulli nafsin zaa'ikatul maut, ta tabbata da gaske na bar duniya kenam? domin nasan nan wurin da nake ba duniya bane, shikenam na bar wa Catrina Abeesh ɗina? Bai kamata na sadaukar da soyayyata wa shaiɗaniyar mace kamar ta ba, ga shi na mutu nabar mata shi, shin a wani hali Abeesh ɗina yake?...." Lokaci guda ta fashe da kuka, zuciyarta ne ya yi wani irin bugawa a razane take furta "Tasleem! kenam na bar ƴan uwana? Amma ina ji a zuciyata cewa babu kwanciyar hankali a tattare da ni, akwai abinda yake faruwa da gida, taya zan koma gida? Ina son komawa gida...." Sauƙo wa daga kan gadon tayi tana ƙoƙarin fita daga ɗakin, abinda ta tarar da waje ne ya tayar mata da hankali, ganin ruwa yana zagaye da gidan da take, babu hanyar tafiya iya ɗakin da take ne kawai yake tsakiyar ruwa, ga ruwan ba'a ganin ƙarshen sa..... Nasreen fashe wa tayi da kuka ganin babu wata mafita... Toshe bakin ta tayi da hannayenta tana jero addu'o'i, cikin ikon Allah idonunta suka sauƙa akan wani tsohon kole-kole wanda ba'a amfani da shi yanzu, da gudu ta isa wurin tana ƙoƙarin juya shi domin a kife yake..... Daƙer ta samu ta tura kole-kolen cikin ruwan itama ta shiga cikin, tana sanye da wata ƴar doguwar riga marar kauri, wanda ya tsaya a iya gwiwa, Sumar gashin ta kuwa a fake anyi mata gyaran gashi, domin Madam Nablah kullum a cikin kula da ita take, tana tsabtace ta sosai duk da dogon baccin da tayi... A firgice Nasreen ta shiga kole-kolen cikin ruwan da icen tuƙawa, haka take sauri zata bar wurin domin tsoro wurin yake bata, ko ɗan tsuntsu babu balle wani dabba ko mutum... Madam Nablah kuwa tana can tana tsare da Abeesh bata san cewa Masreen ta farko ba har tana shirin guduwa, Bayan awa guda Nasreen na cikin ruwa sai yanzu ta je tsakiyar ruwan, ba ƙaramin gajiya tayi ba sai haki take tayi, tayi tafiya mai nisan bala'i sosai amma duk da haka sai yanzu tayi rabin isa, ta tsaya tana hutawa har bacci ya ɗauke ta a cikin kole-kolen..... Har ta fara nisa a cikin baccin kamar a mafarki ta fara jin ƙarar ruwa, ita har ta manta a cikin ruwa take, ruwan da ba'a san ƙarshen zurfinsa ba, a hankali take ƙoƙarin buɗe Idanunta kwatsam idanuwanta suka sauƙa akan wani ƙaton abu a cikin ruwa yana yowa kole-kolen ta, da ta lura dakyau ta ga shark 🦈 ne mai irin wasu hakwara masu kaifin masifa, Nasreen ganin yanda Shark yake gudu a cikin ruwan yana nufo ta yasa ta hanzarta ta ɗauki matuƙin kole-kolen ta fara tuƙawa tana sauri-sauri gudu-gudu tsabar ta gama tsorata bata iya tsere wa Shark ba, haka ya iskota ya kafa bakinsa akan kole-kolen tare da kifar da shi, wani irin ihu Nasreen ta yi ta kife ita da kole-kolen ta... A ruɗe ta fara kokuwa da ruwa tana ƙoƙarin tsere wa Shark, tana gudu a cikin ruwa shima Shark yana bin ta da gudu, gudun shark ya ninka nata sosai nan danan Shark har ya iskota bata ankara ba, taji ya yi mata wani irin kyakkyawan cizo cinyarta wurin tsoka, wani irin gigitaccen ihu Nasreen tayi, kafin ta rufe baki har ya ƙara datsa mata hakwaransa har sai da ya kusan rabe mata ƙafa biyu ta wurin cinyarta, cikin ƙanƙanin lokaci ruwan har ya canza kalar jini, Nasreen ihu sau ɗaya ta ƙara daga nan ta sume a cikin ruwan, Shark har ya buɗe bakin sa zai datsa masa hakwara ta saitin wuyanta sai ga wata halitta ta bayyana mai jikin zinariya, kyanta ya wuce misali, tana sanye da kayan gold, sumar gashin ta kalar na gold, tana riƙe da dogon mashi mai baki uku, ta fito daga cikin ruwan tare da yin sama ruwa na bin jikinta sannan ta sauƙo kan ruwan tare da caka wa shark ɗin nan mashin kafin ya kai bakinsa saitin wuyanta, ta ɗago da shi sama tana tana zazzaro ido mai launin gold, cikin ɗaga murya take faɗin "Kasa na hallaka ka saboda rashin imanin ka, Ni ce sarauniyar ruwa kuma dole duk wani halittan cikin ruwa ya bi umarni na, ita ɗin ba azzaluma ba ce, ka hargutsa mun ruwa da jinin haske, ruwa ba ya karɓan jinin da aka zalunta saboda haka zaka hallaka gaba ɗaya...." Daga nan ta fitar da wani haske daga cikin ƙwayar Idanunta da shi ta tarwatsa Shark, babu ko burbuɗinsa... Daga nan Miemie ta kai idonta kan Nasreen tare da ɗagota ta hanyar haske sannan ta ƙara nitsewa da ita cikin ruwa, a cikin ruwan ta nufi yankin kogin haske wanda babu bil adama da zai iya bayyana a wurin, kuma ruwan baya karɓan duk wani azzalumi...... *ASSALAMU ALAIKUM* *BARKAN MU ƳAN UWANA, NA MANTA BAN SANAR MUKU AN KAI MINZALIN DA YA KAMATA ACE AN DAKATAR DA FREE BOOK BA, MUN SHIGA BOOK TWO DOMIN GEJIN BOOK ONE DAGA PAGE 50 NE, SAKAMAKON RASHIN SANAR MUKU YASA NA CIGABA DA BAKU PAID PAGE A MATSAYIN FREE, TOH INSHA ALLAHU ZUWA PAGE 10 ZAN TSAYAR DA FREE BOOK NA BOOK TWO* *ƊARI UKU NE A YANZU KOWA ZAI IYA FARA TURO KUƊIN BOOK ƊINSA NA HASKEN RUHI....* *NAGODE* *💋HASKEN RUHI💋* *🫀THE LIGHT OF THE SOUL🫀* It conveys a deep and spiritual meaning referring to the inner light, truth, or purity within a person. *WhatsApp 09065443871* *🌹 ASMEETAH WRITER 🌹* *BOOK TWO__________PAID_____₦300* Page 5 to 6 ✦ WURI A CIKIN TEKU — MASAUƘIN RUHI MAI GAGARA FAHIMTA Da suka shiga cikin ruwan, sai abin mamaki ya bayyana. Ruwan da ya kamata ya jika su — sai ya buɗe kamar ƙofar, yana kai su cikin wani babban haske. A cikin ƙasa, ba ruwa, ba laka. Wuri ne da ba a iya bayyana shi da kalmomi — wani ɗaki ne mai faɗi wanda yake a cikin zurfin teku amma ruwa baya shiga. Katangar ɗakin na lanƙwashe kamar gilashi, amma kana iya ganin kifaye suna yawo a waje. Gado mai taushi, labulaye masu launin turquoise, hasken zinariya da yake fita daga saman bango, ga iska mai ƙamshi mai kwantar da hankali.... Duniyar Sarauniyar Ruwa! Nasreen kwanan ta ɗaya ta farfaɗo, tashin ta ke da wuya ta tsinci kanta a cikin wani yanayi mai daɗin gaske, ganin ta a çikin ɗaki wanda ruwa ne a zagaye a wurin ga kyawawan kifaye da suke yawo abun burgewa, ɗakin sai walwali yake yana shining, abinda ya ƙara bata mamaki shine ganin babu wani rauni a jikinta, wurin da Shark ya ciza babu tabon kamar babu abinda ya sameta a jikinta, ta tsinci kanta cikin ƙoshin lafiya, miƙe wa tayi tsaye taje jikin ruwan da baya samun damar ratsowa ciki tasa hannu tana shafan kifayen da suke jiki.... Tana cikin kallace-kallace taji sassanyar murya ta bayan ta, da sauri ta waiwaya tana kallon Miemie dake zaune a bakin wani tsararren gado na gold, sai wani shining take, kana ganin ta kasan ba bil adama bace domin duk matan duniyan nan babu wacce ta kaita kyau, in ba wani ikon Allah ba..... MIEMIE ta ce... "Triplets daughter, fatan kin tashi lafiya..." Nasreen haka take kallonta cikin rashin sanin ko ita wacece... Ta ce "Wace ce ke!?..." Murmushi Miemie ta yi daga bisani ta ce: "Baki san komai game da ni ba, domin bakida alaƙa da yanda zaki sanni.....ita ƴar uwarki da ta kasance ɗaya daga cikin mu ta sanni domin tana ɗauke da littafin mu na hasken Ruhi, dole zata ji labari na ko da bata taɓa gani na ba, amma gani na ma sau ɗaya ta ganni domin ni mai iya ganina kai tsaye sai ikon Allah...." Nasreen cike da mamaki take faɗin: "Kina nufin ke ma Sarauniyar wata jinsi ce?..." Miemie ta ce: "Tabbas! Sarauniyar Ruwa..." Nasreen bata san lokacin da ta tsinci kanta a cikin farin ciki ba, domin tasan ba wurin da zata sha wahala ta zo ba.... Miemie ta miƙa mata hannu ta kuma cewa: "Na ganki kafin ki bar gida, Nasreen. Zuciyarki ta ƙira ni... yanzu lokaci ya yi da za ki huta." Nasreen bata yi magana ba — ta ɗan girgiza kai kawai, hawaye na bin fuskarta... Miemie ta kama hannunta, sannan ta zaunar da ita... Nasreen ta tsaya tana kallon komai da hawaye — wannan masauƙi ba wurin firgici bane, ba wurin ƙaura bane — wurin kwanciyar hankali ne da ta dade tana nema. Miemie ta kalleta da murmushi sannan ta ce: "Ki huta. Ki wanke zuciyarki da kuka idan kina so. Amma ki sani — ba komai ke ƙarewa ba. Wasu lokuta tafiya ce kawai ta canza hanya." Nasreen ta kwanta akan gado, Ruwan sama na ci gaba da tafiya a waje, kifaye na wucewa da annashuwa. Idonta na rufe a hankali, zuciyarta na raguwa da nauyi — wannan daren ba zai ƙare da kuka ba.... Ranar ta waye cikin kwanciyar hankali ga Nasreen. A karon farko tun bayan aurenta, ta farka ba tare da kuka ko tsoro ba. Wurin da take kwana kamar mafarki ne — kamar wata duniya da aka adana domin masu yawan zubar da hawaye. Miemie ta kawo mata abinci mai ƙamshi, sannan ta zauna gefenta tana faɗin: "Zuciyarki tana bukatar lafiya kafin komai. Amma kin cancanci a ƙaunace ki gaba ɗaya ba rabin zuciya ba. Kuma Abeesh... ba zai fahimci darajar ki ba sai ya rasa ki." Nasreen ta lumshe ido da hawaye masu ɗumi. Har yanzu, tana ƙaunar mijinta, a koda yaushe tunaninta baya wuce akan Abeesh, bata san a wani hali yake ciki ba, ta bar shi da Catrina amma daga nan bata san komai akan abinda ke faruwa ba... ★★★★ A rana ya ta yau Madam Nablah ta shirya zuwa yankin da ta ajiye Nasreen, a yayin da ta bar Abeesh a tsaunin da ta ajiye shi, sai dai kuskuren da ta yi shine Catrina ta san a yanda Abeesh ya ke, hakan yasa Catrina itama ta yanke shawarar ɗauke Abeesh, hakan kuwa akayi, bayan tafiyar Madam Nablah, Catrina ta sace Abeesh ta tafi da shi can duniyar ta na duhu, wanda ba wani bil adama da ya isa ya shiga sai da izinin ta, har zuwa yanzu Abeesh bai farfaɗo ba.... Madam Nablah zuwa yanda Nasreen take ke da wuya, tana zuwa ta tarar da gadon da take kwance empty, ƙirjinta ne ya yi wani irin bugawa da ƙarfin gaske har sai da Idanunta suka koma kamar na garwashi tsabar fargaba, haka ta fara dube-dube amma ba labarin Nasreen! fita bakin ruwa tayi tana lelleƙa ruwan dake zagaye da ɗakin amma ba motsin ta, lumshe idanuwanta tayi tana hasasho ƙasin ruwa ta ko ina kota faɗa ciki amma babu komai a cikin ruwan sai baƙaƙen halittun ruwa... Madam Nablah wani tsafi tayi sai ga wani madubi ya bayyana a gabanta, tana son ganin a yanda Nasreen take, amma wani abun mamaki bata iya ganin yanda Nasreen take ba, domin an toshe hanyar yanda baƙin ruhi zai ga sirrin duniyar ruwan Miemie... A fusace Madam Nablah ta rausa ihu tana faɗin: "Kuna ina ne baƙaƙen halittun ruwan nan?....duk ku fito ina son ganin ku yanzu...." Sai ga halittun ruwan sun fara bayyana marasa daɗin gani, tsabar yawan su bazasu ƙirgu ba, baki a haɗe suke faɗin: "Ga mu mun bayyana a gabanki ya sarauniyar wuta..." Madam Nablah tana huci ta ce: "Me ye amfanin ku a cikin ruwan nan in har zaku bar bil adama ta tsere muku?....shin tana inaaa? ta ya zata bi ta ruwa ta tsallake tarkona?..." Suka ce: "A gafarce mu Sarauniyar wuta, wacce ta fi ƙarfin mu ce ta bayyana ta ceceta, amma ba don ita ba bil adama bazata tsere mana ba...." Madam Nablah ta ce "wace ce ta bayyana a cikin tsauni na, nan tsaunina ne babu wata halittar da take da ikon bayyana ko ina wacece, ko aljana ko mutum, nan ɗin masaraunta na ne...." Ta ƙara sa tana ɗaga murya cikin ɓacin rai... Aljanun ruwa suka ce: "Wacce ta ke da iko akan faɗin ruwan duniya da wajen duniya ce ta bayyana, Sarauniyar mu na ruwa, duk da mun kasance baƙaƙen Aljanun ruwa amma babu da ikon dakatar da ita...." Madam Nablah ta ce: "Kuna nufin ku ce Sarauniyar ruwa ce ta ɗauke mun ɗiya? amma wannan ruwan yankin nan nawa ne ba nata ba..." Aljanun suka ce: "Kin manta ne amma ke sarauniyar wuta ce, baki da iko akan ruwa..." A fusace Madam Nablah ta ce: "Ku ɓace mun tin kafin na ƙone ku...." Nan halittun ruwa suka fara komawa cikin ruwa, suka bar ta da takaici, itama bata juma ba ta ɓace.... A wani tsaunin daji ta sauƙa domin bata da ikon zuwa duniyar Miemie dole ta haƙura ta jira lokacin da zata bayyanar mata da ɗiya... Yanda Abeesh yake ta nufa domin yau ta sha alwashin zata sadaukar da ruhi, ko Catrina ta kawo mata Abul tayi sadaukar wa da shi ko kuma ta yi sadaukar wa da Abeesh duk da tana jinsa a ranta amma hakan zata haƙura da shi......abinda ta tarar ne ya ƙara ɗaga mata hankali, ganin babu Abeesh a yanda ta ajiye shi kuma ta dasa masa baccin da bazai farka ba sai da ikon ta, amma da ta tuno da Nasreen itama baccin ta dasa mata kuma ta farka sai abun ya ɗaure mata kai, ganin babu Abeesh yasa ta saddaƙar domin a cikin wannan tsaunin babu yanda zai iya zuwa domin duk mallakin ta ne, tana iya ganin duk wanda ya shigo da wanda zai fita, lumshe idanuwanta tayi tana son ganin yanda Abeesh yake, a cikin kwakwalwarta ta ga Catrina tana ɗauke da shi ta hanyar iska ta ɓace da shi, da sauri ta buɗe idonta tana sakin numfashi, bata san lokacin da ta durƙusa a ƙasi ba tana faɗin; "Kin ci amanata Catrina! Kin yaudare ni Catrina!! Kin butulce ni Catrina!!! meyasa zaki ɗauke Abeesh alhalin ba jinsin ki bane, kin wuce duniyar ki da shi amma zan jarraba ikona ganin na dawo da shi, Indai ke ce bazan ji fargaban ratsa duniyar ki ba...." Wasu zafafan hawayen jini ne suke zuba a cikin ƙwayar Idanunta.... Itama lokaci guda ta ɓace sai ga ta a duniyar Catrina, sai kuma akayi rashin sa'a itama Catrina tana ɗauke da ƙarfin ikon da babu wani wanda zai iya shiga duniyar ta komen ƙarfin ikon mutum. Madam Nablah ba yanda bata yi ba don shiga duniyar Catrina amma ta kasa, tayi tayi ta haɗa da tsafi amma ta kasa da haka itama ta haƙura ta koma yanda ta fito... Catrina tana cikin tsararren gidan ta a cikin ɗaki tana kwance a gefen Abeesh da yake kan bacci har yanzu, ta san da zuwan Madam Nablah amma bata bayyana ba, murmushi tayi tare da faɗin: "Devil Mom kina tunanin ke kaɗai kika iya wasan? kina tunanin ke kaɗai kike da ƙarfin iko? to kinyi kuskure domin nan duniyata ne, bazaki iya shigo wa ba, kuma Abeesh nawa ne babu mahalukin da ya isa ya karɓe shi daga hannuna ko waye shi, zan Aure shi, zan mallake shi sannan zai zama jinsin Aljanu shima...." Wani ƙayataccen murmushi ta sau kan ta akan ƙirjinsa.... Madam Nablah ganin abubuwan da ta tsare su na kuɓuce mata ne yasa ta yi saurin zuwa yanda Tasleem take domin itace babbar matsalar ta shiyasa ta tsareta a wurin da babu wanda ya isa ya je... Tasleem tana can cikin ɓoyayyen kogi a ƙasar duhun ƴan tsafi, inda babu wani haske ko numfashi ke isa. Madam Nablah ce ta bayyana mata, ta kalle ta da tsantsar takaici sannan ta ce: "Ke ce kaɗai za ki iya lalata abin da na ginata tsawon shekaru. Don haka za ki zauna a nan har sai lokacin da numfashin Amaar ya ƙare." Tasleem na kuka tana ƙiran sunan Amaar da karfin hali, amma muryarta na nutsewa cikin ruwa mai tsafin mantuwa. ★★★ Amaar! a gefe guda, ya rasa nutsuwa. Ya yi ta neman Tasleem amma bai ga wata alamar inda ta shiga ba. Zuciyarsa ta karye. Yana tunanin ashe soyayyar da ya fara sake gina wa zata sake dusashewa?... Yana tare da mahaifinsa, yana zazzagar hawaye da zuciyarsa mai rauni ya ce: "Na rasa Tasleem, Abul. Na yi rantsuwa zan kare ta – amma yanzu…" Abul cikin kyarma domin tsufa ta kama shi sosai ya ce: "Wataƙila ba ka rasa ta ba, Amaar. Wataƙila akwai hanyar da za ka same ta – sai dai sai ka sake buɗe zuciyar ka ga tsafi da haske." Amaar cikin rashin fahimta ya ce: "Ban fahimta ba Abul..." Abul ya sau numfashi tare da faɗin: "Zaka fahimta in har kana son ceto abar ƙaunarka..." A cikin ruwan da babu haske, inda hatta rana ke kasa haskakawa, Tasleem na kwance cikin wani ƙaramin ɗaki na ruwa, ƙafafunta an ɗaure su da sarƙar ruhi – wacce ba a iya yankewa sai da zuciya mai gaskiya. Kuka ya ƙure mata, amma zuciyarta na da ƙarfi fiye da yadda Madam Nablah ta zata. Tana faɗin: “ Ya Amaar… Zan dawo gare ka. Idan har zuciyar ka na raye da ƙauna ta... Zan ji numfashinka da yardar Allah....” Madam Nablah tana zaune a cikin masarautar ta dake yankin ta, lissafi yana shirin jagule mata, tana cikin nazari sai agogon hannunta ya fara ƙara, cike da mamaki Madam Nablah ta kalli agogon hannunta domin ta saita wannan agogon bazai taɓa yin ƙara ba sai wani da dalili.... Zaro ido Madam Nablah ta yi tare da washe baki, bata san lokacin da ta kurma ihun farin ciki ba, har sai da Kura da zakin gefenta suka tsorata, suma haka jikinsu yake ci da wuta tsabar an ƙera su da wuta ne, Madam Nablah miƙe wa tayi tana taka rawa da girgiza wutar jikinta na tashi sama, wasan wuta ta fara yi tana furtar da wuta a bakinta, haka jikinta yake ci da wuta duk na farin ciki, Ɗaga hannunta tayi sama tana kallon sama tare da faɗin: "Godiya da jinjina ga shugabana ZULQARNAIN!.....An samu babban rabo a sashen ɗiyata Asmeen da Shapreen, zan zama sarauniyar da babu kamar ta a faɗin duniya, Asmeen ta samu ƙaruwar jariri, a wannan rana ya ta yau...." Farin ciki marar misaltuwa ne yake wanzuwa a zuciyar Madam Nablah, duk wani ƙunci da damuwa sun wanke a zuciyarta....." A fili take faɗin: "Yanzu zan koma duniyar mutane domin ganin abinda yake faruwa a sashen gidana, zan ga lafiyar Asmeen sannan zan bata kariya sosai..." Tana kaiwa nan ta ɓace a cikin wuta, bata tsaya a ko ina ba sai a duniyar mutane a wani filin da ba mutum ko ɗaya... A bakin titi ta tsaya ta ƙira number security gidanta, kafin nan da ƴan mintuna sai ga zafafan motoci sun zo ɗaukar ta.... A babban falon gidan Madam Nablah Asmeen da Shapreen da Amaar da Abul ne suke zaune, suna tattaunawa akan ɓatan yaran gidan, Tasleem da Nasreen da Abeesh... Duk basu san cewa Madam Nablah tana hanyar dawowa ba, har ta shigo gida babu wani ƙara ko alamar tsayuwar mota, tana fito wa daga cikin mota ta nufi ciki.... A mashigar falo Madam Nablah ta saurari tattaunawar su, Abul yana buɗa musu hanyar da zasu samu Tasleem, yana nema musu mafita.. “A cikin zurfin ƙasar da ke ƙarƙashin wuta, akwai wani Malamin da zai iya tona asirin ruwan tsafi. Sai dai wajensa cike yake da haɗari, kuma babu wanda ke iya zuwa wurin sai da ni'imar gaskiya.” Amaar ya kalli mahaifinsa ya ce: “Idan wannan ne hanya guda don in dawo da Tasleem, to ni zan tafi.” Shapreen ya ce: “Ba za ka tafi kai kaɗai ba. Ni da kai zamu je. Na samu ɗaukakan haske daga wurin Asmeen, itama tasan da hakan, zamu tsire da yardar Allah.....” Madam Nablah dake leɓe a bakin ƙofar falo duk ta saurari shirin su, basarwa tayi tare da shiga falon da murmushi akan fuskar ta, da sallama a bakin ta... Asmeen dake zaune ganin Madam Nablah yasa ta miƙe da gudu ta je ta rungume ta tana faɗin: "Oyoyo Mommy! Mommy ina kika je haka tsawon watanni bakya nan, kuma bamu san inda kika je ba..." Madam Nablah tana shafa fuskar ta tace: "Yanzu ga shi na dawo ai, bazan ƙara tafiya na barku ba rabin raina..." Asmeen ta ce: "Mommy baki san abubuwan da suke faruwa ba, nayi ta neman wayanki bata shiga..." Asmeen ta fashe da kuka... Madam Nablah cikin damuwa take faɗin : "Me yake faruwa ne Daughter?..." Ta nuna kamar bata san komai ba... Amma Abul da Amaar da Shapreen duk sun san cewa tasan abinda yake faruwa duk da bata nan... Asmeen tana kuka tana faɗin: "Mom! Nasreen tayi hatsari ta mutu, ga Yaya Abeesh shima an rasa shi ko labarinsa babu, itama Tasleem babu sake jin labarinta ba, shin me yake faruwa ne?..." Madam Nablah ta ce: "Whatttt? me ya faru da su haka?..." A lokacin da aka sanar Tasleem ta bace, Madam Nablah ta nuna alhini da mamaki kamar kowanne mutum. Amma a zuciyarta, tana jin daɗin cewa ta hana soyayyar Amaar girma – domin Tasleem na zama barazana ga ikonta. Sai dai ba ta san cewa a gefe guda, Shaprees ya gano inda ta ɓoye Tasleem. Amma bai sanar da kowa ba, domin yana shirin ya taimaka a sirrance. Asmeen ta ce: "Duk bamu sani ba Mommy..." Madam Nablah jan hannunta tayi suka je su ka zauna, duk babu wanda ya mata magana a cikin su, itama Madam Nablah binsu tayi da ido ba tare da ta furta komai ba... Asmeen ta kalli Shapreen ta ce: "Ya Shaprees baka ga mommy ta dawo bane?tsawon watanni bata nan amma yanzu ta dawo baku nuna farin cikin ku ba...." Shaprees yana hararar Madam Nablah ya ce: "Ba'a irin waɗannan ake nuna farin cikin dawowar su ba, sai dai ayi baƙin ciki domin Annoba ta dawo..." Ya kalli Madam Nablah sannan ya ce; "Kada ki nuna pretending akan baki san abinda yake faruwa a gidan nan ba, domin nafi kowa sanin halinki, da kuma ƙarfin tsafin ki...." Asmeen a fusace ta ce "Ya Shaprees ya isa haka, mahaifiyata ce fa kake faɗa mata maganganu son ranka, oh wato ta gama maka amfani da ta Aura maka ni koh?..." Shaprees ya ce: "Tin kafin kisan waye ni nasan Mahaifiyarki, kuma tin kafin kizo duniya nasan wacece ita, don haka ko me na ƙirata ta cancanci haka domin ita baƙar Annoba ba, wanda bata ƙyale ƴaƴanta ba ma balle wasu, idan baki sani ba mahaifiyar ki ce ta kashe mun matata mafi soyuwa a cikin zuciyata, sannan ta Aura mun ke akan wasu dalilan ta da ƙara ƙarfin ikon ta, jira take ki samu ciki tayi sadaukarwa kuma lokaci ya yi, tasan cewa yanzu kinada ciki shiyasa ta dawo, kuma Tasleem a hannunta take, haka Nasreen da Abeesh...." Madam Nablah tana zaune bata ji komai a ranta ba don Asmeen tasan ko ita wacece domin sauran ma sun sani, ita kaɗai ce aka bari a duhu... Asmeen ta kalli Shaprees dakyau sannan ta ce "Duk waɗannan maganganun ƙarya ne, kunyi don ku tozarta mun uwa, kuma a yanzu nake so ka bani takardar saki na Shaprees...." Shaprees ya ce: "Idan har kika rufe bakin ki akan maganar saki to zan baki kariyar da bazaki taɓa faɗawa cikin tarko ba..." Madam Nablah kanta a sunkuye ta ce wa Asmeen "Daughter kada ki tsaya ɓata yawun bakin ki, a yanzu inason Shaprees ya rubuta miki takardar saki ko kuma mu bar musu gidan..." Asmeen ta fuskanci Shaprees sannan ta ce: "Ka bani takardar saki na Shaprees tin kafin duniya tasan da zaman mu, domin zan maka wulaƙancin da baka yi zato ba, nasan wacece mahaifiyata amma bazan taɓa yadda cewa ƴan uwana a hannunta suke ba, kuma bazan juri ganin kana wulaƙanta mun uwa ba...." Sai a lokacin Amaar ya buɗe baki ya ce wa Asmeen, "Yana dakyau ki kulle wannan bakin nakin tin kafin ke ma ki faɗa tarkon da ba tsira, saboda na fahimci kinada ƙaramar ƙwaƙwalwa, su ƴan uwanki da suke da tunani mai kyau ai sun fahimci komai...." Asmeen ta buɗe baki zata yi magana Amaar ya darara mata tsawa, tare da faɗin "Ki mun shiru, ki nemi wuri ki zauna..." Asmeen ta zauna domin tana shakkar Amaar.. Amaar ya kalli Madam Nablah sannan ya ce: "Idan kin dawo ne don saboda wani iko naki to ki sani komai ya Kusan zuwa ƙarshe..." Madam Nablah tana zaune ita kaɗai sai dariya take ta yi....gaba ɗaya ta mayar su mahaukata. Amaar ne ya ɗago da Abul suka wuce cikin ɗaki, shima Shaprees miƙewa ya yi tare da barin falon, Asmeen ce da mommynta kawai suke nan... ★★★★ A daren yau zuciyar Amaar na ci gaba da girgiza. Tasleem ta ɓace kamar ba ta taɓa kasancewa ba. Sun duba ko’ina Sun shiga duhu da haske. Amma ko alamar sawunta babu. Amaar ya tsaya a bakin ɗakin mahaifinsa, yana duban sa cike da damuwa ya ce: “Na ji kamar ta ƙira sunana a cikin mafarki jiya… amma lokacin da na farka, shiru kake ji. Kamar zuciyata ce ke ƙaryata ni.” Abul yadafa kafadarsa ya ce: “Wasu mafarkai sune gaskiyar da ba za mu iya fassara ba tukuna. Amma kada ka bari bakin ciki ya cinye ruhinka, na fahimci ƙauna ta mamaye zuciyarka har ta kai ga kana ƙoƙarin mance sauran ƴan uwanka, Abeesh da Nasreen, Tasleem yanzu kawai ka sani...." Amaar ya zauna kusa da Abul sannan ya ce . "Abul… ko ka san wata alama da zata taimaka mu wajen gano inda aka ɓoye Tasleem?" Abul ya lumshe ido tare da faɗin: "duk shirin da mukayi nasan Nablah taji komai don haka baza muyi amfani da wancan ba, Idan har zuciyar wadda take da alhakin hakan ba ta karye ba, to sirrin zai ci gaba da ɓoye kansa. Amma akwai wata… wadda ta san wani abu." Amaar ya ƙafe shi da ido ya ce: "Wacece?" Abul ya juyo ya ce da ƙarfi: "Tasleem!" Amaar ya firgita. "Ka ce… Tasleem? Amma ai ita ce aka sace!" Abul ya ce: "Ina nufin… ita kaɗai ce ta san inda za a fara neman kanta. Sai dai kafin hakan… sai an buɗe wani sirri da ke tsakanin dangi." Cikin wannan rikici ne aka bar Amaar da tambayoyi... ★★★★★ A cikin wani wuri mai zurfin ruwa, inda rana ba ta taɓuka komai, kuma iska ba ta motsawa, Tasleem na zaune cikin wani irin ɗakin tsafi wanda aka gina shi da ruwan tsafi masu hasken shuɗi da kore. Hannayenta da kafafunta an daure su da sarkoki na sihiri waɗanda ke hana ta motsi da karfi. Kamar kullum, Madam Nablah ta shigo, cikin baƙar rigar tsafinta, tana murmushin mugunta. "Kin ga yanzu kin dawo inda kika fara." Cewar Madam Nablah tana ɗaukar wani ƙwarya. Tasleem ta ƙafe ta da ido, cike da hawaye da ƙiyayya. Ta ce: "Kina tunanin hakan zai hana su nemo ni? Amaar ba zai taba barina ba." Madam Nablah tayi dariya sannan ta ce: "Amaar…? Shi da yake neman wata hanya ta ceton kansa da mahaifinsa? Ko Shaprees da ke cikin tarkon sihiri? Ko Asmeen da zuciyarta ke da sanyi kamar dusar ƙanƙara?" Ta yi dariya sosai har ta durƙusa a gaban Tasleem ta ce: "Dukansu ba za su gane inda kike ba… sai na kammala abin da na fara shekaru ashirin da suka wuce." --- A gefe guda, Shaprees yana tsaye a gefe yana karanta wani litattafan sihiri da ya mallaka tun kafin ya shiga duhun Madam Nablah. Sai kuma Asmeen ta shigo, cikin mayafinta na gida, da kallo mai cike da damuwa. Domin tinda Amaar ya sanar mata wasu abubuwa gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, sannan tana neman ƙarin bayani a gurin Shaprees... Ta ce: "Na gaji da zama cikin wannan gida na sirri da ƙyale-ƙyale… Ka gaya min gaskiyar zuciyarka, Shaprees." Ta faɗa cikin ƙarfi. Shaprees ya kalle ta, ido cikin ido ya ce: "Zuciyata... cike take da raunuka, Asmeen. Amma na rasa yadda zan yaye su ba tare da na jawo miki ciwo ba." Asmeen ta je kusa da shi ta ce: "Idan gaskiyar ka ce… sai mu nemo mafita tare." Ya kalli fuskarta da ta cika da karfin hali ya ce: "Kin cancanci gaskiya… Amma ki shirya da abin da zaki ji. Domin akwai sirrin da na ɓoye—wanda zai iya karya zuciyar ki." --- Amaar yana zaune a ƙaramin lambu shi da Abul domin baya son barinsa shi kaɗai especially yanzu da Madam Nablah ta dawo... Abul yana jan carbi, shi kuma Amaar Zuciyarsa na can, a cikin ruwan duhu, yana ƙiran sunan Tasleem a zuciyarsa.... "Idan har zuciyar mutum biyu sun haɗu cikin gaskiya," in ji Abul ya ce: "ko sihiri ba zai iya raba su ba. Amma sai zuciyarka ta zama daurarriya da gaskiya da himma.".. Amaar ya ɗaga kai, yana kallon rana da ke fitowa daga bayan gajimare. Wani sabon haske ya haskaka fuskarsa. Ya ce: "Zan nemi Tasleem ko da yaushe, ko da me zai biyo baya.....Auren zuciya ba ya mutuwa, Soyayya ta gaskiya sai da sadaukarwa.”... Har suka ƙarashi zaman su a lambu suka tashi, don komawa cikin ɗakin su... A koda yaushe Madam Nablah idonta akan Abul amma sai dai Amaar ya kasa barin yanda Abul yake, kamar wanda yasan ana harin sa.... Amaar ya zamo mai gadi baya bacci kullum, ga damuwar da ya sako shi a gaba, yana so ya motsa don neman ƴan uwansa amma yana fargaban barin Abul... A Daren yau kamar kullum zuciyar Amaar ba ta da natsuwa kwata-kwata. Yana kwance kusa da mahaifinsa, wanda yanzu ya fara murmurewa daga dogon jinyar da ya shafe shekaru a ciki. Idanun Amaar sun kasa rufuwa, kalmar "Tasleem" ce kawai ke yawo a zuciyarsa kamar sautin kiɗan da ke ƙara karfi a kunne... Yana maganar zuci: "Me yasa kika tafi haka, Tasleem? Ina kike?" ya furta ƙasa-ƙasa, yana ƙoƙarin hana hawaye zubo masa. Bai san me yasa zuciyarsa ke masa kamar tana numfasawa da nata numfashi ba, kamar zuciyarsa da ta Tasleem sun zamo guda.... Ga damuwar rashin Abeesh duk suna cikin zuciyarsa.. Nasreen kuwa an sanar cewa ta mutu amma basu ga gawarta ba hakan yana ɗaure masa kai...... *💋HASKEN RUHI💋* *🫀THE LIGHT OF THE SOUL🫀* It conveys a deep and spiritual meaning referring to the inner light, truth, or purity within a person. *WhatsApp 09065443871* *🌹 ASMEETAH WRITER 🌹* *BOOK TWO__________PAID_____₦300* Page 7 to 8 Nasreen tana zaune a gefen tekun da ke zagayen. Ruwan yana ɗan juyawa, rana na faduwa daga nesa. Gidan ruwa da Miemie ta gina mata yana nan cikin nutsuwa, duk da a zurfin ruwa ne amma ba danshi a jikinta, ba sanyi, ba tsoro, sai annuri. Miemie tana tsaye daga nesa tana kallon ta. Ita kaɗai ce ta san hakikanin abin da ke faruwa a gidan Madam Nablah, kuma har yanzu bata ce uffan ba. Miemie a zuciyarta take faɗin: “Zuciyar Amaar na ƙirana kullum, zuciyar Tasleem tana kukan gajiya da tsaro, zuciyar Abeesh na nadama da kasancewa da baƙar Aljana. Amma wannan faɗan na yara ne…” Nasreen ta lumshe ido. Ta yanke shawara: bazata dawo ba. A ganinta, komai ya ƙare kuma ta fi samun kwanciyar hankali da Miemie.... ★★★★★ Amaar ya tashi daga shimfiɗar da yake a cikin ɗakin yana kallon mahaifinsu da ke numfashi cikin daidaito, amma duk da haka ba ya jin daɗin gidan da yake cike da duhun sirri, da numfashin damuwa, ya zame masa barazana. Daga kowane bango sai ya ji kamar murya ce na Tasleem tana kiransa cikin rauni, tana kiran sunansa a hankali. Ya fita waje don samun iska, amma iska ma kamar ta ƙi karɓar shi. A hankali ya zauna bisa dutsen ƙasa kusa da wani tsohon itace yana kiran sunan da zuciyarsa ke bugawa da shi. "Tasleem... Ina kika je? Kalli zuciyata yanzu, ta rame, ta yi ɗumi kamar asubar da ba ta da rana." --- A can cikin wani wuri mai zurfi, ƙarƙashin ruwan sihiri wanda babu rana, babu wata, Tasleem ta buɗe idanuwanta cikin rauni. Tana kokarin tuna yanda aka kawo ta nan, amma tunaninta yana ba ta sarkakiya. A kusa da ita, wata tsohuwar ƙugiya ce ta rufe ƙofar kogon ruwan. Wani murya a cikin ranta ke faɗa mata: "Ki dage, ki nemi mafita, saboda soyayya da kauna na gaskiya ba ta mutuwa cikin wahala." Tasleem ta kwanta, hawaye na zubo mata. Amma zuciyarta bata yarda da duhu ba. Ta san cewa akwai wanda ke nemanta, wanda zuciyarsa zata iya bugawa da nata... A hankali ta furta "Ya Amaar, ka bar ni ne, ko kuwa?..." ta furta a ƙasan murya, kamar numfashinta ya ɗauke da bege. ___________________★★★ A gefe guda, Madam Nablah ta na satar kallon ruwan sihiri da ke ɗakin sihirinta. Tana murmushi a hankali tana kallon Tasleem da ke kwance cikin wancan wurin sirri. Cikin izzah ta furta "Kin ga yadda nake tafiyar da al’amura ko? Babu wanda zai iya gano yanda kike. Kuma kafin komai ya bayyana, zan mallaki zuciyoyin da nake buƙata.....Ba wanda zai iya shigowa, balle ya cece ki... Sai ni kadai," ta faɗa cikin dariyar mugunta. "Amaar da zuciyarsa mai tsarki, ba zai taɓa gane ina ba. Kuma kafin ya gane, zan canza tafiyar duniyar nan gaba ɗaya." Washegari, garin ya farka cikin sabuwar rana, amma zuciyar Amaar tana ci gaba da ɗauke da rana. Ya zauna kusa da mahaifinsa yana kallon fuskar tsohon cikin kwanciyar hankali. Ya ce,: "Abul..." Amaar ya furta cikin murya mai taushi. "Shekaru ashirin da suka gabata, ban san kana raye ba. Amma yanzu da na sanka, sai zuciyata ke so ta bayyana komai. Amma me zai faru idan sirrin nan ya ɓalle gaba ɗaya?" Abul bai ce komai ba, sai ya ɗaga hannu a hankali, kamar yana so ya taɓa fuskarsa. Amaar ya kama hannunsa, yana jin wani sanyi mai kama da ta'aziyya ya lullube shi. Kamar hannun mahaifi yana ƙarfafa masa zuciya: "Ka nemi abinda ya ɓace... Ka cece ta kafin dare ya mamaye komai, domin ita ɗin Hasken ruhi ce..." Amaar ya lumshe idanuwansa yana faɗin: "Na rantse da mahalicci na, albarkacin soyayyar mu... Zan same ki Tasleem. Ko da kuwa zan faɗa cikin ruwan da ba mai tsira." Bayan kwana biyu.... Falon Madam Nablah ya ƙayatu da fitilun kristal masu walƙiya, kowane lungu da saƙo ya sha ado kamar ana shirin babban taro. Amma ba shagali ake ba—damuwa da shiru sun mamaye zuciyoyin kowa... Ana Alhinin rashin ƴan uwa wato Tasleem da Abeesh da Nasreen har yanzu ba a samu labarinsu... Amaar yana zaune da Shaprees da Asmeen a gefe guda, Abul kuma yana room ɗin sa, suna zaune cikin yanayi na ɓacin rai. Madam Nablah dai tana ta danna wayarta kamar wacce bata damu da damuwar duniya ba... Kafin kowa ya iya sake numfashi, ƙofar babban falon ta buɗe da ƙara mai ɗaukar hankali. Kamar walkiya, wata haske mai launin ruwan sanyi ya lullube wajen na ɗan lokaci kafin ta bayyana... Gaba ɗaya suka ɗago kansu, suka sauƙe idanunsu kan wata kyakkyawar halitta da babu kamarta. Matar da ta shigo kyakkyawa ce tamkar ba a duniya ba, tana sanye da doguwar riga mai ƙirar gold, Sumarta doguwa ce kamar siliki tana lanƙwashe har gadon bayanta. Fuskar ta tsab ce, kamar ba'a taɓa samun ɓacin rai a rayuwarta ba. Idanunta shuɗa ne, amma suna da wata annuri da ke jan zuciya. Kamar ruwan rafi ne mai rai.... Amaar ya miƙe tsaye nan da nan. zuciyarsa ta ɗauki bugun farin ciki. A hankali, kamar yana magana da kansa ya furta: "Miemie..." Madam Nablah ta ɗago kai cikin tsoro. Ba kowa bace wannan da ta shigo—ita ce MIEMIE, Sarauniyar Ruwan Aljanu. Halitta mai iko da daraja a tsakanin makaman tsafi da haske. Miemie ta zauna cikin tsayin daka, tana kallon kowa cikin salama da iko. Cikin izzah take faɗin: "Lokaci ya yi da gaskiya za ta fara tunkarar haske," ta ce da murya mai laushi da raɗaɗi, kamar ana karanta waƙa a cikin ruwa. Shaprees ya gyaɗa kai a hankali, zuciyarsa na bugawa. Ya san wannan ba ƙaramin abu bane. Idan Miemie ta bayyana, to kuwa akwai gagarumin sauyi da zai zo. Madam Nablah kuwa ta ɓoye damuwarta tana ƙoƙarin murmushi, amma Miemie ta hango ƙiyayyar da take ƙoƙarin ɓoye wa. Miemie ta ce: "Nazo ne domin sauƙe nauyin da nake da shi tun shekaru ashirin da suka wuce... lokacin da aka jefa ƙaramin yaro cikin ruwan halakar tsafi, na ceci shi, na bashi kariya da haske. Wanda nake magana akai, shi ne... AMAAAR." Wata guguwa ta tashi a cikin zuciyoyin ɗakin. Kowa ya kalli Amaar, wanda yanzu yana fuskantar Miemie da idanu masu cike da alhini da tambayoyi. Miemie ta cigaba da magana: "Kuma yanzu na dawo... domin tsare zuciyoyin da haske ya taɓa. Ku shirya, domin akwai sirrin da zai girgiza kowa nan ba da jimawa ba." Wani irin sanyi mai daɗi ya bayyana cikin ɗakin lokacin da Miemie ta kammala maganarta. Kamar ana busa iska mai ƙamshi daga rafin aljanna, aka ji zuciya na kokuwa da ƙalubale da kuma tsoro. Amaar ya matso kusa da ita a hankali, idanunsa cike da tambayoyi. A yau ne ya sake ganinta a zahiri bayan shekaru masu tsawo da suka gabata, lokacin da yake ƙaramin yaro, yana cikin hadarin nutsewa cikin ruwan tsafi da Madam Nablah ta jefa shi. Sai Miemie ta bayyana wancan lokacin — kamar haske cikin duhu — ta fitar da shi, ta rufe shi da sihiri mai tsabta, wanda har yanzu ke yawo a jikinsa, duk da ba shi da cikakken sani akan hakan, amma tana yawan zuwa masa a cikin mafarki... A hankali ya furta: "Kina da labarin komai... kin san wacece Tasleem? Kin san inda take? sannan ƙanina Abeesh shima kin san a yanda yake? shin da gaske ke Nasreen ta mutu?...." Amaar ya tambaya da murya mai nauyin kewa. Miemie ta dubi kowane fuska kafin ta ce, "Duk da ikon da nake da shi a cikin ruwa da haske, ba zan iya nuna maku inda aka ɓoye Tasleem ba. Wannan sirrin na cikin zurfin duhu ne da aka ƙarfafa da jinin zuciya. Sannan Abeesh shima yana wani duniyar da banida ikon zuwa wurin Amma zan iya taimaka maku ku ji hanyarsu idan kun tsaftace zukatanku, kuma ku jure gaskiyar da zata bayyana." A wannan lokacin ne zuciyar Madam Nablah ta fara karaya. Ta san cewa idan Miemie ta shiga cikin lamarin, ba ruwanta da tsafi ko dabara. Tana ƙoƙarin ɓoye fargaba ne, amma idon Miemie — waɗanda suka fi ruwa tsarki — sun riga sun karanto dukan damuwar da ke ɓoye a zuciyarta. Madam Nablah ta ce: "Kin iso ne saboda Amaar? Ko akwai wata manufa?" Ta tambaya tana ƙoƙarin nuna ƙwarewa da sarauta.... Miemie ta ƙaraso kusa da ita, ta dubeta cikin idanunta masu ƙasaita ta ce: "Kin shafe shekaru da dama kina amfani da duka ikon da aka baku don girbe fansa da iko, amma kin manta... da tsarkin zuciya ake buɗe ƙofofin aljanna. Kuma idan zuciya ta ƙafe da ƙiyayya — to ruwan tsarki ba zai iya wanke ta ba." Sai ta waiwaya gun Shaprees, wanda tuni zuciyarsa ta fara kaɗawa. Ta ce da shi "Ka kasance kana da zaɓi: ko ka zaɓi bin gaskiya da haske, ko ka cigaba da ɓoye kanka a cikin ruwan duhu. Amma ka sani, ba za ka iya fansar matar da ka rasa ba ta hanyar cutar da wata ba." Shaprees ya sauƙe numfashi, ya kau da kai. Kalaman Miemie sun taɓa jikin sa fiye da yanda ya zata. A hankali ya ɗago yana kallonta— yana mamakin yanda wannan kyakkyawar halitta ke tafiya da ikon da ba mutum ke da shi ba, kuma bai taba ganin kowa yana karantar zuciya kamar yadda take ba. MIEMIE ta matso kusa da Amaar, ta ce a hankali: "Zan taimaka maka neman Tasleem. Komai zai iya faruwa, amma ina jin zuciyarka na ƙiranta da gaskiya. Kuma nasan duk inda take... tana fatan sake ganin ka." Miemie ta sake juyo wa ta dube su duka, sannan ta ce da murya mai ƙarfi: "Na bar haske a cikin ɗaya daga cikinku... wanda zai iya bayyana mafita daga duhun da Madam Nablah ta lulluɓe. Lokaci na kusa. Amma har yanzu akwai sirri mai girgiza zuciya da bai bayyana ba." Idanunta sun ɗan tsaya kan Amaar, ta ce: "Ka tuna hasken da ke cikinka, Amaar... shine zai tsine duhun dake kewayen zuciyarka. Kuma shine zai bayyana Tasleem." Asmeen kallon Mahaifiyarta kawai take, ganin ko wani magana idan ya taso akanta za'ayi... Madam Nablah, duk da tana ƙoƙarin nunawa kamar bata damu ba, amma jikinta yana rawa. Tana tsoron su sauka can inda ta ɓoye gaskiya da tarihi, inda ta adana wani sirri da zai iya rushe komai da ta gina tsawon shekaru ashirin. Zuciya cike da mamaki da firgici kowa ya kasa motsi a cikin falon. Bayyanar Miemie ta zame musu tamkar mafarki. Amma ga Amaar, tamkar wani kaho ne aka buga masa — kaho na kiran tarihi, na farkon rayuwarsa. Wata irin sanyi da haske ya lullube zuciyarsa yayin da yake kallon Miemie... Madam Nablah kuwa ta ƙafe Miemie da ido kamar yadda maciji ke kallon kwallon wuta. Tana jin wani iska mai sanyi yana ratsa ta, alamar cewa karfin da Miemie ke da shi yana cikin nau’in da ke rushe dukkanin duhun tsafi. Sai kawai Miemie ta furta da muryarta mai taushi da ƙarfi, “Lokaci ya yi.” “Lokaci na me?” inji Madam Nablah, tana ƙoƙarin ɗaga ƙirjinta da kangararta kamar yadda take yi a duk lokacin da take son rufe laifinta da iko. “Lokacin da gaskiya zata fara bayyana, ko da kuwa an binne ta cikin dutse tsawon shekaru.” Miemie ta ɗaga hannunta sama, sai wata iska ta kaɗa labulen falo, fitilu suka ɗan yi rawar jiki alamar wani abu mai girma yana gab da faruwa. Amaar, wanda yake ta kallo yana ci gaba da tuna wani abu daga rayuwarsa — ya tuna da ruwan da aka jefa shi a ciki lokacin yana yaro, ya tuna da hannun da ya zame shi daga halaka, ya tuna da muryar da ta ce masa “Zaka girma, zaka fuskanci duhu, amma ka kasance da haske.” Sai kawai ya furta, “Ke ce kika ceci rayuwata, ina matuƙar Alfahari dake…” Miemie ta gyada kai cikin murmushi. Sai ta juya ido zuwa ga Madam Nablah, sannan ta ce: “Na zo ne domin janye garkuwar duhu daga zuciyar ‘ya’yanki kafin abin ya kai ga wuce gona da iri.” Sai ta juya zuwa wani ɓangaren falon. Ta danna kafarta ƙasa sau uku, sai wani ginin ƙasa ya buɗe a hankali. Duk suka zuba ido. Akwati ne _ akwatin gawa mai ɗauke da tambarin tsafi da dutsen haske a jikin murfin sa. Kowa yayi shiru. Miemie ta ce: “ Madam Nablah... kin ajiye gawar mijinki shekaru da dama amma ki sani ruhi ba zai bar duniya ba, saboda tsafin da kika tofa masa kafin ki kashe shi.” Asmeen ta rausa ihu daga gefe, zuciyarta na harbawa. Ta ce: “Mahaifinmu? Ashe da gaske ne kina da ikon kashe shi?” Madam Nablah ta juya da hargowa. Tana faɗin: “Na yi hakan domin ikon da nake nema! Ku da kuke nan da babu shi, babu ni!” Amaar ya ƙureta da ido. Shaprees ya ƙafe ta da kallon da babu wanda zai fassara... Miemie ta durƙusa ta shafi akwatin — wani haske ya fito daga cikinsa... Mahaifin su... yana nan, gawarsa na kwance a cikin akwatin... Gaba ɗaya zaman falon ya koma shiru. Kamar an danna abin dakatar da lokaci, kowa na kallon akwatin gawar da Miemie ta bayyana. Haske yana ci gaba da fita daga cikin akwatin, yana fizgar zuciyoyi da nau’in sanyi wanda babu wanda ya taɓa ji. “Wannan shi ne mijinki, Madam Nablah. Wanda kika daɗe kina ɗauke da gawarsa don ki rufe laifinki. Amma ruhi ba ya mutuwa, musamman idan aka kashe shi da zalunci,” Miemie ta faɗi tana kallon Madam Nablah da idanuwanta masu zurfin gaskiya. Madam Nablah ta miƙe tsaye da sauri tana faɗin: “Ba laifi bane idan domin iko ne!” ta hargitse da murya tana kallon kowa da wani irin kallon hauka... “daman da gaske ke kika kashe mahaifinmu?” Asmeen ta furta da kuka murya na kakkarwa domin abun ya tsaya mata a rai, ta nufi akwatin da zafin zuciya tana fadin: “Kin ɓoye wannan shekara da shekaru, kin hana mu jin ƙaunar uba..” Shaprees ya ja baya a hankali. Ya riga ya san cewa Madam Nablah ba mace ce da za a yarda da ita ba, amma ya kasa tsammanin za ta aikata haka a mijinta, uban ‘ya’yanta! Amaar ya durƙusa kusa da akwatin. Ya kura wa fuskar mai kwance a ciki ido, kodayake an daɗe da rasa numfashi, amma kwanciyar fuskar da sakon ruhi da Miemie ke aika masa suna tada jinin jinƙai da mamaki. “Ya kamata a kawo ƙarshen wannan duhu,” Miemie ta ce, tana matsowa kusa da akwatin. Ta ɗauko wata ƙaramar ƙaho wacce ke haskawa da ruwan zinariya, ta zuba ruwa a jikin akwatin. Sai kuma wani abu ya fara girgiza… Kwatsam, sai jikin gawar ya fara fitar da haske – haske mai launin shuɗi mai ƙyalli – da kamar wani abu yana ƙoƙarin farka daga dogon barci! Gaba ɗaya suka miƙe tsaye da firgici, Asmeen ta tsaya jikin Shaprees... Miemie ta juya tana fadin: “Ruhi yana da ƙarfi idan aka kashe shi da zalunci. A yau, wannan ruhi zai ɗan farka — domin ya bada shaidar gaskiyar da kika ɓoye.” Madam Nablah ta ja baya tana girgiza kai tare da faɗin: “A’a, ba zai iya farfaɗowa ba! Na kulle shi da jinin kansa! Na ƙulle shi da alkawari da tsafi!” “To," inji Miemie, "da haske muke warware duhu.” A wannan lokacin aka fara jin muryar mutumin da ke cikin akwatin, yana fadin... “…Nablah... me kika yi min…? Ƴaƴana… Ina ku ke, ina son ganin ƴaƴana…” Asmeen ce ta fashe da kuka, haka Amaar Idanun sa biyu na cike da ƙwalla — suna kallon jikin mahaifinsu wanda tsawon shekaru suka rayu ba tare da saninsa ba... Kuma Tasleem — ita ce kawai ta san da wannan sirri… amma yanzu tana ɓoye a wani ɓangaren duniya da babu wanda zai iya ganinta. A nan labari ya ƙara ɗaukar sabon salo. Madam Nablah ta fara girgiza tamkar mai hauka. “Ku tafi! Ku barni! Baku fahimta ba, banyi hakan don son raina ba!!” Miemie ta kalle ta da murmushi mai taushi amma mai nauyin hukunci ta ce: “Kina da sauran damar tuba... Amma gaskiya ba zata ƙyale karya ta cigaba da mulki ba.” Falon ya yi tsit, kowa na kallon akwatin da Miemie ta bayyana. Cikin ɗakin akwai Amaar, Asmeen, Shaprees, a cikin wannan falo akwai wata zuciya wadda ke shirin fashewa da tsoro wato Madam Nablah... Suna cikin wannan halin Sai ga takun ƙafafu da numfashi mai nauyi yana karatowa daga saman beni. Kafin kowa ya gane me ke faruwa, sai ga tsohon mahaifin su Amaar, ya shigo cikin rawar jiki da hawaye a idanuwansa. Ya durƙusa a gaban akwatin, yana kallon fuskarsa cikin halin da ba'a taɓa ganin sa ba. Yana faɗin: "Ahmed..." ya furta da kyar, yana maimaita sunan. "Kai ne? Kai ne ƙanina da na rasa shekaru ashirin da suka shuɗe? Nablah... me kika yi masa?!" Kallon kowa ya koma gareta. Miemie ta ɗan matsa gefe, tana kallonsu cikin nutsuwa kamar wata sarki mai hukunci. Madam Nablah kuwa ta kasa motsawa. Sai idanuwanta suka haɗu da na tsohon mijinta cikin akwatin—mutumin da ta kashe saboda ya gaza amincewa da shaidanci da muguntar ta. Tsohon mijin da ta ɗaure da sihiri, sannan ta ɓoye gawar tasa a ƙarƙashin wani lungu na gidan da babu wanda ke iya ganowa. Asmeen ta shige jikin Shaprees tana hawaye.. Amaar kuwa ya ɗan matso kusa da mahaifinsa, yana kallon gawar mutumin – ƙanin mahaifinsa da aka kashe a asirce. "Wannan gawar... shi ne mahaifin su Tasleem, Nasreen da Asmeen?" Amaar ya furta da mamaki. Miemie ta jinjina kai tare da faɗin "Na kwance sihirin da aka ɗaura a jikinsa. Ya cancanci a girmama shi, ba a ɓoye shi cikin duhu ba. Amma akwai wata ƙarin asiri da ba a saniba..." Shaprees ya ɗago kansa da sauri, zuciyarsa na harbawa. Madam Nablah na nan zaune, ba ta motsi kamar wanda ruwa ya cinye, amma idanunta sun cika da wani irin ƙiyayya da tsoro na ɓoye gaskiya. "Wace irin halitta ce ke, har za ki aikata haka ga mijinta?" Abul yace, yana girgiza kai, yana mai tuna irin soyayyar da Ahmed ya nuna wa matarsa – amma a ƙarshe, ta ƙare da kisa.... Amaar ya matso kusa da Miemie ya ce: "Kina da ikon gaya mana gaskiyar komai yanzu, ko akwai wani abin da har yanzu ana ɓoyewa?" Miemie ta kalli Amaar, sai kuma ta juyo zuwa ga Madam Nablah. Sai ta ce da ita: "Na bar wannan dama a hannunki. Kifadi gaskiya da bakinki, ko kuma ni da hasken ruwa na mu karasa tone komai..." A cikin falon da aka cika da zazzafan numfashi, hasken Miemie na kara kyalli a tsakiyar dakin, sai aka ji tamkar duk iska ta tsaya. Idanun kowa sun zube kan Madam Nablah, wadda yanzu zuciyarta ke dukan ƙirjinta kamar za ta fasa. Kamar ba ita ba — uwar da ta jima da ɓoye gaskiya, da ɓoye jikin mijinta na tsawon shekaru, yanzu tana cikin fargaba tamkar wani ƙwararren ɗan laifi da aka cafke a wurin laifi. Amaar yana kallonta, yana ɗauke da tambayoyi a idanuwansa.... "Ki faɗi gaskiya yanzu!" inji Abul murya na ɓarke da ɗaci. "Me kike da shi a wannan lokacin? Me ya faru da ɗan uwana?" Madam Nablah ta ƙi kallon kowa. Sai dai ta ja tsaki ga taurin kai, ta ɗaure fuska ta ce: "Kuna so ku ji gaskiya? To ku saurara..." Sai ta tashi tsaye. Ta ɗan gyara mayafinta kamar wata sarauniya da ba ta yarda ta sunkuyar da kai ba, duk da an kama ta da laifi. "Ahmed ya yi kuskure. Na so ya bani ikon mulkin ruhin aljanu da sirrin nasaba... amma ya ƙi. Ya ce ba za a haɗa duhu da haske ba. Na gargaɗe shi, ya ƙi sauraro. Kuma saboda ƙin yarda da ikon da na samu, na kawo ƙarshen sa. Na kuma ɓoye gawarsa a ƙasan gidan nan domin kada wani ya san cewa ni ce na kashe shi." Zuciyar kowa ta ɗauki bugawa. Asmeen ta rufe fuska da tafin hannu. Shaprees ya ɗan jinjina kai, yana jin tsantsar muguntar da ke cikin zuciyar matar da har yanzu ba ta da kunyar bayyanar gaskiya. "Kin kashe mijinki?" Miemie ta furta cikin daƙilewar murya. "Kin hana 'ya'yanki su san yanda uba ke nan? Kin ɓoye rai da gaskiya saboda kuɗi da iko?" Madam Nablah ta saki murmushin ƙiyayya. "Ni Sarauniya ce. Kuma Sarauniya ba ta roƙon gafara. Ban taɓa nadama ba. Duk wani da ya tsaya a gabana, to ya sha keɓaɓɓen hukunci." Kamar wuta ta faɗa cikin zuciyar Abul mahaifin su Amaar. Ya juya da sauri ya kalli Miemie yana faɗin: "Kada ki bar wannan ta tafi ba tare da an hukunta ta ba!" Amma Miemie ta ɗan dafe ƙirji, sannan ta kalli Amaar da Asmeen da Shapreen ta ce: "Hukuncin wannan ba daga gare ni zai fara ba. Sai zuciyar 'ya'yanta da danginta sun gane hakikanin darajar abin da suka rasa." Nan take wata guguwa ta shigo cikin falon – amma ba iska bace – ruhi ne mai sanyi, mai tsarki, mai haske, wanda ya dudduba kowa ya shiga jikinsu kamar wani abun lura. Nan take kowa ya fara ganin hoto a zuciyarsa – na kisan Ahmed, na ƙiyayya da fushin Madam Nablah, da irin sihirin da ta taɓa yi. Sai Amaar ya ɗauki numfashi mai zurfi. Ya ce da Miemie: "Duk wannan... amma Tasleem ba ta cikinmu. Shin akwai alaƙa tsakanin abin da Madam Nablah ta ɓoye da ɓacewar Tasleem?" Miemie ta jinjina kai a hankali. "Wani ƙarin sirri yana jiranku... Kuma har sai kun nemi da gaske, za ku gano."... Cikin ikon Allah duk abinda ke faruwa Nasreen tana cikin tafkin ruwan MIEMIE tana kallon duk abinda ke faruwa a gidan su, domin Miemie ta bar mata wani madubi yanda zata na ganin video abinda ke faruwa, itama tana nan sai rausa kuka take tana Allah wadai da halin mahaifiyar su, har Idanunta sunyi jawurr.... Itama Tasleem Miemie ta san dabarar da tayi ta bayyanar mata da video abinda ke faruwa ba tare da sanin Madam Nablah ba, Tasleem tana zaune a ɗaure tana ganin abubuwan da ke faruwa, ga mahaifinsu da basu taɓa gani ba yau ya bayyana a matsayin gawa, tasha kuka itama kamar ranta zai fita.... Daga cikin numfashin duhu da tsantsar ruɗani, dakin falon gidan Madam Nablah ya shiga shiru mai nauyi. Miemie ta ɗan yi tsuru-tsuru da idanuwanta masu hasken ruwa, sannan ta juya ta kalli Amaar wanda zuciyarsa ke ƙuna da rasa ƴan uwansa da kuma mamakin makircin Madam Nablah. “Wannan gawar,” Miemie ta nuna akwatin da Ahmed ke kwance ciki, ta ce: “ba kawai jikin mataccen mutum bane. Wannan wuri da aka binne shi ya zama makabarta ce ta ƙiyayya da sihiri, soyayya da jinƙai.” Madam Nablah ta yi dariya mai sauti, tana takawa a hankali kamar wata zakanya mai jin ƙarfinta. “Gawarsa tana nan, so what? Kwana nawa zai canza rayuwar ku? Ko dai na kashe, ko dai na ɓoye – amma na rayu, kuma ina da iko!” Sai wani abu ya girgiza cikin falon. Tagogi suka fara motsawa. Fitilun ruwan hoda suka ɗan ɗauke, sannan aka ji murya – kamar ta sama, mai sanyi da mai nauyi: Ruhin Mahaifin su Tasleem ne ke magana yana faɗin: "Ba wanda ya mallaki zuciyar duniya. Ko kin kashe gaskiya, za ta dawo da rai. Kuma ko kin ɗaure sirri, dare zai zo da rana." Gaba ɗaya suka zuba ido suna kallon sama. Idanun Asmeen sun cika da hawaye. Shaprees ya rufe baki da tafin hannunsa, tamkar yana tunanin wani abu mai girma da ke dawowa masa a hankali. “Ya Allah…” mahaifin su Amaar ya furta. “Na bar ɗan uwana cikin mugun gidan mace da ba ta san mecece ‘yanci ba.” Miemie ta ɗan juya kamar wata sarauniya, ta miƙa tafinta zuwa ga Amaar, sannan ta ce da shi da murya mai laushi: “Idan kana son ku samu Tasleem, to sai kun zurfafa cikin ruwan da ke ɓoye mafita. Amma ku sani — ba ƙarfin jiki zai fito da ita ba, sai ƙarfin zuciya.” Amaar ya runtse ido. Wani zafi na tsananin ƙauna ya zuba masa a zuciya. Bai san yanda yake ji ba — kamar ruwa, kamar wuta, kamar iska. Amma ya san abu ɗaya: Tasleem tana kiransa, duk inda take. A gefe kuwa, Madam Nablah ta wuce zuwa ɗakinta, tana kuka… amma ba kukan nadama ba — kukan fushin da ta tsinci kanta a ciki. Ta na tafiya a hankali, tana jin Miemie ta zo mata da barazana. Kuma wannan ba zata yarda da shi ba. Ta rantse a zuciyarta tana faɗin: “Bari su ci gaba da neman Tasleem. Wuta ce za su tsinta a ƙarshe.” A wannan ranar ne aka sitirta Mahaifinsu Tasleem, Abul da Amaar da Shaprees ne suka yi jana'izar sa a cikin gidan ba tare da sun gayyato kowa ba, cikin dare suka je su ka binne shi.... Bayan sun dawo, Abul yana fama da zazzabin damuwa... Amaar wanda ke zaune a gefen mahaifinsa, yana lulluɓe shi da bargo. Kamar dare ne ya zo masa da nauyin tunani. Amma daga can cikin kunnensa, sai ya ji wata murya mai laushi tana cewa: Miemie ta bayyana cikin hasken ruwa a kusa da tagar ɗakin.. “Amaar, lokaci yana tafiya. Duk da an bayyana gawar da Madam Nablah ta ɓoye, akwai babban sirri da ke can cikin ruwan da ta kulle Tasleem.” Amaar ya ce: “Ina Tasleem take? Ina matata? Me ya sa zuciyata ba ta huta ba har yanzu?” Miemie ta ce: “Kuna bukatar ku shiga tafkin madalla da hasken rana — tafkin da babu wani sihiri da zai iya kare ku sai zuciyar ku. Amma sai kowa ya haɗa hannu — kai, Shaprees, Sirrin wannan tafki yana cikin zanen bango da ke ɗakin Madam Nablah.” Amaar ya zabura. Wannan zance ya birkita masa tunani, amma ya bashi ƙwarin gwiwa. Ya san lokaci bai da yawa kuma yasan ba zai bari Madam Nablah ta ci nasara ba. --- A wannan daren, Madam Nablah ta shiga wani ɗaki mai duhu a ƙarƙashin beni, ɗakin tsafinta mafi ɓoyuwa. Ta ɗauko wani kwanon ruwa mai haske, ta zuba wani ruwan tsafi a ciki. Ta ga fuskar Tasleem a ciki — tana kwance a cikin wata dunƙulalliyar madatsar ruwa, tana numfashi idonta a rufe. Madam Nablah cikin dariyar mugunta ta ce: “Ke Tasleem, ni na haife ki, ni kuma zan hukunta ki. Idan na rasa iko akan sauran ‘ya’yana — ke ba zaki gudu ba.” Washegari da safe ..... Amaar, da idonsa jajaye, ya fito daga ɗakin mahaifinsa. Kamar jarumin da ya taso daga makogwaron haske, zuciyarsa ta ƙazance da niyyar ceton Tasleem — ko da zai shiga ruwan kisa. Ya tunkari Asmeen a falon gaban gida, inda take zaune da kuka a gefen Shaprees. Su biyun sun rasa kwanciyar hankali tun bayan bayyanar gawar mahaifinsu. Amaar cikin murya mai ƙarfi ya ce: “Ya ishe mu zama shiru. Yanzu lokaci ne da zamu gane waɗanda muke da su, da waɗanda suke da mu.” Asmeen ta kalle shi, hawaye na zuba a idonta. Ta ce: “Ya ya zamu fuskanci uwa wacce ta canza mana rayuwa daga tushe?…” Shaprees cikin taushin murya ya ce: “Kuma ya ya zamu shiga tafkin da babu mai dawowa daga ciki — tafkin ruwan tsafi wanda ke ɓoye rayuka da yawa?” Sai aka ji murya daga can gefe — murya mai kama da iska mai kamshi, da sautin ƙaho na ruwa. Miemie ta bayyana a bakin ƙofa, hannunta na riƙe da wani guntu takarda mai ɗauke da zanen da take cewa: “Wannan shine zanen bango na ɗakin Madam Nablah. Da wannan zane za ku iya buɗe kofa zuwa tafkin da take ɓoye da Tasleem. Amma ku sani…” Ta tsaya, ta kalle su ɗaya bayan ɗaya, kafin ta ɗora: “…ba kowa zai iya tsallake wannan tafki ba. Sai wanda zuciyarsa ta tsarkaka, kuma ba shi da wata niyya sai ceton gaskiya.” Amaar ya karɓi zanen, ya ɗaga kai yana kallon Miemie da wani kwarjini. Ya ce: “Zan shiga. Ko da ruwa ne zai cinye ni, bazan bar Tasleem cikin wannan mummunan kulle ba.” Shaprees cikin zurfin tunani ya ce: “Zan raka ka.” Ya kalli Asmeen. “Zan dawo gare ki, da alkawarin cewa wannan karon — ni ne wanda zan kareki, da yaron dake cikin ki ...." Asmeen ta ce: “Idan za ku shiga wannan tafkin, ku sani cewa soyayya ce zata tseratar da ku. Ba ƙarfin tsafi ba.” A cikin dare mai duhu da iska mai ƙamshi, suka fara shirin shiga ɗakin Madam Nablah a ɓoye, domin neman ƙofar ɓoyayyen tafki. Amma Madam Nablah… ta riga ta fara jin motsin shirin su — kuma ta shirya musu wata ƙulli da bazata bar rai ya dawo da sauƙi ba ..… *💋HASKEN RUHI💋* *🫀THE LIGHT OF THE SOUL🫀* It conveys a deep and spiritual meaning referring to the inner light, truth, or purity within a person. *WhatsApp 09065443871* *🌹 ASMEETAH WRITER 🌹* *BOOK TWO__________PAID_____₦300* Page 9 to 10 Madam Nablah duk tasan shirin su Amaar akan zuwa neman Tasleem hakan yasa ta toshe duk wata kafa na fita daga gidan, hanyar da zai sadasu da ɗakinta balle su samu hanya ta toshe nan ma, ko ta ina ta kafa ta tsare, da haka har suka haƙura, yanzu hanyar fita daga gidan ma ta gagare su, ba mai shigowa sannan babu mai fita..... ★★★★★ A cikin ɗakin ruwa mai kariya daga Miemie, Nasreen ta kammala shafa ruwa a fuskarta, tana sanye da wani riga na sanyi da Miemie ta tanada mata. Miemie ta zo ta zauna kusa da ita, tare da wani kwandon ƙamshi da ‘ya’yan itatuwa masu ruwa-ruwa. Miemie ta ce: “Zuciyarki ta fara tsarkakewa. Amma yanzu... zuciyar ki na murɗawa.” Nasreen ta lumshe ido tare da faɗin: “Ina jin Abeesh a raina. Sai dai... ba ni kaɗai ke raye a zuciyarsa ba. Kuma... wannan ciwo ne da bazan iya jurewa ba.” Miemie ta ce: “Zuciyar mace ita ce mafi ƙarfi. Duk wanda ya fasa ta, zai gamu da sakamakon da baya tsammani. Amma na gane... kina da ƙarfin da zai iya ƙara haske a gidan ku.” Nasreen ta ce: “Amma Miemie... bazan iya komawa wurin wulakanci ba. Ko auren da Allah ya halatta, idan bai zo da mutunci ba — bashi da daraja.” Miemie ta kama hannunta ta ce: “Kin girma, Nasreen. Kin gane duhu da haske. Amma kafin ki yanke hukunci na ƙarshe, zan nuna miki abu guda da zai ƙarfafa miki shawara.” Ta sa hannunta zuwa cikin ruwa. Ruwan ya fara zagayawa yana kewaya Nasreen, ta nuna mata wani gani mai kama da haske. A cikin ruwan, ta hango: Tasleem tana kuka, tana kwance a cikin wani zurfin kogi a ɗaɗdaure da igiyar sihiri mai wuta... Nasreen da sauri ta kalli Miemie tana faɗin, "a ina take? kamar itama a cikin ruwa take, kenan a hannun wa take?...." Miemie ta ce "tana cikin tafkin ruwan tsafin mahaifiyarku...." Nasreen ta ce: "Dan Allah ki taimaka mana ki dawo mun da Tasleem..." Miemie ta ce: "Bana shiga duniyar zalunci, na ƙi jinin zalunci saboda haka na haramta wa kaina shiga duniyar baƙaƙen Aljanu..." Masreen tana kuka taga an nuno mata Abul da Amaar suna zaune zaman ƙunci da damuwa, da Qur'ani a gaban su suna karantawa.... Sannan aka nuno mata Asmeen tana kwance a gado tana riƙe da cikin ta, a ya yinda Shaprees yake gefenta yana ƙoƙarin bata ruwan addu'a sakamakon ciwon cikin dake damunta.... Nasreen ta kalli Miemie sannan ta ce: "Meya samu ƴar uwata Asmeen?..." Miemie ta ce: "Juna biyu gare ta na wata biyu, kamar yanda kike ɗauke da cikin wata biyar kema...." A ruɗe Nasreen ta miƙe tare da faɗin "Meeee?..." Miemie ta ce: "Tabbas kina da ciki har na wata biyar, amma babu wanda yasan kinada shi, hatta kema sakamakon bacci mai tsawo da kika yi a hannun Mahaifiyarki, sannan itama Mahaifiyarki bata sani ba sakamakon hasken da ya ɓoye cikin, duhu baya taɓa ganin sirrin haske...." Cike da mamaki Nasreen take kallon Miemie da kuma cikinta tana shafa wa, a hankali ta furta, "menene alaƙata da sirrin haske?..." Miemie ta ce "Hasken Tasleem ke bibiyar ki domin ta sanya hannunta akan lamarin ki...." Hawaye ne yake gangaro wa daga kurmin idon Nasreen, hannunta a dafe da cikin ta... Idonta ne ya sauƙa akan Abeesh dake kwance yana kan bacci, a yayinda Catrina take kwance akan ƙirjinsa... A ruɗe Nasreen ta ja da baya tana faɗin: "Na shiga uku...." Miemie ta ce: "Ki kwantar da hankalin ki, kar kisa damuwa a ranki ko dan saboda jaririn cikin ki...." Nasreen tana kuka tana faɗin: "Abeesh yana duniyar Catrina? taya hakan zata faru? Shikenam na rasa shi kenan?..." Miemie ta ce: "Bani da ikon shiga turken su saboda doka ta haramta haske shiga sashin duhu hakanan duhu bashi da ikon shiga sashen haske......" A hankali Miemie ta rarrashi Nasreen har zuciyata ta nutsu amma ta kasa daina tunanin Abeesh.... ★★★★★ A Duniyar Aljanu... Catrina na Ƙudirin Auren Abeesh A lokacin da Catrina ta bayyana niyyarta na auren Abeesh, zuciyarta ta cika da buri da soyayya. Ta kwashe lokaci mai tsawo tana kallon yadda yake kula da Nasreen da tausayi, duk da cewa zuciyarsa ta fara faɗuwa gareta saboda tsafin da ta dasa masa a cikin ƙwaƙwalwa. Amma burinta ya fi abin duniya, domin burin ta shine ta zama uwar gida ga Abeesh ta har abada. Sai dai, da ta je ƙofar Dutsen Gwal — inda manyan shuwagabannin aljanu ke taruwa — aka dakatar da ita. Murya mai ƙarfi da girgiza daga sama ta fito daga cikin wuta Ana faɗin: "Catrina bint Bahrul Kayan, kin saɓa doka. Bil Adama ba halittar ki ba ce. Don ki aure shi, sai kin shigar da shi cikin danginmu — ya zama Aljani!" Hannu ya fito daga cikin haske mai ja, yana nuna mata hanya biyu: 1. "Ko ki manta da soyayyar Abeesh, ki koma duniyarki ta duhu." 2. "Ko kuma ki cigaba da tsare Abeesh a cikin duniyar aljanu, ki mayar da shi dumi-dumin aljani ta hanyar amfani da Ruwan Zuciyar Sarauta...." wani abu da idan mutum ya sha, sai ruhinsa ya fice ya koma sabon halitta. Ta amsa da cewa zata tsare shi domin mayar da shi halittar su na Aljan... Catrina ta juyo daga dutsen, zuciyarta cike da ɓacin rai. Amma tunaninta bai jinkirta ba. Ta fara shiryawa don mayar da Abeesh halittar Aljani... Zuciyarta ta yanke shawara: Abeesh zai kasance nata — ko da kuwa a sabon duniya ne... Catrina ta dawo daga taron shuwagabannin aljanu cike da nufin aiwatar da umarni. Ta shiga cikin wani ɗaki mai duhu da aka rufe da tabarau na zinariya da zoben tambarin Naƙsar Ruhin Dan Adam. A can, a cikin ƙwarya ta zuba Ruwan Zuciyar Sarauta, ruwa mai launin shuɗi mai haske da ke janyo ruhin mutum, yana tsarkake shi daga jinin ɗan adam har ya koma sabon halitta — Aljani mai rai da ƙarfi. "Dole ne in fara da lalata zuciyarsa gaba ɗaya," ta faɗa a hankali, tana kallon Abeesh da ke kwance akan gado... Cikin lokaci ƙanƙani ta shige duniyar mafarki ta hanyar ruwan, inda take iya sarrafa tunanin Abeesh ba tare da ya sani ba, a cikin baccin sa... Abeesh ne ya fara jin sauyi Tun daga wannan rana, Abeesh ya fara fama da mafarkai masu rikitarwa. A kowanne dare, yana ganin kansa a cikin duniya marar haske, yana tafiya a ruwan duhu, tare da wata murya mai daɗin gaske tana ƙiran sunansa: "Abeesh... zo... in nuna maka gaskiyar ka... kai ba ɗan Adam bane..." A ɓangaren Nasreen ta kasa kwantar da hankalin ta, riƙo hannun Miemie tayi tare da faɗin: "Miemie! Ina son magana da Abeesh, taya hakan zai faru?..." Miemie ta girgiza kai ta ce: "Hakan ba mai yuwa bane, domin a halin yanzu Abeesh bai farka ba amma akwai hanya guda da zaki yi magana da zuciyarsa amma sai dole Catrina idan tana kusa zata ji maganar..." Nasreen ta ce: "Ba damuwa Indai zai jiyo ni zanyi magana da shi..." Miemie ce ta ɗora hannunta akan goshin ta sannan ta ce: " Ki lumshe idanunki sannan kiyi magana tamkar kina gaban ta...." Itama Miemie lumshe idanuwanta tayi yanda zata ji tattaunawar su... A hankali Nasreen take faɗin: "Ya Abeesh, kana lafiya ne? Na lura da kai yanzu ka koma kamar wani daban, baka cikin hayyacinka...." Abeesh a cikin bacci yaji muryar Nasreen, zuciyarsa ce ta fara magana, a hankali bakinsa ya fara motsi... "Ban sani ba, Nasreen... kullum ina mafarki da wata murya... tana cewa ni ba ɗan Adam bane. Kuma yanzu... Ina jin wani abu yana girgiza ni daga ciki." Catrina tana zaune a gaban madubin ɗakin ta, daga sama take jin muryar Nasreen da kuma amsar da Abeesh yake bata, a hankali ta juyo tana kallonsa, idonsa a rufe sai bakinsa dake motsi... Nasreen ta ce: "Abeesh! Kada ka sha komai daga hannunta! Ita ba mutum bace! Ita aljana ce! Kuma tana shirin mayar da kai wani daban!"... Sai a lokacin Catrina itama tayi magana, tana faɗin: "Wannan ba hurumin ki bane, Nasreen. Na fi karfinku duka..!" Nasreen bata iya mayar mata da amsar ba sai Miemie da ta karɓi maganar ta ce: "Catrina! Kin saɓa doka. Ruhi mai tsarki ba zai shiga ƙarƙashin aljani ba — sai da izini daga Tauraron Tsarki. Ki tuba ko kuma a hallaka ruhinki har abada." Catrina jin Muryar Miemie yasa ta firgita, domin muryar ta na daban ne a cikin taurarin mata, kuma muryar ta yana tafiya da sanyi da kuma zafi...." A lokacin Catrina ta fusata nan ta ɗauki wani ruwa ta watsa akan fuskar Abeesh, ta ɗauke sauraro daga gare su, yanda baza su ji wani ƙarin bayani ba, kuma bazasu sake haɗa connection a tsakanin su da Abeesh ba.... A wannan dare mai ɗauke da duhu, Abeesh yana kwance har zuwa yanzu ba ya motsi, ba ya magana. Fuskar sa mai ɗauke da nutsuwa, kamar mai mafarki mai daɗi, amma zuciyarsa a kamamme take cikin bacci mai nauyin sihiri. Catrina tana zaune kusa da shi, tana kallonsa da idanu masu cike da raɗaɗin soyayya da nufin iko. Duk da ya kasance ba ya numfasawa kamar yadda aka saba, jikinsa yana ɗaukan ɗumi... Catrina a fili take furta: "Wannan shi ne mijina... Ko da kuwa bai taɓa faɗar hakan da bakinsa ba," ta ce, tana shafa sumar kansa. "Da zarar na gama shirye-shiryen haɗuwar jinin mu da na ruwa mai rai, zai zama cikakken Aljani – naku har abada." ★★★★ Nasreen tana zaune kan ƙaton dutse mai haske a cikin ruwan lumana. Ruwa mai sanyi yana tafasa da ƙamshi, tana kwance cikin shakatawa, amma ba kwanciyar hankali ba. A zuciyarta, tana jin wani abu yana motsawa — kamar wani abu ya tafi da wani babban sashi na rayuwarta... Ta ce: "Me yasa zuciyata ke kuka ne? Me yasa nake jin babu shi?" ★★★★★ A wani kogi mai zurfi, mai launin shuɗi da ja, Tasleem tana jingine a jikin wani bishiyar sihiri. Tsaron ruhohin tsafi suna kewaye da ita – ba ta da ikon fita, ba ta iya amfani da ikon zuciyarta ba, Tana ji a ranta cewa akwai abubuwan da suke faruwa.... A Ɓangaren Su AMMAAR... Amaar yana zaune kusa da Abul, wanda ke fama da karamin ciwon zuciya da rashin ƙarfin jiki. Basu san me ke faruwa da Tasleem ko Abeesh ba. Amma zuciyar Amaar cike take da wani abu mai nauyi – yana jin tamkar wani mai rai yana fadin: "Ka tashi! Ka yi wani abu!" Amaar ya kalli Abul ya ce: "Abul, ka tabbata baka jin wani abu?" Abul ya ce: "A'a, Ammaar. Kai kaɗai kake jin wannan ƙiran, Ni kuma zuciyata tana girgiza kamar an ɗauke wani na kusa da mu, kamar ana shirin tabka babban kuskure a tsakanin jinsi da jinsi...." A ɓangaren Asmeen kuwa tana kwance a gado, a wannan lokacin Shaprees baya nan, Madam Nablah ce take tare da ita.... Madam Nablah tana zaune a gefen ta tana shafa cikin Asmeen da take fama da ciwon ciki. Cikin nan shine ƙarfin ikon ta – shine zata yi sadaukarwa domin sabunta ikonta da rayuwar da ba ta gushewa... A cikin ranta take faɗin: "Da zarar ta haifi wannan jariri, ba wani mai iko da zai iya dakatar dani. Zan iya cinye kowace rana, da rana, da dare!" Asmeen kuwa tana shan raɗaɗi – tana jin wani murya daga cikin iska tana cewa, "Ki farka, ki gudu!" Amma ba ta iya motsawa – ruhohin tsafi sun daureta da sarka ta ruwa mai rai..... ______________________★ Dogon baccin da ya rufe zuciyar Abeesh kamar wata mai duhu ce da ta rufe duniya. Kamar ba zai tashi ba. Amma a yau, wani iska mai sanyi da ƙamshi ya mamaye ɗakin. Kyandir na kyalli suna lilo, ruwayen zinariya yana shawagi a iska. Catrina na zaune kusa da shi – cikin riga mai sheƙi da haske mai kyau fiye da na duniya. Ta kai hannunta ta shafa kuncinsa cikin natsuwa. Ta ce: "Ka farka, masoyina..." Abeesh ya buɗe idanuwansa a hankali, numfashinsa ya sauƙa kamar wanda ya dawo daga wata duniya. A hankali ya furta: "Ina... nake?" Catrina ta ce: "Kana tare dani, a duniyar da babu azaba. Na ce maka ba zan cutar da kai ba." Ya kalle ta Idonta mai ƙyalli da nutsuwa. Yana jin wani abu mai daɗi yana shige masa. Ya ce: "Kin… kasance tare da ni? Cikin wannan tsawon lokacin?"... Catrina ta ce: "Eh. Na tsare ka da soyayya, ba da sarkar wuta ba. Kuma yanzu lokaci ya yi da za ka kasance dani har abada." Abeesh ya kalli hannunsa babu rauni, babu damuwa. Amma a gefe guda, yana jin kamar wani sabon abu yana gudana cikin jijiyoyinsa. Ruwan ɗumi na hawan kansa rayuwar dan Adam tana rabuwa da shi a hankali... Ya ce: "Me kike nufi?" Ta ce: "Soyayya ta ba zata taɓa tabbata ba sai ka zama tamkar ni. Ka zama Aljani. Sai haka ne za mu yi aure cikin bin dokokin masarautar Aljanu." Abeesh ya lumshe idonsa. Zuciyarsa tana motsi. A can ƙasan zuciyarsa, wani sashi yana jayayya tare da faɗin: “Wannan ba Nasreen bace… Me zai hana na jira Nasreen?” Amma wani sashi yana ɗaga murya da cewa: “Nasreen ta bar ni... Wannan ce kawai ta tsaya tare da ni... wannan ce ke ƙaunata.” Catrina ta kama hannunsa ta ɗora akan ƙirjinta. Ta ce: "Ina sonka. Kuma zan canza ka da soyayya, ba da azaba ba." A lokacin, wani zobe na launin baƙin zinariya ya bayyana a tsakiyar tafin hannunta. Ta ɗora hannunta a saman zuciyar Abeesh. Idanunsa suka canza launi – daga fari zuwa shuɗi.... A kallo ɗaya, wani koren fure ya tsiro a gaban su. Furen aljanu – alamar an karɓi amincewa daga manyan aljanu. Catrina ta ce: "Zamu yi Aure nan da kwana uku." "Ina so." Abeesh ya amsa – cikin murya mai kauri, wanda ba irin na dā ba. Soyayya ta rufe shi, amma soyayyar da ke jujjuya ƙwaƙwalwarsa... Acan ɓangaren Nasreen... Nasreen ta zabura daga mafarkin da tayi a cikin baccin ta, hawaye na zuba take faɗin: "Ina jin shi... amma ba kamar da ba. Ya canza!" Miemie wacce ta ɓace a cikin ruwa bata ganuwa amma tana jin maganganun Nasreen, ta bata amsa da cewa: "Yanzu me kike so ayi Nasreen?...." Nasreen tana hawaye ta ce: "Ina so naje yanda Abeesh yake koda bazaki je ba..." Miemie ta ce: "Kina hauka ne Nasreen? to ko Tasleem wacce take da ƙarfin iko bazata iya cin galaba ba idan taje duniyar Aljanu..." Nasreen ta ce: "Zan yi amfani da ƙarfin zuciyata koda banida iko, bazan taɓa barin Abeesh a cikin wannan halin ba, bazan taɓa barin ya zamo Aljani ba ko dan saboda jaririn cikina...." Miemie ta ce: "Wuri ne mai hatsarin gaske Nasreen, ba lallai ki dawo da rai ba, in ma kin dawo to wata ƙil kema su iya canza ki zuwa halittar su..." Nasreen ta ce: "Inada Ayar Ubangiji, yanda Allah ya yi Ni a halittar ɗan Adam haka zan cigaba da kasancewa har ƙarshen rayuwa ta...." Miemie wacce ta bayyana lokaci guda, ta kalli Nasreen cikin tausayawa sannan ta ce: "Idan baki hanzarta ba, ana iya rasa shi har abada. Amma ki sani, shiga duniyar aljanu ba mai sauƙi ba ce. Za ki rasa wani ɓangare na kanki." Nasreen tana kuka ta ce: "Ina so! Zan bi shi! Ko da kuwa zan rasa komai!" Miemie ta ɗora hannunta a goshin Nasreen – numfashinta ya canza. Sai ga wata ƙofa ta buɗe – ƙofa mai wuta da ruwa da iska. Duniyar Catrina.... Ɓangaren Tasleem! Madam Nablah ta ɓullo mata.. Tasleem tana nan zaune, jikinta a sarkake da sarkar ruwa. Madam Nablah tana gabanta, tana karanto surorin sihiri cikin murya mai ƙarfi. Ta ce: "Zaki zauna a nan har sai ikonki ya kare. Ina buƙatar jinin Nasreen da Asmeen domin in cika ikon mallakar duniya!".. Tasleem ta kalle ta da hawaye ta ce: "Wallahi ba za ki ci nasara ba. Ko da kuwa zaki mallake duniya – ba za ki taɓa mallakar zukatan mu ba!" Madam Nablah ta murɗa wani zobe. Ruwa ya yi ƙarfi, ya lullube Tasleem gaba ɗaya, ta ƙara tsauwala tsaro, daga nan ta bar yanda take... ____________________★★ Amaar yana zaune kusa da Abul wanda ke kallon cikin wani tsohon littafi. Abul ya dago kai yana kallon Amaar.. Murya na rawa cikin damuwa ya ce: "Amaar, na ga wani abu… Abeesh yana cikin hatsari. Kuma wallahi ana shirin ɗaura masa aure da Catrina… kuma Catrina ba mutum ba ce...." Amaar ya ɗago. Zuciyarsa ta tsaya cak cikin hargitsi ya ce: "Abeesh... Aure? Catrina... ta ya ya?" Abul ya ce: "Muna da kwanaki uku. Idan har aka ɗaura auren nan, ba za mu iya dawo da shi ba har abada. Idan muka kuskura muka shiga duniyar Catrina ba da izini ba, za ta iya rufe rayukan mu." Amaar ya ce: "To ina ƙofa? Ina hanyar zuwa can! Idan har zan mutu domin in cece shi, to haka ya dace da Ni...." Abul ya ce: "Kayi hakuri Amaar, inaji a jikina na rasa Abeesh, kaima bazan so na rasaka ba, saboda haka ka bi umarni na ka zauna a yanda kake, bazan bar ka kaje duniyar Aljanu ba domin nasan babu mai dawowa da rai, mu dage da addu'a da yawan karatun Alqur'ani mai girma Allah yana sane da mu...." Amaar ya ce: "Shikenam ba komai Abul..." ---★ A lokacin da Catrina ke shirin sa zoben aurenta a yatsan Abeesh, wani ihu mai ƙarfi ya karaɗe filin wurin... "KAR A YI AUREN NAN!!!" Wani haske mai ƙyalli ya faɗo daga sama. Nasreen ta bayyana cikin ruwan zinariya da numfashi mai ƙarfi. Idonta na zubda hawaye, zuciyarta na huci ta ce: "Ya Abeesh, kar ka manta da ni! Ina ƙaunarka! Wannan ba kai ba ne!" Abeesh ya tsaya... Hannunsa ya yi sanyi... Zoben ya faɗi ƙasa.... Abeesh ya kalli Nasreen da idanuwansa masu shuɗi kamar ruwa mai duhu. Muryarsa ba kamar ta dan Adam ba, tana fito da wata murya mai cakudadden sauti – tsakanin namiji da aljani. Cike da tsana ya ce: "Wa ke ƙirana da suna da ba zan iya tuna shi ba? Wace ke mana cikas da auren da zai cika ni da iko?" Nasreen ta sunkuyar da kanta, hawaye duk ya wanke mata fuska ganin halin da Abeesh yake amma zuciyarta na cika da ƙarfin hali. Ta kalle shi sannan ta ce: "Ni ce Nasreen! Ka tuna ni! Ni ce matar ka wadda ta so ka kafin Catrina ta ɓatar da kai, sannan ina ɗauke da cikin ka a jikina...!" Kafin ta iya ƙara wani kalma, Abeesh ya kai hannu ɗaya, ya kamota tare da shaƙo mata wuya, ya ɗagota sama, yana sakin wani irin numfashi mai ƙarfi, ya ce: "Ke ba komai ba ce sai cikas! Cikin ki ba ni na yi ba – karya kike!" Aljanun wurin sun zuba musu ido. Amma babu wanda ya kuskura ya motsa. Dokar manyan Aljanu ta hana shisshigi. Nasreen tana riƙe da wuyanta, tana hawaye da numfashi mai wahalar fitarwa Abeesh ya cilla ta gefe kamar mataccen ganye. Ta buge da ƙasa da ƙarfi, jiki na karkarwa.... Catrina ta matso da murmushinta mai cike da mugunta. Ta zaro zoben aurenta, tana kallon Abeesh tare da k'yafta ido ta ce: "Zamuyi aure yanzu, masoyi..." Sai dai kafin ta sa zoben a yatsan Abeesh, Nasreen cikin ƙarfin hali ta taso da ƙarfi ta buga hannun Catrina, zoben ya tashi sama, ya faɗi ƙasa, ya narke cikin wata hoda ta zinariya... "BA ZA A ƊAURA AURE BA!" Ta yi maganar da ƙarfi.... Wani guguwa ta taso ruwan wuta da kukan duhu suka gauraya. Catrina ta yi wani irin ihu cikin tsawa ta ce: "Kin cutar da ni! Ya isa haka!" Abeesh cikin fushi ya juyo. Idanunsa na haske da wuta. Ya nufo Nasreen, ya kai mata wani irin matsanancin naushi a cikinta, haka ta fara jin ƙugu-gugu!... A fusace ya ce: "ME KIKAYI MIN!? WACE CE KE!?" Nasreen juyi kawai take tana birgima ga wani irin kukan da take na fitar hayyaci da tsantsar ciwo da cikinta ke yi, a wannan lokacin jini ne ya ɓalle mata yana zuba kamar magudana. An daɗe ba a taɓa ganin mace ta fuskanci azaba irin haka a duniya da aljanu ba.. Murya ciki Nasreen take faɗin: "Wayyo Allah na…wannan wani irin ƙaddara ce?" ta furta a wahalai... Catrina ta matso kusa da Abeesh, tana kokarin rungume shi. Amma idanunsa suka nuna ba a cikin hankalinsa yake ba. Ya kama kansa – yana fitar da wani murya kamar na mahaukaci... Gaba ɗaya jikin Nasreen ya jiƙe da jini, zuciyarta na dukan ƙarshe-ƙarshe. Hankali ya gushe mata. Ta kasa miƙewa, ta kasa magana. Tana kallon Abeesh cikin tausayawa, wanda yanzu ya canza gaba ɗaya, kamar wani halitta daga ɗayan duniya. A hankali take furta: "Ni nake ƙaunarka… wacce ka aura… ka ce zaka zauna da ni har abada..." Amma Abeesh ko kaɗan bai saurareta ba. Idanunsa masu shuɗi suna cike da ƙiyayya. Bai nuna tausayin komai ba. Sai da ya matsa kusa da ita, ya durƙusa kamar zai taimaka mata… sai kawai ya sake naushinta a cikinta yana faɗin: "Ki mutu! Kin kawo tsaiko ga zubin Aljanu da bil’adama! Catrina ita ce rayuwata yanzu!".. Nasreen birgima tayi gefe tana murtsukuku Jinin da ke fita daga gabanta ya ƙara yawanta, Sai dai hakan bai ƙare ba. Catrina ta matso daidai lokacin da Nasreen ke ƙoƙarin numfasawa da ƙyar... Tana sanye da farar rigar aljanu, idanunta suna kyalli da murɗaƙen tsafi ta ce: "Kin cuci zuciyata sau ɗaya, Nasreen. Amma yanzu sai ki ji hukuncin da duk mai tsallake Aljani ke fuskanta!" Ta ɗaga hannunta. Wani murɗaɗɗen ƙaho na wuta ya bayyana. Ta ɗaga shi, ta bugawa Nasreen a kirji da shi. Wani irin gigitaccen ihu marar misaltuwa ya fito daga bakinta. Jikinta ba ƙaramin girgiza ya yi ba, Wata murya daga cikin sararin duniyar ta ce: "Wannan bil’adamar zata mutu kafin safe, ta kar ya dokan jinsi, ta shigo duniyar mu bada izinin mu ba...." Catrina ta sunkuya tana kallonta da murmushi ta ce: "Kina so ki ceci Abeesh? to wannan zoben shi zai dakatar da Auren nan ta hanyar salwanta, kuma ga shi a hannu ba, tashi ki karɓa idan har kina da ikon dakatar wa...." Nasreen ta kasa amsawa saboda tsananin azabar da take sha, Amma cikin zuciyarta, ta fara jin cewa ta kusan mutuwa, Ta yi juyayi sosai. Haka take jin wani abu tsoka-tsoka yana faɗowa daga marar ta... Zubar cikin da ta fara yana ƙaruwa, ɗaya daga cikin manyan Aljanun da ke tsaye ya furta da karfi: "Doka zata fara aiki akan wannan halitta, ku ɗauke ta kuje ku kwantar da ita akan tabarmar ƙaya na wuta, daga nan har ta ƙara sa mutuwa...su kuma ma'aurata su zauna akan shiri domin yanzu za'a ɗaura Auren..." Abeesh ya fuskanci Catrina yana faɗin: "Zan so ki har abada, Catrina." Catrina ta ce: "Zan ba ka iko, Abeesh. Amma za ka sadaukar da komai." Abeesh ya ce: "Na riga na rasa komai." Abeesh ya ɗauki zoben, ya saka a hannunta. Aljanun suka danna ƙara a sama na farin ciki kafin a ɗaura auren gaba ɗaya…domin sai itama ta saka masa zoben kafin Auren ya ƙullu.... Catrina ɗago da nata zoben tayi tana sakin ƙayataccen murmushi zata saka masa a yatsa shima... Duk wannan abun ya faru akan idon Nasreen da take kwance kafin a ɗago da ita, domin Catrina ta sanar cewa a barta tana so a ɗaura Auren akan idonta... Wani irin ƙarfin zuciya ne ya wanzu a jikin Nasreen, a ruɗe ta miƙe ta yo kan su tana jan ƙafa ga yanda jini ya ɓata mata duk ilahirin jikinta, kafin su ankara da ita Nasreen ta fizge zoben hannun Catrina da take ƙoƙarin sanyawa Abeesh.... tana karɓan zoben ta jefa a bakinta ta haɗiye zoben tana kuka... Catrina kamar wata mahaukaciya haka ta zabga uban ihu ganin Nasreen ta haɗiye mata zoben da ta sha wahala kafin ta samo shi... Nasreen tana tsaye lokaci guda ta fara hawayen jini, jini na fita ta bakinta tana murmushi ta ce: "Meye amfanin zuwa na in har bazan iya dakatar da Auren ba? ko yanzu na mutu nasan naci galaba akan ki, na tarwatsa Auren da ƙarfin zuciyata bada ƙarfin iko ba, na karanci littafin ku nasan mahimmancin zoben Auren ku, sau ɗaya kuke mallakar zoben Aure idan ku ka rasa shi shikenam babu Aure har abada.... Catrina! Idan kina son Aure to ki cire zoben hannun Abeesh kiyi amfani da shi wurin Auren wani amma ba Abeesh ba...." Catrina ce ta taho da gudu tare da ɗaga Nasreen sama ta doka ta a ƙasi, ta haura saman cikinta ta fara tsalle tana faɗin: "Kin cuce ni Nasreen! har yaushe zaki barni na huta ne? to kamar yanda kika dakatar da Auren sai naga yanda zaki rabani da Abeesh, kuma bazai taɓa komawa jinsin mutane ba...." Haka Catrina take surutai tana tattaka cikin Nasreen... Nasreen gaba ɗaya ta fita hayyacinta, jini ne yake fita ta ko ina a jikinta, baki da hanci da hawayen jini da jini ta farji gaba ɗaya ya mamaye ta, jini ne yake kwaranya a ƙasin ƙafafun ta still idonta akan Abeesh wanda ya rasa wani irin hukunci zaiyi mata na lalata masa Aure da tayi.... Catrina tsabar baƙin ciki fashewa tayi da kuka ta sauƙa akan Nasreen, da gudu ta bar wurin tana ihu, Abeesh ne ya zo yanda Nasreen take tare da durƙusawa a gabanta yasa hannu ya damƙo sumar gashin ta ya ɗago ta, yana mata wani irin kallo da idanuwansa masu launin shuɗi... Nasreen tsabar taurin zuciya haka tasa hannu ta cakumo gaban rigar Abeesh hannu na kakkarwa, ta rungume shi sannan ta kafa goshinta akan nasa tana gogawa, duk ta ɓata masa kaya da jini, sai cakumarsa take lips ɗin ta na ɓari kamar wacce tayi wanka da ruwan ƙanƙara... Abeesh lumshe idanuwansa ya yi kamar wanda aka hana shi ture ta, Nasreen kwantar da kanta tayi akan ƙirjinsa daga nan numfashin ta ya tsaya, ta tayi doguwar suma.... Abeesh jin bata motsi yasa ya hankaɗata ta yi baya ta faɗi, ya miƙe tsaye tare da barin wurin ya nufi yanda masoyiyarsa take wato Catrina..... Manyan Aljanu ne suka bada umarnin aje a jefa Nasreen cikin ɗakin duhu na tsaro, yanda ake ajiye Aljanu masu laifi..... __________________★★★ Ɓangaren Amaar da Abul... Amaar ya shirya tafiya don neman yanda Tasleem take... Abul yana tsaye a gaban littafin hasken ruhi, wanda ya buɗe da karfin addu’a, sannan wani madubi mai sihiri ya bayyana a tsakiyar ɗaki. Wani haske mai kyalli yana fito wa daga cikin madubin, yana buga cikin zuciyar Amaar da ke tsaye a gefe, yana shirin fita da niyyar neman Tasleem... Abul ya ce: “Ka je da karfin zuciyarka, ka dawo da ita... Allah ya bada nasara.” Amaar ya amsa da Amiin Sai kawai ya shiga cikin hasken kamar wanda aka janye shi ciki, yana shiga madubin ya ɓace. Littafin ya rufe da ƙarfi kamar bai taɓa buɗuwa ba. Abul ya tsaya da kuka a idanunsa yana masa addu'a da fatan nasara... --- Amaar A Dajin Tsafi Amaar ya buɗe idanunsa a wani wurin da ya kasa fahimta. Tsohon daji ne mai haɗari ga Itatuwa jajaye kamar jini. Ganyayen da ke kwance a ƙasa suna ƙamshi irin na sihiri, ga wani ƙawataccen ruwa a zagaye da duhu da walkiya yana yawo a gefe. Amaar da ƙarfi ya furta: “Tasleem!!!” “Tasleeeeeem!!!” Amaar ya ci gaba da ihu da karfin zuciya. Muryarsa na rabuwa gida biyu, kamar tana fita daga sama da ƙasa lokaci guda. Amma babu amsa... A cikin ruwan tsafi, Tasleem tana kwance. Idanunta a rufe, tana shan azabar ruhi da rikicin zuciya, kamar mafarki take jin muryar Amaar tana ƙira. A ruɗe Tasleem ta ɗago tana faɗin: “Ya Amaar... Ya Amaar, ina nan! Ka zo gare ni, don Allah ka zo!” Ta fara kuka. Hawaye na gangarowa daga fuskarta yana gauraye da ruwan da ke kewaye da ita. Amma Amaar…baya jin sautin muryar ta.. Ya ce: “Inda kike, ki bani alamar ki... na zo nemanki ne...!” Ganin ba wata alama ne yasa ya durƙusa tare da dafe hannayensa a ƙasa. Zuciyarsa na bugawa da rashin ƙarfi. A gefe, wani haske a cikin ruwan ya fara kyalli, kamar yana amsa zuciyar Amaar.... Miƙewa ya yi yana cigaba da dube-dube domin Abul ya sanar masa cewa a wannan yanki take... Amaar yana ta yawo cikin dajin sihiri, zuciyarsa na masa zafi da fargaba. cikin sa'a sai idonsa ya sauƙa akan wani sashen ruwa da ke haskakawa da launin zinariya da kumfa masu walƙiya. Haske mai kama da fuskar Tasleem ya bayyana a cikin ruwan. Amaar cikin farin ciki ya furta: “Tasleem! Na ganki… Na sameki! Ina zuwa!” Cikin gudu da ƙauna, Amaar ya nufo wurin ruwan. Amma kafin ya kai… ZAP! Wata irin ƙara mai sanyi ta buga masa kirji. Mashi mai baƙin sihiri ne ya caka masa cikin ƙirjin zuciyarsa. “ARRRGHHHHHH!!!” Wani irin ihu ya yi tare da faɗu wa ƙasi yana riƙe da kirji... Daga cikin duhun dajin, wata annura mai duhu ta bayyana. Cikin iska ta bayyana Madam Nablah ce sanye da baƙaken kaya, tana tafiya a hankali. Idanunta na ci da wuta ja kamar goran wuta. Madam Nablah cikin ƙarfin sihiri ta ce: “Me kake tunani? Za ka iya kubutar da ƴata daga hannuna? Kai yaro mai ruhi, wani irin shirme kake haka ..?” Amaar yana yunkurin miƙewa, amma jikinsa na girgiza cikin ruɗani ya ce: “Ba zan bari ki cutar da Tasleem ba… ko da kuwa zan mutu.” Madam Nablah ta yi tsaki, ta ɗaga hannunta, hasken sihiri ya shiga zagaye shi... Tasleem, wacce ke kwance cikin ruwan tsafi, ta ji ihun Amaar yana karaɗe wurin. Sai ta taso da karfi cikin tashin hankali, idonta cike da hawaye take faɗin: “Ya Amaar! Ya Amaar!! Ki bar shi! Don Allah Mommy! Kar ki cutar da shi!” Amma ruwan yana hana muryarta fita...duk ɗaga muryar da take a iya yanda take muryar take tsayawa.. Ta fara cukuikuya ruwan tana ƙoƙarin fita, amma ruwan yana tura ta baya kamar tsohon azzalumi... ★ Amaar yana ƙoƙarin tashi daga ƙasa, yana jan numfashi, amma mashin tsafi da ke kirjinsa yana sosa rayuwarsa Madam Nablah ta taka kusa da shi, ta dafa kansa da hannunta mai wuta, sai ta furta: “Zan fitar da hasken ruhi daga gareka, ka zo da ƙafa zuwa ga halaka.” Tana faɗar haka, wani baƙin hayaƙi ya fara fita daga jikin Amaar. Madam Nablah ta tsaya a gaban Amaar hannayenta a buɗe, tana busar ƙarshe na sihiri daga cikin bakinta. Wani haske ne ya bar kirjin Amaar, ya shige cikin tafin hannunta. Nan take... Amaar ya faɗi ƙasa – babu motsi, jijiyoyi sun daina gudu, idanuwansa sun rufe, jikin sa ya rame kamar an tsotsa jini... Madam Nablah cikin annashuwa ta ce: “Hasken ruhi ya fita daga gare ka, yaron banza....ke kuma sai ki yi kuka da mutuwarsa, kar ki daina har abada.” Ta saki wata ƙara mai cin kunne kafin ta ɓace cikin duhun daji kamar ba a taɓa ganinta ba... Amaar ya bar duniya gangan jikinsa yanzu taɓo ne bushasshe, mashin tsafi yana kwance a zuciyarsa, rayuwa ta gushe daga jikinsa. --- A Cikin Ruwan Tsafi: Tasleem tana can cikin ruwan tsafi, jikinta yana ɓari amma sannu a hankali ta fara jin wani yankakken sarkar tsafi da ke rataye a wuyan ta yana motsi.. Idanunta sun ci karo da wani kaɗan daga cikin hasken Amaar wanda bai shiga hannun Madam Nablah ba yana shawagi cikin iska sama da ruwan. Tasleem cikin kuka ta furta: “Ya Amaar... ka tafi? Ka bar ni?” Nan take hankalinta ya rikiɗe. Sai ta tsayar da kuka, ta fara karanta addu’o’i da wani salon karatun ruhi da Abul ya koya mata kwanakin baya. Tana faɗin: “Haske ya fi duhu. Ruhin da ya tsira zai iya dawowa. Idan zuciyata ta ƙira shi... zai ji ni!” Sai ruwan tsafi ya fara birkicewa, yana ƙara yin harzuƙa Wani ƙaramin zobe da ke ƙasan ruwan ya bayyana... zoben da Amaar ya taɓa bata a ranar da suka kasance don gudanar da ƙaunar su... Ta kamo zoben da hannunta ya na rawa, ta ɗaga sama, tana ɗaga hannunta cikin addu’a da kuka da ƙarfi: Tasleem cikin karfin murya da hawaye take faɗin: “Ya Ubangiji, kada ka bar shi haka! Idan akwai rabon rayuwarmu, ka dawo da shi… har ya ji sunana.” A daidai lokacin, haske mai launin azurfa ya fito daga cikin zoben, ya nufi cikin sararin sama. --- Jikin Amaar na kwance a ƙasa — kamar gawa. Sai wani haske mai launin azurfa ya sauƙo da sauri daga sama… Ya lulluɓe gaban kirjin Amaar, inda mashin tsafi ke nan... An fara jin dankarewar numfashi, wani ƙaramin amfani ya motsa a gefen leɓensa... Tasleem ta tsallake ruwan tsafi da ikon Ubangiji da ƙarfin hasken da ke cikinta. Ta tarwatsa ruwan da hannayenta, jikinta yana rawa, zuciyarta cike da firgici da fargaba. Bayan ta fito, ta gan shi a hankali ta furta... "Amaar...." Jikinsa na kwance kamar gawa, babu numfashi, fuskarsa cike da dumin mutuwa. Tasleem cikin murya mai sosa rai ta ce: “Ya Amaar... don Allah ka tashi... ka tashi ka kalle ni!” Ta rungume shi tana kuka sosai, ta ɗora hannunta akan mashin da ke tsakiyar ƙirjinsa, tana kuka Tana ƙoƙarin tura hasken ta cikin zuciyarsa, amma hasken nata na koma baya, kamar ana ƙin karɓa. Cikin kuka ta ce: “Ka tashi, don Allah... kai ne fa, kai ne ka ce zaka ƙare min rayuwa da tsaro… ka ce zaka tsaya min!” Amma jikin Amaar bai motsa ba. Komai yayi shiru. Nan da nan wani haske ya bayyana a sararin dajin, yana sauƙowa da nutsuwa da annuri. Wani ruhin tsarki ya bayyana daga cikin hasken, yana ɗauke da wata jita mai launin azurfa, kafaɗunsa na walkiya, idonsa cike da kwanciyar hankali da lafazi mai daɗi ya ce: “Kuka ba zai yi tasiri a nan ba, 'yar haske. Amma wannan—” Ya miƙa jitar sauti gare ta ya cigaba da cewa “—ki raira kiɗan ruhinsa. Wannan sauti zai ƙira shi daga duhun da ya shiga. Amma dole ne ki daure. Zai ɗauki lokaci, kuma bazai yi sauƙi ba a cikin ƙankanin lokaci....” Tasleem ta karɓi jitar, tana kallon ta da hawayen fatan alheri. Sai ruhin ya ɓace, hasken ya lafa. Dajin ya koma shiru. Ta zauna kusa da Amaar, ta haɗa hannayenta a kan jitar, ta lumshe ido tana nufin zuciyarsa da soyayya. Sai ta fara kaɗa jitar da yatsun ta cikin sautin da ba’a taɓa ji ba — kukan tsantsar soyayya da ɓacin zuciyar rashin masoyi. Sautin ya shiga iska, yana shawagi, yana girgiza ciyayi, yana bugawa a cikin duhun dajin... Duk lokacin da ta buga jitar, cikin Amaar na ɗan motsi, amma bai tashi ba. Tasleem cikin murya mai rauni ta ce: “Ina raye ne saboda kai, Ya Amaar… bana so ka tafi… ka dawo gare ni.....” Ta ci gaba da bugawa... duhu ne ya fara mamaye wurin... kuma Tasleem bata fasa ba. *GA MASU SON CIGABAN BOOK A TUNTUƁENI A WANNAN NUMBER 09065443871...* *MASU SON TURO KUƊIN LITTAFIN SU GA ACCOUNT NUMBER 9065443871 ASMA'U MUHAMMAD AUWAL. OPAY BANK....* *GA MASU SON TURA KATIN WAYA GA NUMBER 09065443871 MTN OR 07087352025 ZAIN....* FATAN NASARA 🙏🙏🙏🙏 Kyautar page ya ƙare sai a daure a biya kudin cigaba ... Nagode sosai 🙏 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels